Follow us on social media
Showing 117001 words to 120000 words out of 148866 words
Chapter 40 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
masa ya fita ya wuce ciki. Kiɗane ya ke tashi a gurin, ƴan mata da samari sun cika gurin sai rawa suke yi. Wasu kuma a zaune suna shan drinks da ya ke cike da kayan maye, da alama birthday party ake yi, domin duk an cika gurin da kayan kwalliya da balloons, kuma kowanne ƙananan kayane a jikinsa.
Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya ƙarasa ciki yana raba idon inda zai hango ɗiyarsa. Ganinsa fa hankalin mutane ya fara yin kansa. Wasun ma zaton ko mahaifin uwar gayyarce.
"Kai old me ye haka? Me ka ke yi anan?"
Faɗin wani saurayi da yake gefen Alhaji Mamman shigowarsa kenan.
Kallon saurayin ya yi da ƙyar ya furta.
"Ameera nake nema. Zainab Mamman Bashir."
"Oh kai ne Daddynta. Ga ta can."
Idanuwansa ya kai gurin inda yayi arba da mummunan gani, ƴarsa ce tsakiyar maza tana tikar rawa, tare da wani namiji da ya ke tayata sai shafa jikinta ya ke.
Jirine ya kwashesa kafin ya kai ƙasa ya dafe kujerar gurin, kusan mintuna biyu ya samu ya dawo daidai yana nufar gurin, yana isa cikin zafin nama ya fizgota tare da kwasheta da mari tagwaye. Duk da cikin maye take ta ji marin ya shigeta sosai, ta ɗago kanta da idanuwanta da suka canza launi.
"Abba!"
Ta faɗa da karfi cike da mamaki da tsoro.
Bai iya bata amsa ba sai wani marin da ya kai mata kafin ya hau dukanta tamkar an aikosa. Duk ihu da ake ya rabu da ita kasawa yayi har sai da samarin gurin suka rirriƙesa, tuni Ameera ta sume don ta bugu. Ko ta kanta bai bi ba ya fizge jikinsa ya fita. Cikin sauri samarin suka ɗagota suka fita da ita. Gaba ɗaya sun fahimci mahaifintane
Amma Jidda da ta ga fitowarsa ta fito da sauri.
"Tana ina?"
"Tana ciki."
Ya faɗa yana shiga motarsa. Za ta yi magana ta ga an fito da ita, da sauri ta ƙarasa gurinsu.
"Me ya sameta?"
"Ku sakata a baya."
Alhaji Mamman yace daga cikin motar, bai bari sun bawa Amma Jidda amsa ba, babu musu suka sakata suna matsawa. Da sauri Amma Jidda ta shiga ya kunna motar sai asibiti.
"Dan Allah Abbansu Rahma ka sanar dani me ya sameta."
Amma Jidda tace cike da tashin hankali, fatanta ya sanar da ita ba abin da ta ke zargi bane.
"Bani da lokacin wannan maganar Jidda."
Yace daidai sun isa asibitin. Karɓanta aka yi sai emergency, suka tambaya me ya sameta.
"A buge take, tasha wani abu."
Alhaji Mamman ya faɗa.
Likitane ya dubata ya mata alluran barci da kuma karya garkuwar abin da tasha. Tun lokacin barci take sai yau da ta farka.
...
Shigowar likita Amma Jidda ta fita ta basa guri. Duba Ameera yayi yace.
"Akwai inda ya ke miki ciwo?"
Murya can ƙasa tace.
"Kai na da jikina."
"How old are you?"
"19 years."
Ta basa amsa tana dafe kanta da ya ke ciwo sosai. Kan ya riƙe mata ya ji bugawarsa kafin ya sa ke.
"Me ya kai ki aikata haka? Ba ƙya tsoron lafiyarki ko iyayenki su shiga wani hali. Da ƙarancin shekarunki."
Bata masa magana ba ta lumshe idanuwanta, ya girgiza kai ya fita. Burinta kawai Abba da Amma suyi ƙoƙarin fahimtarta, bata da wani kalma da za ta faɗa ta ƙare kanta. Duk hukuncin da suka yanke mata za ta ɗauka.
Buɗe ƙofar ya sa ta kai kallonta ƙofa. Amma ne ta shigo ranta a haɗe, fuskarta a kumbure alamar tayi kuka.
"Amma zan rama sallolina."
Ta faɗa kamar me tsoro, dama a tsorace take.
Bata kulata ba ta fara harhaɗa kayansu. Bayan ta gama ta nufi ƙofar fita.
"Fito mu tafi gida."
Idanuwanta cike taf da hawaye ta sauƙo daga gadon da ƙyar, hijabinta da ta gani a gefe da bata san yaushe ya zo ba, ta ɗauka ta saka ta fita. Da ƙyar ta ke jan jikinta, dan ciwon da ya ke mata ga ciwon kai. A taxi suka koma gida dan tuni Alhaji Mamman ya bar asibitin tun farkawarta.
Suna isa gidan ta shige ɗakinta, ruwa mai zafi ta haɗa tayi wanka ta ɗauro alwala kafin ta fito ta gabatar da sallolinta ta zauna a ɗaki. Yunwa ta ke ji ga ciwon kai amma haka ta zauna ta hau kuka.
Buɗe kofar ɗakinta ya sata share hawayenta ta kalli ƙofar.
"Ki fito kici abinci ki sha magani."
To tace cikin sanyi ta tashi ta fita, babu kowa falon, ta isa dinning ta zuba abinci ta ci, ta ɗauki maganin da ta gani saman table ta sha ta wuce ɗakinta. Har dare babu wanda ya bi ta kanta, sai ta ƙara jin tsanar kanta. Haka ta zauna har daren.
Ƙarfe takwas aka buɗe ƙofar ta kai kallonta gurin. Abbansu ta gani tsaye bakin ƙofar. A zabure ta miƙe zaune cikin rawar jiki. Shigowa yayi ya rufe ƙofar ɗakin da key, ta ke ta ji zuciyarta ya buga, idanunta ya cika da hawaye.
Takowa yayi ya tsaya saman kanta.
"Abba don Allah kayi hakuri."
Ta samu bakinta da furta haka cikin rawar murya.
"Rufemin baki."
Yace yana kaiwa bakinta bugu, da ƙarfi ta fasa ihu dan zafi. Dukan fitar hankali Abba ya yi wa Ameera da bulalar iccen maina, tana ihu tana kuka tare da ƙiran sunan Amma bai ƙyaleta ba. Amma tana ji ta kasa zuwa kwatarta, domin tasan ita ta jawowa kanta. Sai da ya ga ta daina motsi kafin ya haureta da ƙafa.
"Ki faɗamin uban me ya kai ki hotel."
Da ƙyar muryarta ya ke fita tace.
"Abba ƙawatace ta gayyace ni birthday party. Wallahi ban taɓa zuwa hotel ba, ban taɓa shan wani abun ba, ban san sun saka abin maye ba nasha."
"To babu ke babu fita, makarantar ma na kashe zuwansa, aure zan miki nan da wata biyu."
Ba ta ce komai ba sai kuka da take yi cike da nadama. Fita yayi ya barta warwas.
Side ɗinsa ya nufa ya kulle kansa a daki.
'Hotel kaɗai taje ita ta kai kanta amma na shiga tashin hankali. Nuratu fa da aka yiwa fyaɗe ba tare da son ranta ba. Ya Sadiya ta ji? Wani irin tashin hankali ta shiga? Wani irin rayuwa ta yi? Ita Nuratun fa."
Maganganun da Alhaji Mamman ya ke faɗa a zuciyarsa cike da nadaman abin da ya aikatawa Sadiya da Nuratu. Wani mugun tausayin ƴarsan ya lulluɓesa.
Bai iya runtsawa ba har karfe biyun dare, kafin wani barci ya ɗaukesa. Ƙarfe shidan safe ya bar gidan dan tafiya da zai yi cikin gaggawa. Ko takan Amma Jidda bai yi ba, dan ita ma da laifinta a fitar yarinyar.
***
Da gudu Nuratu ta ƙwace bakinta a gurin Awwab ganin Hanan ta nufo wajen. Yana ƙoƙarin magana ta wuce kitchen da sauri ta shiga tana dariya dan nan tafi kusa da shi. Har zai bi ya kamota ta masa bayanin hakan ya ji muryar Hanan. Turus yayi ya tsaya yana mata wani kallo. Tsorone ya kamata ta fara matse hawayen.
"Zo nan."
Yace da ita yana harararta. Haɗiye kukanta tayi ta isa wajen tana ƙoƙarin durƙusawa ya riƙota. Kuka ta saka masa.
"Yimin shuru."
Yace da ita yana zaunarta saman kujeran dinning ɗin. Jin kukan Hanan ya saka Nuratu fitowa da sauri. Dariyarta ta kunshe ganin itama ta samu tsarabar harara. Zama ta yi ta ɗaura Hanan saman cinyarta.
"Yi shuru My Love."
Tace tana sharewa mata hawayenta.
"Za ki ci abinci?"
Kai ɗaga mata, haka yasata sauƙarta ta miƙe ta zuba mata ta koma ta zauna. A baki ta dinga bata har ta ƙoshi suka koma falon suka bar Awwab zaune ya cika yayi fam. Hira suke yi suna kallo abunsu.
Hanan tana yin barci ƙarfe goma ta ɗauketa suka wuce ɗakin Nuratu. Kwantarta tayi ita ma ta yi shirin bacci ta hau gadon. Miƙewa tayi dan ɗauko ruwa dan kar ko Hanan za ta nema cikin dare.
Cikin tafiyarta mai ɗaukan hankali ta sauƙo. Har lokacin yana zaune a saman dinning, sai lokacin ya samu damar cin abinci shima tea ya haɗa. Yana sha yana aiki a laptop ɗinsa.
Jin motsi ya sa shi kai duba wajen ya ga Nuratu ne.
Kai tsaye dinning ta nufa, gorar ruwan da ba'a buɗe ba ta ɗauka bata masa magana ba. Za ta bar gurin taji maganarsa.
"Za kiyi bayani yarinya. Ki jira zuwana."
Da murmushinta ta juya ta masa wani kallo tana juya idanuwanta.
"Za mu yi bayani tare ni da kai."
Daga haka ta ci gaba da tafiya tana danne dariyarta dan tuna muguntar da ta shirya masa. Galala Dr Awwab ya bita da kallo cike da mamakinta. Wani yanayi ya ke jin kansa, da ƙyar ya ci gaba da aikinsa.
Shuru shuru ba su dawo ba ya saka Dr Awwab kashe Tv da wutan falon ya hau sama. Ɗakinsa ya wuce ya yi shirin barci ya nufi ɗakin Nuratu.
Turus yayi ya tsaya ganinsu su biyun kwance suna barci. Ƙaramin tsaki yaja ya isa bakin gadon ya janye Hanan gefe, Nuratu tana jin shi tayi luf kamar me bacci. Hannunshi ta ji a jikinta ya gyara mata kwanciya ya maidata tsakiyar gadon kafin ya hau gefenta ya kwanta.
"Na san idonki biyu Babyna. Me yasa ki ka min haka bayan ga ɗakinta can."
Murmushi Nuratu tayi tana gyara kwanciyarta jikinshi ta ƙi magana. Hakan yasa yayi ƙasa da murya a kunnenta ya raɗa mata.
"Mu je ɗakina please. Ina son muyi bayani ni da ke, kamar yadda ki ka ce."
Nan ma shuru tayi ya fara ƙoƙarin tashi ta riƙesa.
"Am not clean."
Komawa yayi ya kwanta ya ce.
"What! When kuma hakan ya faru."
"Ɗazu da yamma."
"Dama lokacinshi ya yi? Kuma ki ka sakamin rai."
Kai ta ɗaga mishi, ajiyar zuciya ya sauƙe yana ƙara ƙarfin rumgumeta kamar ba zai ce komai ba can yace.
"Kwana nawa ya ke yi?"
"Kwana biyar."
Daga nan bai ƙara magana ya karanto addu'a har barci ya ɗaukesu.
Da asuban bai tasheta sallah ba ya wuce masallaci. Da ya dawo ya koma ya kwanta. Ƙarfe shida Nuratu ta farka ta haɗa musu breakfast kafin ta tashi Hanan ta mata wanka ta shiryata, ƙarfe takwas saura suka bar gidan ta ci gaba da aikinta.
***
Har ya kwana washegarin da safe yana shirin tafiya ya kasa faɗan meke tafe tashi. Ganin zai yi asaran zuwa babu cikar buri ya sa shi yin ta maza ya sanar da Kawu Muhammadu abin da yake da buƙata.
Murmushin taƙaici ya yi. Tun zuwansan daman yasan ba abin ƙirƙi ya kawosa ba. Yana dubansa kansa ƙasa tamkar mutumin ƙirƙi ya ce.
"Amma Mamman ba ka da ta ido. Kai ko kunya ba ka ji."
"Kawu ba haka bane. Ni dai dan Allah ka saka baki ko za ta amince."
"Ba zan yi ba, ka je ka sameta, idan ta amince to idan ta ƙi shikenan. Ba zan mata dole ba, Sadiya tana da damar zaɓawa kanta abin da ya dace da ita."
Ajiyar zuciya Alhaji Mamman ya sauƙe.
"Shikenan Kawu na gode sosai da karamci."
Daga haka ya musu sallama ya fita. Da kallo Kawu Muhammadu ya bisa. Har cikin ransa ya ji daɗin batun da Alhaji Mamman ya zo da shi, amma yana son sai ya garu ya gane laifinsa kafin Sadiya ta yarda, balle ma yana jin da wuya ta amince.
Ƙarfe biyu da wani abu ya shigo gidan, bai shiga falon Amma Jidda ba ya wuce side ɗinsa. Dirin motarsa ya sa ka Amma Jidda leƙa wajen ta hango motar, fita ta yi ta nufi side ɗinsa. Sallah ta samu yana yi ta zauna ya idar.
"Sannu da zuwa."
"Yawwa ya gida?"
Ya amsa mata.
"Lafiya lau, Ya hanya? In kawo maka maka abinci?"
Kai kawai ya ɗaga mata, ta fita ta kawo masa ta zuba masa ya hau ci. Sai da ta ga ya ci ya ƙoshi ta fara masa magana.
"Don Allah Abbansu kayi hakuri, kar fushin Ameera ya shafeni, ban san duk tana aikata hakan ba, ko ta fita ba."
Kai ya girgiza mata.
"Ya wuce, ki sa mata ido sosai kawai, maganar makaranta na hana. Aure zan mata."
"Hakan ma yayi."
Tace ko ba komai hukuncin da ya ɗauka dai-dai ne da ita, kuma taji daɗin ya sauƙo daga fushin da ya mata dalilinta.
...
Mami ta kwantar da hankalinta ganin Alhaji Mamman bai ƙara dawo mata da maganar ba. Kasuwancinta ta mayar kai sosai, ƙoƙarin buɗe shago take ta zuba kaya ta saka ma'aikata. Kullum sai tayi waya da ƴaranta, ba ta faɗa musu komai ba.
Muhsin yana zuwa mata akai akai dan aikin da ya fara baya samun zama sosai.
***
Washegarin juma'a ƙarfe sha biyu ƴaran Mami suka halarci ƙira da mahaifinsu ya musu. Alhaji Mamman bai dawo gidan ba sai bayan sallar juma'a. Tun a farfajiyar gidan ya fara cin karo da jikokinsa, murmushi yayi ya fita ya ɗauki wannan ya sauƙe yana jin daɗi.
'Me yafi haka daɗi. Sadiya ta ga jikokinmu sun cika mana gida."
Yace a ranshi yana shigan falon Amma Jidda ya samu duk suna falon, Aunti Rahma, Hasiya, Rukayya da Muhsin, hatta Ameera tana rakuɓe a cikinsu, babu Walida da take laulayi.
"Sannu da zuwa Abba."
Suka faɗa suna gaishesa ya amsa ya miƙe.
"Ku same ni a falonal."
Daga haka ya fita kusan mintuna goma su ka bi bayansa. Zama su kayi gaba ɗayansu ba ƙasa. Bayan sabuwar gaisuwa ya dubi yaransan da suke sauraronsa ya ce.
"Ina son mayar da Maminku, sai dai duk yanda zan yi ta ƙi yarda. Taimakonku nake nema, ina son mu koma tamkar daa tamkar babu abin da ya faru, mu mayar da aurenmu."
"Aure dai Abba!"
Aunti Hasiya tace da mamaki, ita kaɗai ta samu damar magana duk cikin falon. Kai ya ɗaga mata.
"Eh in Allah ya yarda. Ku ce wani abun kunyi shuru."
"Ni kam na amince Allah yasa hakan shine alheri."
Faɗin Rukayya harda guntun hawayenta.
"Nima haka Abba."
Aunti Rahma tace cikin sanyin jiki ita kuma.
Dama yasan ita za ta yarda akan Hasiya.
"Ke fa Hasiya?"
Ya tambayeta.
Murmushi ta yi.
"Abba ni kuma me zance, idan har Mami ta yarda babu yanda muka iya, amma in ta ƙi fa babu dole."
"Nima bazan mata dole ba, so nake ku nemo min yardarta kawai. Ko albarkacinku za ta hakura ta amince."
Shuru kowa yayi bayan sun amince. Muhsin sai danne danne yake a wayarsa yana jinsu. Yaji daɗin hakan domin haƙiƙa baya jin daɗin zaman Mami ita ɗaya kuma babu aure. Yasan ko ya ya ana maganarta ko da baya isosu.
"Baban Mami ba ka ce komai ba."
Yaji maganar Abbansu, murmushi ya yi ya ce.
"InshaAllah Abba za ta amince."
Cikin farin cikin da ya kwana biyu bai ji ba yana dubansu ya ce.
"To na gode muku, Allah ya gode albarka. Duk yadda ku ka yi da ita ku sanar da ni Please."
Da ameen suka amsa ya sallamesu suka koma, har ƙarfe biyar suna gidan, kafin kowacce ta fara shirin tafiya gidanta.
***
Mufid Kashim Mufid.
Rayuwa ya ke tsakanin rai ko mutuwa, damin magani shine cikon rayuwarsa. Sosai tsoron Allah ya shigesa, don ya ga ishara tun a duniya. A yau suka wayi garin da samun labarin rasuwar AA, hakan shi ƙara saka tsoron Allah a zuciyar Mufid. Kansa ya kulle a ɗaki yayi kuka ya yi ta roƙon gafarar Allah. Da ƙyar ya samu zuwa jana'izar AA ya dawo gidansu da babu komai, kowa ta kansa yake.
Alhaji Kashim kusan sati biyu da ya wuce aka basa dogon letter na koransa da a ka yi a aiki, bisa kuɗaɗen da ya ɓatar tsawon shekaru cikin rashin sani, aka nemi dalili ya rasa hujjar kare kansa.
Ranar ƙaramin hauka ya yi. Babu kuɗi babu aiki babu sana'a, dan ya dogara da aikin gwamnati da yake satan kuɗaɗen ciki, bai taɓa sha'awar kama sana'a ba.
Hajiya Hindatu zama kawai take da shi dan babu inda za ta je, Hajiya Batula daga wajen iyayenta take samun taimako tana kula da ƴaranta. Yanzu ma shirin aurar da su biyun ta ke.
Ƴaran Alhaji Kashim Mufid masu aure duk sun ji babu daɗin abin da ya samu ubansu, duk sun zo masa jaje tare da taimako daga wajen mazajensu, mijin Rufaida har gida ya zo masa tare da ita da ƴarta ɗaya sai ciki da ta ke fama da shi.
Burin Mufid yanzu ya samu aikin yi, ya dogara da kansa dan ci da shansa da kuma magungunansa, dan idan Alhaji Mamman ya basa kuɗin sai yasha gori. Dukka ya sayar kadaransa ya saya mai yawa kusan na rabin shekara da zai masa amfani.
Abincin kirki basa ci a gidan, balle maganar karatu, hakan yasa ya bazama neman aiki.
Ya zama tamkar ba Mufid ɗan gayu da kwalliya ba, ya zama wani shuru shuru duk ya rame sai haske. Shaye shaye kuwa da bin mata rabonsa da hakan har ya manta. Ko ido ba ya iya ɗagawa ya kalli mace, balle ta basa sha'awa.
...
#vote
#comments
#share
MADUBIN GOBE 55.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Yau weekend (hutun ƙarshen mako), ko wani mahluki ma'aikacin gomnati shi ne ranar hutunsa. Garin babu sanyi kasancewar zafi ya fara gabatowa. Ga sabin aure kuwa wannan ranar ya musu daɗi don ya basu damar kasancewa da juna. Haka ga Dr Awwab da Nuratu ma da suke rama barcinsu, duk da Nuratu ta so farkawar wuri dan Hanan amma ya hanata ya nuna mata sai ƙarfe tara za ta tafi islamiyya, ita ma barci ta ke.
Haka ta biye masa har ƙarfe takwas da mintuna sannan ta lallaɓa ta zare jikinta ta maye masa gurbin da filo ta fita.
Kitchen ta wuce ta dafa mata abu mafi sauƙin dahuwa ta fito, ɗakinta ta nufa ta samu yarinyar ta farka tana zaune saman gadonta.
"Sorry My Baby love. Mu je in miki wanka."
Babu musu ta miƙe tana gaishe Nuratu, ta amsa tana murmushi tarbiyyar yarinyar yana burgeta, kayanta ta cire mata su ka wuce bathroom. Tsaf ta shiryata cikin uniform ɗin islamiyya, kafin su fito. Saman dinning ta ajiyeta ta wuce Kitchen ta ɗauko mata breakfast ta fara, sannan ta wuce dan tashin Awwab.
Ɗaure da rigar wanka ta samesa tsaye gaban mirror yana shafa mai, jin motsi ya sa shi juyawa. Ganin Nuratu ya sake mata murmushi, ita kuwa ganinsa haka ya sa ta juyawa tana faɗin.
"Hanan ta shirya kar tayi latti."
Girgiza kai kawai yayi yana taɓe baki yana mamakinta. Ko me kuma na wani munafurcin kunya, wani darene jemage bai gani ba.
Shirinsa ya yi kamar kullum cikin ƙananan kaya sai ƙamshin turare yake. Bayan ya gama ya sauƙo ya samu Hanan ta gama suka fita yana amsa gaisuwarta.
Nuratu na su breakfast ɗin ta haɗa musu, bayan ta gama ta hau gyaran gidan, tsaf ta gama kamar kullum ta shiga wanka, tana wanka Awwab ya dawo. Ganin ba ta falon ya sa shi hawa sama, ɗakinta ya nufa nan ma shuru, motsin ruwa da ya ji ya sa shi zama yana zaro