Follow us on social media
Showing 6001 words to 9000 words out of 148866 words
Chapter 3 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
lokaci."
A haka suka rabu Alhaji Tukur yana komawa gida ya sanar da mahaifiyar shi yadda su kayi, ya ɓoye mata cewa ga dalilin daya rabu da matar shi, ce mata yayi kawai yana neman auren Jidda. Mahaifiyarsa bata kawo komai a ranta ba tace yaje ya samu Jidda ya sanar da ita duk yadda su kayi shine dai-dai.
Bayan fitar shi ne daga gurin mahaifiyar shi ya sameta har ɗakin ta ya sanar da ita yana da magana da ita.
Bata kawo komai a ranta ba ta amince suka fita falon da ba kowa suka zauna.
"Kin san abokina Alhaji Mamman Bashir ɗan Gombe ko?"
Da mamaki Jidda tace.
"Eh na sanshi Yaya, wani abun ya same shi."
"A'a ko ɗaya, auren ki yake nema, babu dole in har bakya so, amma dai kiyi tunani bisa maganar nan, ɗazu mu kayi magana dashi yace shi dagaske yake yi idan har kin amince baya son a ɗauki lokaci."
"Ni kuma Yaya? Haba dai, dan Allah yayi hakuri, ina zan kai shi ga mata ga yara, kamar kwanaki naji kana cewa matar shi ta haihu. Balle ma ni bazan yi aure ba in bar Muhammad Al-ameen."
Jidda tace tana haɗa rai.
"To ai sun rabu da ita Hajiya Sadiyan, kuma kin san dai babban mutum ba zai iya zama ba mace ba, to shine yace in nema mishi mata ni kuma naga gaki nan mai zai sani neman wata."
Jin furucin shi ya bawa Jidda mamaki tace.
"Rabuwa dai? To ina yaransu?"
"Suna gidan, mai aiki ne take kula dasu."
Sam har cikin ranta bata ji daɗin abin ba na rabuwar Alhaji Mamman da matar shi Hajiya Sadiya ba, kamar yadda take samun labari suna zaman lafiya ta san da kyar in ba wani abun bane ya faru babba da zai raba su.
Lallai akwai wani abun a ƙasa tsakanin miji da matar da har cikin ranta taji tana son sani da kuma jihadin mayar da ita ɗakinta kan ƴaƴanta.
"Tunanin mai ki ke Jidda, ko dai bakya ra'ayi."
"Na amince."
Ta bashi amsa.
"Dagaske? Yazo kenan?"
Kai ta ɗaga mishi, yayi mamaki yaji farin cikin jin ta amince da wuri.
...
Cikin wata ɗaya daya wuce iyaye suka san maganar auren Jidda da Alhaji Mamman Bashir. Lokacin da yayun Alhaji Mamman suka samu labarin fitar Sadiya sun mishi faɗa sosai duk da ba wanda yasan dalilin rabuwarsu. Anan babban yayansu yace maza ya maida matarshi a fili yace to amma a zuciyar shi bai shirya yanzu sai lokacin daya ɗauka ya cika.
Biki saura sati biyu Alhaji Mamman Bashir ya gyara gidanshi, ya maida shi babba bangaren amarya daban, nashi daban sai na Hajiya Sadiya da shima ya gyara mai aikinsu babbar mace ita take zaune taci gaba da lura da yaran da suke ganinta tamkar kakarsu. Sun shaƙu da ita musamman Rukayya. Ita take shirya su suje makaranta ta musu wanka ta musu girki da komai na buƙata dan ta san suna buƙatar kulawa, kuma ko ba Hajiya Sadiya zata iya riƙe mata yara dan kyautatawa da take mata itama lokacin da take gidan.
Sati biyu wata ranar Jumma'ah aka ɗaura auren Alhaji Mamman Bashir da Amaryar sa Jidda Lawal sati ɗaya da biki ta tare a gidan mijinta. Ƙin ɗauko ɗanta Al-ameen tayi ta barshi a gaban mamarta.
...
Zarah da take zuwa ganin yaran Sadiya a ɓoye ko ita Sadiyar bata sani ba daga ita sai Innana mai kula da yaran Sadiya. Anan ta samu labarin auren data kasa barin abin a ranta ta je gidan Hajiya Sadiya ta sanar da ita.
Har hawaye Hajiya Sadiya tayi tana zaune ga katon ciki haihuwa yau ko gobe.
"Yara na Zarah, kar su haɗu da kishiyar uwa mai mugun hali ta cutar min dasu. Gashi ban san wani hali suke ciki ba musamman Rukayya."
Ita kanta Sadiya taji ba daɗi amma ba yadda za tayi da ta goge wannan shafin Ƙaddarar tsakanin su, bata da wani taimakon da zata basu sai na addu'a. Zuwanta gidan jiya ta haɗu da Jidda a yadda ta ganta ta sake mata fuska suka gaisa fatan ta har cikin zuciyarta haka take.
Dogon numfashi ta sauke
"Addu'a za kiyi ta musu inshaAllah babu abinda zai same su, mahaifinsu kuma shima addu'ar yake buƙata Allah dawo dashi hankalin shi ya dube ki."
Kai kawai Hajiya Sadiya ta girgiza tana share hawayenta. Tunanin halin da yaranta suke take.
"*"
Amarya Jidda da angonta rayuwarsu suka kafa cikin amince dan Jidda akwai nutsuwa da hankali. Binshi take sau da kafa tana son bashi lokaci kafin ta fara abin da ya kawota.
Alhaji Mamman Bashir kuwa da ikon Allah sai ya zama babu abinda ya ƙara faruwa daga ɓangaren aikin shi zuwa kasuwanci. Ƙoƙarin shi yanzu ya samu kuɗaɗen shi ya dawo da yayi asarar su.
...
Tun cikin dare take jin ciwon mara duk tasan alamun naƙuda ne, haka ta daure tayi ayyukan ta da basu da yawa. Wajen karfe goma ta lallaɓa tayi wanka ta zurma dogon riga dakyar dan ciwon yana cinta dauriya kawai take. Tana gamawa kayan haihuwa ta ɗauka ta nufi gidan Zarah ta samu bata nan ta bar sallahu kafin ta wuce asibiti.
Kafin ta isa ciwo sai gaba yake tana isa dakyar ta ƙarasa cikin asibitin kai tsaye labour room ta nufa suna ganinta suka karɓeta suka taimaka mata ta shiga ciki. Sosai ta wahala a nakudar har dare bata haihu ba. Zarah data samu labari ta iso amma an hanata shiga haka ta zauna ta jira a waje.
Sai gabanin asuba naƙuda ya taso mata gadan gadan da taimakon Allah ta samu ta haifi ƴarta mace ƙatuwa. Hamdala tayi ta jerowa da godiya ma Allah kafin a gyarata da yarinya, ganin lafiyarsu dukka ƙalau da safe ƙarfe tara aka basu sallama.
Duk yadda Zarah tayi suje gi
idanta ƙi tayi suka wuce gidanta. Wuta Zarah ta hura ta ɗaura ruwan wanka ya tafasa ta wanke yarinya kafin Hajiya Sadiya tayi, Zarah ta kawo mata abincin da tasa mai aikinta ta dafa ta aiko. Bayan taci ta sha shayi data haɗa mata ta samu shayar da babynta da sam bata da kuka sai bacci take, bayan ta gama ta kwanta gefenta itama bacci ya ɗauketa.
Ganin sunyi bacci Zarah ta koma gida ta samu mijinta ya dawo ta sanar dashi, kuɗi ya bata yace ta musu siyayyar ɗan abun buƙata ta karɓa ta mishi godiya kafin ta shiga kasuwa.
Abubuwan da tasan mai jego take buƙata ta siyo da su kayan baby. Data koma ta nuna Sadiya tayi murna tace ta saka mijinta da ita wahala.
"Ba komai wallahi Sadiya, duk garin nan kin manta ke kika fara zama kawata."
Murmushi kawai tayi tace.
"Hakane, nima akwai wasu kuɗaɗe hannuna sai a saya abin yanka."
"Shikenan zan samu wani ko Audu mai gadi in bashi ya sayo."
Anan suka yanke maganar Hajiya Sadiya ta bata kuɗin ta bashi ya sayo.
Washegarin kuwa ya cika alƙawari ya kawo. Kafin satin makota duk sun leƙo mata barka haka har ranar suna gidan da ɗan mutane.
NURATU shine sunan data sakawa jaririyar ta.
Da Zarah taji haka ta tambayeta.
"Mai yasa kika zaɓi sunan nan Sadiya?"
"Haske ce a gare ni in har mahaifinta ta zame masa duhu."
Hajiya Sadiya ta bawa Zarah amsa tana kallon ƴarta dake bacci abinta.
Jinjina kai Zarah tayi tace.
"Allah raya Nuratu. Amma mahaifinta ya kamata ya san da haihuwarta."
"Ameen, bana buƙata, kamar yadda baya buƙatarta nima bana buƙatar ƴata ta san shi."
Kai kawai Zarah ta girgiza tana mamakin ta ya uba lokaci ɗaya yace baya son cikin jikin matarshi bayan duk son da yake ma matarshi da sauran ya'yan sa. Haka aka watse Hajiya Sadiya taci gaba da kula da yarinyarta
...
"Ya ku kayi da Sadiya ta amince?"
Girgiza kai Zarah tayi tana miƙa ma mijinta ruwa a cup.
"Wallahi taƙi yarda, amma ni kam a nawa ganin ka je ka samu Alhaji Mamman Bashir kuyi magana dashi, mai yiwa mu samu takamanmen amsa ko dalilin da yasa yayi sakin."
"Hakan za'a yi kawai. In ba haka ba bana jin daɗin ganin Sadiya zaune ita ɗaya a gida daban anya ma can gidansu an sani."
"A'a bata sanar dasu ba har yanzu."
"Kinji irinta ko, wata huɗu fa yanzu gashi yanzu har ta haihu ta gama idda, ya kamata ƴan uwanta su sani. Amma bari muji ta bakin Alhaji Mamman ɗin in zai mai da aurensu."
"Shikenan sai yanda ta yiwu."
Cewar Zarah tana ajiye abincin data zuba mishi.
...
Washegarin mijin Zarah yana fita bai shiga shagon shi ba ya biya shagon Alhaji Mamman bai zo ba sai da azahar anan ya bar sako ya tafi. Azahar yanayi ya dawo ya samu yana nan. Bayan sun gaisa ya kawo masa maganar da ya zo da ita.
"Dama jira nake ta haihu mu maida auren mu."
Cewar Alhaji Mamman cike da murna
abin ya bawa Alhaji Audu.
"To Allah yasa hakan shine alheri, sai mun jika."
"InshaAllah za kaji ni cikin satin nan, zan zo har gida na same ka."
Alhaji Audu yayi makin maganganun Alhaji Mamman, da ya koma gida ya sanar da matar shi Zarah ita ma tayi mamaki kuma tayi murna jin yadda Alhaji Mamman ya amince da wuri zai mai da Hajiya Sadiya, fatan ta itama Sadiya ta amince ta koma kan yaranta.
...
Fitina Rukayya ta saka mata sai ta goyeta, haka ta saɓata a baya ta goya tana yawo da ita a falon. Yaran gaba ɗaya sun fi wuni a gurinta dan yadda take zuwa har ɓangaren su ta ƙirasu suzo nata, jansu take a jiki sosai tun basa sakewa har suka saba da ita ya zamana watarana har bacci suke a bangarenta.
Rahma tana koyawa Hasiya rubutu a takardunta na makaranta, gefe kuma ɗanta Al-ameen ne da Muhsin suke kallon American film. Al-ameen kasa zama yayi a gidansu Jidda ya dawo gurin mahaifiyar shi. Alhaji Mamman ya amince zai riƙeshi har ya cigaba da biya mishi kuɗin makaranta da yake aji biyu na sakandare.
Sallamar Alhaji Mamman cikin falon ya sa yaran barin abinda suke yi suka tareshi da gudun su, ya ɗaga wannan ya sauƙe yana tambayar su ina Rukayya suka ce tana kitchen da Amma. Sunan da suka sakawa Jidda kenan kamar yadda su kaji yaronta yana ƙiranta dashi.
Samunta yayi tana aikinta ga Rukayya a bayanta ya tsaya baƙin kofar kitchen din.
"Sannu da aiki."
Yace mata ta juya haka Rukayya ma jin muryar Abbanta ta juya, sai ta fara kukan za taje gurin shi tana haɗa sunanshi da hausar da ta fara yi.
"Bazan sauƙe ki ba, tun ɗazu ki ka kafa min fitanar sai na goye ki, yanzu kuma kina kallon Abba kice in sauƙe ki."
"Ki bari in kin haifi naki mana kiyi ta goyon yadda ki ke so, sauƙe ta dan Allah."
Sarai ta gane nufinshi dan ta lura ya sa mata ido cikin kwanakin nan, basar maganar tayi ta juyar kanta tana sauƙe Rukayya da gudu tayi gurin Abban ta ya ɗauketa suka fita a kitchen ɗin.
Da dare suna shirin kwanciya Alhaji Mamman ya sako zancen da yake son mata amma yana son ta fahimce shi.
"Rukayya ta samu ƙanwa."
Kallonshi Jidda tayi ya ƙara da cewa.
"Kin san dai da ciki na rabu da Mamin su Rahma, to ta sauƙa lafiya, shine nake son maida auren mu, banyi hakan dan ɓata miki rai ba ki fahimci ne Jidda."
....
Vote.
Comments.
Share.
MADUBIN GOBE 5.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
....
"Na amince."
Amma Jidda tace da sauri da hakan ya bawa Alhaji Mamman mamaki.
Murmushi tayi.
"Ka na mamaki ko? Wallahi ina son sanar da kai amma na rasa hanya, kamar yadda ba zan iya barin ƴaƴana ba haka bana son kowacce mace ta fita ta bar ƴaƴanta. In sanar da kai gaskiya, na aureka ne dan in sasanta tsakanin ka da matar ka, kuma yanzu allahamdulillahi tun da kanka ka kawo maganar, na amince ka dawo da matar ka."
"Allah miki albarka, ya sauƙe ki lafiya."
Ya furta cike da farin ciki. Shi kam ya godewa Allah da yake azurta shi da mataye nagari.
Ameen! Amma Jidda ta amsa dashi ganin ya gano dai ciki ne da ita na wata ɗaya.
Da safiyar ranar asabar ba aiki bayan ya gama abinda zai yi a gida ya fita kasuwa, shagon Alhaji Audu ya nufa kai tsaye ya sanar dashi zuwa yamma in anyi sallar la'asar zai kai shi gidan da Sadiya take.
Hakan kuwa a kayi ana gabatar da sallar la'asar suka wuce gidan kai tsaye bayan sun biya gida Zarah sun ɗauki Zarah ta musu rakiya.
Nuratu ta ɗan mata rigimar ciwon ciki da take ji, ta goyeta tana jijjigata ta samu tayi bacci tana ƙoƙarin kwantarta a falon saman katifar ta taji sallamar Zarah.
Da murmushi ta amsa ƙasa ƙasa dan kar Nuratu ta farka.
"Sannu da zuwa Zarah."
"Sannu Mamin Nuratu, bacci take ne."
"Eh wallahi ciwon ciki ke damunta."
Hajiya Sadiya tace tana dan bubbuga bayan Nuratu.
"Allah kawo sauƙi tare da baƙi muke suna waje."
"Baƙi kuma? Su waye?"
Hajiya Sadiya tace da mamaki.
"Eh kimin izinin shigowa dasu, sai ki gansu."
"To shigo dasu."
Hajiya Sadiya ta ce tana ɗaukar mayafi ta rufe jikinta dashi.
Fita Zarah tayi ta musu iso zuwa cikin falon, tare da sallama suka shiga. Jin sallamar Alhaji Mamman ya saka Hajiya Sadiya duban shi cike da mamaki ta bishi da kallo.
"Kinyi mamakin ganina Sadiya ko?"
Faɗin Alhaji Mamman yana duban Sadiya da ta haɗa rai.
"Sadiya!"
Alhaji Audu ya ƙirata dashi ta kai kallonta gurin shi tana gaishe sa dan tana ganin girman shi.
"Sadiya ga Alhaji Mamman ya dawo gare ki a karo na biyu yana neman auren ki in har kin amince, bamu san dalilinsa na ƙin cikin ki ba da har ya janyo saki tsakanin ku, amma yanzu tunda kin haifa ya dawo zai aure ki sai ku koma gidanku, fatan za kiyi hakuri ki yafe masa ki karbi buƙatar shi."
Kan Hajiya Sadiya ƙasa.
"Ba zan koma gidan shi ba sai ya faɗa mini dalilin da yasa ya ƙi abin cikina lokaci ɗaya, kuma sai ya amince itama yana sonta zai bata kulawa kamar sauran yaran."
Sai lokacin Alhaji Mamman yayi magana.
"Sadiya ki fahimce ni, yarinyar nan ba alheri a tattare da ita, in har zan rayu da ita gida ɗaya to arzikina da komai nawa sai na rasa, farar ƙafa ne da ita."
Kallon da Hajiya Sadiya take watsa mishi ya sashi kasa ƙarasa maganar ya dakata.
"Ba zaka rayu da ita gida ɗaya ba. Kuma ka ke son in koma gidan ka? Ta ya kenan hakan zai faru?"
Hajiya Sadiya tace da zuciyarta ya fara tafasa tsabar baƙin ciki jin maganganun shi.
"Dama cewa nayi zan kaita gidan marayu, sai muna zuwa muna dubata, ko in kaita can Nijar gurin yaya Muhammad."
Dariyar baƙin ciki Hajiya Sadiya tayi tana girgiza kanta.
"Ba inda ƴata za taje ina raye, ka je kawai duk ranar da ka shirya karɓar mu ni da ita mu zauna a gidan ka sai ka zo."
"Sadiya ki fahimce ni, duk ..."
"Bana buƙata Alhaji Mamman."
Tace tana ɗaga mishi hannu alamar yayi shuru ta ɗauki Nuratu data farka tana ƙananan kuka ta wuce ciki da ita tana jijjigata.
Zarah da mijinta duk sun kasa cewa komai dan Alhaji Mamman ya basu mamaki jin furucin shi. Uba ya haifi ƴa ya tsana tun kafin tazo duniya. To wanene ya faɗa masa wannan maganar da har ya amince dashi ya yarda ya tsaka tsanar yarshi cikin zuciyarsa. Wannan alamar jahilci ne da yake buƙatar ƙarin haske na ilimi.
Hajiya Sadiya lallashin Nuratu tayi ta koma bacci ta kwantar ta ta fito suka ci gaba daga inda suka tsaya.
Duk yadda Alhaji Audu yayi Alhaji Mamman ya fahimci wannan abun jahilci ne kasawa yayi, sam ya toshe kunnuwanshi ya kasa gane gaskiya.
Abun ya ƙonawa Hajiya Sadiya rai daga ƙarshe tace.
"Alhaji Mamman bana ganin akwai sauran zaman aure a rayuwar mu. Rabon ya'ya ne ya haɗa mu kuma na haifesu, Allah raya su, dan haka kawai Allah haɗa kowa da rabonsu."
"Kar kice haka Sadiya."
Zarah tace da sauri ganin ƙawartan zata yanke hukunci bisa dokin zuciya.
Bata kulata ba ta wuce ɗaki ta rabu dasu. Ta tsani Alhaji Mamman da duk abinda ya shafe sa, zata goge babin shi a rayuwarta ta kama mutuncinta kanta ta kula da ƴarta ta bata tarbiyya. Sauran yaran Allah raya mata su, in da rabon tana ganinsu in sun girma su neme ta.
Haka Alhaji Audu da matarshi suka fita cikin juyayin wannan lamarin.
...
Da daren Amma Jidda ta tambayi Alhaji Mamman ya su kayi da Mamin su Rahma dan ko ɗazu Muhsin ya tambaye ta yaushe Mami zata dawo.
"Mun rabu da Sadiya gaba ɗaya, tace ba zata dawo ba."
Da sauri Amma Jidda ta kalle shi.
"Mai yasa? Dan Allah fa, bata tunanin yaranta."
"Ko ɗaya, ki bar maganar kawai."
Alhaji Mamman yace yana canza hiran dan shima ya tsani hiranta yanzu.
Jikin Amma Jidda sanyi sosai ta shiga damuwa jin abinda mijinta yace. Alƙawari ɗaya ta ɗaukarwa kanta sai ta haɗa uwa da ƴaƴanta.
...
Sati biyu da faruwar haka Aunti Zarah tayi tafiya da bata samu damar zuwa duba su Rahma ba. Amma Jidda tayi ta zuba idanu tun lokacin tana jiran zuwan Aunti Zarah shiru, ta damu sosai gashi bata san gidanta ba balle ta je.
Mami Sadiya kuwa hankalinta ta maida kan sana'ar ta na sai da atamfofi da Allah ya albarkacin sana'ar ana saya ba laifi duk da rabi ma bashi ne.
Ana biyan albashi aka tattara mata kuɗinta tayi sari da rabin kuɗin rabi kuma ta fara shirin tafiya Nijar dan sanar dasu halin da ake ciki.
Kwana biyu ta gama shiryawa abinta da ƴarta suka ɗauki hanya.
Yamma lis ta isa kai tsaye gidan Yaya Muhammad ta sauƙa kowa yayi mamakin ganinta da jaririya suna cewa bata sanar dasu ba, sai dai tayi murmushi.
Bata samu sun keɓe da Yayanta ba sai da safe taje gaishe sa ya karɓi Nuratu yana gani ya tambaye ta sauran yaran da mai gidanta.
Kan Mami Sadiya ƙasa tace.
"Mun rabu Yaya, yau wata takwas kenan."
"Rabuwa kuma Halima? Garin yaya? Mai ya faru yayi zafi? Kuma shine bani da labari? A ina kike zaune yanzu?"
A nutse Mami Sadiya ta sanar dashi komai tana yi yana girgiza kansa har ta gama.
"Shikenan Halima Allah yasa haka shi yafi alheri. Ita kuma Allah rayata kici gaba da addu'a Allah zai kawo mafita. Su Rahma kuma Allah rayasu."
Ameen ta amsa dashi yana ta mata nasiha a ƙarshe ta sanar dashi tana son saida kayan gadonta ta ƙara jari dan kula da kanta da ƴarta. Bai hanata ba yace zai saka Shanun a kasuwa zuwa yamma in aka saya zai kawo mata kuɗin. Godiya ta mishi kafin ta mishi sallama.
Kwanan Mami Sadiya biyu ta dawo bayan ta karɓi kuɗin gadonta hannun yayanta da take jin shi tamkar Mahaifinta, sauran