Follow us on social media
Showing 141001 words to 144000 words out of 148866 words
Chapter 48 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
mu, kuma sun kasa tambayar mu dalili.
Idan na sanar da ku lokacin mun mance da babinku a rayuwarmu ka yarda, don shaf mun mance da ku a zuciyoyin mu.
Allahamdulillahi Allah ba azzalumin bawansa bane, kusan shekara uku Allah ya azurtamu da abin da zamu riƙe kanmu da yaranmu, a lokacin Yaya yana jin jiki don yau lafiya gobe jinya, kullum yana sanar da ni ciwon sa bana rashin dukiyarmu bane, akwai wani abu da yake damunsa amma ya rasa menene in masa addu'a. Idan ya min irin maganganun nan irin haka ranar wuni zan yi ni ma zuciyata da kunci.
Abun tashin hankali maimakon ya samu sauƙi ganin arziƙi ya ƙanƙama sai ma jinyar da har yake hanasa fita. Haka wata rana ya ta shi da aman jini, a rikice Zainab ta ƙira ni na zo gidansa. Ina zuwa duk yadda nayi mu tafi asibiti ya ƙi, a hannuna a gabana Yayana ya bar duniya, maganarsa na ƙarshe kafin shahada shi ne Muhammad da Sadiya.
Dukkanmu mun ji mutuwarsa musamman Zainab da ya kusa jawo mata ɓarin ƙaramin cikin jikinta da shi ma kansa Yaya bai sani ba har ita, da ƙyar aka shawo kan abin. Haka muka kai Yaya Abdul muka dawo. Na yi kuka na yi don shi kaɗai ya ragemin a duniya, sai dai sunan mutane biyun da ya ƙira sun tsayamin a rai.
Bayan sadakar arba'in dangin Ummi su ka so ɗauketa na nuna zan kula da ita da yaranta da abin da za ta haifa, ita ma kuma ta yarda don bata son yin nisa da yaranta. Haka ta ci gaba da zama a gidan aka bar mata mace ɗaya tana kula da ita. Duk abin da na samu sai na fara bawa gidan Yaya kafin gidana. Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya har Ummi ta haifi ƴan biyunta mata. Hassana da Hussaina aka raɗa musu babu wani sunan don tace ta bani zaɓi. Har lokacin na kasa tuna mutane biyun su waye su da Yaya ya faɗamin.
Rayuwa ya ci gaba da tafiya abubuwa suna faruwa har zuwa girman yaranmu duk nauyin yana kaina, na yi na yi Ummi ta yi aure ta ƙi, haka danginta ma, ƙarshe muka rabu da ita ko don yaranta.
Bayan shekaru goma na samu labarin rasuwar Alhaji Yousufa bayan karayar arziƙi.
Rayuwa na tafiya yaranmu su ka gama makaranta masu aure sun yi Babban Yaya, Sumayya, Sajeed, Awwab, Zaituna da Ikhram, har yau ga shi yan biyu sun yi aure. Sai dai Sumayya ta rasu a haihuwa shekaru biyu kenan.
Sai dai har yau Ummi da Ammi babu wanda ya ƙara tambayar mu zancen Alhaji Yousufa ko wani danginsa da muke ƙira na mu."
Daga haka ya dakata yana share hawayensa ya kalli Kawu Muhammadu da yake jin zafin rashin ɗan uwansa. Amma a jikinsa ya ji ba lafiya ƙalau ba ko haka kawai ba mutum zai manta da ƴan uwansa.
Cikin raunin murya Baffa ya ce.
"Muhammadu, Sadiya don Allah ku yafe mana, wallahi ba haka kawai ba muka mance da ku, ko muka cinye dukiyarmu ba."
Mami ne ta yi magana daga zaunen da take cikin sauri, cikin muryarta da ya dashe don kuka tace.
"Yaya ka daina bamu hakuri, Allah ya riga ya ƙaddara hakan. Wallahi ni kam na yafe."
"Ni ma hakan. Haɗuwarmu da ku yafi komai daɗi da zamu godewa Allah. Sai dai Yaya ka kula haka kawai mutum zai manta da ƴan uwansa."
Faɗin Kawu Muhammadu har lokacin suna riƙe da hannun juna shi da Baffa.
Alhaji Mamman sai lokacin ya yi magana.
"Kamar akwai asiri a tattare da lamuran. Idan hasashena gaskiya ne, Alhaji Yousufa ya yi amfani da wannan hanyar ya mantar da ku ƴan uwan ku don ya mallake dukiyar ku, ƙarshe kuma ya hanaku shi kuma bai basa amfani ba. Ku ya rabaku da danginku kuma ya hanaku tunanin su."
Wannan lokacin Babban Yaya ne ya sa ka baki.
"Tabbas hakane ni ma nawa tunanin ya ba ni. Amma yanzu allahamdulillahi da komai ya bayyana, shi ma baya raye balle ace za'a ɗauki hukunci."
"Yanzu kam na yafe masa, Allah ya ji kansa shi da Yaya. Na so yaga wannan ranar, ga yaranmu da jikokin mu. Ku matso in ganku."
Baffa ya ce yana share hawaye. Babu musu su Aunti Rahma suka nufi gurinsa da yaransu har Nuratu da Hafiza. Dukkansu sai da suka yi musabaha yana tambayarsu sunansu. Nuratu ce ƙarshe ya damƙe hannunta ya ce.
"Tun ranar dana haɗa ido da ke zuciyata ta buga, da tunaninki na kwana a raina. Ji na ke kamar akwai inda nasan fuskarki. Ashema ƴata ce."
Murmushi ta yi kanta ƙasa.
"Ni ma Baffa haka."
Juyawa ya yi ya kalli Aunti Rahma.
"Wannan Sumayya ta ce ta dawo. Ke kuma sak Kaka."
Ya faɗa yana nuna Hafiza. Gaba ɗaya dariya suka sanya har manyan su ka dara. Ya kalli Muhsin ya ce.
"Wannan kuma Abdallah, amma yafi kama da Yaya Abdul sosai."
Murmushi nan ma aka yi, Nuratu ta ɓata rai jin bai ce tana kama da kowa ba.
"Baffa ni fa?"
Hannunta ya riƙe yana murmushin farin ciki.
"Ke ma kina kama da mu amma ba sosai ba, lotsawar kumatun namu ne don Yaya yana da shi."
Murmushi ta yi ta ɗan saci kallon Dr Awwab, idanu suka haɗa ta ɗaga masa gira ɗaya. Murmushi ya yi yana lumshe idanunsa tare da lasar lips ɗinsa na ƙasa. Kawar kanta ta yi jin Baffa yana magana.
Kallon Hasiya ya yi ganin ta yi shuru ya ce.
"Wannan kuma baƙin halin irin na Sajeed, shegen ƙin ma mutane magana. Sai faɗa, na rasa wa ku ka biyo, iyayenmu bamu taɓa jin kansu ba, ni bani da shi Yaya ma haka da Kawun ku, gwara Sadiya wani lokacin tana taɓawa idan an taɓota."
Dariya gaba ɗaya aka sanya har Sajeed da Aunti Hasiya da ya ce halin su na kama, sai kuma lokacin kowa ya kula da rashin son maganarsa, za ma su rantse tun da aka zauna ko tari bai yi ba.
Haka ya yi ta tsokanar su kamar jikokin sa sun mayar da shi kakan su. Ya karɓi yaransu yana tambayar su sunayensu.
Mami ma ƙarasawa wajen su ta yi ta zauna, hannu Baffa ya miƙa mata suka yi musabaha tana murmushi da kuka.
"Ya isa kuma kukan haka. Ni fa Sadiyar dana sani tana da jarumta."
Murmushi ta yi ta kalli Alhaji Mamman ta kalli Baffa ta ce.
"Yaya ga babansu Rahma."
"Mun san juna na ɗan lokaci a auren Awwab. Amma yanzu za mu yi sabuwar gaisuwa. Matsonan ƙanina."
Da murmushi jin maganarsa Alhaji Mamman ya matsa su ka yi musabaha da sabuwar gaisuwar mutunci. Alhaji Mamman har kunya ya ji tuna rashin mutuncin da ya tsula masa.
Mami gurin ta bari bayan ta kora Aunti Rahma da Hasiya da Rukayya kitchen su ɗaura abinci, domin basu ga na tafiya yau ba. Gurin su Ammi ta ƙarasa sai lokacin suka gaisa ana ƙara jajantawa.
Wai wannan ƙanwar mazajen su ce, yaranta kamar yaran su. Wani abu sai ikon Allah.
Gefe ɗaya su Awwab ne da Sajeed da babban Yaya da Abdallah da Yaya Al-ameen da Muhsin suna hira, hankalin Dr Awwab duk yana kan Nuratu da yake ganin sai ɓata rai ta ke. Ganin hankalin su yana kan hiran da Abdallah yake zuba musu ya miƙe, kai tsaye ya isa inda take ya ɗan rankwafo saman kanta.
"Are you ok My Baby?"
Girgiza kai ta yi duk da ta ji kunyar yadda ya sata gaba, don ma kowa hankalin sa baya gurin su.
"Zazzaɓi nake ji tun ɗazu."
Hannunsa ya ɗaura a saman wuyanta.
"Za ki iya cin abin da su Aunti Rahma suke girkawa."
Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, don ta tsani abu mai suna abinci gaba ɗaya.
"To me za ki ci in siyo miki."
"Zansha Maltina."
"Shi fa ki ka sha da safe kuma yanzuma haka. Wallahi zan fara miki ɗurai."
Dariya ta yi ta miƙe tsaye da ƙyar.
"Bismillah don Allah."
Ƙasa yayi da murya.
"Zan kamaki yarinya, za ki yi bayani."
Wani murmushi ta masa ta bi gefensa ta wuce. Shi ma gurin zamansa ya koma yana gani ta haye sama da ƙyar. Tausayinta yake ji ya kula ƙarfin hali kawai take.
Bayan sun gabatar da sallar azahar a gidan a falon baƙi suka dawo falo, anan suka tarar an jera musu abincin su suka zauna. Can sama kuma iyaye mata ne a falon Nuratu suna cin nasu suna hira, maganar kunya ko surukai tuni sun jinginar gefe don jini ya haɗa su. Hussaina da Zaituna da Ikhram da suka ji labari kamar suyi tsuntsuwa. Nuratu tana ɗakin Dr Awwab a duƙunƙune cikin bargo a gadonsa, mugun zazzaɓi ne ya rufeta.
Kiran wayarta Dr Awwab ya yi tayi don ya tabbatar ta ci wani abun bata ɗauka ba. Haka ya ƙira Rukayya ta sanar masa bata tare da su. Babu shiri ya miƙe ya nufi ɗakinsa don nan zuciyarshi ta kaisa.
Aikuwa halin da ya ganta ya rikitasa, ruwan sanyi ya haɗamata ya mata wanka ya fito ya nema mata kaya cikin kayakin da take bari a ɗakinsa. Kan gadon ya kwantarta ya lulluɓeta.
"Kin ci abinci? Ko in ƙira Dr Sageer ya duba ki. Yau dai babyna ya mana fallasa, kowa fa sai yasan shi yake wahalar ki."
Kamar ta yi kuka tace.
"To ka fita mana."
"Kar wani yayi zargin wani abun muke."
Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya.
Ƙara turɓune fuska ta yi ta ƙi magana.
"Bari in nemo miki abinci da magani kafin su tafi in ƙira Dr Sageer ya zo ya duba ki."
Kai ta daga masa ya fita. Fruit salad ya sa ka Hassana ta haɗa masa ya ɗauki ruwa ya koma ɗakin. Da ƙyar ya lallaɓata ta saka abu a cikinta kafin ya bata maganin me haɗe da na barci. Tuni barci ya kwasheta ya lulluɓeta ya fito.
Ƙarfe huɗu aka gama yanke shawarar Mami za ta kwana gidan Ammi ita da Kawu Muhammadu, yaran gidan Ummi gobe sai su koma. Kowa ya yi farin cikin haka, don ansan ƴan uwan suna buƙatar hira na musamman tsakanin su. Bayan sallar la'asar suka musu sallama suka watse. Ƴan matan sai da suka gyarawa Nuratu gidanta kafin su tafi bayan Dr Awwab ya sanar musu tana barci bata jin daɗi. Murmushi suka yi kowa yayi shuru da bakinsa don sun gano ta.
Suna tafiya Dr Awwab ya kira Dr Sageer ya zo ya dubata, nan ya sanar masa irin haka zai dinga faruwar har sai cikin ya girma. Daga haka suka yi sallama.
Zuwa dai dare jikin yayi sauƙi sai ɗan hajijiya. Daren duk motsinta zai tambayeta me take buƙata.
...
Can gidan Baffa ɗakinsa ya sauƙar da Kawu Muhammadu don cewa yayi sunfi ƙarfin a ajiye su ɗakin baƙi. Kwana suka yi suna hira su biyun suna bawa juna labarin irin rayuwar da ya fuskanta.
Ammi ma a ɗakinta ta sauƙe Mami. Ranar sun ga gata a gidan Baffa. Da asubahi Mami ta samesu suka ɗaura daga inda suka tsaya.
Can ma ɓangaren gidan Ummi haka, ɗakinta ta sauƙe yaran Mamin, da taimakon mai aikinta ta musu komai su da yaransu. Ta ɗauko musu album na aurensu da babansu Awwab suna kallo. Duk su huɗun kamarsu ɗaya, dole yaransu suma kamarsu ya yi ƙarfi. Hassana ma dai ranar dole Abdallah ya barta ta kwana gidan, haka Hafiza ma.
Washegari a gidan Ammi aka taru wajen ƙarfe goma sha ɗaya, hatta matan Baban Yaya da Sajeed sun zo da yaransu. Mami tun da ta ga ƴar Sumayya ta riƙeta duk inda ta yi yarinyar tana bibiyarta. Hatta Nuratu ta lallaɓa ta zo duk da rashin kwarin jiki da take ji. Kowo da ya mata ya jiki ya yi shuru, don sun gano musabbabin ciwon.
Bayan gaisuwa aka zauna sake kafa hira. Har wajen karfe ɗaya suka ci abinci suka gabatar da sallah kafin su ɗauki hanya cike da kewar juna. Daren Baffa ya samu nasarar rokar Kawu Muhammadu ya dawo kusa da su Nijeriya. Ya ƙi amincewa don ya saba da zaman can, haka ya hakura ya barsa akan lokaci zuwa lokaci za suna kai masa ziyara, shi ma ya musu alƙawarin za iya zuwa tun da babu nisa.
Haka kowa ya watse ƴan Damaturu suka koma, kowa ya koma gidansa.
Amma Jidda dai tasha labari wajen Mami, ta mata murna sosai. Amira dai rumgume Mami ta yi tana murnar dawowarta babu kunya.
"Mamina nayi kewarki, gidan duk babu daɗi. Ga fine Baby kin kawomin."
Murmushi kawai Mami ta yi ta kalli Islam (Ƴar Sumayya) da ta saka kukan sai ta biyota, dole aka haɗamata kayanta suka zo tare.
"Ki mata wanka ki bata abinci zan huta. Jikina duk ciwo yake."
Daga haka ta koma ɓangarenta, Amma Jidda ta bita da kallon tuhuma tana murmushi. Amira ma jakar Islam ta ɗauka suka nufi bangaren Mami. Wanka ta mata ta bata abinci kamar yadda Mami tace ta hau mata wasa don yarinya ƙaramace ƴar shekara biyu sai dai bata da ƙiwa ko hayaniya.
...
Bayan kwana biyun Mami ta kasa gane kanta, ciwon jiki ya sata a gaba sosai. Amma Jidda da Alhaji Mamman ido suka saka mata, don gani suke tasan abunta ɓoyewa take. Ita kuma har ga Allah ta ɗauka ta wuce level ɗinnan, bata kawo hakan a ranta ba. Ƙarshe dai dole Alhaji Mamman ya sa ta ziyaran asibiti ta dawo masa da damuwar da ta shiga na sakamakon ciki na wata ɗaya.
Ranar da damuwa ta wuni Amma Jidda na lallashi.
Da ta gaji ta ce.
"Haba Amma. Nuratu ma fa laulayi na barta take yi, ita ce autana Bayan tsawon shekaru ashirin da huɗu na sake haihuwa. Haba don Allah in jera haihuwa da autana."
"To ni ki haifa ki bani. Kinga dai ni biyu ne nawa, kuma ina son haihuwa Allah bai yi ba, ke kuma sun ishe ki naga alama."
"Ba maganar wasa ba Amma. Abbansu ka yi magana asan ya za'a yi da cikin nan."
Mami ta ƙarasa maganar tana kallonsa. Murmushi ya yi ya miƙe.
"Shaidar kin koma gidan uban yaranki, tsohon zumanki, ki haifa muna so mu ko Jidda?"
Kai ta ɗaga tana dariya.
"Sosai ma, Allah yasa ma ki yi kunika(kwalba da indagi)...."
"Ban ji bakinki ba Jidda."
Mami tace tana miƙewa ta wuce ɓangarenta. Idan ta ƙara wani cikin bayan wannan ai ta kaɗe, balle yadda tasan Alhaji Mamman baya son tsarin haihuwa da za ta yi kunika zai so, ko girmansu ba zai duba ba.
"Allah ka rufamin asiri ka sa daga wannan haihuwar ya tsaya. Wanda na haifa Allah ka albarkace su ka rayamin su. Ameen."
Ta ƙarasa addu'ar tana shafawa ta shafa cikinta. Kunya sosai take ji, tana tunanin idan yaranta suka ji ya ya za su ji.
....
Laulayin Nuratu ya fara sauƙi sai rashin ci duk ta rame. Dr Awwab ya rasa ya zai yi da ita, ban da maltina da peack milk bata iya shan komai sai wani lokaci fruit salad, sai kuma idan Ummi ta aiko mata abinci a gidanta na gargajiya, to shi ne za taci da ɗan dama.
Haka suka ci gaba da kula da cikin har ya shiga wata biyar ta fara ƙoƙarin cin abinci kaɗan kaɗan, a hankali kuma kwaɗayi ya biyo baya kamar ta ci babu. Kullum Dr Awwab ya fita idan zai dawo sai ya siya mata duk abin da ya gani a hanya.
Ummi duk bayan wani lokaci sai ta zo dubata haka Ammi ma da matan Babban Yaya da Sajeed duk sun kawo mata ziyara. Can gida ma kullum sai sun yi waya da su suna tambayarta lafiyarta, babu wanda ya sanar da ita labarin cikin Mami.
....
Lokacin da yaran su ka ga ciki jikin Mami babu wanda ya yi magana, Muhsin kam kayansa ya tattara ya bar gidan ya koma gidan da Alhaji Mamman ya mallaka masa. Wannan kayan kunyar har ina. Tsakani da Allah kunya ya ji da ya ga cikin.
Matan a hankali cikin dabara suka tambayi Mami watannin cikin ta sanar musu, suna ƙoƙarin taimaka mata haka Amira da tafi kowa murna. Islam kam ta dawo gurinta da zama ta ƙi komawa. Ammi, Ummi da Baffa duk sun kawo mata ziyara, haka Zaituna da Ikhram ma har da yaran su.
Mami ta sha tsiya wajen Aunti Zarah da ta kawo mata ziyara ta ga cikin.
Nauyin cikinta da laulayi bai sa ta bar sana'arta ba, domin an gama komai saura zuba kayan da tayi order za'a kawo mata.
Haka Alhaji Mamman ma kasuwanci ya bunƙasa, shago sai cika yake, wani arziki da Allah ya bunkasa masa baya kwatantuwa.
'Tabbas Sadiya alheri ce'
Abin da ya ke faɗa kullum don yasan irinta ne masu ƙashin arziƙi da ake faɗa.
...
Bayan wata huɗu.
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 62.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
MURFI.
***
Da ƙyar ya barta ta sauƙo ƙasan jin ana danna door bell kusan sau uku. A hankali take taka matattakalar benin don cikin jikinta ya girma sosai. Bayan ta gama sauƙar ta isa bakin ƙofar falon ta buɗe. Da kallo ta bi bakuwarta su. Yarinyar na neman shiga mata hanci ta kudundune. Rai ta haɗa tana riƙo kugu.
"Lafiya? Ko kina buƙatar wani abu ne?"
Murmushin gefen baki Binta ta yi tana jefa mata wani shegen kallo, kai ta girgiza kafin ta ce.
"Gurin ƴata na zo. Bani guri in wuce Please."
Ta ƙarasa maganarta tana ƙoƙarin bin gefe ta wuce. A zafafe Nuratu ta cafkota ta dawo baya. Cikin ɓacin rai ta hankaɗata baya ta nunata da yatsa.
"Last warning da za ki ƙara kwaso shegun ƙafafunki ki shigomin cikin gidana. Banza marar kamun kai, jahila kawai."
"Ni ce jahila kuma banza?"
Binta ta ce da mamaki da baƙin cikin zagin da Nuratu ta mata ya shigeta. Kafin ta bata amsa ta yi kanta ta cakumo wuyan rigarta ko duban cikinta bata yi.
"Ni ce jahila kuma banza. Don ubanki yau za ki mini bayani, sai in illataki yadda mijinki ba zai iya gane ki ba."
Nuratu jin bayanta ta yi ya riƙe, da ƙyar ta samu ƙarfin kwace wuyar rigarta ta watsa Binta mari.
"Ke kam mahaukaciya ce hala."
A haukace Binta ta ɗaga hannu za ta rama marin da Nuratu ta mata ta ji tsawar da ya hargitsa falon da ƴaƴan hanjinta ta dakata.
"Kuskure mafi muni da ƙazamin hannunki zai taɓa fuskar matata."
Ta mutuƙar tsorata da ganinsa cikin wannan ɓacin rai. Baya ta ja tana ƙoƙarin fita ya buga mata tsawa.
"Zan karya ƙafafunki ki ka kuskura ki ka bar falon nan."
Cak ta tsaya tana rawar jiki, ba ta taɓa tsammani za ta ji tsoronsa haka ba.
Gurin Nuratu ya ƙarasa, lokacin ta samu ta dafa kujera jin ciwon bayan ya kasa falawa, ga shi ya fara sauƙa maranta. Dafa kafaɗunta