Follow us on social media
Showing 147001 words to 148866 words out of 148866 words
Chapter 50 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
cikin so da kauna, yarda da kyautatawa junansu. Kowanne na ƙoƙarin farantawa ɗan uwansa rai.
...
Bayan wata biyar.
Lokacin watan Ahmad takwas, Hassana ta haihu ɗa namiji, bayan sun sha suna da sati Hussaina ta haihu ɗanta namiji ita ma. Haka suka tattara suka tafi suna Ibadan, hatta Mami wannan karon ta je da yaranta don ganin gidan ƴar ƙaninta. Ana suna suka ɗauko Hussaina don yin wanka a gida kamar yarda al'ada yake. Anan Ummi ta dinga kula da yaranta da jokokinta.
Bayan ƴan biyu Rukayya ta haihu, wannan lokacin ma mace da namiji ƴan biyu, dole dai ta zama maman yan biyu sau biyu. Ikon Allah kenan.
Ƴan biyun Mami Haydar da Faruq sai girma suke sunyi wayo. Alhaji Mamman tamkar ya mayarsu ciki, haka Amma Jidda a gurinta suke wuni.
An saka ranar Muhsin da autar gidan Alhaji Inuwa mai suna Laila. Tun zuwan su sunan Mami ya ganta, bai barta ba sai da ya samu shiga cikin zuciyarta. Iyayen sunyi murnar jin hakan. Bayan yin komai aka tsaida ranar biki wata biyar. A lokacin Ameera ma ta gabatar da saurayinta aka haɗa ranar bikin duka lokaci ɗaya nan da watanni biyar.
Ƴan biyun Ummi suna gama wanka kowacce mijinta ya zo ya ɗauketa suka koma. A wannan lokacin Nuratu da Dr Awwab da Hanan suka kaiwa Zaituna da Ikhram ziyarar kwana ɗaya ɗaya suka dawo gida.
...
BAYAN SHEKARU BIYU.
Tun lokacin Nuratu ba ta ƙara haihuwa ba, babu ciki babu alamar sa sai fatan samu. Dr Awwab duk ya damu don ya lura haihuwarta akwai tazara sosai, har shekara biyu. Hakan yasa ya matsa mata ta yaye Ahmad ko za ta samu ciki. Ganin yaron ya yi wayo ga ƙiba, yana cin komai yana tafiya ga haƙora ya sa ta yayesa.
Ai kuwa yayen da wata biyu sai ga ciki, murna gurin Dr Awwab ba a magana, tamkar lokacin ta fara samu, sai dai wannan karon ba jiri ko zazzaɓi sai amai da kasala. Haka su ka ci gaba da rainon cikinsu.
Hafiza ta ƙara haihuwar mace mai sunan Amma Jidda suna kiranta Nana. Walida ta ƙara haifar namiji mai suna Ayaan. Aunti Hasiya ta ƙara haifar namiji mai sunan Alhaji Mamman suna ƙiransa Khalifa. Lailai matar Muhsin ta haifi mai sunan Mami suna ƙiranta Miemaa. Sai Ameera da yau ko gobe don kusan shekara da aurensu kafin ta samu ciki.
Mami tun lokacin babu haihuwa ita ma ɓangarenta. Addu'a ta yi kuma Allah ya karɓa. Ƴan biyunta sun yi wayo sosai, sai kyau da bawa mutum sha'awa.
...
Cikinta ɗan wata shida tasa a gaba ta zauna, duk da yanzu babu amai da kasala sai kwaɗayi, idan babu kayan kwaɗayi kuma yawu. Rai take ta haɗawa bayan barin Dr Awwab gurin. Tun safe take roƙarsa akan maganar fara aikinta yana basarwa.
Gefenta ta kalla da ta ji hayaniyar faɗa, Hanan da Ahmad ne suke wasa sai hargitsa kayan gurin ya ke tana gyarawa tana faɗa. Tsawa ta daka musu don sun isheta.
"Ku bar gurin nan ko in ɓata muku rai."
"Mimi wasa fa muke Ahmad yana ɓatawa ina gyarawa."
Hanan ta faɗamata kamar yadda Dr Awwab ya faɗamata ta daina ƙiranta Aunti sai Mimi.
Tsaki ta yi tana ƙoƙarin magana aka danna bell. Batula ce ta fito ta buɗe daga kitchen tana bawa mai sallamar guri ta shigo. Kallo ɗaya Nuratu ta mata ta ɗauke kai. Ita ko idonta kan Hanan da Ahmad kafin ta dawo da kallonta kan Nuratu da cikinta.
Sallama ta musu, ciki ciki Nuratu ta amsa, ba ta ce mata ga gurin zama ba don kanta ta zauna ɗaya daga cikin kujerun falon tana gaishe da Nuratu.
"Lafiya."
Ta amsa ƙasa ƙasa.
Hannu ta saka a jakarta ta ciro kati ta ajiye saman table ɗin falon.
"Gayyatar ku nake zuwa ɗaurin aurana nan da wata ɗaya, fatan za ku zo ko don albarkacin Hanan."
"Insha Allah, Allah ya kaimu. Allah ya sanya alheri."
"Ameen."
Ta amsa da shi ta miƙe tsaye ta ƙara kallon Hanan. Kwata kwata yarinyar ba ta da niyar zuwa gaisheta. Ƙarfi da ya ji Dr Awwab ya raba su. Ganin irin kallon da take mata yasaka Nuratu ƙiran Hanan.
"Hanan zo nan."
Babu musu ta barwa Ahmad kayan wasan ta taho gurinta tana amsawa.
"Ki gaishe da Aunti Binta. Auntinki ce ita ma, ai kinsanta tana zuwa gidan Ummi."
Kai ta ɗaga ta masa kusa da Binta tana ce mata.
"Ina wuni Aunti."
Rumgumeta Binta tayi ta saka kuka. Tamkar ƴar uwarta Nusaiba sai bambancin kama. Murya kam sak nata duk da muryar yarinya ce. Ita kanta Nuratu ta bata tausayi, ɗan uwan jini ya wuce wasa. Da ƙyar Binta ta tsaida hawayenta ta miƙe.
"Zan wuce Noor sai wani lokaci. Kar Doctor ya dawo."
"Na gode sosai inshaAllah za ki ganmu."
Kai ta jinjina ta fita tana waiwayen Hanan. Bayan fitarta Nuratu ta ɗauki katin ta wuce sama.
Da daren suna kwance akan gado, hannunsa saman cikin Nuratu yana shafawa, har lokacin ta ƙi sakar masa fuska. Tunawa da zuwan Binta ya sa ta ƙiran sunansa ta haɗa da cewa.
"Hayat ɗazu Binta ta zo, ta kawo katin aurenta tana gayyatar mu."
"Allah ya kai mu."
Kawai ya ce bai ƙara komai ba. Jin haka ta ɗaura hannunta saman nasa da ya ke saman cikinta.
"Wai me ya tsorata Binta. Ni duk tausayi ta ba ni."
Murmushi ya yi ya sumbaci kumatunta ya ce.
"Babu komai kawai tsorata ta nayi wancan zuwanta."
Ita ma murmushin ta yi ta ce.
"Aikuwa ta tsorata sosai kusan shekara uku fa. Kuma a tsorace ta ke har yanzu."
Bai ce komai ba shuru ya ɗan biyo baya can ta ce.
"Hayat maganar aikina."
Basarwa ya yi kamar ba zai yi maganar ba sai da ta ƙara maimaitawa ya ce.
"Ki hakura da aikin nan Babyna. Zan biyaki biyun abin da za ki samu, ki zauna a gida ki kula da ni da yarana."
Shuru tayi kusan mintuna biyar tana tunani a zuciyarta. Dama sha'awar aiki take, kuma don ta kula da kanta da Maminta da ta sha wahala akanta. Kuma yanzu ga shi komai ya wuce, sun samu jin daɗin rayuwa tamkar babu abin da ya faru.
"My Baby "
Dr Awwab ya faɗa yana juyar da ita suka fuskanci juna. Kanta ta tura kirjinsa ta rumgumesa.
"Na hakura Hayat, ba sai ka biyani da komai ba, Allah zai ba ni lada."
"InshaAllah ƴar aljanna, Uwar gidan Awwab har a Aljannahtul Firdausi."
Ya faɗa yana ƙara ƙarfin rumgumeta kafin ya ɗago fuskarta ya haɗa bakinsu.
Da ƙyar ya bata damar furta.
"Insha Allah."
....
Bayan wasu watanni cikin daren juma'a Nuratu ta tashi da naƙuda. Cikin sauri Dr Awwab ya kwasheta da kayan haihuwa sai asibiti. Suna zuwa aka karɓeta, sai gabanin asuba ta haiho ƴan biyunta mata. Murna gurin alhalin ba'a magana musamman oga kwata kwata. Kafin wayewar gari dangi na cikin Maiduguri sun cika ɗakin. Sai da suka wuni aka sallamesu. Wannan karon ma Ammi ne ta mata wankan jego.
Washegari cikin ƴan Damaturu su ka zo ciki har da Ameera da bata taɓa zuwa ba da babynta yar wata uku.
...
Da daren Dr Awwab da ya shigo ganin babies Nuratu ta rokesa alfarma.
"Doctor idan har ba ka musu huɗuba ba ina neman alfarma."
"My Baby kinfi ƙarfin alfarma wajena, faɗi ina jin ki."
Ajiyar zuciya ta sauƙe a dadare ta ce.
"Ina son ka sakawa Amna Jidda da Aunti Zarah takwara wato Hauwa da Fatima. Mutane biyun nan sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar Mamina. Ina son kyautata musu in faranta musu, sai dai ban san da menene ba. Ammana tunda Allah ya kawo hakan ina fatan zai faranta musu."
Fuskarta ya shafa da ɗayan hannunsa yana murmushi.
"Me yasa ki ke son sakawa wanda ya miki alheri da alheri kullum."
"Saboda ya ji farin cikin da ya sani lokacin da nake neman farin ciki na rasa."
Sunkuyawa yayi ya sumbaci ƴan biyun ɗaya bayan ɗaya.
"Allah ya raya mana Hauwa da Fatima."
Rumgumesa ta yi cikin farin ciki da ɗan guntun hawayenta ta ce.
"Ameen Hayat na gode."
"Ki riƙe godiyarki sai bayan sati uku."
Kashemasa ido ɗaya ta yi ta ce.
"Allah ya kaimu."
Hancinta ya lakace ya miƙe.
"Ameen yarinya za ki yi bayani, sai kin zo kina kuka kina cewa in barki."
Murmushi ta yi shi ma ya yi yana fita.
Ranar suna yara suka ci sunan Hauwa da Fatima. Bayyana farin cikin mutane biyunan ba a magaba, sun ji abun ba zata a gurin da ba su taɓa tsammani ba. Haka Mami ma ta yi farin ciki sosai har tafi su yi. Duk wadda yasan Aunti Zarah da Amma Jidda ya taya su farin ciki wannan karamci. Aunti Zarah hatta mijinta da yaranta da ƙannenta sun zo. Haka Amma Jidda mahaifiyarta da yayanta Alhaji Tukur ya zo.
A ranar ya nema keɓewa da Alhaji Mamman.
Bayan gaisuwa sama sama don Alhaji Mamman ya ƙi sake masa fuska ya dubesa.
"Mamman sai na ji wani zance kuma. Wai ka mayar da Sadiya, bayan haka ma wannan yarinyar ba ita bace silar komai."
Wani kallo Alhaji Mamman ya masa ya gyara tsayuwarsa.
"Tukur kenan, ka ɗauka har yanzu Mamman ɗin da ka sani a bayane jahili. To wannan wani ne. Kar ka manta Tukur, kai ka jawomin komai kuma ƙarshe ka zare hannunka ka ɗauki iyalenka ka bar ƙasar. Yanzu ka dawo ka ƙarasa sauran rushe rayuwar ma'auratan ne ko yaya. Wallahi alfarmar Jidda ka ci na ke kulaka kar ta fuskanci wani abun, don ban taɓa sanar da ita kai ɗin wanene a baɗini ba. Don haka ka fita a harkata da iyalina, ka sama rayuwata gaba ɗaya."
Daga haka Alhaji Mamman ya kaɗa babbar rigarsa ya barsa a tsaye a gurin. Kafaɗa ya ɗaga yana taɓe baki alamar shi ya sani.
...
Bayan suna Nuratu ta ci gaba da rainon yaranta da taimakon Batula take wasu hidimomin gida, yarinyar akwai ƙoƙari. Nuratu ne take girki, ita ta ke sauran ayyuka.
Rayuwar Nuratu ya zamto haske daga duhun da ya mamaye. Ya yalwarta da so da ƙauna da farin ciki daga rashin komen cikinta. Rayuwarta tafe yake yanzu cikin haske da daidaitacciyar hanya.
Nuratu ta zamto MADUBIN GOBE abin dubawa mai Haske ga wanda suka tsinci kansu cikin hali irin nata
...
Allahamdulillahi ƙarshen labarin MADUBIN GOBE kenan.
Sadaukarwa ga duk ƴa mace babba, tsohuwa, magidanciya, budurwa, ƙaramar yarinya da ta tsinci kanta a hali na fyaɗe. Allah ya ba ku danga da cinye wannan ƙaddara da jarabawar, ba wai Allah baya son ku ba ne ya ɗaura muku. Sai don ya jarabci imanin ku.
Fatan kuma masu wannan hali su dai na. Mai hali irin na Mufid ya tuba ya bari, wanda ya ɗauki duniya ba abun komai ba sai gidan jin daɗi. Ƙarshe tun a duniya Allah ya nuna masa sakamako da danne haƙƙin wani.
Kuskuren da na yi ciki Allah ya yafe mini. Saƙon ciki Allah yasa ya isa inda na ke fata. Ƙofar ƙorafi ko gyara da tambaya a buɗe yake.
Godiya ga masu comments musamman yan wattpad, gaskiya kun nunamin ƙauna. Na gode muku sosai.
Ƴan WhatsApp ma haka musamman yan group ɗina PHARTY BB NOVELS, na gode Allah ya bar kauna da zumunci. Sa sauran manhajar facebook da Telegram. Masu buƙatar tsofin littafaina akwai a Okada book kyauta ne.
Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna DUHUN ZUCIYA bayan Ramadan inshaAllah ya kaimu da rai da lafiya.
Ma su jiran FARHA mu haɗu bayan Ramadan za mu ci gaba.
Kar ka bari a ba ka labarin DUHUN ZUCIYA, labari ne da ya ƙunshi abubuwa da dama kama daga hassada da son zuciya, ƙyashi da tsana.
Sai mun haɗu kawai domin shi ɗin dabanne da sauran.
Bissalam.
#onelove
#phartybb
#vote
#comment
#share
My new Book GOBE DA NISA
WhatsApp me 07037487278