Follow us on social media

Showing 81001 words to 84000 words out of 148866 words

Chapter 28 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

24

ya sa Nuratu kallonta kamar za tayi kuka.

"Maman twins zamu ɓata, ina ganin girmanki dan su twins, kin san ba wani girmana ki kayi ba, just some months kika bani."

"To yi min rashin kunya, ƙarya mu kayi ne?"

Nuratu rai ta haɗa ta kalli mai lallen da take musu murmushi tace.
"Ƴar uwa zan iya wankewa?"

Kai ta ɗaga mata tace eh. Da sauri Nuratu ta fita ta wanke lallen ja da baƙi da ya yiwa fatar jikinta kyau, ta dawo wajensu ta ɗauki jakanta da wayarta ta nufi waje tana cewa.
"Sai mun haɗu anjima."

"To a gaishe mana da Docter Babyn Docter."
Cewar Walida tana dariyar da yake bawa Nuratu haushi, hakan yasa Nuratu fita taƙi kulata.

...

"Kana so kana kaiwa kasuwa."
Rukayya tace bayan fitar Nuratu.

Da murmushi saman fuskar Walida har lokacin tace.
"Shine dai nima na gani, ji fa yana ƙiranta ta fice fit, amma yanzu da za kayi magana zata fara musaka."

Ameera da take jin su tun faruwar maganar ta kasa cewa komai, musamman da taji Dr Awwab irin maganganun da yake zubawa Nuratu ta ji ta kasa kwakkwaran motsi. Bata taɓa tsammani Nuratu za ta samu masoya haka ba har da Dr Awwab da take ganin yafi ƙarfin Nuratu ya wuce ajinta. Bata tammaci zai so Nuratu ba kai ko wasunsa ma bayan yayanta Al'ameen da ya nuna ita yake so. Bayan ma abubuwan da ya faru a rayuwarta ta ɗauka za'a gujeta a ƙyamace ta. Tun tasowarta haushinta take ji har zuwa yanzu da girmansu.

***

Nuratu a waje tayi parking dan tana son komawa bayan la'asar za su gudanar da kamu, motar Dr Awwab da Col Ahmad a waje ta gani sunyi parking. Cikin wani irin yanayi ta ƙarasa cikin gidan har cikin falon da sallama, ta samu Dr Awwab da Col Ahmad suna hira tamkar sun saba. Dr Awwab sai zuba murmushi yake Col Ahmad ne yake magana da yake saka shi murmushi.

Jin sallamar Nuratu ya sasu kallo kofar suna amsawa. Dr Awwab ido ya zuba mata idonshi ya kai kan jan lalle da baƙi da ke jikin hannunta, ji yayi tamkar ya riƙo hannayenta ya sanar da ita sun yi mutuƙar mata kyau ya bata tukuici.
Col Ahmad kallo ɗaya ya mata ya ɗauke idanuwansa tunawa da yanzu da baya ba ɗaya bane, halaliyar wani ce.

Guri ta samu ta zauna tana ce musu.
"Ina wunin ku ya hanya?"

"Lafiya lau masu biki. Ya zirga zirga?"

"Allahamdulillahi."
Ta amsa da shi ta ɗago kanta jin Dr Awwab bai amsa mata ba, idanuwansa fes a kanta yana yawo da su a jikinta. Suna haɗa ido ta watsa mishi harara ganin ya ƙura mata ido. Murmushi yayi bai ce komai ganin Col Ahmad yana gurin.

"Nuratu ƙira Mami za muyi wani magana da ke da ita."
Col. Ahmad yace ya katse shuru da kallon kallo da suke tsakanin su da Dr Awwab.

Babu musu ta miƙe ta wuce ɗakin Mami, Dr Awwab ya bita da kallo, ta masa kyau sosai.

"Ina dai wajen kuma ni babban yaya ne, ana jin kunya mana."

Maganar Col. Ahmad ya dawo da Dr Awwab hankalinshi ya juya yana sosa kanshi, bai san yaushe idanuwansa suka aikata hakan ba. Yasan dai zuciyarshi da gangar jikinshi suna buƙatar ta.
Fitowar Mami da Nuratu yasa su tashi suka zauna a ƙasa, ganin haka itama Nuratu ta zauna a ƙasa suka tsinci muryar Yaya Al-ameen yana sallama.

Bayan sun amsa ya shigo ya zauna yana gaishe da Mami, kafin ya amsa gaisuwar Nuratu yana cewa.

"Gwara da na zo ashe. Ga ni ga angon mu, in bashi amanar ƙanwata, in kuma yayi ba daidai ba in hukunta shi."

Col. Ahmad da Dr Awwab suka yi dariya, har da Mami ta murmusa ban da Nuratu da aka sakata a tunani ta haɗa rai.

"Haka za'a yi Yayanmu, na baka matsayin, ni na ɗauki matsayin Baba."
Col. Ahmad yace yana kai kallon sa kan Nuratu tana binsu da ido.

Dariya su kayi Mami tace.
"Bari in baku guri ku gama maganar, nayi mata sauran bayani daga baya."

Daga haka Mami ta tashi ta shige ɗaki ta bar su, Col. Ahmad yayi gyaran murya yana kai duban shi kan Nuratu da ta kawar kanta daga hiran su ta faɗa tunani daban.

"Nuratu!"
Col. Ahmad yace dan so yake ta fahimci bayanin da zai mata, juyawa tayi tana kallon shi ta amsa.

"Ina son ki bani aron hankalin ki, ina so ki fahimci zance na ko abin da zan faɗa miki, ba mun yi haka ba ne dan cutar ki sai dan kuɓutar da ke daga dukkan sharrin Mufid. Kuma mun san bamu miki banzan zaɓi ba, dan mun kai ki hannu mai kyau nagari wanda zai kula da dake da dukkan lamuran ki, zai share miki hawaye kuma mun ga hakan tun yanzu. Kin san dai dalilin zuwan ki Nijar gurin Kawu Muhammadu ko?"

Ya ƙarashe maganar da tambayar Nuratu, ta ɗaga kanta domin ta kasa bashi amsa tana juya maganganun shi cikin ranta ta ji ya cigaba da bayani.

"Zuwan ki Nijar gurin Kawu Muhammadu kin san duk dan mu kwacewa Mufid ne kuma allahamdulillahi mun yi hakan, kuma baki tambayi dalili ba?"

Sai lokacin Nuratu ta ɗago kanta ta kalleshi, yaci gaba da maganar shi ya sanar da ita komai tun daga barinta gidan da aurenta da aka ɗaura da Dr Awwab wanda sauran bayanan zuwan shi yau Mami ta sanar da shi, ya ƙarasa maganar yana cewa.

"Ga Dr Awwab nan shi yayi nasara cikin mu, Allah ya riga ya ƙaddara shine mijin ki, ɗaura auren ku yau tsawon wata ɗaya da sati biyu. Ni a matsayina na babban Yaya kiyi masa biyayya Nuratu, na sanki baki da wani matsala, kiyi ƙoƙarin masa biyayya Allah baku zaman lafiya. Ki cire komai a ranki ki rumgumi mijin ki ku zauna lafiya, shi ya ganki a haka yake son ki  kuma ya ji zai zauna da ke, dan haka ki cire komai ki mance da abin da ya faru."

Nuratu da idanuwanta suka cika da ruwan hawaye jin abin da suka aikata mata, zuciyarta yayi zafi ɓata ce komai ba har Col. Ahmad ya gama maganganunta shi ta ji Yaya Al-ameen ya ƙara da cewa.

"Ni kam babu abin da zan faɗa Col. Ya gama faɗin komai. Abin da zan ce ƙanwata ki yi biyayya Allah baku zaman lafiya."

"Ameen ya Allah."
Col. Ahmad da Dr Awwab suka faɗa a tare, Col. Ahmad ya miƙe yace.
"Mu basu guri su tattauna."

Bayan fitar Col. Ahmad da Yaya Al-ameen Nuratu ta ɗago kanta jin falon yayi shuru kusan mintuna, ta kalli Dr Awwab ta ga ya zuba mata. Kanta ta ɗauke tana share hawayenta wani haushinsa ne ya kamata tace.

"Ka dai na kallo na."

Murmushin sa ya faɗaɗa yana tashi a in da yake zaune yace.
"Laifine dan na kalli halal ɗina."

Tsaki ta buga ƙasa ƙasa tana miƙewa ganin zai zauna kusa da ita ta nufi hanyar ɗakinta tace.

"Ba zan taɓa karɓar auren nan ba."

"Dagaske?"
Yace ya sata dakatawa ta juya ta watsa mishi harara ta wuce ɗakinta. Murmushi yayi ya miƙe yana fita bai ji zafin abin da ta masa ba, ya shiga cikin motarshi, dan ya samu Col Ahmad da Yaya Al-ameen sun tafi.

...

Nuratu kwanciya tayi bayan shigarta ɗakinta ta fashe da kuka. Haushin kowa take ji musamman mahaifinta dashi ya jawo mata komai, da bai karɓi tayin auren Mufid ba, da babu wanda ya isa ya mata wani aure dan bata shirya yanzu ba.
Bata san mai zata tarar? Bata san ya ya mijinta zai karɓe ta ba. Shine abin da take tsoro yake hanata sha'awar yin aure. Abubuwan da suka faru a rayuwarta suka din ga dawo mata.
Da Mufid bai ɓata mata rayuwa ba da yanzu itama tayi aurenta hankalinta kwance tana rayuwarta.

Sallamar Mami da shigowar ta lokaci ɗaya ya saka Nuratu ɗago kanta ta kalleta da idanuwanta da suka sha kuka.

"Auren ne bakya so ko Dr Awwab ne bakya so. Ki sanar dani"
Mami tace bayan zamanta kusa da ita.

"Dukka Mami."
Tace tana share hawayenta.

"Amma dai wannan kin san shine hanyar tsiratar da rayuwar ki ba?"

Shuru tayi Mami tayi ta mata nasiha sai kuka take har tayi shuru tana sauƙe numfashi.

"Mami tsoro nake ji."

"Tsoron me?"
Mami ta faɗa cike da tausayin ƴarta.

"Kar watarana ya min gori."

"Na san Dr Awwab ba zai taɓa hakan ba. Kici gaba da addu'a, inshaAllah na ji a jikina za kiji daɗin zaman dashi."

Ita dai Nuratu bata ce komai ganin Mami ta goyi bayan auren nan, da kwata Nuratu tana jin ba in da zai je.

Kamun da bata samu zuwa da wuri ba sai ƙarfe biyar, shima sai da Walida ta ƙira Mami kafin Mami ta sata dole ta shirya ta tafi. A motar Mami ta tafi, tayi kyau sosai, kayan ya karɓi fatar jikinta, ba tayi wani kwalliya ba sai hoda, fuskar nan a haɗe ta haɗa giran sama da ƙasa. Tun da taje tana zaune ta ƙi tashi balle sa ran za ta musu rawa, ko ƙarin kuɗi ba tayi ba sai dakyar Aunti Hasiya ta sata tayi mata, tana yi ta fita a hall ɗin ta shiga motar Mami ta kulle kanta ta shiga tunani.

Wayarta ne yayi ƙara ta duba ta ga Dr Awwab ne, ta buga tsaki ta ajiye. Ganin bata ɗauka ba ya saka Dr Awwab tura mata saƙo.

.....

#vote.
#comments
#share

MADUBIN GOBE  40.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Dr Awwab ƙiran Nuratu yaci gaba da yi kusan sau uku bata ɗauka ba, sai yaji babu daɗi gaba ɗaya, hakura yayi ya rabu da ita. Saƙon da ya tura mata ma babu amsa, ƙarshe da ya ƙirata a kashe ma wayar.

'Akwai aiki gaba na.'
Yace a zuciyarsa yana mamakin Nuratu, bai taɓa tsammanin za ta ƙi auren nan kai tsaye ba, duk tsammanin shi zata hakura ta karɓa hannu bibbiyu amma abin ya canza.

Shigar shi Maiduguri gidan Ummi ya nufa, da Hanan ya fara cin karo a filin gidan tana lilo, tana ganin shi da gudu ta sauƙa ta nufi gurin shi ya ɗagata sama suka nufi entrance na gidan.
Ummi bata falon hakan yasa suka wuce sama falonta, zama yayi yana gaisheta tare da ajiye Hanan a gefenshi.

"Kun yi magana da ita?"
Ummi tace sanin in da ya tafi.

Girgiza kai yayi yana miƙawa Hanan wayar shi da ta tambayeshi ya bata game.
"Ummi ta ƙi yarda fa, wai bata shirya ba, yanzu ma haka tun fitowa na ita nake ƙira ta ƙi ɗauka."

"Ko sai naje?"
Ummi tace tana murmushi.

Murmushi Dr Awwab yayi shima yace.
"May be hakan za ayi. Ina yaran nan?"

"Sun fita gidan Baffanku."

"Shine suka bar min My Love ita ɗaya."

"Ƙin zuwa tayi har sun shirya ta."

Miƙewa yayi tsaye yana cewa.
"Mu ma mun tafi unguwa sai anjima. Tashi mu tafi My Love."

Da sauri Hanan ta miƙe ya ɗauketa suka ma Ummi sallama suka fita.

***

DAMATURU.

Ranar Nuratu yanda ta ga rana haka ta ga dare, ta kasa kwakkwaran tunani da zai sama mata mafita bisa abin da suka mata.

'Aure dai!'
Ta faɗa ta sake maimaitawa a fili da zuci. Auren ma tare da Dr Awwab da ta kasa tantance me take ji a kansa.
Gefe ɗaya na zuciyarta haushinsa take ji na shiga rayuwarta da yayi, gefe ɗaya kuma ji take gwara da ya kasance shine mijin ba Col. Ahmad ba domin Yaya Al-ameen ta daɗe da cire shi cikin ranta. Ta kasa tsaida zuciyarta guri ɗaya ta samu shawaran da take nema da zai amfane ta.

Da irin tunane tunanen nan daga ƙarshe wani bacci ya ɗauketa bayan ta gabatar da sallar asuba. Ƙarfe takwas Mami ta ga shuru ta shiga ta sameta tana bacci ta tashe ta. A gurguje tayi wanka ta saka doguwar riga marar nauyi ta fita bayan ta ɗauki wayarta da mukullin motar Mami, ta sanar da ita sai dare ko kuma gobe, ko damar yin breakfast ba tayi ba.

Gidan Aunti Hasiya tayi, anan ta samu Walida tayi ta faɗa da kyar ta bata hakuri kafin ta shiga ciki suka fara aiki. Har azahar kafin su samu zama su ka sake yin wanka suka saka ankon su. Biki aka yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, aka ci aka sha aka watse lafiya, da dare a ka kai amarya gidan mijinta. Nuratu bata koma gida ba bayan sun dawo daga kai amarya ta wuce gidan Aunti Hasiya suka gyara mata gida har wajen sha biyun dare kafin suka kwanta.

Washegarin suka yi wuni, da yamma aka gudanar da dinner da mutane da yawa sun samu halarta, hatta iyaye sun je anan ne Mami tayi ƙoƙarin zuwa dan yiwa Amma Jidda kara kuma ta ji daɗin hakan. Karfe goma aka watse kowa ya wuce gida.
Nuratu tare da Mami suka koma ta wuce ɗakinta ta watsa ruwa ta canza kaya ta kwanta.
Sai lokacin ta dauki wayarta ta buɗe, ƙirane daga mutane daban daban har da na Dr Awwab da tun jiya ya ƙira bata ɗauka ba. Lambar shi ta kurawa ido kamar za ta hangoshi ciki.

Dr Awwab yana cikin mutanen da take ganin mutuncin su, tana jin wani abu akan shi tun ranar da ta ɗaura idanuwanta a kanshi, ji take bata iya jumurin kallon cikin kwayar idanuwanshi, duk yanda taso kasawa take. Zaman aure da shi abu ne mai wahala a tare da ita, bata jin zata iya, sannan bata son rabuwa da shi a rayuwar ta.

Jin tunani babu abin da zai haifar mata ya sata rufe wayar ta ajiye ta runtse idanuwanta, shuɗaɗɗen lokacin da ya wuce kwanakin baya yake dawo mata. Ashe shi yasa yayi ta mata wasu abubuwan da ta kasa fahimtar shi, har yayi ƙoƙarin riƙe hannunta ranar da za su dawo daga Nijar. Ta daɗe kafin ta samu bacci ranar ya ɗauketa.

***

INDIA (New Delhi).

Rayuwa cike yake da dana sani da ƙaddarori ma bambanta da ko wani bawa baya wuce ƙaddarar shi. Duk abin da ka shuka sai ka girba, sannan duk abin da ka yiwa ɗan wani kai ma sai an maka tabbas haka Annabi Muhammad (SAW) yace kuma hakanne.

Zuwan Alhaji Kashim da Hajiya Hindatu India tare da Mufid dan jinyar shi babu abin da ya canza sai ma ƙoƙarin masa aiki da ake a zuciyarshi, domin shaye shaye ya lalata zuciyar saura kiris ya ɓaci da in har hakan ya kasance sai dai su hakura da shi. Alhaji Kashim kuɗaɗen shi da ya taho da shi da kuma wanda yake can gida ya saka aka tattara aka turo mishi ya haɗa ya bada kuɗin aikin da za'a gudanarwa Mufid, babu abin da ya rage masa sai gida da motarshi, domin ƙadaran shi kaf ya saka aka siyar aka aiko masa kuɗin.

Yau talata za a shiga da shi aiki bayan alluran bacci da aka ɗura masa. Hajiya Hindatu duk ta sare da yanayin ɗan tan da yake kwance ya ƙara haske yana fitar da numfashi kaɗan kaɗan ta cikin Oxygen da yake taimaka masa. Hawaye take share lokaci zuwa lokaci tana addu'ar Allah bashi lafiya in kuma lokacin shi ne yayi Allah karɓi abin shi.

Ƙarfe tara aka shigo aka wuce dashi dakin da za'a masa aikin, Ummu ta bishi da addu'a tana kuka sosai, Daddy yana bata baki da shima dauriya yake.

"Addu'a zamu masa Hindatu babu yanda muka iya."

Hawayenta Ummu ta share duk tayi baki ta rame tace.
"Ji nake kamar Mufid ba zai tashi ba. Ina tsoro ya mutu ya barni. Ina tsoron ya mutu bai nemi yafiyar jama'a ba. Ina tsoron ya mutu bai tuba zuwa ga Allah ba bai nemi yafiyar shi ba."

"Nima ina jin hakan, amma InshaAllah zai tashi da yardar Allah, mu mishi addu'a."

Shuru Ummu tayi tana sharewa hawayenta, a ranta ta riga ta saka duk alhakin mutane yake bibiyar ɗanta, musamman wannan yarinyar da sanadinta komai ya faru.

***

DAMATURU.

Amma Jidda da ta ƙira sunan Alhaji Mamman sau biyu bai ji ba dan tunanin da ya faɗa sai ƙira na uku tace.
"Haba dan Allah Abban su, yanzu ba za ka dai na saka kanka a damuwa ba. Ka daina wannan tunanin mana, shi yake ƙara haddasa maka jinin yake hawa, du bi yanzu Docter mai ya gama sanar da kai."

Ajiyar zuciya ya sauƙe yana dubanta, shi kaɗai ya san mai yake ji a ranshi yace.
"Jidda bazan iya daina tunani ba, bazan iya daina dana sanin abin da na aikata ba. Jiya na ji wani wa'azi ga duk mutumin da ya yarda da shirka da boka ko wani wanda zai saka ka yarda da shi ba Allah ba, Allah ya masa haramcin da Aljannah bayan azaba.
Ya zan yi Jidda? Na yarda na bi na amincewa aboki ya jefa ni halaka, ya raba ni da matata da ƴata, ga shi yanzu ban da wutar tsana babu komai a tsakanin mu. Ta ina zan fara? Ta ina zan soma goge tabon da na saka a rayuwar su, musamman ita Nuratu da bata taɓa samun gatan uba ba tun tasowarta har zuwa yanzu. Na saka mata tsanana a zuciyarta da rayuwarta. Ki taimaka mini in samu yafiyarsu ko da kaɗan ne cikin abin da na aikata musu ko Allah zai yafe mini. Wallahi na tuba"

Tabbas duk mai rai baya cire tsammani, ranar da Amma Jidda take jira ya zo. Ranar da Alhaji Mamman zai buɗi baki ya dubi abin da ya aikata har ya nemi gafaran su. Cike da murna da farin ciki tace.
"Kar ka damu Abban su Rahma, Mamin su Rahma za ta fahimce ka ta yafe maka har ita Nuratun."

"Kina ganin hakan. Sadiya tana da sauƙin kai amma tana da zuciya."

"Ka yi kyakkyawar zato."

Tace cikin tsananin farin ciki.
Ya sauke ajiyar zuciya yana fatan hakan, domin in har ya samu yafiyar Mami da Nuratu ya san sauran kudirinsa zai cika cikin sauƙi.

***

Bayan sati biyu.

Tun ranar Dr Awwab bai ƙara ƙiran Nuratu ko nemanta ba, ya barta sai ta sauƙo, baya son takura mata ta ga tamkar wani buƙatarshi ke kawosa gurinta. Ummi bata ƙara masa maganar tarewar Nuratu ba ta saka masa ido.

...

Bangaren Nuratu ta ajiye maganar aure a gefe ta fara kiciniyar mai da hankalinta a kan service da za'a tura su. Mami dai tace ba zata hanata zuwa ba amma ta sanar da Docter kafin ta kammala komai tun da dai da auren shi a kanta.

...

Ranar wata Juma'ah Dr Awwab da wuri ya dawo daga aiki, gidanshi ya wuce yayi wankar Juma'ah cikin blue black din shadda da ya fito da fatar jikin shi ya mutuƙar masa kyau ya saka hula ya nufi gidan Ummi.

Da sallama ya shiga falonta tana can cikin bedroom ya jira fitowarta ta fito tare da Hanan ya gaishe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login