Follow us on social media

Showing 48001 words to 51000 words out of 148866 words

Chapter 17 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

41

Yaushe? Ina zamu sani bayan tun lokacin da abun ya faru baku sanar ba balle a samu shaidar eh lallai anyi fyaɗen. Dan Allah a kiyaye, bama fatan hakan yayi ta faruwa amma mu saka ido kan yaranmu musamman ƙananan yara, yanzu duniya ta lalace.
Wannan shari'ar wata uku da shigar shi amma saboda tun farko an tsaya an ɗauki dukkan shaidu, mun samu cikin sauƙi mun warware shari'ar.
Godiya ga dukkan wanda suka bada shaida domin abune mai wahala a yanzu a samu masu irin haka. Fatan Allah kiyaye mu ya ƙaremu da yaranmu."

Ameen! Aka amsa da shi gaba ɗaya cikin kotun banda Alhaji Kashim da cewa yake ta ya za'a yiwa ɗanshi bulala har ɗari. Haka Ummu ma da har hawaye ta fara shikenan an sawa ɗan ta namiji kwaya ɗaya a gaba.

Cikin wani ɗaki aka kai Mufid da su AA, alƙali da sargent ɗaya. Gefe Nuratu da take jikin Maminta hawayen idonta har sun bushe idon ya kumbura dan kuka. Alhaji Kashim da Hajiya Hindatu hanasu shiga a kayi dan yadda suke bala'i.
Daga waje suna jin ƙaran bulalan da ake zubawa Mufid da abokansa da ana gamawa suka sume a gurin. AA har fitsari ya sake dan azaba ana gamawa aka cicciɓo Mufid aka jefa motar Alhaji Kashim da su Faisal. Kai tsaye asibiti ya wuce dasu dan yadda fatar jikinsu ya tashi, ga Mufid da babu numfashin kirki a jikinshi.

***

Gaba ɗaya ahlin suka dunguma zuwa gidan su Nuratu hatta Dr Awwab da bai taɓa zuwa ba. Nuratu rasa kalmar da za ta musu godiya tayi a bakinta sai murmushi take zubawa da kumburarren idanunta. Idanun Dr Awwab saman fuskarta dimple ɗinta shi ya fi komai masa kyau yadda yake lotsawa dukka biyu.
Yayi kewarta yayi kewar idanuwanta da yadda take watsa masa harara da su. Rigimar ta burgeshi yake.

Mami ta musu godiya haka sauran yayunta suka shiga kitchen suka haɗa abincin dare har da su. Bayan sun gama suka bar musu falon. Col. Ahmad, Dr Awwab da Yaya Al-ameen da Muhsin da ya shige cikin su dan shegen tsawon kafa ne da shi, su kaɗai suka rage a falon, sunci abinci ba laifi ban da Dr Awwab da kaɗan ya ci ya bari.

Matan suka shige ɗaki Mami da Amma Jidda da Aunti Zarah da Rahma. Can ɗakin Nuratu ce da Hasiya da Rukayya da Walida sai Ameera da sai hura hanci take.

Bayan mazan sun gama suka miƙe dan Col. Ahmad da Dr Awwab suna son wucewa Maiduguri komai dare. Mami da sauran suka fito kowa bakinshi in ya buɗe godiya yake musu musamman Col. Ahmad da ya jajirce akan case ɗin har aka hukunta masu laifi.

"Nagode Col. na gode sosai da taimako. Allah ne kaɗai zai biya ka."

"Kar ki damu Nuratu, tamkar ƙanwata haka na ɗauke ki. Sai bayan kwana biyu, ga numbern wayana za muna waya, in na samu lokaci za ina zuwa duba ki."

Kan Nuratu ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta karɓi card ɗin da ya bata kafin ya shiga motar shi ya tafi, ta koma cikin gida. Dr Awwab da tun farkon tsayuwarsu ya ji ya kasa juran ganin su haka ya bar gurin da motarshi ko sallama bai samu ya mata ba.

Nuratu tana shiga ta samu Muhsin da Yaya Al-ameen suna zaune, Rahma da su Hasiya da Walida suna tare dasu, bata zauna cikinsu ba ta wuce ɗakinta in da Ameera take. Bata mata magana ba dan ta lura yarinyar bata da daɗi, alwala tayi ta fito jin ana kiran sallar magriba ta gabatar da sallah.

Sai wajen ƙarfe taran dare kafin kowa ya wuce gidanshi aka bar Nuratu daga ita sai Mami da Munirat.

***

Kwanan Mufid ɗaya kafin ya farka, jikinshi duk shatin duka da ya warke sai tabon da bai gama gushewa ba, yana samun kulawa sosai, a rana na uku aka sallameshi ya koma gida.
Hajiya Batul da yaranta sun shigo sun mishi ya jiki suka koma dan babu jituwa tsakanin matan sai yaransu.

Burin Mufid ya cika sai burin auren Nuratu, yana taso da maganar Alhaji Mamman da ya ji ya nema masa visa zuwa ƙasar Las Vegas wajen abokinsa da yake can, yace ya zauna ya kula da kanshi maganar auren Nuratu ba yanzu ba sai zuwa wani lokaci kafin nan kowa ya mance abinda ya faru. Da wannan ƙaryar ya samu Mufid ya amince ya tafi ba dan ya so ba, haka Hajiya Hindatu ma ta amince.
Rufaida ta fi kowa murna amma dai ta san silar ƙara lalacewarsa ne zuwa ƙasar waje ba wai dan neman sulhu ba.

***

Tun da wannan rana da lokaci Nuratu take ganin mutuncin mutanen huɗu nan, Col. Ahmad, Dr Sadiq da Dr Awwab sai Yaya Muhammad Al-ameen da shima ganin mutunce take masa tamkar sauran. Su kaɗai take ganin mutuncinsu take sakar musu fuska. Maganar aure da soyayya ta cireshi a ranta ba yanzu ba ta ajiye a gefe.
Duk da har lokacin in ta tuna abinda ya samu rayuwarta sai ta zubar da hawaye. Har lokacin tana kan shan magani da yake hanata yawan ciwon kai. Sai shiga cunkuso da ta daina yi sosai.

Dr Awwab yana zuwa duk ƙarshen wata shi ya ɗauke mata wahalar siyan magani, tare da Hanan yake zuwa da tun lokacin ta maƙalewa Nuratu har zuwa yanzu da tayi wayo. Dr Awwab ya riga ya amince ya yarda son Nuratu yake ɗari bisa ɗari.

Col. Ahmad yana ƙiranta suna gaisawa da sabuwar wayar da Mami ta saya mata, shi kam har yanzu ya ɓoye mata cewa sonta yake ya rasa ta inda zai sanar da ita domin shi ya fara jefa zuciyarta ta bashi matsayin Yaya ba masoyi ba, gashi yanzu abin yana damunshi. Bayan wasu watanni yana samun zuwa dubata, lokacin da iyayenshi suka sake mishi maganar aure yace ya samu mata, anan ya sanar da su ga wacce yake so. Nan Umma ta daka tsalle tace ba zai yiwu ba ya aure sauran wasu ba. Numbern Nuratu ta bi ta nema ta ƙirata ta mata tas.
Ranar Nuratu kukan da tayi har wani numfashinta sama sama yake da kyar Mami ta lallasheta tayi shuru bacci ya ɗauketa daga baya ta sanar da ita ga abinda ya faru.
Nan Mami tace tayi hakuri dama dole ta fuskanci irin haka amma kar ta faɗawa Col. Ahmad haka suka bar abin a ransu.

Haka Yaya Al-ameen ma da ya taso da maganar aure Nuratu ta dakatar da shi bai ji zafi ba ya bata lokaci.

Aunti Rahma ta sake haihuwar ƴa mace sai Khair da yanzu take goyo. Aunti Hasiya ta haihu namiji sai wanda ta haifa yanzu. Haka Rukayya ma ta haifi ƴan biyu mace dana miji yanzu shekarunsu uku bata ƙara haihuwa ba cewarta hutu take. Yanzu maganar auren Walida ake.

Alhaji Mamman tun lokacin ya ƙara watsar da lamuran Nuratu da Hajiya Sadiya. Rufaida har gida ta zo ta bawa Nuratu hakuri tace babu komai domin hakan Allah ya rubuta yana shafin ƙaddarar ta, su kaci gaba da mutuncinsu sama sama dan Rufaida baya baya take ja da ita.

Bayan an cinye shekara ɗaya Nuratu ta koma makaranta bisa matsawar yayunta da Mami, hakan yasa ta koma taci gaba da karatunta har Allah ya sa yanzu tana shekarar ƙarshe. Kasuwanci Mami ya dawo arziki Allahamdulillahi ya zauna mata ta ƙara gyara gidan, ta sayi mota, Muhsin ya koya mata ita da Nuratu da karambani ya ke sata ɗauka bata kware ba.

****

Ci-gaba.

"Nuratu!"

Mami da ta tsaya a kanta tsawon lokaci bata sani ba sai da ƙira sunanta kafin ta buɗe idanunta da hawayen yana zuba bayan fuskarta da ta ɓata da ruwan hawaye. Zama Mami tayi kusa da Nuratu, Nuratu ta gyara kwanciyar ta ta ɗaura kanta saman cinyarta.

"Mami na kasa cire abin nan a raina. Ban san ya zanyi ba. Bana kwana na tashi bai faɗo mini ba."

"Addu'a za kiyi duk lokacin da hakan ya bijiro miki. Ki daina tuna baya domin bayanki ba alheri bane. Mu fuskanci gabanmu."

Shuru kawai Nuratu tayi Mami tana ta mata nasiha kamar kullum har ta daina hawaye. Ta san da wuya ta cire abinda ya faru a ranta.
Munirat ce ta musu girkin dare dan Nuratu ciwon kai ne ya zuba mata. Bayan taci ta shige ɗaki anan ta tarar ƙiran Dr Awwab.

"Noor ina ki ka shiga ne ina ta ƙira, har ina tunanin dawowa gobe."

Murmushi tayi tana mamakin Dr Awwab da duba ɗaya zaka mishi kace bashi da magana, ko da yake hakan ne dan in har suna tare baya wuce magana biyu zuwa uku yake yi mai tsayi shikenan kuma yayi shuru. Akwai jan aji da miskilanci a tattare dashi, sai ka zauna da shi yake iya kauda su gefe ya maka magana.

"Dr wayar yana ɗaki ina waje ne. Kun isa lafiya? Ina Hanan?"

"Lafiya ƙalau. Hanan tana wajen su Hussaina. Na manta ban baki sakon Ummi ba ɗazu tana gaishe ki."

"Ina amsawa. Allah dai ya dawo dani Maiduguri in zo gaisheta."

"Za ki zo zuwa na musamman Noor. Ko ba haka ba?"

"Bance ba?"
Tace tana murmushi ganin yana neman kawo mata wani hirar ta canza salon hiran.

"Zanyi sallah ban yi isha'i ba."

"Shikenan a samu a addu'a sosai Noor ina buƙatar hakan."

"InshaAllah kullum kuna cikin addu'ata."

Bayan sunyi sallama ta gabatar da sallar isha'i ta kwanta, bacci ya gagari idanuwanta, mutanen nan uku suna shirin sakata cikin damuwa.

....

Kiɗa ne yake tashi a motar ya shigo gidan, kan shi yasha aski ƙasa an aske, sama an bar gashin da yake kwance irin na asalin fulani. Kyau har kyau babu tarbiyya da kyan hali. Wani shegen wandone jikinshi duk a yayyage, rigar kuwa farace tas sai tarin sarƙoki a wuyanshi har da ɗan kunne ɗaya.
Busar iskar sigarin shi yake yana waya da Faisal akan maganar zuwa birthday party na shi da za'a gudanar anjima yake sanar dashi yana tafe zuwa dare.

Mufid Kashim da shekara ɗaya kenan da dawowarshi daga ƙasar Les Vegas zuwa Nigeria.

....

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE  26.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

...

Shekara ɗaya kenan da dawowar Mufid Nijeriya ya kasa zaman ƙasar waje, duk da kuɗi da Daddynshi yake tura mishi kuma yana jin daɗin zaman gidan abokin babanshi da babu mai shiga harkar wani kowa rayuwarsa yake a gidan.
Kasa zama yayi a ƙasar dan har lokacin son Nuratu ya kasa barin zuciyarshi, wani mahaukacin so yake ji a ranshi na Nuratu, siffanta da zumarta ya kasa barin ƙwaƙwalwarsa. Mafarkin shi take zuwa da hakan yake ƙara kusanta zuciyarsa da sonta, sai ya farka yake ganin mafarki yake. Haka yasa ya tattaro ya dawo gida.
Alhaji Kashim yayi ta faɗa amma Hajiya Hindatu ta nuna tana son zaman ɗanta kusa da ita ya sa Alhaji Kashim hakura ya barshi. Tsakanin shi da AA da Faisal sai dai waya dan basu ƙara haɗuwa ba tsawon shekarun sai dawowar shi suka ci-gaba daga inda suka tsaya. AA mahaifinshi ya kore shi a gidan dan ya gaji da iskancin shi, ya koma gidansu Faisal da zama da shima mahaifinshi ya cire hannunshi a komai na rayuwarshi ya zuba masa idanu.

Yau ake birthdayn Faisal tun jiya suke shirye-shirye, babban hall suka kama inda za su gudanar, sun gayyaci abokansu manya manya har daga wata ƙasa banda ƴan matansu da suma suka zo.
Karfe takwas aka fara gudanarwa gurin cike yake da yara masu ji da kuɗi da iskanci da duniyanci, kiɗa ke tashi wasu na busar sigari, wasu shisha wasu suna kora ruwan wine wasu kuma rawa suke yi kamar ba gobe.

Mufid da busar sigari ya zame masa jinin jikin, yana zaune yana ta busar abin shi yana buɗe idanuwansa lumshashshu yana rufe su yana jin daɗin kiɗan dake tashi. Ƴan matan gurin rabi da kwata duk hankulan su na gurinshi da ya tafi da imaninsu domin yayi kyau sosai, dan Mufid akwai kyau ga haske, sai ya zama tamkar gayun Amurka da suke jin daɗin duniyarsu.

Idonshi ne ya kai kan wata black yarinya da take sanye da bakaken kaya riga da wando ta juya baya, rabin fuskarta yake kallo tana magana da yar gefenta tana murmushi, dimple ɗin ta dake na gefe ɗaya ya lotsa. Zuciyarshi ta kasa hanashi da yarda cewa ba ita bace domin idanuwansa sun nuna masa tabbas ita ce.
Bai yarda ba ita bace sai da ya kai kanshi gurinsu ta juyo ya ga ƙarya idanuwansa suke masa. Tsaki yaja ya bar gurin, cikin hall ɗin gaba ɗaya ya bari ya fita waje, motarshi ya shiga ya cigaba da shan sigarin shi. Sai da ya shanye tas kafin yana ƙoƙarin barin gurin AA ya fito.

"Ina zuwa?"
Fadin AA.

"Gida."
Mufid ya faɗa yana ƙoƙarin kunna motarshi.

"Na ga dai ba'a tashi ba."

"To nace maka gida zan je."

Mufid yace ya kunna motarshi ya ja da ƙarfi yana barin gurin. Kai tsaye gida ya nufa ya samu kowa ya kwanta hakan yasa ya wuce ɗakinshi bai iya ko wanka ba ya zube saman gadonshi.

***

MAIDUGURI.

"Ahmadi wai ba za ka yiwa kanka faɗa ba, shekarunka talatin da bakwai amma har yanzu ka kasa ajiye mata. Abin nan fa yana damuwa, kawai magana ne bana yi."

"Kai ma dai ka mishi magana, nayi faɗan nayi har na gaji. Kamar wanda aka asirce shi."

"Babu batun asiri, ra'ayi ne ina ga har yanzu bashi dashi ko Ahmadi? Ko dai budurwarka ta yaudare ka?"

Baban Ahmad da Umma suke mishi faɗa akan rashin aurenshi, shi kam banda murmushi babu abinda yake yi sai ma dariya da yayi jin abin da babanshi yace ya girgiza kai.

"Abba har yanzu ita ɗince a raina."

"Wacece kenan?"
Faɗin Baban Ahmad.

"Nuratu, yarinyar nan dai."

"Ka isa? Ya mu kayi da kai."
Faɗin Ummu tana watsa mishi harara fahimtar inda maganarshi ta dosa. Kanshi ya ƙara sunkuyarwa ƙasa zai yi magana Abba ya tare shi.

"Gobe da safe za mu yi maganar tashi ka je."

Babu musu Col. Ahmad ya miƙe ya fita. Abba ya juya yana kallon Umma.

"Ke kuma ai ba haka ake yi ba a hankali zaki bishi."

"Wani irin a hankali Alhaji. Kana dai ji abinda yake shirin jajiɓo mana."

"To ya za mu yi a hankali za mu bi mu hanashi auren. Dan gaskiya nima har cikin raina bana son abin nan."

Faɗin baban Ahmad, dan tun shekarun baya Umma ta sanar da shi komai lokacin da suka buƙaci yayi aure ya nuna musu ga wacce yake so. Umma kuwa mamaki take da har yanzu wannan shegiyar yarinya ta kasa rabuwa da ɗanta.

Washegarin Col. Ahmad ya samu zama da Abban shi akan maganar Nuratu.

"Wanene mahaifinta?"

Shine tambaya na farko da Abba ya watsa mishi da ya rasa amsa dan basu bata zancen da Nuratu ba, ya dai san yayunta banda haka bai san komai a kanta ba.

"Kai nake sauraro Ahmadi. Wanene mahaifinta?"

Dakyar ya iya buɗe baki yace.

"Ban sani ba Abba wallahi. Bamu taɓa hiran ba, amma ina tsammani ya rasu ko basa tare da mahaifiyarta."

"To ka binciko hakan da kan ka, in ka samu ka sanar da ni. Amma a yadda na fahimce ka yarinyar nan gaban mahaifiyarta take. Ƴar mace ce."

"Hakane Abba su biyu suke rayuwa asalin su ƴan Nijar ne amma?"

Cike da mamaki Abba yake dubanshi kafin yace.
"Ka binciko sai musan abin yi."

To Ahmad ya amsa dashi yana yiwa Abban shi godiya ya fita. Hutun sati ya samu daga Ibadan yau kwanan shi biyu da zuwa.
Abba da kallo ya bishi. Wannan aure da yake so ba zai taɓa yarda da shi ba. Yarinya ƴar mace tarbiyyar mace ina ta ga nutsuwa da kamun kai, dole rayuwarta ya samu tangarɗa mana balle kuma dangi suna wata ƙasar su suna zaune a wata ƙasar. Ko haka aka sanar da mutum sai ya kafa ayar tambaya.

****

DAMATURU.

"Daddy aure nake so."

Mufid yace kai tsaye yayinda yake zaune saman table suna breakfast su ukun da Ummu da Alhaji Kashim.
Da mamakin jin furucin shi suka kalle shi ya sake maimaitawa cewa aure yake so.

"Zan maka babana. Kana da wacce kake so?"
Alhaji Kashim yace yana duban Mufid.

"Ina da ita mana kai ma ka sani Baby Noor ce."

"Wato har yanzu baka rabu da sonta ba Mufid. Anya yarinyar nan bata tsafeka ba."
Hajiya Hindatu tace cikin ɓacin rai.

Murmushi Mufid yayi da yake fito da kyakkyawar fuskarshi.
"Tsafi kuma Ummu. Ni dai Daddy ka nema min aurenta. In kuma ba haka ba?"

Da sauri Alhaji Kashim yace.
"Dan Allah kar ka kuma jawo wani abun Mufid, zan nema maka aurenta."

"You're the best Daddy thank you."
Mufid yace yana miƙewa ya bar musu gurin.

"Yanzu kai Daddym Humaira da gaske ka ke. Kar ka saka mishi abu a rai ya zo bai yu ba."

Murmushin ƙyeta yayi.
"Hajiya Hindatu ko ince Ummun Humaira, in baki sani ba mun samu hanyar rama abinda suka saka aka yiwa ɗan mu. Alhaji Mamman sai ya gane ƙarfin kuɗi da mulki yanzu dashi ake takama. Auren yarinyar nan tamkar anyi an gama Mufid ya sameta."

"In kuma ta shigo sai ta gane shayi ruwane, sai ta zubar da hawayenta, sai na tarwatsa sauran farin cikinta da ya rage."
Hajiya Hindatu tace suka kwashe da dariyar mugunta dukkansu.

***

MAIDUGURI.

Kwance yake saman gadonshi babu inda yake zuwa a garin, datar wayarshi kunne yana duba sakwanni ya ga notification cewa Nuratu tana online. Kan sunanta ya shiga ya tura mata saƙo.

*"Mai ki ke yi da safe haka a online. Kin bar Mami tana aiki."*

Nuratu da ta kulle kanta tun safe a ɗaki dan sanyi da ake babu makaranta ya ƙare ta shige cikin bargo, bacci tayi har ƙarfe goma kafin ta farka bata iya fita ba ta jawo wayarta ta kunna tare da duba sakwannin safiya da ya wuceta bata online ta samu saƙon Col. Ahmad.

Murmushi tayi ta tura mishi.

*"Sanyi ake sosai, ni kuma ina tsoron sanyi."*

""

Amsar da ta bashi ya sashi yin murmushi ya mai da mata da amsa.

*"Kina tsoron sanyi? In kin yi aure fa? Wa zai miki?"*

Karanta saƙon tayi taƙi bashi amsa ƙarshe ma ta sauƙa a online ta ajiye wayar, kafin ta matsa ya ɗauki ƙara ta ga dai shine. Ɗauka tayi ba dan taso ba ta mishi sallama ya amsa yana haɗa mata da tambaya.

"Muna cikin hiranmu kika sauƙa kuma?"

Rasa amsar da zata bashi tayi tai shuru yaci gaba da cewa.

"Ki shirya karɓa na gobe ina hanya. Fatan ba zan takura miki ba?"

Kamar ta kurma ihu ta girgiza kai ƙasa ƙasa tace.
"A'a sai ka zo Allah kawo ka lafiya."

"Ameen Nuratu ki gaishe da Mami."

"Za ta ji."
Tace ta kashe wayar ta ajiye ta shiga bathroom dan fitsari da ya matseta, brush tayi tai fitsarinta ta fito cewarta sanyi ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login