Follow us on social media

Showing 135001 words to 138000 words out of 148866 words

Chapter 46 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

23

aka fara taruwa, dangin Ummi sun fara zuwa haka wanda su ka yi zaman mutunci a Libya ma sun taho.
Ranar farko su kayi kamu inda iya mata zalla ne, da ƙyar aka lallaɓa Hussaina ta je dan harda kukanta. Ga biki yana matsowa amma har yau babu ango babu labarinsa. Washegari suka yi walima a filin gidansu.

Nuratu tun biki saura kwana biyu ta tare gidan, ita take ƙarfafawa Hussaina gwuiwa akan ta yi hakuri ta yi wa iyayenta biyayya za ta ci ribarsa, balle ta tabbatar mijinta yana sonta.

Hussaina da ke kuka har zazzaɓi ya rufeta bayan dawowar su daga walima, ta ɗago ta kalli Nuratu.

"Aunti Noor a hakanne yana sone, bayan bai taɓa nuna kansa gareni ba. Wallahi bana son aurennan, don Allah ki faɗawa Yaya Awwab a fasa bikinnan."

"Kiyi hakuri."
Kawai Nuratu tace ta kwanta. Zirga zirgar da tayi ya saka duk jikinta take jin yana mata ciwo. Babu jimawa barci ya ɗauketa. Ko da Dr Awwab ya ƙira Hassana ce ta sanar da shi tayi barci.

...

Washegari ƙarfe goma aka shaida ɗaurin auren Abdallah Abubakar da Hassana AbdulRamat sai Col. Ahmad Tafida da Hussaina AbdulRamat akan sadaki mai albarka. Bikin da ya tara taron manyan mutane daga gurare daban daban, sojoji runduna runduna tun daga ibadan har nan Maiduguri da duk garin da ya zauna sun zo. Gefe ɗaya kuma ga dangin Ummi da suka zo daga Nijar wasu Libya, dangin Ammi ma haka.
Bayan ɗaurin auren maza suka tafi reception. Can gida kuma ana ta hidima, amare sunyi ankonsu an musu kwalliya marar hayaniya, Hussaina dai daurewa take. Balle da ta ji sunan ango da ba ta taɓa ji ba ko tayi zargin ko cikin samarinta ne. Wai soja ma kayan haushin.
Nuratu kam tafi kowa murnar jin wanda ya auri Hussaina, tuni ta laliɓo wayarta ta ƙirasa, yana ta ringing bai ɗauka ba ta kashe ta ƙira Awwab. Ringing ɗaya ya ɗauka duk da yana cikin hayaniya, ya matsa gefe.

"Hayat dagaske ne?"
Ta watsa masa tambaya.

"Yes My Baby. Col ya zama angon Hussaina. Ina fatan wannan haɗin ya zamto alheri."

Cikin murna tace.
"Insha Allah Hayat, amma ina da tambayoyi."

"Zan amsa miki amma ba yanzu ba."

Dariya tayi tace to kafin ta kashe wayar. Cikin sauri ta miƙe, jirin da ya kwasheta ya sata zama ba shiri tana dafe kanta, kusan mintuna kafin ta miƙe a hankali ta fita.

Bayan sallar azahar dangin Col Ahmad suka kawo akwati seti biyu, sun zuba kaya na gani a faɗa ciki harda kyautar mukullin mota daga baban ango, haka uwar amarya ma ta saka danƙareren setin gold a bawa amarya. Kallon kallo aka shiga yi mutanen gurin, duk da suma dai akwai arzikin basu tsammaci ganin waɗannan kyautattukan ba. Kaya kam MashAllah.
Ƙarfe uku aka kawo na Hassana abin mamaki ita ma da mukullin mota irin na Hussaina sak da kuma setin gold babu abin da ya banbanta tamkar haɗin baki. Nan fa aka ɗauki kabbara masu guɗa nayi.

Ƙarfe takwas na dare aka fara shirin kai amare, inda aka tsaida za'a fara kai Hassana sai a wuce a kai Hussaina gidan su Col. Ahmad ta zauna a bangarensa bayan sati biyu zai ɗauketa su wuce Ibadan.
Haka kuwa a kayi bayan sun kai Hassana har gidanta mai kyau da tsari aka wuce da Hussaina. Nan fa hankalinta ya ƙara tashi ta ci gaba da kukanta da take tun daren jiya.
...

Rana ta farko da ta fara taka gidan mutumin da yake da muhimmanci a rayuwarta. Bayan anyi fakin suka fito aka nuna musu ɓangaren da amarya za ta zauna suka wuce da ita.
Ana gama ganin gidan amarya aka fara watsewa, nan Hussaina ta riƙo Nuratu ta hanata tafiya sai kuka take. Ganin haka ya sata zama dole suka kwana gidan amarya.

Washegari wuni anyi budan kai da yamma aka shirya dinner. Amare dukkansu cikin ankonsu an musu kwalliya. Ƙarfe biyar aka fara tafiya. Motar da zata kai amarya ta iso wanda ango yake ciki. Har cikin motar Nuratu ta sakata tana gaishe da Col. Ahmad tana faɗin.

"Na ƙiraka ba ka ɗauka ba."

"Sorry ƙanwata ina cikin jama'a ne. But mu haɗu a gurin dinner za muyi magana, ko gobe."

Kai ta jinjina ta rufe motar tana wucewa wajen mijinta da ya ke jiranta.
Bayan tafiyarta Col. Ahmad ya juya yana kallon amaryarsa da ta sunkuyar kanta ƙasa. Idonsa ya lumshe ya buɗe ya riƙo hannunta.
Cikin nutsatstsiyar murya yace.

"Love!"

Hannunta ta zare ta ɗago ta dubesa tana kawar da kanta gefe. Tabbas tasan fuskarsa amma ta rasa a ina ne.
Sauƙar kansa da ta ji a kafaɗarta ya sata tsorata ta ja baya ya riƙota gaba ɗaya jikinsa. Kuka ta fashe masa da shi. Sassauta riƙon yayi yace.

"Is ok Love, ni ne ko? Na ɓatawa twins rai, kullum kuka kina kokonto waye Yayanki zai aura miki ba? I'm sorry kar ki ciremin kunama."

Ba ta san lokacin da ta murmusa ba jin maganarsa na ƙarshe. Ba ta masa magana ba a haka suka isa wajen dinner. Bayan an gama komai suka fito, gefe da gefensu sojojine a jere sun riƙe bindiga. Hassana da Abdallah a gaba sai su biyun a bayansu, a haka suka isa wajen zamansu. Taro aka yi cikin nutsuwa da raha.

Nuratu dai gefe da Dr Awwab ya kasa ya tsare ya hanata ko motsi, duk idon yayunsa da yaran Ammi bai ji kunya ba balle kuma wasu dangi. Ita ma dai bata damu ba dan duk jikinta ciwo yake, burinta ta kwanta, ga jiri jiri da take ji.
Yaya Al-ameen da yake gefensu bayan ya gama waya da matarsa ya kalli Dr Awwab yace.

"Doctor ko za ku je gidane? Kamar ba ta jin daɗin zaman."

Kallon Nuratu Dr Awwab yayi hankalinta yana kan ma'auratan yace.
"Na mata magana ta ƙi, wai sai taga komai."

Kai Yaya Al-ameen ya jinjina yana murmushi.
"Kasan mata da son ganin kwakwaf."

"Hakane, bari in lallaɓa mu yi wa Col sallama mu tafi, in je in kula da kayata."

"Daɗinta kowa yana da na shi kayar."

"Daga can nesa ba."
Faɗin Dr Awwab ya matsa gurin Nuratu.

"Babyna muje ki yi wa Col da twins sallama muje gida."
Kallonsa ta yi tana marairaice masa, za ta yi magana ya miƙe ya riƙo hannunta suka tashi.

Haka suka ƙarasa wajen suka musu sallama Dr Awwab ya basu excuse tana buƙatar hutu. Murmushi Col Ahmad ya yi ya ce.
"To a huta lafiya."

Ita dai bata fahimci komai ba suka bar gurin bayan ta yi wa twins sallama. Kai tsaye gida ya nufa bayan sun fita a hall din ta dubesa. Murmushi ya yi hankalinsa a titi ya ce.

"Tausa zan miki ki yi barci, gobe zan mayarki ki haɗo kayanki."

Daga haka ya rufe bakinta suka isa gida, ruwan zafi ya haɗamata ya taimaka mata tayi wanka ta gabatar sallah ta kwanta gadon. Matsa mata jikinta ya yi a haka barci ya kwasheta ya lulluɓa mata bargo. Ya jima yana ƙaremata kallo kafin ya bar gurin, shi ma ya yi shirin barci ya kwanta.

...

Washegari ta ji sauƙin ciwon sai jiri da take ji, haka ta daure tayi ayyukanta ta shirya suka je gidan Ummi wajen karfe biyu. Zaituna da Ikhram suna ta lallaɓata suna mata korafi ba ta zo musu ba. Ita kam murmushi ta musu sai Dr Awwab ne ya ce.

"Za mu zo sisters. Kuma ai tun biki ba ku zo gidanta ba."

Harararsa Zaituna ta yi ta ce.
"Mun gani, ai ba da kai muke ba. Ke kuma wallahi idan ki ka biya masa ba za kiyi zumunci ba. Kinga Babban Yaya ɗan Ammi, da Yaya Sajeed gari ɗaya suke amma sai suyi shekara basu haɗu ba, gwara Abdallah."

"Kai dai Sister."
Awwab yace yana ma ƙaramin ɗanta wasa ɗan wata shida.

"Ai gaskiya ta faɗa."
Ikhram ta ƙara da haka.

Nuratu dai dariya take musu, shi ma dariyar yake yana ta kare kansa. Ƙarfe uku ya ɗauketa suka je gidan Hassana da kallo ɗaya ta mata ta gano Abdallah bai sarara mata ba. Sun ɗan taɓa hira suka bar gidan ganin yanayi ya canza.
Gidansu Col. Ahmad suka je daga can, bangaren Hussaina suka fara sauƙa, gata nan dai alama ta fara kwantar da hankalinta. Bayan sun gaisa Col.Ahmad da Dr Awwab suka dawo daga masallaci suka ƙira Nuratu ta fito suka shiga cikin gidan.

A falon suka zauna har lokacin da ɗan baƙi, Umma ta sauko ta musu jagora zuwa falon baki ganin nan akwai mutane. Bayan sun gaisa da Dr Awwab tana ce masa tun ranar shuru, Nuratu ta gaisheta. Da fara'arta ta amsa. Col. Ahmad yana kallon Umma ya ce.

"Umma ita ce Nuratu fa."

"Nuratu dai? Wacece? Banganeta ba? Ba matar likita ba ne. Na gansu tare wajen dinner jiya."

Murmushi Col Ahmad yayi ya ce.
"Eh matarsa ce. Ita ce yarinyar nan, wacce na taimaka. Na so aurenta ki ka hana ni."

Nadama tare da kunyane ya lulluɓe Umma, ta matsa kusa da Nuratu da kanta yake ƙasa, kamo hannunta ta yi cikin sanyin murya tace.
"Kiyi hakuri don Allah, na kullace ki ba tare da kin mini komai ba. Sai ga shi Allah ya ba ki jin daɗin rayuwa da miji nagari."

Nuratu da har lokacin kanta yana ƙasa tana tuna baya. Matar da ta ƙirata ta ci mata mutunci yau ga shi tana bata hakuri. Murmushi ta yi ta ce.
"Babu komai Umma, dama Allah yariga ya rubuta haka."

"Ya gida ya mutane gidanku."

"Duk lafiyarsu ƙalau."

Ta amsa. Sun dan jima suna hira tun Nuratu bata sakewa har ta sake, Umma ta cika musu guri da kayan ciye ciye, Nuratu ba komai ta ci dan ji ta yi komai ya fita a kanta. Wajen karfe biyar suka mata sallama suka raka Col Ahmad sashen amaryarsa suka sake musu sallama suka tafi.

Gida suka koma, ruwan zafi ta haɗa ta gasa jikinta ko zai daina ciwo. Bayan ta yi sallah ta kwanta ta rufe jikinta har saman kai, jiri da mugun zazzaɓine ya rufeta, ga yunwa amma komai ta tuna tashin zuciya take ji. Haka Dr Awwab ya dawo ya sameta, saman gadon ya hau ya yaye bargon ya ga barcin wahala take. Jikinta ya taɓa ya ji da zafi rau, bargon ya mayar mata zuwa kafaɗunta ya sauka ya shiga ɗakinsa ya ɗauko magani da ruwa ya fita. Kitchen ya shiga ya haɗamata tea ya koma ɗakinta.
Bakin gadon ya zauna ya fara tashinta, da ƙyar ta farka ya lallaɓata ta sha kaɗan ya bata magani ta sha ta koma ta kwanta ya rufeta. Barcin kirki bai yi ba ranar duk motsinta yana tambayarta lafiya, cikin dare zazzaɓin ya sauƙa ta samu barci.

Washegari da sauƙi amma haka ya sata ta shirya suka nufi asibiti, duk yadda taso haka ya ɗauketa suka shiga ciki. A office nasa ya zaunarta ya ƙira abokinsa ya zo asibitinsu. Bayan ya dubata ya ɗebe jininta zai mata test gobe zai kai masa gida, daga nan ya musu sallama ya tafi.
Dr Awwab bai yi aiki ba ya koma ya ci gaba da kula da Nuratu, duk da jikinta da sauƙi sai jiri wanda kuma rashin cin abinci ne.

Da daren Nuratu ta samu ƙiran Mami. Lokacin tana kwance jikin Dr Awwab yana lallaɓata ta sha maltina da peack na ruwa da ya haɗamata, don Doctor ya ce jininta ya hau shi yasa ta ke jin jiri kuma da rashin ci. Wayar ya jawo ya saka mata a kunne yana cewa Mami ce.
Bayan ta mata sallamarta ta gaisheta ta amsa, sannan ta sako mata zancen da ya sa ta ƙirata. A zabure ta miƙe har ra kusa bige cup ɗin hannun Dr Awwab tana cewa.

"Da gaske Mami?"

...

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE  60.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

"Yi a hankali mana."

Faɗin Dr Awwab yana ajiye cup ɗin hannunsa sannan ya riƙota. Jikinsa ta faɗa ta sa masa kuka, duk ya rikice yana tambayarta menene, sai da tayi mai isarta ta ɗago kanta tana kallonsa kafin ta ce.

"Na gode sosai Hayat, bani da abin da zan saka maka da shi."

Hannunsa ya sa ya tallafo kumatunta.

"Me ya faru don Allah duk kin tayarmin da hankali."

Fuska duk hawaye ga dariya ta ce.
"Ka biyawa Kawu Muhammadu zuwa Umrah har jibi zai tafi, yanzu Mami ta faɗamin. Amma shi ne ba ka taɓa faɗamin ba."

Ta faɗa tana haɗa rai.
Leɓɓenta ya sumbata yana jan hancinta ya ce.
"Ai badan ke nayi ba balle ki sani. Oya zo kisha kar ya huce."

Ya ce ya ɗauki cup ɗin ya kai bakinta. Murnar da take ciki ya sata sha sosai, sai da tace masa ta fara jin amai ya rabu da ita.
Ranar wuni ta yi cikin farin ciki, yayunta duk sun ƙira suna cewa ta miƙa godiya ga Dr Awwab, haka Kawu Muhammadu ma da maganar ta zo masa ba za ta ya ƙirata.

Haka su ka cinye wunin, da daren wani mugun zazzaɓi irin na daren jiya ya ƙara lullubeta, duk taimakon da zai bata ya bata kafin wayewar gari ta ɗan ji dama dama. Tuni ya harbo jirginta, amma bai sanar mata ba yafi son sakamako ya nuna.

Da safe ta farka da ji sauƙi sai jiri da ta ke ji. Maganar girki kam babu sai fita yayi ya siyo musu dan ya hanata yin aikin komai.
Shi ya taimaka mata ta yi wanka ta saka doguwar riga ta kwanta a falon. Tea ya haɗamata da ƙyar tasha kaɗan ta koma ta kwanta, duk ta zama so weak, gaɓoɓin jikinta duk ciwo.

Ƙarfe sha ɗaya yana zaune saman kujera ta yi matashi da cinyarsa idanuwanta lumshe tamkar mai barci, jinta take tamkar ta yi ta kuka. Yadda yake shafa mata gashinta tana ɗan jin sauƙin abin da take ji. Kallon tv yake amma hankalinsa yana kanta, gaba ɗaya tausayinta yake ji, ya lura irin masu shegen laulayi ne, danma ba ta amai kuma tana ƙoƙarin cin abu me ruwa, abinci kam rabonta da shi tun shekaran jiya.
Ƙarar wayarsa ya sa shi duban wayar da yake saman Center, Nuratu ta buɗe idanunta ta dubesa. Ɗauka yayi ya ga mai ƙiran, ya kalleta kafin ya ɗaga wayar ya amsa.

"Ina zuwa."

Kawai ya faɗa ya kashe wayar, ɗaga Nuratu ya yi yana kallonta ya ce.
"Dr Sageer ne, za ki iya fita."

Kai ta ɗaga masa ya taimaka mata ta miƙe tsaye, mayafi ya saka mata yana riƙe da ita suka sauƙa ƙasa. Saman kujera ya zaunarta ya fita ya shigo da Dr Sageer. Bayan sun gaisa, Nuratu ta gaishesa ya amsa yana ciro result ya miƙawa Dr Awwab.

"Congratulations Doctor, you're lucky."

Da murmushi Dr Awwab ya amsa musabahar da ya masa yace.
"Thank you Doctor Sageer."

Ita dai Nuratu ta zama ƴar kallo ta kasa fahimtar su. Dr Sageer ne ya kalleta ya ce.
"Congratulations Madam you're pregnant."

Zut ta ji maganar ya shigeta, sai kuma ta ji kunya ta sunkuyar kanta ƙasa ta kasa yin magana. Dr Awwab ne ya tashi ya isa wajenta ya rumgume.

"Thank you My Baby."

"Umuhm."

Dr Sageer yayi gyaran murya, hakan ya ankarar da Dr Awwab ya sake Nuratu. Miƙa masa wani paper ya yi.

"Prescription na drug ɗinta, maganin da zai taimaka mata jininta ya sauƙa da kuma wanda zai sa ta cin abinci. Sai kuma zazzaɓin dole sai cikin ya yi ƙwari za ta samu sassaucinsa. Allah ya raba lafiya Madam."

Murmushi kawai ta yi Dr Awwab ya masa godiya tare da masa rakiya har waje ya dawo. Ɗaukar Nuratu ya yi cak suka koma sama. A gaba ya sa ta yana kallo tare da yin murmushi ya kasa faɗin komai.

"Kallon fa? Ko Babyn za ka hango."
Ta faɗa da murmushin kunya.

Fuskarta ya shafa yana murmushi shi ma.
"Da zan hangosa zan fi kowa jin daɗi. Wani abu kawai yake bani mamaki."

"Na me fa?"

Kwantarta ya yi a cinyarsa ya riƙo hannunta.

"Haka ki ke da dagiya, sai da ki ka dage ki ka samo sakamako mai kyau tun wata ɗaya bai rufe ba, sati uku fa. Shi kuma ya nuna mahaifinsa yana tafe ya bayyana kansa da wuri."

Dukan wasa ta kai masa a kirji, cikin shagwaɓa ta ce.
"Bana so Allah."

Yana murmushi ya rumgumeta yace.
"Babyna mamar Babyn."

"Sai ka dai na ƙirana da Baby."

"Har abada ke Babyna ce."
Ya ce ya sunkuya ya sumbaci leɓɓenta.

Da daren har gida ya taka ya sanar da Ummi cewa suna buƙatar mai taimakawa Nuratu bata jin daɗi. Fadar haka Ummi ta gano nufinsa abin ka da manya.

"Zan yi wa Hajjo magana ta baku aron ƴarta Batula kafin ta sauƙa lafiya."

Murmushi Dr Awwab ya yi ganin Ummi ta fahimci zancensa. Sallama ya musu akan su taho da Hanan tare tunda biki ya ƙare.
Daga nan gida ya koma ya ci gaba da kula da matarsa.

Washegari Batula da Hanan suka taho tare, ɗakin ƙasa ta zauna. Ita ke shara da goge goge sai girki, ba laifi ta iya komai.
Hassana da Hussaina sun zo dubata tare da mazajensu, anan Hussaina ta sanar mata jibi za su wuce Ibadan. Daga kallonta tasan ta kwantar da hankalinta ta fara son mijinta. Wuni guda suka mata har dare kafin su tafi.

...

Bayan sati biyu allahamdulillahi Nuratu ta fara jin sauƙin jiri sai zazzaɓi da kuma ciwon jiki. Har lokacin ba ta son cin abun kirki duk ta rame sai haske da ta yi. Dr Awwab yana bakin ƙoƙarinsa na ganin ta samu dukkan kulawa, baya fita aiki da wuri, idan ya fita kuma da wuri zai dawo.
A gida babu wanda yasan tana da ciki, Dr Awwab ya kasa sanar musu ita ma kuma haka.

...

Yau Kawu Muhammadu ya kammala aikin Umrah bayan tsawon sati uku da ya ɗauka. Ya so wucewa gida Dr Awwab ya riƙesa tun da jirgin Nigeria ya bi ya zo kamar yadda ya tafi, haka idan zai dawo ma a jirgin Maiduguri zai dawo, to ya sauƙa a gidansu, idan ya huta zuwa kwana biyu zai bada mota a kaisa har gida. Da ƙyar ya yarda ganin nauyin zai masa yawa.
Da yamma jirginsu ya sauƙa a Maiduguri. Dr Awwab da kansa ya je ya ɗaukosa ya kaisa gidan su. Har ɗakin da ya tanadar masa ya kaisa dan huta gajiya. Bayan ya huta Nuratu da Hanan su ka zo gaishesa, sun jima suna hira kafin su barsa ya huta, Batula ta kawo masa abinci da abun sha.

....

Dubanta yake sai ɓata fuska take yi, tun jiya ya lura da ita kamar akwai abun da yake damunta. Balle kuma yanzu da ya kawa mata maganar tafiya. Ita kuwa taƙaici goma da ashirin ne ya haɗe mata.

"Ni fa bana jin daɗi balle ayi tafiyarnan. Balle ma me abun sai mun masa sannu da zuwa har gidanta. Bayan haka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login