Follow us on social media

Showing 66001 words to 69000 words out of 148866 words

Chapter 23 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

29

suka koma gida.

***

Bayan kwana biyu ya ji shuru Baba bai masa magana ba akan maganar da suka yi, yana son masa magana baya son ya ga tamkar ya matsa masa ne amma haka kawai zuciyar shi yake jin akwai abin da yake faruwa, musamman in ya ƙira Nuratu wayarta ba ya shiga.
Aniyar tunkarar shi da maganar yayi yau daren juma'a, da daren ya same shi har falonshi.

Ƙanshi sunkuye ƙasa ya rasa ta ina zai soma zancen, Baba yana lura da shi kuma ya san mai yake tafe da shi sannan dole ya sanar da shi abin da yake faruwa.

Ƙiran sunan shi yayi kansa a ƙasa ya amsa kafin ya ɗago da kyar.

"Na san magana ne yake tafe da kai akan maganar da mu kayi ba?"

"Eh wallahi Baba na ji shuru ne, na ce ko lafiya."
Al'ameen yace yana sosa kanshi.

Murmushi Baba ya faɗaɗa.
"Lafiya lau, mun yi waya da Alhaji Mamman ya sanar da ni ya riga ya yi wa ƴarshi miji."

"Miji dai Baba, Nuratu fa?"
Yaya Al-ameen yace cike da tashin hankali da ruɗani.

"Ita dai na sanar da shi ta wajen tsohuwar matar shi."

Girgiza kai Yaya Al-ameen yayi yana dariya.
"Kai Baba ba dai Nuratu ba sai dai Walida."

"To shikenan tun da baka yarda ba."
Baba yace yana komawa ya jingina kansa da kujera.

Tashin hankali da ruɗani Al'ameen ya shiga jin maganganun Baba, gani yake tamkar tatsuniya yake sanar da shi ya miƙe da sauri ya fita ya nufi bangaren su na samari.
Saman kujera ya zauna ya ɗauki wayar shi yaci gaba da ƙiran numbern Nuratu a kashe har lokacin, sai yaji zuciyarshi ya ƙara shiga ruɗu ya kasa nutsuwa.

Daren ranar bai iya runtsawa ba washegarin da safe karfe bakwai ya nufi hanyar Damaturu dan tabbatar da gaskiyar maganar da yake jin ba zai iya hakura Nuratu ta auri wani bashi ba, yarinyar da yake sonta yake kaunarta yake burin aure tun shekaru biyar baya.

***

Dr Awwab yana zaune yana jiran Hanan ta fito su wuce. Shigowar shi gidan cikin shirin ƙananan kaya zai yi tafiya ta saka masa kuka sai ta bishi jin in da zai je ya barta tun da weekend ne babu makaranta, islamiyya kuma an ba da hutu. Bai so ba dan kar ta takura masa dole Ummi ta saka baki yace Hassana ta shiryata su tafi tare da kayan sawanta kala biyu.

Mintuna arba'in suka sauƙo tare da Hassana ta mata wanka ta saka mata riga gown brown color da takalminta cover shoe, kanta da hula an rufe dogon gashinta na fulani da sai an buɗe ake ganin yawan shi.
Har bakin mota suka masa rakiya, Hanan ta shiga gidan gaba kusa dashi aka saka mata ƙaramin jakarta gidan baya kafin ya kunna motar suka bar harabar gidan.

Tafiya suke cikin nutsuwa Hanan na ta zuba mishi surutu yana amsa mata sai lokacin ya ji daɗin tahowa da ita dan tana ɗeba mishi kewa. Tun yana amsa mata har ya ji tayi shuru ya juya ya ga bacci ya ɗauketa ya gyara mata kujeran da kwanciyarta kafin yaci gaba da tuƙi.

Sai da suka shiga cikin Damaturu ya tsaya ya saya musu abinci da abin da ya san za taci in ta farka kafin ya ɗauki hanyar Nijar dan ganin hasken zuciyar shi da yau ya ɗauki aniyar zuwa ganinta. Yayi kewarta yayi kewar jin muryarta da ganinta.

***

Yamma lis Al'ameen ya shigo Damaturu bai iya biyawa gidan mahaifiyarshi ba dan tabbatar da gaskiyar maganar ya wuce kai tsaye gidan Mami. A ƙofar gida ya faka motarshi ya sauƙa ya shiga gidan da sallama kai tsaye cikin falon ya nufa.

Mami tana cikin yin waya da Kawu Muhammadu ta sanar da shi duk yadda tayi da Alhaji Inuwa da hukuncin da suka yanke ta ji sallamar Al'ameen ta mishi sallama akan za ta ƙira su ƙarasa maganar.

Fita tayi ta amsa tana mamakin ganin shi cikin wannan lokacin.

'Yana da labari kenan.'
Zuciyarta ya bata amsa ta zauna tana karɓar gaisuwar shi. Fuskar shi cike da damuwa take duban shi.

"Mami dagaske ne abin da naji labari?"
Yace cikin murya cike da karaya.

Kai ta ɗaga mishi.
"Gaskiya ne Al'ameen, bamu da mafita? Har na rasa ya zan yi, ya dage sai an yi auren nan."

Kai ya girgiza yana share gumin fuskarshi.
"Ina ƙanwata?"

"Tana Nijar wajen Yayana, ka san shi ai Yaya Muhammadu."

Kai ya ɗaga alamar ya gane shi ya miƙe.
"Shikenan gobe zan zo ki ban address zan je gurinta za mu yi magana da ita."

"To shikenan Allah ya kai mu gashi ko ruwa baka sha ba Munirat bata nan."

"Kar ki damu Mami ni ma ɗan gida ne kamar kowa."

Yace ya fita ta bishi da kallo tare da godewa Allah da ya kawo shi cikin lokacin da dai-dai suke buƙata. Fatan ta gobe in ya samu Nuratu da zancen da take fata ta amince balle ma bata tunanin ba zata ƙi ba dan neman mafita da gujewa auren Mufid.

Kai tsaye Al'ameen gidan Amma Jidda ya nufa, anan tayi ta bashi hakuri da bashi goyon baya ya tafi Nijar wajen Yaya Muhammadu suyi maganar auren Nuratu kafin lokaci ya ƙure.

***

NIGER.

Ƙarfe biyar na yamma Dr Awwab ya isa cikin garin bayan tsaye tsaye da yayi a hanya dan sun tsaya a Geidam da Garin Gada Hanan ta farka tayi fitsari taci abinci kafin yaci gaba da tuƙi. Bacci ta koma kafin su isan.
Parking yayi kofar gidan ya sauƙa ya fito da Hanan a kafaɗarshi kafin ya shiga cikin gidan da sallama.

Nuratu da take tankaɗen garin tuwo da Nazifa za ta tuƙa ta ji sallamar shi ta ɗago kanta dai-dai lokacin ya shigo ciki Nazifa ta amsa suka haɗa ido.
Da sauri ta mayar kanta ƙasa tana mamakin ganin shi cikin wannan lokacin ko nisan hanya baya dubawa.
Tun komawar shi bai ƙirata ba ita kuma ba tayi tunanin ƙiran shi ba.

"Sannu da zuwa."
Ta tsinci muryar Nazifa na masa ta shimfiɗa masa abin zama, ya fara ƙoƙarin zama da Hanan ya kasa ya kalli Nuratu da ta gama ta miƙe tana karkaɗe jikinta.

"Noor zo ki karɓeta ki kwantar."

Babu musu ta isa wajen ta saka hannu ta karɓeta, garin haka fatar hannunsu ta haɗu ta ji wani yarr, kaɗan ta sake Hanan a ƙasa ta ji yace.
"I miss you Babyna shi yasa na zo ganin ki musamman. Na kasa hakurin rashin ki kusa da ni."

Ba ta mishi magana ba amma kaɗan ya hana ta sakar masa ƴa jin abin da yace, dakyar ta samu ta karɓi Hanan ta wuce ciki ta kwantar ta, ta fito ta samu Nazifa ta kawo masa ruwa a randa mai sanyi cikin kofin silba, duk tsamaninta ba zai sha ba sai ta ga ya kafa baki ya sha sosai.

"Ina Kawu da Mama na ji gidan shuru."
Ya tambaye Nuratu bayan ta zauna kusa da shi a saman kujera.

"Kawu sai yayi sallar magriba yake dawowa, Mama Yawuro ta shiga maƙota barka. Ya hanya?"

"Allahamdulillahi hanya sai kewar ki Noor, babu waya babu number ki, ke kuma baki ƙira ni ba, kina ja min aji Noor. Shine tayi taktaki na zo zance gurin ki."
Ya ƙarasa maganar yana aika mata murmushi mai tsada da take jin zuciyarta yana amsa.

Idanunta ta ɗauke bayan kallo ɗaya da ta masa, na shi idon cikin nata kamar kullum yana son kallonsu.

"Kun sha hanya, ina Ummi?"
Ta faɗa tana kawar da maganarsa na farko.

"Allahamdulillahi lafiyarta ƙalau."
Daga haka tayi shiru ganin haka ya miƙe.

"Bari in shigo da kayan Hanan."

Ya faɗa yana fita ya shigo da kayanta da katan katan na drinks da ya kawo da kwalin indomie da su madaran gwangwani dan ya tsaya yi musu tsaraba a hanya rasa mai zai saya kawai ya saya wannan.

Baki Nuratu ta sake tana bin shi da kallo har ya gama shigo da shi ya dubi Nazifa cikin harshen fillancin yace.
"Zo ki kai kitchen."

Tsaf ta jide ta kai kitchen kafin Nuratu tayi magana ya nufi waje yana cewa.
"Na tafi masallaci in an yi sallah zan dawo hira, kimin kwalliya Babyna."

Tana kallo ya fita ta kasa kwakkwaran motsi har ya fice da kyar ta ja ƙafarta ta zauna saman abin shimfiɗar da ya ta tashi tayi tagumi.
Dr Awwab ya shammace ta sosai, lamuran shi na burgeta a rayuwa musamman kwanan nan da yake saka zuciyar jin wani abu da ta kasa tantance menene hakan yake nufi.

....

To fa ga Dr Awwab ya zo ga Yaya Al-ameen yana hanya?
Ko waye me rabo?

Col. Ahmad fa shin ya hakura?

#vote
#comments
#share

MADUBIN GOBE  34.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Sai bayan sallar isha'i, Kawu Muhammadu da Dr Awwab suka dawo gidan da Musalle. A tsakar gidan aka shimfiɗa musu taburma biyu dan kunya ya hana Dr Awwab zama kusa da shi.

Nuratu da Hanan a saman baranda tana bata abincin bayan farkawarta ta ganta wani gida daban tare da Nuratu ta rumgumeta, bini bini duk in da tayi tana binta tace yunwa take ji ta zuba tuwo miyar kuka ta fara bata, ta ɗauka ma ba za taci ba sai taga har neman ƙari take.

Idanu ta ɗago suka haɗa ido da hasken lantarki da ya haska wajen da farin wata ya basu daman ganin fuskar juna, Dr Awwab ya ɗaga mata gira tare da sakar mata murmushi, da sauri Nuratu ta mayar kanta kan Hanan da take cewa.
"Aunti ki bani na cinye."

"Ɓingel ma? (Yarinyar ka?)"
Kawu Muhammadu ya tambayi Dr Awwab cikin harshen fillanci bayan sabon gaisuwa da su kayi. Dama fulani ba dai afkin gaisuwa ba ayi a sake.

"Eh ita ɗaya ce, rigama tasa min sai ta biyo ni."
Ya mayar masa da amsa ta nashi fillacin.

"Yayi kyau. Ashe dama kana da iyali?"

Girgiza kai Dr Awwab yayi.
"Yanzu dai babu sai fatan samu. In har za'a bani?"
Ya ƙarasa maganar ƙasa ƙasa cike da kunya.

Murmushi Kawu Muhammadu yayi fahimtar maganar Dr Awwab.
"Insha Allah za'a baka in ka shirya."

Da sauri Dr Awwab yace.
"A shirye nake ko yau wallahi Kawu. Ta ƙi bani dama ne."

Dariya Kawu Muhammadu da Musalle suka saka ganin ya basu amsa da sauri. Halin Dr Awwab ya burge shi, duka duka sau biyu ya zauna dashi amma ya yaba da halin shi da nutsuwar shi.

"Za mu yi maganar da safe. Musalle kai shi ɗaki yaci abinci kasan dai ba zai iya ci a nan ba gaban suruki."

"Allah ya kaimu. Nagode."
Dr Awwab yace ya miƙe cike da kunya ya bi bayan Musalle zuwa ɗakin shi.

Bayan wucewar Dr Awwab, Kawu Muhammadu ya kalli Nuratu da ta gama bawa Hanan abinci tana wanke hannunta.

"Ke Nuru zo ki kai mishi abinci."

Babu musu ta isa gurin ta ɗauki kayan abincin da Mama Yawuro ta jere a tray ta wuce ɗakin Hanan ta biyo bayanta da sauri. Cikin sallama ta shiga ɗakin Hanan tana ganin mahaifinta ta isa gurinshi ta rumgume ya zaunarta jikinshi tana cewa.

"Aunti Noor ta bani abinci mai daɗi."

"Dagaske?"
Yace yana kallon Nuratu da ta ajiye abincin ta kasa tashi kuma. Ya mayar kallonshi kan Hanan. Kai ta ɗaga mishi ya ajiyeta a gefe ya miƙe ya nufi gurin Nuratu.

Tana ganin haka ta miƙe da sauri ya tare hanyar ta ja baya tana watsa mishi harara da manyan idanunta da hasken kwan lantarki ya haska fuskarta ya bashi damar ganin haka.

"Wannan kallon yana hanani nutsuwa Babyna."

Rai ta haɗa tana neman bin gefe ta wuce ya saka hannunshi ya tare ta turo baki.

"Dan Allah ka bani guri in wuce, Hanan tana kallon mu fa."

Kallonshi ya kai kan Hanan da ta zuba musu ido, yayi murmushi ya juya yana kallon Nuratu da ta kawar da kanta gefe yace.
"My Love je ki waje ki jira Aunti, Daddy zai yi zance da Babyn shi."

Juyowa Nuratu tayi idonshi a kanta.
"Me haka dan Allah kai ko kunya baka ji. Ni ka daina ƙira na da Baby dan Allah."

Ganin Hanan ta fita ya sashi matsawa kusa da Nuratu sosai, ta ja baya ta haɗu da gini, tsoro ne ya ziyarci zuciyarta, muryarta har ya fara rawa tace.
"Me haka dan Allah in wani ya shigo fa."

"Soyyaya ce Babyna. Yau dai rana ɗaya ki bari muyi hiran masoya."
Yace yana bin fuskarta da kallo.

Rai ta haɗa kamar za tayi kuka tace.
"Dan Allah ka bar ni in wuce."

"Sai kin ce kina so na."
Ya bata amsa har lokacin yaƙi matsawa ta wuce. Jin abin da ya faɗa ya sata kallon shi, idonshi cikin nata ta ɗauke da sauri dan wani kallo da ya aika mata.

"Ba zaki faɗa ba? Zamu kwana a haka kenan Babyna."

"Dan Allah kayi hakuri. Ni wai ce maka a kayi ina sonka? Ko ce maka a kayi zan aureka? Na faɗa maka babu aure cikin rayuwar Nuratu."

Bai ji haushin kalamanta ba ya san duk cikin ruɗu ne kuma ta kasa bawa zuciyarta daman duba abin da take so. But soon zai tabbatar mata da haka. Matsawa yayi gefe ya bata guri ta wuce.

"Shikenan sai da safe."

Ta tsinci muryar sa cikin sauri ta fita a ɗakin, ta samu filin gidan kowa ya shiga ɗaki dan sanyi da ya sauƙo, ɗakin da take kwana da Nazifa ta shiga ta samu ta kwantar da Hanan ta sauya mata kaya zuwa na bacci, ita ma kwanciyar tayi gefenta, Hanan ta da idonta biyu ta matsa kusa da Nuratu ta shige jikinta, jin haka ya saka Nuratu rumgumeta a jikinta.

"Aunti mai Daddy ya miki?"

"Babu komai, kiyi bacci."
Tace ta rumgume yarinyar tana ji bacci ya ɗauketa. Tunani ta faɗa sai taji kwata kwata bata kyauta mishi ba, shi da yake tasowa daga can wani gari dan ita ta tsaya mishi wulaƙanci.

Da safiyar ƙarfe tara ya shigo cikin gidan bayan Kawu Muhammadu ya sameshi da asubanin ranar sun tattauna, sun jima suna magana kafin su rabu. Har ya mishi godiyar kayan abinci da ya kawo yace babu komai.
Cikin shirin tafiya ya shigo ya gaisa da Mama Yawuro.
Hanan da ke cikin ɗaki taji muryar Daddyn ta ta fita da sauri cikin kwalliyarta da Nuratu ta mata. Sanin da wuri zasu wuce ya sata ɗumama ruwan zafi ta mata wanka ta shiryata cikin kayanta ta haɗa sauran da ta cire ta saka a jakanta.

"Zamu wuce Mama kar dare ya mana a hanya."
Dr Awwab yace bayan sun gaisa da Mama Yawuro.

"To Allah ya kiyaye muna godiya. Kun yi sallama da Kawu Muhammadu?"

"Eh mun yi."

Yace ya kai idonshi kan Nuratu da ta fito ɗauke da jakan kayan Hanan, bai jira ta ƙaraso wajensu ba ya fita ganin haka ta bi bayansu har waje. Ya saka Hanan a front seat ya zagaya ya shiga.

"Ina kwana?"
Nuratu tace tana rufe ƙofar baya da ta saka jakan Hanan.

"Lafiya ƙalau Babyna. Ya kika tashi?"

Ita dai bata son wannan sunan da yake ƙiranta dashi sai kace ƙaramar yarinya. Duk tsammaninta yayi fushi kan abin da ta masa daren jiya sai taga akasin haka.

"Sai na dawo."
Yace ya kunna motar yana barin gurin cike da kewa Hanan tana ɗaga mata hannu. Haka ta koma cikin gida.

Tafiya yake farin ciki yana ratsa zuciyarshi tuna maganar da Kawu ya zo masa dashi da asuba.
Cike da farin ciki Dr Awwab ya yi godiya sosai dan bai taɓa tsammanin haka lokaci ɗaya ba, bai taɓa tsammanin zai samu Nuratu a kwana kusa ba. Har musayar lambar waya su kayi har lambar Alhaji Inuwa ya bashi kafin su rabu.

***

Al'ameen Pov.
Tun asuba ya ɗauki hanyar Nijar akan yana son isa komai cikin dare hakan bai samu ba dan matsalar mota da ya samu a Babban Gida. Sai yamma lis ya shiga Geidam hakan yasa ya kwana da safe ya ɗauki hanya.

***

MAIDUGURI.

"Ummi na samu Baffa mun yi magana da shi, na sanar da shi akan ranar asabar nake buƙatar mu je, ya sanar da ni babu komai."

"Kana ganin babu gaggawa cikin lamarin nan Awwab?"

Ummi tace dan Dr Awwab bayan dawowarsa ya sanar da ita maganar da su kayi da Kawu Muhammadu. Bayan sun gama maganar ta turashi wajen baffansa, yanzu yake sanar da Ummi yadda su kayi.

Kai ya girgiza.
"A'a Ummi kiyi addu'a kawai."

"To Allah kaimu ya sanya alheri."

Da ameen ya amsa ya tashi ya wuce gidanshi.

***

Azahar ya shiga cikin garin dan sammako da yayi, lambar wayar da Mami ta bashi na Kawu Muhammadu ya ƙira ya sanar da shi wanene bayan ya saya sabon Simcard da katin waya.

"Bari azo ɗaukar ka zan turo yaro."
Kawu Muhammadu yace bayan sauraran bayanin shi.

To Al'ameen ya amsa da shi ya kashe wayar ya zauna zaman jira. Mintuna ashirin wayar ya ɗauki ƙara ya ɗauka Musalle ya sanar da shi ya iso ya fita suka haɗu suka koma motar kafin su nufi gida.
Sai da ya huta yayi sallah yaci abinci ya gaishe da Mama Yawuro kafin ya zauna jiran Kawu Muhammadu zuwa dare dan baya nan. Nuratu ba ta da labarin zuwan shi sun fita kasuwa ita da Nazifa.

***

DAMATURU.

Mufid party daban daban yake haɗawa shi da abokansa Faisal da AA, Daddyn shi ya sanar dashi an rage kwanakin auren shi da Nuratu saura kwana biyar, in da hakan ya sashi amsar kuɗi wajen mahaifinsa miliyoyi kusan biyar da ya bashi damar wasa da su.
Party yafi kala biyar suka shirya, sun gayyaci abokansu da su kayi karatu a tare. Wanda tun daren jiya suka fara gudanar da shi.

Har office ya kaiwa Sufyan invitation card mijin Rukayya yana ta mamakin wannan aure da Rukayya bata da masaniya da ta sanar da shi.
Kasa barin abin yayi a ranshi ya samu Rukayya da dare ya sanar da ita.

Tana kwance tana kallo jin bayanin mijinta ta miƙe cikin sauri tana kallonshi.

"Ba dai Nuratu tamu ba Lovely?"

"Ga IV ɗazu ya kawo min office, nima nayi ta mamaki ban tsamman ita bace, amma na kasa barin abin a rai na."
Yace yana miƙa mata IV da ya shigo dashi falon ta karɓa cikin gaggawa.

Sunan Nuratu ta gani ɓaro ɓaro tare da Mufid za'a ɗaura aure ranar asabar ƙarfe ɗaya da rabi bayan sallar azahar a cikin gidansu.

"Ba zai yiwu ba."
Tace tana yaga IV ta laliɓo wayarta ya kwace.

"Me za kiyi."

"Mami zan ƙira na san bata da labari wallahi. Wannan shegen yaro tsinannen ɗan iska Abba zai haɗa aure da ita. Baya tuna ko halin da ya jefata ciki zai ɗauki aurenta ya bashi. Anya Abba yana tsoron haɗuwar shi da Allah na tauye mata haƙƙinta da yake kanshi."

Da sauri Sufyan ya toshe mata baki kar ta kwasa zunubi.
"Kar kice komai Lovely, mahaifinki ne. Tabbas Mami bata da masaniya amma ba haka lokaci ɗaya ya kamata ta sani ba. Ki ƙira Aunti Rahma da Hasiya kuyi magana in ya so sai gobe kuje ku sameta dan samun mafita. Amma yanzu sai ki hanata bacci ai."

Hawayen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login