Follow us on social media
Showing 72001 words to 75000 words out of 148866 words
Chapter 25 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
ka yi?"
"Ban sani ba Jidda."
Yace cikin ɓacin rai ta buga tsaki ta wuce ɗakinta haushin sa take ji, bata taɓa tsammani haka halinshi yake ba.
Gefe ɗaya kuma zuciyarta taji farin ciki jin Nuratu bata auri Mufid ba, duk da ta so Al'ameen ya aureta amma Allah bai yi ba.
***
"Sadiya ki riƙe ki damƙa mata hannu da hannu dukiyar tane na aure. An riga an ɗaura aurenta da Dr Awwab Allah yayi shine mijinta. Sai ranar tarewa duk lokacin da suka saka daidai ne kar suyi gaggawa."
Cike da murna Mami ta karɓi kuɗin tana kallo. Sadakin ƴar ta, ƴarta Nuratu wacce ta cire rai ga aure da zaman aure.
"Nagode Yaya Allah ya biya ka da mafificin alheri."
"Babu komai wallahi, Nuratu tamkar sauran na ɗauketa infact ma kamar ƴata take nima ubanta ne. Sai abu na ƙarshe duk abin da Mamman zai zo miki da shi kar ki kulashi ki sanar dani. Sannan ke ma ya kamata ki yiwa kan ki faɗa zama ba naki bane, tun da yarintar ki gashi har girma ya zo."
Kanta kasa ta girgiza kai da sauri.
"Yaya mun barwa yaran dai. Nagode sosai."
"A'a Sadiya kiyi dai tunani, ina da wani tsoho ma zan baki."
Jin ya maida maganar wasa ta murmusa su kayi sallama ya tafi ta koma cikin falon ta ƙira Yaya Muhammadu ta sanar da shi yadda aka yi. Yayi murna sosai yace nan da sati zai turo Nuratu tun da komai ya daidaita tace to kafin su kashe wayar ta ƙira sauran ƴaƴanta ta sanar da su an ɗaura auren Nuratu da Dr Awwab. Har lokacin ta gargadesu kar su sanar da Nuratu ba yanzu ya kamata ta sani ba suka ce to.
***
Dr Awwab bayan fitar su kayi sallama da Alhaji Abubakar ya wuce gidan Mami suka ɗauki hanyar Maiduguri.
Suna tafe Alhaji Abubakar ya sako masa tambayar da ya tsaya masa a rai.
"Awwab wai mai yake faruwa a wannan iyalin?"
Dr Awwab da yake cikin farin ciki ji yake babu mahalukin da ya kai shi farin ciki ya shafa kan shi idonshi akan titi yana jan motar yace.
"Baffa mahaifinta wannan yaron yake son aura mata kuma ɗan iska ne, to kowa baya so kuma shi ya dage sai ya aura mata shi, shi wannan yayan shi ne, shine ya dage sai an yi auren da ni."
"Allah sarki amma ya kyauta wallahi. Shi kuwa wannan wani irin uba ne."
"Baffa sai addu'a kawai."
"Hakane kam. Ai naga alaman yaron akwai iskanci a tattare dashi har uban na shi."
"Hakane."
Dr Awwab yace yaci gaba da tuƙi bai sanar dasu wanene ainihin Mufid ga rayuwar Nuratu ba, dan wannan sirrinta ne da ya kamata a rufe mata har dashi yanzu da ya zama cikon rayuwarta.
Shigar yamma lis su kayi Ummi ta tare su cikin mutumci kamar kullum bayan sun gabatar da sallah suka sanar da ita yadda a kayi.
"Allah sanya albarka da alheri."
Tace buɗan bakinta suka amsa da ameen kafin su mata sallama.
Bayan fitar su ta kalli Dr Awwab da yake shirin tashi.
"Sai ka fara shirin gyaran gida da kayan akwati."
"InshaAllah Ummi, Ikhram da Zaituna zan tura kuɗi su haɗa su taho da shi zuwa kafin nan da a saka ranar tarewar ta."
"Hakan ma ya yi."
Tace ya fita ko Hanan bai nema ba, gidan shi ya bayan yayi wanka ya daura alwala ya wuce masallaci ya yi sallar magriba ya daɗe yana addu'a da nuna godiyar shi ga Allah kafin aka gabatar da sallar isha'i yayi ya dawo ya zube cikin falon dan huta gajiya ya kunna kallo tare da ɗaukar wayar shi.
Missed call ɗin Nuratu ya tarar guda ɗaya da wanda ba za'a rasa ba, ya ƙirata.
....
Tana kwance bacci bai ɗauketa ba tana ta buga game da wayar da shi yake ɗebe mata kewa babu kallo ta samu ƙiran Dr Awwab. Zaune ta tashi dan ɗazu ta ƙira ta sanar da shi magungunan ta sun kusa ƙarewa kuma ba zata samu anan ba ya za tayi bai ɗauka ba ta hakura.
Ɗauka tayi ta saka a kunne tare da sallama taji yace.
*"Babyna."*
...
#votes.
#comments.
#share.
MADUBIN GOBE 36.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
*"Babyna."*
Dr Awwab ya furta cike da nishaɗi da farin cikin da yake shigar shi a ko wani daƙika.
Ɓangaren Nuratu kamar yana gabanta ta ɓata rai tana turo baki tace.
"Ni bana so ka daina ƙirana da wata Baby."
Yadda tayi maganar da shagwaɓe murya sai da ya saka Dr Awwab runtse idanuwansa ya buɗe, ƙasa ƙasa yace.
"Babyna kar ki sa cikin daren nan in taho ganinki."
"Ni dai dan Allah ka tsaya in faɗa maka abin da zan faɗa."
Nuratu tace cikin sauri jin muryar shi ya canza mata gaba ɗaya, da ya haddasa mata bugawar zuciya.
"Ina jinki Babyna faɗi damuwar ki."
Dr Awwab yace yana nemawa kanshi nutsuwa.
"Magunguna na za su ƙare nan da kwana biyu, kuma babu anan infact ma dai ka san kai kake kawo mini. To zai ƙare."
"Ki ce dai kinyi missing ɗina kina son gani na."
Da sauri Nuratu tace.
"Ni wallahi ba haka bane, Allah dagaske nake maka."
Murmushi yayi cike da nishaɗi yace.
"Shikenan zan aiko miki zuwa nan da kafin ya ƙare."
Shuru Nuratu tayi sai taji kamar bata kyauta mishi ba tace.
"To kai baza ka zo ba?"
"A'a ina da aikin yi."
"Shikenan sai anjima."
Tace ta zare wayar a kunnenta ta kashe tana ajiyewa a gefe. Sai ta ji bata kyauta masa ba.
...
'Yarinya ki yarda kin faɗa tarkon so.'
Dr Awwab yace yana murmushi lokacin da ta kashe wayar ya ajiye wayarshi yana mai da hankali kan laptop dake gabansa. Sai da ya gama ayyukan da zai yi ciki kafin ya runtsa.
***
DAMATURU.
Zagi da ashar Mufid kawai yake zubawa cikin falon Ummu bayan buge buge da fashe fashe da ya mata na asarar kayan falo, da kyar Daddy ya bashi hakuri da alƙawarin ƙarya ya masa zai aura masa Nuratu.
"Haba babana nace maka kar ka damu in dai yarinyar nan ne zan aura maka ita."
A harzuƙe Mufid ya daka Daddyn shi tsawa.
"Akan me? Dalla ka rufemin baki, kana gani dai ya bada aurenta a wancan tsami gayen. Wallahi sai na kashe sa."
Mufid yace yana zuƙan karan sigari na biyar kenan yana bankawa a cikin shi ko zai ji dai-dai.
Ummu da ido kawai ta zubawa uba da ɗan taƙaici kamar ya kasheta abun Mufid ya fara isarta, shaye shaye har gida gabansu, duk da ba yau suka saba kama shi ba amma yau ɗin a gabamsu suna kallo ba yanda za su hana shi.
Daddy da shima abin ya fara ci masa rai amma kwanciyar hankalin Mufid ya fi masa komai ya sashi miƙewa.
"Ka bani lokaci Mufid zan neme ka dan Allah ban da wani rigimar, kar ka janyomin wani abun ka rabu dashi. Waya sani ma ba'a ɗaura auren ba."
Daga haka ya fice Mufid yana ganin haka ya miƙe zai fita Ummu ta tare shi.
"Ina za kaje?"
"Dalla ki bani guri, in da kika aike ni."
Daga haka ya bi ta gefenta ya wuce ta matsa da sauri kar ya bigeta. A buge ya fita ya faɗa cikin motarshi ya nufi club dan neman abun da gusar masa da hankali da samar masa nutsuwa.
***
Washegarin yaran Mami su ka zo mata, Rukayya ce ta fara zuwa da ƴan biyunta da sunyi wayo sai ƙaramin cikin dake jikinta babu wanda ya sani sai ita da mijinta. Da gudu yaran su kayi kan Mami ta ɗaga su suka zauna saman cinyarta.
Mami kallo ta bi Rukayya da shi yadda tayi wani haske ga ƙiba.
"Mami wannan kallon fa?"
"Babu komai, mamakin wayon yaran yanzu nake."
Tace tana murmushi.
Ganin Mami zata sako wani zancen da sauri Rukayya ta miƙe.
"Mami mai za'a ɗaura na rana kar wannan yaran masu ci suzo su dame mu da yunwa yunwa."
"Ki ɗaura ko ma menene, ci kuma ke suka biyo."
Mami tace tana murmushi ganin ta basar da maganar.
"Uwarsu dai Aunti Hasiya."
Rukayya tace ta wuce kitchen.
Bayan sallar azahar Aunti Rahma da ƴaƴanta suka taho bayan an tashi a makaranta ta ɗauko su, Aunti Hasiya da nata yarinyar ta ɗaukota su ka wuce gidan Mami sai da ta tashi a aiki ta biya gidan.
Cikin sauri ta shiga ɗakin Nuratu ta ɗaura alwala ta fito ta samu Aunti Rahma na cirewa babynta pampers.
"Ya cika da fitsari ko tun safe fa."
Ta tambayeta tana ƙoƙarin saka hijab.
Kai ta ɗaga mata tana ɗaukar yarinyar su kayi bathroom. Ita kuma ta tada sallah. Bayan ta fito ta canza mata pampers da kaya cikin baby bag dinta ta ɗauketa suka fita, Aunti Hasiya bayan ta gama ta fita ta samesu a falon gaba ɗayan su ta ƙarasa wajen Mami suka gaisa kafin ta zauna Munirat ta kawo mata abinci.
"Mami mai kuke shiryawa ne?"
Aunti Rahma tace tana bawa Babyn Hasiya kunu, Allah ya ɗaura mata son yarinyar kuma kowa ya lura da hakan, yarinyar bata da kiriniya.
Jin zancen da ta sako ya saka kowa caa a akan Mami.
Mami tace.
"Ni kuwa mai zan shirya, kuyi komai tsakanin ku, bari ita Nuratun ta dawo ta sani kafin komai."
"Hakane amma an saka ranar tarewar ta."
Aunti Hasiya ta tambaya.
Mami ta girgiza kai.
"Ni fa ban san komai ba, sai yadda su kayi da Dr Awwab, in ma ta yarda da auren ba. Bana son fushin autana."
"Kar ta yarda ɗin, aure an riga an ɗaura sai kuma tayi, shikenan yanzu sai ta dawo asan mai za ayi."
Aunti Hasiya tace tana tauna abincin bakinta. Burinsu kowa ya bawa ƙanwarshin gudunmowa kafin ranar tarewarta, su kimtsa ta ko ba komai tayi ƙima a idon mijinta. Har dare suna gidan kafin su mata sallama suka tafi.
****
Cikin magagin maye ya shigo gidan tun fitarsa na rana, duk abin da yasha bai gusar masa da tunanin Nuratu ba sai da ya danganta da yiwa kansa allurar kwaya yaji hankalinshi ya gushe ya nufo gida. Allah kaɗai ya kawo shi gida ya shigo cikin falon a hargitse.
Ummu da ke zaune ganin har karfe ɗaya bai dawo ba ya sata zaman jiran shi ta ji hankalinta ya kasa kwanciya. Yadda ya shigo mata ya mugun tsoratata ta miƙewa.
"Baby Noor."
Shine kalmar da Mufid ya faɗa ya nufi Ummu da shi domin idanuwansa gizau suke masa baya gani mai kyau.
Ummu da taji abin wani iri ta ja baya zuciyarta na bugawa da ƙarfi.
"Mufid ni ce Ummu fa ba wannan shegiyar yarinyar ba."
"Baby Noor."
Ya sake maimaitawa ya yi kanta. Da sauri ta ja baya duk ƙoƙarin ta nuna masa ita ce mahaifiyarshi abun ya gagara gadan gadan yayi kanta.
Ganin babu sarki sai Allah ya sata faɗawa ɗakinta ta kulle da mukulli kafin ta fashe da kuka tana dafe kirjinta da yake bugawa sosai.
"Ya Allah wani irin masiface wannan? Wani iri ɗa na haifa?"
Mufid kam bugun ƙofar yake yana kiran Baby Noor har ya hakura ya shige ɗakinsa ya faɗa saman gado yana sumbatu kafin wani mahaukacin bacci ya ɗaukeshi.
...
Washegarin da safiyar ranar juma'a Alhaji Mamman Bashir ya shiga cikin Companyn su, kai tsaye ofishinsa ya nufa baya amsa ko gaisuwar da ake masa ya san duk gulmace. Abin mamaki ofishin a kulle an canza gurin mukullin, duk yanda yayi ya buɗe kasawa yayi haka yasa ya nufi ofishin Oga Dauda rai ɓace.
Ƙwanƙwasa ƙofar yayi aka bashi izinin shiga ya shiga, ganin wanda ya shigo ya saka Oga Dauda haɗa rai yana dubanshi har ya zauna.
"Oga mukullin office ɗina naga kamar an canza."
Alhaji Mamman yace cikin ƙarfin hali kar abin da yake gudu ya faru.
Oga Dauda bai yi magana ba har ya gama maganarshi ya miƙe ya ɗauki doguwar letter cikin envelope ya ajiye gabanshi ya koma ya zauna.
"Mun gode da ƙoƙarin da kake cikin Companyn nan tsawon shekaru, amma yanzu bama buƙatar ka a gaskiya. Mun sallame ka."
Cikin ruɗu da tashin hankali Alhaji Mamman yake duban Oga Dauda ya kasa kwakkwaran motsi ya kasa ɗaukar envelope ɗin.
"Ka ji mai nace ai. You can go out please."
"Sir me yasa aka min haka? Me yasa haka? Me nayi? Kar dai kace min Alhaji Kashim ya saka ka aikata min haka."
Sai lokacin Alhaji Mamman ya samu bakin furta haka.
"Ko ɗaya, ka je kawai ina da abun yi bani da lokacin tattauna wannan maganar."
Oga Dauda yace ya miƙe yana barin gurin.
Alhaji Mamman ya daɗe zaune cikin ofishin kafin ya miƙe ya fita, ya san duk aikin Alhaji Kashim ne da ba zai iya ja da shi ba, da babu abin da zai hana shi shari'a da shi da, daɗinta ma in ya tuna ya banzar da maganar kuɗaɗen shi da ya ci.
Tafe yake cikin motarshi yana tunane tunane, bai san ya iso traffic light ba jan wuta ya tsayar da su ba, sai da ya bugawa motar da ke gaban shi da ƙarfi, da kyar ya tsayar da motarshi kafin ya fito mutanen gurin har sun cika gurin ganin asaran da ya jawowa mai motar gaban shi.
Samari ne biyu yan jagaliya cikin motarsu mai tsada suka fito.
"Motar Dad!"
Ɗaya yace da karfi yana ɗaura hannu a kai.
"Wallahi sai ya biya."
D'ayan yace yana nufan Alhaji Mamman da ya fito dan ganin abin da ya aikata.
"Kuyi hakuri zan biya. Zan biya ku ko nawa ne wallahi."
Alhaji Mamman yace da sauri dan ya lura yaran basu da mutumci za su iya masa komai.
Ɗaya ne ya shiga motar Alhaji Mamman d'ayan yaja nasu su ka bar gurin bayan mutane sunyi ta tofa albarkacin bakinsu. Kai tsaye gurin gyara suka isa in da suka san mutumin, gyaran da bai fi dubu ɗari ba sai da ya kai su ga gyaran miliyan biyu.
Cike da mamaki Alhaji Mamman yake kallon mai gyaran da ya maze yayi tamkar ba daidai ya faɗa ba.
"Haba makanike, ko motar za'a canza ai za'a samu na miliyan ɗaya. Wannan gyaran bai fi na dubu sittin ba fa."
"To sai ka gyara mu gani."
"Ba zai yiwu ba. Wallahi ko ka bada a gyara yanzu ko mu maka shegen duka kuma ka biyamu kuɗin gyara. Ka san waye uban mu a garin nan."
D'ayan da ya fisu iskanci yace yana yin kan Alhaji Mamman da cikinsa ya ɗuri ruwa.
"Kayi hakuri zan biya ku abin bai kai haka ba."
Alhaji Mamman ya faɗa da sauri yana zaro wayarshi.
"Transfer zan muku ban da cash."
"Hakan ma yayi."
D'ayan yace ya bashi lambar asusun bankinsa ya tura masa miliyan ɗaya da rabi.
"Wallahi bani da shi ku bini bashin dubu ɗari biyar."
Kallon kallo su kayi tsakanin su ɗayan mafaɗacin yace.
"An yafe maka Alhaji wannan ma yayi. Mun gode."
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana cewa.
"Nagode nagode sosai."
Daga haka ya shige motarshi da shima yana buƙatar gyara ya bar gurin. Sai da su kaga ɓacewar shi kafin su kwashe da dariya.
"Oga mun ja kuɗi wallahi."
"Sosai ma. Yanzu bari mu gyarawa mai mota motarshi kafin ya dawo, yau akwai cin kaji."
Cewar Ogansu yana juyi sun canki kuɗi. Daga sun gama gyaran motar da aka kawo musu suka ɗauka su gwada ya gyaru suka nufi cikin gari tsautsayi ya haɗasu da Alhaji Mamman suka yaudare shi.
A birkice Alhaji Mamman ya shiga gidanshi yana saɓaɓi da in mutum bai lura ba baya fahimtar mai yake faɗa. Amma Jidda da ta ga wucewar shi side ɗinshi ta fito ta nufi can.
Waya yake da yayanta Alhaji Tukur ta tarar yana sanar da shi halin da yake.
Daga can ɓangaren Alhaji Tukur yake cewa.
"Kai ma Mamman ka yi gaggawa, sai da aka sanar da kai yarinyar nan babu alheri a rayuwarta amma ka biyewa son zuciya gashi yanzu ta jawo maka asara garin kallo zata zame maka hanyar arziki. Babu aikin babu kuɗi. To kuma kana tsammanin Alhaji Kashim zai bar maka kuɗaɗen da ya baka ne? To wallahi ka shirya haɗuwar ku dashi."
"To ni ya zan yi, dubi fa yanzu abin da ya same ni. Kuɗaɗen gurina sun fara ƙarewa gashi kasuwan cin ma ya ja baya. Ni kam yarinyar nan ta zame min bala'i."
"To ya za kayi. Haka zaka hakura ka tattara masa kuɗin shi in ya nema ka bashi, gwara ku rabu lafiya dan abin ya wuce haka kasan ba zaku kwashe da daɗi ba. Ni lokacin da ka bani shawara zan hanaka amma tun da yanzu abu ya lalace ka sanar da ni, na baka shawara ka haɗa masa kuɗaɗen shi kafin ya nema ka bashi."
"Shikenan Alhaji Tukur zan yi yadda kace."
Alhaji Mamman yace su kayi sallama. Wani tsanar Nuratu na shiga cikin zuciyarsa, duk ita ta jawo masa wannan asaran.
Zuwan Amma Jidda ya sashi ɗan mance damuwar shi duk da har lokacin tana fushi da shi abin da yayi amma ta ajiye a gefe ganin shima ba'a dai-dai yake ba.
***
NIJAR.
"Nuru gobe za ki koma gida, kun yi waya da Maman ki?"
Kawu Muhammadu ya ke faɗawa Nuratu lokacin da ta zo gaishe sa da safe. Kai ta ɗaga masa alamar eh tana cewa.
"Eh jiya ta sanar da ni in dawo."
"To sai ki shirya inshaAllah gobe sai kiyi fitar safe dan ki samu isa da wuri."
"To Allah ya kaimu."
Tace tana miƙewa ta koma.
Bayan taci abincin safe tayi wankin kayanta Nazifa na taimaka mata da ɗauraya.
"Ni kam Nazifa har zan koma baki kai ni naga kogi ba."
"Idan kina so zuwa da yamma sai mu je ai yafi daɗin zuwa."
Nazifa ta bata amsa, duk da Nuratu ta girmeta da shekaru kusan uku amma ta ɗauketa tamkar sa'ar ta haka Nuratu ma hankalin Nazifa na burgeta.
"Ai kuwa bari in na gama sai mu je."
To Nazifa tace suka gama wankin kafin su ɗaura abincin rana, bayan sun gama wajen karfe uku, sallah su kayi kafin su ci abincin suka yi wanka suka shirya.
Abaya Nuratu ta saka da ya amshi baƙin fatar jikinta, ba tayi wani kwalliya ba ta feshe jikinta da turare suka fita, tayi kyau sosai cikin abayan daga hoda sai chappate a bakinta.
Bakin kogi suka nufa garin babu rana dan sanyi da ya shigo, yamma yayi sosai, a bakin kogin suka tsaya in da babu mutane sosai, Nuratu gurin ya mata kyau ta zubawa cikin ruwan ido ta lumshe idanuwanta iska yana kaɗawa, wani ƙamshi mai daɗi yana shigarta da ya sauƙar mata nutsuwa.
"Is so romantic right Baby?"
Ta tsinci muryar Dr Awwab cikin kunnuwanta har tsakar kanta da sauri ta buɗe idanunta ta juya in da taji muryar, ganinshi tayi daf da ita sai lokacin ta ankara da ƙamshin turaren shine ya mamayeta.
Baya taja kaɗan tana ɗauke idanuwanta cikin nashi tana tambayarshi.
"Yaushe ka zo? Ina Hanan?"
Ƙara matsawa yayi kusa da ita kaɗan ganin idanunta suna wani gurin yace.
"Yanzu zuwana na samu labarin kin zo nan na biyo kayana. My Love tana lafiya, ta so zuwa na hanata kar ta hanani