Follow us on social media
Showing 27001 words to 30000 words out of 148866 words
Chapter 10 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
sauran suka kwashe da dariya.
***
Mami ta mugun shiga tashin hankali marar misaltuwa, ta ka sa zama ta ka sa nutsuwa, hawaye kawai take fitarwa tana addu'a Allah ya sa Nuratu tana hali mai kyau. Haka Munirat ma da dauriya kawai take.
Sun je gidan Aunti Zarah babu Nuratu, ta ƙira Amma Jidda babu Nuratu, ta ƙira Rukayya Aunti Rahma da Hasiya duk Nuratu ba ta je musu ba. Kawayenta biyu ta sani kuma ba ta tunanin za ta je musu ba tare da izininta ta ba, har ta kai karfe goman dare bata dawo ba. A ranta kawai ji take an sace mata Nuratu.
***
Sai washegarin da kusan azahar iyayen Mufid suka san baya gidan, shima sai da ya ƙirasu da wayar ɗan sanda ya mishi ƙaryar abinci zai kira a kawo mishi. Anan ya ƙira Daddyn shi ya sanar dashi yana police station an kama shi. Sababi da faɗa Alhaji Kashim Mufid ya hau yi kafin ya sanar da shi yana zuwa yanzu.
Ummu kawai ya sanarwa ya kaɗa babban rigarshi ya fita. Rufaida da take zaune kusa da Ummi jin an kama Mufid yana Division ta shiga ruɗani.
"Kar dai fyaɗe ya yi wa Nuratu?"
Cikin sauri tambayar yazo kanta, da sauri ta miƙe ta shige ɗakinta, kukan da take dannewa ta fashe dashi. Shikenan dalilinta rayuwar Nuratu ya lalace, addu'a take da fatan Allah yasa ba haka bane wani abun daban ya aikata.
...
Nuratu bata farka ba bata san in da kanta yake ba har ƙarfe goman safe, Nurse da take kula da ita ta gama duty nata ta sanar da Dr Sadiq ya canza wata bayan ya duba jikin Nuratu, drip ɗin ya ƙare ya canza mata wani, yana mamakin har yanzu bata farka ba balle ta sanar da su iyayenta a sanar da su dan ya san zuwa yanzu hankalinsu a tashe yake.
***
"Uban waye ya ce ba za'a ba da bailing ɗana ba? Fyaɗe to kanshi aka fara ko kanta aka fara? Shi waye da zai hana ba da bailing ɗin a sanar da ni wanene shi. In Kuɗi yake buƙata ko nawa ne ya sanar da ni in bashi ya a sakar min ɗa na?"
"Ni ne nan na hana."
Gaba ɗaya suka juya gurin Ahmad da isowar shi kenan ya juyo maganganun Alhaji Kashim Mufid.
"Kai waye? Kuɗi ka ke buƙata ko menene? Ka sanar da ni zan baka ko nawa ne ka saka a fitar min da yaro."
Faɗin Alhaji Kashim Mufid.
Guri Ahmad ya samu ya zauna cikin kujeran ofishin yana nuna kanshi da yatsar shi manuniya.
"Ni Col. Ahmad Tafida bana buƙatar kuɗinka domin za su maka amfani, ka shirya sammaci kawai domin yau ba gobe ba court za'a taru mu."
Cikin faɗa Alhaji Kashim ya miƙe.
"Ka isa? Wallahi baka isa ba! amma ba komai muje mu gani waye zai faɗi, ina jiranka."
Daga haka ya sa kai ya fita ko ta kan Mufid bai bi ba ya bazama neman lauya da zai kare ɗanshi kamar kull dan ya lura wannan yaron yana neman shiga masa hanci.
Bayan fitar Alhaji Kashim, Ahmad ya kalli DPO Salisu.
"Thank you da ku ka bi magana na, ina son a tura mu court zuwa gobe, zan je duba jikin yarinyar sannan in sanar da iyayenta in sun zo su shirya."
"Babu komai Sir Allah taimaka."
Cewar Salisu sali yana mamakin ƙarfin hali irin na Ahmad da ya jajirce sai an kwatarwa Nuratu haƙƙinta. Ko ba komai ya burgeshi dan da wuya shari'a na fyaɗe yake faruwa a ɗauki mataki a yanzu.
....
Asibiti kai tsaya Col. Ahmad ya wuce dan duba jikin Nuratu, ɗakin da take ciki ya leƙa ya samu Nurse zaune kusa da ita.
"Ya jikinta bata farka ba?"
Ahmad ya tambayi Nurse ɗin yana ƙarasa bakin gadon.
"Eh tun jiya har yanzu."
Ta bashi amsa.
"Iyayenta fa? Har yanzu? Sun samu labari?"
Yace yana kai kallonshi kan Nuratu da bata san wani duniya take ciki ba.
"A'a ba wanda ya zo a matsayin nata har yanzu?"
Shuru Ahmad yayi kafin ya fita a ɗakin ya wuce office din Dr Sadiq Shima dai maganar ɗaya ne har yanzu babu wani nata da yazo. Ya tambayi jikinta yace sai ta farka za su ga yanayin.
Har karfe uku kafin Ahmad ya kama hanyar Maiduguri dan gudun fushin Umma.
***
"Officer yarinyana tun jiya da ta fita dan zuwa makaranta bata dawo gida ba, na duba duk in da zan duba mun bincika amma babu labarin ta."
Mami ke wannan bayani tana sharan hawaye da idanuwanta da suka kumbura tsabar kwana da tayi tana kuka. Safiyar yau ya sameta a police station dan ba da report ko zasu taimaka mata.
#vote
#comments
#share
MADUBIN GOBE 15.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Me ye sunanta da shekarunta da kuma unguwa?"
Faɗin ɗan sanda da yake ɗaukar rohoto.
"Sunanta Nuratu Mamman Bashir, shekarunta ashirin tana unguwar nan."
Faɗin Mami hawaye wani yana bin wani.
Report suka ɗauka da komai na dangane da Nuratu da lokacin fitarta kafin su sallame Mami cewa Insha Allahu zasu yi ƙoƙari akan maganar.
Mami gidan Aunti Zarah ta nufa tana kuka ta sanar da ita har yanzu Nuratu ba ta dawo gida ba kuma ta ƙira kowa bata tare dashi.
Tashin hankali Aunti Zarah ta shiga, shuru kawai tayi ta rasa abinda za tace kafin ta hau lallashin Mami.
...
"Ina son ganin Mufid Kashim Mufid domin mishi tambayoyi."
Faɗin lauya da Alhaji Kashim ya ɗauko har zuwa Division dan a fitar masa da ɗansa. Ba musu DPO Salisu ya ba da umarni aka ciro Mufid ya zo. Tambayoyi lauya ya mishi akan abinda ya sani. Buɗar bakin shi yace ya aikata abinda lauya baya son ji kenan. Haka ya saka AA da Faisal gaba da tambaya dukka cewa suke ba su yi ba su. Sallamar su yayi aka mai da su cell.
"Yara dai sun ce basu aikata ba. Dan haka wannan abun ya zama tuhuma a bamu belin su kafin a shigar da ƙaran koto a saka ranan zaman shari'a, na maka alƙawarin su Mufid za su halarci wannan zaman domin ni ne lauyan da zan kare su."
Faɗin lauya bayan an shigar dasu Mufid cell.
DPO cike da mamakin ƙaryar su Mufid yake duban lawyer da yabi bayansu. Sun amsan laifinsu har sun saka hannu a jiya yanzu kuma suce basu aikata ba.
Murmushin taƙaici ya yi.
"Haka suka ce, amma da idona na gani. Ba wannan ba ma, ba zan bada bailing ɗinsu ba sai wanda ya kawo ƙarar ya amince."
"Waye shi?"
Cewar Barrister Auwal cikin jin haushi.
"Zuwa gobe ku dawo za ku haɗu dashi yanzu baya nan."
Ya basu amsa.
"Wani asibiti take yarinyar?"
Barrister Auwal ya nemi sani dan samun ƙarin wani bayanin.
"Mai za ku mata? Gargadinta akan kar tayi ƙara da ku? Ko kuɗi zaku bawa Dr ya ɓoye gaskiyar lamari?"
DPO Salisu yake zuba musu wannan tambayoyin kai tsaye.
Murmushi Barrister Auwal yake kamar maganganun DPO Salisu bai shige sa.
"Ko ɗaya DPO. Tambayoyi kawai zan mata, ina son tabbatar da su Mufid sun aikata laifinsu in nemi hanyar ɓullowa lamarin kafin a shiga koto."
Kamar mai nazari sai kuma DPO Salisu ya sanar da su sunan asibitin da Nuratu take, Alhaji Kashim da lauyan shi Auwal suka nufa can.
***
Ita kaɗai ce cikin duniyar da babu komai sai duhun da ya mamaye, babu kowa sai ita, gabas da yamma ta duba babu wani haske balle hanyar fita, kamar daga sama ta dinga jin kuwar dariyarsu da tashin muryoyinsu cikin kunnuwanta suna ƙoƙarin kusanto ta. Bata ganin mai zuwa dan duhun da yake mamaye da ita, hakan yasa tasa hannuwanta take kai naushi a cikin duhun da bata ganin komai.
A zahirin gaske kuma Nuratu ce da tun farkawar ta take kokuwa da Nurse da Dr Sadiq.
Nurse dake zaune tana lura da ita ta ga ta fara motsi da sauri ta ƙarasa wajenta tana dubata. Buge buge kawai ta fara tana jijjiga gadon da jikinta. Nurse ɗin ta tsorata da ganin haka ta fita da sauri ta ƙira Dr sadiq Tare suka dawo ta sanar dashi abinda ya faru.
Jin muryoyinsu shi ya ƙara rikita ƙwaƙwalwar Nuratu ta fara kuka tana bugunsu tamkar mahaukaciya dan ganinsu take kamar su Mufid, abin da suke faɗi kuwa jinsu take kamar kalaman su Mufid suke maimaitawa yayin da suke saman kanta.
Sai da taimakon Nurse biyu mata suka danneta Dr Sadiq ya samu ya mata alluran bacci ta sulale ta kwanta a gadon.
"Hauka take ko me?"
Su ka tsinci muryar Lauya Auwal a baƙin kofar ɗakin da sauri suka juya dan babu wanda ya ankara da shigowarshi.
"Ba hauka take ba. Who are you?"
Faɗin Dr Sadiq ya kalli Nurse.
"Kar ki bari kowa ya shigo ɗakin har sai iyayenta sun bayyana."
Daga haka ya fita yana rufe ƙofar Auwal ya bishi da sauri.
"Gurin ka na zo Dr."
"Biyo ni office ɗina."
Yace yana yin gaba.
Bayan ya shiga ya zauna Auwal da Alhaji Kashim suka shigo tare, hannu suka miƙa masa ba musu ya amsa su ka yi musabaha.
"Ina jinka?"
Cewar Dr Sadiq.
"Iyayenta fa? Ba su da labari?"
Barrister Auwal ya faɗa.
"Yes." Dr Sadiq ya bashi amsa.
Gyaran muryar Barrister Auwal ya yi.
"Akan rape case ɗin Mufid Kashim Mufid ne na shekaran jiya an kama su sun yi, yarinyar tana asibitin nan. Ko dai ita ce wannan mai haukan?
Shin dagaske ka ga alamar fyaɗe a tattare da yarinyar ko kuma da son ranta a ka mata haka? You know what i mean you're a doctor."
Wani kallo Dr Sadiq ya ke masa yana juyi saman kujeransa har Barrister Auwal ya gama magana kafin ya gyara zaman kujeransa yana fuskantar shi.
"This is rape case, rape ne da na jima ban haɗu da irinshi ba, ba zan baka any proof ba dan nema maka hanyar kare masu laifi, mu haɗu a koto kawai.
Sannan yarinya yes tana hauka, tana hauka ne bisa abinda ɗanku ya mata, but inshaAllah zuwa nan da wani lokaci muna sa ran samun sauƙinta a shiga koto. And you can go out please."
"Haka ka ce?"
Cewar Alhaji Kashim da sai lokacin yayi magana.
"Yes akwai wani abun?"
Dr Sadiq ya ce yana watsa masa wani kallo.
Alhaji Kashim zai faɗi wani abun da sauri Barrister Auwal ya tare shi.
"Mu je Alhaji za mu san yadda zamu ɓullowa lamarin."
Bayan fitarsu Dr Sadiq ya cire eyeglasses ɗinsa, halin da Nuratu take ciki ya faɗa tunani. Ya kamata ƴan uwanta su san halin da take ciki musamman mahaifiyarta.
Abinda ya faru da ita yayi ƙoƙarin taɓa mata lafiyar ƙwaƙwalwarta da tana bukatar taimakon gaggawa.
....
Alhaji Kashim Mufid da Barrister Auwal Division su ka koma. Bayan sun zauna da DPO Salisu, Barrister Auwal yace.
"Muna son magana da wannan yaron da ya kawo karan."
"Sai dai gobe ku dawo idan ya shigo zan sanar dashi ya jira ku."
DPO Salisu ya basu amsa yana mamakin ƙarfin halinsu da su ka jajirce sai an bada belin su Mufid ko duba da laifin da suka aikata basa yi.
"Shikenan ka tabbatar ka sanar dashi dan Allah."
Barrister Auwal ya faɗa daga haka suka fita Barrister Auwal yayi ta kwantarwa Alhaji Kashim hankali akan zuwa gobe zai san yadda ya ɓullowa lamarin tun da dai yarinyar bata hankalinta za su samu bailing su Mufid, maganar shiga koto dole za'a jingina a gefe har sai ta warke.
***
Hijabinta kawai ta zurma saman kayan jikinta ta fita waje ko duba lokaci ba ta yi. Adaidaita ta shiga ta sanar dashi in da zai kaita, tafe suke tana sharan hawaye tausayin halin da Nuratu take ciki take.
Tana jin sadda Daddyn su yake sanar da Ummu yadda aka yi. Ba abinda yafi ɗaga mata hankali sai jin Nuratu bata hankalinta ga har yanzu iyayenta basu da labarin, ta gwammace ta sanar dasu ko da rabin abinda ta sani ne.
Ba tasan sun shiga unguwar ba sai da mai adaidaita ya sanar da ita wani layi za su shiga ta ankara ta sanar dashi, har ƙofar gidan su Nuratu ta nuna mishi ya sauƙeta ta bashi kuɗin kafin ta shiga cikin gidan da sallama.
Munirat ita kaɗai ne a gidan ta amsa tana shimfiɗa mata abin zama dan ta ganeta.
"Mami bata nan."
"Bata nan tana gidan Aunti Zarah."
Cewar Munirat.
"Ko gidan da nisa ina son sanar da ita wani abu ne."
"Kin san inda Nuratu take?"
Ta tambayeta da sauri.
Idanuwan Rufaida cike da hawaye tace.
"Ban sani ba amma ina tsammani na kusa sani."
"Dagaske, tashi mu je."
Munirat tace da sauri ta miƙe suka fita, sun samu Mami na ƙoƙarin barin gidan suka isa Rufaida ta sanar da ita cewa ta san dai Division da suka san in da take, su za su san asibitin da take, kwata kwata ta kasa sanar dasu abinda ya faru balle su ji haushinta.
Mami, Aunti Zarah da Munirat suka nufi station ɗin Rufaida ta koma gida ganin anyi magriba. Tafiya suke zuciyar Mami bugawa yake burinta ɗaya abinda take hasashen ya faru da Nuratu addu'a Allah yasa ba haka bane.
Bayan sun gabatar da kansu shi kan shi DPO Salisu ya yarda ita ce mahaifiyar yarinya duba da yadda take fitar da ruwan hawaye ga kamanni, anan ya haɗasu da investigator Lawan ya ɗauki information na su kafin ya musu rakiya zuwa asibiti akan in sunje Dr ya sanar da su abinda ya faru dan su ma sun gagara sanar da su. Abin ne da ciwo.
Suna isa asibitin kai tsaye ɗakin da take ciki suka shiga basu jira fitowar Dr Sadiq da aka ce yana ciki ba. Yarta ta hango ana ɗirka mata allura sai rirrike ta ake tamkar mahaukaciya dan buge buge take.
Salati Mami ta saka tana fashewa da kuka da sauri ta ƙarasa wajen Nuratu tana ƙiran sunanta, hakan shi ya ƙara hargitsa kan Nuratu ta dinga wani kuka kamar ba ita ba, wani ihu ta fasa tana neman kwace kanta dan tun jiya in sun mata alluran ji take kamar ranta zai fita, ga hannu da ya kumbura da ciwo ko zafin shi ba ta ji.
"Mama ku fita dan Allah."
Dr Sadiq yace bayan ya samu ya yiwa Nuratu allura ya riƙeta yana son bacci ya ɗauketa.
Kasa motsi Mami ta yi jiri yana neman ɗaukarta da sauri Aunti Zarah ta riƙeta suna ganin ikon Allah. Domin ana yiwa Nuratu allura bata jima ba bacci ya kwasheta.
"Mu je waje."
Dr Sadiq yace bayan ya kwantar da Nuratu yayi gaba su ka bishi a baya har office ɗinshi.
"Menene haɗin ki da ita?"
Dr Sadiq ya tambaye Mami da take jin kamar ta zauce dan tashin hankali.
"Yarta ce, tun shekarsn jiya take nemanta daga fita makaranta bata dawo ba."
Aunti Zarah take wannan bayani dan Mami ta kasa magana sai kuka da take yi.
"To allahamdulillahi tun da kun samu labari, dan yau kwana biyu muna jiran ta dawo hankalinta ta sanar damu inda iyayenta suke amma abin ya gagara, dan a birkice take farkawa domin abinda ya faru da ita yana neman shafan ƙwaƙwalwarta."
"Me ye faru da ita Dr. Bani da labarin komai."
Cikin sauri Mami ta tambaya sai lokacin ta iya magana.
"Baku da labari?"
Dr Sadiq ya tambayesu cike da mamaki.
Kai kawai suka ɗaga masa.
Nauyi bakinsa ya mishi da kyar ya furta.
"Fyaɗe aka mata wasu samari uku, yanzu haka suna kame domin wanda ya taimaka mata ya saka an kamasu sai an bi mata haƙƙinta."
Numfashin Mami ne ya tsaya cak cikin tashin hankali, da kyar ta samu tayi kokuwa dashi ta fara shaƙa, hawayenta ya kafe zuciyarta ya bushe tana duban Dr da gani take tamkar a mafarki yake faɗa mata haka.
A hankali take furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihin rajiun.
Aunti Zarah da take kuka ita ma ta kasa magana domin ba su san mai za suce ba.
Ganin halin da suke ciki Dr Sadiq yayi ta kwantar musu da hankali duk da ya san da wuya hankalinsu ya kwanta. Ƙarshe yace.
"Za ku iya shiga ku zauna da ita mu ga zuwa tashin ta."
Miƙewa su ka yi suka fita basu iya mishi godiya ba Mami ta wuce ɗakin Aunti Zarah ta tsaya magana da investigator Lawan.
Mami idanu kawai ta zubawa Nuratu mata duk ta hargitse gashin kanta duk ya warware. Kallo ta bita dashi gaba ɗaya ta canza cikin kwana biyun. Kifa kanta tayi jikin gadon ta fashe da kuma mai cin rai.
Shikenan rayuwar ƴarta ya lalace akan wani yaro. Basu da wani gata da ko kuɗi da zai kwata musu haƙƙin su sai Allah. Kuka take har maganganun zuciyarta yana fitowa waje taji an dafata.
"Kiyi hakuri Hajiya Sadiya ƙaddarar ta kenan, ke in ta farka ta ganki wannan halin a hakan za ta ji kwanciyar hankali a duniyar ta."
"Ki bar ni nayi kuka Zarah, rayuwar yata ya lalace, duniyarta ya tarwatse, farin cikinta ya gushe, maza uku fa? Nuratu nawa take? ko namiji ɗaya ya mace take ji balle maza uku! Tsakani na dasu sai Allah ya isa domin ba zan taɓa yafe musu ba. Bamu da wani gata ko kuɗi da mulki da zai kwatawa ƴata haƙƙinta, sun riga sun cuce ta sun cuce ni."
"InshaAllah Allah ya nan zai taimaka mana."
Shuru kawai Mami take tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.
"Ƙira min Munirat taje gida ta kwaso mana kayanmu da duk abin buƙata."
"Bari mu je mu dawo."
Aunti Zarah tace ta fita suka wuce gida da Munirat tare bayan sun kwaso komai Aunti Zarah ta wuce gida dan har lokacin Nuratu bata farka ba.
***
Washegarin ranar Ahmad bai samu zuwa ba sai wajen sha ɗaya, bai isa asibitin ba ya fara wucewa station dan tun safiya ya samu labarin ana neman shi. Anan ya tarar Barrister Auwal ya iso tare da Alhaji Kashim.
Kallo ɗaya ya musu ya zauna yana gaisawa da DPO.
"Belin Mufid suke buƙata Col. Ahmad."
"Akan wani dalili?"
Yace yana ƙara haɗa rai.
"Akan dalilanmu. Na farko dai alƙawari na maka in an tashi case ɗin nan za'a shiga kotu da kai na zan kawo su Mufid domin za muyi yarjejeniya kowa ya saka hannu ka ga babu batun yaudara. Na biyu kuma yarinyar da ake case a kanta har yanzu iyayenta basu bayyana ba, sannan bata cikin hankalinta balle ta bada shaidar eh an mata fyaɗe a'a ba'a mata ba. To ka ga ana buƙatar lokaci dan samun lafiyarta. Shine nake neman alfarma a bamu belinsu dan Allah Sir a taimaka."
Barrister Auwal ya ƙarasa maganar cikin kwantar da kai da roƙo.
Col. Ahmad kallon DPO Salisu yayi kafin yace.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 16.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
****
"Sir! Za'a iya bada bailing su sai har yarinyar ta warke a shigar da ƙara kotu, muna da every record na case ɗin nan kuma na maka alƙawarin babu abinda zai canza a ciki Insha Allahu. Kuma za muci gaba da zuwa dubata har ta samu lafiya muna