Follow us on social media

Showing 138001 words to 141000 words out of 148866 words

Chapter 47 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

26

yarannan."

Ƙara sassauta murya ya yi yace.
"Dan Allah fa, ba zai ji daɗi ba, balle an sanar masa za ku je. Wuni kaɗai za muyi mu juyo."

"To ni dai babu yadda na iya idan ba haka ba babu inda zanje."

"Ki ɗaure dai."

Dole ta miƙe ta shirya ta fito ta samesa, yaran duk sun iso har da yaransu. Gaba ɗaya suka dunguma a mota babba da ya nema musu suka ɗauki hanya.

....

Kallonsa su ka yi dukkansu ganin ya tarasu ya ƙi cewa komai. Abba ne ya yi tsaki.

"Kai wai me haka? Zan saɓa maka fa, ka girma ba kasan ka girma ba."

Marairaice fuska yayi ya kallin Babban Yayansa.
"Yaya to ka sanar da su ba anan zan nuna musu abun ba. Su taso mu je can."

Abba miƙewa yayi cikin jin haushi. Da sauri Babban Yaya ya tsayarsa.
"Abba kayi hakuri mu je mu gani, idan shirme ya yi ni da kaina zan masa hukunci."

Tsaki yayi yana cewa.
"Mu je to."

Dukkansu suka nufi waje, cike da murna ya ciro wayarsa ya yi ƙira.

"Done, gamu tafe nan da mintuna goma."

Daga haka ya kashe wayar ya bi bayansu da sauri.

...

Ƙarfe sha biyu suka iso gidan, da murna Nuratu ta tari Maminta da yayunta. Kallo Mami ta bita da shi ganin yadda ta rame, Aunti Hasiya marar haƙuri ta ce.
"Jinya ki ka yi Nuratu?"

"Eh. Mami ki shigo."

Ta faɗa ta basar da zancen ta musu jagora zuwa falonta, ta kawo musu abinci da Batula ta girka dan har lokacin ba ta iya yin aikin kirki don ciwon jiki. Da ƙyar Dr Awwab yake samun kanta ta yarda da shi wani lokacin har da kukanta.
Alhaji Mamman da Muhsin wajen Kawu Muhammadu su ka zarce su na hiransu, Dr Awwab kuma yana waje don jiran isowar Ummi.

...

Aunti Hasiya da ta kasa haƙura tana duban Nuratu tace.
"Wai wani irin ciwo ki ka yi haka, kin ga yadda kika rame."

"Zazzaɓi ne fa."
Ta faɗa kamar tayi kuka, wannan sa idon na Aunti Hasiya ya isheta.

"Zazzabi kaɗai."
Rukayya tace tana dariya ƙasa ƙasa don ta harbota.

"Kai ku daina takurawa autana."
Faɗin Mami ta jawo Nuratu jikinta.

"A faɗa mana gaskiya, idan kuwa ya fito dole mu ji mu gani."
Rukayya ta ce tana fita da sauri gani saƙon harara daga wajen Mami.

Zuwansu babu jimawa Hafiza ta iso don ma mahaifinta sannu da zuwa kamar yadda Yaya Al-ameen ya faɗa.

....

Kusan tare motar Ummi da Ammi da Abba suka shigo gidan. Ammi kallon Abdallah ta yi da shi yake jan motar tace.

"Nan ai gidan Awwab ne."

"Na sani Ammi."

Abba girgiza kai kawai ya yi, shirmen ɗansan ya fara basa mamaki ba haushi ba. Fita su kayi gaba ɗayansu suka gaisa da Ummi da ita ma kallon mamakin ganinsu ta ke. Hatta Babban Yaya da Sajeed da bai cika magana ba, ko miskilanci ne ko jan aji ne oho.
Awwab da ya samu labarin shigowarsu ya fito ya musu jagora zuwa babban falon. Bayan gaisuwa kowa ya zuba ido da kunne ganin me ya tarasu a gurin.
Dr Awwab ne ya fara magana.

"Ummi, Ammi, Baffa, Yayan mahaifiyar Noor ne za ku gaisa da shi sai mahaifinta. Na san hakan bai taɓa faruwa ba tsakaninku, shi ne nayi tunanin bayan dawowarsa daga Umrah kafin ya wuce ya kamata asan juna har da mahaifinta. To mahaifiyarta ma ta zo duk zan ƙirasu yanzu saboda suna son wucewa a yau suma."

"Kayi tunani mai kyau."
Baffa ya ce cikin wani muguwar buguwar zuciya da ya kamasa ya rasa dalili.
Kowa ya yaba da tunaninsa hakan yasa ya miƙe ya nufi stairs, da sauri Abdallah ya bi bayansa. A stairs suka tsaya.

"Kana ganin za su gane juna Yaya?"

"InshaAllah, matan su fara fitowa sai mazan, suna falon ƙasa na baƙi."

Yarda da shi ya sa shi nufan falon Nuratu, da sallama ya shiga ya durƙusa.

"Mami, Ummi, Ammi sun zo, za ku gaisa, sun zo ma Kawu sannu da zuwa.

"Har da wahalar su?"

Mami ta tambaya tana miƙewa.
Fita ya yi ya basu guri suka ta shi dukkansu su ka bi bayansa, har da Nuratu da take jin ciwon jiki.

Ɗakin da Alhaji Mamman da Muhsin da Kawu Muhammadu ya ke ya shiga ya sanar da su, su kam tare su ka fito su huɗu harda Muhsin.

Fitowar su ya yi dai-dai da sauƙowar Mami da yaranta, wanda ya yi dai-dai da kallon Abba zuwa ga Muhsin. Da mamaki ya kalli Muhsin ya kalli Abdallah. Bai gama fita a mamaki ba ya kalli Alhaji Mamman, tabbas shi ne mahaifin matar Awwab da ya musu rashin mutunci a aurensu.
Kallon sa na biyu zuciyarsa kaɗan ya koma ciki lokacin da ya haɗa ido biyu da na gefensa.
Salatin da ya ji a gefensa ya sa shi duban inda ya ga an nufa da sauri. Babbar macece take neman kaiwa ƙasa yaran gefenta suka riƙota da sauri cikin tashin hankali. Bayan an samu ta zauna ya samu damar ganin fuskarta da ƙyau.

Kansa ya riƙe da sauri jin yana juya masa, jiri ya fara gani kafin yayi wani ƙara numfashinsa ya ɗauke.
Gaba ɗaya yaransa su ka yi kansa suna jijjigasa. Falon ya hargitse da hayaniya har an rasa na wanne za'a saurara.
Gefe Mami tana kuka da suka rasa dalili, gefe Kawu Muhammadu zaune ya kasa motsi sai ido yake bin su da shi, gefe ɗaya Baffa ya suma yaransa a kansa Dr Awwab yana ba shi taimakon gaggawa.

Kusan mintuna biyar ya samu numfashinsa ya dawo, sannan ya buɗe ido da ƙyar. Babban Yaya ya basa ruwa ya sha. Bayan samun nutsuwa ya dubi Babban Yaya murya ƙasa ƙasa yace.

"Aliyu! Muhammadu da Sadiya na gani. Dama suna raye? Ko kuma ni ne na mutu na dawo?"

Kowa shuru ya yi ya zuba masa ido jin zantukan bakinsa, shi kuwa sai kallon Mami da Kawu Muhammadu ya ke ya kasa musu magana, haka su ma ɓangrensu. Sun rasa ta ina za su fara.

"Kowa ya zauna."

Abdallah ya ce daga tsayen da ya ke.
Hakan yasa yaran Mami suka zauna kusa da ita sun zagayeta suna bin Baffa da kallon mamaki ganin kammanin Mamin su a fuskarsa, hatta Hafiza da take hango kamannin mahaifinta a gurinsa ta yi jugum. Gefe Ummi da Hassana da ta zo da Ummi. Gefe ɗaya kuma Kawu Muhammadu da Muhsin da Alhaji Mamman sai Yaya Al-ameen da bai jima da shigowa ba. Gefen Baffa kuma Ammi da yaranta ne.

Abdallah ne ya fara magana ganin an samu nutsuwa.

...

#vote.
#comment
#share

MADUBIN GOBE  61.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

GANGARA.

***

Abdallah ne ya soma magana bayan kowa ya baza kunnuwa don jin wannan sarƙaƙiyar. Gyaran murya ya yi kafin ya soma da cewa.

"Tsawon shekaru huɗu kenan. Watarana da yamma ina zaune Yaya Awwab ya zo ya same ni har makaranta, nayi mamakin ganinsa a lokacin saboda bamu cika haɗuwa ba sai irin a biki ko a sallah idan ya zo gidanmu, ko idan mun je na su.
Bayan mun gaisa na basa gurin zama, anan ya dubeni ya ce.
"Abdallah naga abin da ya bani mamaki yau, naga abin da ya birkita tunanina da ƙwaƙwalwata, na kasa tunani na kasa gano komai balle samun haske, na rasa wa zan tunkura in sanar balle ya taimaka mini sai kai."

Dubansa nayi yadda yake cikin damuwa, ni ma cike da damuwar dan maganganun sa sun rikitani na ce.
"Yaya Awwab me ya faru? Na kasa gane maganganun ka, na kasa fahimtar su ko sanin ina su ka dosa."

Kallona ya yi a karo na biyu ya ce.
"Shin Baffa ya taɓa sanar da kai suna da wasu ƴan uwa bayan Babban Yayan su Alhaji Yousufa?"

Tambayar da ya min shi ya ƙara dilmaye ƙwaƙwalwata, sai girgiza masa kai da nayi alamar a'a. Numfashi ya sauƙe ya miƙe tare da fara zagaye cikin ofishin da muke zaune. Ni dai kawai idanu na saka masa dan na rasa bakin magana. Haka ya ci gaba da yi tsawon lokaci kafin ya dafa teburin da nake zaune.
Tamkar ba zai ce komai ba ya ɗago ya dube ni da idanuwansa da su ka canza launi.

"Abdallah naga mai kama da iyayenmu, ba kuma namiji ba mace, babbar mace, in taƙaita maka hatta ƴarta babba tana kama da ƴar uwarka Sumayya."

"Kama kuma? Kamar ma da iyayenmu kuma mace?"
Na tambayesa da mamaki.

Kai ya ɗaga mini yana cewa.
"Tabbas hakane Abdallah. Marar lafiya aka kawomin kwana biyu da ya wuce, ƙwaƙwalwarta ya samu matsala. Wallahi farin ganin babbar ƴar matar na ɗauka Sumayya ce, amma da na ji sunan da aka ƙirata da shi sai na tabbatar ba ita bace. Sannan matar ita da su Abba bambancin su kawai ita macece sai ƙarancin shekaru. Hatta ita marar lafiyar tana kama da su."

...

Shuru Abdallah ya yi yana neman guri ya zauna don ya gaji da tsayuwar. Falon tamkar anyi ruwan sama an ɗauke, babu mai iya kwakkwaran motsi sai idanu da suke bin juna da shi cike da mamaki da son fassara kalaman Abdallah.
Bayan zamansa ya ci gaba da cewa...

"Ban san me yasa ya zaɓi ya faɗamin ba. Ban san me yasa ni ƙarami a cikinsu ba kuma ya zaɓe ni. Ban yarda da zantukan sa ba a lokacin haka muka rabu.
Sai dai abun mamaki bayan lokacin Yaya Awwab ya ci gaba da kawomin bayanai akan waɗannan mutane har Allah ya sa watarana na kai masa ziyara asibiti na gansu da idanuna. Tabbas na shiga rudu, sai dai Yaya Awwab ya nunamin kar mu tono maganar ko mu tunkari wani da shi a cikin iyayenmu sai wani burinsa ya cika.
To allahamdulillahi bayan aurensa da Noor mu ka dinga samun ƙarin haske. Misalin ganin Ammi da ta yi ma Aunti Rahma da ita kanta Mamin da kuma Muhsin. Ammi tafi nuna damuwarta a kan Ummi. Na yi ta bibiyarta ta sanar dani damuwarta duk da na fahimci akan menene amma ta ƙi. Anan kuma burin mu idan ta sanar da ni sai in sanar da ita ga yadda abun yake, sai mu tunkari Abba da maganar kamar yadda muka tsara da Yaya Awwab, amma ƙarshema dai ta ƙi maganar gaba ɗaya ta watsar. Hakan ya sa Yaya Awwab neman sabuwar hanya."

Daga haka ya yi shuru yana sauƙe numfashi, ruwa ya tsiyaya yasha ya kalli Dr Awwab ya marairaice masa.
"Yaya ka ƙarasar musu ni na gaji."

"Ka ƙarasar kawai."
Dr Awwab ya ce yana ƙoƙarin miƙewa.

Cire kunya Mami ta yi ta ajiye gefe ta ce.
"Awwab ka warware mana wannan abun. Har yanzu mun kasa fahimtar maganganun Abdallah?"

Kunyar Mami ya sa shi komawa ya zauna kansa a ƙasa ya fara magana.

"Tun ranar da na ɗora idona akan ku na dasa ayar tambaya a lamarin ku. Sai dai na rasa ta ina zan soma binciken abin da bani da tabbas. Abban mu har ya rasu bai taɓa sanar damu yana da wasu ƴan uwa ba bayan Alhaji Yousufa da ahlinsa da suke Nijar. Balle ma lokacin da ya rasu ban wuce shekaru goma ba.
Rasa wanda zan tunkara da wannan batun ya sani sanar da Abdallah, duk da bai yarda da ni ba, haka na dinga kawo masa wasu bayanan har ya zo ya fara yarda kamar yadda ya sanar da ku.
Gefe ɗaya kuma ga Noor da na gani ina son aure, duk da tasha sanar da ni babu aure a ranta yanzu saboda ƙaddarar da ta tsinci kanta. Wani lokacin ji nake tamkar in hakura, amma idan na tuna burina fa da nake mafarkin ya kusa cika. Dan na sha yin mafarki da Abba yana sanar da ni yarinyar da nake neman aurenta alheri ce a tare da ni, ita ce silar bayyana ɓoyayyen sirrin da yake rufe, kar na yarda na karaya, Insha Allahu zan yi nasara. Wannan kalaman mafarkin su suka ƙarfafa mini gwuiwa na dage da cusa kaina gurinta.
Ranar da Ummi ta je gidansu Noor na ɗauka tun a hanya za ta fara tambayata akan abin da ta gani, sai dai abin mamaki har yau Ummi ba ta taɓa kawomin maganar ba, kuma ban san dalili ba.
Haka na dage sai da naga aurena da Noor, bayan auren ni da Abdallah mu ka ci gaba da bin duk hanyar da zamu ɓullowa lamarin. Ammi ta ƙi bamu gamshashshiyar bayani, Ummi sam ta ƙi maganar. Ƙarshe dai bayan zuwan mu Damaturu na samu Abba da maganar. Anan na sanar masa komai, shi ma ya ce mini tabbas yaga kamar Mami a fuskar Baffa lokacin ɗaurin aurenmu, sai dai lokacin ya rasa a ina yasan mamallakin fuskar, sai daga baya ya gano, dalili babba da ya saka shi dagewa ya mayar da Mami. Anan ya bani shawara. Shawarar da ya bani shi na samu Abdallah da shi akan in biyawa Kawu Muhammad Umrah, sannan in dage ƴan uwa zu so masa sannu da zuwa. Hakan mu ka yi da taimakon Abdallah nayi komai har zuwa yau.
Iya abin da na sani, ku za ku sanar damu sauran domin mu ma ƙarin haske muke nema a gurin ku.
Kawu, Baffa, Mami shin ku ƴan uwa ne?"

Yin shurunsa ko in ce dasa ayarsa shi aka fara surutu a falon. Kowa da abin da yake faɗa, burin kowa mutane ukun nan su amsa tambayoyin da yake zuƙatansu.

Nuratu da kanta yake saman cinyar Mami ta ɗago tana kallonta tana share hawayenta. Girgiza kai ta
yi ta riƙo hannunta cikin ƙarfin hali don zazzaɓine ya rufeta ta ce.
"Mami kiyi haƙuri don Allah kiyi shuru ki mana bayani tun da Kawu da Baffa sun ƙi magana. Yin maganar ki ina ga zai saka sauran yi."

Kai ta ɗaga mata ta kamo hannunta da take share mata hawaye. Gyaran murya ta yi kafin ta soma maganar da ya sa ka yan falon shuru da dubanta.

"Mu ƴan asalin Niger ne kamar yadda ku ka sani, iyayenmu mu huɗu suka haifa. Yaya Abubakar, Yaya AbdulRamat sai Yaya Muhammadu sai ni autar su. Iyayenmu bani da wayo sosai suka rasu, dalilin haka riƙon mu ya dawo hannun kakarmu. Da ɗan wayona Yaya Abubakar da Yaya Abdul suka fara kasuwanci da kuɗin gadonmu tun bayan gama karatun su. Yaya Muhammadu ya bada rabin nasa dukiyar haka ni ma, suka bar bar mana abin da zamu riƙe, a haka Allah ya albarkaci abun har su ka fara fita garuruwa har Allah ya yi zamansu a garin Agadez inda aka fi kasuwanci sosai. Anan suka kafa kasuwancin su tare da taimakon wani Alhaji Yousufa. Ba mu taɓa kallonsa ba, kuma basu taɓa kawosa ba, har Allah yayi su biyu suka yi aure acan Alhaji Yousufa shi ya tsaya musu matsayin dangin su. Auren duk labari suka bamu ta hanyar waya da ya fara zuwa lokacin. Ba su gayyaci kowa ba, da muka nuna ɓacin ranmu musamman Yaya Muhammadu, haka ya sa suka zo suka bamu haƙuri sai dai basu kawo mana matansu ba. Sun mana alheri sosai kafin su tafi, musamman ni da ake shirin aurena lokacin da Abban su Rahma.
Wannan tafiyar shi ne na ƙarshe sai waya da suke mana, har aka yi aurena aka kawo ni Damaturu ban ƙara saka su a ido ba, Kawu Muhammadu ya yi aure, har kakarmu ta rasu. Ƙarshema wayar suka daina kiran mu, idan mun ƙira ba ya shiga. Wannan lokaci ni da Yaya Muhammadu mun shiga tashin hankali ba don dukiyarmu da yake gurin su ba, burinmu ƴan uwanmu da su kaɗai suka rage mana su dawo garemu.
Tun muna saka ran dawowar su har muka fara haƙuri, mu ka fara addu'ar idan da sauran saduwarmu a duniya Allah ya haɗa mu.
Sai bayan tsawon shekaru talatin yau gani ga Yaya Abubakar amma babu Yaya Abdul."

Nan falon ya ƙara hargitsewa da kuka, musamman wanda suka tuna mahaifinsu da baya raye. Ummi da Ammi banda hawaye babu abin da suke. Kawu Muhammadu shi ma hawayen yake sharewa lokaci zuwa lokaci domin yariga ya fahimci ɗan uwansa baya raye. Ɓangaren Baffa abubuwan da suka wuce ne suka dinga dawo masa a hankali cikin ƙwaƙwalwarsa tamkar bidiyo.
Kallon Mami yayi ya maida kallonsa kan Kawu Muhammadu. Tsam ya miƙe ya nufi gurinsa, mutanen falon gaba ɗaya suka zuba masa ido.
Durƙushewa ya yi gabansa ya rumgumosa jikinsa, manyan mazan hawaye kawai suke fitarwa cike da jarumta. Kawu Muhammadu ne ya fara janyewa ya riƙo hannun Baffa.

"Yaya Abubakar."

Damƙe hannunsa Baffa ya yi ya ɗago kai suka haɗa ido.
"Muhammad.."

Kawai ya iya faɗa ya yi shuru don wani ɗaci da ya sarƙe masa a maƙoshi, ya rasa me zai fara furtawa, ta ina zai soma.
Fahimtar haka ya saka Kawu Muhammadu ƙara damƙe hannunsa.

"Ka fadi wani abun don Allah. Ina ku ka shiga?"

Girgiza kai ya yi bakinsa yana rawa ya ce.

"Bansan me zance ba amma tabbas tun da mu ka barku kullum ku na cikin ranmu, ni da Yaya Abdul ba mu taɓa zancen ku ba amma shi ma nasan yana tunaku a ransa. Sai dai me? A lokacin mun kasa sanar da junanmu balle tunanin komawa gida, da zaran hakan ya bijiro mana sai ɓacin rai ya ziyarce mu.
Farko mun haɗu da Alhaji Yousufa a Agadez amma ɗan asalin Libya ne. Da dukiyarmu da nasa muka haɗa hannun jari muna juyawa, sai dai namu yafi nasa yawa kaso saba'in namu kaso talatin nasa. Bayan aurenmu Alhaji Yousufa ya samu dole muka tattara muka koma Libya da zama mu da matanmu. Duk matanmu tsammanin su shi Yayanmu ne, danginsa kuma namu ne.
Bayan tafiyarmu Libya Ammi ta haifi Babban Yaya Aliyu, Sajeed, sai lokacin Ummi ta haifi Zaituna daga baya suka haihu kusan tare, Ummi ta haifi Ikhram ita kuma Ammi ta haifi Sumayya, sai bayan shekaru uku Ummi ta haifi Awwab, Ammi kuma sai bayan shekaru huɗu ta haifi Abdallah.
Shekarun Awwab biyar mu ka baro Libya muka dawo Maiduguri da zama, lokacin Alhaji Yousufa ya yi bake bake akan dukiyarmu shi da yaransa, ya hana mu amfani da shi sai yadda ya yi, kuma ya hanamu magana don mugun tsoron sa muke ji da bamu san dalili ba. Rabuwar mu bai yi daɗi ba don ya hanamu ko da rabin abin da muka saka a ciki. Dalilin haka Yaya AbdulRamat ya haɗu da hawan jini har ya kwanta jinya wanda ƙarshe ya yi ajalinsa.
Bayan mun samu mun saida wasu kadarorinmu mun samu gidan zama, mun saka yaranmu makaranta, mun samu sana'ar yi, a Lokacin muka sanar da Khadijah da Zainab zamu zauna ne a garin kafin zuwa wani lokaci, har zuciyoyin su basu yarda ba amma haka suka ci gaba da zama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login