Follow us on social media

Showing 39001 words to 42000 words out of 148866 words

Chapter 14 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

45

Allah bi miki haƙƙin ki ya saka miki."

"Ameen ya Allah."
Nuratu tace idanuwanta na cika da hawaye da kullum sai ta zubarsu cikin dare.

Kallonta yayi jin muryarta ya canza suka haɗa ido ya hango kwantaccen hawaye cikin kwayar idonta.

"Bana son kukan nan Please kar ki yi. Ko kina tunanin dan wannan abin ya faru Muhammad Al-ameen zai ja baya ko fasa auren ki. Hasalima ƙara son ki yake, ki saka wannan a ranki. Jira nake a sallameki ku koma gida in tada maganar auren mu, kin tuna ke kika min alƙawarin haka."

Tabbas ita ta mishi maganar aure a lokacin da take ƙoƙarin raba kanta da Mufid. Yanzu kuma fa da komai ya lalace, bata da wani daraja da ƙima da za tayi tinkaho a matsayin ta na ƴa mace. Ita da shi ɗin basu dace ba yanzu, ko ta aureshi cutan shi za tayi.

A zahirin girgiza kai tayi tana share hawayenta.
"Yaya Al-ameen ka bar wannan maganar ba yanzu ba dan Allah."

"Saboda mai yasa. Wani tunanin ki daban?"
Yace kamar ya karanci maganar zuci da take.

"Ni dai ba yanzu dan Allah."

Bai so ba amma ganin kamar zata shiga damuwa har yanayin fuskarta ya fara canza ya miƙe.

"Shikenan na bari ƙanwata. Tashi mu je ciki."

Da sauri ta miƙe ta fara tafiya ya bi bayanta suka koma. Ƙarfe huɗu suka musu sallama suka tafi.

***

Cikin kwana biyun Dr Awwab ya kauracewa idanuwansa da zuciyarsa ganin Nuratu. Bai yarda tana da muhimmanci a rayuwar sa ba sai da ya rasa ganinta, haka ya ɗauka a cikin zuciyarsa shaƙuwa da su kayi ne sam ba sonta yake ba. Aikin shi yake zuwa yayi ya koma, wataran yazo da Hanan wataran ya barta wajen su Hussaina.

....

Col. Ahmad ranar da ya zo da kwana biyu ya bi mahaifinshi ƙasar Egyp, allahamdulillahi ya samu jikin da sauƙi dan har ya fara gane mutanen kanshi yana magana ƙasa ƙasa. Burin Umma ya cika ta rabashi da wannan jarababbun mutanen da suka liƙe masa.

***

DAMATURU.

Mufid ban da Shaye-Shaye da kashe kuɗi bashi da aiki tunanin Nuratu ya sashi a gaba, ko bacci yake sunanta yake ƙira. Tin Ummu bata sani ba har ya zamto ta lura da halin da yake ciki.
Ummu tsorata tayi cewa take ko aljana ya yiwa fyaɗe ta shiga jikinshi dan ɗaukar fansa tana neman haukatar dashi.
Rufaida tun ranar da su kayi, ta haɗa kayanta da duk abinda zata buƙata ta tafi gidan babban yayarsu Aunti Humaira sai ƙura ya lafa, daga can take wucewa makaranta hankalinta a kwance.

***

Bayan sati uku.

Jikin Nuratu yayi sauƙi sosai, babu wani matsala ko damuwa sai in har ta fara tunanin za taji ciwon kai ko shiga cikin hayaniya tuni zata birkice.
Maza kuwa duk ta haɗa su ta tarkata ta watsa a kwandon shara. Mutum biyu take ganin kutumcin a rayuwarta Dr Awwab da Yaya Al-ameen da take ganinshi matsayin yayanta.

Yau ta cika wata biyu cib, wajen ƙarfe biyu na rana bayan taci abinci tasha maganinta ta koma ta kwanta. Tunani kawai take mai ya hana Dr Awwab zuwa yau tsawon sati biyu babu shi babu labarin shi. Maimakon ya zo duba ta kullum sai ma wani Dr da yake zuwa a madadin shi.

Zumbur ta miƙe daga kwancen da take ta saka hijabin Mami tare da zura silifas ɗinta.

"Ina zuwa?"
Cewar Munirat kasancewar Mami tana sallah.

"Waje zan leƙa ba zan jima ba."
Daga faɗar haka ta fita Munirat ta bita da ido.

Kai tsaye in da ta taɓa bi suka je ofishin sa ta bi, wasu suna kallonta wasu suna harkar gabansu har ta isa bangaren da ofishinsa yake.
Bakin kofar ta tsaya ta riƙe handle ɗin shiga, sai kuma ta ji ta kasa, ta sake handle din har za ta juya taji muryar Hanan ta dawo ta buɗe tana shiga da sallama.

Jin muryar mai sallama ya saka Dr Awwab kallon gurin suka haɗa ido, rai ta haɗa. Wato ma yana zuwa gurinta ne kawai baya zuwa.
Hanan da ta ganta ta rarrafa ta taho, hannu Nuratu ta saka ta ɗauketa kafin ta zauna tana fuskantar Dr Awwab da ido kawai ya saka musu, sun mutuƙar masa kyau.

"Mai yake hanaka zuwa duba ni yau tsawon sati uku."

Nuratu tace tana kallon cikin idanuwanshi da sosai tayi ƙoƙarin saka nata cikinsu domin yadda suke lumshashshu ya zuba mata su wani abu sai fitowa yake yana shiga cikin nata da ya haddasa zuciyarta dukan uku uku.

....

#vote
#comments
#share

MADUBIN GOBE  21.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Dr Awwab idanuwanshi ya ɗauke cikin na Nuratu da ta sarƙesa da nashi ya kawar gefe ya ɗaura saman Hanan da ta kwanta luf a jikin Nuratu tamkar ta santa.

"Babu abinda ya faru Noor, aiki ya min yawa. Idan har hakan ya ɓata miki ki gafarce ni."

Ajiyar zuciya Nuratu ta sauƙe tana miƙewa.
"Babu abin ɓacin rai, Allah ya baka hakuri bisa katse maka aikin ka da nayi."

Daga haka ta ajiye Hanan, yarinya tace bata san zancen ba ta fara kuka sai ta ɗauketa. Dr Awwab ya saka hannu ya ɗauketa ya fara lallashinta.
Nuratu har ta kai bakin kofa ta juyo ta kalleshi.

"Nagode Dr da taimakon daka min a rayuwa, ka sani kai ne mutum na farko dana fara yarda da shi bayan abinda ya faru a rayuwata. Nagode."

Maganganunta sun shige shi yana kallonta har ta juya ta fice ya kasa cewa komai. Tafiya Nuratu take yi haushin kanta take ji da tayi saurin amincewa da shi ta shigar da kanta rayuwarshi da ƴarshi da matarshi.

Tana komawa ɗaki Mami ta dinga tambayarta ina ta je.

"Nan ne ba nisa. Mami na gaji a sallame ni mu koma gida ni na warke."

Kallonta Mami tayi fuskarta sam ba alwala.
"Sai Dr Abbas yazo zan mishi magana mu ji mai zai ce."

Bata ce komai ba ta kwanta.

***

Col. Ahmad yana ƙasar Egyptian amma hankalinshi yana Nijeriya a gurin Nuratu, tsoronsa ɗaya kar a sallami su Nuratu su koma gida bai san address ɗinsu ba. Jikin mahaifinshi da sauƙi dan har ya fara takawa, paralise ne ya kama shi kuma yanzu da sauƙi.
Kullum sai sunyi waya da ƴan gida, musamman ƙannenshi mata da suke yawan ƙira da jin jikin babansu.

Watansu ɗaya yau cib a can ya samu ƙira daga gurin aikin shi, dole ya sashi shiryawa ya musu sallama ya taho Nijeriya in da yake saka ran suma sati mai zuwa zasu taho . Gida ya nufa duk ƙannenshi sun zo masa sannu da zuwa da tambayar jikin mahaifinsu yace da sauƙi suma nan da sati ɗaya za su taho.
Abinci kawai yaci ya kwashi mukullin motarsa ya fita burinshi da addu'ar shi Allah yasa Nuratu ba'a sallamesu ba. Yayi kewarta sosai da fushin da take mishi. Murmushi kawai yayi dan tunawa da kwata kwata bata mishi magana sai ta ga dama.

A harabar asibitin ya samu wanɗansu wanda zai iya cewa yayunta ne dan ya sha ganinsu tare da ita. Gaishesu yayi ya ga babu Nuratu cikinsu ya nufi ciki, a hanya suka haɗu da ita Mami suna fitowa. Har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da Mami ta amsa kafin duk su fito waje.

Yaya Al-ameen shima ya zo da Rahma ɗaukarsu a yau aka sallamesu zuwa gida bayan magunguna da aka ɗaura Nuratu a kai da wanda za tana zuwa karɓa.

"Dr in da zai yi wu za muna aikowa a karɓa mana saboda zuwan watarana ba za'a samu ba."
Mami ta tambayi Dr Awwab da zuwanshi yau bayan tsawon wata ɗaya da ya kaurace musu. Shima dan Nuratu ta matsa a sallameta ne kuma ya ga dacewar hakan, kewarta zai yi ya sa baya son sallamarta.

"Zan aika mata, ki bani Address."

Cewar Dr Awwab yana kai dubanshi kan Nuratu ta watsa mishi harara ta ɗauke idanuwanta. Murmushi kawai yayi, hararan yana taɓa mishi zuciya da tsaya mishi a rai, ya karɓi address ɗin su gurin Aunti Rahma.

"My patients an sallame ku ne."
Col. Ahmad yace ganin suna shiga motar Yaya Al-ameen.

Kai ta ɗaga mishi, Mami ta zagayo gurinsu.
"Yaro gashi har zamu rabu ban san ko sunanka ba balle in maka godiya. Nagode da irin dawainiya da kayi damu Allah saka da alheri."

"Mama! Nuratu ta san ni, sai dai tana min ganin mai laifi. Amma komai zai bayyana. Ku bani address ɗinku saboda za'a nemeku kwanan nan."

"Nema kuma."
Mami ta tambaya da mamaki.

"Kar ki damu, ba wani abu bane, za ki ji komai."

Ko ba komai ya nuna ƴarta kulawa hakan yasa ta bashi address ɗinsu kafin su shiga mota Yaya Al-ameen ya ja suna barin harabar wajen. Sai da yaga fitar motarsu kafin ya koma gida.

***

"Ummu wai ina Rufaida? Bana ganinta kwana biyu shegiyar yarinya."

Dubanta Ummu ta kai kan Mufid dake kwance rashe rashe saman kujeran falon ta yau sunyi faɗa da Faisal akan ya damesu da zancen Nuratu ya dawo gida.

"Tana gidan Humaira."

"Au can ta gudu?"

"Ban sani ba nima. Na rasa mai aka mata ta kauracewa gidan nan."

Dariya Mufid ya kwashe da shi yana tafa hannunshi, wato dan shi ta gudu, ai kuwa zai bita can sai ta nemo mishi Babyn shi Noor.

Ƙarfe biyar na yamma a ƙofar gidan Yayarshi Humaira ya sameshi ya yi parking a waje ya tura get ɗin gidan ya shiga har falon babu sallama.
Humaira dake falon jin an buɗe kofa ta ta juya ta kalli ƙanintan.

"Sannu babbar yaya."
Yace yana zama ta watsa mishi kallon banza.

"Wallahi ka ji kunya Mufid, ace za ka shigo gidan mutane babu sallama."

"Allah baki hakuri mantawa nayi. Assalamu alaikum."

Tsaki ta buga.
"Mai ya kawo ka?"

"Wajen ƙanwata na zo. Ina Ruffy?"

"Ban sani ba, ka bani ajiyarta. Ka ga in tsiyace ta kawoka gidana ka tattare kan ka da iskancin da ka ke ji dashi ka fitar min a gida kar ka tsorata min ƴaƴa."

Baki sake yake duban Aunti Humaira, ita ce ƴar farinsu kuma kowa yana bata girma.

"Allah baki hakuri Aunti Humaira, laifine dan na zo wajen ƙanwata, amma ba komai ni na zo gidanki, ki faɗa min komai son ranki. Sai anjima"

Mufid yace yana tashi, sai kuma taji ba daɗi ɗan uwa dai ɗan uwane balle ciki ɗaya.

"Kai ne ai Mufid ban san yaushe nutsuwa zata shigeka ba. Dawo ka zauna muyi hira, na aiki Rufaida yanzu zata dawo."

Dama ba son tafiyar yake ba jin haka ya sashi dawowa ya zauna.

"In baki labari. Na san ma kina da labarin."

"A'a faɗa min. Mai kuma ya faru?"

"You know Baby Noor?"

Girgiza kai tayi alamar a'a.

"Oh baki da labari kenan, wacce dalilinta na shiga cell da nayi raping ɗinta, three month ago."

Murmushin taƙaici Aunti Humaira tayi ko kunyar faɗar hakan baya ji, tana da labarin komai da yake faruwa.

"Na gane ta. Mai ya sameta?"

"Aurenta nake son yi, sonta nake yi wallahi kin ji. Idan na rasata mutuwa zan yi, in kuma ta auri wani to wallahi kashesa zanyi."

Dariya Aunti Humaira ta kwashe dashi, wani ubane zai ɗauki ƴarshi ya bawa Mufid.

"Allah baka Sa'a."
Kawai tace dan gudun bambamin shi ta miƙe ta kawo masa ruwa da abin motsa baki.
Rufaida da ce ta shigo falon ganin Mufid kamar ta koma, ta haɗa rai ta ƙaraso ta bawa Aunti Humaira saƙonta zata wuce ɗaki ta dakatar ta.

"Gurinki Mufid ya zo."

Rai ta haɗa ta dawo ta zauna.

"Wato nan ɗin ma sai da ka biyo ni."
Rufaida tace tana duban shi ta wani haɗa rai.

"Eh mana rasa kunya. Ina aikin dana saka ki."

"Ban yi ba! Ni ma neman in da take nake."

Miƙewa yayi ya nufi gurinta ta fasa ihu.
"Wallahi kar ka taɓa ni gaskiya na faɗa maka. Allah ban san inda take ba har yanzu, naje gidansu har yanzu a kulle, amma zan ƙara zuwa gobe."

"Ko ke fa. Aunti na tafi dama abinda ya kawo ni."
Mufid yace ya fita ko kallon ruwan da ta kawo mishi bai yi ba yasa kai ya fice.

"Menene ya faru."
Aunti Humaira ta tambayi Rufaida. Anan ta zayyana mata komai tun daga farko har ƙarshe da zuwa yanzu.

"Allah dai ya shirya Mufid, Daddy da Ummu sun gurɓata masa rayuwa a matsayin so da ƙauna. Dan Allah ya baka namiji haka ya kamata ka mai dashi, yanzu da su da yawa ne fa haka duka zasu tashi a lalace. Allah shiryasa ita kuma Allah bi mata haƙƙinta ya saka mata dan in ba hukunta irinsu aka fara ba, ba za'a samu ragowar fyaɗe a Nijeriya ba."

Ameen Rufaida ta amsa da shi ta miƙe ta wuce ɗaki dan sallar magriba.

****

Da karfe uku suka shigo gari, tayi ta bin garin da kallo abubuwa da yawa suna dawo mata ƙwaƙwalwar kanta, idonta ta runtse har suka shigo layinsu da komai anan ya fara. Har kofar gida Yaya Al-ameen yayi parkinga suka sassauƙa. Nuratu taƙi sauƙa.

"Fito mana Nuratu."
Faɗin Mami tana buɗe gefen da take.

A'a tace tana ƙamƙame jikinta tamkar gani take tana fita Mufid zai kamata.

"Fito babu komai gida zamu shiga."

Nan ma kan ta girgiza, sai da su kayi da gaske kafin ta fito ta rirriƙe su suka shiga cikin gida. A falon suka sauƙa, Munirat ta hau tattare da share kura kura kafin su ƙarasa cikin ɗakunan suka ajiye kayansu.

"In babu komai Mami zan wuce gida, Yaya Al-ameen zai sauƙe ni."
Aunti Rahma tace tana gyara zaman ƴarta a kafaɗarta.

"Babu komai Rahma. Ki je gida sannu da ƙoƙari Allah ya miki albarka."

"Ameen Mami, babu komai."

Daga haka ta fita Yaya Al-ameen ya sauƙeta a gida kafin ya wuce gida ya sanar da Amma Jidda sun dawo.

Da daren abinci marar nauyi Munirat ta girka musu, bayan sunci Nuratu tayi wanka tasha magungunanta ta kwanta, a tare suka kwana da Mami a ɗakinta dan sam ƙi tayi ta kwana a nata ɗakin. Da taimakon maganin da tasha ta samu bacci ya ɗauketa.

Washegarin gidansu cike da yayunta da mazajensu da suka zo dubata, Aunti Zarah da ƙanwarta itama ta zo har da mijin Aunti Zarah ya duba Nuratu yayi tama Mami nasiha akan abinda ya faru, ta mishi godiya domin cuta an riga an cuci ƴarta da ita.
Har dare suna gidan har da Amma Jidda da su Walida, zuwansu ya saka Nuratu fargaban da take ciki ya ragu.

Abin mamaki da daren ta samu baƙoncin Alhaji Mamman, duk yadda su kaso Mami ta fita ta saurareshi ta ji da mai ya zo kasawa tayi dan bata buƙatarsa a rayuwarta har abada. Nuratu dai ƴarshi ce zai iya iko da ita amma ban da ita, Nuratun ma bashi da hurumi tun da bai san haihuwarta da girmanta da wahalar ta ba sai ita.
Dan yanzu abu ya samu rayuwarta zai ce zai shiga ciki shi a wa?
Ya mata mai? Kar duniya ta zageshi.

****

MAIDUGURI.

"Awwab tun jiya na lura baka da walwala duk da dai dama fuskar a haka take."

Ummi ta ƙarasa tambayar Dr Awwab cike da zolaya ko zai sanar da ita abinda yake faruwa dashi, fuskar shi babu hayaniya in anyi abin dariya zai yi murmushi amma baya haɗa rai.

Murmushi yayi da shi kaɗai yake yi shima sai Ummi da wanda suke da muhimmanci yake musu.

"Babu komai Ummi. Ki taya ni da addu'a kawai."

"To Allah yaye maka damuwarka, amma matsayina na mahaifiyar ka ya kamata in sani tun da dai ka nuna akwai damuwar."

"In lokaci yayi zan sanar dake Ummi na."

Daga haka ya miƙe ya fita yana ɗaukar Hanan da tayi bacci dan su wuce gidansu.


...

#vote
#comments
#share

MADUBIN GOBE  22.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Shirin kayansa yayi tsaf ya fito da akwatin shi, Umma ta bishi da kallo.

"Ina kuma zuwa da kaya haka? Ko hutun ya kare ne?"

Col. Ahmad da ya zaune saman kujera yace.

"Umma ya ƙare zan tafi an neme ni. Amma ba zan jima ba zan dawo bai fi in yi sati biyu ba. Ki mini addu'a akwai yaƙin da nake son cimma nasara a kai."

"Allah baka sa'a ya dawo da kai lafiya."

Ameen ya amsa dashi ya tashi ya fita direba ya kai shi har airport ya bi jirgi zuwa Ibadan.

***

"Amma ni fa har yanzu ina kan bakana."

"Na me kuma?"

Amma Jidda ta tambayi Al'ameen duk da ta fahimci akan mai yake magana.

Kai tsaye yace.
"Na auren Nuratu."

"Ni dai ba zan hanaka auren Nuratu ba, amma da ka bari zuwa wani lokaci kaɗan, yaushe ma ta samu lafiya?"

Ya san hakan amma dai so yake a san har yanzu yana nan akan bakarshi na son aurenta babu abinda ya canza wai dan ƙaddara ya faɗa rayuwarta.

"Shikenan Amma zan ba ta lokaci, amma ba mai tsayi ba."

....

Tun ranar da su Nuratu suka dawo ba ta fita ko nan da ƙofar gida, daga falo sai ɗaki, tsoron fita take, duk bayan kwana biyu sai yayunta sun zo dubata tana jin daɗin haka. Magungunanta baya wuce lokaci take sha akai akai da hakan yana mutuƙar taimaka mata, maganar makaranta ta jinginar shi a gefe ba yanzu ba.

Yau suka samu baƙoncin Rukayya da Walida, gidan ya mata daɗi. Mami ta fita sarin kaya da ɗan kuɗaɗen hannunta da suka rage dan duk ta cinye jarin a jinyar Nuratu dan ma tana samun taimako daga ƴaƴanta da mutane.
Har dare kafin suka tafi, da daren Mami na duba kayan data saro Nuratu na gefe tana gani har ta nuna wani atamfa da ya mata kyau, Mami tace ta ɗauka ta ba ta.
Godiya tayi ta ajiye a gefe tana kallon Mami.

"Mami ina son miki wani magana, sai dai ban san ya za ki ɗauka ba."

"Ina sauraronki."
Mami tace taci gaba da duba kayanta.

"Ina son shigar da ƙara, ina son kwatar haƙƙina. Ina son ɗaukar fansa bisa abinda aka min."

Kallonta Mami tayi ta hango tsantsan buƙatar hakan a fuskarta. Numfashi ta sauƙe.

"Kina ganin hakan mai yiwa ne? Ko kin shirya yaƙi da masu hannu da shuni? Ko kina da wani wanda zai tsaya miki ya taimaka miki ya kwatar miki haƙƙin ki. Ko kina da kuɗaɗen da za ki shigar dan samun nasara. Zamani ya canza Nuratu, masu kuɗi ba'a hukunta su, duk abinda suka aikata komin munin shi rufewa ake. Kai talaka in an cuce ka sai dai ka ɗauki hakuri ka kai kukan ka wajen Allah. Cuta an riga an cuce mu an cuci rayuwar ki, bamu da ikon ɗaukar hukunci. Allah kaɗai zai saka miki."

"Mami zan kashe Mufid."
Nuratu tace tana fashewa da kuka mai cin rai bayan gama bayanin Mami, rayuwarta ya lalace ya tarwatse dalilin shi.

"Kul na ƙara jin maganar kisa a bakin ki, ki barshi da Allah kaɗai ya isa da shi. Sannan ki godewa Allah da basu shafa miki wani cutar ba ko sun bar ki da ciki ba."

Nasiha da faɗa Mami tayi ta mata tun tana kuka har tayi shuru, wani mugun ciwon kai ne ya zuba mata a daren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login