Follow us on social media
Showing 63001 words to 66000 words out of 148866 words
Chapter 22 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
baya so yawan canje-canje wajen aiki da yake samu ba zai iya yawo da iyalai ba. Rashin aurenshi da Nuratu ya riga ya amince cewa babu aure tsakaninsu sai dai wani ikon Allah. Ko kuma Alhaji Mamman ya janye kudirin shi na auren Mufid da Nuratu.
Ganin ƙiran lambar Nijar ya san daga Nuratu ne, ya sashi miƙewa tsaye.
"Umma zan wuce ku gama magana da su Baba."
"To yaushe za ka dawo? Kar fa ka tafi ka ƙi dawowa kamar kullum."
"Zan dawo Umma inshaAllah zuwa nan da wata ɗaya da kwanaki."
Yace ya ja akwatin shi ya fita a falon.
Driver ne ya kai shi airport, jirgi zai bi ya tafi, bayan ya sauƙe shi ya ƙira Nuratu da tana waje tana ta ya Nazifa aiki da duk yanda taso ta hanata taƙi. Jin ƙarar wayar ya sata miƙewa daga wanke wanke da take yi ta shiga ɗaki tana ɗauka.
"Col. Ina kwana? Na ƙira baka kusa, na isa lafiya ƙalau tun jiya da yamma."
"Ya hanya ƙanwata, to allahamdulillahi, kin same su lafiya?"
Ya faɗa ta ɓangaren shi yana taka matakalar hawa jirgi.
"Eh ya mutanen gida?"
"Lafiya ƙalau, nima ina hanyar komawa Ibadan."
"Allah ya kiyaye hanya, sai anjima aiki nake."
"To shikenan ki gaishe da mutanen gida in na dawo zan zo."
To ta amsa dashi ta kashe wayar ta fita taci gaba da aikinta.
***
Waya suke da Yayan marigayin mijin matarshi yana shaida masa akan zai shigo zuwa nan da kwana biyu dan tattauna wani magana.
Alhaji Mamman sauraron shi kawai yake har ya gama kamar yana son fahimtar mai yake shirin zuwa yi yace.
"Amma Alhaji da ka sanar da ni dalilin zuwan dan zan yi tafiya zuwa Gombe."
Alhaji Mamman yace dan son sanin dalilin shi kawai na zuwa.
"Laa ba wani abu bane, ƴar wajen tsohuwar matar ka Al'ameen yake neman aure, shine za mu zo muyi maganar."
Dama yaji hakan a ranshi in ba haka ba menene zai neme shi abinda bai taɓa faruwa tsakanin su ba.
Murmushi taƙaici yayi yace.
"Ita Nuratu ce ta turo shi bata sanar daku na mata miji ba. To aurenta saura sati bakwai ba sai kun zo ba Alhaji."
Da mamaki Baba yace.
"Ikon Allah wallahi bamu da labari ina tsammani ko shi Al-ameen ɗin bai sani ba."
"Ai yanzu kun sani."
Alhaji Mamman yace ya kashe wayarshi yana buga tsaki. Wannan yarinya na gaza mishi maganganu.
...
Ɓangaren Baba yaji wani iri sosai jin wacce Al'ameen yake nema an mata miji, da ma bai fita aiki ba ya leƙa ɗakin matar shi ya sanar da ita yadda su kayi da Alhaji Mamman ya ce ta sanar Al'ameen shima za suyi maganar da shi.
"Wallahi kamar ya san bama son auren nan."
Tace cikin farin ciki.
"Zan wuce aiki sai anjima."
Yace ya fita sai yaji gaba ɗaya bai ji daɗin haka ba ko dan yanda Al'ameen ya so aurenta duk da abin da ya faru da ita.
...
Bugun ƙofar gidan yayi ya ji shuru babu kowa ya shiga kai tsaye cikin falon gidan kamar yanda ya saba.
"Wai ke Sadiya wace irin ƴa kika haifa? Anya yarinyar nan jinina ce? Ko dai aljana ce ba mutum ba ce?"
Mami da ke zaune tana bin Alhaji Mamman da kallo yana wannan maganganun, huci yake kamar zaki da zai ci babu.
"Me kuma ta yi?"
Ta tambayeshi cikin jin zafin munanan kalamai da yake jifan Nuratu da shi.
"Wato yarinyar nan sai tayi ajalina ta haɗa ni da hawan jini na mutu ko? Wannan da gida ɗaya muke raye ashe da ta daɗe da kashe ni. Duk iskancinta bai tsaya anan ba sai ta turomin samarinta da suke hure mata kunne suna neman aurenta ko? To ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau, na matso da auren nan da kwana goma. Ko taƙi ko ta so sai ta auri Mufid domin shine dai-dai da ita."
Taƙaici da baƙin ciki ne suka cika zuciyar Mami ta girgiza kai, tabbas zai aikata abin da ya faɗa amma za tayi maganin shi, dan haka ta miƙe tana nufan ɗakinta.
"To mun ji Allah ya kaimu."
"Wato ina miki magana kin mai dani mahaukaci ko?"
Yace ganin Mami ta shiga ɗakinta. Bata kulashi ba hakan yasa ya sa kai ya fita yana surfa ruwan bala'i.
Jin ya fita ya saka Mami fitowa, mukullin motarta ta ɗauka da mayafinta ta fita, gidan Aunti Zarah ta nufa ta tare ta da fara'a, bayan sun zauna sun gaisa Mami ta sanar da ita komai dan ita ɗaya ta yarda da ita zata bata shawara mai kyau ta ƙara da cewa.
"Zarah. Gombe zan tafi in sanar da yayansa komai, in har ni yafi ƙarfina ai shi ba zai fi ƙarfin sa ba, ya ishe ni, ya cire mu a rayuwar shi tsawon shekaru, bai san cinta ba, bai san shan ta ba, tun da take bai taɓa sayo ko minti da sunan na Nuratu ba. Sai yanzu rana tsaka yace zai aura mata yaron da ya ɓata rayuwarta ya lalata ya kawar mata da dukkan farin cikinta."
Mami dake wannan bayanin ta share hawayenta da ta samu damar zubarsu yau dan zuciyarta ya karaya.
Ajiyar zuciya Aunti Zarah ta sauƙe tace.
"An ya ba wani abun Alhaji Kashim yayi wa Alhaji Mamman ba? Kina hasashen abin da nake yi."
"Duk nayi tunanin wannan Zarah, Alhaji Mamman zai aikata komai akan kuɗi tun da har ya guji jinin shi."
Jinjina kai Aunti Zarah tayi tace.
"Hakan nake tunani nima. Mafita ɗaya ki sanar da yayansa kafin lokaci ya ƙure in har ya kasa ɗaukar mataki sai mu jingina abin da kotu daga nan komai ya tonu. Ko kuma ita Nuratun ta fitar da miji a ɗaura aure balle lokaci ya ƙure mana."
Shuru Mami tayi tana sauƙe ajiyar zuciya.
"Shikenan Zarah hakan zan yi. Gobe zan tafi."
Sun jima suna maimaita zance har wajen la'asar kafin Mami ta mata sallama ta tafi. A daren ta shirya kayanta kala ɗaya na tafiya ta sanar da Munirat gobe za tayi tafiya.
Da safe karfe takwas ta kama hanya a motar kasuwa bayan ta tura Munirat gidan Aunti Zarah dan bata son su Aunti Rahma su sani sai abu yayi tsanani.
***
MAIDUGURI.
Dr Awwab bayan ya sauƙe gajiyar hanya ya huta, bacci yayi daren ranar sosai dan gajiyar tuƙi da yayi, bai taɓa tuƙi mai tsawo ba.
Da safe ya leƙa asibiti ko gida bai shiga ba, bayan ya gama abin da zai yi wajen la'asar ya bar asibitin ya nufi gida dan ganin sanyin idaniyar shi. Ai kuwa yana shiga falon ya sameta zaune ta baje takardunta na makaranta a dole ance suyi karatu za'a fara exam next week.
Tana kallon mahaifinta tayi watsi da takardun ta nufeshi ta.
"Daddy!"
Tace da ƙarfi bayan ya ɗagata sama ya cafke suna dariya ya nufi kujera da ita ya zauna tana zaune jikinshi.
"My Love Ina Ummi?"
"Tana sallah."
Tace tana ƙara shigewa jikinshi.
"Ke kin yi sallar?"
Ya tambayeta yana ɗagota ta ɗaga masa kai.
"Na yi da Aunti Husna tare."
Shuru ne ya biyo baya Hanan tace.
"Daddy za ka kai ni wajen Aunti Noor in munyi hutu in kwana mata."
"Kina son Aunti Noor? Nima ina sonta."
"Dagaske Daddy? To ta dawo gidanmu da zama dan Allah ka ga sai muna ganinta kullum."
Murmushi yayi ya shafa kanta.
"Ni ma zan so hakan My Love, in kunyi waya ki sanar da ita ko zata yarda."
"To ka ƙira min ita."
Tace cike da murna.
Wayarshi ya ɗauka ya lalibo lambar Nuratu da yayi saving da Noor da hoton heart a gaba, murmushi yayi sai kuma yayi tsaki tunawa da ya manta layin nan ba zai shiga ba kuma ya manta bai karɓi na Nijar ba.
"Menene Daddy?"
Hanan tace kamar zata fashe da kuka ganin ya ajiye wayar.
"My Love wannan number is not available, sorry zan ƙira miki ita wani lokaci."
Kuka ta saka mishi ya hau lallashi, fuskar nan duk hawaye Ummi ta sauko ta ƙarasa wajen.
"Meye faru?"
Ta tambaya cikin harshen fillanci.
"Rigima ce Ummi, wai na ƙira mata Noor kuma numbern ta is switch off."
"Zo nan Hanan, da kai na zan kai ki wajen Aunti Noor in kin gama exam."
Ummi tace ta ɗauketa, haka suka lallasheta ta mance ta koma kan takardunta.
"Ummi ina yaran nan?"
Yace yana maida kallonshi kan Ummi.
"Sun fita makaranta."
"Yunwa nake ji."
Yace ya miƙe yana isa table ya samu abin da zai iya ci yaci ya musu sallama ya tafi. Hanan na mishi bye bye ƙarfi da yaji taƙi binshi gida.
***
GOMBE.
Bayan Mami ta isa bata sha wani wahala ba dan bata mance unguwar da gidan ba dan sai canje-canje da aka samu sosai a garin.
Bayan ta sauƙa ta shiga ciki da sallama aka amsa mata, matar gidan ta tare da da mutumci da karamci suka shiga cikin falon, bayan gaisuwa tace.
"Sai dai kamar na gane fuskar, Hajiya Sadiya ko?"
"Hakane ni ce baki mance ba, shekaru dayawa."
"Wallahi dai tun abubuwan da suka faru."
"Eh wallahi ya kuma abin da ya faru? Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba. Lokacin bamu samu zuwa ba sai daga baya muka samu labari"
Da murmushi saman fuskar Mami tace.
"Babu komai, Allahamdulillahi. Wajen Alhaji na zo yana nan ma kuwa."
"Yanzu ya fita wallahi sai zuwa yamma zai dawo, sai dai in zaki jira shi."
Shuru Mami tayi kafin tace.
"Wallahi ina son komawa a yau in da zan samu."
"Kar ki damu in dai akan matsalar wajen kwana ne Hajiya Sadiya na gane nufin ki. An zama ɗaya fa, jini ya haɗa ko dan albarkacin yara ai an zama ƴan uwa. Ba dan Abban su Rahma ba ai da zumuncin yafi haka."
Hajiya Maimuna tace tana murmushi ta nunawa Mami har yanzu matsayinta na Hajiya Sadiya take a gurinta ko dan albarkacin yara ai an zama ɗaya.
Mami ta ji daɗin karamci da Hajiya Maimuna ta nuna mata, duk da ta girme mata amma matar ta nuna mata kamar ƙawarta ta ɗauketa, ta kaita har bedroom ɗinta tayi alwala ta rama sallolinta ta kawo mata abinci da ruwa.
Da rana yaranta sun dawo a makaranta suna ta binta da kallo dan yanayin kammani da suka gani na yan uwansu a fuskarta.
"Mamin su Aunti Rahma ne ƴaƴan Alhaji Mamman ƙanin Babanku."
Hajiya Maimuna tace musu ganin kallon kallo da suke yi bayan sun gaisheta.
"Haba naga kama wallahi, sak Aunti Rahma sai yanayin Nuratu da take dashi, shuru kawai nayi."
Ƙaramar ƴarta ta faɗa duk su kayi murmushi kuma hakanne banda Aunti Rahma babu mai kama da ita dan har tafi kama da ƴan uwanta na Nijar, sai Nuratu da ta ɗaukota kaɗan sai dai ita baƙace da sai ka kula za kaga kamar. Sauran duk mahaifinsu suke kama dashi sai farin fatar Mami da suka ɗauka.
Muhsin tun da ya tafi makaranta kusan shekaru huɗu bai ƙara dawowa ba sai waya da yake ƙiran Mami kullum, dan ma ya kusa gamawa burinshi ya zo yaga ƴan uwanshi su ganshi.
Daga nan hira ya barke tsakanin su suna tambayarta sauran har suna sanar da ita suna son zuwa Babansu baya barinsu.
Sai yamma lis Alhaji Inuwa ya dawo bayan ya ci abinci ya huta har bayan magriba kafin Hajiya Maimuna ta sanar da shi yana da baƙuwa.
Da mamaki yace.
"Sadiya da kanta kuma yau. Sanar da ita ta shigo."
Babu musu Hajiya Maimuna ta miƙe ta fita ta sanar da Mami suka dawo tare cikin hijabinta har ƙasa. Bayan sun gaisa yake tambayarta ya yara da yar wajenta.
"Duk lafiyar su ƙalau."
Ta amsa da shi a nutse ta sanar da shi abin da ke tafe da ita.
"Dan Allah Alhaji ka mishi magana ya janye maganar auren nan da yaron nan da Nuratu, yaron da ya lalata mata rayuwa ya cuceta yanzu kuma shine zai haɗa su aure in ba wani abun nashi daban ba. Albarkacin yara nake barinshi wallahi, bana so yayi rashin hankali in yi rashin hankali abin ba zai mana daɗi ba, in ba haka ba shari'a ce zata rabamu."
"Gaskiya bai kyauta ba, amma kiyi hakuri zan ƙira shi zuwa gobe a gabanki mu yi maganar in ya kama ma zan je can Damaturu in same shi. Kinyi tunani da kika zo baki biye mishi ba Sadiya."
Alhaji yace yana mamakin halin ƙaninshi da gaba ɗaya ya canza akan dukkan lamuransa tun ba yau ba, ba shekarun yanzu ba tun shekarun baya.
Godiya Mami ta mishi kafin ta koma ta barshi da Hajiya Maimuna.
....
MADUBIN GOBE 33.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Da safiyar ranar Alhamis bayan Alhaji Inuwa ya gama abin da zai yi kamar ƙarfe goma ya aika Hajiya Maimuna ƙiran Mami da ta shirya tana zaune da zaran sun gama magana ta koma.
Bayan sun isa ta gaishesa ya ɗauki waya ya ƙira ƙanin shi Alhaji Mamman da sai su yi wata ba su yi waya ba sai idan shi ya ƙira, gani yake ko dan ya fishi arziki.
Ya jima yana ƙara bai ɗauka har ya kusa tsinkewa kafin ya ɗauka da sallama. Bayan sun gaisa yake cewa.
"Mamman ina buƙatar mu yi wani magana in har kana da lokaci, maganar mai muhimmanci ne, da son samu ne ma zan shigo Damaturu amma abin gaggawa ne."
"Ina da shi Yaya Inuwa, ka sanar dani menene. Wani abun ya faru?"
Alhaji Mamman yace ta ɓangaren shi jin maganar yayan shi.
"Labari na ji ko in ce dagaske ne ka bayar da auren Nuratu ga wannan yaron Mufid?"
"Eh hakane babu maganar ƙarya."
Alhaji Mamman yace ranshi ya fara ɓaci jin maganar da ya zo masa dashi yana mamakin ina ya samu labari.
"Amma Mamman kana tsoron Allah? Kana tsoron ranar da Allah zai tuhume ka da haƙƙin yarinyar nan. Yanzu abin naka har ya kai ka ɗauki aurenta ka bada ba tare da izinin mahaifiyarta ba wacce tasha wahalarta tun haihuwarta har girmanta. Ina laifin a mutumin kirki ne tun da dole sai an zo wajen ka neman aurenta amma sai wancan banzan yaron."
Sai da ya gama sauraron shi har ya gama kafin yace.
"Kayi hakuri Yaya amma yarinya ƴata ce ko?"
"Eh ƴarka ce?"
"To kayi hakuri ka fita cikin maganar nan dan Allah ina ganin girman ka. Ita Sadiyar ta ƙira ta faɗa maka, to ka sanar da ita babu fashi domin aure tamkar an yi an gama. Sai anjima ka gaishe da yaran."
Daga haka ya kashe wayar shi cike da jin haushin Nuratu da Mami.
Jin ya kashe Alhaji Inuwa ya ajiye wayar cike da taƙaici.
"Kin ji mai ya faɗa Sadiya ko. Mamman ya canza, dama haka yake amma yanzu kwata kwata ya sake canzawa. Mutanen nan ba a banza suka barshi ba Sadiya. Kuyi magana da Nuratu ta turo yaron da take so zan samu Mamman za ayi abu ɗaya."
Mami da kanta ke ƙasa hawaye ya taru a idonta jin har lokacin Alhaji Mamman ya kasa janye kudurin shi ta ɗago kanta.
"Alhaji har yanzu babu aure a cikin ranta tun abin da ya faru, tana da wanda suke sonta, amma yanzu na san dole ta zaɓi ɗaya cikinsu."
"To ki sanar da ita ta turo ɗaya cikinsu wanda ya kwanta mata a rai, ni zan gama komai. Zan nunawa Mamman ina da iko a kanshi, ko shari'a ce shi zai wahala domin tauyewa yarinyar nan haƙƙinta."
"Ba ta nan tana Nijar wajen Yayana tsoron auren ya sa na tura ta can."
"Au to shikenan ki sanar da Yayanki ku yi magana ɗaya cikin gaggawa. Ku sanar da ni duk abin da kuka yanke."
"To nagode Alhaji."
Mami tace ta miƙe tana mishi godiya.
Bayan fitarta ya tura Hajiya Maimuna da dubu goma ta bata tayi kuɗin mota, da kyar ta karɓa, ta saka yaron su babba ya kaita tasha ta hau mota.
***
DAMATURU.
Bayan gama wayarsu Alhaji Mamman faɗa ya hau yi sosai cikin gidan Amma Jidda na bashi hakuri da bata san kan zancen ba har sai da ya sauƙo ta tambayeshi da ta gwanmace bata tambaya ba dan amsar da ya bata.
Dakyar ta samu bakin furta.
"Amma Alhaji baka kyauta ba, yanzu wannan yaron zaka bawa auren Nuratu ko duba da halin da ya jefata baka yi. Wannan yaron da babu tarbiyya a tattare da shi."
Amma Jidda tace cikin ɓacin rai da tsananin mamaki.
Ƙara haɗa rai Alhaji Mamman yayi.
"To sai me? Na ga dai shine dai-dai ita dama shi ya lalata abin shi, ko kina tunanin akwai wani wanda zai fito yace zai aureta a yanda taken nan."
"Akwai su da yawa, ko Al'ameen neman aurenta yake."
"Na riga na gama magana Jidda. Ina ganin mutumcin ki dan haka ki rufe bakin ki babu ruwanki cikin wannan maganar."
Miƙewa tsaye tayi cike da takaici bata mishi magana ba ta wuce ɗakinta, yaja tsaki ganin kowa yaƙi bashi goyon bayan auren Mufid da Nuratu. A yanda yake jin daɗin ƙarin girma da ya samu banda kuɗaɗe miliyan goma da Alhaji Kashim ya bashi bayan amincewar shi baya jin zai iya fasa auren nan, auren za'a yi sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Amma Jidda da ta shige ɗaki tausayin halin da Nuratu zata shiga take ciki, wani haushin Alhaji Mamman ya mamaye ta.
'Al-ameen fa?'
Zuciyarta ya tambaye ta da ya ɗauki aniyar ganin ya aureta in ya ji wannan labari bata san ya zai ji ba, yana son Nuratu tun ba yau ba har ƙaddara ta gifta a rayuwarta zuwa yanzu babu abin da ta canja.
***
Da karfe uku Mami ta shigo garin Damaturu gidan Aunti Zarah kai tsaye ta nufa, bayan ta huta taci abinci tayi sallah ta sanar da ita yanda su kayi da Alhaji Inuwa.
Bayan ta gama sauraronta cikin haushi tace.
"Ki sanar da Yaya Muhammadu kawai ya aurar da ita ga duk wanda ya masa, na san dai ko ba komai za tafi jin daɗi da shi akan Mufid. Domin Alhaji Mamman ba zai taɓa fasa abinda ya yi niya ba ko da shari'a zata hana, balle ma babu lokacin kai ƙara. Ina ma zamu iya shari'a da su Sadiya, kuɗi za su zuba yayi aiki, mu zamu sha wahala."
Mami idonta cike da kwalla tace.
"Ni ko Al'ameen da ya shirya zan tura shi wajen Alhaji Inuwa ayi auren, amma abubuwan gaba ɗaya sun kwaɓe har na rasa tunanin mai zan yi. Bana son Nuratu ta auri yaron nan, wahala kawai za tasha."
"Kin sanar da Amma Jidda ne?"
Aunti Zarah tace.
Girgiza kai Mami tayi.
"A'a ba mu yi maganar ba, ko su Rahma babu wanda ya sani."
Shuru ɗakin ya ɗauka kowa ya rasa tunanin da zai yi dan ɓullowa lamarin kusan mintuna goma Mami ta miƙe.
"Bari in je gida zuwa nan da kwana biyu inshaAllah zamu samu mafita, zan yi waya da ita Nuratun da Kawun ta mu yi magana."
"To shikenan ki kwantar da hankalin ki Allah yana tare da ku."
Aunti Zarah tace ta miƙe ta mata rakiya har waje tare da Munirat