Follow us on social media
Showing 99001 words to 102000 words out of 148866 words
Chapter 34 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
yana ji da ya dafa kanta, hakan bai sakasa barinta ba ko fasa niyarsa ba ya ci gaba. Bayan ya gama suka shafa ta hau linƙe sallayun. Dr Awwab zamansa ya gyara saman kujera yana ɗaukar takeaway da ya shigo da shi ya buɗe ya kalli Nuratu.
"Idan kin gama ki zo mu ci."
"Na ƙoshi."
Ta ce jin maganarsa ya daki dodon kunnenta. Ji tayi abincin da komai ya fita a ranta. Shi ya barta da halin da take ciki mana ya tsaya mata ta abinci.
Murmushi yayi yana ci gaba da kallonta ta gama linƙe sallayun ta ɗauka a hannayenta, ya ce.
"So kike in ba ki yau ma a baki kenan. Is ok babu matsala zo na baki, daren yau naki ne ai Babyna."
"Ni fa na ƙoshi Allah."
Nuratu tace tana wucewa ɗaki ko kallonsa ba ta ƙara ba, tare da ajiye sallayun da ta shiga ta shiga kenan.
Kyakkyawan murmushi Dr Awwab ya sake yana cije lips ɗinsa na ƙasa, mamakin tsoronta yake dan abun yanzu dariya ya soma ba shi. Baya yayi ya ɗaura kansa saman kujera yana faɗin.
"Ki fito, ko in zo in fitarki da kai na wallahi. Duk wayonki da tsoronki bazan fasa abin da nayi niya ba."
Ba ta masa magana ba ta barshi, amma maganarsa na ƙarshe da ta jiyo ya sake tsananta bugun zuciyarta, hawaye ta ji ya cika idanunta, kafin ta ankara har sun zubo. Bayan ta ajiye ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta saka rigar baccinta marar nauyi, duk tana yi tana share hawayen da suke zuba bisa kumatunta lokaci zuwa lokaci. Turare kawai ta saka ta haye gadon ta kwanta bayan ta kashe wutan ɗakin.
Har kanta ta rufe da bargo tsoro kawai take Dr Awwab ya zo mata. Tana tsoron wannan ranar domin bata da komai da za ta iya bashi washegarin yayi alfahari da ita. Baƙar ranar da lokacin da Mufid ya kwace mata komai ya tarwatsa mata farin ciki ne ya dinga dawo mata tamkar yanzu yake faruwa.
Kuka ta fashe da shi ƙasa ƙasa tana share hawayenta, kusan mintuna talatin ta ji an taɓa ƙofa.
A hankali ta ciro kanta cikin bargon Dr Awwab ne ya shigo tare da haska ɗakin da fuskar wayarsa. A mugun tsorace ta mai da kanta cikin bargo zuciyarta yana ci gaba da bugawa, da ƙyar ta ke jawo numfashinta tana shaƙa.
Kan gadon ta ga ya nufo, tana ji yayinda hawayenta ya ci gaba da silalowa bisa kumatunta ta kasa sharewa. Zama Dr Awwab yayi yana ajiye wayarsa a saman bedside drower, tare da ya janye jallabiyan jikinsa ya cire yana ajiyewa a gefe daga shi sai boxer. Bargon ya ɗaga ya shiga ciki.
Nuratu tana jin haka ta juya tana matsawa baya a tsorace.
Dr Awwab yana jinta ya saka hannunshi ya riƙota, fizgota yayi ta faɗa saman jikinsa ya saka hannayensa ya rumgumeta, kafafunta ya harɗe da na sa.
Murya cikin raɗa ya mata magana cikin kunnenta, tare da hura mata sanyayyar iska ciki.
"Dan jiya na ɗaga miki ƙafa yau babu ita Babyna."
Kasa masa magana tayi taci gaba da ƙoƙarin kwace jikinta. Bai kulata ba ya mirginata ta koma kasa ya haye samanta ya rumgume. Jin hakan ya saka Nuratu sake fashewa da kuka, kukanma da karkarwa yake fita dan tsoro.
"Menene kuma?"
Dr Awwab ya faɗa yana sassauta riƙon da ya mata, kukanta taci gaba da yi kusan sakwanni. Ganin ba zata kulashi ba ya sashi cewa.
"Shikenan bari in miki abin da za kiyi kukan dagaske."
"Ni bana so Doctor. Tsoro nake ji."
"Tsoron me kuma? Na faɗa miki bana son wannan tunanin naki. Kar ki ɓatawa Awwab darensa mai cike da alheri, babu abin da zai canza dan wani abu ya faru, ki bari a daren nan mu haɗe mu zama abu ɗaya Babyna. Kar ki hanani wannan damar."
Shuru ta masa tana sauƙe ajiyar zuciya tana jin wani sanyi a ranta da Dr Awwab kullum yana cikin fahimtarta, ko ba komai ta ji nutsuwa amma tsoron nan na dankare a ranta. Za tayi magana taji ya rufe bakinta da nashi ya hanata ya fara kissing ɗinta, a hankali ya fara mata wasu abubuwan da ƙwaƙwalwarta ya kasa ɗauka, tun tana iya jurewa har ta zo ta fara tureshi tana hanashi. Dr Awwab yayi nisa baya jin ƙira, ta rikitashi sosai, daren bai bar Nuratu ba sai da ya cika burinshi na ganin sun haɗe sun zama abu ɗaya. Duk kuka da magiyan Nuratu ya rabu da ita bai ji ba. Sai kuka take mishi domin ba za tace ba tasha wahala ba, abu da ba sabo. Wahala kam ta shashi dan Dr Awwab ya gurjeta son ranshi daren, ya hanata duk kan motsi ko ƙoƙarin kwatar kanta.
"Allah ya miki albarka ya ba ki dukkan farin ciki kamar yadda kika bani."
Dr Awwab yace yana sauƙe numfashi tare da kissing ɗin forehead na Nuratu cike da farin da ta sakashi.
Tureshi tayi cikin rashin kuzari, tana share hawayenta ta juya bayanta tana jan bargo ta rufe jikinta, kukanta ta ci gaba da yi, jikinta duk ciwo yake mata ban da kanta da ke sarawa shima dan ciwo, ga wani zafi da ke ratsata tamkar yau aka fara saninta.
'Shikenan yanzu mijinta ya sameta bata da komai, ba a budurwa ba.'
Maganganun da suke dawo kwanyar kanta ta ƙara sautin kukanta.
Shuru kusa mintuna biyar ɗakin shuru sai sheshshekar kukan Nuratu. Kasa lallashinta Dr Awwab yayi, haka ya sakasa miƙewa ya kunna ƙananun wutar gefen gadon, ya shiga bathroom ɗinta ya tsarkake jikinsa, ruwan zafi sosai ya haɗa mata ya fito ya hawo gadon.
"Tashi in taimaka miki kiyi wanka, ko in ɗauke ki."
Ya faɗa tare da juyo da Nuratu ya ga tayi bacci tana sauƙe numfashi tare da ajiyar zuciya a tare wani na bin wani. Ɗagata yayi ya ɗaura saman kujera ya yaye bedsheet din ya saka wani kafin ya maidata ya kwanta ya rufe su da bargo bayan ya musu addu'a. Bacci ya kauracewa idanunsa ya zuba fuskar Nuratu ido da hawaye ya bushe, idanunta duk sun kumbura dan kuka. Hannun ya saka ya shafa kumatunta.
'Ƙadan ya rage hankalinsa ya bar jikinsa kukanta ya dawo da shi, ta zautarsa ta rikitasa yadda bai yi tsammani ba, idan ba dan duk ƙaddarorinta ya sani ba zai iya bugan kirji ya ce shi ya fara saninta, bayan haka ma a budurwa ya samu Nusaiba. Ba dan abubuwan nan biyu ba, da zai iya cewa ba budurwa ba ce.'
Maganganu dai iri iri yayi ta saƙawa a ransa a daren nan, wani so da ƙaunarta ne yake huda tsoka da jijiyoyin jikinsa yana shiga jininsa. Mutuncin da ƙimarta yana girma a idanuwansa. A haka bacci ɓarawo ya sacesa.
...
Washegarin sai ƙarfe tara Nuratu ta farka bayan farkawar asuba da Dr Awwab ya sa ta. Ya rigata farkawa karfe huɗu na asuba, bayan ya farka ya wuce bathroom ɗinta ya haɗa ruwan zafi ya zo ya tasheta, da kyar ta iya tashi ya taimaka mata shiga bathroom, duk yanda ya so ya taimaka mata ƙi tayi ya fita ya barta, haka ta gyara kanta ta gasa jikinta sosai, duk da tana yi tana hawayen zafi haka ta daure dan shine hanyar warakarta, kafin ta fito ta samu baya ɗakin. Kaya ta saka ta tayi sallah tana hauwa gadon sai bacci dan wani mugun gajiya take ji da zazzaɓi zazzaɓi.
Haka Dr Awwab da ya dawo daga sallah ya sameta ya kwanta gefenta.
...
Da kyar ta lallaɓa ta miƙe ta wuce bathroom ko kallonsa ba tayi ba, ta sake yin wanka ta fito baya ɗakin. Riga doguwa na atamfa ta saka ta ajiye jakanta da mayafinta da komai da za ta buƙata kafin ta hau tattare ɗakin duk cikin dauriya take yi aikin, har lokacin jikinta babu daɗi. Bayan ta gama da ɗakin ta fita ta ɗauki tsintsiya ta dawo ta share. Tana cikin sharan Dr Awwab ya shigo kusan karfe goma da wani abu.
Da sauri ya ƙarasa wajenta yana karɓar tsintsiyar.
"Waya faɗa miki amarya tana aiki. Please ki bari, ki zo muyi breakfast in kai ki kar kiyi latti. Zan ƙira twins su zo su miki."
"Ka bari zan iya."
Nuratu tace a hankali dan wani mugun kunyarshi take ji, ta kasa ko kallon fuskarsa balle cikin idonshi da yake yawo jikinta. Da ma bata juran kallo balle yau da anyi me gaba ɗaya.
"Zo muje."
Yace ya ajiye tsintsiyar ya kama hannunta su ka fita waje. A hankali ta dinga sauƙa a matattakalar benen. A dinning table ya zaunarta bayan ya ja mata kujera, ya zauna shima. Abincin da Ummi ta aiko musu ya ɗauka ya zuba ya saka cokali mai yatsu dan dankaline da kwai. Shayi mai zafi da madara ya haɗa musu.
"Mu ci sai muje, ko in ciyar ki."
Yace da ita yana ɗaukan fork ɗin kafin ta ɗauka ya ɗauki dankali ya nufi bakinta da shi. Sai lokacin ta ɗago kanta suka haɗa ido ta kawar kanta gefe.
"Zan iya."
Ta basa amsa a hankali.
"Karɓi wannan tun da na ɗebo."
Dr Awwab yace ya kai saitin bakinta, dole ta buɗe ya saka mata ta fara ci a hankali. Fork biyar ya bata bai ci ba, a hankali tace.
"Kai ma ka ci mana."
Murmushi yayi yayinda ya ƙara ɗauka ya kai bakinta yace.
"Sai na gama ciyar da amaryata.".
Shuru ta masa tana tauna na bakinta taji yaci gaba da cewa.
"Kin sani farin ciki sosai daren jiya. Allah ya miki albarka ya bani ikon baki farin ciki kamar yadda kika bani."
Ɗago idanuwanta Nuratu tayi da suka cika da ruwan hawaye ta kalli Dr Awwab jin maganganunshi, shi kuwa ya zuba mata ido yana murmushi. Ganin ruwan hawaye kwance cikin idanuwanta ya haɗa rai yace.
"Bana son kukan nan Babyna. In kuma so kike mu ɓata to shikenan kiyi ki ga yadda ake shanye hawaye."
"Ni bana so."
Nuratu tace tana turo baki tare da murmushin da bata san ta yi ba ta ci gaba da cewa.
"Doctor ban taɓa tsammani za kayi alfahari da ni ba, shi yasa kullum nake tsoron kasancewa matar aure, dan bani da abin da zan bawa mijina yayi alfahari da ni har in sa shi farin ciki."
"Ya isa Noor."
Dr Awwab yace yana ɗaura yatsansa saman leɓɓenta ya hanata ƙarasa sauran maganganunta.
Shuru ta masa tana share hawayen idonta da su ka zuɓo, lokacin da ya cire yatsarshi a leɓɓanta taji yace.
"Bana son ki ƙara irin maganar nan Please, in kuma ba haka ba zamu ɓata. Kin ma shiga ruwan zafi sosai, naga da ƙyar ki ke jan ƙafar."
Kai ta ɗaga mishi ta miƙe cike da kunyar jin maganarsa, ya dubeta yana dakatar da ita.
"Ina zuwa ba dai kin ƙoshi ba, shayinma ba ki sha ba."
"Eh! zan ɗauko jakana."
Daga haka ta wuce sama ya bita da kallon tausayi, so, kauna. Yana mutuƙar tausayawa rayuwarta da halin da ta tsinci kanta, dole ta dinga tunanin cewa bata da komai amma shi kam daren jiya ta sashi farin ciki sosai. Kuma zai yi alfahari da ita, dan ta riƙe mutumcinta ko bayan abin da ya faru da ita saɓanin wasu da suke faɗawa wani halin.
Sauƙowar Nuratu ya sa shi dubanta, cikin mayafinta babba ta yane har kanta, da handbag ɗinta da duk tasan za'a buƙata. Har ta iso gurin Dr Awwab bai daina binta da kallo ba domin tayi kyau sosai, ba abin da yafi jan hankalinshi kamar jambakin leɓɓanta. Yadda ta rufe kanta da jikinta yafi burgesa tayi shigar mutunci.
"Na shirya."
Nuratu tace tana kai dubanta gurin Dr Awwab da ya kafeta da ido, ɗauke kanta tayi domin wani kallon da yake watsa mata ya kasa hanata kallon cikin idonshi da sakewa.
Miƙewa yayi daga in da yake zaune ya isa gurinta yace.
"Ina zuwa minti biyu."
Sama ya wuce ɗakinta, hakan yasa ta isa table din ta tattare gurin ta kai Kitchen ta fito falon. Kusan mintuna uku ya dawo ɗauke da hijab ruwan gyalen jikinta, da kallo ta bishi har ya ƙarasa kusa da ita ya saka hannu ya fara warware gyalen jikinta. Ba ta hanasa ba.
"Zai ba ki wahala sosai gyalen, ki saka hijabi za ki fi jin daɗi da shi dan zirga zirga."
Ba tace komai ba ya gama warwarewa ya saka mata hijabin ta gyara ta ɗauki handbag ɗinta ta saƙala a kafaɗarta ya riƙo hannayenta.
"Saura abu ɗaya."
Yace ya rage tsawonshi ya rankwafo tare da ɗago kanta da hannunshi ɗaya, fuskarsu ya haɗe numfashinsu ya gauraye guri ɗaya. Nuratu runtse idanuwanta tayi domin ta fahimci mai yake shirin yi, tana shaƙar numfashinsa da ƙamshin turaren jikinshi. Tana jinshi ya ɗaura bakinsa saman nata, a nutse ya fara kissing ɗin bakinta, sai da ya shanye jambakin tas kafin ya saketa. Kasa tsayuwa tayi dai dai, ta yi tangal tangal za ta faɗi ya riƙota jikinshi tana sauƙe numfashi.
Sai da ya ga ta samu nutsuwa ya tsayarta yana riƙo hannunta suka nufi waje.
Falon ya kulle ya buɗe motar ta shiga kafin ya zagaya yana shiga ya kunna motar mai gadinsa ya buɗe get suka fita. Babu wanda yayi magana har sai da suka hau titi ta ji yace.
"Bana son wani ya gani shi yasa na shanye abu na, ina da kishi sosai Babyna."
Shuru ta masa magana sai juyar kanta da tayi tana bin garin Maiduguri da kallo. Murmushi yayi yasan ba za ta tanka ba, ya kai hannunshi ya kunna wakar Ali Abed, Nuratu tana jin waƙar ta juyo, ba ƙarya waƙar sau ɗaya ta ji amma ya mata daɗi, tana saurara har suka isa ya sauƙeta a bakin get in da za su taru su tafi.
"Sai yaushe kuma Babyna?"
"Nima ban sani ba, in mun gama zan ƙiraka."
"To Allah yasa ki samu da wuri."
Yace ya saka hannun cikin aljihunsa na jeans ya ciro kuɗi da ba tasan nawa bane ya ɗaura saman cinyarta.
"Gashi ko za ki buƙaci wani abun."
"Akwai kuɗi a hannuna."
Ta faɗa tana ɗauka ta mayar masa.
"Wannan ni na baki a matsayina na mijinki. Ki riƙe ki je kar kiyi latti."
Nuratu ba taso ba ganin ya haɗa rai ya sata ɗauka ta fita tana masa sallama, sai da ya ga shigarta kafin ya ja motarshi ya bar gurin, kai tsaye gidan Ummi ya wuce dan ganin sanyin idaniyarshi.
****
DAMATURU.
"Abban su tun jiya nake tambayar ka ina za ka je baka sanar dani ba. Kasa na haɗa maka kaya."
Alhaji Mamman da yake gyara hulan kanshi yana sauraran Amma Jidda da tun jiya ya sata haɗa kaya take masa wannan tambayar. Juyowa yayi bayan ya saka yana kallonta tana zaune bakin gadonshi yace.
"Gombe zan je wajen Yaya Inuwa."
"Lafiya? Gombe dai"
Ta tambaya cike da mamaki dan ya jima da ta ji ya ambaci sunanshi cikin lumana sai dai da faɗa.
...
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE (Haske) 48.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Lafiya lau Jidda ki kwantar da hankalin ki, babu komai sai alheri."
Ajiyar zuciya Amma Jidda ta sauƙe tana fatan hakan, tare da miƙe daga zaunen da take ta ɗauki jakan kayansa da babu komai sai kaya kala ɗaya da abubuwan buƙatarshi. Har cikin motarshi ta ajiye masa jakan tana ce masa.
"A dawo lafiya ka gaishe da su."
"Za su ji. Ki kula da gidan."
Kai ta gyaɗa masa yaja motar ya bar harabar gidan kafin ta koma ciki.
...
Hanyar Gombe ya ɗauka dan tunkaran Yayansa da buƙatarshi, wanda yake fatan bayan yafiya da zai masa ya amshi buƙatarshi, ya tsaya masa bisa cikar burinshi a karo na biyu, ba shi kaɗai ba har sauran yayunsa.
***
Dr Awwab minti minti yake ƙiran Nuratu ya ji ta gamane, sai tace masa da saura domin abin da yawa kuma suna da yawa. Duk ta gaji kamar tayi kuka haka take ji, ba ta taɓa tsammani akwai wahala ba sai yau ga tayi lattin zuwa. Dan ma matan aure na su layin daban da masu ciki da masu shayarwa da kuma wanda ƴan kudune aka turosu nan.
Sai ƙarfe shidan yamma da mintuna ta samu ta karɓi komai nata tun daga uniform, takalma da komai da ya danganci abin shiga camp. Aka sanar da su sai bayan sati biyu za su dawo dan babu zaman camp ga matan aure. Tayi murnan jin haka kuma dama taji labari. Tana gamawa ta ƙira Dr Awwab.
"Na gama Doctor."
Da sauri yace.
"Gani nan zuwa Babyna, kar ki tafi ko ina."
To tace masa ta kashe wayar ta zauna tana bin gurin da kallo, kowa da abinda da yake yi. Mintuna kusan ashirin ya ƙirata ta ɗauka.
"Ki fito na iso."
Kayanta ta ɗauka ta fita tana fita bakin get ɗin ya nufeta da sauri ya karɓi kayan hannunta yana mata sannu. Bayan boat ya sakaa zagaya ya buɗe mata ƙofa ta shiga ta zauna kafin shima ya zagaya ya shiga motar suna barin gurin.
"Sannu duk kin gaji."
Dr Awwab yace yana mai da kallonshi kan Nuratu da ta jinginar da kanta kan kujeran motar ta lumshe idanuwanta. Jin maganar Dr Awwab ya sata buɗe idanunta tana faɗin.
"Na gaji sosai wallahi."
"Naga alama. Kina buƙatar hutu da tausa."
Yace yana murmushi ya ɗaura hannunshi saman cinyarta ya matsa kafin ya riƙo hannunta.
Kanta ta kawar gefe. Sauƙar hannunshi da ta ji saman nata ya sata juyowa ta kalleshi, fuskarshi ɗauke da murmushi ya ɗaga mata gira ɗaya yace.
"Ko ba haka ba?"
"Ni bana so."
Tace ta zare hannunta cikin nashi, bai ce mata komai ba yayi murmushi yaci gaba da tuƙi. Wahalar da ya bata jiyama kaɗai ya isheta, da nashi da na yau duk sun mata rubdugu.
Horn yayi aka buɗe ƙofar gidan ya shigar da motar ciki, bayan ya faka Nuratu ta sauƙa tana ɗaukar jakanta. Shi ya shigo da kayanta ciki falon ya samu bata nan, ya wuce da shi ɗakin ƙasa ya saka, ya fito ya wuce bedroom ɗinshi. Alwala yayi ya wuce masallaci jin ƙiran sallar magriba.
Nuratu tana shiga ta cire hijabinta tayi wulli da shi saman gadon da jakan ta faɗa kan gado dan ta gaji sosai. Ƙiran sallah ya sata tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta ɗauro alwala, riga marar nauyi ta saka ta gabatar da sallah. Bayan ta idar har ta kwanta ta miƙe tsaye ta fita da sauri dan ɗaura musu abincin dare. Ba dan dole ba, ba za tayi ba, ta gaji sosai.
Cikin kitchen ɗin ta tsaya tana tunanin mai zata girka marar nauyi mai saurin dahuwa, tana tunanin hakan ta ji an buɗe ƙofar falon ta fito dan ganin waye, Dr Awwab ne ya shigo da ledoji hannunshi. Ƙarasa tayi tasa hannu ta karɓa ya miƙa mata.
"Abinci ne ba sai kin wahalar da kan ki