Follow us on social media
Showing 51001 words to 54000 words out of 148866 words
Chapter 18 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
sai azahar za tayi wanka.
A falon ta samu Mami ta farka, Munirat har ta ɗaura abincin rana dan sha ɗaya ta gota. Bayan ta gaishe da Mami ta ci abincinta da har yayi sanyi. Anan ta sanar da Mami cewa Ahmad yana zuwa gobe.
"Wannan yaran dai basa gajiya da zirga zirga. Ke kuma kin zuba musu ido ba za kiyi abu ɗaya ba kowa ya huta."
"Ni kuma Mami mai zan musu. Duk wanda ya gaji ya hakura kawai."
Nuratu tace tana tauna abincin bakinta.
"Au haka kika ce. Shikenan ni zan zaɓa miki wanda ya dace dake."
"Waye? Yaya Al-ameen?"
Nuratu ta tambaya.
Mami ta girgiza kai, Nuratu tace.
"Dr Awwab?"
Nan ma ta girgiza kai.
"Limamin unguwar nan zan haɗa ki dashi."
Mami tace tana dariya ganin yanayin fuskar Nuratu ya canza amma jin maganar Mami ta faɗa ya sata fashewa da dariya har tana neman faɗuwa.
"Ki dai yiwa kan ki faɗa. Kiyi ta addu'a Allah cire miki mafi alheri a cikin su."
Mami ta faɗa haka bayan ta tsagaita dariyarta ta miƙe ta bar mata gurin.
Kullum dai magana ɗaya, aure, aure, ba za'a barta ta ji da abinda yake damunta ba, ko gaba basa dubawa abin da zai biyo baya bayan auren.
Bayan ta gama cin abincin ta kwanta sai azahar tayi wanka ta fito. Ranar haka ta wuni a gida babu inda ta je. Da dare ita ta musu abincin dare dan hutar da Munirat da ake shirin aurenta a ƙauyen Buni Gari dan har an bada ita ga ɗan uwansu da yake aiki a birni, har gidan Mami yake zuwa hira wajenta. Kuma ba laifi Mami ta yaba da hankalin shi.
***
MAIDUGURI.
"Yaya Awwab!"
Hussaina tace da ɗan saurinta dan ganin zai shige mota. Jin ƙanwarshi na ƙiranshi ya sashi dakatawa yana dubanta.
"Yaya Awwab da ma nace kuɗin da kace zaka bani ne na siyayyar Hanan."
"Oh na mance. Zan miki transfer."
To tace ya wuce ta koma cikin gida, wajen sha biyu ta samu saƙon kuɗin daya turo mata na siyayyar Hanan da yana ji yana gani ta fara ƙin zama gurinshi sai gidansu ba kamar da ba.
Tare da Hanan su ka je da Hassana su ka mata siyayya.
Da dare da ya dawo suke nuna mishi yace babu komai. Ummi dake gefenshi tana kallonsu ta saka baki.
"Tun da dai taƙi zama sai kayi ƙoƙari ka ajiye mata in kana son ta koma."
Murmushi Dr Awwab yayi.
"Ummi har yanzu taƙi bani damar gabatar da kai na a gida."
"Mata kenan, hakuri za kayi ka bita da sannu za ta amince."
Ummi tace kasancewar ya riga ya sanar da ita ga wacce yake so duk da ya ɓoye mata sirrin Nuratu da yake ganin bai dace kowa ya sani ba. Ummi tayi na'am da buƙatar shi fatanta Nuratu ta amince ta auri ɗanta ta maye gurbin Nusaiba da ya rasa.
Murmushi kawai Dr Awwab yayi ya mata sallama ya suce gidanshi, da babu kowa sai mai mishi gadi, ya sallami duk masu kula da Hanan dan taƙi zama.
***
DAMATURU.
Cikin takama ya shigo Companyn da yayi bincike ya samu nan ne wajen aikinshi da ya san ta wannan hanyar kaɗai zai amince da buƙatarshi.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 27.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Tunda ya samo bayanin sa yana sauraran shi har ya gama kafin ya gyara zaman gilashin idonshi.
"Kar ka damu Alhaji Kashim wannan abun tamkar anyi an gama domin in dai akan kuɗi ne Alhaji Mamman zai iya komai ballantana abin da ya shafi aikin shi."
"Kana gana babu wani matsala da zai biyo baya."
Alhaji Kashim ya tambayi Oga Dauda jin yayi saurin amincewa da buƙatarshi.
"Kana kokonto ne? Ni na san waye Alhaji Mamman. Tashi muje idanuwanka su baka shaidar haka."
Daga haka suka fita dukkansu zuwa ofishin Alhaji Mamman Bashir, yana tsaka da aiki ya samu baƙoncin su. Kallon kallo su ka yi tsakanin Alhaji Kashim da Alhaji Mamman.
"Mai kuma ya kawo ka ofishi na?"
"Laifi ne dan mutum ya zo wa da ɗan uwanshi alheri?"
Alhaji Kashim yace yana zama cikin ɗaya daga kujerun dake ofishin bayan zaman Oga Dauda.
Alhaji Mamman kallon Oga Dauda yayi yana neman ƙarin bayani dangane da maganar Alhaji Kashim, fahimtar haka ya saka Oga Dauda gyara babban riganshi.
"Alheri Alhaji Kashim ke tafe dashi Alhaji Mamman. Buƙatarshi ɗaya ne zaka biya masa ka samu alheri mai yawa ban da ƙarin girma da zai biyo baya ta ɓangare na."
Ya faɗa yana nuna kanshi.
"Mai ka ke buƙata?"
Tambayar Alhaji Mamman ga Alhaji Kashim yana binshi da kallo. Kuɗi da mulki ya zauna a jikin Alhaji Kashim sosai, duk tinkahon arzikin shi ashe akwai wanda ya fishi. Shaddar jikinshi ma kaɗai abin kallo ne.
"Auren ƴar ka nake nemawa ɗa na Mufid."
"Wace ƴar? Ba zai yiwu ba."
Alhaji Mamman ya tambaya da sauri tsammanin sa duk Ameera ce ko Walida.
"Mai ka ke sauri haka? Wannan yarinyar auren ɗa na shine rufin asirinta ko baka ganin hakan?"
Alhaji Kashim ya ce ga Alhaji Mamman da yake binshi da wani kallo.
"Kana nufin ƴar wajen Sadiya?"
Ya tambaye shi dan neman ƙarin bayani.
"Wacce dai aka yi shari'a da ita shekaru huɗu da suka wuce. Nuratu take kowa?"
Shuru Alhaji Mamman yayi a ranshi yana jin zafin Nuratu da duk ƙoƙarin shi na ganin ya rabata da rayuwarshi abin ya gagara. Ance masa itace silar ƙarayar arzikin shi gashi yanzu kuma dalilinta arziki na tunkaro shi da in yayi wasa, zai rasa baya ya rasa gaba.
"Tunanin mai ka ke Alhaji Mamman? Babu batun takura, kayi tunani a kai."
Faɗin Alhaji Kashim yana miƙewa tsaye tare da saka hannu cikin aljihunsa ya ciro tailan kuɗi da tun a gida ya saka hannu na miliyan biyar. Ajiye masa saman teburin shi yayi.
"Ga wannan na bani lokacin ka da kayi mu kayi magana, ina jiran amsar ka, duk shawaran da ka yanke ka sanar da Ogan Dauda sai na jika."
Daga haka suka fita Alhaji Mamman ya bisu da kallo kafin ya juyo da hankalin shi kan tailan dake ajiye ya ɗauka ya gani.
'Milayan biyar.'
Ya faɗa da sauri yana ajiyewa sai kuma ya miƙe tsaye kafin ya ƙara komawa ya zauna.
Ya ma rasa wani irin tunani zai yi bisa wannan lamari da yake tunkaro sa na wannan yarinyar da bai taɓa jin sonta a matsayinta na ƴarshi ba.
***
Ƙarfe biyu ya shigo cikin Damaturu bayan ya gabatar da sallar azahar ya ƙarasa gidan, ya gaishe da Mami har cikin falon kafin ya fito waje in da Nuratu ta ajiye musu fararen kujeru a ƙarƙashin bishiyar dake filin gidan.
Bayan gaisuwa tsakanin su shuru ya biyo baya dan nauyin Col. Ahmad take ji sosai. Matsayin babban Yaya ta bashi da take ganinshi tamkar uba dan abinda ya mata a rayuwa ko jinin jikinta albarka.
Maganarshi shi ya dawo da ita hankalinshi lokacin da ta ji ya ƙira sunanta.
"Nuratu!"
Idanuwanta ta ɗago ta kalleshi da su ta juyar kanta tana amsawa bugun zuciyarta na ƙaruwa.
"Sai ki ka ji ina son ganin ki."
"Eh." Ta bashi amsa kanta ƙasa.
"Ya kamata Nuratu in san wasu abubuwa a kan ki, kar kimin fassarar wani abu, hakan na gani ya kamata ko dan gaba, duba da yadda alaƙar mu ya daɗe kuma ina neman ya ƙara ƙarfin da yafi na baya. What i means ina son gabatar da kai na wajen dangin Baba ko Mami a san da zamana?"
Maganganun shi na ƙarshe ya sata ɗago idanuwanta ta kalleshi dashi nashi idanun a kanta.
"Bangane ba?"
Ta tambaye shi dan neman ƙarin bayani da sauri.
Murmushi yayi yace.
"Kin fahimce ni kawai dai kina son basar da maganar ne kuma na lura da hakan tun ba yau ba. So nake ki sanar da ni wanene babanmu ina son zuwa gaisuwa wajen shi ko dangin shi."
Fara'ar fuskarta ne ya ɗauke tana kawar da idonta. Tun da take bata taɓa ji ko ganin labari irin nata dana mahaifinta ba, ba tasan mai ta mishi ba, ba tasan mai ta tsare mishi ba a rayuwa ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata. Da mahaifinta a raye amma ta zamto tamkar wata marainiya marar gata, wani marayan ma tasan ya fita jin daɗi dan tasan ko ya ya dai yaji daɗin mahaifi kafin ya rasashi. Ita fa? Sai dai kallo daga nesa.
Col. Ahmad da ya hango tsantsan damuwa a fuskar Nuratu sai yaji jikinshi yayi sanyi. A ranshi yaji cewa akwai wani abu tsakanin uba da ƴar.
Gyaran murya yayi da ya sata juyowa ta dubeshi.
"Maganganu na sun ɓata miki rai ko?"
Girgiza kai tayi tana ƙirƙiro murmushi ta ɗaura saman fuskarta.
"Ko ɗaya Col. Mahaifina Alhaji Mamman Bashir sunan shi, nima ban gama sanin shi ba saboda sun jima da rabuwa da Mami na."
Iya abinda ta sani ta sanar dashi domin Col. Ahmad ya cancanci ya san komai game da ita har da wanda ita kanta bata sani ba.
Mamaki da al'ajabi su suka cika zuciyar Col. Ahmad kawai ya zubawa Nuratu ido bayan gama sauraron bayaninta tana share hawayen da suka zubo mata. Rayuwarta na baya ne ya dinga dawo mata da ya ƙara saka zuciyarta karaya. Ba dan Col. Ahmad ba da shikenan Mufid yaci bulus a rayuwar ta babu mai kwatar mata haƙƙinta.
Numfashi ya sauƙe har lokacin yana dubanta.
"Shikenan dai na kukan. Muna tare da ke Allah yana tare dake Nuratu, shine gatan ki."
"Haka ne."
Tace tana share hawayenta da yatsun hannunta.
Daga nan hiran ya tsaya kowa da abinda yake saƙawa a zuciyar shi kafin Col. Ahmad ya miƙe.
"Zan wuce kar yamma yayi kin san hanyar garin mu."
"Haka ne Allah kiyaye hanya Nagode sosai ka gaishe da mutanen gida."
Nuratu tace bayan ta miƙe ta ƙira Mami su kayi sallama ya wuce.
Tafiya kawai yake labarin Nuratu na mishi yawo a zuciyarshi tamkar yanzu take bashi. Ta yi ƙanƙanta da fuskantar waɗannan jarabawar rayuwa, sai dai Allah ne ya ɗaura mata babu yadda za tayi sai karɓa hannu bibbiyu dan cinye jarabawar.
***
"Aikin ka yana kyau Daddyn Humaira."
"Kina wasa dani ne? Sai Alhaji Mamman da yarshi sun fuskanci hukunci daidai da yadda suka aikata wa Mufid har ma wanda yafi nashi."
Faɗin Alhaji Kashim bayan ya sanar da Mufid da Hajiya Hindatu yayi magana da Alhaji Mamman amincewar shi kawai yake jira kuma ya san nan ba da jimawa ba zai amince. Bayan sauraronsu Mufid ya miƙe ya wuce ɗakin shi cike da farin cikin ya kusa mallakar Baby Noor.
Wayarshi ya jawo ya lalibo lambar wayarta da yasha wahala wajen samu tun dawowar shi ƙasar. Kullum sai ya tura mata saƙo ta WhatsApp da baya ganin ta gani balle amsa da baya samu. Bai taɓa ƙiranta ba dan gudun kar ta ƙi ɗauka sai yanzu da ya ƙira har ya gama ringing bata ɗauka ba ya hakura ya san zuwa nan da wani lokaci kaɗan zai mallaketa.
***
Tun da Alhaji Mamman ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, Amma Jidda na tambayar shi ko baya jin daɗi ne ya tabbatar mata da lafiyarshi ƙalau. Mai neman shawara yake nema zuciyar shi ta raya mishi abokinsa Alhaji Tukur.
Girgiza kai yayi domin Alhaji Tukur yayi nisa baya ƙasar da iyalansa kusan shekaru uku, kuma baya jin zai goyi bayan sa akan hukuncin da ya yanke.
Hukuncin da zuciyarsa ya yanke mishi dashi ya kwana ya tashi washegari ya wuce aiki.
....
Tun jiya Mami take lura da yanayinta gaba ɗaya babu walwala a tattare da ita tun tafiyar Col. Ahmad jiya, dan daren ko abincin dare ba taci ba ta kwanta. Yanzu kuma tun safe ko wanka ba ta yi bayan ta taɓa abinci kaɗan ta kwanta saman doguwar kujera.
Shirin da ake maimaitawa da safiya take gani wanda ya wuceta jiya da yamma dan bata cikin yanayin kalla ba ta samu gani ba.
Kallon take amma hankalinta yana wani waje daban, idonta saman talabijin.
"Aunti Nuratu wayar ki yana ƙara."
Ta ji muryar Munirat saman kanta kafin ta kai dubanta saman fuskar wayarta dake saman center table yana ruri ta ɗauka.
'Sis Walida' Ta gani ta ɗauka da sauri tana miƙewa zaune.
"Fatan kin shirya ba ki manta ba?"
Walida ta watsa mata tambaya bayan amsa sallamar Nuratu.
"Ina kenan? Au sorry Sis ki zo, bari in shirya."
Nuratu ta faɗa duk lokaci ɗaya tunawa da sunyi magana da Walida yau za su je raba ankon aurenta.
"Ai na fito ina hanya. Ki yi sauri."
Kit Walida ta kashe wayar Nuratu ta miƙe da sauri ta wuce ɗakin Mami ta sanar da ita ta amince kafin ta wuce ɗakinta ta yi wanka. Tana cikin shiri Walida ta iso bayan ta gaishe da Mami ta wuce ɗakin Nuratu ta samu ta shirya cikin doguwar riga abaya ta yane kanta da maroom gyale. Yayi mutuƙar amsar baƙin fatar ta.
"Kinyi kyau Sis. Da ma Yaya Al-ameen yana nan ya bada kyautar wannan kwalliyar."
Rai Nuratu ta ɓata tana ɗaukar jakanta ta fita tana cewa.
"Ki fito mu tafi in har za ki."
Girgiza kai Walida tayi ta fita suka ma Mami sallama suka fita. A cikin motar da ango ya turo suke tafe Nuratu ta jawo wayarta anan ta ga missed call din Dr Awwab guda ɗaya.
Sanyin halin Dr Awwab yana burgeta abinda yake ƙara kusantasu dan bashi da takura, in har ya ƙirata sau ɗaya bata ɗauka ba, ba zai ƙara ƙiranta ba gani yake tamkar takura mata yake.
Col. Ahmad akwai zafi a lamuransa a yadda ta fahimta amma Dr Awwab sanyin gareshi ga miskilanci da yake taɓawa.
Ƙiran shi tayi bai ɗauka ba har sai da ya yanke, shigowar ƙiran shi ya shigo ta ɗauka tare da sallama.
"Ina wuni, ya weekend?"
Nuratu tace bayan ya amsa mata sallama.
"Lafiya lau Noor, ya gida da su Mami?"
Ya amsa mata ta ɓangaren shi yayin da yake kwance bisa doguwar kujeran falon Ummiz gefenshi ƴan biyu ne sun saka Hanan gaba suna mata tsifa.
"Kowa lafiya ƙalau. Ina Hanan?"
Kallonshi ya mai da kan Hanan da ta zuba masa ido jin ya ambaci Noor ta san Aunti Noor ce.
Kanshi ya ɗauke ƙasa ƙasa ya ce.
"Lafiyarta lau. Mun yi kewar ki fa?"
Murmushi kwance saman fuskar Nuratu jin amsar Dr Awwab, wani maganar in ya faɗa mata mamakinsa take tamkar bashi yayi maganar ba. Ɗayan sashi na zuciyarta kuma sam bata son abinda suke nema wajenta dan ba za su taɓa samu ba, duk yanda zata kauce musu sun kasa fahimta kowa burinshi ya samu gurbi cikin zuciyar ta.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa.
"Dr ina hanya in na koma gida za muyi waya."
"Wayo kawai zaki mini Noor."
"Dagaske nake."
Tace alamar ya yarda da ita.
Baya son takura mata hakan yasa yace.
"Shikenan ki dawo lafiya, ki kular mana da kan ki."
Kit ta kashe wayar tana jefawa jaka daidai sun iso gidan kawar Walida da za su fara kaiwa kuma ta kasance kawar Nuratu a baya dan tare su kayi sakandare. Har karfe shida kafin suka gama suka koma gida, sai da suka sauƙe Nuratu kafin Walida ta wuce.
***
ZARIA.
Ƙarfe taran dare ya sameshi a babban falon gidan Alhaji Isma'il Yaya ga mahaifin shi, yana zaune a falon tare da matarshi yana kallon labarai. Yaran duk sun wuce ciki.
Guri ya samu ya zauna bayan ya sake gaishesa sai kuma yayi shuru ya rasa ta ina zai soma maganar abinda ya kawo shi.
"Al-ameen menene? Kana da magana?"
"Eh Baba."
Yace kamar yadda suke ƙiran shi da sauran yaranshi gaba ɗaya.
"Faɗa mini meke tafe da kai?"
Alhaji Isma'il yace yana maida kallonshi kan Al'ameen da kanshi yake ƙasa.
Bai san ko zasu karɓi buƙatar shi ba? Bai san ko sun san har yanzu yana kan bakarshi ba na son ganin ya auri Nuratu ya share mata hawaye.
"Baba ina son ku nema mini auren Nuratu dan Allah in har hakan mai yiwa ne?"
Al-ameen ya samu kanshi da faɗar haka zuciyarshi yana bugawa ko wani daƙika dan jiran amsar da zai fito daga bakin mutumin da yake ganinshi tamkar mahaifin shi.
***
MAIDUGURI.
"Abba mun yi magana da ita ta sanar dani wanene mahaifinta."
Col. Ahmad yake sanar da Abban shi bayan tashin Umma a gurinsu. Jin maganar Col. Ahmad ya saka Abba fuskantar shi cikin zuciyarsa yana mamakin ƙarfin hali na yaronshi na ganin ya dage da son auren wannan yarinya.
"Shikenan zan maka magana zuwa nan da kwana biyu sai ka mana jagora. Amma baka sanar dani komai ba dangane da ita?"
"Abba gaban mahaifiyarta take sun rabu da mahaifinta amma duk a cikin Damaturu suke zaune, dangin mahaifinta yan Gombe ne mahaifiyarta ƴar Nijar."
Jingina kai Abba yayi zarginshi ya tabbata jin girman ƴar mace, tarbiyyar mace, dole rayuwarta ya samu tangarɗa, a zahiri kuma yace.
"Shikenan za muje da yardar Allah. Amma maganar gaskiya Ahmad ba dan ka saka kan ka dole ba, da babu abinda zai sani nema maka auren ƴar mace, nawa mace take da har zata bada tarbiyya ita ɗaya, kasan girman ƴar mace? Sam ban yarda da tarbiyyar ta ba."
Shi dai shuru Col. Ahmad yayi yana sauraron Abban shi, babu abinda ya canza a ranshi dangane da neman auren Nuratu domin bata farin ciki da nuna mata itama mace ce tamkar kowa.
***
ZARIA.
#vote
#comments
#share
MADUBIN GOBE (Haske) 28.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
ZARIA.
"Na amince zan nema maka aurenta. Amma ka sani Al'ameen duk abin da ya biyo baya babu ruwana cikin auren ku."
Kan Al'ameen ƙasa jin maganganun Baba har ya gama yace.
"Na amince Baba, inshaAllah babu abinda zai biyo baya."
"Allah ya sa."
Baba yace kafin Al'ameen ya miƙe ya mishi sallama. Bayan dawowar Hajiya A'isha cikin falon Baba ya sanar da ita yadda su kayi da Al'ameen.
"Ni dai bana son auren nan."
Hajiya tace har cikin ranta take jin hakan.
Shima Baba haka nashi bangaren zuciyar.
"Nima dai Hajiya, ace yaron nan shekaru talatin da ɗauri babu aure amma ya tsaya kan wata da babu komai tattare da ita, shi ko tsoron bata da wani ciwon ma baya yi."
"Nima abin da nake gudun masa kenan."
Hajiya tace cike da jimami da taƙaici.
***
DAMATURU.
Ƙarfe goman safe ya shigo office ɗin da har yau bai mance kamaninsa ba tsawon shekaru huɗu da ya wuce, an gyara sosai anyi canje canje zamani tamkar ba cikin garin Damaturu yake ba dan tsaruwarshi da kuɗi da aka zuba aka kashe.
Da tambaya ya samu iso cikin ofishin da numfashinsa kaɗan ya ɗauke dan haɗuwar shi, yana iƙirarin da takama shi mai kuɗi ne amma yaji bashi da komai ganin wannan haɗaɗɗen ofishin da mutumin cikin shi, ya san in har ya yarda da hukuncin da ya yanke zai samu sabon matsayi ban da arziki da yake jiyo ƙamshin sa yana tunkaro sa.
Mamallakin ofishin yana zaune saman kujera yana juyi, fuskarshi ɗauke da murmushin ƙyeta ganin wanda ya shigo ya nuna masa gurin zama.
"Bismillahi Alhaji Mamman."
Zama yayi saman kujeran da Alhaji Kashim Mufid ya nuna mishi tare da miƙa masa hannu