Follow us on social media
Showing 54001 words to 57000 words out of 148866 words
Chapter 19 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
su yi musabaha, babu musu Alhaji Kashim ya miƙa hannu su kayi musabaha dan shi yake neman abu a wajenshi in ba haka ba bai kai ba.
"Fatan zan ji alheri Alhaji Mamman?"
Faɗin Alhaji Kashim bayan ya bada umarni a kawo wa Alhaji Mamman coffee da wayar landline dake ofishinsa.
Bsbu musu babu tsoron Allah Alhaji Mamman yace.
"Na amince zan bawa ɗanka auren ƴata, sai ku zo da ƴan uwa ayi magana in son samu ne zan haɗa auren da na ƴar uwarta da za'a yi nan da wata biyu."
Faɗaɗa murmushin sa Alhaji Kashim yayi cike da farin ciki.
"Allahamdulillahi, ai mu ko yau ka tashi a shirye muke kasan bamu da matsalar komai. Za ka ganmu cikin weekend da yardar Allah. Nagode sosai."
Tabbas hakane basu da matsalar kuɗi a rayuwar su kamar yadda ya faɗa, miƙewa tsaye yayi.
"Zan wuce Alhaji Kashim sai na ji ka."
"Ko ruwa baka sha ba?"
Alhaji Kashim yace yana miƙewa tsaye shima.
Girgiza kai Alhaji Mamman yayi yace.
"Na ƙoshi. Sai wani lokaci."
"Nagode sosai."
Yace ya masa rakiya ya dawo ofishin sa.
Wayarshi ya ɗauka yayi ƙira ringing daya aka ɗauka.
"Ka ƙara masa matsayi ya amince da buƙatar mu. Maganar kuɗi za kaji alert."
"An gama ranka daɗe."
Oga Dauda yace cikin farin ciki jin ta dalilin Alhaji Mamman zai samu wani alheri.
Yana ajiye wayar ya rubutu shaidar ƙarin girma ya aika ofishin Alhaji Mamman aka ajiye masa.
****
Yau tun safe wanki take yi duk ta gaji sai mita take kamar tayi kuka, mai wankin su yayi waya ba zai samu zuwa ba ya saka Mami tace tayi. Kuka ne kawai ba tayi ba dan a rayuwar ta ta tsani wanki, tana yi tana turo baki ran nan a haɗe dan ma Munirat tana taimaka mata.
Saura kiris ya ƙare ta ji Mami na kwala mata ƙira ta ɗauraye hannunta ta shiga falon.
"Wayar ki yana ta ƙara tun ɗazu."
Mami tace hankalinta a kan talabijin. Gurin socket ɗin da wayar ta yake caji Nuratu tayi ta ɗauka, ƙira ne daga Yaya Al-ameen kusan uku da sakwanni biyu. Ɗaukar wayar tayi ta buɗe ta karanta saƙon.
*"Na kira ki baki ɗauka ba na so muyi magana mai muhimmanci, zan shigo gari gobe ƙanwata. Zan zo ganin ki, nayi wani karambani cikin rayuwar ki amma ina fatan zaki amince da hakan domin alheri ne."*
Ta karanta sakon yafi sau biyar ta kasa fahimtar takamemmen mai yske nufi, abinda ta gane daga ciki shine yace zai zo, sai kuwa ya zon za tafi fahimtar maganganun shi.
"Waye ne haka?"
Ta tsinci muryar Mami ta juya tana mai da wayar ta ajiye.
"Yaya Al-ameen ne. Gobe yana zuwa."
"Su dai basa gajiya."
"Ni fa sun ishe ni Mami, na faɗa musu ba zasu taɓa samun abinda suke nema gurina ba sun kasa fahimta. Babu aure a rayuwar Nuratu."
Cikin fushi Nuratu ta ƙarasa maganar tamkar a gabansu take, duk yadda tayi dan ta sanar da su sun kasa janye kudirin su a kanta.
Shuru kawai Mami tayi ganin ran Nuratu ya ɓaci yanzu in ta biye mata wani abin zai biyo baya ya sata yin shuru ta rabu da ita da ta gama faɗar ta fita dan kanta.
Bayan ta gama wankin tayi wanka kafin ta gabatar sallar la'asar ta kwanta hutu, Munirat ce ta ɗaura abincin dare dan Nuratu cewa tayi ta gaji haka Mami ta rabu da ita.
Tana danna wayarta tana jin daɗin hiran da suke gudanarwa a group ɗinsu na mata su ƴan uwan juna, Aunti Rahma, Aunti Hasiya, Walida, Ameera sai ita da ta shigo daga baya, tsokanar Walida suke akan yadda take juya wanda zata aura tana sassauta mishi duk ya zauce a kanta.
Wani magana da Walida ta faɗa ya saka Nuratu shiga tunani, zuciyarta ya faɗa wani tunanin da bata taɓa kawo hakan a matsayin duk so ba ne, inda Walida tace.
'Kun san Allah duk abin da nake masa bana iya kallon kwayar idonshi.'
Ƴan uwan su kayi caa akan ta cewa hakan shine soyayya zazzafa.
Wayar ta kifa tana dafe kanta tare da girgiza kan lokaci ɗaya dan ƙaryata zuciyarta. Shi ɗaya ne take jin nauyin shi da nauyin kallon cikin idonshi duk yadda ta so hakan, duk lokacin da tayi ƙoƙarin haɗa kwayar idanuwan su to harara take watsa masa da ita kanta ta rasa dalili domin idanuwansa lumshe suke tattare da wani sihirtaccen kallo da yake watsa mata ya hana idanuwanta sukuni.
Idanuwanta ta buɗe jin har lokacin sakwanni suna shigowa cikin wayar ta ɗauka ta rufe data, ta kasa ci-gaba da hiran dan ji take hiran zai jefata cikin wani yanayi da bata shirya hakan a rayuwar ta ba sam, musamman akan wanda ba ta taɓa tsammani ba.
***
Da daren Amma Jidda ta samu ƙiran Al'ameen akan yana hanya ga kuma abin da yake tafe dashi.
"Kun yi magana da Nuratu?"
Tambayar da ta aika masa bayan ta gama sauraron jawabinsa.
"Na ƙira ta bata ɗauka ba amma gobe inshaAllah in na zo zan sanar da ita komai."
Ajiyar zuciya ta sauƙe.
"Ba zan ɓoye maka ba amma kayi gaggawa Al'ameen."
Ya san da hakan amma in ba ta nan ya ɓullo mata ba, ba zata taɓa amincewa ba yadda ya lura da ita kuma ta faɗa masa hakan.
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana fatan ta amince yace.
"InshaAllah Amma zata amince ki mini fata mai kyau."
"InshaAllah ina maka."
Tace suka yi sallama.
"Ke dawa haka?"
Taji Alhaji Mamman na tambayarta ta juya da sauri tana murmushi.
"Al-ameen ne yake sanar dani gobe yana tafe."
"Allah kawo shi lafiya."
Yace ya wuce side ɗinshi ta miƙe ta bi bayan shi.
...
Da safen Nuratu bayan ta gama abin da za tayi wajen ƙarfe hudu na yamma ta zauna jiran Al-ameen da ya ƙira ya sanar mata ya shigo zuwa dare zai shigo. Har bayan magriba ta cire rai da zuwan shi har tana cewa ta huta ta samu sallamar shi.
Har cikin falon ya shigo suka gaisa da Mami tana tambayar shi ya hanya.
Da lafiya ya masa mata ta shige cikin bedroom ta bar su daga shi sai Nuratu. Shuru falon ya ɗauka sai ƙarar Tv da yake yi.
Al-ameen ne yayi ƙarfin halin furta abinda yake tafe dashi domin so yake ta fahimce shi.
"Kin ji na nemi ganin ki ko ƙanwata?"
"Eh. Fatan ba wani laifi nayi ba?"
Ta faɗa tana kai dubanta gurin shi.
Murmushi yayi yace.
"Babu laifi ko ɗaya sai dai ma ni ne na aikata laifin. Fatan zaki karɓi buƙatana a karo na biyu ƙanwata, ga Muhammad Al-ameen ya dawo miki da bukatar aurenki Please kar ki ce wani abu, domin har na sanar da su Baba za su samu Abba suyi maganar."
Kallonshi take cike da mamaki shigar sauri da ya mata ba tare da neman shawara ko tuntuɓarta ba, a zahiri kuma murmushin yaƙe take tace.
"Amma Yaya Al-ameen abin har ya kai haka? Da ka bani lokaci ai."
"Gani nake ba zaki amince ba ƙanwata."
Rasa mai za tace mishi tayi kawai sai tayi shuru ta dafe kanta, amsa ɗaya za ta bawa duk wanda ya tunkareta da maganar da Al'ameen ya zo mata da shi, dan shi kam a yanzu haka ba zata iya bashi amsa kai tsaye ba domin tana jin nauyin shi ko dan Amma Jidda.
Fes zuciyar Yaya Al-ameen ganin yake tamkar Nuratu ta amince da buƙatar shi, da ma ya san hakan in har ta samu labari iyaye sun shiga maganar ba zata ƙi ba.
Da farin ciki ya koma gida ya sanar da Amma Jidda yanda su kayi. Itama tayi farin ciki sosai da jin Nuratu ta amince. Ko ba komai auren shine rufin asirinta.
...
Tun bayan rabuwarsu ta mishi rakiya ta dawo gidan faɗa take zubawa tamkar akwai wanda zai kulata. Mami da Munirat suna jinta babu wanda ya mata magana. Da Mami ta gaji ne ma tace.
"Ai wallahi ya mini dai-dai, maganin ki sai shi, yaran nan suna binki duk kin mai da su mashirmata."
"To Mami na faɗa masa ina son shi har yanzu ne? Ko ina da ra'ayin auren shi, ni fa bana son shi haushinsa ma nake ji. Wallahi ki sanar da su ni ba zan aureshi ba, kunyar Amma nake ji ya saka ni ƙin sanar mishi."
"Ke ki ka sani. Aure ne da Al'ameen sai kin yi."
Kuka Nuratu ta fashe dashi tun Mami tana kallon abin da wasa har ta koma lallashi domin kuka take kamar babu gobe.
Bayan ta tsaida hawayenta Mami tace.
"Auren ne ba za kiyi ba ko Al'ameen ɗin ne bakya so?"
Girgiza kai tayi tana share hawayenta.
"Ko ɗaya Mami, ban dace da Yaya Al-ameen ba Mami, ba da mace irina ya dace ba, dan Allah ki sanar dashi hakan."
Cikin kwantar hankali Mami tace.
"Shi ya gani a hakan ya ji yana sonki ya amince zai aure ki sai ki godewa Allah."
Mami da take tsammanin zata fahimceta ta kasa dan ita ma tana son ganin tayi aure, amma ita ta san zafi da kunci da take ji a zuciyarta duk lokacin da aka mata maganar aure. Ba ta da komai da zata bawa mijinta a matsayin babbar kyauta daga wajenta matsayinta na budurwa.
Kwanciya tayi tana share hawayenta ta ji shigowar saƙo wayarta. Ƙin ɗauka ta yi ta san duk Al'ameen ne ƙarshe ma ta kashe wayar ta san zai ƙira daga baya. Ranar bata iya runtsawa ba, kwana tayi tana juyi da neman mafita ma kanta dan kaucewa wannan aure na Yaya Al-ameen.
Idanuwanta a kumbure ta farka bayan bacci da ta samu ya kwasheta bayan sallar asuba da ta gabatar. Ƙarfe tara tayi breakfast ta kimtsa ɗakinta ta fito falon ta kwanta. Munirat ce ta gyara falon ta share wajen sha biyu ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana.
Cikin falon Mami ce zaune tana duba kayan da tayi order ta samu isowar shi yanzu lokaci zuwa lokaci tana kai kallonta kan Nuratu da idonta ke rufe kamar mai bacci.
Cikin sallama da ya iya yi bai manta ba ya shigo falon cikin manyan kaya da ya amshi farin fatar jikinshi har da hula a saman kanshi, yayi mutuƙar yin kyau sai ƙamshi yake zubawa.
...
To fa ga Alhaji Mamman ya bada auren Nuratu ga Mufid.
Ga Al'ameen yayi shigo shigo.
Col. Ahmad fa?
Dr Awwab da yayi shuru fa🙄
Ko waye mai nasara?
...
Wattpadian bana ganin Comments ɗinku 🥺😌
#vote
#comments
#share
MADUBIN GOBE (Haske) 29.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"My Baby Noor."
Mufid yace yana zama saman kujeran da Nuratu take zaune, ta fasa wani ihu tana miƙewa tsaye jikinta duk rawa yake ta nufi gurin Mami, Mufid ya saka hannu ya fizgota ta dawo baya ya zaunarta saman kujeran.
Ji tayi numfashinta baya fita dai-dai da kyar tayi ƙoƙarin saita kanta kafin tayi yunƙurin saka jarumta a ranta ta fizge hannunta tana ja baya.
"Ina wuni Mamin mu?"
Faɗin Mufid yana dan durƙusawa dan gaishe Mami da ta zama kamar dutsi tana binshi da kallo da mamakin rashin kunyar Mufid da har zai iya shigo mata gida har cikin falo.
Yaron da ya tarwatsa ƴarta farin ciki, ya hargitsa mata rayuwa ya mai da duniyarta baƙi babu komai ciki sai damuwa da tashin hankali.
Tana mamakin yaushe ma ya dawo ƙasar. Bata iya amsawa ba sai kallonta da ta kai kan Nuratu dake duƙunƙune waje ɗaya ta cure, jikinta duk rawa yake ta kasa kwakkwaran motsi, hawaye ya wanke fuskarta.
Kallonshi Mufid ya mai da kan Nuratu yana ƙara matsawa kusa da ita.
"Oh My Baby Noor, wannan kuka haka in mu kayi aure kuma fa? Haka zaki dinga min kukan nan, share hawayenki My Baby Noor, kar ki ɓata min kyakkwayar fuskar ki. Na zo muyi maganar bikin mu kuma kin tsaya min kuka. Bana so."
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin kai hannunshi saman fuskarta dan goge ruwan hawayenta ta ja baya cikin kuka tace.
"Kar ka taɓa ni, ka fitar mana a gida. Allah ya kiyaye in aure ka. Mugu, macuci, azzalumi sai Allah ya saka min cutar da ka yiwa rayuwana, Allah ba zai taɓa barinka ba. Ba zan taɓa yafe maka ba. Ka fita nace."
Tace cikin kuka tana nuna masa hanyar waje da hannunta dake rawa.
"Tashi ka fita ko ka sani aikata abin da banyi niya ba."
Suka tsinci muryar Mami saman kansu riƙe da wuta sai sheƙi yake ta nuna Mufid da shi, ranta a mutuƙar ɓace ji take in Mufid yayi wani abun zata buga mishi. Ta nuna masa hanyar fita.
"Fita min a gida. In ma ubanka ya aiko ka kaje ka sanar da shi Nuratu tafi ƙarfin ka, duk cutar da ka mata bai isheka ba sai ka sake shigowa rayuwarta? Mai kake buƙata?"
"Auren ta Mami."
Mufid yace yana miƙewa tsaye cike da tsoron wuƙar hannun Mami.
"Ka fita nace ko in buga maka! Ɗan iska macuci."
Mami tace cikin tsawa tana kai mishi wuƙar ya wani buga tsalle ya koma gefe kafin cikin sauri ya bar falon dan ya tsorata da Mami.
Yana fita Mami ta ajiye wuƙar ta zauna kusa da Nuratu, Nuratu tana ganin haka ta faɗa jikin Mami ta ƙara sautin kukanta.
"Dalla kimin shuru, ni da nake son ganin kin zama jaruma kin kwatarwa kan ki ƴanci za ki tsaya masa kuka. Ki cire tsoro ki tsoratar shi ki nuna masa bakya tsoron shi, balle daga yanzu ba zai ƙara gigin shigowa ba. Shegen ashe matsoraci ne."
"Mami fa cewa yayi zai aure ni?"
Nuratu tace tana share hawayenta maganganun Mufid na yawo saman kanta da taji ta yarda da hakan domin Mufid zai iya aikata komai yace musamman ubanshi da ya goya masa baya.
"Ƙarya yake, ki cire komai a ranki."
Mami tace cikin kwantar mata da hankali amma ita ma ƙasan ranta tana juya kalaman shi.
Wayar Nuratu ne yayi ƙara Mami ta miƙa mata ganin Dr Awwab ne, kasa ɗauka tayi ta kashe.
"Ki ɗauka mana."
Mami tace Nuratu ta girgiza kai.
"Zan ƙira shi anjima, kai na ya fara ciwo."
"Kin sha maganin ki?"
Kai ta ɗaga mata ta kwanta saman doguwar kujeran bayan Mami ta miƙe tana ɗauke wuƙar ta fita.
***
Wayar ya ajiye saman kirjinshi bayan taƙi ɗauka ya lumshe idanuwanshi yayin da yake kwance saman doguwar kujeran falon Ummi. Bai cika ƙiranta ba dan kar ta ga kamar ya takura mata amma sosai yake kewarta da son jin muryarta, sau biyu ya ƙirata tun bayan dawowarsa daga gurinta amma bata ɗauka balle ta bashi amsar shi da yasan har lokacin da kyar ta karɓi buƙatar shi.
"Awwab lafiya kuwa?"
Ummi tace cikin harshen fillanci ganin yanayin ɗanta kamar da damuwa tun kwanciyar shi.
Idanuwansa lumshashshu ya buɗe da suke ciki da damuwa ya miƙe zaune.
"Mami bata ɗaukar waya na sau biyu ina ƙiranta."
"Noor?"
Tace dan sunan da yake ƙiranta da shi kowa tsammanin sa shine asalin sunanta.
Ɗaga kai yayi yana ɗan yamutsa fuskarshi.
"Ni dai Ummi zan ƙara komawa, sai ina jin kamar ba lafiya ba."
Zama Ummi tayi ɗayan kujera tana fuskantar shi.
"InshaAllah lafiya, amma kyanta ka samu zuwa a weekend ka dubata kar ka mata wani maganar. Kawai ka duba lafiyar ta."
"Hakan za'a yi Ummi. Kar Hanan ta sani."
Murmushi ta faɗaɗa ita ma kanta tana mamakin soyayyar Hanan da Noor, duk da ba ta taɓa ganinta ba amma haka kawai tana jin ƙaunar Noor, haka kawai take jinta a ranta.
Sun yi waya sau biyu zuwa uku, biyu Hanan ce ta haɗa su ɗaya Dr Awwab bayan ya sanar da Ummi ita yake son aura ya haɗa su suka gaisa. Nuratu tana jin kunyar ummi sosai da ta rasa dalili.
"Sai ka mata wayo kasan dai weekend tare ku ke wuni."
Ummi tace ta miƙe. Hanan ce da Hassana suka shigo falon da gudu Hanan ta ƙarasa jikinshi.
"Daddy Aunti Hassana ta siya min takalmi."
"Allah My love kin mata godewa."
Dr Awwab ya ce yana shafa kan yarinyar shi da yake mutuƙar ƙaunarta.
Ta ɗaga mishi kai tana cewa.
"Zan nunawa Aunti Noor."
"Sosai ma zamu nuna mata."
Ya ce ya miƙe yana ɗaukarta.
"Za muje gidanmu ko za ki zauna wajen Aunties da Ummi."
Zamewa tayi daga jikinshi bata son gidan babu kowa sai su biyu, ba ta da aiki sai kallo da wasa da teddy sai kuma makaranta.
"Bana so, zan zauna gidan Ummi."
Hanan tace da gudu tayi gurin Hassana.
"Ki kula da ita Hassana."
Yace yana sa kai ya fita, Hassana tayi murmushi, kullum sai ya faɗi hakan kamar wadda ba'a kula da ita.
***
Bayan kwana biyu.
Ranar jumma ƙanin Alhaji Tafida da amininsa ɗaya da ya kamata su san da batun zuwa Damaturu dan nemawa Col. Ahmad auren Nuratu duk sun shirya a yau dan tafiya har da shi Col. Ahmad din da shi zai yi jagorancin tafiyar, Alhaji Tafida bai sanar da Umma ba har yanzu yafi son sai yaje yaji abin da ya biyo baya.
Alhaji Tafida cikin kwana biyun yayi iya abin da zai yi na bincikar waye Nuratu bai samu ba balle sanin halinta sai dai wani abu kaɗan da ya samu game da Alhaji Mamman Bashir.
Bayan samun haka ya nemi zama da Alhaji Mamman akan zai zo har gida saboda muhimmanci abin da zai zo mishi dashi. Alhaji Mamman da farko yaƙi sai kuma yayi tunanin kar yazo masa da wani alherin ya sashi amincewa.
Har ƙarfe sha biyu basu iso ba Alhaji Mamman sai mita yake, yana zaune a babban falonshi na baƙi cike da kayan abinci da abin sha an tara musu, an gyara falon an share sai ƙamshi yake.
Sai ƙarfe biyu suka iso bayan sun gabatar da sallah a masallaci.
Gaisuwa suka gudanar cikin mutunci kamar sun san juna, Alhaji Mamman yana kallon Col. Ahmad yace.
"Kamar na so gane fuskar ka."
Kan Col. Ahmad ƙasa ba dan yana jin nauyin Alhaji Mamman ba yace.
"Eh Baba Col. Ahmad Tafida ne, a court muka haɗu shekaru huɗu"
"Akan case ɗin yarinyar can ko?"
Alhaji Mamman yace da sauri dan har cikin zuciyarsa mance sunan Nuratu yake.
Kai Col. Ahmad ya ɗaga cike da mamakin Alhaji Mamman, gaskiyar Nuratu da ta sanar da shi wanene mahaifinta, bai ga laifinta da tace ta tsane shi ba.
Gyaran murya Alhaji Mamman yayi.
"Sai dai har yanzu baku sanar da ni mai ke tafe daku ba?"
"Ka faɗa mishi Alhaji Inusa."
Alhaji Tafida ya nemi hakan wajen abokinsa.
Hakan ya saka Alhaji Inusa gyara zama yana fuskantar Alhaji Mamman.
"Da alheri muke tafe Alhaji wanda mu ke saka ran inshaAllah zai zame mana alheri gaba ɗaya."
"To to ina jinka."
Alhaji Mamman yace yana ƙara baza kunnuwa.
"Auren ƴarka ta wajen mahaifiyarta muke nemawa ɗan mu Ahmad in har baka mata miji ba balle ma inshaAllah muna da labarin babu wani."
"Ita Nuratun ce ta turo ku, ko ita ta sanar da ku ban mata miji ba?"
Cewar Alhaji Mamman fara'ar fuskarsa yana ɗaukewa.
"Ko ɗaya bata sanar damu an mata miji ba, maganar zuwa kuma ita ta bamu adireshi da komai a matsayin ka na mahaifinta."
"To na