Follow us on social media
Showing 84001 words to 87000 words out of 148866 words
Chapter 29 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
ta.
"Daddy kayi kyau."
Hanan tace tana matsawa kusa da shi, yayi murmushi ya shafa kanta da aka parker mata gashinta mai tsawo da tsantsi yana reto yace.
"Thank you My Love. Ummi zan wuce masallaci."
"To a dawo lafiya. Akwai in da za muje in ka dawo."
"To Allah kaimu."
Yace ya fita Hanan ta biyo shi da gudu.
"Daddy ka kawo min abu mai daɗi."
"To My Love."
Yace ya sunkuya ya sumbaci kumatunta kafin ya wuce ta koma ciki.
Masallaci ya wuce kai tsaye ya gabatar da sallar juma'a ya dawo, karfe biyu da rabi ya dawo gidan yaci abinci, Ummi ta shiga ɗakinta ta shirya ta sauƙo kasa ƴan biyu suka fito.
"Ummi unguwa za kije."
Faɗin Hussaina da mamaki.
"Eh ba jimawa za muyi ba, ku kula da gidan za mu kai magriba amma."
"To Ummi Allah kiyaye."
Ameen tace ta kama hannun Hanan da ta saka Hassana ta canza mata kaya suka fita Dr Awwab ya bi bayan su. Sai da suka hau titi Dr Awwab yace.
"Ina za muje Ummi."
"Damaturu wajen Noor."
"Ummi na."
Dr Awwab yace yana murmushi har hakoransa suka bayyana wushiryar shi ya fito. Daga haka bai ce komai ba yaci gaba da tuƙi suka ɗauki hanya. Kamar ta san gobe yake da niyar zuwa wajen Babynshi su yi magana ɗaya. Yayi missing ɗinta sosai, yana buƙatar ganinta.
Ƙarfe uku da mintuna ya same su ƙofar gidan Mami, bayan yayi parking suka sauƙa yana riƙe da hannun Hanan suka shiga cikin gidan da sallama. Filin gidan babu kowa suka nufi cikin falon.
Nuratu ne kaɗai a gidan Mami ta tafi auren Munirat da yau ake ɗaurawa.
Tana kwance tana canza tashoshi dan neman abun kallo ya shigo cikin falon, kallon baƙin kofar tayi jin muryar wanda take tunanin me ya hanashi ƙiranta, ko yayi fushi ne?
Ido suka haɗa ya bita da wani kallo, da sauri ta miƙe ta faɗa ɗakinta dan ba wani rigar kirki bane a jikinta, ta laliɓo hijab ta saka ta fito falon ta same shi da Ummi da Hanan, ta taho gurinta da gudu ta rumgume ta.
Kallo ɗaya Nuratu ta ma Ummi ta hango tsantsan kama da take da Dr Awwab, wani kunya ne ya lullubeta ta zauna a ƙasa tana gaishe da ita kafin ƙasa ƙasa ta gaishe da Dr Awwab ya amsa idon shi saman fuskar wayar shi amma hankalinshi yana kanta.
"Maman ki bata nan ne Noor?"
Ummi ta tambayi Nuratu da har lokacin ta kasa kwakkwaran motsi a gurin, Hanan na jikinta ta cukwuikuyeta.
Girgiza kai tayi cike da kunyar sunan da Ummi ta ƙirata da shi tace.
"Eh ta fita, amma tace ba zata jima ba."
"Shikenan bari mu jira ta zuwa nan da wani lokaci."
To Nuratu ta amsa da shi ta miƙe ta wuce kitchen Ummi ta bita da kallo.
"Noor akwai hankali, na lura tana da nutsuwa ga kunya."
Murmushi kawai Dr Awwab yayi jin Ummi ta ya ba da zaɓinshi. Nuratu ne ta dawo ɗauke da tray babba da plate a sama ruwa ne sai zoɓon da Mami ta yi da rana da doughnut ta ajiye kusa da Mami ta wuce ɗakinta. Wayarta ta ɗauka ta ƙira Mami ta sanar da ita zuwan su kafin ta fito ta zauna nesa da su kusa da Hanan da take bata labarin makaranta tana amsa mata.
Kusan mintuna goma Mami ta shigo da sallama, suka amsa Ummi ta ɗago idanuwanta ta bita da kallo cike da mamaki. Wani bugawa zuciyarta yayi ganin fuskar Mami.
'Suna kama.'
Faɗin Ummi a zuciyarta cike da mamakin kamannin da ta hango saman fuskar Mami da wanda ba zata taɓa mance kamannin ba.
"Sannun ku da zuwa."
Mami tace tana zama. Sai lokacin Ummi ta amsa tana murmushi tare da dawowa hankalinta.
"Sannu da dawowa."
"Sannu ya hanya, kun sha hanya."
"Allahamdulillahi na biyo ƴata ne."
Ummi tace tana murmushi.
"Ai kuwa gaki ga ita nan."
Mami tace Ummi ta kai kallonta kan Nuratu da kanta yana ƙasa, a ƙarshe ta miƙe ɗauke da Hanan, Ummi tana ganin haka ta dakatar ta.
"Dawo ki zauna Noor, magana za muyi dan ke na zo."
A kunyace Nuratu ta dawo ta zauna kamar ta nutse ƙasa, ban da nauyin Ummi da take ji har shi Dr Awwab ɗin da yaƙi barin gurin idanuwanshi suke yawo a kanta sun takura mata.
"Noor sai kuma abu ya zo lokaci ɗaya. Kuma na ji shuru nace bari in yi tattaki in saka baki."
Nuratu da ta kasa cewa komai nauyin matar take ji sosai, ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa.
Mami ne tace.
"Nima dai ido na saka musu, amma kar ki damu, inshaAllah za ayi abu ɗaya za ku ji daga gareta kwana kusa."
"To Allah ya kai mu."
Ummi tace ta miƙe tsaye tana kallon Dr Awwab da ya kasa cewa komai.
"Ta shi mu tafi kar muyi dare."
Sallama suka ma Mami ta yiwa Ummi rakiya, Nuratu a bakin kofar falon ta koma tana sauƙe numfashi bayan ta yiwa Hanan bye bye ta koma. Mami a ƙofar gida ta tsaya kafin ta dawo ta samu Nuratu da ta koma ta kwanta.
"Sai kiyi hakuri ki rumgumi ƙaddarar ki, kin ga dai matar nan takanas ta tako kafa dan ke. Dan haka ki saurari Doctor kuyi magana ɗaya."
Mami tace tana zama kusa da Nuratu da ta saka kunne tana sauraron Mami.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 41.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Mami na amince na yarda zan zauna."
Nuratu tace cikin sanyin jiki.
"Ko ke fa Allah yasa haka shine alherin gaba ɗayan ku."
Faɗin Mami.
"Ameen."
Nuratu ta amsa da shi ta wuce ɗakinta ta kwanta, wani zazzaɓi zazzaɓi ne ma ya kamata ta rufe jikinta. A hankali wani siraran hawaye suka zubo mata da ta rasa na menene.
...
Dr Awwab bayan ya sauƙe Ummi da Hanan ya wuce gidanshi, ruwa ya watsa ya saka jallabiya ya sauƙo falon ƙasa yana neman lambar Nuratu. Yana ta ringing bata ɗauka ba ya tura mata saƙo.
*"Babyna ki ɗauka ko gobe ki ganni na zo."*
...
Nuratu da tana ganin ƙiran ta kasa ɗauka ta rasa mai za tace masa ta ga shigowar saƙon shi ta karanta, haka ta kasa ɗauka, ƙarshe ta kashe wayar gaba ɗaya.
Ƙiranta Dr Awwab yayi yaji wayar a kashe yayi murmushi, yana son rigimar Noor. Tana son abu tana kaiwa kasuwa. Allah nuna masa ranar da za ta buɗe baki tace tana son shi.
....
"Suna kama su biyun."
Ummi tace riƙe da hoton marigayin mijinta da take hango fuskar Mami a jiki, duk da hoton ya tsufa ya jima amma kamannin bai ɓuya ba.
Tun da ta dawo ta kasa nutsuwa, zuciyarta ya kasa tsayawa waje ɗaya. Hoton ta laliɓo cikin ma'ajiyar kaya da suke adanawa. Anan ta ƙara hango tsantsan kama da su biyun suke yi. Tayi mamakin Awwab da bai hango hakan ba tun tsawon shekaru.
'Akwai wani abun.'
Ummi tace cikin zuciyarta kafin ta ajiye hoton ta fito falon jin hayaniya. Anan ta samu Binta ƙanwar mamar Hanan ce ta zo. Matashiyar budurwa, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe da Ummi ta amsa tana tambayar mutanen gida.
"Duk lafiyar su ƙalau. Kwana biyu shuru shine na zo gaishe ku."
"Yayi kyau mungode sosai."
Ummi tace ta saka Hussaina kawo mata ruwa.
Binta bata jima ba ta miƙe tsaye.
"Ummi zan wuce sai anjima."
Har waje suka rakota, duk yanda taso Hanan ta zo gurinta yarinyar ƙi tayi ta wuce, zargin su da mahaifiyarsu ya tabbata sun rabasu da jininsu.
***
New Delhi.
A hankali ya buɗe ido har ya buɗesu gaba ɗaya, tsawon kwana ɗaya kenan da masa aiki bai farka ba sai yau. Ummu da ke zaune da sauri ta danna wani guri da zai sanar da Dr ya farka kamar yadda suka nuna mata. Cikin sauri Dr ya shigo ya duba shi.
Mufid sai binsu yake da ido. Ummu ta fita ta ƙira Alhaji Kashim suka dawo ɗakin tare.
"Barka ya farka, a bashi abu mai ruwa ya sha sai ya fara shan magani. Zai ci gaba da shan magani na tsawon wata ɗaya kafin mu sallame shi. Sannan ya kiyaye shan duk wani abu da zai taɓa masa zuciya, in kuma ba haka ba aiki zai koma baya. Ko da ya warke ne ya ƙauracewa duk wani kayan maye dan lafiyarshi."
Faɗin Dr Kushal cikin harshen turanci da yake gauraye da indiyanci.
Alhaji Kashim ma cikin harshen turanci ya mayar masa da amsa.
"Mun gode Dr Kushal. Amma har tsawon wata ɗaya bamu da isasshen kuɗin da zamu zauna anan ƙasar, in har zai yu zuwa nan da sati biyu a sallame mu."
"Sai mun ga yanayin jikin shi."
Dr Kushal yace yana fita. Alh
aji Kashim ya matsa kusa da Mufid da ya rufe idanuwanshi.
"Sannu Mufid ya jikin?"
Sai lokacin ya buɗe ido ya kalleshi ya buɗe baki ƙasa ƙasa yace.
"Da sauƙi."
"Mufid ya jikin. Mai za kaci in kawo maka."
Ummu tace tana matsawa kusa da shi ya kalleta.
"Da sauƙi Ummu. Bana jin yunwa."
"Ka daure dan Allah."
Girgiza kai yayi ya juya.
"Ki haɗamin black tea."
Da sauri Ummu ta haɗa ta kawo masa da taimakon Daddy ya zauna, bathroom ya kaishi ya wanke bakinshi ya fito ya zauna yana jingina da filo dan jikinshi ba ƙarfi ko kaɗan. A baki Ummu ta dinga bashi ya sha kaɗan ta bashi magunguna kamar yadda Dr ya faɗa ya sha ya koma ya kwanta.
Bai san mai ya faru da shi tsawon lokaci ba, shi dai ya farka ya ganshi kwance babu lafiya.
***
Nigeria (Maiduguri).
"Mama wallahi yarinyar nan ba yanda ban yi ta zo guri na ba taƙi. Ke kin ga har da kukanta kamar taga dodo."
Binta tace da Mamarta bayan dawowarta daga gidan su Dr Awwab dan tabbatar da gaske ne kamar yadda su ka ji yayi aure, sai dai bata ga alamar hakan ba ya sata dawowa gida.
Mama da ta ji mai tace tayi kwafa tace.
"To ya maganar auren?"
"Ban ji komai ba Mama."
"To dai Allah yasa karyane, dan ba zan taɓa bari jikata ta tashi wajen matar uba ba."
"Ah to dai."
Faɗin Binta cike da jin haushin jin labarin da suke Dr Awwab yayi aure. Duk tsawon shekaru da aka ɗauka tsammanin su zai nemi auren Binta bayan su da suka nemi hakan ya nuna a'a, sun tsammaci bayan lokaci zai yarda, ta zauna ɗakin yayarta ta kula da ƴarta, sai suka ji labari ya sha bambam.
***
Washegarin ranar Asabar babu aiki bacci Dr Awwab yayi har wajen goma kafin ya farka, yayi wanka ya shirya cikin ƙananan ya fita. Gidan Ummi ya biya suka gaisa yayi breakfast kafin ya musu sallama ya fita. Kai tsaye Damaturu ya nufa dan yana son suyi magana ɗaya da Nuratu.
Ya ƙirata taƙi ɗauka ya tura mata saƙo babu amsa yana son ya ji mai ta yanke game da shi. In ta yarda ta zauna to in kuma ta ƙi su san abin yi.
Ƙarfe ɗaya ya shiga cikin garin, sallar azahar yayi kafin ya ƙarasa gidansu. A waje yayi parking ɗin motarshi ya ɗauki wayarshi yana ƙiranta har lokacin yana ringing taƙi ɗauka ya tura mata saƙo.
*"Babyna ki fito ina ƙofar gida."*
...
Nuratu da tun safe take aiki dan babu mai yi, a lokacin ta samu ta kwanta bayan tayi wanka ta ɗauki wayarta ta ga missed call ɗin Walida ta ƙirata tana mata tsiya. Bayan sun gama wayar tana ajiyewa ta ga kiran Dr Awwab ta kasa ɗauka ta ajiye, shigowar saƙo taji ta ɗauka ta karanta.
Da sauri ta miƙe daga kwancen da take jin abin da yace cike da mamakin rashin hutu da baya bawa kanshi kullum yana hanya.
Kamar ba zata tashi ba ta miƙe ta ɗauki hijabinta ta ɗaura saman riga da skirt din jikinta ta fita, dan tunawa da nasihar Mami da ta mata akan tayi hakuri ta bawa zuciyarta dama.
Ɗakin Mami ta shiga ta samu ta runtsa ta ja ƙofar ta fita, waje tayi anan ta hango motar shi ta tabbatar da gasken yake ya zo.
Ido ya zuba mata yana murmushi, yana son Babynshi sosai. Fuskarta yake kallo har ta ƙarasa wajen shi kanta ƙasa ya buɗe gilashin motar yana ci gaba da kallonta yace.
"Shigo ciki Babyna. Magana za muyi."
Sai lokacin ta iya kallonshi, ya sakar mata murmushi ta ɗauke kanta zuciyarta yana bugawa ta girgiza kai.
"Mu ƙarasa ciki dai da zai fi."
"No wannan maganar sirri ne tsakanin mu. Please ki daure ki shigo ciki dan Allah ba danni ba."
Dr Awwab ya ƙarasa maganar cike da roƙo. Haka ya saka Nuratu zagayawa cikin sanyin jiki tare da bugun zuciyarta da yake ƙaruwa ta buɗe ɗayan gefen ta shiga. Ƙamshin turaren shi dana morar ya haɗa ya bada wani ƙamshi mai daɗi da sanyaya rai, ga sanyin AC da ya gauraye cikin motar.
Bayan ta shiga ta zauna ya juya yana kallonta yana ƙoƙarin juya kan motar yace.
"Bari in nema mana wajen da za muyi maganar zai fi."
"Ni dai muyi anan, ban sanar da Mami ba fa."
Tace cikin sanyin murya cike da tsoro tsoro.
"Mami ba abin da za tace in ta samu labarin kina tare da mijinki."
Nuratu dai bata so haka ba, tana gani ya juya kan motar suka fita a unguwar bugun zuciyarta ya ƙaru. Tafiya suke babu wanda yayi magana sai kiɗan da yake tashi a motar na wakar larabci na Ali Abed, waƙar soyayya ne da Nuratu tana fahimtar wasu kalmomin, hakan ya sakata yin baya ta jinginar da kanta waƙar da sautin yana ratsa dodon kunnenta da ilihirin jikinta.
Sosai Dr Awwab ya fahimci waƙar ya mata daɗi, hakan yasa ya kai hannu ya ƙara Volume su kaci gaba da tafiya. Kusan mintuna biyar dai dai waƙar ya ƙare sun tsaya a wani gurin shakatawa da babu mutane sosai ya shiga da motarshi gurin ajiye motoci da babu mutane a gurin, ya kalli Nuratu da take bin gurin da kallo.
"Za mu shiga ciki ko za muyi maganar anan."
"Muyi a nan dan Allah."
Tace da sauri yayi murmushi yana gyara zamanshi ya rage volume din wakar da ya shiga na biyu ya fuskanceta. Kanta ƙasa tana wasa da zoɓen hannunta tana jiran ta ji mai zai faɗa mata.
"Noor!"
Ya ƙirata da sunan da ya jima bai ƙirata ba, ta ɗago ido ta ga nashi idanuwan cikin nata ta kawar da kanta gefe tana amsawa ƙasa ƙasa.
"Baki za ki buɗe muyi magana Babyna."
"Ina jin ka."
"Ina so ki sanar da ni abin da yake cikin zuciyarki game da ni da auren mu. Shin kin yarda kin amince za ki zauna da ni a matsayin mijinki ko kuma har yanzu babu zancen aure cikin zuciyarki da rayuwarki. Ki sanar da ni gaskiya kar ki ɓoye min zan fahimci zancen ki."
Shuru ne ya kauraye cikin motar bayan gama maganar Dr Awwab yana jiran amsar Nuratu da tayi shuru tana juya maganganushi cikin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta. Bata ankara ba taji saukar hannunshi duka biyun saman nata ya riƙo. Wani ɗumi taji a hannuwansa duk da sanyin AC dake kunne a motar.
Da sauri ta ɗago kai tana ƙoƙarin kwacewa tace.
"Me hakan dan Allah. Ka sake min hannuna."
"Sai kin bani amsa."
Dr Awwab yace yana ƙara damƙe hannunta.
Kamar za tayi kuka tace.
"Ni tsoro nake ji."
"Tsoron me? Ni ko kuma waye?"
Kan Nuratu ƙasa tana kallon hannunta da ke cikin na Dr Awwab da ya damƙe tace.
"Tsoron gori nake, bani da abin da zan baka Dr, bani da komai, baka cancanci haka ba, baka cancanci mace kamata ba, ina tsoron watarana ka mini gori, ina tsoron danginka su mini gori ko su dinga jifa na da munanan kalamai, ba zan iya jura ba."
Shuru Nuratu tayi wani abu ya tokare mata wuya, hawayen da ya taru a idonta ya zuba saman hannun Dr Awwab da sai lokacin ya ankara, wani tausayin Nuratu na ƙara shiga zuciyarshi.
Hannunta ya ƙara damƙewa cikin nashi da hannu ɗaya, ya saka ɗayan hannunshi ya ɗaura saman fuskarta Nuratu ya ɗago kanta yana kallon cikin idanuwanta, ta runtse idanuwanta da sauri. Hannu ya saka ya share mata hawayenta yana cewa.
"Nasha faɗa miki cewa Awwab ba abin da yake buƙata wajenki sai soyayyar ki da neman amincewa ki aure shi. Ni fa musulmi ne Babyna na san ƙaddara, ni Awwab na miki alƙawari ba zan taɓa buɗe baki in miki gori ba da sunan wani abu daban ba. Ba zan ce miki babu abin da zai shiga tsakaninmu ba, amma duk yadda ki ke haka na ji na gani zan karɓe ki."
Wani nutsuwa ne ya shiga Nuratu, ajiyar zuciya Nuratu ta sauƙe tana kwace fuskarta a hannun Dr Awwab dan wani iri take ji a fuskarta, kanta ta sunkuyar ƙasa.
"Faɗi maganar ki Babyna. Na lura kina da abin faɗa."
Dr Awwab yace yana ƙara matse hannuwanta ta lumshe idanunta buɗe jin yadda yake matsa hannuwanta, ƙasa ƙasa tace.
"Yanzu Ummi ma ta san mai ya faru da ni, da kowa ma cikin family?"
Girgiza kai yayi yace.
"A'a, babu wanda ya san mai ya faru da rayuwarki daga ni sai ni, ban sanar da kowa ba. Sirrin mu ne fa Babyna, in na faɗa tamkar tonawa kai na asiri ne. Kuma babu ranar faɗar hakan har abada. Zuwan Ummi na jiya kawai ta zo ne gani take tamkar dole na miki bakya so na na aureki, nima ban san da tafiyar ba sai da muka fito."
"Nagode."
Nuratu tace cike da nutsuwar da ta ji ya sauƙar mata a zuciya da gangar jiki. Murmushi Dr Awwab yace.
"To ya muke ciki yanzu? Kin yarda za ki zauna da ni?"
Kunyane ya kama Nuratu ta kwace hannunta ta rufe fuskarta da shi tana murmushi. Dr Awwab ya matsa kusa da ita daf da kunnuwanta ta ji ya furta.
"Nagode sosai da ki ka yarda da ni ki ka amince dani na zama mijinki. Ina mana fatan alheri. Ina son ki sosai Babyna."
Baya Nuratu ta yi tana jan hijabinta ta rufe fuskarta da shi cike da wani mugun kunyarshi da ya lulluɓeta.
Dr Awwab motar ya buɗe ya fita ya shiga ciki ya fito kusan mintuna ɗauke da ledoji ya saka a baya ya shiga motar yana barin gurin.
A ƙofar gidan su yayi parking, Nuratu tana ƙoƙarin fita ya kwaso ledojin baya gaba ɗaya ya ɗaura mata saman cinyarta.
"Na san ba kici komai ba na ɗauko ki."
"Yamin yawa ai. Na ci abinci fa."
Tace tana marairaice masa.
"To raba mana."
Babu musu Nuratu ta buɗe tarkacen, ice cream ne da burger da shawarma. Ta raba kashi uku ta haɗa kashi biyu ta ɗauki kashi ɗaya, duk Dr Awwab yana kallonta, ganin abin da za tayi ya sashi saka hannu ya karɓi na hannunta, babu musu ta sakar mishi ya ɗauki mai yawan ya ɗaura mata.
"Ki gaishe da Mami sai munyi yawa. Wannan ma ya ishe ni ba ci zan yi ba My Love zan kai wa."
Nuratu ba