Follow us on social media
Showing 36001 words to 39000 words out of 148866 words
Chapter 13 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
ciki har zuwa yau da suka je dubata. Kallonta kawai yake yana sauraron ta idanuwanshi sun kaɗa sunyi jajir, ɓacin rai da baƙin ciki ne cike, ya shiga tashin hankali jin abinda ya samu Nuratu da bashi da labari.
"Ko gobe sai ka je dubata duk da jikin da sauƙi."
Kai kawai ya girgiza ya fice a ɗakin ta bishi da kallo. Ta san duk wanda yaji abin da ya samu Nuratu dole hankalinshi ya tashi. Ta hango tsantsan tashin hankali cikin idanuwanshi.
Yaya Al-ameen kasa bacci daren ranar yayi, hawaye ya zubar sosai daren ranar na tausayin Nuratu. A ranshi ya kudurta ko mai zai faru ba zai taɓa fasa niyar abinda yayi niya ba, dole ya nuna mata itama abin so ne ya share mata hawaye.
Washegari weekend da kyar Amma Jidda ta saka shi yayi breakfast kafin ya ɗauki hanyar Maiduguri, tafiya kawai yake shima baya jin daɗin jikinshi dan rashin baccin da bai samu ba. Karfe sha ɗaya ya shiga cikin asibitin da Amma Jidda ta bashi address ɗin. Garin anyi ruwa, ɗauke da iska mai sanyi yake kaɗawa ga garin ba rana a lumshe.
Allahamdulillahi sauƙi sai samuwa yake, jiki ya fara warwarewa sai dai har yanzu bata son cikin hayaniya, sai kuma in ta zauna ita ɗaya sai tunani da yake haddasa mata damuwa daga nan kuma sai kuka da ciwon kai. Dr Awwab duk safiya da rana da yamma yana zuwa dubata kamar kullum. Sun saba tana sakar mishi fuska, shine namiji na farko ta ji ya burgeta bayan abubuwan da suka faru, tana ganin mutuncinshi dan taimakon da ya mata ta dawo hankalin kanta.
Yau weekend da safe bayan ta yi wanka dan tana iya yin wanka da kanta yanzu, kullum sai tayi kuka in ta zo gasa kanta dan baƙin ciki da yake ziyartan zuciyarta in ta tuna shikenan Mufid da abokansa sun ɓata mata rayuwa. Ji take zata kashe Mufid da za ta ganshi, ta tsane shi ta tsani komai nashi.
Wanka ta yi ta fito ta saka kayan asibitin riga da wando, Mami tana zaune tana jiranta har ta gama tana shirin kwanciya, Dr Awwab ya shigo yau tun safe bai shigo ba har take tambayar Mami yau bai zo ba.
Harara ta watsa mishi lokacin da ya iso wajenta ta kawar kanta tana ɓata rai. Duk ya lura da hakan ya tsugunna ya gaishe da Mami ta amsa kafin ya ƙarasa kusa da ita sosai yadda za taji shi.
"Sorry Noor amin afuwa."
Kafaɗa ta maƙe alamar a'a, murmushi yayi da yake karɓar kyakkyawar fuskarshi.
"I said I'm sorry. Hanan ce ta samun rigima sai ta biyo ni."
Sai lokacin ta juya ta kalleshi taƙi magana ya ɗaga mata gira ɗaya, ta ɗauke idanuwanta cikin nashi.
"Muje ki ganta."
Yace da dan yana son ta fara fita kuma tana yin doguwar tafiya ya faɗa haka. Ƙi tayi hakan yasa ya kalli Mami.
"Mami ki mata magana ko za taji."
Murmushi tayi tana mamakin diramarsu.
"Tashi Nuratu ku je kin ji. Yanzu fa ki ke tambayana bai zo ba, kuma yazo ki ƙi kulashi."
"Ni dai Mami."
Nuratu tace haka kawai ta je matarshi ta gansu ta zata wani abu ne tsakanin su da har ta saka rigimar biyo shi.
"Please Noor."
Dr Awwab yace dole ta miƙe ta ɗauki Baby hijab ta saka suka fita tare. A hankali take tafiya suna wuce ɗakuna ɗakuna duk tsoro ya kamata dan rabon da ta ganta a waje har ta manta, da za'a tambayeta ina take ma za tace bata sani ba.
Waje taga sun nufa ta kalle shi hankalinshi yana kan hanya.
"Ina za muje?"
"Office ɗina, ai tana can."
"Ba zan iya ba."
Tace tana tsayawa ya kalleta.
"Please ki daure mu ƙarasa."
Ganin zata koma ya sashi shan gabanta yana saka idanuwansa cikin nata data marairaice su.
"Please Noor nan kusa ne fa, kuma ba jimawa za muyi ba."
Ji tayi ta kasa masa mutsu ta juya suka ci-gaba da tafiya. Har suka fita tana bin filin asibitin da kallo mai kyau cike da shuke shuke anyi ruwa garin yayi kyau yayi luf dashi. Ɓangaren ofishin likitoci suka nufa.
Shigowar shi kenan da motar shi ya hango wata kamar Nuratu da Dr suna shiga floor da yake ɗauke da ɗakunan likitoci. Da sauri yayi parking ɗin motarshi ya bi bayansu.
Abin mamaki da Nuratu ta tarar cikin ofishin yarinya ƙarama ƴar shekaru biyu, kyakkyawa mai hasken fatar mahaifinta, kama suke sosai da Dr Awwab, sanye take da gown ja kanta da ribbon kala kala an mata kitson kalaba.
Kallon yarinyar Nuratu tayi ta kalli Dr Awwab ta sake kallonta yarinyar da take hannun Nurse da Dr Awwab ya bata ta kula da ita kafin ya wuce wajen Nuratu.
"She's My Baby. Hanan."
Sai Nuratu ta ji wani iri ta miƙa hannu ta karɓi yarinyar.
"Za ki iya?"
Faɗin Nurse ganin Nuratu itama kamar bata da lafiya, Nuratu ta ɗaga kanta ta karɓi Hanan tana zama.
Shima Dr Awwab zama yayi saman kujera yana sallamar Nurse ta fita.
"Ina mamanta ta yarda ta biyo ka?"
Faɗin Nuratu tana ma Hanan wasa yarinyar ta shiga ranta.
Kafin Dr Awwab ya bata amsa su ka ji knocking ya kai dubanshi kofa ya ba da izinin shiga, da kallo ya bi wanda ya shigon.
"Ƙanwata!"
Faɗin Al-ameen da yayi ƙoƙarin ƙarasawa wajen Nuratu.
"Yaya Al-ameen."
Tace cike da mamakin ganinshi a wannan lokacin, kwata kwata ta mance dashi da wani abu da ya shafesa.
Dr Awwab ido kawai ya zuba musu wani abu yana taso masa ganin kallon da Al'ameen yake bin Nuratu da shi, ganin ba zai jura ba ya sashi miƙewa yana shirin fita Al-ameen ya miƙa masa hannu su kayi musabaha, da kyar ya iya sakin fuska suka gaisa.
"Mu je ko?"
Dr Awwab yace yana karɓar Hanan, haka yasa Nuratu miƙewa ta dubi Yaya Al-ameen da ya kasa faɗin komai.
"Yaya Al-ameen mu je wajen Mami."
A kofar ɗakin da Nuratu take suka rabu da Dr Awwab ya wuce ɗauke da ƴarshi data saka kuka sai ta bi Nuratu.
Bayan sun shiga ɗakin Nuratu ta ƙarasa wajen Mami, Al'ameen ya shigo. Mami tayi murnan ganin shi suka gaisa yace ya mai jiki tace da sauƙi. Har yamma yana nan duk yadda ya so ya samu guri shi da Nuratu su gaisa abin ya gagara, har biyar kafin yace zai koma.
***
Dr Awwab bai wuce gidanshi ba ya wuce family house nasu, da ƙannen shi ƴan biyu mata ya fara cin karo suka karɓi Hanan da ta hakura ta yi shuru. Babban falon mahaifiyarshi ya isa ya samu tana gishinkiɗe ya rissuna yana gaidata. Cikin sakin fuska da walwala ta amsa. Mace ce da kallo ɗaya zaka mata ta kalli dattako da kamala a tattare da ita.
Yanayin damuwa ta gani kwance saman fuskar ɗan nata da kwata kwata bata son haka. Shekaru biyu kenan suna ƙoƙarin bashi dukkan farin ciki da mance damuwar da ya shiga ta dalilin rashin matar shi abin son shi da yayi a haihuwar Hanan.
Cikin yaren fillacin ta canza harshe take tambayarshi lafiya. Girgiza kai yayi shi kan shi in da za'a kwana ana tambayarshi ba zai ce ga damuwarshi ba, kawai dai ya ji ba daɗi irin kallon da tsakanin Nuratu da wanda ta ƙira yayanta, haka kawai ya ji ba yaya uwa ɗaya uba ɗaya suke ba. In da hakan ta kasance da ya ga kama ko jini a jikin junansu.
Ganin kamar zai saka Ummi damuwa ya miƙe ya mata sallama zai wuce.
"Ummi zan wuce. Hanan zata zauna kwana biyu tare da ku."
Ta san da damuwa tare dashi amma yaƙi sanar mata, bai cika barin Hanan ta zauna a gida ba kullum tana maƙale dashi dan ko da ta fara wayo ya ɗauke abarshi suka koma gidanshi, sai dai ya kawota su ganta in an ce ya kawota hutun kwana biyu ji yake kamar za'a rabasu.
Kai kawai ta ɗaga mishi har ya fice. Bai biya inda su ƴan biyu su ka yi da Hanan ba ya bar gidan.
***
Washegarin da safe Col. Ahmad ya zo gaishe su Mami tare da breakfast da ya saka aka haɗa musu. Nuratu dai ta sanshi kuma har lokacin taƙi sake mishi fuska. Mami bata san komai ba ido kawai take binshi da shi, kuma yaƙi basu fuskar tambaya dan da zaran yazo ya tambayi mai jiki yake tafiya.
Haka yau ma suna gaisa da Mami ya tambayi jikin Nuratu tace da sauƙi ya ajiye musu abincin da ya kawo ya musu sallama. Nuratu ko kallon inda yake ba tayi ba, shi kam ma dariya take bashi sai da ya murmusa.
A yau da karfe goma suka samu ziyarar Aunti Zarah da Rahma sun zo duba Nuratu. Allahamdulillahi yadda su kaga ta samu sauƙi abin ya musu daɗi. Suka wuni har yamma kafin su fara shirin tafiya.
***
Sati biyu kenan Mufid ya rasa mafita ina zai ga Nuratu, ya je makaranta babu ita babu labarin ta, har ana shirin fara exam. Ya je gidansu har yanzu da kwaɗo rufe. Rufaida kuma duk hanyar da zai haɗasu ta toshe balle ya tambaye ta inda kawarta take.
Ita kanta Rufaida ta je asibiti ta je gidansu Nuratu duk bata samun su, abinda ya zo ranta shine ko sun bar garin, gashi ta gagara ƙiran wayarta dan tafi son suyi magana gaba da gaba.
Da daren Rufaida ta fito wajen su Hajiya Batul, zata shiga ɓangaren su wajen ƙarfe goma sha ɗaya sun gama hira, abinda ya jimarta ma wani film suke kallo da aka saka a Mbc Bollywood mai suna Hichki, shi ya sata zama har aka gama kafin ta fito.
Mota ta gani yayi parking ta juya ta kalli mai fitowa ta ga Mufid ne, kai ta ɗauke ta wuce ciki da sauri, bata kai ga ƙarasawa ɗakinta ba ta ji an fizgota ta juya a fusace.
"Ni fa ba ƴar iska bace da zaka din ga taɓa ni. Dan ina matsayin ƙanwarka hakan bai baka damar shiga cikin rayuwata ba."
A buge yake yasha yayi tatil, burinshi tunanin Nuratu ya fita a ranshi ko zai samu yana runtsawa domin har cikin baccin shi zuwa take.
"Bari in nuna miki halinmu mu ƴan iska."
Mufid yace cikin maye ya fara jan Rufaida zuwa ɗakinshi. Ihu ta fara ya rufe mata baki ta fara kai mishi duka. Ummu tana bangaren Daddy abinda Rufaida ta manta da shi kenan domin duk ranar girki acan mai girki rake kwana.
Tsakiyar ɗakin ya wurgata ta tashi da sauri za ta gudu ya sakawa ƙofar mukulli ya zare mukullin ya jefa a aljihunsa. Bugun kofar take tana kuka jikinta duk rawa yake.
"Dan Allah Mufid ka buɗe min ƙofa. Ummu ki zo ki cece ni."
Bathroom ɗinshi ya shige ya barta anan, wanka yayi duk cikin magagin maye ya fito ɗaure da towel Rufaida na ganin haka ta ƙara sautin kukanta tana bugun ƙofar tare da ƙiran duk sunan wanda ya zo bakinta dan neman taimako.
Mufid bai kulata ba ya juyo ya ɗauki kayan bacci ya saka ya koma kan gadon ya kwanta.
"In kin gama ihunki ki zo muyi magana, amma ki tabbatar zaki bani amsa gamsashshiya, sai in buɗe miki ƙofar."
"Ni dai dan Allah ka buɗe min ƙofar in fita."
Rufaida tace cikin kuka.
"Baki yarda ba kenan. Bani da lokaci bacci nake ji."
Yace ya mayar da kanshi ya kwanta.
Kamar mai tsoronshi dama tsoron take ji ta matsa kaɗan.
"Gani nan."
"Matso dai mana."
Mufid yace yana ɗago kansa daga kwancen wanda yake masa nauyi ya kalli Rufaida.
....
#vote
#comments
#share
MADUBIN GOBE 20.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
"Baki da niyar tafiya kenan kin fi so ki kwana anan."
Mufid yace yana maida kanshi ya kwanta. Ganin haka da sauri Rufaida ta matsa bakin gadon.
"Gani na zo."
Jin muryarta kusa dashi ya sashi buɗe lumshashshun idanuwansa da suke cike da maye suka canza kala.
"Ki sanar dani ina Baby take, na san kin san komai a kanta."
"Wace Babyn kuma?"
Ta tambaye shi duk da tasan akan wa yake maganar.
"Kin fini sanin ta. Babyna Nuratu."
"Ni ma ban san inda take ba."
"Au haka ne, haka ki ka ce."
Yace yana miƙewa zaune.
"Eh wallahi Mufid ban san ina take ba, ko makaranta bata zuwa, na je asibiti ma bata nan, na je gidansu a kulle ina tsammanin an turasu babban asibiti ko sun bar garin."
Shuru Mufid yayi kamar ba zai yi magana ba har Rufaida ta dinga rantse mishi.
"Shikenan ta shi ki je na baki aikin nemo min in da take in ba haka ba in baki mamaki. Mukullin yana cikin kayan dana cire yana bathroom."
Da sauri Rufaida ta wuce ciki ta ciro mukullin ta buɗe ta fita. Ɗakin Ummu ta wuce bata nan anan tayi kwanciyarta bayan ta sakawa kofar key. Da kyar ta iya bacci dan firgita tayi tai gani take tamkar zai mata.
***
MAIDUGURI.
Washegari Dr Awwab ƙarfe takwas a gidansu ya same shi. Ummi da ido kawai ta bishi, kanshi sunkuye a ƙasa.
"Ummi na kasa bacci ne wallahi."
Yace yana zama.
"Naga alama. Ga ta nan bacci take bata farka ba."
"Zan leƙa asibiti in dawo."
Dr Awwab yace ya miƙe ya isa kan gadon Ummi ya sumbaci kumatun Hanan dake bacci ya fita, sai da yayi breakfast kafin ya fita a gidan. Kai tsaye asibitin ya wuce ya hau aikin shi bai leƙa wajen Nuratu ba.
***
"Ina kuma za ka kai wannan abincin haka Ahmad?"
Umma ta tambayi Col. Ahmad da yasa aka haɗa masa breakfast mai rai da lafiya aka jera mishi a gabanshi.
"Asibiti zan kai Umma."
Yace yana murmushi.
"Wato har yanzu baka cire kan ka cikin abinda babu ruwanka ba ko?"
"Umma dai taimako nake."
"Wani irin taimako? Mahaifinka nan yau kwana nawa da tafiyarshi ka kasa binshi ka duba jikin shi ka tsaya wajen wanda basu san ma kana yi ba. To wallahi kaji na rantse ka shirya ka bi bayansu ban amince ka dawo ba sai in har ya samu lafiya ko hutunka ya ƙare. Kai kana zaune ba aure sa'anninka duk sunyi aure wasu da ya'ya biyu, du bi fa Suwaiba itace ƙarama amma da aurenta har da ƴa. To wallahi na gaji da rashin zamanka ba aure, ido kawai na zuba maka in ga gudun ruwanka."
"Kiyi hakuri Umma zan yi, lokaci ne bai yi ba."
Col. Ahmad ya tari maganganunta da sauri ta dakata tana kara haɗa rai.
"Na dai faɗa maka, ka bishi in ka dawo muyi maganar auren."
"Shikenan Umma zan yi ƙoƙarin yin hakan."
Daga haka Col. Ahmad ya miƙe ya fita tare da warmers ɗin da aka haɗa masa abinci. Daga gida asibiti ya nufa ya samu Mami bata nan daga Munirat sai Nuratu dake wanka bata fito ba. Bayan sun gaisa da Munirat yake tambayarta mai jiki tace da sauƙi,
yace Mami fa tace ta fita.
Sai da ta gama shiri cikin bathroom ta fito cikin doguwar abaya da tace zata saka ta gaji da sa kayan asibiti. Waje ta fito dan yunwar cikinta ta samu Col. Ahmad. Bata kalli in da yake ba ta nemi guri ta zauna tana haɗa rai. Lokacin da ta nemi taimako bai mata ba sai yanzu zai zo yana bibiyarta to mai zai mata ko za ta mishi.
Murmushi kawai Col. Ahmad yayi da bai cika yi ba sai ya kama ya miƙe ya nufi gurinta, ganin haka Munirat ta miƙe ta fita dan basu guri tsammaninta duk wata alaƙa ce tsakanin su.
Nuratu da ta ga sun rage su biyun zuciyarta ya fara bugawa ta fara waige waige neman hanyar gudu. Ganin da gaske yake zai iso gurinta ta ce.
"Kar ka ƙaraso dan Allah."
Dakatawa yayi daga in da yake yana hango tsantsan tsoro a tattare da ita hakan yasa ya tsaya yana dubanta.
"Wata kila daga yau ba za ki ƙara ganina ba sai wani lokaci."
Bata mishi magana ba sai ido da ta zuba mishi yaci gaba da faɗin.
"Please ki daina fushi dani akan na kasa kubutar da rayuwarki daga waɗancan azzaluman, Allah ya riga ya rubuta hakan zai faru, ƙaddara ce, amma Insha Allahu na miki alƙawarin ɗauka miki fansa bisa abinda suka aikata miki. Zan yi tafiya na ɗan wasu kwanaki, fatan kafin na dawo kin ƙara samun sauƙi."
Kasa ce mishi komai tayi ya nufi hanyar waje ganin bata da niyar mishi magana.
"Allah kiyaye hanya."
Ya tsinci muryar ta da saurinshi ya juyo ta kawar kanta gefe. Murmushi yayi ya amsa da amin kafin ya fita.
Munirat tana ganin ya fita ta koma ɗakin, suna zaune Mami ta dawo ɗauke da breakfast da ta sayo musu. Ganin Warmers ya sata tambayar Munirat waya kawo duk tsammaninta Dr Awwab ne, tace a'a wani ne ita ma bata sanshi ba.
Mami ta kalli Nuratu ganin kamar tana cikin damuwa ya sata fasa tambayarta wanene ko ta sanshi. Abincin suka buɗe ferfesun kan rago ne sai fankasu da ya soyu mai kyau, Munirat da Nuratu su kaci, Mami kasa ci tayi.
"Mami! Dr ya zo ina bacci ne?"
Nuratu ta tambaya tana zuba magungunanta a baki.
"A'a ban sani ko kina wanka ba."
"Bai zo ba."
Cewar Munirat tana tattare gurin da suka yi breakfast.
Ba wanda ya ƙara magana Nuratu tayi baya ta jingina da gini tana tunanin mai ya hana Dr Awwab zuwa yau har gurin ƙarfe goma. Ranar haka ya wuni har yamma bai leƙa wajen Nuratu ba, so yake ya yakice kanshi daga inda zuciyarsa yake son kanshi.
Haka ya gama aikinshi ya wuce gida.
Hanan da take saman cinyar Hussaina tana bata kunu ta dinga miƙa masa hannu ya ɗauketa, hannu ya sa ya ɗauketa sama yana kai mata kiss kumatunta.
"My love nayi missing ɗinki."
Yace yana zama saman kujeran falon ya ajiyeta saman cinyarshi sai baki take buɗe masa da hakwaranta biyu a baki da jagwalgwalon maganarta.
"Ina Ummi?"
Dr Awwab ya tambayi Hussaina da take ƙoƙarin barin gurin.
"Tana falonta."
Miƙewa yayi ya nufi cikin falon bayan sun gaisa yayi alwala ya fita, sallah yayi ya dawo ya ɗauki Hanan suka tafi gidansu.
***
Washegarin zuwan su Aunti Zarah, Hasiya da Rukayya tare da Yaya Al-ameen shi ya mantar da Nuratu komai. Ba laifi ta shiga cikinsu sun yi hira, kasancewar sun san matsalarta suka rage surutun sai sama sama da suke yi.
"Muje waje ƙanwata."
Yaya Al-ameen yace da Nuratu da ya sata kallon shi ya ɗaga mata kai alamar roƙo ta dubi sauran kowa yana harkar gabanshi.
"Mu je."
Ta miƙe ganin ya miƙe ya fita ta bi bayanshi, da kallo suka bisu sauran.
Marasa lafiya da suka fara samun lafiya suna filin asibitin tare da masu kula dasu. Ƙarƙashin wani bishiya ya sama musu suka zaune saman kujeran wajen. Idonshi yana gefe ya zubawa bishiyar dake gefensu ido.
"Ƙanwata ya kuma mu ka ji da abinda ya faru? Bana son tada abinda ya wuce amma ya zamemin dole ne, fatan