Follow us on social media

Showing 21001 words to 24000 words out of 148866 words

Chapter 8 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

10

ta tambaye ta lafiyarta sai lokacin taji tana son sanar da ita komai.

Ran Mami ya ɓaci da jin abinda yake faruwa bata sanar da ita ba har sai da ta buɗe baki ta tambayeta. Kallon da Mami take mata ya sata shan jinin jikinta.

"Dan Allah Mami kiyi hakuri ban abin zai kai ga haka ba."
Nuratu tace kanta ƙasa.

"Dole ki ban hakuri ai tun da kinyi laifi. Rayuwar ki tana hatsari kin kasa sanar mini ina matsayin mahaifiyarki. To bari kiji tun da abin ya kai haka zan sanar da Amma Jidda ta yiwa Al-ameen magana, ke ma ki sanar dashi ya tura iyayenshi can wajen Yaya Muhammadu ayi maganar auren ku. Allah yasa haka shi yafi alheri, sannan ki dage da addu'a Allah ya kareki daga sharrin sa bayan haka ki gujema duk hanyar da zai haɗa ku. Ban da yawan fita in ba makaranta ba shima sai kin tabbatar baya nan."

"InshaAllah Mami zanyi yadda ki kace."
Cewar Nuratu cikin sanyin jiki.

Nasiha Mami tayi ta mata daya ƙara kashewa Nuratu jiki.

"Wallahi Nuratu kinga dai bamu da wani gata sai Allah in wani abu ya faru a rayuwar ki Nuratu sai dai mu shige ɗaki muyi kukan mu babu mai taimaka mana, mahaifinki har yau bai taɓa sanin ko sunanki ba balle rayuwarki da matsalar da kike ciki ba, kamannin ki ma ya iya mantawa zuwa yanzu, to kina jin in wani abu ya sameki zai iya tsaya miki ya taimaka miki, ko kina ganin shi yaron da kika cewa ba'a shari'a dashi za'a hukunta shi. A'a sai dai mu, mu gujewa duk hanyar da zai jawo faruwar wani abu marar kyau tsakanin mu, fatan mu Allah tsaremu da dukkan sharrin sa."

Nuratu dake hawaye kamar wani abin ya faru ta amsa da ameen. Har yanzu tana son sanin mai ta yiwa mahaifinta da ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata. Ga kuma Mufid da yake neman shiga mata rayuwa kai tsaye.

.....


Vote.
Comments.
Share

MADUBIN GOBE (Haske) 12.


Pharty Bb.
Wattpad phartybb.



....


Da daren Nuratu bata iya bacci ba sai da ta ƙira Yaya al'ameen bayan sun gaisa sai kuma taji kunyar sanar dashi yadda su kayi da Mami.

"Akwai magana ƙanwata a bakin ki, faɗa min menene?"
Al'ameen yace dan sai inda inda take mishi kuma bata cika ƙiranshi ba in ba abu zata faɗa mishi ba.

"Zan tura maka saƙo."
Cewar Nuratu a hankali.

"Yau kuma kunyata kike ji? To shikenan ina jira."
Yace ya katse ƙiran.

Saƙon ya karanta yana murmushi kafin ya fita a gidan saƙonnin ya ƙirata. Ɗauka tayi tai shuru.

"Allahamdulillahi."
Yace kafin yaci gaba da faɗin.
"Allahamdulillahi! nagode
ƙanwata da wannan dama da ki ka bani wanda na jima ina jiransa a gurinki, Allah yasa da rai zamu gani."

Ameen Nuratu ta amsa ƙasa ƙasa ta kasa sakewa suyi hira kamar yadda ta saba, shi kuma sai janta da hira yake ƙarshe wajen sha biyu su kayi sallama. Kasa bacci tayi ta tashi ta ɗaura alwala tayi ta nafiloli a saman darduma kafin bacci ya kwasheta.

Washegarin ranar Lahadi bata da makaranta bacci tayi har ƙarfe tara ta farka, breakfast tayi tayi wankin kayanta kafin ta ɗaura musu abincin rana, data gama kafin ta huta.

....

Tun daren jiya take zaman jiranshi bai dawo ba har sha biyu hakan yasa ta hakura ta kwanta. Washegarin da wuri ta farka har ƙarfe goma bai fito ba balle yayi breakfast hakan yasa kawai tayi shahada ta nufi ɗakinshi.
Ƙwanƙwasa tayi ya bata umarnin shiga bai tambayi waye ba yadda yake kwance da alama ko sallar asuba bai yi ba.

Ganin wacce ta shigo ya sashi ɓata rai.
"Mai ya shigo min dake ɗaki?"

Dakewa Rufaida tayi ta samu guri ta zauna.
"Magana na zo muyi Mufid."

"Ke kam dai anyi fitsararriya kowa a gidan nan yana ƙirana Yaya ban da ke. Ina jinki dan bani da lokacin ki."
Mufid yace yana ɓata rai.

"Nima bani da lokacin ka dole ta sani. Akan Nuratu ne."

Da sauri ya tashi zaune.
"Meye samu Babyna? Wani abin ya samu Baby."

Harara Rufaida ta watsa mishi ƙasa ƙasa.
"So nake ka fita daga rayuwarta dan Allah na haɗa ka dashi. Wai mai yake damunka ne? Abinda kake so a gurinta ba zaka taɓa samu ba."

"Tashi ki fita ko in ɓata miki rai, fitsararriya idan naje ta hanani gurinki zan dawo, ai ke sai ki bani, kuma ki jira ki gani."

A mugun tsorace ta kalleshi.

"Yes and i means it, ki cigaba da ƙoƙarin rabamu zan baki mamaki."

Bai ƙarasa maganar ba Rufaida ta tashi da sauri ta fita. Lallai Mufid ba shakka abinda yake sha ya fara taɓa ƙwaƙwalwarsa da har zai mata wannan maganar. Duk iskancin dan iska baya haurowa gida.
Ɗakinta ta shiga ta ma rasa wani irin tunani za tayi dan ta rabashi da Nuratu, gashi kuma ita da take ganin zata iya ga abinda ya faɗa mata ko kunya balle tsoron Allah. Addu'a kawai za ta mata dan gudun ɓata nata rayuwa dan da wannan mummunan ƙaddarar ta afka mata gwara ta kashe kanta take ji.

....

Yaya Al-ameen sun yi maganar da Nuratu da kwana biyu ya samu yayan mahaifinshi da maganar,bai ɓoye masa komai ba dangane da Nuratu iya wanda ya sani. Yayi mamakin jin cewa yar gidan Alhaji Mamman Bashir ne. Haka kawai yaji wannan haɗin bai mishi ba amma ya bar abin a ranshi. Anan yace zai faɗa sauran ƴan uwa za suyi ɗan tattauna akai har da mahaifiyar shi.

Godiya ya masa yana fita ya ƙira Nuratu bata ɗauka ba ya hakura zuwa anjima.

***

Tun karfe uku yana kofar gidansu yana jiranta dan ganin ta fito har ƙarfe huɗu kafin ya hango ta sauƙa a adaidaita.
Sarai ta gane shine cikin motar dan haka cikin sauri ta sauƙa ta miƙa mai adaidaita ɗari biyar ya ɗauki kuɗin shi ya bata canji garin sauri har ta zubar takardunta a jaka dan burinta ya bata ta shige cikin gida dan kaucewa Mufid a tarkonsa da bata san da mai yazo mata ba.

"Babu canji nima duk shine a gurina, baki sanar dani ba da ba zan ɗauko ki ba. Canjin duk nasha mai dashi."

Cikin jin haushi Nuratu tace.
"Nima baka faɗamin ba da bazan shiga ba, bari in dubo maka a cikin gida."
Tace da sauri zata shiga taji an fizgota ta juyo da sauri taga Mufid ne da ya ƙaraso kusa da ita.

"Ka sake ni."
Tace tana dukanshi a tsorace. Mugun tsoronsa take ji.

"Ki rufe min baki."
Mufid yace yana watsa mata mari a fusace dan ta bashi haushi. Kamar shi yana binta tana gudunshi.

Bai jira ta ƙara magana ba ya miƙa mai adaidaita dubu ɗaya.
"Jeka dashi an bar maka."

Nuratu dake ƙoƙarin kwace jikinta ga hawaye ya wanke mata fuskarta, mai adaidaita ya kalla ya kalli kuɗin.
"Ba zan karɓa ba. Ka saketa ta shiga gida."

"Ina ruwanka dani ko ita, yanzu sai in kifa ma mari, bar gurin nan."

"Ka taimaka min!"
Nuratu tace tana kallon mai adaidaita da duk tsoro ya cika shi da a daku da shekaru Mufid sai girmeshi zai dake shi.

"I said leave here!"
Mufid yace yana dakawa mai adaidaita tsawa da sauri ya kunna mashin ɗinshi ya bar gurin. Ganin haka Nuratu ta fasa ihu iya ƙarfinta tana kai mishi bugu.
Baya ji haka ya jata ya buɗe motar shi ya jefata ya zagaya yana shiga ganin mutane sun fara maida hankali gurinsu ya ja motar yana barin gurin.

Ihu Nuratu take yi tana bugan gilashin motar tare da ƙoƙarin cire lock ta gwamnace ta buɗe ta faɗi da ta keɓance da Mufid.
Ta samu nasara ta cire lock tana ƙoƙarin buɗe ƙofar Mufid ya ankara da haka ya wani fizgota tare da yin wani wawan parking ya juyo yana kifa mata mari.

"Kashe kan ki za kiyi?"

"Gwara na kashe kai na da ka kai ni in da zaka kai ni. Dan girman Allah kayi hakuri ka rabu dani ka bar ni. Bana sonka bana kaunar ka. Ina da wanda nake so zan aura. Duk matan duniyar nan basu isheka ba sai ni . Ka rufamin asiri ka rabu dani. Bani da wani gata sai Allah in ka cutar dani ba zan taɓa yafe maka ba."

Idanu kawai Mufid ya zuba mata har ta gama tana ƙara sautin kukanta.

"You're so cute Baby Noor."

Wani kallo ta watsa masa da jajayen idanuwanta murmushi kwance saman fuskarshi ta gani.
"Ni ke kaɗai nake so kin isheni rayuwa. Duk macen dana kyalla ido na gani burina in samu abinda nake so wajenta in rabu da ita, kuma bana shan wahala wajen haka so mai yasa zaki bani wahala Baby. Na biki amma kin nuna min bakya so to naji na hakura. Zaki aure ni?"

Wani harara ta kuma watsa masa cikin muryar kuka tace.
"Allah kiyaye in auri mutum irin ka. Gwara na mutu babu aure, ko baka ji mai nace ba akwai wanda nake so zan aura ka rabu dani."

"Haka ki ka ce?"
Mufid ya faɗa yanayin fuskar shi yana canzawa. Ko ɗar ba taji ba ta ɗaga kai. Yayi wani dariyar shaƙiyanci yana kunna motar ta dube shi da sauri.

"Ina zaka kai ni?"

Bai kulata ba yaci gaba da tuƙi, Nuratu ta juya ta kalli garin magriba ta kusa saura mintuna ga wani lumshi da garin yayi alamar haɗari yana haɗuwa har iska ya fara kaɗawa.

"Ka sauƙe ni."
Tace cikin faɗa, tsoro yana ziyartan dukkan ilihirin jikinta da zuciyarta, ta fara ƙoƙarin buɗe lock ɗin motar Mufid yasa hannu ya damƙo hannayenta taji zafi ta kwace tana jan baya.

"Dan girman Allah ka sauƙe ni inje gida. Ina zaka kai ni?"

"In da ki ke buƙata mana, can za muje in kwashi rabona kafin wani ya kwashe."

Nuratu ji tayi duniyarta ya tsaya jinin jikinta ya daina aiki ta tsaya dubanshi tana son fassara maganganun shi bata san lokacin da tayi wani kukan kura ba ta cafko hannayen shi dake saman sitiyari.

"Wallahi baka isa ba, gwara na kashe mu daka cuci rayuwata."

Zuciyarta gaba ɗaya ya bushe burinta ya tsayar da motar ta fita, ta gwammace ta mutu ko ta kashe kanta da taga wannan ranar, hawayenta ya kafe da duk wani kalma da zai fito daga bakinta.

Mufid da kyar ya samu ya saita sitiyari yana riƙo hannun Nuratu da hannunshi ɗaya, ya samun gefen titi da babu mutane yayi parking, ganin haka Nuratu ta buɗe da sauri ta fita ganin yana ciro waya a aljihunsa yana ganin haka ya fita ya bi bayanta. Gudu ta fara dai-dai lokacin da ruwan sama ya sauƙa da ƙarfi lokacin duk ana cikin masallaci ana sallah mutanen dake waje suka fara shiga cikin gida.

Ihu take tana gudu a taimaka mata kwata kwata ba wanda yake ji dan ƙarar ruwan saman da yazo da iska kowa burinshi ya shige gida, ta jiƙe sharkaf har ɗisa take a hakan bata fasa gudun ba.
Gaf taji an bugeta da ƙarfi dai-dai lokacin da ta hau kan kwalta ta zo tsallakawa, ihu ta sake tayi sama ta faɗo saman hannun damanta da taji zafi ya ratsata ta saki wani azababben ƙara taji hannun ya saƙe. A hakan bata hakura ba ta fara ƙoƙarin miƙewa ganin wanda ya bugeta ya fito cikin sauri ya nufo ta.

Dai-dai lokacin Mufid ya iso da nashi motar ya hangosu, cikin sauri ya fito ya isa wajensu.

"Sorry Baby motar ne sai yanzu ya tashi. Muje ko."
Mufid yace ya riƙo Nuratu ganin tana shirin barin gurin. Ganin haka ta kalli mutumin da ya fito yana binsu da kallon tuhuma ta girgiza kanta ta kasa magana.

Zargine ya ɗarsu a zuciyarsa yaji ya kasa gaskata abinda ya gani ya nufi gurinsu dai-dai mota ta shiga tsakaninsu ya dakata yana kallo saurayi ɗaya ya fito daga cikin motar, kafin yayi ƙoƙarin zagayawa dan musu magana d'ayan ya jefa Nuratu cikin mota Mufid ya zagaya ya shiga motarshi suna barin gurin.

Cikin sauri shima ya koma motarshi ya bi bayansu a guje, gudu kawai suke yana bin bayansu shima, wayar shi yana ta ƙara ya kasa ɗauka burinshi ya taimakawa budurwan da ya kalli tsantsan buƙatar taimako a cikin idanuwanta.

Can cikin motar Mufid kuwa Nuratu ke fitar da hawaye tana roƙarsu da bakinta ke rufe da su rabu da ita, AA yana riƙe da ita ya samu nasarar cire mata hijab da ɗankwalin kanta ya ɗaure bakinta dan ta damesu da ihu.

"Kayi sauri ka rigamu isa ka buɗe mana get, kaga wannan mutumin bin mu yake zai ɓata mata shiri."
Mufid ke wannan wayar zuwa ga Faisal da yake d'ayan motar.

Jin haka ya saka Faisal ƙara gudunshi har cikin unguwar da yake can bayan gari red brick, gidane madaidaici da suke kawo ƴan matansu suyi abinda suke so dasu su barsu. A waje yayi parking motarshi ya sauƙa ya buɗe get ɗin dai-dai lokacin Mufid ya shiga ya rufe get ɗin suka kulle gidan.
AHMAD da yana shawo kwana yaga shigarsu da sauri ya ƙarasa da motar shi ya sauƙa.
Bugun get ɗin gidan ya fara yaji basu da alamar buɗewa ya koma motar shi ya bar gurin cikin sauri.

...

"Munirat shuru dai har yanzu Nuratu bata dawo ba, ga magriba ta wuce ruwan ma har ya fara tsayawa. Zuciyata bugawa yake, ji nake wani abu ya faru da ita ko zai faru da ita."

Munirat dake zaune kusa da Mami da ko abincin dare sun kasa ci ta ce.
"To Mami ko zaki ƙira Aunti Rahma ko Hasiya ko Rukayya ko taje gidansu."

"Hakane kuma ɗauko min wayar, tunanin haka bai zo mini ba."

Da sauri Munirat ta ɗauko wayar Mami ta ƙira Rahma da Hasiya sannan Rukayya duk amsa ɗaya suke faɗa mata bata zo ba, har Amma Jidda ta ƙira ko ta wuce nan amma duk amsar ɗaya ne. Mugun tashin hankali Mami ta shiga.

"Munirat banga ta zama ba. Nuratu! Nuratu ban san ina ta shiga ba."

Dauriya itama Munirat take amma idanuwanta cike suke da hawaye.
"Mami ko ruwa ya tsayar da ita a hanya, mu bari zuwa anjima."

Mami bata saurareta ba ta ɗauki mayafinta ta fita waje duk da har yanzu ana ɗisɗisa, bakin layi ta tsaya ko za taga zuwanta, hanyar shal kowa ya shige gida babu mutane sai ɗaiɗaiku dan har duhu ya fara shiga balle in anyi ruwa gari yana duhu.

***

Kamar ƙaramar yarinya haka Mufid ya ɗauko Nuratu ya jefa saman gado ta faɗa saman hannunta, duk da bakinta rufe hakan bai hanata fasa ihu ba, ta saka d'ayan hannunta tana warware ɗankwalin bakinta domin d'ayan hannun jinshi take tamkar ba'a jikinta ba.

"Please!"
Tace cikin muryarta da baya fita tana jan baya ganin Mufid ya dumfaro ta.
Tsoro, tashin hankali, ruɗani, gaba ɗaya Nuratu ta shiga. Bak'ar rana take gani a wannan ranar da lokaci ɗaya farin cikinta da mutuncinta zata rasa zai tarwatse.

Faisal da AA ne suka shigo ɗakin, Faisal ya kalli Nuratu yadda ruwa duk ya jiƙa mata jikinta ya cije leɓɓensa da shaye-shaye ya mayar dasu baki.

"She's so hot MK."

"Ni zan fara da farko."
Cewar Mufid ya nufan Nuratu, tana jin haka ta bi gefe zata sauƙa, AA ya saka mata ƙafa ta faɗi tim a ƙasa, ƙoƙarin tashi tayi tana ja baya.

"Dan Allah na haɗa ku da Allah ku rabu dani. Kar ku cutar da rayuwata, wallahi na amince zan aure ka. Ka barni in tafi gida."

"No Baby, sai mun fanshe wahalar da kika bamu."
AA yace ya saka hannu ya ɗagata sama ya jefa saman gado yabi bayanta. Mufid da sauri ya hana shi ya tare tsakanin su yana cewa.
"She's mine, dan haka ni zan fara."

Kan Nuratu Mufid yayi ya fizgota ta fasa ihu tana ja baya. Mufid ya damƙota tare da saka hannun iya ƙarfinshi ya yaga rigar dake jikinta daga sama har ƙasa. Kuka ta fashe dashi tana saka hannunta ɗaya marar ciwo dan kare jikinta tare da duk addu'ar daya zo bakinta. Ji take duniyarta ya tashi, komai nata ya tsaya cak.

BAƘAR RANA..



#vote
#Comments.
#Share

MADUBIN GOBE (Haske) 13.


Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

.....


Runtse idanunta tayi wani hawaye mai zafi ya zubo bisa kumatunta, da sauri ta buɗe idanunta jin ƙiran sallar assalatu ta duba agogan wayarta.
Baƙin dare baƙin rana shine sunan da ta ɗaurawa wannan daren da sanadin shi farin cikinta da komai nata ya tarwatse, duniyarta ya zamto babu komai sai duhu da ya kewaye, cike da damuwa da tashin hankali.

Motsi taji bakin ƙofar ɗakinta da sauri ta miƙe tana haska gurin da hasken wayarta.

"Waye?"
Tace cikin dashashshiyar muryarta da tasha kuka cikin tsoro.

"Ni ce Mamin ki, ki tashi kiyi sahur."

Sai lokacin ta tuna da yau za tayi sahur dan azumin da take yi Litinin da Alhamis.

"To ina fitowa."
Tace ta koma ta zauna kusan mintuna biyar ta mike ta shiga bathroom ɗinta tayi brush ta wanke idanunta ta fita, bata san lokaci ya ja haka ba.

Tea kawai tasha tace ta ƙoshi Mami ta bita da kallo.

"Kin yi bacci kuwa?"

Girgiza kai tayi tana barin gurin ta ɗauki maganinta tasha dan safiyar ba zata samu sha ba ta wuce ɗakinta. Alwala tayi ta fara nafila har aka fara sallar asuba kafin ta gabatar ta hau saman katifarta ta kwanta, sai lokacin wani bacci ya kwasheta da bata samu yinsa ba.

Babu abinda za tayi da safiya hakan ya sata yin bacci har karfe goman safe kafin ta farka shima ƙarar wayarta ya tasheta ta ɗauka.

"Aunti!"
Taji da ƙarfi cikin wayar, muryar Hanan ne, yarinyar Dr Awwab, tun ranar da yarinyar ta ganta ta maƙale mata da hakan yake ƙara sakata kusanci da Dr Awwab.

"Baby Hanan, ya makaranta? Yau mai ya hana ki zuwa?"

"Aunti yau hutun mid term, Aunti zan zo wajen ki dan Allah kice Daddy ya kawo ni."

Murmushi Nuratu ta yi jin shagwaɓar yarinyar.
"Shikenan zan faɗa mishi, bawa Daddy wayar."

Cikin ɗoki Hanan ta miƙa babanta wayan da yana aiki cikin computer a office ɗinshi, kasancewar ba makaranta ya shirya Hanan ta biyo shi. Bayan ya karɓa sun gaisa da Nuratu take faɗa mishi saƙon Hanan.

"Kin amince in kawota kenan? Za ki gan mu a weekend Insha Allah."

"To sai na ganku, ka gaishe da mutanen gida."

Dr Awwab ya amsa da za suji kafin suyi sallama ya sanar Hanan ran Saturday za suje gurinta, cikin murna ta rumgume shi.

....

Nuratu wanka kawai tayi ta fita falon ta kwanta saman kujera, dama in tana azumi bata iya ɗaukan ko tsinke amma a hakan dole take yi. Wayarta ta ɗauka ta buɗe data. WhatsApp ta shiga tayi dube dubanta da ganin status ɗin wanda zata gani, tana shirin rufe data ta ga shigowar saƙo. Kamar ba zata buɗe ba ta je kan sabuwar lambar da ya turo mata ta buɗe.

*"Baby Noor."*

Kawai ta ga an saka bata gama karanta sauran saƙon ba, ya haddasa mata tsoro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login