Follow us on social media
Showing 129001 words to 132000 words out of 148866 words
Chapter 44 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
haɗa breakfast mai rai da lafiya dan wanke kanta gurin Autar uwargidanta. Ko ta kansa Nuratu bata bi ba ta shiga kitchen ta dafa indomie ta fito ta ci. Suwaiba kamar tayi kuka ta durƙusa ta gaisheta. Lafiya kawai ta amsa da shi ta jawo wayarta ta ƙira mijinta.
Yana cikin shirin fita ya samu ƙiran, da sauri ya ciro ya ɗauka.
"My sweetest baby girl."
Rai ta ɓata tana tura baki.
"Bayan sai da na neme ka?"
"Sorry Sweet amini afuwa. Gani tafe."
"To sai ka zo."
Kit ta kashe wayar bata bari ya ƙara magana ba. Ƙiranta yayi ta ƙi ɗauka ya hakura ya fita. Gidan ya nufa, bayan ya shiga suka gaisa da Mami ta koma tana masa godiyar kaya. Da ƙyar ya ci abincin da Nuratu ta kawo masa kafin ta shiga tama Mami sallama za taje gidan yayunta sai ta dawo. Murmushi kawai Dr Awwab ya yi ya fita.
Gidan Aunti Rahma suka fara zuwa, bayan sun gaisa ta ja Nuratu ɗaki, kayan gyara nasha da ke cikin fridge ɗinta su dangin kayan itace ta kwaso wanda ba'a rasa abubuwan da aka saka ciki ba ta bawa Nuratu. Sai da ta shanye tas ita ma ta ji zagi kafin ta barta. Ta haɗata da turaren kwanaki.
Mintunansu ashirin ya ce su tafi, babu yanda ta iya bayan Doctor ya ajiyewa yaranta kyautar kuɗi dan dukkansu sun manta batun tsaraba. Godiya ta masa sosai Aunti Rahma.
Daga nan gidan Aunti Hasiya suka nufa, nan ma dai sai da ta haɗa Nuratu da shan
natan abun kafin ta barta. Nan na ya yiwa ƴaranta kyauta.
Sai gidan Rukayya suna kule ɗaki.
"Wai da gaske yarinyar nan kike ba ki da ciki."
Faɗin Rukayya dan dai ta ɗauka duk ƙarya take.
Dariya Nuratu tayi.
"To wai yaushe aka yi auren. Ko wannan watan nayi period."
"To Allah yasa kar ki wuce next."
A zuciyarta ta amsa a fili bata amsa ba ta miƙe tana ɗaukar handbag ɗinta.
"Idan babu abin da za ki bani zan tafi."
Fahimtarta ya saka Rukayya yin dariya.
"Yarinya ta shigo gari."
Dariya Nuratu tayi bata ce kala ba, wasu kayan fruit da ta ma haɗi dan kanta ta saka a fridge ya yi sanyi ta ɗauko ta bawa Nuratu.
"Kinga wannan haɗin fruit ne zalla. Yarinya sai na ji ƙira."
Sosai Rukayya ta koro mata bayani tana sha, tas ta shanye dan taji daɗinsa. Bayan ta gama ta miƙe.
"To na gode. Sai wani lokaci."
"A dai tausayawa Doctor. Sannan ayi jarumta, dan nasan su Aunties sun cika ki da nasu."
Faɗin Rukayya dariya. Dan tasan me raba Dr da Nuratu yau sai Allah, yadda kowanne ya bata gudunmowarsa. Burin su tayi daraja da mutunci idon mijinta, tausayinta suke ji. Ita ma ya mata kyauta.
Gidan Walida ne ƙarshe ita ma sunsha hira tana ta tsokanar Nuratu, dariya kawai take tana cewa ke ce abin tsokanar dubi ciki duk ya mayar da ke ƙatuwa. Sun ɗan yi hira ta mata sallama, ita ma Doctor ya bata nata kyautar. Bayan sun fito ya ce sai ina.
"Gidan ƙawata Rufaida."
"Wacece ita?"
Dan shi ya ɗauka bata da ƙawaye sam sai ƴan uwanta.
"Za ka santa."
Daga haka ta dinga masa kwatance har kofar gidan yayi fakin.
"Bazan jima ba yanzu zan fito. In kuma zamu shiga."
Kai ya ɗaga mata ta fita ta shiga, da sallama ta shiga cikin gidan. Rufaida da ke fama da cikinta ta fito jin yadda zuciyarta ya buga da taji muryarta tamkar a mafarki. Ido biyu suka haɗa. Murmushi suka sakarwa juna dan tsakani da Allah suna kaunar junansu.
Da sauri Rufaida ta isa wajen Nuratu ta rumgume tana fashewa da kuka.
"Nuratu ke ce, dama za ki neme ni."
Ita ma cike da kewar ƙawarta ta kamo hannunta.
"Ni ce Rufaida, ya gida ya bayan rabuwa."
"Lafiya lau, mu shiga ciki."
Bayan sun zauna suka sake sabon gaisuwa, Rufaida ta rasa me za ta yi wa Nuratu ta faranta mata. Ta cika gabanta da kayan ciye ciye. Ganin ta kasa nutsuwa ta kamo hannunta ta zaunar.
"Ya isa Maman Baby kar ki wahalar mana da shi."
Murmushi Rufaida ta yi tace.
"Ya wajenki? Fatan lafiya?"
"Lafiya lau. Ba ki neme ni ba kema?"
"Ina son zuwa wajen Mami amma kunya da tsoronta nake ji."
"Haba dai, ko da Mami bata riƙe ki ba balle ni. Komai fa ya wuce Rufaida. Ina ɗayan Babyn mu."
"Sun fita da babanta."
Shigowar mijin Rufaida da Babyn da kuma Dr Awwab suka basu guri.
"Ke kuma za ki bar miji a shanye."
Ya faɗawa Nuratu cikin zolaya, dan kallo ɗaya ya mata ya gano ita ce wacce kullum Rufaida take maganarta.
"Zamu wucene."
Ta faɗa tana gaishesa ya amsa.
Ba su jima ba suka musu sallama bayan Nuratu ta ɗauki Babyn Rufaida ta mata kyauta. Rufaida na ta godiya har da hawayenta ta musu rakiya. Nurata tana jaddada mata ta faɗa mata idan ta haihu, suka yi musayar lambar wayar.
Sun ɗauki hanya Dr Awwab ya dubeta.
"Wacece ita Baby, sai dai kamar nasa fuskarta."
"Ƙawatace kut da kut, sai dai ƙaddara ta rabamu wanda take ganin samuwar ƙaddarar rayuwata da saka hannunta."
"Ki mini bayani. Ban fahimta ba."
Ya ce dan sam bai fahimci zancenta ba.
Rana ta farko da Nuratu ta so bawa Dr Awwab labarin wacece ita tun farko har zuwa inda ya sani. Ta sanar da shi menene tsakaninta da mahaifinta, ta ba shi labarin yadda Mufid da abokansa suka lalata mata rayuwa. Da irin gudummawar da Col. Ahmad da Yaya Al-ameen da shi kansa suka bawa rayuwarta. Ƙarshe ta sanar da shi Rufaida ƙanwar Mufid ne.
Tana yi tana hawaye har ƙarshe, bayan ta gama ta yi dariyar taƙaici.
"Amma komai ya wuce dalilin samunka a rayuwata, ka maida duhuna haske, ka maye soyayya da gurbin tsana da yake cikin zuciyata, ka kyautatawa rayuwata, ka nuna mini so da kauna, ka nuna mini nima macece tamkar kowa me daraja da ƙima. Ta ya bazan kauna ce ka ba?"
Shuru kawai Dr Awwab yayi bai yi magana ba illa hannunsa ɗaya yasa ya jawota jikinsa ya rumgume. A haka suka isa harabar hotel ɗin. Kashe motar yayi ya juya ya rumgumeta tsam a jikinsa.
"Komai ya wuce tunda komai ya daidaita, ki daina tuna baya. Ina kaunarki sosai."
Sun jima haka kowanne na sauƙe numfashi. Dr Awwab mamaki kawai yake cike da al'ajabin rayuwar da Nuratu ta gudanar, bai taɓa tsammani haka nata rayuwar yake ba. Lallai ta ga rayuwa tun tsowarta bayan fyaɗe da aka mata.
Kusan sakanni ya saketa suka fito ya riƙo hannunta suka nufi cikin hotel ɗin. Bata ma lura hotel bane sai da suka shiga ciki.
'Ko me ya kawosu kuma nan.'
Ta tambayi kanta da mamaki.
...
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 58.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Har ɗakin da ya sauƙa ya musu jagora su ka shiga ciki, bayan sun yi wanka ya musu odan abinci. Daga nan sai barci dan huta gajiya.
Washegarin ƙarfe goma suka je har gidan Mami da Amma Jidda suka musu sallama, sannan sai shagon Abbanta. Ta yi murna sosai ganin kasuwanci ya ƙanƙama.
Ƙarfe sha biyu suka bar cikin Damaturu cike da kewanr ƴan uwanta, sai ta waya ta musu sallama.
Kai tsaye gidansu su ka sauƙa duk roƙonsa da take yi masa su fara biyawa gidan Ummi yace a'a yana da uzuri. Yana shiga yayi fakin ta fice ta barsa, da sauri ya buɗe motar ya fita ya bi bayanta. A falon ya sameta ya ɗauketa cak suka nufi sama.
"Muje in duba."
Yace ya nufi ɗakinsa da ita.
"Me kuma?"
Ta faɗa da mamaki. Ido ɗaya ya kashe mata yana buɗe ɗakinsa suka shiga. Bai tsaya ko ina ba sai saman gado ya kwantarta yana ƙoƙarin ɗaga doguwar rigar jikinta. Da mugun mamaki ta riƙo hannunshi.
"Me haka Doctor?"
Kansa ya ɗago yana faɗin.
"Dubawa zan yi inga ko ya tafi. Ke fa ki ka ce in duba."
Sam ta manta da ta faɗa hakan. Karyar da wuya tayi a maraice ta ce.
"Ni wasa nake maka. Kuma kai ba likitan mata ba ina kai ina dubawa."
"Dan ina likitan ƙwaƙwalwa ai ni likitan matata ce. Bayan hakama duk namiji shi likitar matarsa ce, balle ma ko da likitan ƙwaƙwalwa na ke ina da damar taɓaki."
"To na ji, yanzu ka yi hakuri."
Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa ya hanata.
"Ai sai na dubata."
Bai bata damar motsi ba ya yaye doguwar rigar ya duba. Ganin da gaske babu shi babu alamar sa ya sa shi tun daga nan ya fara aika mata sakonsa. Luf tayi tana jinsa har ya ɗago ya haɗa bakinsu. Daga nan suka buɗe shafin so da ƙauna. Ranar ta banu hannun Dr Awwab, sai da ta fara masa kuka abun da bata masa kenan. Ashe gaskiyar Rukayya da tace ta yi jarumta, bayan hakama ita ta jawowa kanta yadda duk wanda ya bata abu sai ta ɗura a cikinta har da neman ƙari wajen Rukayya. Aikuwa da ƙyar ya barta, ta gurzu mutuƙa a gurinsa.
Barcin wahala ne ya kwasheta sai wajen ƙarfe huɗu ta farka da kukan shagwaɓa, shi ya dinga lallaɓata ta samu tayi wanka ta fito ta zurma riga marar nauyi ta gabatar da sallah. Abinci kam sai takeaway ya musu suka ci.
Washegari Dr Awwab ya wuce aiki bayan ya dameta da fitinarshi ta samu ta korasa.
Tun lokacin kusan kwana huɗu bai samu zama sosai ba dan aiki da yake tukuru, haka ya cinye satin kafin ya samu nutsuwar ruhi.
A gida suka cinye hutun ƙarshen mako babu inda ya je ko ya bar Nuratu ta fita, sabuwar amarci yake yi.
Ranar Litinin yasa ta shirya suka fita, passport ya kaita aka mata kafin ya dawo da ita gida. Tun a hanya take masa magiyar ya kamata Hanan ta dawo.
Murmushi yayi yace.
"Za ta dawo ba yanzu ba amma."
"To wai me yasa?"
"Akwai suprise da zan miki."
"Suprise?"
Ta tambaya, kai ya ɗaga mata. Haka suka isa gida ya sauƙeta ya koma aiki.
Bayan kwana biyu da maganar har ta manta wani ranar laraba da karfe biyu ya dawo gidan. Tayi mamakin dawowarsa da wuri, bayan ta taimaka masa yayi wanka ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya. Abinci ta gabatar masa ya ci kafin ya ce ta haɗa kayanta da nasa akwai inda za su je. Babu musu ta haɗa musu cikin babban akwati.
Bayan ya gama ɗaukar wayarsa da mukullin mota ya kashe komai na wuta ya sameta a ɗaki ta gama.
"Muje ko."
Ya faɗa yana jan akwatin, ta ɗauki mayafinta babba ta rufe jikinta suka fita. Ita dai ta kasa tambayarsa ina za su je. Haka suka shiga motar bayan ya gargaɗi me gadi ya kula da gidan kafin su bar gidan. Hanyar gidan Ummi suka yi, sun gaisheta anan ta samu labarin za su yi tafiya, sai dai bata san ina ba. Sallama suka musu suka fito akan sai sun haɗu acan.
Anan ya bar motarsa drivern Ummi ya kai su airport. Nuratu baki buɗe take bin gurin da kallo.
'Tabbas airport ne.'
Ta faɗa a ranta suna shiga ciki. Bayan an gama musu komai suka shiga cikin jirgin suka zauna. Nuratu kallon Dr Awwab kawai take.
Ganin tana buƙatar amsa ya sa shi saƙale yatsun hannunsa cikin nata.
"Suprise My Baby."
Murmushi tayi har dimple ɗinta ya lotsa, ta matse yatsun hannunsa.
"Thank you Hayat. Amma ina za muje?"
Hannunta ya kai bakinsa ya sumbata.
"Dubai zuwa honeymoon."
"Dubai dai ni Nuratu."
Tace da tsantsan mamaki. Kai ya ɗaga mata yana murmushi.
"Ban tambayeki ra'ayinka ba sorry."
Naushi ta kai masa a damtsen hannunsa hawaye na silalowa bisa kumatunta.
"Ka shammace ni sosai but zan rama. Na gode sosai Noor Hayat."
Hawayenta ya share mata yana cewa.
"No need My Noor Hayat."
Daga nan jirginsu ya lula ƙasar United Arab Emirates ƙarƙashin birnin Dubai. Hotel mai kyau mai tsada ya kama musu, bayan sun huta sai barci. Tun ranar suka buɗe sabuwar rayuwa, soyayya suke gwadawa junansu tamkar su haɗiye juna, da dare ko yamma su zaga gari. Duk wani kunya Nuratu ta ajiye a gefe ta fara kula da mijinta.
...
Can Nigeria kuwa yau safiyar juma'a Mami ta samu baƙoncin Yayanta, ta karramasa sosai suka yi ta hira har suka gangara hiran Al'ameen da Hafiza da aka saka biki bayan sallar azumi da sati biyu. Dalilinsa ya zo faɗamata har take cewa da ya mata waya ai, ya ce babu matsala.
Daga nan masallaci ya nufa tare da uzurin da ya kawosa. Tafiyarsa da mintuna goma yaran Mami suka iso gidan.
Fitar Kawu Muhammadu bayan an idar da sallar juma'a ya yi uzurin da ya kawosa ya koma gidan Mami. Tare da yaran gaba ɗaya a falon an haɗa Suwaiba da reno a tsohon ɗakin Nuratu. Bayan gaisuwa ya zaro kuɗin aljihunsa dubu hamsin ya ajiye gefen Mami.
"Sadakin kine Sadiya, bayan fitana ko ince dalilin zuwana kenan, na miki wakilci an ɗaura aurenki da miji ko mutumin da nake ga shine daidai da ke. Wannan zaman ba naki bane haka Sadiya, yaranki ba sa jin daɗin zamanki haka, haka ni ma. Kuma ko ba komai mutane za su yi ta magana har da masu ƙazafi, don haka na zaɓa miki rayuwar aure akan wannan rayuwar na kaɗaice. Allah ya ba ki sa'ar ma mijinki biyayya, ki zama mace ta gari tamkar yadda na sanki. Allah ya ba ku zaman lafiya."
"Ameen."
Yaran suka amsa banda Mami duk bata saurara sauran maganganunsa ba, burinta ya sanar da ita waye ya aura mata. Ita dai da aure, da girmanta da yara har da jikoki.
Kawu Muhammadu ne yaci gaba da cewa.
"Sati biyu masu zuwa za ki tare, mun riga mun gama magana da shi. Zarah da makota za su miki rakiya. Mama wuro za ta zo ta taimaka miki da wasu shirye shiryen sai kuma su Rahmatu suma gasu nan."
A hanzarce Mami ta dubesa.
"Sati biyu dai Yaya? To waye mijin?"
Sai lokacin ta samu bakin yin magana.
"In kin je za ki gansa. Kinga tafiyana ina son isa gida duk dare. Sai munyi waya."
Daga haka ya miƙe ya musu sallama Muhsin ya kaisa tashar mota, ya biya masa kuɗi ya basa kuɗin shan ruwa. Bai so karɓa ba dole ya sa shi amsa.
Mami ta kasa zaune ta kasa tsaye duk wanda ta tambaya ko yasan da labarin sai yace a'a, balle su san wanene mijin. Duk ta zama shuru shuru har dare ya yi suka mata sallama bayan Rahma da Hasiya sunyi ta kwantar mata da hankali.
...
Cikin sati biyun Mami ta yi su cikin fargaba, har wani rama tayi. Aunti Zarah ta zo sunyi maganar sai dai duk hasashe sun kasa gano wanene. Har Aunti Zarah tana ce wa.
"Ko dai Abbansu Rahma ne."
Girgiza kai tayi ta ce.
"A'a, duk wulaƙanci dana masa bana zaton haka. Amma dai."
"Menene?"
Aunti Zarah tace.
Nan Mami ta sanar da ita yadda suka yi da Nuratu kamar yadda ta sanar da ita. Shuru Aunti Zarah ta yi can tace.
"Amma ai bata miki maganar kome ba tunda bai mata ba. Kinga kuwa ba shi bane. May be shi ma ko ba shi da labari."
"Hakane kuma fa. Ni koma waye fa sai dai ya gaji ya rabu da ni."
Tace cikin fushi.
...
Washegari Asabar Mama Yawuro ta iso gidan da Hafiza. Da yamma yaran Mami suka iso dan kwana za su yi. Tun daren suka fara shirye shiryen haɗamata kayanta da duk abun buƙata, mota babba da mijin ya aiko ya ɗeba ya kai gidanta.
Da ƙyar Aunti Zarah da Rahma suka saka Mami yin jan lalle, Hafiza ta mata ƙananan kitso a gashinta me tsantsi da tsayi. Ban da haka babu abun da ta yi, amma ta yi masifar ƙyau, ta saka lecca da ya amsa sunan sa lecca, ya zauna a farin fatarta ya haskakata, kana ganinta kasan amaryace tamkar kowacce amarya ranar bikinta sai tayi sheƙi, haka Mami ma. Yaranta sai hotuna suke mata suna yi tare.
Sai dare ƙarfe takwas motoci kusan biyar suka zo ɗaukar amarya. Kaf sai da suka kaita har gidanta cikin ɗakinta. Wasu suka zauna anan wasu suka koma gida dan gyarawa.
Yaran tun da suka ga gidan da Maminsu ta shiga murnarsu ya ƙaru.
Ango bai shigo ba sai ƙarfe goma bayan ya gama lallashinta uwargidansa da duk ƙoƙarinta ta danne kishinta kasawa tayi sai da ta zubar da hawaye.
Bayyanarsa falon me cike da tarihin da baya son tunawa ya saka mutanen ciki dubansa. An gyara falon da komai na zamani an ƙawatasa ya zamto tamkar falon amarya ƴar sha takwas.
"Sannunku ina wuni."
Ya faɗa yana ƙarasawa ciki. A hanzarce ta ɗago ta dubesa jin muryarsa, idonsa tar a kanta. Nata idon ta janye cike da baƙin cikin da ya taso mata.
"Abba bismillahi, ko in maka jagora."
Faɗin Rukayya tana tasowa ta riƙo hannun Abbansu ta shigo da shi falon.
Saman kujera ta zaunarsa kusa da Maminsu ta koma gefe. Cikin dabara ta dinga musu hoto tana dariya. Bayan tsawon lokaci iyayensu sun kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.
Doguwar nasiha Aunti Zarah ta musu mai kashe jiki, kafin su musu sallama zuwa ɓangaren baƙi aka bar amarya da angonta. Bayan watsewarsu falon ya ɗauki shuru tsawon mintuna.
"Sai kuma ki ka ga bazata ko Sadiya?"
Matsawa Mami tayi tana masa wani mugun kallo.
"Kar ka ga ka mini fin ƙarfi ya tabbatar maka ko na yarda. Har abada ba zan ƙara amincewa da kai ba."
"Na sani amma ki ƙara bani dama don Allah."
Ya faɗa yana kamo hannunta. Da sauri kuma ya sake jin sabon abu ya ziyarce sa.
Mami ta shi tayi, ɗaki ta shige ta bar zauna dan wani iri ta ji lokacin da ta ji saukar hannunsa a nata.
Ya jima zaune kafin ya koma sashinsa yayi shirin barci ya kwanta, baya son takura mata sam.
Ganin bai dawo ba ita ma ya sata shirin barci ta kwanta.
Washegari kowa ya gama shiri suka haɗa Amma Jidda da Mami suka musu nasiha da sallama suka tafi. Mamin kunyar Amma Jidda take ji sosai, gani take bata kyauta mata ba duk irin ɗawainiya da yaranta da tayi.
Fahimtar haka ya saka Amma Jidda ajiye kishinta a gefe ta ƙara shiga jikinta, tasan dai ba dan ƙaddara ba, da tsawon lokaci tana matsayin matarsa, bayan haka ga yaransu.
Kwana biyun Alhaji Mamman ya kasa gane kan Mami duk hanyar da zai bi ya yi ta ƙi yarda masa. Zai sameta suna hira da Amma Jidda amma da zaran ta gan sa take barin gurin.
Amma Jidda dai ido ta saka musu, tasan komai daren dadewa za su shirya kansu.
...
A haka aka soma azumi bayan sati biyu daa tarewarta. Har lokacin babu wani shiri tsakanin ma'auratan, Mami fa ta kasa ta tsare, tsakaninta da Alhaji Mamman ta girka ta basa. Shikam har wani rama yayi dan ya kasa gane kanta fa.
***
Ɓangaren Dr Awwab da Nuratu har azumi suna