Follow us on social media
Showing 93001 words to 96000 words out of 148866 words
Chapter 32 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
Allah ka bari Dr, baka ganin akwai mutane."
Bai mata magana ba ya sassauta riƙon amma har lokacin hannunshi a jikinta ya riƙo kugunta yana cewa.
"Soon zan riƙe ki son rai na."
Bata mishi magana ba ta turo baki tana juyar kanta.
Daga haka aka fara tafiya har ƙofar gidansu Nuratu, aka fara sauƙa, tana ƙoƙarin fita taji Dr Awwab yace.
"Ki shirya gobe da wuri zamu zo."
Fit ta fice bata gama sauraranshi ba, ya bita da kallo har ta shige kafin ya fita ya koma gaba suka bar harabar gidan.
...
Washegarin da safe aka fara shirin kai amarya, inda amarya Nuratu tana can ɗakin Mami tun safe ta rufe kanta da bargo tana ta kuka sosai kamar wanda aka mata dole. Anyi lallashin anyi taƙi shuru sai ma ƙara kuka da take, Aunti Hasiya faɗa ta dinga mata kamar za takai mata bugu.
Mami da taga kukan ƴartan yayi yawa ya sata koran duk wanda suke ɗakin ya rage su biyun ta zauna kusa da ita.
"Wai menene Autana? Auren ne bakya so ko kuma Dr ne bakya so. Ko dai har yanzu ba ki cire wannan abun a ranki."
Ita dai Nuratu shuru tayi tana share hawayenta, wani mugun tausayin kanta take ji da irin sabuwar rayuwa da za ta tsinci kanta. Hannunta Mami ta kama ta ɗagota zaune.
"Ki cire komai a ranki ki rumgumi ƙaddararki kinji, ki riƙe mijinki, tun da shi ya nuna yana sonki a haka to kuma menene za ki damu kan ki? Uwar mijinki tana sonki da kowa nashi to menene abun damuwa. Kiyi hakuri kinji inshaAllah zaki ji daɗi zama da Dr Awwab."
Nasiha Mami tayi ta mata har Nuratu tayi shuru ta kwantar kanta saman cinyar Mami.
"Ni Mami bana son yin nisa dake."
"Hakuri za kiyi aure ya gadi haka, wasu fa wani ƙasa ake ɗaukarsu akai balle ke nan zuwa Maiduguri da ko ihu kinyi zanji. Tashi kiyi wanka ke kaɗai ake jira."
Da kyar ta miƙe Mami ta fita ta turo mata mai gyaran jiki ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka da turare da sabulu mai ƙamshi tayi ta fito ta lulluɓeta da bargo ta saka wuta da turaren wuta ciki na tsugunno da na jiki ta ɗumamata sosai, har wutan ya mutu kafin ta bata kaya atamfa da zani ta saka ta lullubeta da luffaya suka fita. Ƙamshi kawai take fitarwa tayi kyau.
Motoci dayawa sun zo ɗaukar amarya duk an shiga ciki, motar da amarya za ta shiga har cikin gidan Mami ya shigo aka shigar da Nuratu da kyar dan yadda ta ƙamƙame Mami sai kuka take. Motar daga ita sai Rukayya dake gaba, baya da Walida da Aunti Zarah sun sata tsakiya, suka ɗauki hanya ta kwantar kanta saman cinyar Aunti Zarah taci gaba da kukanta.
Ƙarfe sha biyu aka suka shiga cikin Maiduguri, kai tsaye gidanta aka fara wucewa da ita in da mutane suka saki baki ganin kyan gidan da kuɗi da aka kashe masa. Kayan ɗaki da su Aunti Rahma suka zo jerawa a ɗakin ƙasa suka saka domin Dr Awwab ya gama komai na ɗakin sama da falon. Kayan falon ƙasa ma abubuwa kaɗan suka ƙara mata sauran suka saka a wani ɗaki, sai kitchen da shine kaɗai bai saka komai ba amma ya mata komai na zamani. Banda kayan akwati jeri 4 da ya haɗa na lefe.
Har cikin ɗakinta da yake sama aka sakata aka zaunarta saman gadon kafin su fita kallon cikin gidan, sosai gidan yayi kyau dan Dr Awwab yayi ƙoƙari ya zuba kuɗi an masa gyara.
"Gidan ki yayi kyau Sister, Docter yayi ƙoƙari sosai."
Walida tace tana cire kayan da Nuratu za ta saka dan zuwa buɗan kai gidan su Dr Awwab da suke shirye-shirye buɗar kan amarya.
Nuratu da ta zama wata shuru shurun ƙarfi da yaji ta karɓi kayan ta wuce bathroom ta watsa ruwa ta canza kayan ta fito, mai kwalliyar da suka zo da ita ta mata suka lullubeta da luffaya sai ƙamshi yake. Bayan kowa ya gama shiryawa abokan Dr Awwab suka zo suka ɗauke su suka wuce gidan Ummi dan buɗan kai.
Gidan Ummi cike yake da ƴan uwa da dangi da abokan arziki ana ta shirye shirye dan buɗan kai.
A falon gidan har ciki aka ajiye Nuratu saman darduma da aka shimfiɗa, kanta a sunkuye a ƙasa ta kasa ɗagowa, mayafin jikinta taja ta ƙara rufe fuskarta dashi. Hussaina ce ta zo ta buɗe mata fuskarta bayan ta raɗa mata suna.
"Haske." Kamar yadda ma'anar sunanta yake haka suka bi.
Daga nan ango Dr Awwab ya iso ya zauna kusa da Nuratu aka fara basu kyautan kuɗi, zubasu ake saman cinyar Nuratu, wani Dr Awwab wasu dukkansu biyu suke bawa. Aunti Rahma a gefenta ganin sun fara mata yawa ta fara kwasa tana sawa a jakan gefenta.
"Suna kama da marigayiya Sumayya."
Ummi taji Ammi ta faɗa mata ga Baffa Abubakar tana duban Aunti Rahma da tun shigowar su ta bisu da kallo gaba ɗaya ƴaƴan Mamin, musammam Aunti Rahma da take kama da marigayiyar ƴarta da ta rasu wajen haihuwa shekara biyu da ya wuce.
Ummi ma kallon Aunti Rahma take tana ƙara hasko kamanninta da mutane biyun sai ta ga har tafi kama da shi akan Mami, ga kuma Ammin Sumayya da ta ƙara sakawa zuciyarta ruɗani da kalamanta, dan tabbas tana kuma kama da ƴarta Sumayya fiye da shi.
'Akwai wani abun tsakanin su tabbas.'
Tace a zuciyarta a fili kuma tace.
"Sosai ma nima na ga hakan."
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 45.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Biki aka gudanar me tsafta kamar yadda al'ada ya koyar, bayan an gama bada kyauta aka buɗe fuskar amarya aka fara ɗaukar hoto. Ita dai Nuratu ta zama mutum mutum dan duk yadda aka juyata bi take. Anyi hotuna sosai aka fara ƙoƙarin cin abinci, aka saka ƴan uwan amarya a falon Ummi bakin Ummi suka sauƙo falon ƙasa.
Nuratu kasa cin komai tayi, ko ruwa ta kasa sha, kanta ta mayar cikin luffaya dan masu shiga da fita.
"Ga amaryar."
Taji ance daga saman kanta, ta cikin luffayan ta ɗago ido ta kalli mai faɗar haka. Matashiyar budurwa da za takai sa'arta tana tsaye kanta tana nunawa wata Nuratu da yatsa. Kanta ta mayar ta sunkuya duk tsammaninta ƴar uwar Dr Awwab ce, ta ji fitar su.
"Gashi Dr Awwab yana ƙiranki."
Walida ta miƙa mata wayarta da yake hannunta tun fara hidimar.
Karɓa tayi ta ɗauka ta kafa a kunne tana masa sallama ƙasa ƙasa.
"Babyna ya taro? Fatan kinci wani abun?"
"Ni na ƙoshi."
"Au hakane, shikenan babu matsala anjima zan ciyar da ke da kai na. Dama ki sanar da su Aunties ne za a mayarsu zuwa la'asar, dan babu mai kwana."
Cikin sauri Nuratu da bata san yaushe ta ciro kanta cikin mayafi ba ta jero masa tambaya.
"Kamar ya? Akan me? Wallahi zancen ka ke, kasan dai ba zai yiwu ba, kuma ba za a fara a kai na ba."
Murmushi yayi har taji sautinshi.
"Haka al'adar garinmu yake, ba a kwana in an kawo amarya."
Kuka ta saka mishi ganin haka Aunti Hasiya ta karɓi wayar tana tambayarshi.
"Menene ya faru Docter ka saka amaryar ka kuka?"
Cike da kunya yana murmushin kukan da Nuratu ta saka mishi yace.
"Babu komai Aunti, ce mata nayi kawai zuwa la'asar za'a mai da masu tafiya."
"Shikenan shine za ta tsayawa mutane kuka. Ka sanar da masu zuwan su same mu gidan amarya yanzu zamu wuce."
To yace yana kashe wayar.
'Akwai drama.'
Yace a ranshi yana dariya, dan ya san dai mutane ba za su bar kowa ya kwana ba kamar yadda al'adarsu yake.
...
Ƙarfe uku da rabi aka mayar da su gidan amarya bayan godiya da suka ma Ummi da mutanen ta na karamci da suka musu da kyautatawa. Bayan sun isa motocin suka iso aka fara ɗaukar mutane, inda aka ce Aunti Zarah da Rahma za su kwana zuwa gobe, nan abokan ango suka ce sam ba'a haka anan. Ko su tafi ko kuma su ɗauke amarya su kai wa ango.
"Amma dai ko ina ana kwana a gidan amarya in an kawota."
Aboki da ya kasance makusancin Dr Awwab ya kalli Rukayya da ta faɗi haka yace.
"A wani wajen ba, amma mu nan ba a haka. Ku fito kawai mu tafi kar dare ya mana, muna son dawowa a yau."
"Ikon Allah."
Aunti Rahma tace ta ƙara da cewa.
"To ku bamu minti goma dan Allah."
"Shikenan kuyi sauri."
Suka ce dan alƙawari suka ɗauka yadda ba'a kwana a gidan amarya a al'adarsu, haka za suyi in sun dage su kwana su ɗauke amarya su kaita wajen ango kamar yadda shima ya buƙaci haka.
Aunti Rahma da Hasiya, Zarah, Rukayya da Walida, Nazifa da sauran mutane suka haɗu suka gyara gidan cikin sauri suka saka turaren wuta, suka saka Nuratu tayi wani wankan ta saka lace suka feshe jikinta da turare suka zaunarta. Aunti Hasiya ta ajiye mata wayarta kusa da ita tana cewa.
"Kuma ki fito waje ni da ke."
Baki Nuratu ta tura tana gunguni faɗan Aunti Hasiya yana damunta, shekaru huɗu ta bata amma kamar itace gaba da Aunti Rahma.
Waje suka fita dukkansu ɗaya bayan ɗaya dan kar Nuratu ta lura da hakan, kafin su shiga mota aka tafi da su suna ma ƙanwarsu fatan zaman lafiya.
Shuru taji gidan ya ɗauka bayan dirin motocin sun ɗauke, zuciyarta ya bada wani irin sauti ta miƙe tsaye ta isa bakin window ta ɗaga labulen ta ga filin gidan babu kowa, da sauri ta sake tana nufan ƙofar waje. Babu kowa a falon sama ta sauƙa ƙasa nan ma shuru gidan sai ƙarar Ac da Tv.
'Shike nan sun tafi sun barni."
Tace wani hawaye yana zubo mata ta share, da sauri ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta sanan gado ta shiga ƙiran Aunti Rahma ta san ita kaɗai zata saurareta. Bata ɗauka ba ya saka Nuratu fashewa da kuma ta faɗa saman gado taci gaba da kukanta.
Tun bata so har wani bacci ya fisgeta dan ta jima ba tayi baccin kirki ba.
Ƙarfe takwas na dare Dr Awwab ya shigo cikin gidan, shuru babu kowa sai Tv da Ac da ya wuce sama kai tsaye ɗakin Nuratu ya nufa ya tura. Saman gado ya hangota tana bacci tayi ɗaɗɗaya bata ma san in da kanta yake ba, luffayan jikinta ta cire ta ajiye gefe daga ita sai riga da skirt na lace din jikinta da ɗankwalin kanta bai fita ba.
Zama yayi ya zuba mata ido yana bi da kallo. Bai taɓa tsammani zai samu Nuratu cikin sauƙi cikin kwana kusa ba. Allah kenan da ya saka ya zamto shine mijinta cikinsu. Allah ne ya ɗaura masa sonta tun ranar da ya ganta har zuwa yanzu kuma yake fatan har ƙarshen rayuwarsu da aljanna.
Hannunshi ya ɗaura saman nata yana ɗan bubbugawa ganin ta fara motsi yace.
"Tashi kiyi sallah Babyna. Na san ba kiyi ba."
Jin muryar Dr Awwab ya saka Nuratu tashi da sauri tana gyara zamanta ta ja baya kaɗan ganin sun yi kusanci, tana watsa mishi harara, haushinsa take ji da ya hana kowa kwana, tasan aikinsa ne.
"Kiyi sallah ki sauƙo ina jiranki a falonki."
Ba ta kula shi ba ta miƙe ta sauka ta ɗayan gefen ta wuce bathroom ya bi bayanta da kallo kafin ya miƙe ya fita a ɗakin.
Alwala tayi ta fito ta buɗe wardrobe ɗinta ta ga gurin komai daban-daban in da aka jera mata, hijab ta ɗauka ta gabatar da sallar magriba da isha'i, ta ga agogon bango ta ga an jima da yi, bayan ta idar ta zauna tana addu'o'inta ta kasa fita.
Dr Awwab fitar shi ɗakinsa ya wuce shima yayi wanka ya saka jallabiya ya fito ya sauƙa ƙasa ya ɗauko ledan da ya shigo da shi ya wuce falon Nuratu ya zauna zaman jiranta. Kusan mintuna talatin babu ita babu labarin ta ya kalli agoga ya ga ƙarfe tara da mintuna. Miƙewa yayi ya nufi ɗakinta ya buɗe ya shiga, tana zaune har lokacin saman darduma.
"Babyna ke nake jira fa kin sani."
"Ina zuwa ai."
Tace sai lokacin ta miƙe ta linƙe darduman ta ajiye ganin haka ya fita ta bi bayan shi cikin hijabin ta sameshi a falon. Saman kujera ta zauna yana ganin haka ya ɗauki ledar da ya shigo da shi ya juye kazar ciki ya ajiye a ƙasa kusa da Nuratu ya sauƙa ƙasa.
"Sauƙo kici na san ba abinda ki kaci na kirki."
"Na ƙoshi."
Tace tana ɗauke kanta saman plate ɗin kazar da kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta taji kazar ya fita a ranta da yunwar gaba ɗaya.
"Kina so in dura miki kenan."
Dr Awwab yace yana murmushi dan ya fahimceta tsaf.
"Ni na ƙoshi Allah."
Dr Awwab bai saurareta ba ya miƙe ya hau saman kujeran da Nuratu take, tana ganin haka ta fara ƙoƙarin tashi ya fizgota jikinshi, a mugun tsorace ta fara ƙoƙarin raba jikinsu.
"Ka barni dan Allah me haka?"
"Abinci zan baki. I told you ai daman ai."
"Wallahi na ƙoshi dan Allah ka barni."
Tace gab take da fashe masa da kuka.
Bai kulata ba ya saka ɗayan hannunshi ya ɗauko plate ɗin ya ɗaura saman center table, ya ɗauki yanka ɗaya ya riƙo fuskar Nuratu ya tura mata a baki.
"Cinye in ƙara miki."
"To ka sake ni."
Tace bakinta cike da naman da ya saka mata, ganin haka ya sassauta riƙon da ya mata ta fara taunawa a hankali. Yana ganin ta haɗiye ya ƙara ɗauko ɗaya ya tura mata a baki ta fara ci. Yunwar da take ji shi ya sata cin yanka kusan goma Dr Awwab yana bata yana kallon ƙaramin bakinta da yadda take tauna abincin kyau yake masa. Take yaji ranshi ya biya.
"Na ƙoshi ya ishe ni."
Nuratu tace tana janye kanta ganin Dr Awwab zai ƙara bata wani.
"Saura milk."
Yace ya ajiye ya ɗauki cup ya tsiyaya mata ya miƙa.
"Sha ko shima sai na baki."
Karɓa tayi tasha kusan rabi ta miƙa masa sauran kafin ya matsa baya ya fara ciyar kanshi. Ganin haka ya saka Nuratu tashi ta bar gurin.
Ɗakinta ta wuce ta watsa ruwa ta buɗe wardrobe ɗinta wajen kayan baccinta ta duba ta ɗauki riga mai kauri ta saka ta kashe wutan ɗakin ta kwanta.
Dr Awwab sai da yaci ya ƙoshi kafin ya kwashe komai ya kai kitchen ya kashe wutan falon ƙasa da Tv ya kashe na falon Nuratu kafin ya wuce ɗakinshi ya kwanta. Bai yi gigin zuwan mata ba dan kar ta tsorata ko tunanin wani abin daban.
...
"Aunti A'isha kin ganta dai kinga danginta. Babu abin da zata nuna mini sai ma in nuna mata hasken fata da arziki."
"Hakane Binta. Ni nayi mamaki ma, Dr Awwab ban san ina yake kallo ba ya kwaso wannan baƙar yarinyar, an daina yayin baƙaƙe fa, ko da baƙinka sai ka ƙara da mai ka yi haske, samarin yanzu shi suke ganin kyan ka."
Aunti A'isha tace ga ƙanwarta Binta Yaya ga Nusaiba. Tun dawowar su daga buɗan kai suke mai da zancen akan Nuratu da Dr Awwab dan sun so bayan rasuwar Nusaiba ya auri Binta ko dan Hanan amma sam hakan ya kasa yiwa wa. Har Ummi mahaifiyar Nusaiba ta samu da zancen tace ba za ta mishi dole ba amma in ya yarda shikenan.
Ummi da ta samu Dr Awwab da maganar ya nuna sam lokacin bashi da ra'ayin aure, kuma ko zai yi banda Binta.
Da suka samu labarin auren Dr Awwab sunyi mamaki kuma har lokacin basu cire rai ga cikar burinsu ba. Dalilin zuwan buɗar kan da Binta da Aunti A'isha su kayi kenan, dan ganin amarya da kuma nunawa Dr Awwab har yanzu suna da alaƙa da shi tun da jinin Hanan ya haɗasu.
"Ku bi komai a hankali dai, sannu sannu baya hana zuwa."
Mahaifiyarsu tace da sai lokacin ta saka baki.
"Za muyi komai cikin nutsuwa babu zargi Mama."
Aunti A'isha tace suka ci gaba da hiran da Binta.
***
Ƴan biki sun koma gida lafiya kowa maganarshi gidan Nuratu ya masa kyau. Sun kwana Washegarin suka haɗu suka tattarewa Mami gidanta suka gyara tsaf kafin kowa ya kama tafiya.
Sai da kowa ya watse Mami ta fara kewar Nuratu gidan ya zama ita ɗaya sai wanda ɗaiɗaiku basu gama tafiya ba.
...
Kwance yake cikin ɗakinsa ya zubawa silin idanu, burinshi da addu'arshi Allah yasa Nuratu ta buɗe enbulof ɗin da ya bata, ta karanta me yake ciki tayi hakuri ta bawa zuciyarta hakuri ta yafe masa cuta da ya mata a rayuwa.
Baya fita ko ina daga gida sai gida yana ɗakinshi a kwance rai da rai, ko falon Ummu baya zama sai ya zama dole, abinci ma in ya ɗeba ya shiga ɗakinshi yaci ya kai plate din kitchen ya ajiye. Ya je duk gidan Yayunshi da ƙannenshi sun sada zumunci, musamman Rufaida da yafi jimawa a can suna hira kamar ba ita ba, yayi ta roƙanta gafara.
Sau ɗaya yaje duba AA da yaga halin da ya shiga shi ya mugun tayar masa da hankali, wani tsoron Allah da duniya ya shigesa, ya san shima da yanzu shine kwance a mummunar halin da yake ciki. Ko da yake shima menene bai yi ba tun da yayi hauka tukuru da kashi da fitsari sai an wanke masa.
Bashi da buri yanzu ya wuce ya gyara karatunshi ya samu aikin yi ya tsaya da kafafunsa yayi nisa sa iyayenshi da yake jin duk su suka nuna masa hanyar rayuwarsa ta ɓaci.
***
Ƙaran wayarshi shi ya farkar da shi daga nannauniyar baccin da ya ɗaukeshi bayan dawowarsa daga sallar asuba, wayar ya jawo ya ɗauka yana sakawa a kunne.
"Yaya Awwab ka buɗe mana kofa."
Yaji muryar Hassana, tsaki yayi ciki ciki yace.
"Ina zuwa."
To tace ta kashe wayar ya miƙe da kyar ya fita yana zubawa ƙofar ɗakin Nuratu ido. Ƙofar falon ya buɗe musu ya samu Hassana ce da kayan breakfast da Ummi ta aikota da shi, a saman dinning ta ajiye ta mishi sallama ta koma.
Sama ya nufa ɗakinshi ya shiga ya wuce bathroom dan yin wanka domin baccin duk ya wartsake, wanka yayi ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya feshe jikinsa da turare ya nufi ɗakin Nuratu. Har lokacin ba ta farka ba, ya isa bakin gadon ya zauna daf da ita kafin a hankali ya rankwafo saman fuskarta har numfashinsu ya gauraye yana shaƙar numfashinta da ke fita a hankali.
...
InshaAllah daga yau sai kuma wani lokaci, zan fara jarabawa kwana kusa ku sani a addu'a.
Masu jiran Farha zan ƙoƙarta na turo ko page ɗaya, sai kuma bayan exam.
Allah bamu sa'a gaba ɗayan mu da wanda su ka yi da wanda za mu