Follow us on social media

Showing 60001 words to 63000 words out of 148866 words

Chapter 21 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

51

bakya ɗaukar ƙira na. Kin san ƙira nawa na miki daga gida zuwa kafin in iso."

"Kayi hakuri, wallahi wayar yana cikin jaka ban ji ba."
Ta iya bashi amsa bayan kallo ɗaya da ta masa yana sanye da ƙananan kaya kamar kullum yayi mutuƙar yin kyau.

"Ba wannan ba ina za kije babu sanarwa? Ko dai ina takura miki ne Noor in hakura?"

Sai lokacin tayi ƙoƙarin kallonshi karo na biyu suka haɗa ido tayi saurin ɗaukewa zuciyarta yana bugawa jin maganar shi na ƙarshe da ya sakata shiga ruɗani da ta rasa dalili. Girgiza kai tayi.

"Kayi hakuri Docter."
Tace muryarta yana rawa, ya ƙara matsawa kusa da window sosai jin muryarta ya canza.

"Kar ki min kuka, bana son muyi rabuwar da ba daɗi."

"Ni fa tafiya zan yi ba wani gurin zan je ba."
Tace tana turo baki tare da ƙoƙarin mai da hawayenta.

Idanuwansa ya ɗauke saman fuskarta yanda ta yi da bakinta ji yayi har tsakar kanshi. Da kyar ya furta.

"Ina za ki je?"

"Nijar gurin Yayan Mami."

"Sauƙa ki fito."
Yace da ita ta juyo da sauri ta kalleshi shima lokacin ita yake kallo ta ɗauke kanta.

"Na ce ki sauƙo. Magana za muyi kafin a cika."

Daga haka ya bar baƙin window ya koma gurin boat ya saka aka ciro mata akwatin ta.

"Lafiya Oga? Ko ta fasa tafiyar ne?"
Faɗin mai motar.

"Ku je kawai kuyi hakuri."

Dr Awwab yace ya ja akwatin Nuratu yayi gaba da shi, Nuratu da ta fito jin maganganun su ta bi bayanshi da sauri cike da mamakin ina kuma zai kai mata kaya ita da take son isa kafin dare.

Cikin boat din motarshi ya saka akwatin ya zagaya ya buɗe wajen zaman banza dai-dai lokacin Nuratu ta iso ta ja ta tsaya.

"Shiga mu je."
Yace da ita ta kalli cikin motar tana girgiza kai.

"Dan Allah kar ka mai dani gida. Rayuwana yana cikin hatsari ka bar ni in tafi."

"Ni ma ba gida zan maida ke ba, tafiya a motar kasuwa akwai wahala Noor."

Girgiza kai tayi tana rau rau da idanuwanta za tayi magana ya rigata.
"Zan saka ki da kai na in baki shiga ba."

Kallonshi tayi ya ɗaga mata gira.
"Yes ko in gwada ne?"

Da sauri ta shiga ya rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana fita a cikin tashar, babu wanda yayi magana har su kayi nisa ya samu babban mall ya tsaya.

"Bari in mana guzuri."

Ba ta kulashi ba ya fita ya shiga ciki ya fito da kaya niki niki a hannunshi daga snack da drinks ya saka a kujeran baya ya koma ya shiga yana kunna motar suka bar gurin, tafiya suke har suka fita a garin Damaturu suka ɗauki hanyar Geidam ya ɗauki wayarshi ya ƙira Ummi.

"Ummi ki min addu'a zan yi tafiyar gaggawa."
Ya faɗa bayan Ummi ta ɗauka.

"Ka isa Damaturu ne?"
Ta tambayeshi ta ɓangaren ta.

"Eh zan yi nisa kaɗan zuwa gobe zan dawo inshaAllah, a kula min da My Love."

"To Allah ya kiyaye a dawo lafiya."

Ameen ya amsa ya kashe wayar yana ajiyewa a gefe ya kai dubanshi gurin Nuratu da ta kwantar da kanta saman kujera tayi baya.

"Bacci zaki min a mota?"

Sai lokacin ta juyo hankalinshi yana kan hanya ta ɗauke kanta ba tace komai ba.

"Bari in kara gudun AC sai kiji daɗin baccin ki, mai da kujeran baya kaɗan."

Babu musu ta maida kujeran yayi baya ta kwanta ta ja gyalenta ta rufe fuskarta da shi, ya ƙara mata gudun AC.
Tafiya yake yana tuƙi ba ji ba gani, Nuratu bacci ne ya ɗauketa bata san lokacin ba.

...

#vote
#comments
#shar#share
MADUBIN GOBE (Haske) 31.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Sun yi tafiya mai nisa tsawon awa huɗu kafin su shiga cikin garin Geidam, lokacin karfe biyu na yamma. Hotel mai kyau ya nema dakyar ya samu ya kama dan su gabatar da sallah kafin su wuce.

*"Noor."*

Yace yana buga seat din Nuratu ta buɗe idanunta fes cikin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi, da sauri Nuratu ta runtse idanuwanta bayan ta watsa mishi harara dan kallon da yake mata.

"Ni ka dai na kallo na."

Murmushi Dr Awwab yayi.
"Why Noor?"

Bakinta ta tura tana juyar da kanta gefe ta fara ƙoƙarin fita taji yace.
"Bamu iso ba, sallah za muyi muci abinci sai mu ƙarasa."

Kai ta ɗaga mishi ta fita shima ya fito ta ga ya nufi cikin hotel ɗin ta ja ta tsaya. Juyowa yayi yana kallonta yaga ta tsaya.

"You don't believe me Noor?

Girgiza kai tayi yayi gaba yana cewa.
"To mu je."

Babu musu ta bi bayanshi har cikin hotel ɗin ba laifi yana da kyau da komai har cikin ɗakin sai taji gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, zuciyarta ya fara bugawa, tsoro ya fara ziyarar ilahirin jikinta, jikinta ya fara rawa.
Kallo ɗaya Dr Awwab ya mata bayan ya gabatar da alwala a bathroom ya fito ya karanci yanayinta.

"Kiyi sallah kafin na dawo sai mu wuce."

Daga haka ya fita sai lokacin ta ɗan ji sauƙin ta samu nutsuwa ta miƙe ta shiga bathroom, jikinta ta gyara ta fito dan ba sallah take ba ta zauna jiranshi.
Bai jima ba ya dawo ɗakin ta miƙe tsaye ganinshi, da kallo ya bita.

"Kinyi sallar ma kuwa?"

Tambayar da ya mata kenan kai ta ɗaga mishi ya juya suka fita yana riƙe murmushin sa dan fahimtar yanayinta. Cikin motar suka koma ya ja suna barin harabar wajen, suna cikin tafiyar ya faka ya miƙa hannunshi baya ya ɗauki snack da drinks da ya saya a cikin Damaturu ya juyo ya ɗaura saman cinyar Nuratu.

"You can eat, duk abincin su bai min ba."
Kai ta ɗaga masa yaci gaba da tuƙi.

Har suka fita cikin garin ya ga bata da niyar ci ya sashi faka motar ya juya yana kallonta kafin ya kai hannu ya ɗauki snacks din dake saman cinyarta ta kasa ci, ba wai dan bata jin yunwa ba sai dan kunyarshi da take jin ba zata iya cin abu a gabanshi ba.

Tana kallo ya ɗauka ya buɗe ya miƙa mata.
"Karɓi kici ko in ɗura miki dan na san kina jin yunwa gulma ce ta hana ki."

Rai ta ɓata ta karɓa ya ɗauki drinks din ya buɗe mata.
"Karɓi ki haɗa."

Shima karɓa tayi ta riƙe yana kallo bata da niyar ci ya haɗa rai.
"Sai na miki ɗurai ko?"

"To ni ka daina kallo na."
Nuratu tace tana ɓata rai ita ma.

Murmushi yayi ya juya yana kallon titi ya kunna motar yana ja, ganin haka ta fara ci kaɗan kaɗan har taci sosai tasha drinks din, tana ƙoƙarin ajiyewa a gefe taji yace.

"Ban sauran."

Kallonshi tayi ya juyo ya saka ɗayan hannunshi ya karɓi snacks din hannunta ya kai baki yana ci, sai da ya cinye ya ɗauki sauran drinks din ya shanye ya buɗe gilashin motar ya jefar da robar yaci gaba da tuƙi.
Nuratu idanu ta zuba mishi ganin baya kallonta kafin ta ɗauke ta mai da kan titi, shuru babu wanda yayi magana har sun kusa shiga border ya sako zancen da yake son mata.

"Me za kiyi a Nijar?"

Shuru tayi bata bashi amsa ba ya sake maimaita tambayar ta buɗe baki da kyar ta sanar dashi. Sai da ta gama tayi shuru yace.

"To a bani dama mana na fito Noor, a shirye nake ko yau kika bani dama."

Shuru ta mishi taƙi bashi amsa ya canza salon maganar.
"Allah yasa hakan ya zamto rushewar auren, amma fa ba zan hakura ba har yanzu ina kan bakana, kinga in munje ma sai in gabatar da kai na wajen Kawu."

"Ni dai bana so dan Allah."
Tace tana haɗa rai yayi murmushi yana shafa kanshi cike da gashinsa na fulanin asali kwantacce.

"Allah ni ina so Noor, bani da wani burin ya wuce in aure ki."

Bata kulashi ba ta juyar da kanta tana haɗa rai, ganin da gaske tayi fushin ya sashi yin shuru dai-dai sun isa border suka tsaya.

Fita yayi a motar ya nufi masu kula da shiga da fita, yayi duk abinda zai yi dakyar suka bashi damar shiga ƙasar bayan katin shaidar ƙasa dana aiki dana tuƙi da ya nuna musu kafin su barshi.
Bayan ya koma motar ya ja aka barsu suka wuce cikin Maine anan ya tambayi hanyar garin Doso aka nuna masa.

Ƙarfe biyar ɗin yamma suka shiga cikin garin, Nuratu sai bin garin take da kallo, bata taɓa zuwa ba sai dai shi Yaya Muhammadu ya zo wani lokacin.

Guri ya samu yayi fakin motarshi yana fuskantar Nuratu.

"Sai kuma ina Noor, ina ne hanyar gidan."

"Dama in na sauƙa ne zan ƙira in sanar dasu da wayar direba, kuma yanzu kam sai dai in sayi sabon sim."

"Bari mu nema to."
Yace yana jan motar ya fara neman masu sai da kati ya sayi sim da kati ya karɓi wayarta ya buɗe, sim ɗinta ɗaya na Mtn hakan yasa bai cire ba ya saka sabon da ya saya ya kunna yana miƙa mata.

"Saka numbern ki ƙira su."

Karɓa tayi ta saka numbern sai da ta ƙira sau biyu aka ɗauka, Yaya Muhammadu ne.

"Ina wuni Kawu."

"Lafiya ƙalau sai dai ban gane waye ba?"
Yace daga ɓangaren shi.

"Nuratu ne ƴar Hajiya Sadiya, na shigo garine dama shine na ƙira a zo a ɗauke ni."

"Oh Nuru, to to kina ina ne in turo Musalle."

"Nima ban sani ba."
Ta fada, ƙasa ƙasa Dr Awwab yace mata.
"Ya same mu a tasha ko ma shigar gari."

"Kawu ina tasha yazo."
Nuratu ta faɗa jin me Dr Awwab yace.

"To yana zuwa kar ki je ko ina."

To ta amsa dashi ta kashe wayar Dr Awwab ya ja motar bayan sun tsaya an musu kwatancen tasha suka isa gurin.

"Bari in yi sallah in dawo."
Dr Awwab yace Nuratu ta ɗaga masa kai ya fita, bayan yayi sallah ya dawo Musalle ya ƙirata ta ɗauka.

"Kai ne ka sauƙa a mashin yanzu?"

"Eh kina ina?"

"Gani nan a cikin farin mota ka ƙaraso."

Daga haka ta kashe wayar Musalle ya juya ya kalli motar gefenshi kafin ya ƙarasa wajen ta buɗe ta fita suka gaisa ta koma ya shiga baya.
Suna tafiya yana nuna musu har cikin unguwar su, unguwa babu laifi amma akwai rashi tattare da unguwar dan babu sosai, ginin bulo da bulo ma babu sosai balle kwalta da wani abun more rayuwa.
Baƙin ƙofar gidan ya faka motarshi suka sassauƙa, Dr Awwab ya fito da akwatin Nuratu suka shiga cikin gidan da sallama.

An shimfiɗa musu taburma a filin gidan, Nuratu ta zauna Dr Awwab ya zauna a gefenta shi kanshi yana mamakin ƙarfin halinshi. Yaya Muhammadu zaune gefensu saman nashi taburman matar shi da ƴarshi budurwa suna gefe a saman kujeran tsungunno.
Bayan gaisuwa da aka gudanar tsakanin su, Yaya Muhammadu na tambayar ƴan gida ya juya kan Dr Awwab suka gaisa.

"Amma dai dole za ka kwana, ka ga dai dare yayi."

"Eh Kawu nima hakan nace, zan nemi gurin kwana."

"Wani irin kuma za ka nemi gurin kwana bayan ka zo gida, ka ga nifa ɗaya na ɗauke ka da ƴaƴan Sadiya. Ga ɗakin Musalle in har zaka iya kwana sai ya bar maka."

Idanu Dr Awwab ya ɗago ya kalli Nuratu ta juyar kanta gefe.

"Shikenan Kawu nagode babu komai."

"Ko kai fa, Musalle ɗauki abinci da kindirmo ka kai masa, in akwai abinda yake buƙata ka sanar mishi."

Yaya Muhammadu yace Musalle ya miƙe ya ɗauki abinci da ruwa ya kai masa ɗakinsa ya dawo ya ɗauki kindirmo suka koma tare da Dr Awwab. Ɗakin bashi da laifi, lailaye ya ke da leda sai babbar katifa da bedsheet a kai da ɗan hasken shi sai akwatinan kayan shi a gefe, yaron da gani akwai tsafta. Dr Awwab mamakin kanshi yake in aka sanar da shi zai kwana a irin wannan ɗakin ba zai yarda ba amma gashi yau har daɗi yake ji zai kwana gida ɗaya da Noor ya wayi gari ya buɗe ido ya sata a idonshi.

Bayan wucewar Dr Awwab ciki Kawu yace wa Nuratu.
"Yaron akwai hankali kamar mahaifiyar shi, sau ɗaya na haɗu da ita ko biyu ne, auren Rukayya da zuwana na ƙarshe."

"Kawu ba fa ɗan Amma Jidda bane, ba Yaya Al-ameen ba ne."
Nuratu tace ganin Yaya Muhammadu duk zaton sa Yaya Al-ameen ne.

Da mamaki Yaya Muhammadu yace.
"To wanene shi kuma? Duk na ɗauka ɗan wajen babar su Rahma ne."

"Bashi bane, Dr Awwab ne, shi ya ci gaba da kula da ni a Maiduguri a asibitin su."

"Allah sarki, oho sai yanzu na shaida fuskar na ganshi a kotu tabbas, Allah sarki akwai hankali daga ganin shi. Ko dai shine surukin mu."

Da sauri Nuratu tace.
"A'a wallahi Kawu mutumci muke, ya zo ni kuma zan taho shine ya kawo ni."

"Oho hakane. Ki ci abinci ki hutu anjima zan zo muyi magana. Hafiza shigar mata da akotin ta(akwati ta) ɗaka."

To tace yarinyar ta miƙe ta ja akwatin Nuratu ta shigar da shi ɗakinsu, Nuratu taci abincin sosai dan rabonta da abinci tun safe.

Bayan magriba ta watsa ruwa ta saka dogon riga da hijabinta har ƙasa ta kasa fitowa filin gidan.
Tare Kawu da Dr Awwab da Musalle suka dawo daga masallacin sallar isha'i, a soro suka rabu Dr Awwab ya shige ɗaki, Kawu da Musalle suka shige cikin gida.

Abincin dare aka jera musu Kawu Muhammad ya dubi matar shi.
"Ki bawa Nuru ta kaiwa bakonta ɗaki yana ciki, kin san dai da kunya ya zauna cikin mu."

To ta amsa dashi ta zuba a food flask mai haɗe da tuwo da miya tuwan biski miyar ɗanyar kuɓewa da ya sha kifi ta tura Hafiza ta ƙira Nuratu a ɗaki.

"Ga abinci ki kaiwa bakon ki."

"Mama Yawuro ki bawa Musalle ko Hafiza dan Allah."
Nuratu tace dan gaskiya bata so.

"Wuce ki kai mishi Kawun ki ne ya faɗa, baƙon ki ne fa ki girmama shi, Annabi yana girmama baƙi kuma yana son mai girmama shi."

Shuru Nuratu tayi ta ɗauki flask din da ruwan sha a jug haɗe da plate na silba a babban tray ta nufi ɗakin dake soro in da Dr Awwab yake.
Da sallama ta shiga yana zaune a ƙasa ya kwantar rabin shi akan katifar yaji sallamar Nuratu ya miƙe zaune yana amsa mata ta shigo ta ajiye a gaban shi.

"Ga abinci nan, fatan zaka iya cin abincin su."

"Saboda me yasa, duk abin da Noor taci nima zan iya ci ko rai na baya so. Balle ma na san abincin ƙauye da daɗi."

Murmushin Nuratu tayi da bata san dalili ba har dimples ɗinta suka lotsa dukka biyu.
Yana son abin ba zai iya ɓoyewa a ranshi ba. Dr Awwab yace a ranshi a fili ƙasa ƙasa yace.

"I like your dimples Noor."

Fuskarta ta rufe da tafin hannunta, zuciyar Dr Awwab cike da nishaɗi ganin Nuratu ta fara amsar saƙonshi da jin abin da yake ji a kanta.

Fuskarsa cike da murmushi yace.

"Bana son wannan kunyar da babu ita tsakanin mu. Zai cuce ni."

"Ni dai ka bari dan Allah."
Nuratu tace tana cire hannunta saman fuskarta ta ƙara da cewa.

"Ya gajiyar hanya, nagode sosai na baka wahala."

"Ni ne da godiya Noor kin kawo ni har gida ban sha wahala ba, kin ga gaba ba zan ji wahalar gabatar da kai na ba in na dawo."

Miƙewa tsaye tayi jin maganar da ya sako.
"Sai da safe."

"Allah kai mu, thank you Babyna."
Dr Awwab yace da sauri Nuratu ta fita dan bata iya hanashi wanɗannan maganganun da yake mata ba, kunya yake sakata ya jefa zuciyarta cikin wani shauƙi.

Abincin Dr Awwab yaci kaɗan dan bai jima da ci ba, Musalle ya shigo ya kwashe komai ya fita kafin ya kwanta dan huta gajiya.
Ɓangaren Nuratu ba ta ci abinci ba dan ta ƙoshi bayan Kawu Muhammad ya gama cin abincin ta ƙira Mami suka gaisa tana tambayarta ya hanya, bata ɓoye mata ba ta sabar da ita Dr Awwab ne ya kawo ta.

Mami tace.
"Ya zo na sanar dashi kuna fita ya iso. Mai yasa kika bashi wahala."

Nuratu tace.
"Shi yasa kansa."

Bayan sun gama magana ta miƙawa Kawu Muhammad dan jin bayanin Mami.

...

#vote.
#comments
#share

MADUBIN GOBE  32.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Kawu Muhammad sauraran bayanin Mami yake har ta gama ya sauƙe numfashi yana cewa.

"Sadiya anya Alhaji Mamman kan shi ɗaya."

"Ni ma ban sani ba Yaya Muhammadu, ni dai ga Nuratu dan Allah ta zauna zuwa nan da wani lokaci."
Mami tace ta ɓangaren ta.

"Shikenan amma kar ki damu, kinyi dabara da ki ka turo ta, sannan kar ki damu wannan lokaci ba zamu barshi ba."

Sun jima suna waya kafin ya kashe ya miƙawa Nuratu wayar ta karɓa ta shige ɗaki bayan dogon nasiha da Kawu Muhammadu ya mata akan kar ta damu komai zai wuce.

Da safe ƙarfe tara Dr Awwab ya shirya zai wuce, bayan ya yiwa su Kawu Muhammadu sallama tare da godiya suka ce sune da godiyar dawainiya da yayi da Nuratu. Har ƙofar gida suka suka rakoshi kowa ya koma ciki aka barshi da Nuratu.

Yana zaune cikin motar, ƙofar a buɗe Nuratu ta riƙe murfin motar, duk yanda ya so su haɗa ido ta ƙi yarda.

"Babyna."

Yace yana riƙe da wayarshi ya saita dai-dai fuskarta yana ɗaukar hotanta da bata ma san mai yake ba. Jin abin da ya faɗa yasa Nuratu haɗa rai ta watsa mishi harara.

"Ni ba Baby bace, bana so."

"To Babyn waye? Mami? Kin ma Mami girma. Babyna ce ke soon za ki yarda da hakan Noor."

"Ni dai ka gaishe da Hanan da Ummi sai anjima, Allah ya kiyaye hanya."
Tace ta rufe motar.

"Ameen Babyna za su ji."
Yace ya kunna motar yana barin gurin ta juya cikin gidan cike da kewa. Haka kawai ta ji kewar rashinsa kusa, yana sakata nishaɗi.

Tana komawa gida wanka tayi ta kimtsa jikinta ta canza kaya ta ɗauki wayarta ta ƙira Col. Ahmad, yana shirin tafiya duk ya harhaɗa kayansa zai koma Ibadan ya samu ƙiranta suna tare da Umma tana mishi faɗan da har jiya ta kasa dai masa akan ya rabu da Nuratu ko ta ɓata masa rai, kuma aure ne ta bashi nan da sati biyu in ba haka ba zata aura masa ƴar uwarsa ƴar ƙanwar babanshi.

Col. Ahmad bayan ya gama sauraran faɗan Umma yace.

"Mami maganar gaskiya ba zan miki ƙarya ba bazan iya rabuwa da ita ba amma maganar aure na janye tsakanin mu da ita. Kallon ƙanwata nake mata Umma, abin a tausaya mata ne wallahi, tana buƙatar taimako da kulawan uba ko yaya, dan Allah kar ki rabani da ita. Maganar aure kuma na amince in har hakan zai saka ki yarda da ni."

"Ka amince har ranka, kuma ka min alƙawari ba zaka taɓa kawo min maganar auren wannan yarinya ba ko gaba, in har kayi hakan ka tabbatar zan nuna maka ni na haifa ka."

"Na amince Umma in har za ki barni in taimaki rayuwar Nuratu."

Col. Ahmad yace har cikin ranshi.
Shi ba wai auren bane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login