Follow us on social media
Showing 111001 words to 114000 words out of 148866 words
Chapter 38 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
ƙi sakinta.
Jin sallamar Dr Awwab ya sasu kai duba wajensa. Cike da kunya ya ƙarasa ya gaishe su suka amsa, ya wuce sama cikin sauri.
"Tashi ki kai masa abinci Nuratu."
Faɗin Aunti Hasiya tana duban Nuratu da ba ta da niyar tashi.
"Ni kuma."
Tace tana kallon Mami, Mami ta ɗauke kanta. Aunti Hasiya ta daka mata tsawa.
"Ba dake nake ba."
Gunguni ta fara ta miƙe ta wuce wajen table, ta ɗauki warmers ɗin dake jere a cikin babban tray, plate da cup da ruwa ta ɗaura a sama, ta ɗauka ta wuce falonta ganin nan ya wuce. Da sallama ta ta tura ta shiga.
Jin sallamarta ya saka Dr Awwab miƙewa zaune daga kwancen da yake. Nuratu ta ƙaraso ta ajiye warmers ɗin center table da yake tsakiyar falon.
"Ga abinci nan."
Wani kallo ya mata dan ta masa kyau sosai.
"Da haka kike bani."
Girgiza kai tayi tana buɗe warmers din dan zuba masa.
"Wai ma taron me ake na ga har da motar Ummi tana ina?"
"Yau bakwai ai, shine su ka zo. Suna falonka."
"Menene shi?"
Ya tambaya domin yama manta da wani abu sunanshi bakwai.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 52
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Kinyi kyau."
Ya faɗa yana kamo hannunta da ya sha lalle, gefenshi ya zaunarta ya zame ɗankwalin dake saman kanta yabi ƙananan kitson da aka mata da kallo. Nuratu da idanu take binsa.
Kitson ya shafa har zuwa jelan gashinta dogo yaja mata kaɗan.
"Ban taɓa tsammani kina da dogon gashi ba, na ɗauka kawai tsantsine sai ƙananu da suke kwance na goshi."
Murmushi ɗauke saman fuskar Nuratu tace.
"Abincinka zai huce."
"Ni ki bani a baki."
Ya faɗa yana narke mata tare da kamo hannunta.
Idanuwanta ta waro farare masu haske tace.
"Ka rufamin asiri don Allah. Ummi, Mami sunanan ga Aunties. Ka ga tafiyana ma kar ace na daɗe."
Daga haka ta fara ƙoƙarin tashi a gefensa, ya saka hannunsa ya riƙo hannunta tare da jawo jikinshi ya mata kyakkyawar masauƙi bisa cinyarsa, mamaki dai duk ya kama Nuratu, ga tsoro da kunyar kar aga tajima.
A cikin kunnenta ya mata raɗar da ya sata cikin sauri ta ƙwace jikinta tana tashi ta fita tana dariya cike da kunyar maganar da ya faɗa mata. Sai da ta saita kanta ta gyara ɗaurin ɗankwalinta kafin ta sauƙa falon ƙasa.
Har yamma ƙarfe huɗu kafin kowa ya fara haramar tafiya, duk a tare suka shirya. Yayunta sun gyara mata gidan sai ƙamshin turaren wuta yake. Mami da ƴan matanta su suka fara fitowa za su tafi bayan sunyi sallama da su Ummi da Dr Awwab da ya sauƙo.
Nuratu har da guntun hawayenta ta hana Mami tafiya. Muhsin da daga baya ya shigo sai dariya yake mata tana ƙara turɓune fuska.
"Ni wallahi Mami bana son ki tafi."
Tace tana ƙara riƙe Mami. Itama dai dauriya take dan tana son Nuratu. Kara da kawaici kawai take da ta zauna ta lallashi abunta.
"Za ki saketa ko sai ɓata miki rai."
Aunti Hasiya tace tana zagayowa ta wajensu. Ganin haka ya saka Nuratu sakin Mami tana ɓata rai tare da turo baki.
"Da kar ki saketa kiga, na zagayo sai na ɓata miki rai da dalili."
Baki ta ƙara turawa ta ƙi kulata. Tana kallo suka shige mota suka barta. Hawayenta ta share tana rufe fuskarta dan Ummi da bakinta. Sosai za tayi kewar su kuma tasan za su jima basu haɗu ba.
Ammi kawai kallonsu take dukkansu, musamman wanda yake jan motar da take ganin tamkar nata ɗan Abdallah. Ji tayi kamar ta ƙirashi ko zai ƙi amsa sunan dan ta tabbatar ba ɗanta Abdallah bane.
Dariya yake yiwa Nuratu har da gwalo kafin su fice a gidan Nuratu tana cewa.
"Yaya Muhsin zamu haɗu ai."
Sunan da Nuratu ta ƙirasa da shi ya bawa Ammi tabbacin ba Abdallah bane, sai da tsantsan kama da yanayi da suke, kamar yadda ƴar uwarshi ke kama da ƴar uwarsa Sumayya.
...
"Yaya Awwab ka zo in ji Ummi tana waje."
Hussaina tace da Dr Awwab da yana falon yana jin duk abin da ake. Babu musu ya miƙe ya fita wajen.
"Ummi ga ni."
Yace idonshi kan Nuratu da ta kasa motsi tana sharan hawaye ta cikin mayafinta.
"Ja matarka ka je ka lallasheta. Mu zamu tafi sai wani lokaci."
Cike da kunya ya ƙarasa wajen Nuratu ya kamo hannunta suka shiga falo.
Ganin haka ya saka Ummi da baƙinta tafiya, har da Hanan da kamar tayi kuka dan tana son zaman gidansu.
"Ummi zan wuce gida kawai."
Faɗin Ammi tana tsaye.
"Ammin Sumayya lafiyarki ƙalau? Na lura kwata kwata ba ki da walwala tun zuwanmu."
Ummi tace tana duban Ammi da tsabar tunani ya sauƙar mata ciwon kai.
Kai ta girgiza tana nufan motarta.
"Kai na ya fara ciwo, zan wuce gida na huta."
"To mun gode. Sai wani lokaci."
Faɗin Ummi, daga haka kowa ya shige motarshi direba ya ja suka bar harabar gidan.
...
Me ta haɗa da su? Me ta haɗa da matar da ƴaƴanta da suke kama da yaranta? Me yasa take kama dashi? Me yasa hakan?
Me yasa Ummi da Awwab basa ganin hakan sai ita ɗaya. Ko dai gizau suke mata?
'Ko dai ko dai?'
Ta tambayi kanta tana lumshe ido dan ciwon kai da yake addabatar.
...
Rumgumeta Dr Awwab yayi cikin jikinshi bayan shigarsu falon. Ajiyar zuciya kawai take sauƙewa, ɗumin jikinshi yana ratsata da ya haddasa mata kasala. Sun jima a haka kafin ya ɗagota yana riƙo fuskarta. Cikin idonta yake kallo, kasa janye nata Nuratu tayi. Rana farko da ta kai tsawon mintuna ta jure kallon cikin idanuwanshi.
Tana gani ya ɗaura bakinsa saman nata ya bata light kiss. Idanuwanta ta lumshe ta buɗe sai lokacin ta janye daga kallonshi tayi ƙasa da idanunta.
Har lokacin yana riƙe da fuskarta taji yace.
"Kin cika shagwaɓa Babyna."
Baki ta tura ta juyar kanta gefe. Kwantowa yayi jikinta tana jin hannunshi na yawo jikinta ta kasa hanasa.
"Muje ki cika alƙawarinki."
Ta ji yace murya ciki can da ƙyar ta iya jiyoshi da kyau.
"Wani alƙawari kuma?"
Ta ambata kamar dole duk da ta fahimci zancensa. Hannu ya saka ya juyo da fuskarta da ƙyau yace.
"Wanda na faɗa miki ɗazu mana."
"Ai ni banyi magana ba."
"To ai shine kin yarda kenan."
"Zan maka kuka wallahi."
Tace tana kifta idanuwanta. Murmushi yayi ya sumbaci goshinta.
"Shikenan, zuwa dare na miki afuwa yanzu."
A haka suka zauna har aka ƙira magriba yayi alwala ya wuce masallaci. Wanka tayi ta gabatar da sallah. Riga doguwa marar nauyi ta saka, tabi duk lungu da saƙo na jikinta ta shafa turaren da Aunti Rahma ta bata tace idan ya ƙare ta ƙira ta faɗa mata za ta aiko mata wani, dan yana da amfani sosai. Bayan ta gama ta zauna zaman jiranshi, duk tsoro ya kamata dan gidan ya mata girma sosai.
Sai bayan sallar isha'i ya dawo ɗauke da takeaway da ya musu. A falonta ya sameta kwance tana kallo ya zauna kusa da ita.
"Zan fara bin ka masallaci wallahi."
Tace daga kwancen da take cikin doguwar kujera.
Dariya yayi yana jan yatsun kafarta.
"Me ya farune My Queen?"
"Ba ka dawowa da wuri ba. Ni kuma tsoro nake ji."
"Da gaske."
Yace yana rankwafowa saman kanta, ganin haka ta runtse idanuwanta tana ɗaga masa kai. Ƙamshin turarenta ne ya bugi hancinsa ya kasa janyewa daga saman kanta. Kansa ya kai jikinta ya fara shinshina duk inda ya ji ƙamshin yana sumbata, domin ya tafi da tunanin ainun. Kasa hakura yayi dan gaba ɗaya ta rikitashi da ƙamshinta. Ya ɗauketa suka wuce ɗakinta, rikice mata yayi sosai, ita kanta Nuratu ta tsorata, dan bai taɓa mata haka ba. Haka tana ji ta kasa hanashi abubuwan da yake mata, duk ya kashe mata jiki, har sai da ya sakata itama ta fara tilawar karatun da yake koya mata, ya sata bin umarnin maganar da ya faɗa mata. Abincin da basu ci ba kenan daren ranar.
Da asubanin kusan a makare suka farka wajen Shida saura, a gurguje yayi wanka yayi alwala ya fito ya tasheta kafin ya fara gabatar da sallah. Wanka Nuratu ta gasa jikinta dake ciwo dan ta murzu wajensa. Tayi ɗaura alwala ta fito ta saka kaya tana gabatar da sallah, lokacin ya idar yana azkhar.
"Ina kwana?"
Tace bayan ta durƙusa kusa dashi. Kai ya ɗaga mata, ta miƙe ta nufi gadon ta janye bedsheet ɗin saman cike da kunya, ta wuce bathroom dashi ta saka a washing machine. Fitowa ta ciro wani cikin wardrobe ɗinsa ta hau canza wani, tana jin ya gama azkhar ɗin duk tsammaninta fita zai yi sai ta ga ya nufota. Mazewa tayi taci gaba da aikinta ba zato taji ya riƙota sun faɗa saman gadon ya rumgumeta. Hijabin jikinta ya zare.
"Bari mu biya barcinmu na daren jiya da bamu samu yi ba."
Za tayi magana ya ɗaura yatsansa saman leɓɓenta.
"Barci Please. Da safe zan bada tukuici mai tsada, ko ki zaɓi abun da kike so daga gareni, in har Allah ya hore mini zan ba ki."
Kunyane ya rufe Nuratu ta tura kanta cikin jikinshi.
"Please ki faɗamin. You're so sweet My Love. Ina alfahari da ke kasancewarki matata, ina fatan ki zama uwargidana a matan Aljannahtul Firdausi. Allah yayi miki albarka."
Ta ji maganarshi cikin kunnuwanta yana hura mata iska. Cikin mutuwar jiki da ya sauƙar mata ta lumshe idanuwanta tana ƙara gyara kwanciyarta cikin jikinsa. Wani yanayi take ji yana bin jinin jikinta game da Dr Awwab. Murya ƙasa ƙasa tace.
"Ban baka kaina ba dan ka biyani, asalima farin ciki nake da yadda ka ke shiga farin ciki a kullum idan mu kayi tarayya, wannan kaɗai ya isheni, addu'aarka ya wadatar da ni."
Matseta yayi har sai da tayi ƙara ya sassauta riƙon, ji yake kamar ya haɗiyeta ya huta dan kauna.
"Ina sonki sosai Matata."
Ita dai Nuratu ta kasa magana dan kunya da farin ciki, idanuwanta suna cika da hawaye tana ƙoƙarin shanyewa kar su zubo. Ita shaida ce dan taga so jiya wajensa, dan abubuwan da Dr Awwab ya mata ba za ta iya faɗarsu ba sirrinsu ne. A haka wani baccin ya ɗaukesu.
***
Sha biyu da mintuna uku.
"Kamar sallama nake ji Hajiya Sadiya?"
"Nima hakan na ji kamar."
Mami tace ga Aunti Zarah kafin ta yi shuru, dan jin da gasken sallama ake. Ba zato taji muryar da bata tsammaci ji yanzu ba, domin alaƙarsu ya jima da yankewa. Kuma bata burin sake ganinshi a rayuwarta.
Aunti Zarah ne ta amsa tana gyara zaman mayafinta, ta kalli Mami da ta kasa daina tunanin me ya zo yi a wannan lokaci kuma. Me ya dawo dashi rayuwarta.
"Hajiya Sadiya ki gyara mayafinki zai shigo fa, kina jin na bashi umarni."
Wani baƙin ciki ne ya rufe Mami, cike da taƙaicin da ya rufeta ta haɗa rai tana jan mayafinta ta rufawa jikinta.
"Suwaiba ki je ɗakin can ki jira ni."
Aunti Zarah tace tana nunawa matashiyar budurwa da ta kawo dan taimaka mata ɗakin Munirat na da. Babu musu ta miƙe tare da kullin kayanta ta shiga, dai-dai lokacin ya shigo cikin falon haɗe da wani sallamar a bakinsa.
Aunti Zarah kaɗai ta amsa. Jin rashin amsar Mami ya kai dubanshi gareta, ranta a haɗe ta juyar kanta gefe.
Tana nan a Sadiyarta mai son ƙamshi da gayu, duk yaran da ta tara har da jikoki amma jikinta bai nuna ba, ko dan ta jima babu aure kuma babu haihuwa, sai jin daɗin rayuwa, babu takurar miji balle wani aikin gida da dawainiyar shi kansa miji.
"Bismillahi Alhaji Mamman."
Ya tsinci muryar Aunti Zarah, a dadare ya zauna yana cewa.
"Ina wuninku?"
"Lafiya ƙalau, ina Amman yara?"
"Lafiyarta ƙalau."
Yace yana sake kallon Mami a karo na biyu dan har lokacin ta ƙi duban inda yake balle yasa ran zata gaishesa ko ta masa magana.
'Maganar da ya zo mata da su fa?'
Ya tambayi kansa, ganin haka ma ta ƙi masa magana balle ya sako zancen da yake son mata tsawon lokaci. Yana jin za ta koreshi, kora na ƙare.
Bai san me zai yi ba? Bai san ta yaya zai warware wannan abun ba? Bai san ko zata karɓi buƙatarshi ba? Yana son faranta ranta ta wannan hanyar da shi kaɗai zai saka ta gane cewa shi Mamman ya gane gaskiya. Ba Mamman da ta sani a baya bane. Wannan wani ne da yake da buƙata da burin ƙara haɗa rayuwa da ita.
Jin shurun yayi yawa tsakanin mutane biyun ya saka Aunti Zarah miƙewa.
"Bari in baku guri."
Sai lokacin Mami ta juya ta kalleta, kafin tace wani abu Aunti Zarah ta ƙarasa inda take ƙasa ƙasa tace.
"Ki ji mai zai faɗa miki Please Hajiya Sadiya."
Girgiza kai tayi, kafin tace wani abu Aunti Zarah ta nufi ɗakin Mami. In har hasashen da ta hango zai zama gaskiya, ita kam bata san da me zata ƙira wannan abun ba.
...
"Ina wuni?"
Suka faɗawa juna a tare, sai Mami ta ji wani iri tayi shuru, hakan yasa Alhaji Mamman cewa.
"Shikenan bari ni in amsa lafiya ƙalau. Ya labarin wajen Nuratu?"
"Lafiya."
Mami tace taba jin wani abin banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Jinjina kai yayi cikin ƙarfin hali ya kai dubanshi gareta. Tattare da ƙarfi da jarumta ya samu bakinsa da furta.
"Sadiya aurenki nake son yi a karo na biyu in har kin amince? Kar kice a'a don Allah. Sannan in za kiyi duba da abin da ya faru a baya kice a'a, to ina jin kamar har yanzu ba ki yafe mini ba."
***
"Ammi menene? Ammi tun jiya nake lura da rashin walwalarki. Ko dai har yanzu ciwon kai ne muje asibiti."
Ammi dake zaune bakin gadonta ta kalli ɗanta matashin saurayi ɗan shekaru ashirin da takwas. Tun jiya yabi ya damu kanshi da rashin fara'arta, tace masa kanta yake ciwo amma yaƙi kwantar da hankalinsa. Zuwa safiyar yau ya tambayeta rashin walwalarta yafi goma.
Murmushin dole tayi tana dubanshi.
"Abdallah babu komai fa. Kawai dai?"
"Kawai me Ammi? Dan Allah ki sanar dani wani abun in yana damunki?"
Ya katseta da sauri.
Yanda yayi da fuskarshi sai ya ƙara jefa zuciyar Ammi cikin kogin tunanin da ta kwana tana yi, domin fuskar sai ya koma mata na matashin saurayin da ta gani tare da Mami sak.
Ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa tamkar yau ta fara ganinsa.
"Ammi!"
Abdallah yaja sunan da hakan ya fargar da ita tunanin da ta faɗa.
"Kace menene?"
"Ki faɗamin damuwar ki don Allah. Ko dan kinga ni ƙaramine, sai Babban Yaya ko Yaya Sajeed."
"A'a ba sai ka ƙirasu ba, na faɗa maka babu komai."
"Ammi wani abun ya faru?"
Ya tambayeta da sanyin jiki ganin cikin sanyi take masa maganar.
Kai ta girgiza tana ƙoƙarin mai da hawayenta da ta rasa na menene tace.
"Wani abu ne. Amma bansan ta ina zan fara ba, ban san ta ina ba Abdallah. Ka bani lokaci."
Hannun mahaifiyarshi ya kamo ya damƙe.
"InshaAllah Ammi za kiyi na nasara. Za muyi nasara. Kar ki damu, ina tare dake."
"Ina fatan hakan."
Tace tana sauƙe numfashi tare da murmushi. Sai lokacin taji sauƙin abin da take ji.
Sallama ya mata ya fita dan zuwa aiki. A harabar gidansu ya shiga motarsa da yake wanke sai sheƙi yake. A hankali ya murɗa sitiyarin ana buɗe masa get ya fita. Yayi nisa cikin tafiyar ya jawo wayarsa yayi ƙira, ya kusa tsinkewa aka ɗauka. Bayan gaisuwa ya sanar da wanda ya ɗauka.
"Ka ƙara bani lokaci."
Banji na gefen me yace ba su kayi sallama ya ajiye wayar yana cigaba da tuƙi.
***
Ba ta taɓa tsammani rainin hankali da rashin tunani na Alhaji Mamman ya kai haka ba, sai yanzu da ya furta mata kalmomin rainin hankali, kallonshi tayi duk da ya kasƙantar da kai ya zama wani abun tausayi hakan ba zai sa yayi nasara akanta ba. Ɗauke kanta ta yi ganin idanuwansu sun haɗu yana aika mata saƙonnin hakuri da yarda da buƙatarshi.
"Kar kice a'a Sadiya dan Allah na haɗa ki dashi. Wallahi wannan ba Mamman da kika sani bane. Wani ne wanda yayi sabon tuba yake muraɗi da burin auren Sadiya, in har ta amince. Dan Allah Sadiya wannan shine rufin asirin mu."
Girgiza kai tayi duk maganganunsa ba suyi tasiri akanta ba.
"Da baka san auren shine rufin asiri na ba sai yanzu? Da da ka rabu da ni kasan bani da uwa da uba, babu inda zanje, baka san auren shine rufin asirina ba. Kai ko kunya baka ji? Ko kuma kana ganin idan ni na yarda da buƙatarka na kyautata Nuratu?
Ba zan iya ba, ba zan koma aurenka ba, na riga na gama magana zaka iya tafiya."
Bai ji haushin kalamanta ta ba domin shi ɗin ya san mai laifi ne gurinta, da ƙyar ta yarda da buƙatarshi cikin lokaci ɗaya ba. Zama ya gyara yana dubanta, ranta a haɗe cikin fushinta da yake burgeshi.
"Sadiya ko dai dan kinga bani da arziƙi yanzu ne? Ko kuma har yanzu ba ki yafe mini bane?"
Wani kallo ta jefeshi da shi.
"Da da arziƙin na aure ka?"
"To yanzu ma bani da shi sai mu koma rayuwarmu na baya. Dama ance wani arziƙin masifa ne, kuma na yarda. Sannan nima bana cire haƙƙin ciki, shi yasa Allah ya jarabceni da hakan. Sannan aboki wanda ba nagari ba shi ya sani wannan hanyar, bai nuna mini hakan ƙaddara bane da rashin cire haƙƙin ciki ba ya sani aikita dana sani. Dan Allah ki yafe mini mu koma rayuwarmu kamar baya."
A fusace tace.
"Nace maka bazan iya ba ko. To na gama magana. In auren kake son ƙari ka tafi ga can mata a titi."
Daga haka ta miƙe za ta wuce ɗaki taji yace.
"Ni ke nake so. Kuma inshaAllah sai mun mai da auren mu Halima."
Juyawa tayi ta watsa mishi wani kallo tana jan tsaki kafin ta wuce ta barshi zaune. Ya jima kafin ya miƙe ya fice.
Dama ya san da wuya ta amince dan abubuwan da ya mata, sai dai hakan ba zai sa ya hakura ba fa sai ya sake mallakarta a karo na biyu domin cikar burinshi.
...
Gida ya nufa kai tsaye, a harabar gidan ya ciro wayarshi ya ƙira Aunti Rahma. Bayan amsa sallamarta ya bata umarni.
"Rahma ran Juma'a ina son ganinki da ƙannenki, ki sanar da su hakan, ku zo gida."
Daga haka ya kashe wayar ya jefa a aljihunsa yana shiga falon. Amma Jidda cikin fara'a ta tareshi kamar kullum duk da yana ɗan ƙoƙarin ganin ya danne abin da yayanta ya sashi aikatawa, domin laifinsa ba zai shafeta ba kuma halinsu ya bambanta. Ruwa ta kaeo masa tana masa sannu da hanya.
"Ina Ameera?"
Shine tambayar da ya mata jin shurunta yayi yawa ga yamma ya gabato.
"Tana ɗaki."
"Ƙiramin ita."
Yace dan ya tabbatar, ya fara lura da yawan fitarta ko bata da lecture.
Babu musu ta miƙe ta leka ɗakin ta dawo.
"Wallahi yanzu na barta nace bari in gama ayyukana."
"Ƙirata a waya."
Babu