Follow us on social media
Showing 87001 words to 90000 words out of 148866 words
Chapter 30 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
taso ba ta ɗauka ta fita tana mishi godiya, sai da yaga shigewarta cikin gida kafin ya ja motarshi yana barin harabar wajen. Zuciyarshi fes ciki da farin ciki Babynshi ta amince ta yarda zata zauna da shi a matsayin miji, ya san gaba kaɗan zata fahimci soyayyar da take masa.
...
Tana shiga cikin gidan a falo ta samu Mami ta farka ta bita da kallo.
"Ina ki ka je ne tun ɗazu ina ta neman ki."
"Na ɗan fita ne."
Nuratu tace ta ajiye kayan hannunta ta wuce ɗakinta, alwala tayi ta gabatar da sallar la'asar kafin ta fito falon ta zauna tana buɗe kayan da Dr Awwab ya saya mata. Burger ta iya ci ta sha ice cream din kaɗan ta tarkata sauran ta saka fridge. Mami dai ido ta saka mata har ta gama ta kwanta.
"To mai amfanin kin saya kin kasa ci."
"Na ƙoshi sai anjima."
Nuratu tace ta canza salon hiran.
***
MAIDUGURI.
Dr Awwab yana isa Maiduguri gidan Ummi ya nufa, a falo ya samu Hanan tana kallon cartoon ya zauna kusa da ita yana ajiye mata kayan hannunshi kusa da ita. Juyowa tayi tana buɗewa lokacin da yace.
"Ga tsaraba My Love."
Ihu ta saka ganin abinda ya kawo mata ta rumgumeshi.
"Thank you so much My Daddy."
Ihunta shi ya fito da ƴan biyu da sauri, duk tsamanin su wani abin ya sameta ne suka ga ita da mahaifinta ne suka koma. Ice cream din ta sha dayawa da shawarman, ta ɗauki sauran ta kai kitchen ta saka fridge ta fito ta samu baya nan taci gaba da kallonta.
Dr Awwab gidan shi ya wuce dan huta gajiya, wanka yayi ya gabatar da sallar magriba ya kwanta saman doguwar kujera ya laliɓo numbern Nuratu.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 42.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
....
"Babyna shine babu ƙira ki tambaye ni na isa lafiya."
Dr Awwab yace jin Nuratu ta ɗauka tayi shuru.
Kamar ba za tace komai ba ƙasa ƙasa tace.
"Ya hanya? Ina Hanan?"
"Allahamdulillahi lafiyarta ƙalau. Me ki ka cewa Mami da ta tambayeki ina ki ka je?"
"Babu komai."
"Sai ki sanar da ita mijinki ya ɗauke ki kun fita."
Yace yana murmushin da take jin sautin shi.
"Ni dai sai anjima, bacci zan yi."
Nuratu tace da sauri ya dakatar da ita.
"Wayo za ki mini dai. To ki yi bacci lafiya sai da safe."
Kit ta kashe wayar ta ajiye tana sauƙe numfashi, ji take kamar yau suka soma waya da shi, dan jin yanda numfashinta yake riƙewa kamar budurwar da take hira da saurayin da ta mutu a son shi da ko muryarshi ta ji sai jinin jikinta ya tsaya.
***
New Delhi.
Ɓangaren Mufid yana samun dukkan kulawar da ya kamata a bashi daga Ummu da likitoci, jikin shi yayi sauƙi har ya fara wasu abubuwa da kanshi. Daddy kuɗaɗen hannunshi duk ya ƙare burin shi su cika sati uku a sallamesu. Can gida yayi waya a turo masa kuɗi, an sai da motar Mufid da nashi ɗaya an haɗa an turo shima ya kusa ƙarewa.
Cikin ikon Allah Mufid tun farkawar shi bai ƙara musu maganar Nuratu ba, hakan ya yiwa Ummu da Daddy daɗi, na shi bangaren kuwa har lokacin da tunaninta yake kwana yake tashi. Duk da ya san zuwa yanzu ta masa nisa ta zama matar wani ya san abu ne mai wahala ya cireta a ranshi. Wahalar da ya sha ganin ya kusa mutuwa ya sashi jin tsoron Allah da duniya ta shigesa. Ya cire komai na harkar barikanci a ranshi, yaji komai ya fice masa a rai.
Burin shi ya koma gida ya nemi yafiyar duk mutanen da ya zalunta ko zai samu rahamar Allah. Bashi da aiki kullum sai zama cikin tunanin rayuwar da ya gudanar da babu komai na khairi sai lalaci da hakan yake saka shi nadama sosai.
Shuru shurun da ya zama shi yafi damun Ummu, take cewa ko dai bashi da lafiya, ya nuna mata lafiyar shi lau kawai hayaniya ne baya so.
***
DAMATURU.
Ranar wata alhamis karfe taran safe Alhaji Mamman ya shirya bayan ya yi breakfast ya miƙe yana kallon Amma Jidda.
"Zan leƙa kasuwa in dawo. Ki shirya za ki min rakiya in na dawo."
"To a dawo lafiya."
Amma Jidda tace ta miƙe ta tattara wajen ta koma ɗaki. Ameera ce ta shigo ta mata sallama za ta wuce makaranta ta ciro ɗari biyar ta bata.
"Gashi kiyi kuɗin mashin, har yanzu Abban ku bai samu kuɗi ya gyara wancan motar ba."
"Amma, Amma ya haka dan Allah yau fa wajen sati biyu mashin nake hawa."
Fuska Amma Jidda ta ɗaure tana duban Ameera.
"Eh sai aka yi ya? Ke da fa ba yanzu bane komai ya lalace sai addu'a. Kina ganin dai abubuwan da suke faruwa a gidan nan. Abban ku bashi da aikin yi sai kasuwanci da yanzu shima ba tafiya yake ba."
Gunguni Ameera tayi ta fita, ita dai ba zata iya sabuwar rayuwar da aka soma a gidan ba da hatta cimarsu ta fara canzawa. Abin da basu sani ba tun tasowarsu, sunga kuɗi sunga jin daɗi, yanzu lokaci ɗaya ace za su fara wani rayuwar.
....
Alhaji Mamman ƙarfe uku ya dawo, sai da ya gabatar da sallar la'asar yaci abinci kafin yace.
"Ɗauko mayafinki mu je."
Da sauri ta saka mayafinta babba suka fita a gida. Tafe suke tana ganin ikon Allah da bai mance unguwar da gidan ba har kofar gidan Mami ya faka motarshi yana kallon Amma Jidda da take bin shi da kallon mamaki.
"Shiga ki sanar da ita zuwa na."
Babu musu ta fita ta shiga cikin gidan Mami da fara'a ta tare ta suka shiga falon. Bayan sun gaisa Amma Jidda tace.
"Tare muke da baƙo Maminsu Rahma."
Da mamaki Mami tace.
"Baƙo kuma? Waye haka da ba zai shigo ba."
"Abbansu Rahma ne. Dan Allah kar kice ba za ki saurareshi ba. Wallahi ya canza, komai ya canza Mami. Yanzu da baya ba ɗaya bane, nadama ya shigesa ya gane laifinshi."
Fuska Mami ta ƙara ɗaurewa.
"Jidda ina ganin mutumcinki da ƙimarki albarkacin yara, dan haka in dai abin da ya kawoki ne kiyi hakuri ki dai na min maganar nan. Na riga na cire shafin Alhaji Mamman a rayuwata haka Nuratu ma."
"Yafiyar ki ya zo nema. Shin ba zaki yafe masa ba."
"Ki bar maganar nan Jidda."
Mami tace tana ƙara haɗa rai.
Duk yadda Amma Jidda tayi Mami ta saurareta ƙi tayi, haka ta hakura ta mata sallama ta fita.
"Ya ya ta amince?"
Alhaji Mamman yace bayan zaman Amma Jidda a motar.
"A'a wallahi ta ƙi sauraro na."
"Shikenan kar ki damu na san mai zan yi."
Daga haka ya ja motar suka bar ƙofar gidan.
***
Bayan sati uku.
Yau an tashi da sanyi sosai dan sanyi da ya shigo. Har ƙarfe goma Nuratu tana cikin bargo bata farka ba, duk faɗan Mami ta fito ta ɗaura abincin safe ko ta mata shara kasawa tayi dan tana tsoron sanyi sosai. Bacci ta koma bayan sallar asuba, sai karfe goman ta farka ta ƙi fita, duk da yunwar da take ji kasawa tayi tana duƙunƙune cikin bargo, wayarta da ƙaranshi ya farkarta da ita ta ga Dr Awwab ne.
Kwana biyun ba suyi waya ba, ji tayi kewarshi da sauri ta ɗauka.
"Babyna."
Yace daga ɓangaren shi da ya saka Nuratu lumshe idanuwanta ta buɗe. Dole ta fara amsa sunan da duk lokacin da ya ƙirata dashi sai taji yafi kowa iya furtawa akan leɓɓanshi. Katse mata tunanin da take yayi ta hanyar cewa.
"Babyna yau sanyi ake sosai gashi na kasa fita aiki, na san da kina kusa za kimin maganin sanyin."
Nuratu kamar ta zuba ihu jin abin da yace ta ɓata rai kamar yana gabanta tace.
"Ni ma sanyin nake ji ai."
"Don't tell me kina cikin bargo har yanzu."
Yace da mamaki.
"Eh ban fita ba tun safe."
Dariya Dr Awwab yayi har taji sautin shi yace.
"Babyna in kin zo ma haka za kina mini. Tsoron sanyi kike ji."
"Sosai ma."
Tace tana turo baki.
"Kin cika ragwanta Babyna. Allah dai ya kai mu in rage miki wannan ragwantar."
Nuratu kamar za tayi kuka jin abin da yace tace.
"Wallahi zan kashe wayar in ba zaka daina min irin wannan maganar ba."
Dariya ya sake yana ɗaukar tissue ya tare atishawar da zai yi, dan mura ne ya kamashi saboda sanyi, bayan yayi yace.
"To na bari. Yaushe zaki tare ne? Na fara gajiya wallahi."
"Ni ba yanzu ba dan Allah. Sai nayi service nan da shekara ɗaya."
"Service dai Babyna? Ke da service sai dai a gidanki, kafin lokacin mana. Ki tausayawa maraya mana, kin ga yau ma ban da lafiya, mura yamin mugun kamu, na san da kina kusa rashin lafiyan zai zo da sauƙi."
Wani tausayin shine ya kama Nuratu jin bashi da lafiya tace.
"Allah sarki Allah baka lafiya. Ni dai sai nayi service dan har sunan mu ya kusa fitowa a second batch."
"Dan Allah fa maganar gaskiya Babyna? Har lokacin ya kusa."
"Dagaske nake Allah."
'Na shiga uku.'
Dr Awwab yace a zuci da ya fito har fili ya saka Nuratu yin dariya ƙasa ƙasa, shima dariyar yayi jin ta ji yace.
"Allah yasa kar su tura min ke wani garin can mai nisa su duba aure, balle ma inshaAllah ba za suyi haka ba tun da mun sanar da su akwai aure."
Ba tayi magana ba dan ita ma bata son yin nisa da gida. Jin shurunta ya saka Dr Awwab cewa.
"To Allah kaimu lokacin, mu ga ina aka tura ki sai mu san abin yi."
Ameen ta amsa da shi yace.
"Zan ƙoƙarta in fita office."
"To a dawo lafiya. Ka biya ka gaishe min da Hanan."
"An gama ranki daɗe."
Yace Nuratu tayi murmushi ta kashe wayar ta miƙe, bathroom ta shiga tayi brush ta fito falon ta samu Mami.
"Mami breakfast ɗina?"
"Kina kwance zan dafa miki? Ki je ki dafa abin ki."
Kitchen Nuratu ta wuce ta tafasa indomie da kwai ta dawo falon ta zauna ta hau ci.
...
Satin biyu kafin hakan wata ranar juma'a Dr Awwab ya zo ya taimaka mata ta bada shaidar aure, ta canza sunan mahaifi zuwa sunanshi dan yin hakan shi zai saka su turata guri mafi kusa ko garin mijinta.
***
Ƙarfe shida ya kama hanyar dan so yake ya isa da wuri ya dawo komin dare. Wajen ƙarfe sha ɗaya ya shiga cikin ƙasar ya kama hanyar garin da ba zai taɓa mantawa. Abubuwa da yawa suna dawo mishi na shekaru da ya shuɗe. Bai kyauta ba, bai kyautawa rayuwarta ba a matsayinta na marainiya babu uwa babu uba. Nadama da dana sani ne yake shiga zuciyarshi dangane da abinda da ya aikata mata da kwanshi.
Ya bi ruɗin shaidan da zuciya da aboki da ƙarya ya wulaƙanta jininshi da matarshi da tun haɗuwar saurayi da budurwa.
Har ƙofar gidan yayi parking bai mance ba tsawon shekaru ashirin da huɗu. Sauƙa yayi ya tsaya kofar gidan tare da sallama. Musalle da yake ɗakinshi ya amsa ya fito ya bishi da kallo.
"Yaya Muhammadu yana nan?"
Alhaji Mamman ya tambaya yana amsa gaisuwar Musalle.
"Ya fita kasuwa tun safe."
"Ko zan iya jiran shi, Baban Nuratu ne."
Alhaji Mamman ya faɗa cikin wani irin yanayin danganta kanshi da yayi da Nuratu.
"Baban Nuratu dai? Shigo ciki babu damuwa."
Musalle ya faɗa yana bashi hanya ya wuce ciki, har ɗakinshi ya shigarshi ya shimfiɗa masa darduma ya kawo masa ruwa.
"In kana saura in ƙira shi ya dawo."
Faɗin Musalle.
"Da hakan zai fi ina son in koma gida a yau."
To kawai Musalle yace ya kira Kawu Muhammadu ya sanar da shi yayi baƙo daga Damaturu, kuma a yau zai koma in zai samu ya zo.
"Bari in zo sai ka zauna min in kaji sauƙi."
Faɗin Kawu Muhammadu ta ɓangarenshi
Daga haka ya amsa da to ya kashe wayar ya sanar da Alhaji Mamman yana zuwa ya fita.
***
Maiduguri International Airport.
A hankali ya sauƙo cikin jirgin yana takawa a hankali tare da taimakon sandarshi da take tukarawa. Bayan shi Ummu da Daddy ne suka bin sa a hankali suna riƙe da jakakkunan kayansu, har suka gama fitowa suka fita a airport ɗin suka tare taxi dan wucewa gida.
Mufid sai bin garin yake da kallo da mutanen ciki yanda kowa yake gudanar da rayuwarshi hankali kwance a nutse.
'Duk su suka gurɓata mini rayuwa.'
Yace a ranshi, dan duk abinda ya samu rayuwarshi laifin kwacakom ya ɗaura akan Ummu da Daddy da kwata kwata baya sake musu fuska, baya marmarin sake rayuwanda su.
Har ƙofar gidansu mai taxi ya ajiyesu, Alhaji Kashim ya bashi kuɗinshi kafinsu ƙarasa shiga cikin gidan. A falon Ummu suka sauƙa, suka samu Aunti Humaira da sauran yayun Mufid biyu sun zo da mai bin shi da Rufaida da ƴaƴansu. Kowa ya gaishe sa ya mishi ya jiki ya amsa yana wucewa ɗaki, Rufaida ta bishi da kallo tana addu'ar Allah yasa shiriyarshi kenan.
Da daddaren ya samu baƙoncin Faisal ban da AA, hanashi shigowa falon yayi ya lallaɓa suka filin gidan duk da sanyi da ake yi ya saka rigar sanyi.
"Gaye ka ga mutuwa ashe."
Murmushin ƙarfin hali Mufid yayi.
"Sosai da taimakon Allah na taso. Ina AA ne? Babu wanda ya neme ni cikin ku, da mutuwa nayi sai dai ku zo ta'aziyya."
"Komai ya lalace MKM, bamu da gabas da yamma da tudun dafawa. AA yana asibiti ya kamu da cuta mai karya garkuwar mutum, bayan ciwon jeji da yake shirin kamashi. Ni kuma nan da ka ganni gurin kwana ma ya fara gagarana balle ci da sha."
Faisal yace cike da jimamin halin da suka tsinci kansu.
Mufid yana duban shi da haske kwan lantarki da na farin wata yace.
"To Allah dafa mana, domin ni kam bani da wani burin sake gurɓattacciyar rayuwa."
Dafa kafaɗarshi Faisal yayi.
"Anya Mufid ba alhakin yarinyar nan yake bibiyar rayuwar mu ba?"
***
Bayan dawowar Kawu Muhammadu Musalle ya wuce kasuwa dan zama masa a shagon, ya rage daga Alhaji Mamman sai Kawu Muhammadu da yake cike da mamakin ganin Alhaji Mamman bayan tsawon shekaru ashirin da huɗu. Bayan haka ma rashin mutumci da ya shuka kwanan nan akan auren Nuratu bai tsammaci ganin shi ba a daidai wannan lokaci.
"Ina sauraron ka Alhaji."
Kawu Muhammadu yace fuskarsa babu alamun fara'a babu alamun ɓacin rai dan jin da me ya zo.
...
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 43.
Pharty Bb
Wattpad phartybb.
***
"Alhakin Nuratu ke bibiyar rayuwar mu Faisal, alhakinta da na mutanen da muka cuta ne yake bin rayuwarmu da har abada ba zai daina hakan ba sai mun samu yafiyarsu musamman Nuratu, bata ji bata gani ba na cuci rayuwarta, na gurɓata mata rayuwa, na tarwatsa farin cikinta da komai nata."
Mufid yake faɗan haka da Faisal ya ji jikinshi yayi mugun sanyi. Lalle rayuwar bariki ba rayuwa bace.
"Mufid mun zaɓarwa kan mu rayuwa mafi muni, fatan mu Allah ya yafe mana, duk da wuya mu bar wasu abubuwan domin ya riga ya zama jinin jikinmu."
Girgiza kai Mufid yayi yana kallon taurarin da suka fito ɗaiɗaiku dan hazo yace.
"Na tuba Faisal, na tuba daga yin komai, burina da addu'a na Allah yafe min kura kurai na, sannan Nuratu ta yafe min abin da na aikata mata, in samu aikin yi nima in yi aure in ga nawa kwan a duniya kafin in koma ga mahalicci na, in bar iyaye na da sune duk sanadin ɓacin rayuwana."
Faisal da yake kallon Mufid tamkar ba shi yake furta kalmomin ba yace.
"Allah baka nasara Mufid, nima zan so neman yafiyar yarinyar nan."
"Ameen. Zan koma ciki akwai sanyi. Ka gaishe da AA in na ƙara jin sauƙi zan leƙo in gaishe sa."
"Zai ji da yardar Allah."
Faisal yace, anan su kayi sallama Mufid ya koma cikin falo, Faisal ya fita.
***
Kawu Muhammadu yana sauraran bayanin Alhaji Mamman har ya gama ya kara da cewa.
"Wallahi Yaya Muhammadu sharrin shaiɗanne da zuciya da kuma biyewa shawaran aboki. Dan Allah ka taya ni neman gafaran Sadiya, na san na cutarta ita da ƴata, amma wallahi nayi nadamar abin da na aikata musu. Dan Allah ka nema min gafarar su."
Ajiyar zuciya Kawu Muhammadu ya sauƙe sai lokacin ya sake fuska yace.
"To dai Alhaji Mamman taimako ɗaya zan maka shine in ƙira Sadiya in mata magana, idan amince to. In kuma ta ƙi ba yanda zan mata."
"InshaAllah za ta amince in kai ne."
Alhaji Mamman yace har lokacin zuciyarshi tana hasko masa tsantsan kamanni da su biyun suke, har da ita Sadiyar da kamanceceniyar da nasu da ita kaɗan ne.
"To zamu gwada mu gani."
Kawu Muhammadu yace ya miƙe ya fita dan kawo masa abin sha.
'Suna kama sosai.'
Alhaji Mamman yace duk da wahala da girma ya kama Kawu Muhammadu amma hakan bai ɓoye kamanceceniyar fuskar su da shi ba, duk da shi wancan kuɗi da jin daɗi ya ɓoye girman fuskarshi da shekarunshi.
Shigowar Kawu Muhammadu ya dawo da shi hankalin shi ya karɓi abun hannunsa ya ajiye. Abinci ne da kindirmo mai kyau. Kaɗan ya ci yace ya ƙoshi ya miƙe.
"Zan tafi Yaya sai na ji daga gurin ka."
"To Allah kiyaye."
A gurin su kayi musayar lambar waya kafin Alhaji Mamman ya tafi. Ji yake komai zai zo da sauƙi tun da ya samu Kawu Muhammadu kuma ya yarda da batunshi.
***
Kwanakin da suka gabata Nuratu bata samun zama dan zirga zirga da take na tafiya service in da sunansu ya fito suka turata Maiduguri kasancewar tana da aure.
Nuratu bata so hakan ba ganin sun turata Maiduguri ta sanar da Mami.
"Sai ki tare kawai kinga kin hutar da kowa."
Jin abinda Mami tace yasa Nuratu ɓata rai.
"Mami sati biyu fa ya rage, haba dan Allah ku bar ni na gama mana abun shekara ɗaya."
Rai Mami ta ɓata.
"Bana son wannan shashancin, idan har Dr Awwab ya tambayeki mafita, sannan ya buƙaci ki tare ki sanar da shi kin amince."
"Amma Mami ba ayi gaggawa ba. Dan Allah kiyi hakuri ki barni."
"Ba zan yi ba, aure ne a kan ki, umarnin mijinki za ki bi, ba na kowa ba, duk abin da ya nema ki yarda dashi ki masa biyayya."
Daga haka Mami ta shige ɗakinta ta bar Nuratu zaune da turɓunannen fuska.
Mami tana shiga ɗaki ta ƙira Rahma ta sanar da ita ta zo gida tana nemanta, ƙiran Aunti Zarah ma tayi tace ta zo za suyi magana. Dukkansu suka ce da yamma suna tafe.
Nuratu babu walwala ta wuni, Mami na lura da ita ta ƙi mata magana. Zamanta ya isheta haka ta je itama gidanta ta zauna tayi bautar aure kamar kowa, tasan Dr Awwab ya mata hakuri har tsawon wata ɗaya da wani abun bai mata maganar tarewa ba.
Da yamma Aunti Zarah da Rahma har da Aunti Hasiya suka zo, bayan Nuratu ta gaishesu ta ƙi barin gurin ko za su sako maganar su saka baki Mami ta janye kudurinta. Amma abin mamaki Mami tana sanar da su hukunci da ta yanke suka amsa.
Aunti