Follow us on social media

Showing 114001 words to 117000 words out of 148866 words

Chapter 39 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

33

musu ta ƙirata. Kiɗane yake tashi inda take basa jin maganar da ake, hakan yasa ta kashe ta tura mata saƙon ta dawo gida yanzu.

*"Tana cikin maye, ku zo ku ɗauketa a Gat hotel."*

Shine amsar da aka turo musu kenan da ya saka Amma Jidda buga ihu iya ƙarfinta.

...

Aci gaba da comments, ku sha karatu.

#Vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE  53.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

...

Zuciyarta zafi yake, ta kasa magana, ta kasa aiwatar da komai, ta kasa kwakkwaran tunani dangane da abin da ya wuce cikin ƙanƙanin lokaci. Aunti Zarah da ta ji komai ita ma ta kasa magana sai bin Hajiya Sadiya take da kallo, yanayin fuskarta kaɗai zai nuna maka tsantsar ɓacin ranta.

A hankali ta bar gurin zamanta ta zauna kusa da ita ganin shurun ya yi yawa.

"Hajiya Sadiya."

Ta ƙirata a hankali cikin nutsuwa. Sai lokacin ta kalleta ta kasa amsawa. Hakan yasa Aunti Zarah ci gaba da maganarta.

"Na ji komai. Naji bayanin Abbansu Rahma."

"Kina ji ko. Kinji komai ko? Ko kunya baya ji fisabilillahi. Wani irin mutum ne Mamman, wani irin mutum na haɗa jinin ƴarana da na shi."

Mami tace cikin ɓacin rai sai lokacin ta samu bakin magana.
Da sauri Aunti Zarah ta rufe mata baki.

"Har yanzu uban yaranki ne, basu da wani uban sama dashi hatta ita Nuratun. Abin da ya yi yai tsaurin ido. Idan wani ne ko dan abin da ya aikata bai kamata ya dawo da niyar sake aurenki ba. Amma ba komai ki yi ta addu'a Allah shige miki gaba."

"Ba zan iya ba Aunti Zarah. Ba zan iya ba ko dan Nuratu. Kar ya ƙara shigomin gida, babu shi babu ni, yara ne suka haɗamu gasu can da shi dama ban raba su ba."

Ita dai Aunti Zarah shiru tayi domin abin ma ta rasa me zata ce akai. Wani gefe na zuciyarta yana son ganin Mami tayi aure tun ba yau ba, wani kuma yana ganin rashin dacewar ta komawa Alhaji Mamman.
Miƙewa tayi dan bawa Mami damar yin tunani tace.

"Zan tafi Hajiya Sadiya, fatan Suwaiba ta miki."

"Nagode ta minin sosai tamkar Munirat."

"To yayi kyau. Iyayenta nan PomPomari su ke, in kin shirya sai muje ku gaisa su ganki."

"InshaAllah na gode sosai. Ki gaisheta da yaranmu."

Daga haka Aunti Zarah ta fita ta bar Mami tsamotsamo cikin kogin tunanin lamarin Alhaji Mamman Bashir.

***

Washegarin.

Maiduguri.

"Ka tashi kar ka makara fa.*

Nuratu tace tana kama dogon hancin Dr Awwab dake kwance yana barci wajajen karfe taran safe. Tun kafin ya kwanta ya sanarta gobe zai fara fita aiki, hakan ya saka da ta yi sallah duk yadda yaso ta koma barci ƙi tayi. Da yaga haka ya ja ta jikinshi ya dameta da fitinarsa, dole ta hakura bayan komai ya lafa suka koma bacci.
Wajen takwas ta farka, a gaggauce ta yi wanka ta sauƙa ta haɗa masa breakfast ta hayo dubawa ko ya farka. Abun mamaki barci ta samu yana yi shine ta hau tashinsa, yana jinta yaƙi magana.

Hancinsa ta ƙara ja ya riƙo hannayenta ya jata ta kwanto saman jikinshi, hakan yasa fuskarsu ta zo daf, tana sauƙe masa numfashinta, yana shaƙa yana fitar da na shi tana shaƙa. Har lokacin idanuwansa rufe yana riƙe da ita.

"Ke fa ki ka hanani barci da asuba, kuma yanzuma ki hanani."

"Na hana kuma? Ka hanamu dai."
Tace tana tura baki gaba.

Sai lokacin ya buɗe idanuwansa ya saka cikin nata. Dakyar ta yi ƙoƙarin bata janye nata ba, dan so take ta fara jure kallonsa, tunda dai zama ya haɗa kuma babu abin rabawa sai ikon Allah. Tana son yanayin da take shiga in ƙwayar idanuwansu suka haɗu. Ta rasa menene amma tana ji tun daga ƙwaƙwalwar kanta har yatsun ƙafarta cikin wani shauƙi. Wani kallone me tattare da bata san me za ta faɗa ba, ko sai nan gaba in ta fahimta.

Sauƙar iskar bakinsa me ƙamshi ya fargar da ita daga kallonsa, ta lumshe idanuwanta ta buɗe akansa.

Ƙara matseta yayi jikinsa ganin kallon da take masa.

"Muje ki mini wankar, duk kin gajiyar ni wallahi."

Fahimtar inda zancensa ya nufa tace.

"Sharri zaka mini Doctor, kai fa ka hanani runtsawa."

Hannunsa dake bayanta ya kai kan kugunta ya damƙe, wani ƙaramin ƙara ta sake tana kallonsa. Dan ba ƙarar zafi ta ji ba, sai na yanayin da ya tsarga mata a jinin jikinta.

"Ni nace ayi, ke kuma kina so amma kin cika ragwanta. Ina son mayarki jaruma, ko yaushe na zo za ki amsheni, sannan ba za ki nuna min gajiya ko ragwanci ba."

Shurunta ya sashi sake murza hips ɗinta, ta buɗe idanunta da suke lumshe da sauri.

"Please My Baby."

Murya can ciki tace.

"Ni dai.... Na ji zanyi ƙoƙari."

Bayanta yaci gaba da shafawa yana sama da hannunsa, jin yana neman fara wuce gona da iri ya saka Nuratu miƙewa.

"Za ka yi latti. And you're not clean."

Daga haka ta fita da sauri a ɗakin. Da kallo ya bita yana mamakin baki da ta fara yi, and yaji daɗin haka yadda ta fara sakewa da shi, hakan shi zai ba shi damar nuna mata so da kulawan da ya ke son nuna mata.
Wanka yayi ya shirya cikin coat sai ƙamshi ya ke ya fita ya nufi falonta. Bata ciki sai ƙamshin turaren wuta yake. Falon ƙasa ya sauka  ya samu tana sharewa ya ƙarasa dinning. Tana ganin haka ta ajiye moppern hannunta, ta ƙarasa ta zuba masa plantain da dankali da ta soya masa, sai coffe ganin yafi so akan tea. Duk abin da take Dr Awwab kawai kallonta yake yana murmushi.
Tea ta haɗa nata ta zauna ta dubeshi.

"Bismillahi."

"Thank you My Baby."
Yace ya fara ci, ya ci sosai ya sha coffee, har lokacin bata gama ba ya miƙe ganin me ƙiransa a waya, abokin aikinsa.

"Na tafi Babyna, sai zuwa uku in Allah ya yarda."

"A dawo lafiya."

Tace tana ƙoƙarin miƙewa dan masa rakiya. Murmushi yayi ya matsa kusa da ita, sauƙar lips ɗinsa taji a goshinta ya sakar mata kiss.

"Nagode da rakiya, koma kiyi breakfast ɗinki."

Daga haka ya fice ta koma ta zauna ta ƙarasa abinta, kafin ta miƙe ta hau aikin gidan sai wajen sha ɗaya ta gama gyara ɗakinta, falonta, ɗakinsa, falonsa da falon ƙasa, ruwa ta watsa ta zube cikin kujerun falonta dan ta gaji. Bacci tayi har ƙarfe biyu ta farka ta gabatar da sallah, kafin ta fara ƙoƙarin ɗaura musu abincin rana.

***

Ƙarfe biyu ya dawo gidan, da safen ba su samu yin maganar ba ya wuce aiki cikin gaggawa. Da sallamarshi ya shiga cikin falon idanuwansa sai kan abar sonshi, murmushinsa ya faɗaɗa ya shiga cikin falon. Tun da taji sallamarshi ta daburburce zuciyarta ya fara bugawa, bata tsammaci ganinsa yanzu ba, dan duk so take suyi sauri su koma kafin yamma lokacin dawowarsa, sai akayi rashin sa'a. Guri ya samu ya zauna kujeran da yake facing Hassana.

"Zo yarinyata."
Ya ce da Hanan da take jikin Hussaina, sanin wanene shi ya sata barinta ta nufi gurinshi ya ɗagata saman jikinshi.

"Ina Daddynki?"

"Yana lafiya?"

"To ya school?"

"Lafiya lau."

"Ina wuni."

Ƴan biyun suka haɗa baki wajen gaishesa, ya ɗago yana kallon Hussaina ya amsa kafin ya maida kallonsa kan Hassana, kanta yana ƙasa ta kasa nutsuwa. Murmushi yayi.

"Ƴan matana."

Yace yana son ta ɗago idanuwanta ya kalli fuskarta ta hanasa hakan.

"Bari in baku guri."

Hussaina tace tana kama hannun Hanan suka hau sama wajen Ammi.
Ganin haka ya saka Abdallah tashi ya zauna kusa da Hassana.

"Ni kam dai wannan kunyar yana cutana. Tun da nace ina sonki shikenan kika canza min, wani kunya kunya ya fara shiga tsakaninmu. Please ni bana so don Allah. A haka za muyi auren."

Ita dai Hassana ta kasa ko tari domin numfashinta ma da ƙyar take shaƙa, ƙamshin turarensa duk ya cikata. Tsoronta kar wani ya shigo ko Ammi ta sauko, hakan yasa ta miƙe tsaye.

"Ina za ki je bamu ko gaisa ba."
Abdallah yace yana shan gabanta.

Kamar za tayi kuka ta ɗaga kanta suka haɗa ido tace.
"Dan Allah kayi hakuri Yaya Abdallah."

"Wuce to, amma ku jira zan maidaku gida in gaishe da Ummi."

Daga haka ya bata guri ta wuce saman da saurinta ya bi bayanta.
Tun shekaru biyu da ya dawo daga karatu a UK ya faɗa sonta. Dama ya sansu amma sunfi sabawa da ita dan tafi Hussaina nutsuwa, surutun Hussaina da tsokana yasa basa shiri. Duk ƙoƙarinshi ya danne hakan a ranshi kasawa yayi, sai da ya sanar da ita watanni biyu da suka wuce. Tun lokacin wani mugun kunyarshi Hassana take ji. Ta kasa bashi amsar tana sonshi, domin ba za tayi ƙarya ta cuci kanta ba tana sonshi, amma mugun kunyarshi take ji bata iya sakewa su gaisa balle hira. Shi kuwa Abdallah bai fasa koya mata sonshi ba, kuma bai faɗa a gida ba har sai sun gama daidaita kansu. Hussaina kaɗai ta san tsakaninsu, Hassana ce ta sanar da ita sannan ta roki ta ɓoyewa Ummi.

Samu yayi suna ma Ammi sallama za su tafi. Ammi dake zauna ta dubi Abdallah.

"Ko za ka sauƙe su a gidan indan baka gaji ba."

"Babu komai muje."

Yace yana ɗaukar Hanan suka fita. A cikin motarshi suka sameshi ya saka Hanan a baya, Hussaina tayi saurin shiga itama bayan, Hassana kamar tayi kuka ta shiga gidan gaba. Tafe babu wanda yayi magana sai surutun Hanan da Hussaina.

"Ya school ya kusa ƙarewa?"

Hassana taji tambayar Abdallah. Kai ta ɗaga kamar me ciwon baki tace.
"Eh saura shekara ɗaya."

"Allah ya kaimu."

Ameen ta amsa da shi, a haka suka isa gida ya gaishe da Ummi tare da Dr Awwab da ya iso gidan bayan barinshi aiki, kafin Abdallah ya musu sallama ya koma.

Da gudu Hanan tayi gurin Dr Awwab ta maƙalƙaleshi tana tsalle dan duk yau kwana biyun bai zo ba.

"Daddy don Allah ka tafi dani."
Faɗin Hanan kamar tayi kuka. Kanta ya shafa kafin yace wani abu Ummi tace.

"Ka taimaka mata ko sati ɗaya ta bika tayi."

"Ummi driver nake nema mata da zai dinga kaita school da islamiyya daga can, shi yasa ki kaga shuru banyi maganar ɗaukarta ba. Nima ina son ganinta kusa da ni."

"To hakan ma yayi Allah taimaka."

Ameen yace ya miƙe.
"Zan wuce Ummi sai gobe."

"To ka gaishe da gida da Noor."

"Za taji."
Yace ya ajiye Hanan dake hawaye. Ya nufi hanyar fita.

"Daddy."
Tace tana binshi a baya tana kuka. Hakan ya saka ya dakata ta iso wajenshi ta rumgumeshi. Sai yaji tausayinta ya ɗauketa.

"Hussaina haɗamin kayanta ko kala biyu ne, zuwa gobe ku gama haɗa sauran zan zo ɗauka."

Tashi Hussaina tayi ta wuce ɗakinsu ta ɗauki kayan Hanan a ƙaramin jaka kusan kala biyar da kayan makarantarta da jaka dana islamiyya da takalma kala biyu ta fito. Karɓa yayi da d'ayan hannunshi ya sauƙe Hanan.

"Je kima Ummi sallama."

Da gudu ta isa gurin Ummi da taji bata son tafiyarta kuma, dan ta saba da ita sosai. Rumgumeta tayi ta bata sumba a kumatunta.

"Ummi zan tafi."

"Allah bada sa'ar karatu, kiyi ta ƙoƙari kinji Nusaiba."

"To Ummi."

Tace ta rumgume Hassana da Hussaina duk basa son tafiyarta, kafin ta isa gurin Dr Awwab ta riƙo hannunsa suka fita. Murna fal ran Hanan sai surutu take zuba masa.
A haka suka isa gidan me gadi ya buɗe masa get ya shiga ya faka motar suka sauƙa, suka nufi cikin gidan. Da gudu ta shiga falon tana kwalawa Nuratu ƙira.

Shigowar Dr Awwab ya hanata yace.
"Ke! Ki nutsu. Tana falon sama."

Da sauri ta haye tana nufan falon Nuratu da take ta sharan bacci bayan gama aikinta. Bin bayanta Dr Awwab yayi ya samu ta dakata tana turɓune fuska.

"What?"

"Tana bacci."

"Ok then muje in nuna miki ɗakinki."

Ɗaya ƙofar dake cikin falon Nuratu suka shiga ciki. Ya zuba mata komai na yaro ɗan shekaru biyar, duk da ba ta ciki, ba zama take ba.
Wardrobe nata ya buɗe ya sa ka mata kayanta da duk abin cikin akwatin, kafin ya juyo ya ganta saman gadon tayi ɗaiɗaya.
Kallonsa tayi kamar za tayi kuka.

"Ni kaɗai za ina kwana? Ba tare da Aunti Noor ba ko kai."

"Za ki iya, zamu na tayaki kwana kinji My Love."

Murmushi tayi ta miƙe ta rumgumeshi.
"I love You Daddy."

"I love you too My Love."
Yace ya rumgumeta shima, kafin ya saketa ya kunna mata ƙaramin Tv dake ɗakin ya kai mata cartoon.

"Kiyi kallo bari in tashi Aunti Noor."

Kai ta ɗaga mishi ya fita.
Bacci take sosai, ya tsungunna kan kafafunsa ya zuba mata ido.
'Noor akwai kyau, baƙace amma baƙinta glowing yake, kyakkyawace sosai da ake ƙira da black beauty. Sai ka nutsu zaka hango kyawunta.'

Haka ya faɗa a cikin ranshi kafin murmushi ya suɓuce masa, ɗaura hannunsa yayi saman cikinta yana tura hannun cikin rigarta. Cikin bacci taji abu yana yawo a jikinta, ta buɗe idanunta suka sauƙa saman na Dr Awwab.

"Sleeping beauty."

Murmushi tayi ta lumshe idanuwanta ta buɗe, har lokacin hannunsa na cikin rigarta yana taɓe taɓensa.

"Yaushe ka dawo?"

"Ban jima ba Babyna. Na zo kina barci, ko dai me barci na samu."

Yace yana zare hannunsa ya miƙewa ya mikar da ita, bai bata damar yin wani magana ba, ya riƙeta suka nufi ɗakinsa. Wanka yayi ta ciro masa kaya ya fito ya shirya suka fito. Sun fara sauƙa a stairs yace.

"Tare muke da Hanan tana ɗakinta."

"Dan Allah. Kuma shine baka sanar mini ba tun ɗazu."

Bai mata magana ba ta zare hannunta cikin nashi ta koma. Ɗakin Hanan ta buɗe tana shiga. Hanan da sauri ta diro a gadon ta isa gurin Nuratu ta ɗagata sama suna dariya. Sun jima haka kafin ta riƙeta.

"Aunti mun zo kina bacci."

"I'm sorry ban sani ba, yanzu na farka. Muje kici abinci My Baby."

Daga haka suka fita tana ɗauke da ita ko nauyinta bata ji. Ido Dr Awwab ya saka musu har suka ƙaraso saman dinning ta zaunar da Hanan. Abinci ta zubawa Dr Awwab ta zuba nata da Hanan. Wani kallo ya watsa mata.

"Yau kaɗai Doctor please."

Nuratu tace tana marairaice masa. Kai ya girgiza ya ɗauki nashi ya juye cikin plate ɗinsu.

"Mu ci tare dukka."

Ya faɗa ya fara ci, Hanan kam ta saba cin abinci dashi hakan yasa ta saka nata spoon ɗin ta fara. Ganin haka ya saka Nuratu fara ci a hankali. Bayan sun gama ta tattare gurin duk inda ta shiga Hanan tana binta. Hakan ya yiwa Dr Awwab daɗi ganin ta ɗauketa matsayin uwa, saɓanin wasu da suke ɗaukar matar uba maƙiyiya. Ko dan ita bata san nata mahaifiyar ba.

Daren hana Nuratu girki yayi ya sasu suka shirya suka fita, wajen shan ice cream ya kai su da kayan ciye ciye, suka ci suka sayo wasu wajen karfe goma. A fridge ɗin falo suka ajiye. Ɗakin Hanan ya kaita ya kwantarta ya lulluɓa mata bargo tare da tofeta da addu'a.

Yana shirin fita Nuratu ta shigo da shirin kwanciya. Kallonta yayi ya kamo hannunta suka fita ta ƙofar falonta, bayan ya kashe mata wuta.

"Ita ɗaya zamu bari. Ba za taji tsoro ba."

"Za ta saba kafin siblings ɗinta su zo."
Yace yana kashe mata ido ɗaya ta ɗauke kanta.

"Ni dai da ka barni na tayata kwana, ko kuma ta zo mu kwana a ɗakina."

"Ni kuma fa kiyi ya dani?"

Kallonshi tayi ya ɗaga mata gira ɗaya ta girgiza kai tana wucewa ɗaki, bayanta yabi yana murmushi ya hangota gaban mirror. Bakin gadon ya zauna.

"So kike ki zautar ni ko, kina ta zuba turare."

Bata kulasa ba taci gaba da shafe shafenta ta gama ta kashe wutan ta isa bakin gadon ta zauna. Addu'a tayi ta shafa.

"Ni fa ki shafa mini."

Wani tayi ta shafa masa a fuska, tana ƙoƙarin ɗauke hannunta ya cafke dan ƙamshin turaren jiki ya shigesa. Daga kan hannun ya fara sumbata har zuwa wuyanta, dan ƙamshin ya ƙara rikitashi. Daga nan komai ya canza suka mance da kowa da komai. Bai iya barinta ta yi bacci ba sai da suka tsarkake jikinsu.

Da asubanin bayan ta idar da sallah ta gaishesa ya amsa yaci gaba da azkhar ɗinsa kafin ya kwanta wajen ƙarfe shida. Nuratu tana jin yayi bacci ta lallaɓa ta fita. Breakfast ta haɗa masa da Hanan ta ajiye saman dinning table, ta sakawa Hanan a lunch box nata, kafin ta wuce ɗakin Hanan ta cikin falonta ta shiga tasheta.
Wanka ta mata ta ciro kayan makarantarta da yake goge ta saka mata, ta shafa mata mai da turare suka fito falonta.

"Ki zauna bari in taso Daddy."

Kai ta ɗaga mata ta wuce ɗaki. Samu tayi ya farka.

"Ina kika je?"

"Ni kayi wanka ka shirya, za kayi latti."

Agogo ya kalla bakwai da wani abu ya koma ya kwanta.
"Da sauran lokaci."

"To wa zai kai Hanan makaranta."

Sai lokacin ya tuna ya miƙe zaune.
"Ta farka."

"Tun yaushe, kai muke jira muyi breakfast."

"Ɗauko min kaya to."
Yace ya miƙe tsaye yana wucewa bathroom. Fita Nuratu tayi ta wuce ɗakinsa, kamar yadda taga jiya ya saka coat haka ta ɗauko masa wani launi ta feshe da turare, hatta boxer da singlet sai da ta fesawa turare ta kai masa. Ta samu ya fito daga shi sai tawul, ta ajiye saman gado tana fita da sauri domin har yanzu tana jin kunyarsa.

Sai da ya gama shirinsa tsaf ya fito ya samesu a falon ƙasa suna jiransa.

"Good morning Daddy."

"Good morning My Love."

Yace yana sunkuyawa ya sumbaci kumatunta. Dinning su kayi Nuratu ta zuba musu breakfast a babban plate ta haɗa masa coffee ta haɗa musu tea kafin su fara. Cikin 20mins suka gama ta goya Hanan jakanta ta riƙe mata lunch box ɗinta. Har bakin mota ta rakasu ta saka Hanan ta rufe mata, kafin ta zagaya gurin Dr Awwab.

"Sai ka dawo Allah ya kiyaye."

"Ameen My Baby."

Yace kafin ta ankara ya sakar mata kiss a kumatunta. Da sauri tayi baya tana harararsa. Ya gane nufinta, yayi murmushi ya shiga motar suka bar gurin, kafin ta koma ciki.
Aikinta tayi kamar ko yaushe tayi wanka ta zauna hutawa wajen sha ɗayan safe.

***

DAMATURU.

"Ta farka."

Faɗin Amma Jidda da take tsaye saman kan Ameera ta fara motsi, bacci take tun daren shekaran jiya har yau da safe. Da sauri Alhaji Mamman ya fita ƙiran likita.

...

#vote
#comments
#share

MADUBIN GOBE  54.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Awanni saba'in da huɗu kafin faruwar haka.
Da ƙyar Amma Jidda ta sanar da Alhaji Mamman abun da ya ke rubuce a saƙon da aka turomata. Wani jirine ya kwashesa kafin ya daidaita nutsuwarsa sannan ya miƙe.

"Bari in je wajen."

"Muje tare don Allah."

Amma Jidda tace, hawaye take zubarwa mai zafi. Kai kawai ya ɗaga mata ya fita. Da sauri ta ɗauki mayafinta ita ma ta fita, samunsa ta yi har ya kunna motar. Tana shiga a guje ya fita.

A harabar Hotel ɗin ya yi parking ya dubi Amma Jidda da ke kuka.
"Bari in shiga in fito da ita."

Kai kawai ta ɗaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login