Follow us on social media

Showing 123001 words to 126000 words out of 148866 words

Chapter 42 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

47

zagayeta da hannunsa ya rumgumeta, ajiyar zuciya ya ke sauƙewa akai akai. Allah ya nuna masa ranar da Nuratu ta buɗe baki ta ce tana sonshi. Abu ɗaya zai hanasa nuna mata tsantsar son da yake mata yau. Kusan mintunan su biyar a haka ta dago kanta ta ga idonsa a rufe.

"Doctor karmu manta da Hanan yauma."

Sai lokacin ya buɗe ido suka sauka cikin nata, sakinta yayi kafin ya miƙe.

"Bari inje in ɗaukota."

Kai ta ɗaga masa ya fita.
Ita ma ta shi ta yi ta ci gaba da aikinta. Yau ranar na musammanne a gareta. Ita kanta ta manta kanta wacece lokacin da take faɗa masa kalamannan.
Kusan mintuna ashirin ya dawo da Hanan, da gudu ta nufi Nuratu suka rumgumi juna. Ɗakinta suka wuce ta canza mata kaya suka fito.
Abincin da ta haɗa bayan fitarsa ta gabatar musu, suna ci Hanan na bata labarin islamiyya, Nuratu mamakin surutunta take, ita dai taga alamar Dr Awwab ba shi da surutu, sai dai ko mahaifiyarta ta biyo. Sai lokacin taji tana son sanin wacece ita.

"To aku sarkin surutu, na nemo miki driver, daga gobe zai fara kai ki ya ɗauko ki."

"Driver kuma Daddy."
Tace tana kallon mahaifinta ta kalli Nuratu tana turɓune fuska.
"Aunti ni dai bana son driver."

Rankwashi ta ji saman kanta ta dafe gurin tana matso hawaye. Harararta yayi.
"Ni fa bana son taɓara, yanzu zan bubbugeki kin sani. Ni kike so na zama driver naki, to bazan iya ba, nima ina da aikin yi."

Shuru tayi ta haɗiye kukanta ta matsa gurin Nuratu. Ɗaukarta tayi ta ɗaura saman cinyarta ta share mata hawayenta.
"Daina kuka kin ji, Daddy yana da aikin yi da safe da yamma, kuma idan ya ce zai ɗauki nauyin kai ki makaranta zai takura. Ki bari driver yana kai ki kinji."

Kai ta ɗaga tana murmushi.
"Na hakura Aunti."

"Yawwa My Baby."

Daga haka Hanan ta miƙe ta basu guri. Kallon Dr Awwab ta yi tana ɗaga masa gira ɗaya alamar kallon fa.
Murmushi ya yi yana shafa sajensa ya kashe mata ido ɗaya.

"Ina son tambayarka Doctor?"
Ta faɗa masa.

"Ina jinki My Baby."

"Dangin mahaifiyar Hanan fa? Suna ina."

Abin mamaki sai taga ya haɗa rai yana miƙewa tsaye.
"Sunanan. Zan je in dawo."

Baki sake ta bisa da kallo, mamaki ƙarara shimfiɗe a fuskarta. Ko me abun ɓata rai kuma? Bata da amsa ya sata miƙewa ta fara gyara wajen.

Sai dare kusan takwas ya dawo har lokacin babu fara'a a fuskarsa, abincin ma kaɗan ya ci ya wuce ɗakinsa ya barsu. Nuratu ma kasa ci ta yi, ta jira Hanan ta kammala ta gyara gurin, ɗaki ta wuce ta mata shirin wanka ta kwantarta, kafin ta fito ta wuce ɗakinta, wanka ta yi ta shirya cikin kayan barcinta masu kyau, lungu da sako ta bi da turare, kafin ta wuce ɗakin Awwab.
Samu ta yi yana aiki a laptop ɗinsa, bakin gadon ta ƙarasa ta zauna gefensa. Duk yana lura da ita ya basar, kusan mintuna uku suna haka, ganin shurun yasa Nuratu tashi ta hau gadon ta kwanta tare da jan bargo tana rufe rabin jikinta. Juyawa yayi ya kalleta ta juya masa baya, aikinsa ya ci gaba da yi kusan mintuna talatin ya gama ya ajiye laptop ɗin saman bedside drower ya miƙe. Bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito bai saka komai ba sai boxer ya feshe turare ya hau gadon.
Bedside lamp ya kashe ya gyara kwanciyarsa tare da rumgumo Nuratu cikin jikinsa, ita ma ba tayi barcin ba har lokacin, kwanciyarta ta gyara a jikinsa, a tare suka sauƙe numfashi. Shuru kusan mintuna biyar.

"I'm sorry please Doctor."

"Is ok My Baby."
Yace yana karanto musu addu'ar barci. Haka barci ya kwashesu.

...

Washegari bayan sun gama breakfast ta masa rakiya zuwa compound ya ce.

"Ƙarfe sha biyu zan dawo mu je gidan Ummi da Ammi."

"To Allah dawo da kai lafiya."

"Ameen My Baby."
Ya ce ya shafa kumatunta kafin ya shiga ya kunna motar yana barin wajen.

Ayyukanta ta gama ta haɗa miyar allayahu da kifi sannan cous cous sai kunun gyaɗa mai kysu da ta dauraye da nono, wajen sha ɗaya ta gama. Abbanta ya ƙirata suka yi maganar da yake son faɗa mata, sun jima suna wayar kafin ta kashe.
A gaggauce ta shiga wanka, har lokacin bai dawo ba. Cikin doguwar rigar shadda ruwan ƙwanduwa ta shirya kanta, zama tayi ta tsara kwalliya marar hayaniya, ta feshe jikinta da turare, tana cikin ɗaura ɗankwali ya shigo.

"Masha Allahu."

Ya furta yana ƙarasawa wajenta. Ta cikin mirror suka haɗa ido ya mata murmushi ta mayar masa da amsa ta ci gaba.

"Sannu da zuwa."

Jikin mirror ya tsaya ya fuskanceta.
"Kina da kyau kuma kinyi kyau."

"Na gode, sai ka yi sallah zamu je."

Kai ya jinjina mata.
"Da sauran lokacin sallah, saura mintuna goma sha biyar, kuma zai ishemu mu isa. Mu je kawai."

To tace ta gama ɗaurin ta yafa gyalenta Babba ta ɗauki handbag ɗinta. Shi dai bin ta kawai ya ke da ido, tasan dressing wadda ya dace da ita.

"Mu je to."

Tace yayinda da take saka takalminta memai tudu kaɗan. Hannunta ya kamo suka nufi waje, har tsakar falon ta tsaya tana miƙa masa handbag ɗinta.

"Zan ɗauki abubuwa Please."

Da mamaki ya kalleta sai dai bai tambaya ba, fahimtar hakan yasa marairaicewa ta ce.
"Please mana."

Karba ya yi ba musu yayi gaba ya barta. Kitchen ta wuce da sauri ta ɗauki babban basket ɗin da ta zuba komai ta fito. Tun da ta fito da kallo ya bita, hankali da tunanin da tayi amfani da shi dan kyautatawa mahaifiyarsa ya yi mutuƙar burgesa. Wani sonta da mutuncinta ya ƙara girma a idonsa.
Kujeran baya ta buɗe ta saka tana komawa gaba ta shiga, motar ya ja su na fita a gidan, mai gadi ya kulle.

Sai da su ka hau titi ya ɗan juya ya kalleta, hannunta ya kamo.

"Thank you Babyna, haƙiƙa nayi dace a duniyata da Allah ya haɗani da ke har ya mallakamin ke matsayin mata, mace mai nutsuwa, haƙuri, tunani da hangen nesa duk ƙarancin shekarunki. Ina sonki sosai, ina fatan Allah ya sa ki zamto uwargidana a gidan Aljannahtul Firdausi."

Da murmushi saman fuskarta tace.
"Ameen Ya Allah. Daga Mamin Hanan sai ni dai."

Kallonta ya yi ya maida hankalinsa kan titi, kamar ba zai yi magana ba can ya ce.
"Kowa da matsayinsa a zuciyata. Ki amsa da ameen kawai."

Bata daddara ba a dadare ta leƙa fuskarsa tace.
"Na amsa, amma ai ita ma matarka ce, kuma nasan kunyi zaman daɗi da ita. Idan aka ba ka zaɓi fa?"

Kusan mintuna biyar ya yi tamkar bai ji ta ba. Mamakine ya kamata da kwata kwata baya son tuna baya ko wani abun da ya shafe su. Ta buɗe baki za ta basa haƙuri ta ji yace.

"Hakane kam, munyi zaman lafiya da Nusaiba, kuma har yanzu ina yaba kyautatawarta da soyayyarta gareni. Ina mata fatan samun sakamako mai kyau. Zaɓi kuma idan aka bani dukkanku zan so ku kasance matana a Aljannah. Amma matsayi a zuciyata kowa da nasa, saboda kowa da yanayin yadda na fara sonsa duk da silar son gaba ɗaya tausayine. Bayan aurena da Nusaiba na fara sonta sakamakon cikin Hanan da ya bayyana jikinta, duk da ita tun farko haɗuwarmu na fahimci tana sona sai dai kunya ya hanata nunawa, taimako da kyautatawa rayuwarta da nake ta kamu da sona amma haka ta danne, babu batun sonta a raina mu kayi aure, amma kyautatawa, kulawa da tausayi yasa ni fara sonta ga kuma cikin Hanan. A haihuwa na rasata, rashi na har abada kamar yadda na sanar miki. Amma ke..."

Ya ƙarasa maganar yana kallon Nuratu da ta kura masa ido, murmushi ya yi yana mayar da hankali ga tuƙinsa. Ita dai ba haka ta so ba, ya ci gaba da bata labarin rayuwarsa da Nusaiba, ya faɗaɗa mata ba a dunkule zai bata ba.

Iska ya furzar ya ci gaba da cewa.
"Amma ke shigar ba shiri ki ka mini, ki ka ma zuciyata bake bake ki ka hanani runtsawa. Ranar da na fara ganinki tausayinki ya kamani, na kasa barci kullum cikin tunaninki, halin da ki ke ciki, zafin da ki ke ji a zuci. Idan za ki iya tunawa akwai lokacin da tsawon sati biyu na kauracewa zuwa gurinki a asibiti, to wallahi so nake na rarrashi zuciyata akan ki, amma ina na kasa. Tun ina iya ɓoyewa Ummi har na kasa, duk zurfin cikina haka na sanar mata na samu macen aure duk da ke ban faɗa miki ina sonki ba. Ta yi mamaki ganin duka duka shekara biyu da rasuwar Nusaiba, haka ta yi ta bani baki dai tana ƙarfafa mini gwuiwa. Ɓangarenki kuma yadda kika nuna baƙya son aure yanzu ya ƙara tada hankalina, duk rashin son takuwara mutum a rayuwata haka ki ka sani na fara takura miki. Ƙarshe dai ban hakura ba har na mallake ki, ga ki gabana. Kinga kuwa kowacce da matsayinta a raina."

Dogon numfashi Nuratu ta sauƙe tana ɗaura kanta saman damtsen hannunsa.
"Allah ya ji kanta ya gafarta mata."

"Ameen ya rabbi."

Ya furta can ƙasan maƙoshi. A haka suka ƙarasa gidan Ummi, da taimakonsa ta shigar da basket ɗin. Da sallama suka shiga falon, kullum a gyare fes yana ƙamshi. Hassana da take kitchen ta fito ta amsa tana ƙarasawa wajensu ta rumgume Nuratu.

"Sannu da zuwa Aunti. Ya hanya?"

"Lafiya ƙalau. Ya gida?"
Dan ta kasa tantance Hassana ko Hussaina.

Da murmushi Hassana ta masa tana sakinta ta matsa ta gaishe Awwab ta karɓi basket ɗin hannunsa.

"Mu je sama wajen Ummi. Ina Hussaina."
Ya tambayeta.

"Tana can ita ma."

Ita ta musu jagora har falon Ummi. Jin masu sallamar ta faɗaɗa fara'arta tana musu sannu da zuwa. A kunyace Nuratu ta gaishe da Ummi ta amsa tana tambayarta gida. Hassana da Hussaina duk sun bi sun dabaibayeta suna mata hira, dan ma Hassana ba ta da surutu. Ummi da Awwab hiransu suke. Sallar azahar da aka ƙira ya sa su miƙewa suka sauƙa ƙasa dakin ƴan biyu da Nuratu, Dr Awwab ya wuce masallaci. Bayan ya dawo ya ƙira Hussaina ta zuba musu abincin shi da Ummi wanda Nuratu ta kawo, sauran kuma ta kai musu. Sun ci sunyi santi sun yaba da girkinta, ta ji daɗi Awwab ma yaji daɗin yabon matarsa da aka yi.

Har lokacin tashin Hanan suna can, driver ma da ya ɗaukota gidan ya kaita. Tare suka shiga kitchen da ƴan biyu suka yi girki. Bayan la'asar ƙarfe huɗu suka musu sallama za su je gidan Ammi. Acan suka bar Hanan faɗin Dr Awwab ta kwana musu biyu. Ita ma yarinyar ko dan tayi kewarsu ya sa ta bata damu ba.
Kyautar turare mai tsada da ƙamshi Ummi ta bawa Nuratu, tana ta godiya haka suka fito. Gidan Ammi suka nufa. A falon suka yada zango har ta fito a kitchen. Har ƙasa Nuratu ta durƙushe ta gaisheta.

Da murmushi ta amsa.
"Amaryace a gidanmu. Sannu da zuwa."

Ita dai Nuratu kunya ya hanata motsi, kusan mintuna biyu ta miƙe ta koma kitchen, fahimtar kamar aiki take ya saka Nuratu ta shi tabi bayanta. Da ido Dr Awwab ya bita yana mamakin kuma me za tayi.
Da sallama ta shiga kitchen ɗin Ammi ta juyo.

"Kina buƙatar wani abu?"

"A'a Ammi. Bari in ƙarasa miki aikin."

"Ayi haka kuma amarya daga zuwa. Na kusa kammalawa, ki je ki huta."

Ƙarasa shiga ciki tayi ta karɓi muciyar hannunta.
"Don Allah Ammi ki kawo."

Babu musu ta sakar mata.
"Abincin kawai za ki tuka sai ki haɗa miyar kuɓewa na haɗa ruwa da komai. Mai gidan yafi son in girka da hannuna."

"To Ammi."

Tace ta zare mayafinta ta ajiye ita kuma Ammi ta ɗauki ruwa ta fita.
Abincin ta tuƙa ta rufe, ta hau haɗa miyar.

Har magriba Dr Awwab da ya samu Abdallah ya shigo da Yaya Sajeed suna hira bata fito ba, masallaci suka wuce suka dawo. A dinning ya hangota da Ammi suna jera abinci, can suka ƙarasa.

"Amarya dai ta zo ba muje ganinta ba. Wannna kayan kunyar har ina a matsayinmu na manyan yayu."
Faɗin Abdallah.

Murmushi Nuratu tayi ta durkusa ta ce musu.
"Ina wuninku?"

"Lafiya lau amarya. Ya ki ke?"

"Lafiya lau."
Ta amsa.

Ɗago ido tayi ta ma Dr Awwab kallo daya ta ɗauke tana miƙewa ta koma kitchen dan ɗauko sauran abubuwan buƙata.

"Ga abincin amarya ku zo ku ci."
Ammi ta ce tana ɗaukar abinci Abba.

"Da gaske Ammi."

Faɗin Abdallah yana zama.
Haka sauran suka zauna har Dr Awwab a table, Ammi ta kwashi na mijinta ta wuce sama da shi. Fitowar Nuratu ya sa ta ajiye abin da ta ɗauko ta bar gurin. Duk kaɗan ɗin abincin haka suka ci suna yabawa. Dr Awwab wanda ya zuba ya ɗauka ya nufi inda Nuratu take zaune. Kusa da ita ya zauna ya saka plate din abincin tsakaninsu. Bai mata magana ba ya ɗauki loma ɗaya ya kai bakinta.

"Ke kin cikawa mutane ciki da abinci ke za ki zauna da yunwa. Buɗe bakin in ba ki."

"Zan ci da kaina."

Tace tana girgiza kai ganin idon mutane. Ga kuma abin mamaki da take kallo, kammannin yayanta Muhsin a gurin wanda aka ƙira Abdallah. Abin ya ɗaure mata kai.
Hannu ta kai za ta fara ci, hanata yayi ya kai abincin bakinta, dole ta buɗe ya sakamata.
Shi ya bata yana ci har suka cinye, dama ba wani yawane da shi ba.
Shi ya ɗauke ya kai dinning ita kuma ta tattara gurin ta gyara ganin sun bar gurin.
Har ƙarfe taran dare kafin Ammi ta sauƙo ta sanar musu su hau su gaisa da Baffa. Ita ta musu jagoranci har falonsa.
Haka kawai dukkansu biyun zuciyarsu ya buga tare bayan haɗa ido da suka yi. Nuratu ne ta janye nata ta durkusa tana gaishesa. Amsawa yayi yana mata godiyar abinci da ta girka masa, can ƙasan zuciyarsa kuma wani tunani yana taso masa amma wani abu me nauyi yana dannewa.

Bayan gaisuwar kusan mintuna goma suka masa sallama, nasiha ya musu tare da ma Nuratu kyautar kuɗi, da ƙyar ta karɓa, haka Ammi ma turaren wuta ta ba ta da kayan shafe shafe. Ta rasa me zata bata ya faranta mata ranta. Tana son yarinyar tun ranar da ta fara ganinta.
Haka Abdallah da Sajeed ma kyautar kuɗi suka bata har Abdallah na cewa.

"Babban Yaya yayi missing, amma za mu kai miki ziyara."

"Dan ku cika tunbinku ba."
Awwab yace yana harararsa.

"Afuwan Baban Hanan. Za mu je ganin ɗakin ƙanwarmu ne."

"To sai kun zo na gode sosai."
Ta faɗa tana murmushin rigimarsu.

"Mune da godiya amarya."
Abdallah ya faɗa, Sajeed ma ya musu sallama kafin Awwab yaja motar suna barin harabar gidan.

Sunyi nisa a tafiya Dr Awwab ya riƙo hannunta.

"Don Allah ki sanar da ni me zan miki in nuna miki farin cikin da na ji."

Hannunta ɗaya ta ɗaura saman nasa da ya riƙe nata.
"Farin ciki ka ke? Ka godewa Allah."

"Na gode masa. Allah na gode maka da ka mallaka mini Noor a matsayin mata."

"Ameen Ya Allah."

Ta faɗa tana godewa Allah a ranta ita ma.

"Ina da wani buri Noor, ki tayani addu'ar cikarsa kwana kusa."

"Allah ya cika maka dukkan burinka My Doctor."

Ta basa amsa cikin zuciyarta tana masa addu'ar cikar burinsa.
Hira suke sama sama, barci take ji sosai. Suna isa gidan wanka kawai suka yi suka bi lafiyar gado.

...

Washegarin bayan farkawarsu ta ga ba shi da niyyar tafiya aiki sai ma shiga da fita da yake. Ta gama gyaran ɗakinsa da shine ƙarshen aikinta, tana riƙe da burner ya sake shigowa ta bisa da kallo.

"Wai lafiya Doctor?"

Ta tambayesa tana ajiye burner ta isa wajensa. Hotunan hannunsa take ƙoƙarin karɓa ya hanata ya tura cikin file ɗin gabansa.

"Ki shirya zamu fita."

"Amma lafiya? Aikin fa."

Fuskarta ya shafa yana cewa.
"Lafiya ƙalau. Baƙon bai tafi bane?"

"Wani bako kuma?"

Murmushin gefen baki ya yi yana ɗaga mata gira ɗaya.
"Baƙon da ya mini shamaki da ke. Ya hanani jin daɗin matata."

Babu shiri ta bar masa gurin sai da ta kai bakin kofa ta juya tana masa murmushi.
"Dubawa za ka yi ka gani."

Daga haka ta fice da gudu tana dariya. Shi ma dariyar ya yi yana girgiza kansa. Zai bata mamaki kuwa, tunda ita ta faɗa hakan da bakinta.

Tsaf ta shirya cikin riga da skirt na atamfa me ratsin ja da yellow, sai gold kaɗan, hakan yasa tayi amfani da kalar gold a jakanta da takalmi da mayafi. A gurin wanka ta ga bakonta ya tafi, dama tun asuba ta gani. Haka tayi wankar tsarki da wanka ta fito ta hau shiri.
Kwalliya tayi ba wani sosai ba ta fito, kusan mintuna biyar ya fito shi ma cikin manyan kaya. Sosai ya mata kyau cikin shaddar kalar gold da ya amshi fatarsa, harda hula ya ɗaura, sai ƙamshi yake. Abin na su sai ya zama tamkar haɗin baki tamkar anko suka so yi.

Falon ya kulle bayan sun fita, shi ya buɗe mata ta shiga motar kafin ya zagaya ya shiga shi ma yana kunnawa suka bar harabar gidan.
Tafiya ta ga suke sun nufi hanyar fita a gari duk da bata gama sanin garin ba.

"Damaturu za mu je fa."
Ya faɗamata.

"Da gaske."
Tace cikin murna.

"Ga alama nan."

"Na gode, zan ga Mamina."

"Uhmmm."

Kawai ya ce ya ci gaba da tuƙi. Tun Nuratu na sauraransa har barci ya kwasheta. Ba dan bata sallah ba da ya ce yayi ajiye a gurinta dan wannan barcin. Ƙarfe sha ɗaya suka isa cikin Damaturu.
Sai da ya shigar da motarsa har harabar gidan kafin ya tasheta ta hanyar shafa fuska. Baki ta tura tana yamutsa fuska. Sumbatar leɓɓanta ya yi ya ce.

"Wakeup Baby, mun iso."

Idanuwanta ta buɗe a hankali, sai lokacin ta tuna da inda take. Harabar gidan ta bi da kallo, gani take ta san gurin amma ta manta. Kallonta ta maida kansa. A shagwaɓe tace.
"Gidan Mami fa?"

"Mu fara shiga nan, daga baya sai mu je wajen Mami."

Ba dan taso ba ta sauka shi ma ya sauƙo suka nufi falon ɓangaren da suka isa. Da sallama suka shiga falon aka amsa musu.

"Amma!"

Ta ce da mamaki tana nufarta ta faɗa jikinta. Tun bikinta basu haɗu ba. Ita dai Amma kunyane ya kamata ga Dr Awwab ya shigo. Hakan yasa ta zare Nuratu a jikinta suka zauna. Gaisawa suka yi da har ƙasa ya durkusa ya gaisheta. Da fara'a ta amsa masa kafin ta ƙira Ameera ta fito ta kawo musu ruwa. Babu musu ta fito, kallon kallo suka yi da Nuratu kowanne ya ɗauke kansa. Ko Dr Awwab bata iya gaishewa ba ta wuce Kitchen. Duk ta koɗe ta rame sai duhu, babu makaranta sai zaman gida da aiki, aurenma ba'a ƙara mata maganarsa ba.
Haka ta dawo da ruwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login