Follow us on social media

Showing 132001 words to 135000 words out of 148866 words

Chapter 45 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

14

can suna amarci. Sunyi kyau dan tsabar hutu, danma Dr Awwab yawanci yana aiki ta hanyar kwamputa. Duk abun da ya faru Nuratu tana da labari duk da kowa ya ƙi sanar mata.
Sallar azumi saura kwana goma suka tafi Umrah daga nan za su koma gida Nigeria. Hakan kuwa aka yi, acan suka samu Ummi da Hanan hatta ƴan biyu sun zo Umrah. Murna gurin Nuratu ba'a cewa komai, nan ta tattara ta koma ɗakin ƴan biyu duk kashedin Dr Awwab. Dole ya hakura ya barta dan suyi ibada mai kyau.
Tun lokacin suka dage da yin ibada hatta Hanan.
Anyi sallah da kwana ɗaya suka dawo Nigeria, a gidan Ummi suka yada zango. Bayan an gyara musu gidansu washegari suka tafi.

Tun da suka dawo Nuratu take roƙon Dr Awwab ya barta ta je Niger auren Hafiza saura kwana uku Mami da yara za su tafi. Shikam dai ganin yadda tayi wani haske da kyau kallon mai ciki ya ke mata, dalilin da ya sa baya son yawan zirga zirganta.
Amma yadda yau ta sa shi gaba da kuka ya sa shi cewa ta shirya zai kaita da kansa. Murna har da tsalle tsallenta. Da sauri ya riƙota.

"Ki yi a hankali kar ki mini asara, na yi wahala kafin na samu."

Da mamaki tace.
"Asara me kuma? To na bari."

Hancinta ya lakace ganin bata fahimcesa ba ya rabu da ita.
Da taimakonsa ta haɗa musu kayansu dan yace ƙafarta ƙafarsa. Washegari sai Damaturu ta samu duk an shirya za'a wuce har Abbansu da za su je ɗaurin aure da dangin mahaifin Yaya Al-ameen daga Zaria.
Keɓewa Nuratu da Abbansu ta yi bayan gaisuwa suka tattauna kafin su wuce. Kowa yayi mamakin ganin bata damu ba da maganar auren iyayenta ba, hasalima babu wanda ta ma magana hatta Mami da ta ke wasi wasi kar ƴarta ta ga bata kyauta mata ba.

Tafiyar ta kasance Mami da Alhaji Mamman motarsu daban. Ɗayar motar da Abbansu ya basu Aunti Zarah, Aunti Hasiya, Rukayya, sai yaransu. An bar Ameera a gida da Abba ya haɗawa zafi akan ana gama auren ta ciro mijin aure. Amma Jidda kuma da Aunti Rahma an barsu a gida dan kula da baki, Walida ciki ya girma ya sata a gaba dole ta zauna, don ma ana ɗaura auren za su juyo su taya Amma Jidda hidima sauran. Mami ma badan dole ba, don ƴar yayanta ne ba zata ba. Motar Dr Awwab kuwa daga shi sai matarsa suna tafiya suna shan soyayya.
Shigar yamma suka yi gidan cike da baki, Kawu Muhammadu ya rasa ina zai saka ƙanwarsa da ahlinta. Abinci kala kala aka kawo musu, masauƙi daban daban aka bawa Alhaji Mamman da Dr Awwab.

Washegari ango da yan uwansa suka iso da abokansa ciki har da babban abokin ango Col. Ahmad Tafida, anan suka haɗe da Dr Awwab. Ga mazan Yayun Nuratu anan suka fara haɗuwa suka gaisa. Ƙarfe sha daya aka shaida ɗaurin auren Muhammad Al'ameen da Hafiza Muhammad. Bayan ɗaurin auren aka buƙaci tafiya da amarya. Dole aka basu bayan doguwar nasiha da tasha, suka kama hanyar komawa.
Bayan isarsu gidan Amma Jidda aka kaita dan za su yi event kafin ya ɗauki amaryarsa su wuce Zaria wajen aikinsa.
Hakan ko a kayi da yamma suka yi dinner. Amarya tayi kyau haka ango ma, sai yan uwa masu anko, Nuratu ma ta samu sun ɗinka mata ta saka. Dr Awwab ne ya kaita bata bi motar kai kawaye ba ko bin yayunta ba.
Bini bini ya hanata motsi hatta kari tare suka yi yana tareta kar wani ya ganta, haka suka koma wajen zamansu. Bayan an tashi kowa ya watse suka koma gida.

Bayan Nuratu tayi wanka taci abinci ta dale gadon Maminta. Rukayya ana can ana sallama da miji da ya ɗauke daga wajen dinner ya dawo da ita gida, shigowar da ba tayi ba har yanzu, Aunti kuma suna falon Mami kowa yana faɗar hiransa akan yadda bikin ya gudana.

..

"Mami za muyi magana idan kin gama."
Faɗin Nuratu tana kai dubanta gurin Maminta.

"Magana kuma Auta? Lafiya dai ko?"

Ta tambaya dan gudun faɗawa tambayar me yasa ta aikata haka bayan abin da ya faru.
Girgiza kai Nuratu tayi ta sauƙo a gadon ta zauna kusa da Mami.

"Mami me ya sa kike wa Abba haka? Ko har yanzu ba ki yafe masa ba? Don Allah ni kam idan dan ni ce na hakura ki bar komai. Ko kin san ni nasa Abba ya aureki kai tsaye tun bayan da ya nemi yardarki ki ka ƙi.
To ranar da za muje Nijar munyi magana da shi ya sanar da ni duk irin zaman da ku ke. Ni kam idan ta ni ne kiyi hakuri don Allah ki sassauta masa."

"Kece Nuratu?"
Mami ta tambaya da mamakinta. Kai ta daga mata.

"Tun bayan ya nemi yafiyana na yafe masa nuna waya har ya sanar da ni buƙatarsa, anan na basa shawara kawai ya samu Kawu da maganar, ya sanar da ni sunyi magana da Kawu kuma Kawu yace sai da yardarki. Ni kuma yadda fahimta ke ba za ki taɓa yarda ba. Shi ne kawai na ƙira Kawu na sanar masa komai.
Daga nan shi ne Kawu ya zo aka ɗaura auren, kuma ya ɓoye miki wanene akan sai an kai ki. To sai ga shi Mami kin ki kwantar da hankalinki kamar yadda mu kayi fatan idan kinga inane gidan auren za ki hakura."

Bayan ta gama bayanin, Mami ta kai hannunta fuskar Nuratu ta dan bugi kumatunta. Babu alamun ɓacin rai a fuskarta.

"Autar Mami ta girma ta yi hankali."

Murmushi Nuratu ta yi ta ce.

"Kin yarda za ki kyautatawa Abbanmu."

Kai ta ɗaga hakan ya sa Nuratu ta faɗa jikinta ta rumgumeta tana murna. Mami kam mamaki yake yadda uba da ƴar suka fara faɗawa juna sirrinsu bayan tsawon shekaru. Ringing ɗin wayarta ya sata sakin Mami ta ɗauka ta ga mijinta ne. A gaban Mami ta fara zuba masa shagwaɓa, haka yasa Mami ta lallaɓa ta bar mata ɗakin.
Sun jima suna waya kafin ta kashe ta kwanta. Murmushi take yi yadda duniyarta ya canza lokaci ɗaya.

Ta yi aure ta samu miji nagartacce, mai ilimi addini da boko, mai dukiya mai albarka, kyakkyawa mai kyakkyawar zuciya. Iyayenta sun koma rayuwarsu tamkar babu abin da ya faru. Komai ya wuce tamkar babu abin da ya faru sai an sanar maka.

...

Washegarin ango ya ɗauki amaryarsa suka wuce, Aunti Rahma da Hasiya sun bita ganin ɗakinta dan bata da yayu mata. Duk yadda Nuratu taso zuwa Dr Awwab ya hanata. Ƴan biki kuwa ƙarfe sha biyu suka watse ciki har da Nuratu da Dr Awwab ya ɗauka sai fushi ta ke.

Bayan biki da sati ɗaya Alhaji Mamman ya ga canji wajen Mami. Tun lokacin suka buɗe sabuwar rayuwa, a lokacin ta basa damar yin amarci, aikuwa yana amarcinsa yadda duk yabi ya nane mata. Sun mance da komai duk da lokaci zuwa lokaci abin yana faɗowa Mami a rai, haka shi ma amma suna dannewa. Burinsa ya faranta mata ya kyautatawa rayuwarta. Kwata kwata baya son ɓacin ranta dan yasan ya wahala kafin ya sameta kuma. Tsakaninta da Amma Jidda suna zaman lafiya. Ameera kam tuni ta koma bangaren Mami ganin iyayenta har lokacin sun kasa sake mata fuska.
Abba ya sake mata maganar aure, Mami tace ba yanzu ba karatu za tayi, tun da tayi nadama kuma ciki har da sharrin ƙawaye. Dole ya hakura ya barta taci gaba da sharaɗin tana gamawa sai aure, ta ce ta yarda.
Ameera murna harda kuka, tayi ta godewa Mami da yabawa karamcinta. Sai lokacin take jin haushin kanta na rashin fahimtarta da bata yi ba ita da Nuratu.

Rayuwar gidan ya dawo sabo.

...

Bikin Hafiza da wata ɗaya aka tsaida wata biyu akan ranar auren Hassana da Abdallah, Hussaina da wanda ya tako har gida ya sanar da Dr Awwab yana sonta. Yarda da shi da kuma sanin wanene ya sa shi basa aurenta kai tsaye.
Hassana da Abdallah dama suna son juna. Hussaina kuwa tashin hankali ta shiga da jin yayanta ya bada aurenta ga wani wanda bata sani ba. Kuka take yi kullum ta kasa kwantar da hankalinta duk ta rame dama ba wani abincin kirki take ci ba. Hassana ma kanta sai ta ji wani iri. Ummi kaɗai Dr Awwab ya sanar da ita wanene, kuma ya hanata fadawa musu duk da yasan da wuya su san sa.

...

Komai yayi farko.

#vote
#comment.
#share

MADUBIN GOBE  59.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Tun da kwanakin bikin ya rage saura kwanaki hankalin Hussaina ya ƙara tashi, ta yi kukan t ayi har ta gaji, ta roƙi Ummi ta saka Dr Awwab ya janye ƙudirinsa ya ƙi, ta je da kanta ta samesa ta sa shi a gaba tana kuka ya ƙi sauraronta, sai ma faɗa da ya rufeta da shi yana cewa ai ba zai mata zaɓin da zai cutarta ba. Haka ya ƙara tada hankalinta ganin babu me sauraranta sai Hassana.
Mai gyaran da Ummi ta ɗauko take musu da ƙyar take lallaɓata ta yi mata, duk ta rame sai haske. Kayan baƙin cikinma angon bai ƙirata ba balle suyi maganar biki ko event. Kuma jiran ƙiran sa take ta zuga masa rashin mutunci.

...

Yau talata ƙarfe uku suna zaune Dr Awwab Nuratu yasa ka a gaba ya koma kalar tausayi, tun da ta sanar da shi bata sallah. Ita ma ɓangarenta tasan dai babu cikin, amma yadda ya nuna damuwarsa sai ta ji babu daɗi, tana buƙatar hakan ko dan faranta masa. Aure kusan wata huɗu.

Kallonsa ta yi ta matsa kusa da shi ta kwantar kanta saman cinyarsa tare da laliɓo hannunsa ta rumgume a kirjinta.

"Hayat ka daina damuwa, Allah zai kawo a lokacin da ba muyi tsammani ba."

"Na sani Babyna, kawai dai na jima ina miki kallon mai ciki a ko wani wata, musamman wannan watan."

Murmushi ta yi tana kallon cikin idonsa da yanzu take iya kallo, don yanzu ta fahimci wannan rashin jumurin kallon duk cikin so ne.

"Ni ma haka fa."

Sunkuyawa yayi ya sumbaci leɓɓanta ya ɗago yana kashemata ido ɗaya.
"To ki bada himma next month mu samu."

Kanta ta ɗago ita ma ta sumbaci nasa leɓan tace.
"Insha Allah Hayat."

Lips ɗin ya hanata ɗaukewa ya ci gaba da kissing ɗinta. Door bell da ake dannawa ya dawo da su hankulansu. Wani mugun tsaki ya ja yana sakin bakinta ya koma ya kwanta. Miƙewa Nuratu tayi tana gyara rigarta ta nufi ƙofar fita.
Buɗewa tayi ta tsaya tana kallon mai danna door bell din daga sama har ƙasa ta tsayar kallonta kan fuskarta kafin ta ba ta hanya ta shiga falon. Cikin takunta mai jan hankali ta ƙarasa falon tana bi da kallo.

'Lallai munyi asara, amma kissa yafi magani.'
Ta faɗa a ranta, har lokacin sun kasa nasara akansa sai asaran kuɗi da suke yi.

Nuratu na ƙoƙarin rufe ƙofar drivern Hanan ya shigo gidan. Tana tsaye har ta fito cikin shirin makaranta ta ƙarasa wajenta ta ɗagata sama suka shiga falon. Zuciyarta ne ya buga ganin Binta ta saka mijinta a gaba tana masa hira sai wani fari da ido take yi. Kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta.
Ta rasa wacece ita tun ranar bikinta.
Kanta ta ɗauke tana wucewa ciki da Hanan. Wanka ta mata ta canza mata kaya suka sauƙo. Samu ta yi Dr Awwab har lokacin yana wajen.

Kitchen suka wuce ta zuba mata abinci ta zauna ta bata. Suna cikin haka Dr Awwab ya shigo.

"Babyna kinyi baƙuwa ba za ki bata ko ruwa ba."

Wani kallo ta watsa masa.

"Na santa ne? Baƙuwar ka dai. Wai wacece ma?"
Ta faɗa tana tambayarsa ranta a haɗe.

"Za mu yi maganar anjima, yanzu ki kai mata ruwa."

Ɗauke kanta ta yi daga kallonsa ta miƙe tana ɗaukar Hanan tabi ta gefensa ta wuce. Murmushi yayi ya ƙarasa ciki ya ɗauki ruwa a plate ya koma falon wajen Binta kafin ya bi bayan Nuratu. Ɗakin Hanan ya fara shiga ya samu tana kallo, fita yayi ya wuce ɗakin Nuratu, a saman kujera ya sameta kwance a falo.
Sheshsheƙar kukanta ya ji da sauri ya ƙarasa yana ɗagota. A rikici ya fara tambayarta.

"Menene kuna Babyna, don Allah ki sanar da ni."
Zama ya yi yana rumgumeta.

Fizge jikinta tayi cikin kuka.
"Ka rabu da ni."

"Ba zan iya ba, ki sanar da ni me ya faru?"

"I said ka rabu da ni."
Ta faɗa da ƙarfi tana ƙwace jikinta. Rumgumeta ya yi sosai a jikinsa ta fashe masa da kuka, mugun kishi ke cin ranta. Sai da ta yi kukanta ta fara sauƙe ajiyar zuciya yana shafa bayanta sannan ya mata raɗa a kunne.

"Ƴar uwar mahaifiyar Hanan ne, ban taɓa sake mata fuska balle ta samu gurbi a gurina, ɗazuma kar ki fahimci wani abun ya sani tsayawa sauraronta. But I'm sorry My Baby."

Ɗago idanuwanta ta yi da suka yi jajur don kuka.
"Really?"

"Yeah."
Ya faɗa yana sumbatar lips ɗinta. Ba ta bari ya cire nasa ba ta ci gaba da kissing ɗinsa, bai musu ba ya karɓeta. Sun fara sakin layi ta tuna bata da tsarki ta zare jikinta ta kwanta. Ganin haka ya miƙe tsaye.

"Bari in sallameta."

Kanta ta juyar ganin haka ya fita.

...

Da sauri ta bar gurin tana mayar da hawayenta. Tun hawarsa sama ta bisa ta ga me zai yi. Kasa kunne ta yi tana leƙar su ta ga faɗa suke sai dai kasa jurewa tayi lokacin da ta ga Nuratu na kissing ɗin Dr Awwab ya biye mata, bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba. Ganin zai fito ya sata sauka ƙasa, bata tsaya a falon ba ta fita a gidan gaba ɗaya.
Bai sameta a falon ba ya koma ɗaki ya samu Nuratu ta rage kayan jikinta za tayi wanka.

"In zo in taya ki?"

Girgiza kai tayi ta wuce bathroom ta barsa zaune. Har ta fito yana nan yadda ta barsa, kaya ta canza ta fita ta barsa. Ajiyar zuciya ya yi ya fita. Har dare ta kasa sakar masa fuska duk da ta ga zuwan Binta, dalilin kissing ɗinsa da tayi.
Da daren bayan ta gama Hanan hidimarta ta kwantarta ta wuce ɗakinta. Wanka tayi ta saka night gown nata ta kwanta. Haka Dr Awwab ya shigo ya sameta. Kansa ya dafe, wannan fushin dai ya ishesa.
Wanka yayi ya hau gadon yana jawota jikinsa ya rumgume.
Kansa ya tura tsakanin wuyarta ya fara mata magana a hankali, hannunsa a saman cikinta yana shafawa a hankali.

"Wai ba ki huce ba, ni kam fushin nan ya ishe ni. Please i said I'm sorry. Wallahi babu komai tsakani na da Binta."

Kwanciyarta ta gyara a jikinsa, tana jin daɗin yadda yake mata, iskar da ya hura mata a kunne yafi komai kashemata jiki. Sai lokacin ta buɗe baki.
"Idan kana so na huce za ka bani amsar tambayata?"

"Ina ya jinki."

"Me ya ka ke raba Hanan da dangin mahaifiyarta. Sam na lura ba ka son abun da ya shafe su. Abar maganar Binta a gefe don ni bansan ita ɗin ƙanwar mahaifiyarta bane sai yau. So ka faɗamin Please."

Ƙara rumgumeta yayi cikin jikinsa sosai, har ta cire ran zai yi magana ta ji ya fara a nutse tamkar baya so.

"Na haɗu da Nusaiba a hanyar unguwar su bayan na kai abokina unguwar, a hanyar dawowana na haɗu da ita cike da buƙatar taimako.
Kinsan taimakon me take buƙata?Abinci.
Abinci take buƙata da za taci. Ganinta da nayi budurwa da ita tana neman taimako nayi tunanin kar ta faɗa halaka yasa na taimaka mata. Bayan ta ci ta ƙoshi tayi ta mini godiya. Daga nan na kaita har gidansu bayan ta nunamin. A raina ina mamakin to me ya fito da ita neman abinci bayan suna da gida tana da iyaye.
Kinsan dana koma gida na kasa cire abin da ya faru a raina, haka washegari na dawo unguwar ko zan ganta. A ƙofar gidansu na tsaya, kusan mintuna ta dawo da bokatin ruwa a kanta, ina ganinta na taimaka mata ta kai gida ina mata faɗar ya mata nauyi. Bayan ta kai ciki ta fito ta gaisheni tare da mini godiya jiya na taimaketa, ban ce mata komai ba na ɗauki siyayyar dana mata na bata.
Ƙin karɓa tayi kuma alama ya nuna tana buƙata. Dana matsa mata tana kuka ta ce ƙwacewa za ayi.
Da ƙyar dai na bata ta koma ciki.
Kullum idan bani da aikin yi sai na je wajenta, abun mamaki tun lokacin na fahimci ta ɗauka sonta nake, ni kuma burina in taimaka mata kar ta lalata rayuwarta tun da na fuskanci kamar tana matsin rayuwa a gidan.
Mun shaƙu da Nusaiba sosai har na zo nasan a gaban matar babanta take, mahaifinta bai jima da rasuwa ba, mahaifiyarta kuma tun tana ƙarama ta rasu.
In taƙaita miki dai dalilin haka tausayinta da son taimaka mata ya sani auren Nusaiba duk da ita ta ɗauka sonta nake. Da ƙyar aka bani aurenta, dan matar baban ta dage sai dai ƴarta kamar yadda ta faɗawa dangin mahaifinsu ai ita zan aura. Sai ranar ɗaurin aure na gane ƙullin da ta mini ta canza sunan Nusaiba zuwa Binta.
Bayan auren bata haɗata da komai ba, ni kuma ba haka nake buƙata ba dama. Haka muka yi rayuwar mu kamar yadda na sanar miki har Allah ya kawo Hanan.
Kinji dalilin da yasa duk ƴan gidan bana sake musu. Bayan haihuwar Hanan basu san da komai nata ba har sai da ta shekara uku kafin su ce za su shigo rayuwarta. No bazan yarda ba, nasan wani abunsu daban ne."

"Ko dai sonka take ka aureta?"

Dr Awwab ya tsinci muryar Nuratu. Ɗago kansa ya yi ya kalleta ta rufe idonta.

"Na yi tunanin hakan. Idan kuwa hakane har abada babu shi, domin basa cikin jerin mutane da suke da muhimmanci a rayuwata balle samun gurbi a rayuwata ko wani so."

Ba ta masa magana ba daga nan, kowa yana juya abin da ya faru a zuciyarsa har barci yayi awon gaba da su.
Washegari kamar babu abin da ya faru suka farka, bayan ta shirya Hanan ta tafi makaranta shi ma ya wuce aiki.

...

Biki sai matsowa yake yau saura sati biyu, ƴan biyu banda Hassana babu mai shiryawa bikin, Hussaina ta barwa Hassana komai tace idan tayi daidaine. Cikin satin sunyi kyau na fitar hankali hatta Hussaina da bata son gyaran. Zaituna da Ikhram su saka haɗawa ƙannensu komai na kayan ɗaki da Kitchen da taimakon Ummi da Awwab. Ɓangaren Ammi ma shiri suke na aurar da autan gidan.
Ciki sati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login