Follow us on social media

Showing 30001 words to 33000 words out of 148866 words

Chapter 11 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

49

ɗaukan wasu bayanai da za'a rasa ba."

Col. Ahmad ya yarda da zancen DPO Salisu da kafin yayi magana ya sanar dashi haka. Anan ya amince DPO ya rubuta takardan yarjejeniya su kayi signing. A take DPO Salisu ya saka aka fito da su Mufid da Faisal a gaban Col. Ahmad.
Kallon kallo Mufid da Col. Ahmad su kayi kafin Mufid yayi wani yunƙurin Col. Ahmad ya ciro bindiga Piston cikin coat ɗinshi ya saita Mufid dashi.

Mutuwar tsaye mutanen gurin su kayi hatta Mufid ɗin duk iskancin shi yana tsoron harbi da mutuwa.

"Dan Allah kar ka kashe sa."
Cewar Alhaji Kashim cikin rikicewa.

"Calm down Sir, kar ka aikata abinda za kayi dana sani."
DPO Salisu ya faɗawa Col. Ahmad.

Bai kulasu ba ya saita Mufid dashi tare da sakin harsashi, dukkansu suka fasa ihu zatonsu duk ya harbeshi su ka ga ya harbi ginin gefenshi.

"Sai haɗuwa ta biyu."
Daga haka Col. Ahmad yasa kai ya fita yana mayar da bindigarshi riga ya wuce asibiti.

Daga nan Alhaji Kashim ya ɗauki Mufid suka koma gida bayan ya cika Barrister Auwal da kuɗi in da ya mishi alƙawarin case yasha ruwan kanwa tunda dai har Mufid ya fito, zai san yadda za suyi ta kaucewa case ɗin har a hakura dashi.

....

Col. Ahmad yana kan hanyar shi ta isa asibiti ya samu ƙiran Umma tana tambayarshi yana ina.

'Ina zuwa.'
kawai ya sanar da ita ya kashe wayar. Asibitin ya isa ya sanar da Dr Sadiq cikin kwana biyu ba zai samu zuwa ba, sannan an ɗaga case har sai Nuratu ta samu lafiya, kafin ya bashi card ɗinshi ko wani abu zai taso.

Ɗakin da Nuratu take ya shiga ya samu Mami zaune sai su Rahma, Rukayya da Walida a ɗakin tare da Amma Jidda ba'a sanar Muhsin ba dan yana makaranta. Aunti Zarah da Munirat suna gida dan haɗa musu abincin rana.
Ɗakin tamkar wanda aka yi mutuwa shuru, har lokacin Rahma ta kasa saida hawayenta, tayi kukan tayi ta kasa daina yi.
Rukayya da Walida in ka gansu suma fuskar nan a kumbure alamar sunyi kukan sun gaji, Mami Kam ta zama tamkar mutum mutumi. Hasiya na emergency dan tana samun labarin jini ya ɓalle mata da ya jawo sanadin zubar cikin jikinta na wata uku.

Nuratu na kwance tun safe da ta musu haukarta aka ɗirka mata alluran bacci ta koma, Mami ne ta goggoge mata jikinta da ruwan zafi ta gasa mata hannunta, anan ta dubata in da ta ƙara shiga tashin hankali dan har ɗinki aka mata kuma tana buƙatar shiga ruwan zafi. Tana kuka tana yi Rahma da Rukayya suka shigo daga baya Amma Jidda da Walida suka shigo.
Anan Mami ta sanar da ita tana buƙatan shiga ruwan zafi suka samu Dr Sadiq yace a yanda take haukan nan in za'a samu masu riƙeta sai a shigarta ciki a riƙeta. A haka suka bari akan in ta farka zasu haɗa karfi da ƙarfi su sakata ko dan samun lafiyarta.

Mami da kowa na ɗakin bin Col. Ahmad da kallo su ka yi, ya tsaya kusa da gadon yana gaishe Mami da sauran suka amsa yana tambayar mai jiki suka ce da sauƙi bai iya sanar dasu shi waye ba ya fita.

Bayan fitar shi Amma Jidda tace.
"Kun san shi?"

"A'a ko ɗaya."
Kowa yace hakan sai kowa yayi shuru su kaci gaba da zaman su haka kusan mintuna goma Amma Jidda ta miƙe.

"Bari in dubo Hasiya, tashi muje Rukayya."

Ba musu ta miƙe suka fita tare suka dubo Hasiya ta farka sai kuka take mijinta yana lallashi. Suma lallashinta su ka yi tace sam zata bisu ta duba Nuratu, Dr ya hanata aka mata alluran baccin ita ma.

Da ƙarfe taran dare bayan sunci abinci wanda suka iya ci, Mami tace su koma gidajensu in yaso gobe su dawo. Basu so ba suka tafi aka bar Mami da Munirat, Hasiya aka bar mata Walida a wajenta.

***

Wanka yayi bayan yaci abincin da Ummu ta girka masa ya shige ɗakinsa ya banka sigari kusan biyar dan ya jima basu haɗu ba. Babu sallah balle azkhar ya mingire da bacci a kan gadonshi da ya jima bai samu ba cikin kwana biyun.
Sai biyar ya farka ya fito falon gidan ya samu ƙannen shi sun shigo wajen Rufaida. Da kallo ya bi Rufaida ta watsa mishi harara tana jan tsaki suka bar gurin suka wuce sashin Hajiya Batula.

Yana zaune har karfe taran dare kafin Rufaida ta dawo ta ɗauka duk ya fita, tana ganin shi ta nufi hanyar ɗakinta ya tashi ya biyo bayanta da sauri. Tana ganin haka ta saka key a ƙofar ɗakin.

"Iskanci ka bai ƙare ba har sai ka dawo kai na? Anya Mufid kana tsoron haɗuwar ka da Allah?"

"Ina tsoro mana. Kin san dai duk iskancin na bazan iya haura miki ba tsorata ki nake. So nake mu gaisa kwana biyu kowa yayi kewata banda ke uwar rashin kunya."

Tsaki ta buga har yana ji.
"Allah dai wadaran naka ya lalace. A rayuwar ka burinka ka cuci yaran mutane, to wallahi ka sani akwai ranar kin dillacin da za kazo ka zubar da hawaye kana neman gafarar su suƙi yafe maka, banda na Ubangijinka da bani da tantama sai ya hukunta ka. Sanadina ka cuci rayuwar Nuratu Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya saka mata tun a duniya na faɗa na sake faɗa, mugu azzalumi."

Daga haka Rufaida ta fashe da kuka zuciyarta ya raunana tuna halin da Nuratu take ciki, ta kasa zuwa dubata gani take tamkar da ita aka shafawa rayuwarta baƙin fenti.

Mufid da ya gama sauraronta ya wuce ɗakin shi, duk zagin data mishi bai ji komai ba domin shi yaga Nuratu yaji yana sonta tun a wajen dinner abokinsa mijin Rukayya. Ya nuna mata yana sonta taƙi ji tana da wanda zata aura dole yasa ya mata haka. Kuma har yanzu yana sonta in har za'a hukuntashi a kanta zata aure shi ya yarda zai amince a mishi hukunci ya aureta.

....

"Ɗan gidan uban waye ya aikata mata haka?"

Amma Jidda dake zaune bayan Alhaji Mamman ya sata gaba da tambayar ina taje tun safe da yara ya dawo basa nan ya ƙira bata ɗauka ba ta sanar dashi halin da Nuratu take ciki bai gane wacece ba sai da ta sanar dashi ƴarshi ta wajen Hajiya Sadiya da ya mance da ita a rayuwar shi. Tayi mamakin jin abin da ya faɗa sai kuma ya hau kame kame.

"Waye shi? Waye uban shi?"

"Ɗan gidan Alhaji Kashim Mufid."

"Allah rufa asiri."
Kawai yace ya mike ya shige ɗakinsa Amma Jidda ta bishi da kallon mamaki.

***

Ƙarfe takwas na safiya kamar kullum Nuratu ta farka cikin ihu da buge buge da take yi, wannan lokacin har ƙiran sunan Mami take ta zo ta taimaketa zasu kasheta.
Rukayya da Rahma da su kayi safiyar zuwa tare da taimakon Nurse suka taimakawa Mami da rirriƙe Nuratu suka shiga bathroom. Ruwan zafi da ta haɗa suka sakata ciki ta fasa ihu tana kai musu bugu suka rirrike ta sosai, Mami tana riƙe da kafafunta dan so take ruwan ya shigeta sosai.
Kuka take tana zare musu ido babu wanda ya kulata har ruwan ya huce suka fito da ita suka zaunar da ita ta kwasa a guje suka riƙota.
Nurse da sauri ta fita ta ƙira Dr Sadiq ya zo ya mata allura kafin ta samu bacci.

"Ku same ni anjima za muyi magana."

Dr Sadiq yace yana juye ruwan allura a drip ɗin hannunta bayan ya ɗaura mata, ya saka mata robar da ake dura mata kunu ta hanci ya dura mata. Mami ta saba ganin hakan banda Rahma da Rukayya da a take hawaye ya cika idon Rahma dan ita kam ba dai saurin kuka ba.

Bayan fitar Dr Sadiq, Munirat da Aunti Zarah suka shigo ɗauke da abincin safe bayan sun gaisa sun tambayi mai jiki, Mami da Rahma da Rukayya suka fita dan amsa ƙiran likita. Sai da suka biya suka duba jikin Hasiya da sauƙi har ta farka tana ƙoƙarin shiga wajen su. Daga nan ofishin likita suka wuce kai tsaye bayan sun shiga da sallama suka zauna.

Kanshi a ƙasa ya cire eyeglasses ɗinsa ya ajiye yana haɗa hannayensa waje ɗaya kafin ya fara musu jawabi.

"Mama ko ince Mami kamar yadda na ji suna faɗa. Akan maganar patient ɗin nan ne, maganar gaskiya wannan rashin lafiyarta gwara a dangana da psychiatric hospital domin abinda ya faru yana neman taɓa mata ƙwaƙwalwarta. Nan in muka barta anan maganar gaskiya kuɗinku kawai za'a ci, amma batun sauƙi babu shi amma can za su dubata su duba mai ya dace da ita, kuma Insha Allahu muna fatan samun sauƙi daga can duk da Allah ne yake warkarwa. In kun amince sai in muku hanya zuwa gobe sai kuje ku, ko zuwa nan da Maiduguri ne sai mu gwada sa'ar mu."

Bayan gama jawabin Dr Sadiq shuru ɗakin ya ɗauka Rahma ta kalli Mami ta kalli Dr.
"Za mu yi hakan Dr inshaAllah mun gode da taimako. Maganar tafiya bamu shirya zuwa gobe ba, za mu yi shawara zuwa anjima zamu sanar da kai in ya so jibi sai mu tafi."

"Shikenan duk yadda ku kayi."

Daga haka suka fita suka koma ɗakin da Nuratu take suka samu Amma Jidda da Ameera da Walida sun zo har da Hasiya da ta saka na cin sai ta zo ganin Nuratu. Kuka kawai take ganin halin da ƙanwarta take ciki.

***

Kallonshi take yadda yake cin abincin kamar ya kwana biyu bai ci irin shi ba. To ba dole ba shekaru huɗu ya tafi can garin iyamurai yana cin nasu dubi duk ya zama wani kato.
Tas Col. Ahmad ya cinye abincin gargajiya da Umma ta dafa masa ya sha ruwa tare da hamdala.

"Yayi daɗi Umma na daɗe ban ci irin shi ba."

"Ba dole ba. Ni kam dai wannan aikin sojan ya gama dani ace mutum bashi da zama."

Murmushi Col. Ahmad yayi.
"To Umma nan Allah ya tsaga abincina yake, sai kuyi ta mana addu'ar samun nasara."

"InshaAllah muna yi. Amma mai yake kai ka Damaturu kwana biyu, ina sane fa da shiganka da fitarka. Kar ka saka kan ka abinda ba'a gayyace ka ba ka jawo mana wani fitinar Ahmad."

"Babu komai Umma, taimako nake yi kuma Insha Allahu ina fatan samun nasara."

"Wani irin taimako."
Tace tana haɗa rai.

Anan Col. Ahmad ya sanar da mahaifiyar shi komai dangane da abinda ya sani. Ta ji wani iri amma haka kawai taji bata son ɗanta cikin case ɗin.

"Ka min alƙawari bayan taimako babu wani abin da zai biyo baya?"
Cewar Umma tana kafeshi da idanuwanta.

"InshaAllah babu komai Umma daga zaran an yanke hukunci, zan tattara in koma wajen aikina dama hutun ƙarshen shekara na ɗauka."

"To Allah yasa, amma in ka zo min da wani maganar zan baka mamaki."

Murmushi kawai Ahmad yayi bai kawo komai a ranshi ba yace babu komai, daga nan suka gangara hiran fitar da mahaifin shi zuwa ƙasar Egypt domin duba lafiyar shi.

****

A hargitse ya shigo office ɗin tare da banka ƙofar, mutanen da suke ciki suna meeting suka bisa da kallo yana huci kamar zaki yana dubansu ɗaya bayan ɗaya ya kasa banbance waye Alhaji Kashim Mufid. Hakan yasa ya ƙarasa ciki.

"Waye ko wanene Kashim Mufid?"

"Gani!"
Cewar Alhaji Kashim Mufid yana tashi tsaye ya isa wajen shi yana miƙa masa hannu suyi musabaha ya ƙi bashi hannu. Ganin haka ya sallami baƙin shi suka fita sum sum kafin ya juya yana kallon bakonsa.

"Bismillahi have a sit."

"Ba zama ya kawo ni ba, gargadi na zo maka."

"Ina jinka."

Faɗin Alhaji Kashim yana juyi saman kujeransa ya haɗa hannayensa yana duban baƙonshi fuskarsa cike da alamar yana sauraron shi.

.....

#vote
#comments
#share

MADUBIN GOBE  17.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

"Idan har kuɗi yana danne gaskiya ya hana a kwatarwa mai haƙƙi gaskiyar shi to kuɗi zai saka a hukunta mai laifi. Dan haka mu zuba ni da kai."

Dariya Alhaji Kashim ya kwashe dashi ko a jikin shi yace.
"Who are you."

Teburin gaban Alhaji Kashim ya dafa yana dubanshi.
"I'm Alhaji Mamman Bashir father of Nuratu Mamman Bashir. Wanda ɗanka ya ɓatawa rayuwa. Dan haka ka shirya shari'a."

"Oh shikenan ina jiran ka."

Alhaji Kashim yace ko a jikinshi. Daga haka Alhaji Mamman ya fita a fusace.
Tun da Amma Jidda ta sanar dashi maganar kasa zaune yayi, tun yana son kawar da maganar ya ji ya kasa hakan. Duk da haushin Nuratu da na Hajiya Sadiya da yake ji amma abin da ya faru da ita yaji ya kasa hakura ko ba komai kwansa ce itama kamar sauran, rayuwa ne da ita har lokacin yake jin ba zai iya gida ɗaya ƙarƙashin inuwa ɗaya da ita ba, baya son duniya ta zageshi ya sashi saka kanshi cikin shari'ar.
Dole ya bincika wajen aikin Alhaji Kashim dan shaida mishi shirye yake ya kwatarwa ƴarshi haƙƙinta.

***

Asibiti.

Da azahar Mami da Rahma suka hau shirin tafiya Maiduguri bayan sun sanar da Dr Sadiq ya basu copy na komai dangane da rashin lafiyar Nuratu da abin da ya jawo hakan har zuwa yanzu da babu wani canji.
Rahma ce kawai za ta raka Mami, ta sanar da mijinta ya amince ta shirya ita da Babynta. Sauran duk sai sun isa za su bi bayansu daga baya. Hasiya taso zuwa mijinta ya hanata cewa sai ta warke zuwa nan da kwana biyu.

Ƙarfe uku su ka ɗauki hanya cikin motar asibiti da Dr Sadiq ya basu. Nuratu alluran bacci aka mata dan karta farka musu a hanya.
Isan su kai tsaya asibitin Asylums suka isa kasancewar an san da zuwansu aka tare su, Dr Awwab da aka sanar da zuwansu ya dubata aka bata ɗaki.
Bincike sosai yayi a foldern ta da ita kanta kafin ya samu zama da su Mami.

"InshaAllah zata samu sauƙi, firgicin da ta shiga ya haifar mata da haka. Amma sannu a hankali komai zai wuce. Daga gobe zamu fara ɗaurata saman magani in ta farka, babu batun alluran bacci sai dai zuwa dare dan ta samu bacci. Muna so mu ga yanayin yadda sauƙin zai samu."

"Nagode Dr. Allah biya ka."
Mami tace tana sharan hawaye.

Murmushin sa mai kyau yayi duk da abinda ya samu Nuratu yana jin shi a zuciyar shi dan ya taɓa masa zuciya ba kaɗan ba, tausayinta ya cika masa zuciya.
"Babu komai. Mu ci-gaba da addu'a."

Daga haka suka koma ɗakin da Nuratu take babu kowa, tsakanin su da ita akwai gilashi suna ganin komai na ciki. Tana kwance kamar kullum cikin bacci ba ta motsi sai in har alluran ya saketa. Kuɗaɗen Mami na hannunta duk ya ƙare dan kafin ta zo ma sai da ta saida ɗan kunnenta mai tsada ta samu suka taho.
Burinta kawai Allah tashi kafaɗar Nuratu ta samu lafiya, maganar hukunci da shari'a duk bai dameta ba, burinta lafiyar ƴarta. Ta manta rabonta da taci abinci kwakkwara sai kunu shima sai an matsa mata.

Hira sama sama Rahma take mata tana sanar da ita kyan asibitin da kuma halin Dr Awwab da ta kula ya san kan aikin shi, hiran ne ya ja lokacin har aka ƙira magriba suka gabatar da sallah. Sai da Mami tayi kafin ta riƙewa Rahma ƴarta mai shegen ƙiwa kafin itama tayi.

Cikin daren ƙarfe goma Nuratu ta farka, Mami da Rahma suka rirriƙeta suka kai ta bathroom, Mami ta sakata cikin ruwan zafi sai bugesu take tana ture su. Haka suka fito da ita suka canza mata kaya kafin Nurse ta mata allura wani bacci ya ɗauketa suka samu suma suka kwanta.

Washegarin har karfe sha ɗaya kafin ta farka lokacin Dr ya iso, hana kowa zuwa kusa da ita ya yi suna kallonta ta cikin gilashin ta farka tana zare idanuwa kafin ta miƙe ta isa ƙofa tana bugawa a buɗe mata sai ƙiran Mami take, da ta gaji ta koma ta samu lungu ta shige tare da fashewa da kuka ta kama jikinta, sai kuma ta saka hannu tana rufe bakinta alamar kar kukan ya fito.
Ji take kamar tana tare da su, gani take za su zo mata, mafaka ta samu ta ɓoye kanta daga gare su da har bata son su juyo sautin kukanta.

"Tana cikin damuwar abin da ya faru da ita ne, tsoro ne a tare da ita. Gani take za su zo mata"
Faɗin Dr Awwab yana kallonta yana karantar yanayinta.

Kallonsu gaba ɗaya suke idanuwan Rahma cike da kwalla, Mami kam ta fara sabawa domin ta ɗauki dangana ta sakawa zuciyarta.

Buɗe ƙofar gilashin Dr Awwab yayi ya shiga, Nuratu tana kallon shi ta fara jan baya tana roƙarshi ya rabu da ita kar ya ƙaraso. Ganinshi take tamkar Mufid da kamannin shi ya juye mata zuwa fuskar shi.

A bakin kofar ya tsaya yana dubanta can kuma ya miƙa mata hannu.
"Shit babu mai zuwa."

Dube dube ta fara ta zaro ido tana kallon shi ya ɗaga mata kai yana nufanta, tana ganin haka ta fasa ihu ta fara ƙoƙarin gudu ya riƙota, ta sake fasa wani ihun tana son kwace jikinta. Kokuwa su kayi sosai da ita duk yana son ta nutsu ta ƙi, dole a ƙarshe ya mata alluran da ya kashe mata jiki ta kasa motsi amma ba bacci take ba ya kwantar ta ya fita.
Ita ɗaya cikin ɗakin tana binshi da kallo ta kasa magana balle ɗaga yatsun hannunta, jikinta yayi nauyi.

Mami da Rahma suna kallon komai har ya fito ya tsaya kusa da su.

"Tsoro ne ya shigeta sosai, gani take har yanzu za su iya zuwa mata, wani lokacin kuma gani take duk mutanen da take tare dasu cutarta za suyi, wani lokacin kuma yanayin da ta kasance shi yake dawo mata ta dinga kallon mutane a matsayin su. Mu fara barinta tana samun zama ita ɗaya na wasu mintuna."

"InshaAllah Dr za muyi hakan."
Cewar Mami cikin gamsuwa da bayanin shi.

"Dr. Ba ta cin abinci fa kwata kwata."
Rahma ta ce cike da damuwar hakan.

"Kar ki damu za ta fara, ba tana shan kunu ba. Abincin ma zamu fara gwada mata ko zuwa gobe."

Shikenan suka amsa dashi kafin ya fita, sun gamsu da bayaninsa ko ba komai sun samu wani kwanciyar hankali jin sauƙi ya zai fara samuwa.
Bayan fitarshi suka saka idanuwa suna kallonta sai juya idanunta take tana lumshe su har bacci ya ɗauketa da yau cikin hankalinta tayi shi.

***

Abincin dare da ta haɗa masa take zuba mishi har ta gama ta ajiye masa kafin ya wanke hannunshi ya fara ci yana kallon labarai.

"Wani asibiti su ke ne?"

cikin mamaki furucin shi Amma Jidda tace. "Su waye?"
Sai kuma da sauri tace.
"Nuratu?"

Shi sau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login