Follow us on social media
Showing 57001 words to 60000 words out of 148866 words
Chapter 20 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
mata miji. Na yiwa yarinya ta miji, aurenta saura wata biyu da kwanaki."
Ya ce yana miƙewa tsaye, da yasan abun da ke tafe da su ba zai ɓata lokacin shi ba.
"Hakane?"
Alhaji Tafida yace cikin ɓacin ran game da halin da Alhaji Mamman ya fara nuna musu.
"Eh ko da akwai wani abun? Na ga dai ƴa tawa ce, to na mata miji."
Col. Ahmad da yake kallon Alhaji Mamman cike da baƙin cikin wulakanci da cin fuska da yake neman yi wa iyayenshi sai lokacin yayi ƙoƙarin saka baki yace.
"Amma Baba ba muyi haka da ita ba."
Wani kallon banza ya watsa masa.
"To yanzu ka sani."
Col. Ahmad zai kuma magana Alhaji Tafida ya miƙe.
"Kar ka sake magan Ahmad tashi mu tafi."
Babu musu suka miƙe ko damar mishi sallama ba suyi ba dan ya zubar da ƙimar shi a idonsu suka fice. Shima ya kaɗa babban rigarshi ya fita.
Suna tafe kowa yayi shuru suna jajanta abin da Alhaji Mamman ya aikata musu babu wanda ya sako Ahmad da yayi shuru yana jinsu sai tuƙi yake zuciyarshi yana cike da baƙin ciki da tunanin da kyar in Nuratu tana da labarin abin da mahaifinta ke shirin aikata mata, in ba haka ba da ta sanar da shi.
"Ahmad ka ji abin da ya faru ko, sai ka janye niyar ka, ka hakura, dan ba zan sake taka kafana in je gurin wannan marar mutuncin in nema maka auren ƴarshi ba. Haba no wonder ƴar ta zama marar yanci mana, ban da girman mace abin da gado wajen uba."
"Abba bata da labari."
Col. Ahmad yace cikin sanyin murya.
Abba ya buga tsaki.
"Sai kuma kayi ta yi."
Shuru yayi yaja bakinsa kawai yaci gaba da tuƙi burinsa ya samu zama ya ƙira Nuratu suyi magana.
***
Washegarin ranar asabar haka kawai Nuratu tun daren take jin bugun zuciyarta ya ƙaru, har Mami ta sanarwa tace tayi ta addu'a inshaAllah alheri ke tunkaro ta kar ta saka damuwa. A cikin zuciyar Mami kuma duk ta saka abin ne a matsayin zuwan Mufid ne.
Kamar ƙarfe uku tana kwance cikin falon taƙi fita tun safe tun bayan ta gama ayyukan ta, Munirat ta wuce islamiyya daga ita sai Mami.
Cikin muryar da basu taɓa tsammani ba ko manta mamallakin murya ba ya shigo cikin gidan kai tsaye zuwa falon bai nemi umarnin shiga ba yana kwalawa Mami ƙira.
"Sadiya! Ke Sadiya."
Mami da ke kokarin shiga ɗaki jin muryar shi ya bata mamaki ta dawo baya ta ganshi tsaye kyan a tsakar falon yana bi da kallo har idanuwansa suka sauƙa saman kan Nuratu da ta tashi zaune tana bin wanda ake ƙira da mahaifinta da ido ba wai dan bata taɓa kallonshi ba sai dan halinshi da ya kasa canzawa.
"Lafiya?"
Mami ta ce ta dawo cikin falon tana haɗa rai dan jin yau kuma da mai ya zo mata.
Nuratu da ke zaune ta saka musu ido tana kallo. Yatsa ya nuna mata kar zai saka cikin indanuwanta in da tana kusa dashi.
"Wato ke kin girma kin san aure ko? Har ni zaki turawa mutane su je nema miki auren ɗan su, to ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau. Ni Alhaji Mamman Bashir a matsayina na mahaifin ki na zaɓa miki mijin aure dai-dai da ke. Ba kowa bane sai wanda ya fara lalata ki wato Mufid. Ke kuma Sadiya dan munafurci har da ke za'a haɗa baki ko? To ki fara shiri dan da Walida zan haɗa ayi auren rana ɗaya."
Murmushin taƙaici Mami ta yi kafin ta haɗa rai.
"Kar ka kai ni bango Alhaji Mamman. Ina ganin darajar ka har yanzu albarkacin ƴaƴa."
"Kar ki gani Sadiya ki fito ki sanar da ni meke ranki."
Tsayuwarta ta gyara tana fuskantar shi.
"Mamman ka taɓa kallon Nuratu a matsayin ƴarka ƴar da ka haifa kamar sauran, ko ka taɓa ɗaukar nauyinta ko sauƙe haƙƙinta a matsayin ka na mahaifinta, baka taɓa nunawa ka santa ba tun kafin haihuwar ta har zuwa yanzu, dan haka ka fita harkar ƴata bata buƙatar ka a rayuwarta da har za ka zama wani abu balle ubanta. Maganar aure kuma in ka fasa to wallahi shari'a ce zata rabamu."
Dariya ya kwashe da shi yana mamakin ƙarfin halin Mami.
"Haka kika ce? To mu zuba. In shari'a ce ke zaki wahala domin aure tamkar an yi an gama."
Daga haka ya juya ya fice a fusace. Da sauri Mami ta koma ɗakinta tana ɓoye hawayenta kar Nuratu ta gani. Nuratu da ke zaune dafe da kanta ruwan hawaye ya kasa daina zuba a idanuwanta.
Duniyarta da rayuwarta babu komai sai baƙin ciki da damuwa, daga wannan sai wannan.
Jin taɓa ƙofar ɗakin Mami ya sata ɗago kanta ta kai kallonta ƙofar. Tura ƙofar ɗakin tayi tana shiga.
"Ki koma ina buƙatar hutu."
Mami tace da ta juya mata baya tana sharan hawaye. Ƙi Nuratu tayi ta lallaɓa ta rumgumeta ta baya ta ɗaura kanta saman gadon bayanta taci gaba da kukanta.
Shuru dukkansu su kayi kowa yana zubar da hawaye, bayan Nuratu tayi mai isarta ta sako tambayar da kullum yana damun ranta da Mami ta kasa sanar da ita gaskiya.
"Mami mai nayi wa Abba? Ya tsane ni, baya so na, ya hana ni zuwa gidanshi, baya mini komai a matsayina na ƴarshi baya sauke haƙƙina dake kanshi, yanzu kuma yazo yace zai haɗa ni aure da Mufid. Mami ki taimaka ki sanar da ni menene ko zuciyata za ta samu nutsuwa duk da banga ranar nutsuwa a tare da ita ba."
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 30.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Mahaifinki ya tsane ki ne Nuratu bisa wani canfi nasa can da ya yarda da shi. Ni da Alhaji Mamman auren soyayya mu kayi har Allah ya bamu Rahma, Hasiya, Muhsin da Rukayya. Ina da cikin ki wata biyar mahaifinki ya fara samu ƙaddara cikin dukiyar shi da ya kasa yarda da hakan cewa komai daga Allah ne ya nemi aka masa duba aka sanar da shi cewa cikin jikina ne in bai rabu da shi ba to ƙarayar arziki yanzu ya fara.
Duk yanda na so ganar da shi yaƙi yarda, ya so a zubar da cikin ki na ƙi daga ƙarshe ya jawo rabuwar auren mu.
Bayan haihuwar ki ya dawo akan mu mai da aurenmu akan mu kai ki gidan marayu ko Nijar wajen Yaya Muhammadu na ƙi amincewa. Daga nan na ci gaba da kula da ke har zuwa yanzu. Kin ji dalilin da yasa mahaifinki baya son ki raɓe shi, gani yake farar ƙafa ne da ke."
Kuka kawai Nuratu take jin bayanin Mami, rayuwarta daga wannan sai wannan.
'Ya ake so tayi?'
Ba ta san maganar zuciyarta ya fito fili ba sai da taji Mami tace.
"Ki ɗauki ƙaddarar ki inshaAllah za ki ga sakamako mai kyau."
Sai a sannan Nuratu ta ɗago ido fuska shaɓe shaɓe da hawaye tayi murmushi mai ciwo.
"Mami na jima da rumgumar ƙaddarar rayuwata, tun ban kai haka ba nake fuskantar yanayin rayuwa har zuwa yanzu. Shin sai yaushe zan ji daɗin rayuwa tamkar sauran mutane?"
"Za ki ji Insha Allah Nuratu, Allah yana tare da ke."
Kai ta ɗaga ta yarda ta amince jarabawa ce daga Allah duk abin da ya sameta.
"Mami kina ganin zai aikata abin da ya faɗa. Mami zai iya aura min Mufid, Mami ki taimaka mini in gujewa auren Mufid, Mami na tsaneshi, tsoron shi nake ji."
Hannunta Mami ta kamo murmushi mai ciwo take yi.
"Alhaji Mamman zai iya aikata duk abin da ya faɗa, sai dai kar ki damu domin wannan lokacin shari'a ce zai raba mu, sai in da ƙarfina ya ƙare."
Girgiza kai Nuratu tayi wani hawayen na zuba bisa kumatunta.
"Mami shari'a? Shari'a ba zai yi magani ba, shari'a bata aiki a zamanin yanzu musamman in sun haɗu da marasa tsoron Allah. Mami zan yi nisa da garin nan da ƙasar nan, zan yi nisa da kowa in kafa sabuwar rayuwa ko zan samu kwanciyar hankali. Ki nema min mafita."
Shuru ɗakin ya ɗauka Mami tana juya maganganun Nuratu, tabbas in har Alhaji Mamman ya faɗi abu to zai aikatawa musamman akan kuɗi dan bata da shakka wani abun Alhaji Kashim ya masa.
"Za ki iya rayuwar ƙauye?"
Mami ta tambayi Nuratu da itama tunani ta take.
Kallon Mami tayi tana neman ƙarin bayani.
"Za ki iya rayuwar ƙauye, in har za ki iya ki shirya gobe in tura ki can Nijar wajen Yaya Muhammadu ki zauna mu gani zuwa wani lokaci, zan ƙira shi in sanar da shi komai na san shi kanshi ba zai yarda da abin da Alhaji Mamman ya faɗa ba."
"Zan iya Mami, zan tafi wallahi."
Nuratu tace da sauri ko ba komai za ta gujewa auren Mufid da kowa da yake shiga rayuwarta ko zata samu kwanciyar hankali.
"Shikenan ki shirya kayan ki gobe sai ki tafi."
Kai Nuratu ta ɗaga tana tashi ta fita, ji tayi damuwarta rabi ya kau ta san dai duk tsiya in bata nan ba za su ɗaura mata aure da mutumin da tafi tsana a duniya ba, wanda ya ɓata mata rayuwa ya cuceta.
***
Col. Ahmad bayan isar su yayi ta ƙiran Nuratu bata ɗauka ba har ƙarfe biyar na yamma bai sanar da kowa ba ya fita a gidan ya kama hanyar Damaturu, so yake komai cikin dare ya isa ya sameta su yi magana, shi ba ma ta kanshi yake ganin iyaye sun ƙi yarda da aurenshi da ita ya sashi jin neman aure ya fita a ranshi, dan share mata hawayenta ya sashi neman aurenta, tausayi take bashi, matsayin ƙanwa ya ɗauka ya bata tun ranar da ya fara sanin ta.
Taimakon rayuwarta kawai yake jin yake son yi ta samu ƴan ci da farin ciki tamkar kowa. Ya riga ya hakuri ya cire son auren a rayuwar shi ko duba da yadda iyayenshi basa so ya san ko anyi ba daɗi zata ji ba.
In har akwai wanda take so ta sanar da shi suyi magana ayi aurensu cikin wata ɗaya kafin kudirin mahaifinta ya cika a kanta.
Karfe bakwai ya isa hotel ya kama ya gabatar da sallar magriba kafin ya watsa ruwa yaci abinci da rabon shi dashi tun safe. Sai da ya gama ya fito ya nufi gidan su Nuratu. A waje yayi parking kafin ya shiga da sallama, babu kowa cikin gidan ya sashi nufan falon tare da sallama.
"Kamar muryar Ahmad."
Mami tace cike da mamaki, Nuratu da ke cin abincin ta zubawa ƙofar ido.
Shi ɗin ne ya shigo cikin sallama bayan sun amsa, Nuratu ta miƙe ta bashi gurin ya zauna a ƙasa ya gaishe da Mami, tana shirin tashi ta shiga ciki dan basu guri yace.
"Mami gurin ki na zo muyi magana."
Komawa tayi ta zauna.
"Ni kuma Ahmad? Fatan dai lafiya."
Ƙanshi ƙasa ya fara mata bayani.
"Mami nayi karambani cikin rayuwar Nuratu, bayan na nemi ta sanar dani waye mahaifinta na samu iyayena da maganar son nema min aurenta, ɗazu da safe mun zo mun samu Alhaji Mamman da maganar ya sanar damu ya riga ya mata miji. Mami iya sani na da yanda Nuratu ta sanar da ni bata da wani karfaffan shaƙuwa ko alaƙa dashi tun haihuwarta. Ina tsoron Mami ya cutar da ita, kar ya aura mata wanda ba za taji daɗin rayuwa da shi ba. In har tana da wanda take so ta sanar dashi ya fito ayi maganar aurensu, in son samu ne ma a ɗaura auren kafin lokacin da ya ɗauka."
"Mufid zai aura mata ya sanar damu ɗazu."
Mami tace bayan gama sauraron bayanin Col. Ahmad.
Cike da mamaki yace.
"Mufid dai wannan yaron?"
Kai Mami ta ɗaga.
"Shi dai, gata nan yaran nan Al'ameen da Dr Awwab suna binta tana kaucewa bayan koran Dr Sadiq da tayi, ga ka kai ma. Ta sanar da kai in har akwai wanda ya kwanta mata cikin su kuyi magana da shi. In kuma babu mun riga mun yanke hukunci ni zan turata can Nijar wajen Yayana Muhammadu ta zauna zuwa wani lokaci."
Kallon Nuratu Col. Ahmad yayi dan son jin ta bakinta ta ƙara sunkuyar kanta ƙasa tace.
"Ni babu wanda nake so. Nijar kawai zan tafi."
"Hakan shine dai-dai Nuratu?"
Col. Ahmad ya tambayeta ta ɗaga mishi kai.
"Shikenan Mami Allah yasa haka shi yafi alheri, amma ki yi wa kan ki faɗa Nuratu, zama ba naki bane ya kamata kiyi aure a matsayin shekarun ki."
Bata ɗago ba bata amsa ba tana jinshi har ya gama ya miƙe ya musu sallama bayan Mami ta sanar da shi gobe ƙarfe goma Nuratu za ta tafi ya mata alƙawarin zai zo dan a gari zai kwana.
Bayan fitar shi Mami ta koma kanta.
"Kowa in ya tashi maganar aurenki kiyi tunani Nuratu, ba fa rayuwa za tayi ta tafiya a haka ba, dole kina buƙatar aure dan ganin kin kama mutuncin kan ki, ko dan in ga ƴaƴan ki auta na."
Rai Nuratu ta ɓata tana turo baki.
"Ni dai Mami bana so ba yanzu ba."
"Ke ki ka sani."
Mami tace ta tashi cikin jin haushi.
Tunani Nuratu ta faɗa, shigo shigo ba zurfi Col. Ahmad ya mata da sai an gama komai zai sanar da ita sai dai ta ji labarin an sanya ranar aurensu. Bata taɓa jin sonshi ba hasalima kunyarshi take ji, tana bashi girma da daraja a rayuwarta na ganin shine mutum na farko da ya fara taimaka mata a rayuwa ya kwata mata ƴancin ta, ganin babban Yaya da uba take mishi. Da bata san ta ya ya za suyi zaman aure ba balle ma bata jin zata amince da auren shi.
Bayan ta gama cin abincin ta ɗauke plate din ta kai kitchen ta wuce ɗakinta, kasancewar tana hutun sallah wanka ta yi ta saka rigar baccinta marar nauyi ta duba kayanta wanda ta haɗa ko akwai abin da ta manta ta ga babu komai ta yi addu'a ta kwanta tare da jawo wayarta.
Buɗe data tayi sakwanni suna ta shigowa wanda za ta iya buɗewa ta buɗe ta leƙa groups ɗin su ta ga hiran duk Rukayya da Walida ne sai Ameera sama sama take jefa musu baki, tana mamakin baƙin halin yarinyar.
Tana gama dubawa tana shirin sauƙa aka nuna mata alamar Dr Awwab yana online, searching ta yi ta shiga gurin sunan shi ta gani yana online sai lokacin ta tuna da ɗazu ya ƙirata bata ɗauka ba.
....
Dr Awwab kwance yake saman gadonshi wayarshi a hannu yana duba sakwannin da yayi sati bai buɗe datar ba ya ga an nuna mishi Noor tana online, saman sunanta ya hau kamar zai tura mata saƙo ya zubawa fuskar wayar ido tamkar zai hangota.
Wani mugun sonta da ƙaunarta yana fizgar zuciyarshi, yayi kewar kwayar idanuwanta da suke ɗauke da wani sihirtaccen kallo da yake son gani duk lokacin da ta watsa masa harara. Neman nutsuwar sa da numfashin sa yake, sai yayi ƙoƙarin dai-daita kan shi.
Ya san ya so Nusaiba amma Nuratu daban yake jinta, shi ya ganta yaji ta shiga ranshi da bai taɓa jin son wata sama da ita ba, yana buƙatar kasancewa kusa da ita, ya ganta ya ƙirata a matsayin matar shi amma taƙi bashi dama.
Ya ƙirata bata ɗauka ba kuma bata ƙira shi ba, gata nan a online ta kasa mishi magana, yana son mata magana baya son ta ga kamar ya takura mata.
Hakan ya sa ya hakura ya sauƙa yana ajiye wayar a gefe ya rufe idanuwanshi yana tuna every movement na su da ita.
....
Nuratu tana kallo ya sauƙa ya nuna mata last seen ɗinshi hakan ya sa itama ta sauƙa ta ajiye wayar, sai taji kwata kwata bata kyauta mishi ba zuciyarta yayi wani iri da ta kasa fahimtar menene. Addu'a tayi tun tana tunane tunane har bacci ya ɗauke ta.
Washegarin kasancewar ba sallah take ba ya sata sai karfe takwas ta farka, wanka tayi ta shirya cikin abaya da ya amshi baƙin fatar jikinta ta yane kanta da gyale, ba tayi wani kwalliya ba sai hoda da man baki da ta saka, ta jawo akwatinta babba ɗaya ta fito falon.
Breakfast tayi ta zauna jiran Col. Ahmad da ya ƙirata yana hanya. Mintuna ashirin ya iso bayan sun gaisa da Mami yace Nuratu ta fito ya kaita tasha.
Kuɗi dubu talatin Mami ta bawa Nuratu da lambar wayar Yaya Muhammadu in ta sauƙa ta ƙira shi azo ɗaukarta, Nuratu sai taji bata son tafiya ta bar Mamin ta, tun da tayi wayo basu taɓa rabuwa ba ko tayi nesa da ita ba.
Shan kwanar motarsu kawai ya gani dai-dai isowar shi garin ya nufo gidan dan kawai ya sata a idanuwanshi ko zai ji sauƙin abin da yake ji dan daren jiya bai iya baccin kirki ba tsabar tunanin da ya kwana dashi.
Sauƙa yayi a motar ya shiga cikin gidan tare da sallama Mami ta amsa cike da mamaki.
"Dr Awwab."
"Ina kwana Mami, sai ki ka ga bakon safiya."
"Laa ba komai mu shiga ciki."
Tace tana shiga falon ya bi bayanta cike da kunya, a ƙasa ya durƙusa ya gaisheta tana tambayarshi mutanen gida ya amsa da lafiya.
"Sai kuma a kayi rashin sa'a yanzu Nuratu ta bar gari."
"Gari kuma lafiya Mami?"
"Lafiya ƙalau, ina jin ma warhaka ba ta tafi ba ka ƙirata ko ka sameta a tashar mota kuyi sallama."
Bai iya jira Mami ta ƙarasa maganar ba ya miƙe.
"Bari in sameta."
Daga haka ya fita daga gidan gaba ɗaya, motarshi ya shiga ya ja tare da ƙiranta a waya yana ta ringing bata ɗauka ba ya ajiye wayar cikin jin haushi. Tuƙi kawai yake cikin sauri har ya isa cikin tashar ya fito cikin motarshi tare da wayar a hannunshi yana cigaba da ƙiranta.
Bata ɗauka ba ya fara juye juye tare da tambayar motar da zai tashi yanzu suka sanar da shi a akwai na state akwai na local government.
"Ga can mota za ta tashi saura mutum biyu."
Faɗin kwandasta yana nuna mishi wani mota yaga an rubutu Geidam local government.
Da sauri Dr Awwab ya ƙarasa wajen yana raba ido ko zai ganta. Har ya hakura zai juya ya hango Nuratu ta kifa kanta da kujeran dake gabanta, bai yarda ita bace sai da ya ƙarasa sosai ya ƙira sunanta.
*"Noor."*
Da sauri Nuratu ta ɗago kanta jin wanda take tunanin shi a zuciyarta ya ƙira sunanta, tsammanin ta duk cikin tunanin ne sai da taji ya maimaita lokacin da ya iso gurinta ta dai-dai window da take.
Kallo ɗaya ta iya mishi ta kawar da idanuwanta kamar kullum ta kasa saka idanuwanta cikin nashi, shi nashi bangaren kuma ba haka ya so ba, yayi kewarta yayi kewar ganin cikin idanuwanta kar ta mishi rowar gani.
"Mai yasa