Follow us on social media
Showing 144001 words to 147000 words out of 148866 words
Chapter 49 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
ya yi.
"Babyna lafiya? Ta ji miki wani ciwon ne."
Tamkar jira take ya yi magana, wani juyi da maranta yayi ya sata durƙushe ta dafe cikin.
"Bayana. Marana, marana Hayat."
Ta ce tana yarfe hannu. Ɗagota ya yi ƙoƙarin yi ta ƙasa miƙewa, kuka ta saka masa tana cafko wuyar rigarsa iya ƙarfinta.
"Ka taimaka mini mana ka sakamin ido kana kallo."
Rikice mata ya yi ya kasa komai, karshe ya ɗauketa gaba ɗaya suka nufi waje sai kuka take masa, bayan ya sa ta ya koma falon da sauri ya wuce ɗaki ya ɗauka mata mayafi ya sauko. A rabe ya samu Binta ya watsa mata wani mugun kallo.
"Ki shirya shiga gidan yari idan wani abu ya samu matata ko abun cikinta."
Daga haka ya wuceta ya fita. Ba tasan fitsari ya ɗisa a jikinta ba sai da ta fara tafiya ta ji danshi. Ko takai ba ta bi ba a gaggauce ta bar gidan, kai tsaye gidan yayarta Aunti A'isha ta nufa, sai lokacin ta samun damar yin kuka, ta sa ka Aunti A'isha a gaba.
"Aunti wallahi na hakura da shi, ni ban zauna ba, kuɗina bai zauna ba, ku ba ku zauna ba, kun hanani kula masu so na, ga shi yanzu wa gari ya waya. Wallahi ko shi ne autan maza na hakura da shi. Yanzu idan wani abu ya samu matarsa ko cikinta fa ni Binta na shiga uku gidan yari zai kai ni. Wallahi zai aikata ko?"
Ta rushe da kuka har da ɗaura hannu a saman kai, can ta miƙe zumbur ta shige ɗaki ta kulle kanta. Kamar tayi hauka take ji, burinta Nuratu da abin cikinta suna lafiya don ta hango tsantsan rashin tausayi a idanuwansa.
....
Can asibiti suna isa aka karɓi Nuratu aka wuce da ita ɗakin masu haihuwa. Likita tana dubata ta fita ta sanar Dr Awwab haihuwace ya kawo kayan haihuwa, bai gama sauraren su ba ya fita a ɗakin. Gida ya je ya dauko kits din da suka gama haɗawa jiya don EDD ɗinta saura sati biyu. Yana ɗauka ya koma asibitin.
A hanyar dawowa ya sanar Ummi, tuni ta nufi can bayan ta sanar da Ammi.
Dr Awwab dai ya kasa ya tsare ya ƙi fita don likitar tayi tayi ya fita a ɗakin ya ƙi, ƙarshe ya sanar mata shi ma Dr ne amma na ƙwaƙwalwa kuma abokin Dr Sageer ne shi. Dole ta barshi, duk ya cikata da korafin matarsa tana shan wahala tasan ya za tayi. Nuratu kam haushinsa take ji yadda ya sata a gaba ya zauna, duk motsinta da juyi yana taimaka mata kamar shi ya ke karɓar haihuwar.
Ba tayi wani dogon naƙuda ba awarta ɗaya ta haiho yaronta namiji. Murna gurin Dr Awwab ba a magana, a gaban likitar ya sunkuya ya sumbaci leɓɓenta.
"Thank you My Baby."
Murmushi kawai ta masa, aka miƙa masa Babyn ya karɓa ya rumgume abunsa yana sumbata.
Bayan an gyara Nuratu aka mata alluran barci aka kaita ɗakin hutu. Waje ya kaiwa su Ummi yaron suka gani kafin ya koma ɗakin ya kwantarsa kusa da mamarsa.
Kafin Nuratu ta farka ɗakin ya cika da ƴan uwan su. Sai yamma lis ta farka da taimakon Ammi ta yi wanka da ruwa mai zafi har da kukanta. Bayan ta fito aka bata abincin da Hassana ta kawo, ta ci sosai da ta gama ta jingina jikin gadon. Kowa ficewa yayi ya bar musu ɗakin daga ita sai Dr Awwab sai babyn su.
Ɗaukar Babyn yayi ya ɗaura mata saman cinyarta.
"Ba ki tambayi me ki ka haifa ba, sannan kin cika cikinki saura na Babyna."
A kunyace ta girgiza kai.
"To ai zan gani ka yi sauri ne."
"Na yarda da wannan, kunyar fulani za ki nunamin akan ɗan fari, daɗinta jini ɗaya mu ke dake. Yanzu abawa Babyna abinci, ya yi hakuri fa don ma na basa zamzam da dabino."
Yana faɗar hakan ya ɗaura hannunsa saman zip ɗinta ya zuge. Riƙesa tayi tana turɓune fuska.
"To ka juya ko ka fita."
Kumatunta ya sumbata yana murmushi. Kunyar Nuratu yana burgesa wani lokaci. Juyar kansa ya yi gefe yana cewa.
"Me kuma ya rage, abun da ragowana za'a basa."
Yi ta yi tamkar bata ji sa ba. Mayafi ta jawo ta rufa musu, a nutse ta ciro abincinsa tamkar dama ta iya, saitama Babyn ta yi a baki sai dai ya kasa isowa don kansa ya yi ƙasa, haka ta ɗan sunkuya sai dai za ta gaji da wuri. A hakan ta soma basa, tuni ya karɓa tamkar jira yake. Kanta ta ɗago dan jin shuru, gani ta yi Dr Awwab ya zuba musu ido yana kallo. Harara ta watsa masa ta sunkuya ba ta ce komai ba.
Miƙewa ya yi ya fita, tun da ta fara kokuwar bawa Babyn abinci ya ke kallon su, ya taimaka mata yana tsoron ta ƙi. Yana fita Hassana ya ƙira ya aiketa gurin Ammi.
"Ki cewa Ammi ƴarta na buƙatar taimako."
Daga haka ya fita a asibitin ya nufi gida.
Aiken ta kai gurin Ammi, da sauri Ammi ta shiga ɗakin, ita ta taimakawa Nuratu ta nuna mata yadda za ta shayar da Babyn, ta ɗago mata shi sama, sai lokacin ta ji daɗi. Bayan ya ƙoshi ta cire masa ta kwantarsa. Yaron dai ba za tace ga wanda yake kama da shi ba, don jaririn awannine, sai dai hasken fatar mahaifinsa ya ɗauko.
Ammi ne ta kwana da ita, Ummi da Hassana gida suka koma, don ita ma cikinta har ya fito kusan watanni huɗu.
Washegari da safe aka sallamesu, gidanta aka wuce da ita. Hauwa matar Babban Yaya, da Amina matar Sajeed, da Hassana da Batula su ka haɗu su ka taimakawa Nuratu da gyaran gidan da girki, su suka mata komai. Ammi ta tare ɗakin Nuratu ita take mata wankar ruwan zafi mai rai da lafiya, Ummi dai da akwai ɗan kunya tsakinin su, ko ita Nuratun ba ta sakewa da ita duk da ta kasance matar ƴaƴan mahaifiyarta.
Abdallah, Baban Yaya, Sajeed duk sun zo mata barka har Baffa, sun mata alheri ita da Babyn.
Ƙarfe biyu na rana Aunti Hasiya da Aunti Zarah suka iso, har da Walida da babynta da ta girma, sai Amma Jidda da ba ta taɓa zuwa ba. Aunti Rahma laulayi take, Rukayya kuma cikinta ya fara girma sai washegari suna za su zo. Amira tana son zuwa halin da Mami take ciki ya sa ta haƙura sai Islam da ta bi Amma Jidda. Cikin Mami ya fito sosai kamar yau za ta haihu.
Nuratu ta yi murnan ganin ƴan gidansu, nan gidan ya ƙara hargitsewa da hayaniya. Musamman Nuratu ta ƙira Rufaida ta faɗamata. Ai kuwa washegari sai ga ta da mijinta da yaranta. Ƴan uwan Nuratu sunyi mamakin ganin Rufaida sanin ƙanwar Mufid ce. Wuni ta mata guda da yamma ta koma akan washegari suna tana tafe.
Gidan bai rabu da mutane ba har washegari suna.
Ana washegari suna Col. Ahmad ya zo shi da Hussaina da cikinta ita ma wata huɗu daidai watannin cikin Hassana. Mama yawuro da Kawu Muhammadu sun zo. A ranar Aunti Rahma da Rukayya su ka zo.
Ranar suna Yaya Al'ameen ya zo wuni a tsaitsaye don Hafiza haihuwa yau ko gobe ita ma.
Alhaji Mamman da Mami sun haɗawa yar sun kayan goyo na ban mamaki, tamkar amarya za a haɗawa lefe haka Alhaji Mamman ya haɗawa Nuratu setin akwati guda shida da Babynta gudu shida, har kayan ƴan shekaru biyar ya zuba. Har lokacin ji yake bai kyautata mata ba, kamar ya yi kaɗan abun da ya bata. Har sai da Mami ta nuna ɓacin ranta akan ya isa kayan kafin ya hakura, amma sai da ya saka mata kyautar mukullin mota.
Nuratu ta yi kuka da idanuwanta na farin ciki, ta rumgume Abbanta tana godiya.
Haka ƴan Maiduguri ma sun haɗa mata. Dr Awwab ma ya yi nasa na fitar suna.
Oga kwatakwata Col. Ahmad Tafida da ya samu takwara ya haɗo nasa kayan. Umma da ƙannenshi ne mata suka kawo kayan. Ya ce kuma kar a ɓoye masa suna a ƙirasa Ahmad ɗinsa. Ƴan gidan su Col. Ahmad sun ga karamcin wannan bayin Allah, Umma har kunya ta ji.
Nuratu dai ranar ta rasa wani irin murna za tayi. Musamman da ta ji sunan da ya saka jariri. Sunan mutumin da ya fara taimaka mata a rayuwa tun kan yasan ita wacece, ya tsaya mata ta ƙwaci haƙƙinta.
Haka taro ya watse lafiya aka ci aka sha kowa ya koma gida. Da ƙyar Dr Awwab ya bar yayun Nuratu suka tafi da ita gida wanka kamar yadda ake yi a al'adance, har sai da Ummi ta sa baki ya haƙura akan wata ɗaya tak yaba su ba zai jira arba'in ba.
Bayan isar su gida ɓangaren Amma ta zauna don Mami ma na ji da kanta. Amira na kula da Mami sosai, Amma na kula da Nuratu da Babynta, gefe ɗaya kuma tana mata gyara na musamman ciki da waje.
Lokacin da Nuratu ta ga cikin Mami kasa shuru tayi ta hau murna. Har da cewa.
"Yanzu Mami ƙanwa za ki haifa mini. Shikenan ni ba auta bace. Ki haifamin mai kama da ni."
Ta faɗa kuma tana ɓata rai.
"Sai ki haɗa da naki ki raina."
Mami ta ce tana harararta daga haka tabar mata gurin. Dariya Nuratu ta yi ta riƙe baki.
'Wannan rabo haka, Mami da ciki.'
Tace tana kuma sakin murmushi ita ɗaya.
...
Satin Nuratu biyu Hafiza ta haihu, duk gargaɗin Dr Awwab kar ta yi tafiyarnan haka ta yi kunnen ƙashi ta bi masu zuwa suna. Anyi suna lafiya yaro ya ci sunan Abban sa suna ƙiransa Aarif. Washegarin su Nuratu su ka dawo, da mugun mura Ahmad ya dawo don sanyi ya shigesa.
Duk yadda taso ɓoyewa Dr Awwab sai da ya sani. Ranar ya ƙirata Ahmad yana mata kuka ya ji muryarsa a shaƙe. Ranar taga ɓacin ransa da faɗa. Ƙarshe ta kashe faɗar in da ta saka masa kuka.
"Wallahi na kula yanzu ka fi son Ahmad a kai na. Dama an faɗa ai, da zaran mace ta haihu son ya ke komawa kan yaransu."
Dafe kansa yayi ya ajiye fushin a gefe ya hau lallashi.
"Idan ba so ki ke ki ganni yanzu cikin dare ba ki daina kukan nan Please. Ahmad kuma ƙarami ne bana son kina yawo da shi, gobe zan shigo amma kafin nan ki kaishi asibiti don Allah Babyna. And you know i missed you."
"Babu wani missing ɗina da ka yi."
Ta ce tana tura masa baki kamar yana kallonta.
"Seriously a aikomin kiss."
Kafin ya rufe baki ta sakar masa wani kiss mai ƙara, har sakar kansa ya ji kafin ta yanke wayar tana dariya. Yau da tana gabansa tasan sai ta faɗi yaren garin su. Bangarensa kasa ƙiranta ya yi don yasan idan ya ƙira komai zai iya faruwa.
Washegari ta kai Ahmad asibiti aka basa magunguna suka dawo gida, ƙiransa tayi ta sanar masa, anan ya bata hakuri rashin zuwansa aiki ya tsayar da shi sai wani sati. A ranar Rufaida ta kawo mata wuni guda, sun sha hira sosai har daren kafin mijinta ya zo ɗaukarta. A tsorace Rufaida ta sanar da ita Mufid ya kusa aure. Da mamaki buɗar bakin Nuratu ta ce.
"Allah ya basu zaman lafiya. Ina labarin waɗannan abokansa biyu?"
"AA ya rasu kusan shekaru biyu yanzu, Faisal kuma ya koma gurin dangin mahaifiyar sa. Ina ƙara ba ki hakuri Nuratu..."
Da sauri Nuratu ta hanata ƙarasa maganar ganin za ta dawo da hannun agogo baya.
"Don Allah ya isa haka Rufaida, komai fa ya wuce. Allah ya ji ƙansa, shi kuma Allah ya sa sanadin shiryuwarsa kenan."
...
Kwana biyar da sunan Hafiza, ranar wata juma'a Mami ta tashi da naƙuda. Cikin gaggawa Abba ya dawo suka wuce da ita asibiti, wuninsu guda kafin ta haifi ƴaranta biyu maza. Murna cikin dangin ba'a magana. Muhsin ajiye kunya ya yi ya zo kallon ƙannenshi maza da su kaɗai ya ke da su a duniya.
Kafin suna mutane da yawa sun zo daga Maiduguri, Gombe, Nijar. Alhaji Inuwa da matarsa da yaransa duk sun zo, Kawu Muhammadu, Ummi da Hassana, Ammi da yaranta da matansu. Haka Zaituna da Ikhram sun zo takanas daga Abuja ganin ƙanwar mahaifin su. Hussaina da Col. Ahmad duk sun zo. Hatta Munirat ta zo, Suwaiba ma da ta koma gida bayan auren Mami ta zo. Hafiza kam dama tana gida yin wanka ita ma.
Ranar suna yara suka ci sunan Aliyu Haydar da Umar Faruq. Alhaji Mamman ya taka rawar gani tamkar yanzu aka soma masa haihuwa. Haka Amma Jidda ma tamkar ita ta haihu. Haka yaran Mami ma su suka tsaya mata kan komai da Aunti Zarah. Ba su yi wani taro ba, tsakaninsu suka yi komai.
Ranar suna bayan an watse wajen ƙarfe takwas, Mami ta shige ɗaki tare da yaranta, sunyi wanka sun kwanta don huta gajiya. Amma ta koma ɓangarenta, Ameera ta yi wa Islam wanka suma sun shige ɗakinta suna kallo. Hakan shi ya bawa Nuratu damar yin shirinta a nutse. Wanka ta yi ta saka kayan barci mai kauri, ta yi wa Ahmad wanka ta saka masa kayan barci shi ma sai ƙamshin turare da hoda ya ke. A kafaɗa ta ɗaukesa suka fita zuwa bangaren baƙi.
Yana zauna ɗaya daga cikin kujerun falon ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya. Sallamarta ya sa shi ɗago ido ya amsa yana buɗe hannayensa alamar su ƙarasa jikinsa. Gurinsa ta ƙarasa ta ajiye masa Ahmad a cinya tana murmushi ta ce.
"Ina zuwa."
Daga haka ta fita, Ahmad ya ɗauka ya hau sumbata yana ƙiransa tamkar zai amsa. Yaron ya yi bulbul yanzu kam kamanninsa da shi sai fitowa ya ke.
Dawowar Nuratu ya sa shi dubanta, faranti ne ɗauke a hannunta ta ƙarasa ta ajiye saman table ɗin falon.
Ahmad ya kwantar gefe ya saka hannu ya fizgota jikinsa. Zama ya gyara mata cikin jikinta kafin ya fara sumbatarta daga fuska zuwa wuya, ƙarshe ya tsaya a bakinta bai mata magana ba, martani ta fara mayar masa tuni suka kusa mantawa da gidan surukai suke. Shi ne ya yi ƙoƙarin dakatar da su ya rumgumeta yana kissing ɗin tsakanin wuyarta. Idanuwanta lumshe tana shaƙar ƙamshin turarensa, duk ya kashemata jiki. Ƙasa ƙasa ya yi da murya ganin yanayinta ya canza ya ce.
"Ki na son abu amma shi ne ki ka kasa komawa inda za a ba ki."
Numfashi ta sauƙe ta ɗago jikinta, maganar ta basar tana ce wa.
"Abinci fa? Ko ruwa ban ba ka ba."
Hancinta ya ja yana murmushi ya ce.
"Yawunki ya wadatar da ni komai."
"Ni wallahi sai ka ci. Don kai fa na shiga kitchen na girka da kai na."
Ta ce tana bubbuga ƙafa a ƙasa.
"Yarinyar nan kin girma har da yaro amma kina ƙara shagwaɓewa. To zubamin kaɗan."
Gwalo ta masa ta miƙe ta fara aikin zuba masa.
"Ai rainon ka ce."
Murmushi ya yi ya ɗan kishingida yana mata kallon ƙasa ƙasa ya ce.
"Seriously yaushe za ki koma?"
Sai da ta gama saka masa couscous da yasha kayan lambu ta zauna kusa da shi ta ɗaura plate ɗin saman cinyarta, don ita za ta basa tasan zai faɗa. Hannunta ta wanka ta ɗiba ta kai bakinsa ya buɗe ta saka masa yana murmushi.
"Saura sati biyu kuma sai nayi yawon arba'in. Zan bi gidajen ƴan uwa da abokan arziki na gaishe su. Sai dai kusan nan da sati uku."
Ƙwarewa ya kusa yi, da sauri ta basa ruwa yasha tana masa sannu. Sai da ya nutsu ya riƙo hannunta na hagu da yake empty.
"Bana son wannan al'adar Hausawar don Allah. Idan kuma ya zama dole to kiyi cikin sati biyun da ya rage miki. Next upper week zan zo ɗaukar ku, na gama magana."
Dariya ta yi ta ɗaga masa kai.
"Yes Sir an gama."
Kusan goman dare kafin ya musu sallama da ƙyar ya tafi hotel ɗin da ya kama. Ita ma kayan ta tattare ta wuce ɗaki ta kwanta cike da buƙatar mijinta.
Washegari Dr Awwab ya zo ya musu sallama ya koma Maiduguri.
...
Cikin sati biyun kamar yadda ya faɗa ta gama ziyaran ƴan uwa da abokan arziki, da taimakon Ameera ta haɗa kayanta gaba ɗaya. Ameera da Islam basa son tafiyar don sun saba da ita musamman Ameera da wani mugun son Ahmad take, don ma ga ƴan biyun Mami.
Ranar da Dr Awwab ya zo ya kama weekend, bayan ta yi sallama da ƴan gida ya ɗauki matarsa da ɗansa suka koma. Gidan Ummi suka fara sauƙa don ɗaukar Hanan da Batula. Daga nan sai gidansu. Batula girki ta ɗaura na dare, don gidan babu datti jiya ta zo ta gyara.
Nuratu ɗakinta ta wuce ta watsa ruwa ta ma Ahmad shi ma suka yi shirin barci, sallar isha'i ta gabatar. Kasa suka sauƙa lokacin Dr Awwab ya dawo daga sallah. Bayan sun ci abinci kusan ƙarfe goma Dr Awwab ya kora Hanan da Batula ɗaki ya kashe telebijin ɗin.
Dariya Nuratu ta yi ta ɗauke Ahmad suka wuce sama. Wani wankar tayi ta bi lungu da sako na jikinta da turare. Bayan ta gama ta saka wani kayan barcin mai shegen ƙyau, ta ɗauki Ahmad suka nufi ƙofar fita. Dr Awwab yana shirin shigowa suka haɗu a ƙofar. Ahmad ya karɓa ya kwantar cikin gadonsa ya lulluɓesa ya masa addu'a, kafin ya juya gurin Nuratu.
Janta kawai ta yi ta faɗo jikinsa suka zube saman gadon, da mukunnin gefen gadonta ya kashe wutar ɗakin.
Daga nan ya buɗe musu shafin soyyaya, sai da abu ya ƙanƙama ganin Dr Awwab yana shirin bin hanyarsa ta taresa da sauri.
"Menene kuma?"
Ya faɗa da ƙyar jin wani sabon salon da za ta masa.
Ƙasa ƙasa ta ce.
"Hayat babu wani irin tsarin haihuwa da za mu yi?"
"Wani irin kuma tsarin haihuwa? You means family planning?"
Kai ta ɗaga masa ƙasa ƙasa tace eh. Tsaka ya yi ya saketa yana komawa gefe yana sauƙe numfashi. Ganin ransa ya ɓaci ya saka Nuratu rumgumesa.
"Ka yi haƙuri don Allah, ban san hakan zai ɓata maka rai ba."
"Bana son tsarin haihuwa Noor kwata kwata. Ko har kinyi?"
Da saurinta ta girgiza kai alamar a'a. Rumgumeta ya yi ya ce.
"To bana so. Ki haifamin ko ɗari ne ina so in dai daga gareki ne ina so."
Kirjinsa ta buga cikin shagwaɓa.
"Ɗari dai Hayat."
"Yes My Baby love."
Ya ce ya rufe mata baki da nasa ya fara kissing ɗinta. Duk kwanakin da ya ke binta bashi sai da ya fanshe a daren. Tamkar yau ya fara saninta haka ya rikice mata ya hanata sakat.
...
Tun ranar da lokacin ahlin suka buɗe rayuwarsu