Follow us on social media
Showing 102001 words to 105000 words out of 148866 words
Chapter 35 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
ba."
Hamdala tayi cikin zuciyarta, taji daɗi da yayi hakan, zama tayi saman kujera, ya wuce kitchen ya ɗauko musu plate da spoon da ruwa mai sanyi ya fito ya zauna shima, ya buɗe ya juye naman cikin plate ɗin ya ajiye mata gabanta tare da saka spoon biyu ya kalleta.
"Bismillahi sa hannu ko in baki a baki, na lura bakya son cin abinci da hannu sai dai a ba ki. Amma babu komai in dai aikin Babyna ne zan yi dan na samu lada a wajenta."
"Zan ci da kai na."
Nuratu ta faɗa tana ɗaukan spoon ta buɗe ɗayan takeaway ta fara cin abincin ciki shinkafa da miya ne da kayan lambu. Murmushi Dr Awwab yayi ya saka hannu shima ya fara ci bayan ya ture naman gefe. Sosai taci abincin dan rabonta da abincin mai yawa ta manta, dan na safe ma ba sosai taci ba.
Bayan ta ƙoshi ta miƙe ta ɗauko cup saman fridge ta tsiyaya ruwa ta sha ta ajiye masa sauran ta wuce ɗakinta. Sallar isha'i da taji ana yi ta gabatar ta hau saman gado ta kwanta cike da gajiya. Sosai ta gaji fatanta ta samu barci me yawa.
Bayan Dr Awwab ya gama ya kwashe komai ya zuba a dustbing sauran ya saka a deep freezer kafin ya wuce masallaci, sallah yayi ya dawo ya shiga bedroom ɗinshi, wanka ya yi ya saka boxer da jallabiya ya feshe ya jikinsa da daddaɗan turarensa yana wucewa ɗakin Nuratu. Wutan ɗakin a kunne hakan yasa ya kashe ya hau saman gadon. Nuratu tana ji amma bacci ya cinye idanuwanta ya hawo gadon, yaye bargon yayi ya shiga ciki. Jallabiyar jikinsa ya cire kafin ya kwanta tare da rumgumota jikinshi.
"Please Doctor."
Ta furta da ƙyar ƙasa domin ta gaji mutuƙa, in yace zai mata wani abun mai ɗagata a gadon gobe sai ya dage. Ba ta son maimaici dan ba ƙaramin wahala tasha jiya a hannunsa ba.
Kissing ɗin tsakanin wuyanta yayi yana goga hancinsa a wajen tare da lumshe idanunsa, ƙamshin jikinta na buganshi, da ƙyar ya danne abin da ke taso masa, murya cike da kasala yace.
"Ba abin da zan miki, kiyi baccinki na daga miki ƙafa yau."
Sai lokacin ta ji sanyi a ranta ta lumshe idanuwanta tana juya masa baya ta ci gaba da baccinta. A hankali ya saka hannunshi ya zagayo ta kugunta da cikinta ya matsota jikinsa ya rumgume, fuskarsa saman gashinta da yake fitar da wani ni'imantaccen ƙamshi, a hankali kafin shima baccin ya ɗaukeshi.
***
GOMBE.
Alhaji Inuwa yayi mamakin zuwan ƙaninshin, amma bai nuna masa komai ba ya karɓe shi hannu bibbiyu suka gaisa yana tambayarshi kwana biyu.
"Lafiya ƙalau, Yaya ya yaranmu?"
Faɗin Alhaji Mamman cike da kunyar Yayansa da ya sauƙar masa.
"Lafiyan su ƙalau. Ina na wajenka?"
Alhaji Inuwa ya faɗa dan ganin ya sake jikinsa da shi. Ko ba komai cike ɗaya ya wuce wasa.
Har lokacin Alhaji Mamman ji yake tamkar abin da ya aikata yana jikinsa. Ƙara ƙasa da kansa yayi yana cewa.
"Duk lafiyar su ƙalau wallahi. Sai kuma abubuwan da suka faru. Yaya ina neman afuwa bisa abin da na aikata dan Allah ka yafemin. Idan da son rai wallahi da sharrin shaiɗan, domin ɗan Adam dole a rayuwarshi ya aikata wani laifin a lokacin da duk yadda za'a fahimtar shi ba zai gane ba sai daga baya. Kayi hakuri ka yafemin bisa laifin dana aikata maka."
Ranar yake jira, kuma ya hango tsantsan nadama a fuskarsa da neman gafara, dogon numfashi ya sauƙe yana murmushi yace.
"Allah ya yafe mana gaba ɗaya Mamman. Amma gaskiya abin da kamin ya ɓata mini rai, amma ni dama ban riƙe ka ba, jira nake duk lokacin da ka zo da ƙafarka neman yafiya in yafe maka. Haƙiƙa ka aikata kuskure sosai a rayuwarka Mamman, Sadiya da yarinyar nan ka tauye musu haƙƙi, musamman yarinyar nan da ka cutar tun tana ciki."
"Yaya na nemi yafiyar Sadiya ta yafe mini, saura Nuratu."
"Ya kamata kam, duk da tana ƴarka akwai haƙƙin neman yafiyarta a kanka, domin amanar Allah ce gurinka, kuma zai muku hisabi. Ƴaƴan nan amanace a wajenmu, Allah zai tambayemu irin tarbiyyar da muka basu, cinsu, shansu da komai nasu na rayuwa. Mu zama masu kyautata musu da jihadi a cikin tarbiyyarsu, sannan ka da mu cutarsu ba bisa doka ba, kar mu musu tsatstsauran hukunci."
Nasiha sosai Alhaji Inuwa ya yiwa Alhaji Mamman cikin kwantar da hankali da nutsuwa, dan so yake ya ci gaba da gane kuskurensa da ya aikata. Misalai na rayuwa da hadisin Annabi shi ya saka Alhaji Mamman ya ji jikinshi ya ƙara sanyi idanuwansa suka cika da hawaye har suka samu zuba ya saka babban rigarshi ya share.
"Wallahi Yaya sharrin shaiɗan ne da kuma aboki, son duniya da dukiya ya rufe mini ido, ga shi yanzu kuɗin babu, matar babu, ƴar ta gujeni ta tsaneni na sani."
Anan Alhaji Mamman ya sanar da Yayanshi duk abin da suka aikata da Alhaji Tukur shekaru ashirin da huɗu da suka wuce.
Tun da ya fara jinjina kai Alhaji Inuwa yake har ya kai aya. Idanu ya tsura masa, wannan wai ƙaninsa duk ya aikata haka. Kai ya girgiza yana cewa.
"A'uzubillahz subhanallahi, Mamman da hankalinka ka yarda da wannan shirkar. Inna lillahi wa inna ilaihin rajiun, gaskiya ka tafka babban kuskure a rayuwarka, kayi gaggawar neman yafiyar Allah kafin na kowa. Gaskiya ka bani mamaki amma tun da har ka gano illar haka allahamdulillahi Allah karɓi tubanka."
"Ameen ya Allah."
Alhaji Mamman yace cike da dana sani marar adadi. Duk yadda Sadiya ta so fahimtar da shi lokacin ya kasa fahimta, irin wannan ranar take gudun masa ashe, ga shi yanzu ba shi da komai, komai ya kare masa.
A gidan ya kwana bangaren baƙi, dan duk yanda yaso kwana a hotel Alhaji Inuwa hana shi yayi ya saka aka gyara masa bangaren.
***
Nuratu sai ƙarfe goma ta farka da mintuna na safiyar ranar, Dr Awwab baya ɗakin, wanka tayi da ruwa mai ɗumi dan ta warware gajiyarta, kuma ta ji daɗin haka, ta gyara jikinta tayi cikin riga da skirt na leshi kalar madara, simple makeup tayi ta feshe jikinta da turare, kana ganinta kaga amarya sabuwa fil sai ƙyalli take da tashin daddaɗan ƙamshi. Gyara ɗakin tayi ta fito falonta ta gyara ta share shi ta goge kafin ta sauƙa falon ƙasa, ba tayi gigin shiga ɗakin Dr Awwab ba ta wuce kitchen. Dankali ta kwaso ta fara fere daidai wanda zai ishesu, har ta gama babu motsinshi, ta soyawa ta gama ta kwashe a flask mai kyau ta soya ƙwai ta ɗaura a sama ta ɗaura ruwan shayi.
Tsaf ta gama aikinta cikin nutsuwa har lokacin ba taji motsin Dr Awwab ba, ta jera a dining ta gyara kitchen ɗin ta fito falon ƙasa ta fita waje, ƙiran mai gadi da Baba.
Yana ganin ta fito da sauri ya nufeta.
"Hajiya kina buƙatar wani abu ne?"
"Abinci ne dama."
Nuratu tace ta miƙa masa flask ɗin hannunta ya karɓa yana zuba godiya da karamcin Nuratu.
Cikin falon ta koma ta share ta goge ta wuce sama dan duba Dr Awwab ko bai farka bane.
A hankali ta tura kofar falon ta shiga ciki, babu komai sai ƙaran Ac, cikin falon komai blue black, ya mata kyau, sai ta ga color ya shiga ranta, a kimtse komai tsaf, ana nan ta tsaya ko za taji motsinshi shuru, hakan ya sa ta wuce cikin bedroom ɗinsa cikin tsoro. A tsorace ta ƙwanƙwasa ƙofar amma shiru babu amsa, hakan ya sata tura ƙofar ta shiga, yadda colorn falon yake haka ɗakinma sai sanyi, komai tsaf sai ƙamshi, anan ta ƙara jinjinawa Dr Awwab ba shi da ƙazanta sam.
"Doctor! Daddyn Hanan!!"
Nuratu tace idanuwanta suna yawo a ɗakin tana bi da kallo har ya tsaya ƙofar bathroom. Shuru babu amsa ya sa ta juyawa ta fita da sauri a cikin ɗakin, tana mamakin ina ya tafi da safiyar nan bai sanar mata ba.
'Ko office ya wuce?'
Zuciyarta ya tambayeta yayin da ta ɗauki wayarta ta sauƙo ƙasa ta fara ƙoƙarin ƙiranshi.
Ringing ɗaya bai ɗauka ba domin ya shigo gidan. Sake ƙiranshi tayi daidai ya sako kansa cikin falon ɗauke da takeaway da sauri ta ƙarasa wajenshi.
"Ina ka tafi tun safe?"
Tace tana karɓar abin hannunshi ta kallesa tana duƙunƙune fuska.
Hancinta ya lakace ya rankwafo saman fuskarta ya hura mata iskar bakinsa yace.
"Abinci na sayo mana kina bacci. Please ki sa ki ran mana."
"Ai na dafa mana. Na haɗa breakfast ɗin."
Tace tana ƙara haɗa rai ta kawar fuskarta daga kallonsa.
"To ya za mu yi da wannan Babyna?"
"Ka kyautar wallahi dan ba zanyi asara ba."
Nuratu tace ta wuce saman kujera ta zauna bayan ta ajiye ledan saman dining, bayanta ya bi yana ɗauka .
"Shikenan bari in bawa mai gadi."
Kai ta ɗaga masa ya fita ya bawa mai gadi ta harshen fillancin yace.
"Modibbo gashi ka ƙara ta riga tayi abinci, ko ka sadakar in almajiro yayi bara."
"Ya mini yawa Alhaji nima ta ƙirani na karɓa bayan wanda ka bani ma zan ajiye da rana."
Dariya Dr Awwab yayi cikin farin cikin tunanin Nuratu yace.
"Duk yadda kayi."
Godiya ya masa yana ƙara cewa ama amarya godiya kafin DrAwwab ya dawo falon ya ƙarasa kusa da Nuratu ya zauna.
"Babyna zuba mana to. Amma ki sa ki fuskar nan."
Murmushi ta yi har dimple ɗinta suka lotsa, babu musu ta miƙe ta ɗauki plate ta zuba, ta haɗa musu tea a cup biyu ta ajiye musu kafin ta zauna ta ɗauki fork ta fara ci, a plate ɗaya su kaci kamar yadda ta ga yake musu . Ita ta fara tashi ta koma cikin falon ta zauna, ba dan ta ƙoshi ba sai dan idanun Dr Awwab da yake yawo a jikinta ya hanata sakewa, duk ɗago ido da za tayi sai ta kamasa yana kallonta, sai dai ya mata murmushi ba dai ya janye daga kallonta ba. Ko dan rigar jikinta ya kamata kuma yana bin jikinta ne.
Tv ta kunna ta ɗauki remote ta fara canza tasha, Dr Awwab daga can yana kallon duk abin da take amma baya samun damar ganinta fuskarta, dan kujeran da take zaune ya basa baya.
Tashi yayi ya nufi wajenta bayan ya ƙoshi, zama yayi saman ɗayan kujeran falon, ganin ya haka Nuratu tashi ta kwashe kayan saman dinning ɗin, sai da ta wanke tas dan kar su zama mata aiki ta fito ta koma falon ta zauna saman dogon kujera ta mai da hankalinta kan wayarta ganin Dr Awwab na wani kallon daban a Tv.
Daga inda yake ya tashi ya zauna gefenta. Duk Nuratu bata lura ba, domin hankalinta ya tafi kan wayarta tana duba saƙwannin da ba ta samu dubawa ba jiya zuwa yau, duk da ƙamshin turarenshi ya cika mata hanci ba ta kawo sunyi kusanci haka ba.
Ba ta ankara ta ji sauƙar kanshi saman cinyarta ya gyara kwanciyar shi ya kwanta. Idanu ta zaro tana kallonshi, ya kashe mata ido ɗaya tare da sakar mata murmushi da yake karɓar kyakkyawar fuskarsa, murmushin da yake haddasa Nuratu bugun zuciya da kasa jure ganin idanunsa.
"Kar ki ce komai."
Dr Awwab yace ya ci gaba da kallonshi a haka. Baki ta tura ta ƙira Mami yayin da ta kashe Data ta fita a manhajar WhatsApp.
"Mami na!"
Nuratu tace da ɗan ƙarfi bayan Mami ta amsa da sallama, ɓangaren Mami ta amsa da.
"Nuratu! Ya gida ya kowa da kowa."
"Lafiya ƙalau Mami, na yi kewarki sosai."
"Za ki saba. Ina Doctor? Fatan komai lafiya?"
A shagwaɓe Nuratu ta amsa da.
"Lafiya lau, duk nayi kewarku wallahi."
Dr Awwab yana jinta yana jin daɗin shagwaɓan da take zubawa Mami, ya lumshe idanuwanshi ya buɗe ya kai hannunshi saman cinyarta ya mintsina. Jin zafi ya rasata ya sakata sakin ƙaramin ƙara tana cire wayar a kunnenta.
"Me ye haka dan Allah, akwai zafi fa."
"Ki rage min shagwaɓan nima ki mini."
Harara ta watsa mishi ta maida wayar kunnenta ta ji Mami ta kashe ta kalleshi tana ajiye wayar.
"Ka ga ta kashe ko?
"Ta san kina tare da mijinki."
Yace ya miƙe zaune ya zauna daf da ita, ganin haka ta ja baya ya ƙara matsawa ya riƙota jikinshi. Idanuwanta ta runtse yayinda zuciyarta ya tsinke da ya haddasa mata rawar jiki. Ba abin da ya zo mata kai sai wahalar da ya bata shekaran jiya.
...
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE (Haske) 49.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Har ya gama bayaninsa yana sauraranshi tsaf, bayan ya gama ya sake dubanshi, kansa a ƙasa, numfashi ya sauƙe yace.
"Amma Mamman idonka babu kunya? Duk abin da ka aikata har zaka iya buɗe baki ka faɗi haka ko neman buƙatar haka daga gurinta."
"Yaya ka taya ni addu'a, sannan kai ma ina buƙatar taimakon ka."
Alhaji Mamman yace yana ƙara yin ƙasa da kansa.
Jinjina kai Alhaji Inuwa yayi yana cewa.
"Allah yasa ta amince. Amma a jikina nake jin babu nasara a wannan buƙatar ka."
Miƙewa tsaye Alhaji Mamman yayi yana cewa.
"Zan wuce Yaya a gaishe min da yarana. Zan yi latti."
Daga nan su kayi sallama Alhaji Mamman ya kama hanya, zuciyarshi fes yake ji domin ji yake buƙatarshi kamar ya biya. Burinsa na farko ya cika, saura wannan da yake fatan shima ya cika, kafin na gaba dan sai na biyun ya cika kafin na ukun.
***
"Mene ne hakan Docter?"
Nuratu tace tana ja baya tare da buɗe ido ɗaya tana kallon Dr Awwab. Shigar da ita jikinshi yayi sosai tare da riƙo fuskarta da hannunshi, ta runtse idanuwanta da ƙarfi. Sumbatar saman hancinta yayi yace.
"Inyi kissing ɗin bakinki?"
Girgiza kai tayi tana buɗe idanunta da sauri, mamakin rashin kunyar Dr Awwab take,kai tsaye yake faɗa mata abu babu maganar jin kunya. Shima girgiza kai yayi yana murmushi yace.
"Ko bakya so sai na yi."
"Ni dai a'a."
Tace har lokacin idanuwanta rufe, hakan yasa ya ɗaura yatsansa saman leɓɓenta ya fara zagayewa, taushi gare su. Bai mata magana ba sai jin sauƙar nashi leɓɓan tayi saman nata ya fara kissing ɗinta. Da kansa ya saketa domin Nuratu ta kasa hanashi.
Fuskarta ya riƙo har lokacin idanuwanta rufe yace.
"Buɗe idonki."
Ƙi tayi ta girgiza kai, jikinta na rawa. Ganin haka Dr Awwab yace.
"Shikenan bari in sake bai isheki ba."
Da sauri ta buɗe idanunta suka sauƙa cikin nashi da suka ƙara ƙanƙancewa da fitina, ya ɗaga mata gira tare da jifanta da murmushin da yake hanata kallon cikin idanuwanshi. Da sauri ta ɗauke kanta tana juyarwa gefe. Sakinta yayi yana murmushi. Tashi tayi da sauri ta shige kitchen dan nan tafi kusa da shi.
Jingina tayi jikin ƙofar kitchen ɗin tana lumshe idanuwanta tare da dafe kirjinta dake bugawa tamkar yanzu yake mata abubuwanshi.
Dr Awwab kan saka zuciyarta da kanta cikin wani shauƙi da nutsuwa duk lokacin da suka kasance tare, Yanzu kam jin abin da yake mata take har cikin kahon ranta, wani farin ciki na shiga kofofin jinin jikinta da zuciyarta. Murmushin da bata san daga ina yake ba ta yi, sai dai tasan zuciyarta na farin ciki. Jin maganarshi tayi da ya ankarar da ita, in da yake sanar da ita zai fita sai anyi sallah zai dawo.
Kanta ta saita kafin ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana. Tsaf ta gama haɗawa ta jera a saman dinning table tana wucewa ɗakinta, sallah tayi ta sauko ƙasa ta ɗauki wayarta ta ƙira Aunti Rahma da su Hasiya. Kowa dai in ya buɗe bakinsa cewa yake ta cire komai a ranta ta riƙe mijinta sannan taci gaba da gyara kanta, dan duk kwalliyar mace da kyau sai ta ƙara da wanka. Da to ta bisu ƙarshe ta ƙira Walida suka sha hiransu, Walida tana tsokanar ta kafin ta kashe ba tayi gigin ƙiran Ameera ba.
Haƙurin nan dai za tayisa dan ganin ribarsa. Babu shskka zuciyarta ya fara amincewa da Dr zai bata dukkan farin cikin da take tsoron rasawa. Wanka tayi ta zuba kwalliya cikin doguwar riga sai ƙamshi turare ke ta shi a jikinta.
***
"Wai ba za ki fito ki wuce ba, rana yayi fa."
"Gani nan Mama, turare na fesa."
Binta tace ta fito cikin doguwar abaya baƙi da ya amshi farin fatar jikinta, ta yane kanta sai ƙamshin turaren da ke cike da surkulle take. Binta farace kyakkyawa tamkar Nusaiba, banbanci su hali.
"Na tafi Mama."
Tace tana gyara zaman jakar mta da ke kafaɗarta.
"Kinyi kyau sosai, ki gaishe su."
Da to ta amsa ta fita, adaidaita ta ɗauki shata ya ɗauketa har ƙofar gidan ya ajiyeta, ta biyashi tana shiga ciki. Cike da farin cikin ganin motarshi yana nan ta gyara tafiyarta kafin ta ƙarasa babban falon gidan da sallama.Babu kowa a falon hakan ya sata wucewa sama falon Ummi tayi sallama aka amsa mata ta shiga.
...
Shigowar Dr Awwab kenan ya gaishe Ummi, ya sauƙa ƙasa ɗakinsu Hassana dan duba Hanan, tana ganinshi ta maƙale masa sai ta bishi gidansu wajen Aunti Noor.
"Gobe zan zo mu tafi My Love, ke da bakya son gidan."
"Ai wajen Aunti Noor zan je?"
Tace tana turɓune fuskarta cike da shagwaɓa.
"To gobe zan kai ki."
Ya faɗa yana jan kumatunta ya miƙe yana sumbatar kumatunta kafin ya fita tana ta turɓune fuska. Baya son zuwa su haɗu a gidan dan sai ya mata wayo yake tafiya. Bai shiga wajen Ummi ba ya fita dan sun riga sun yi sallama.
...
"Ummi ina Hanan? Ban ji motsinta ba."
Binta ta tambaya bayan sun gaisa da Ummi, kamar kullum da fara'a ta karɓeta, dan Ummi macece da ba'a ganin ɓacin ranta, kullum cikin fara'a sannan akwai dattako.
Yanzu ma murmushi tayi tace.
"Tana wajen su Hussaina, yanzu Awwab ma ya wuce ganinta."
"Allah sarki. Mama tace a miki ya gajiyan biki, bata samu zuwa ba."
"Ina amsawa sosai wallahi, kun wakilceta ai."
Ummi tace ko bayan rasuwar Nusaiba basu cika mu'amala ba sai yanzu da su da kansu suka dawo garesu.
Miƙewa Binta tayi tana ɗaukar jakarta tace.
"Ummi zan wuce zan leƙa Hanan daga nan."
"Nagode sosai ki gaishe da Mama, tsaya ina zuwa."
Miƙewa Ummi tayi ta shiga bedroom ta ɗauko dubu biyu kuɗin mashin ta bawa Binta, da ƙyar Binta ta karɓa. Daga haka ta mata sallama ta sauƙa fatan ta Allah yasa Dr Awwab yana ciki su haɗu. Da sallama ta tura ƙofar ɗakin ta shiga lokacin Hussaina ta fito tare da Hanan a bathroom ta mata wanka.
"Aunti Binta."
Hussaina tace da mamakin ganinta, dan Hassana bacci take tun bayan fitar Dr Awwab.
"My Baby zo gurin Auntin ki."
Binta ta ce idonta kan Hanan ko gaisuwar Hussaina bata amsa ba. Ganin haka itama ta watsar ta buɗe wardrobe dan ɗaukarwa Hanan kaya. Jin shuru da kuma Hanan ta matso