Follow us on social media
Showing 96001 words to 99000 words out of 148866 words
Chapter 33 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
yi.
...
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE (Haske) 46.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Fuskarsa ya haɗa da nata ya sumbaci leɓɓenta, ƙasa ƙasa ya fara ƙiran sunanta.
"Babyna! Baby!!"
Cikin baccinta mai daɗi taji ƙiran daf da ita, buɗe idanuwanta ta yi cike da bacci, fes cikin nasa idon da ya saka cikin nata. A zabure ta miƙe garin sauri ta haɗa goshinsu ya bugu.
"Awwch."
Su ka faɗa a tare, kowanne ya dafe goshin sa, Dr Awwab ya yi ta maza ya sa ke goshinsa, yana ƙoƙarin ɗaura hannunsa saman goshin Nuratu ta ja baya ta sauƙa a gadon gaba ɗaya, hakan ya sa ya basar.
"Ki yi wanka ki zo mu ci abinci, Ummi ta aiko."
Jin abin da ya faɗa ya sa ta shigewa bathroom ya bita da kallo. Kusan minti ashirin ta gama wankan, ta leƙo kanta, tsammaninta duk Dr Awwab ya fita. Jin ƙarar buɗe ƙofar ya sa shi kai kallonsa gurin su ka haɗa ido, da airpods a kunnensa da alamar waya ya ke amsawa.
Da sauri Nuratu ta koma ta rufe ƙofar, hakan ya sa shi ya taso zuwa bakin ƙofar ya tsaya, bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron bayanin da ake masa ta wayar.
Jin shuru ya sa ta buɗe kofar a hankali tare da leƙo kanta, ganinsa tsaye a gurin daf da ita a mugun tsorace za ta koma ya fizgota ya fito da ita ya haɗata da ginin gurin.
"Wai tsorona ki ke ji?"
Yace bayan ya cire airpods a kunnensa yana mayarwa. Za tayi magana ya ɗaura yatsarsa saman leɓɓenta alamar tayi shiru. Dolenta ta haɗiye maganarta. Yana sauraran bayanin wayar yana amsawa da eh ko a'a, idanuwansa akan Nuratu yana bi da kallo, kanta ƙasa zuciyarta yana bugawa, domin haƙiƙa ta ji idanuwan Dr Awwab suna yawo a jikinta gaba ɗaya, towel ne jikinta ko gwiwa bai kai ba.
Sun kusa mintuna shida a haka kafin ya gama wayar ya kashe ya ƙara kusanta kanshi gareta, tsorone ya ziyarci zuciyar Nuratu jin yadda ya matso daf da ita, numfashinsa yana bugun fuskarta, ta ƙara mannewa da gini, jikinta ya hau rawa, sai lokacin ta samu bakin yin magana murya yana rawa.
"Don Allah ka matsa kin in wuce, kaya zan sa ka."
Yatsun hannunshi ya sa ka a fuskarta ya ɗago kanta suka hada ido da idanuwanta da suka cika da ruwan hawaye, tayi saurin juyar kanta gefe. Murmushi Dr Awwab yayi yana bin fuskarta da kallo.
"Hausawa su ka ce duk wayon amarya sai ansha zumarta, gashi ni tawa amaryar kwananta ɗaya har yanzu ban sha ba."
Jin abin da ya faɗa shi ya ƙara tsorata Nuratu ta fara ƙoƙarin kwace fuskarta ta wuce ta gefenshi ya sa ka hannunshi ya riƙeta sosai yana haɗa fuskar su waje ɗaya, numfashinsa yana sauka bisa na ta tana shaƙa.
"Daga yau zuwa gobe ki bar angonki ya ɗanɗani zumar ki Babyna please.'
Dr Awwab yace cikin wani irin yanayi da ya jima bai ji shi ciki ba.
Nuratu ta kasa motsi kwakkwara dan yadda ya mata riƙo ba wasa ba
Hawayen idonta ne ya zubo bisa kumatunta lokacin da ta ji ya ɗaura leɓɓensa saman nata. A hankali cikin nutsuwa ya fara tsotsan bakinta da ya jima yana burin tsotsa. Ta kasa hana shi ta kasa kwacewa, tana jin shi har tsawon mintuna kafin ya sa ki bakinta ya sassauta riƙon da ya mata.
"Ki shirya ki fito ina jiran ki."
Haka kawai yace ya saketa gaba ɗaya ya fita a ɗakin, idan ya ci gaba a wannan safiyar za a yi wani abun.
Nuratu ka sa tsayuwa tayi ta zauna bakin gado dan shi tafi kusa da shi ta fara share hawayenta, kusan mintuna biyar ta miƙe ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗauki riga da skirt na atamfa mai ratsin ja da ruwan goro ta saka. Ba ta yi kwalliya sai hoda da ta shafa ta saka kwalli da jan baki ja kaɗan ta saka turare kafin ta fita.
Ba ya falonta hakan ya sa ta fita ta fara sauƙa, mamakin girman gidan da kyawunshi da uban kuɗin da Dr Awwab ya kashe ta ke.
A saman dinning ta hangosa, har bakin dinning table ɗin ta ƙarasa ta zauna ta ka sa haɗa ido da shi balle ganin in da yake.
Kasa taɓa komai tayi bayan zamanta, ganin haka ya sa ka Dr Awwab yin murmushi ya jawo warmers ya zuba a plate ya ajiye mata gabanta ya saka fork, ya ɗauki cup ya haɗa tea ya hau sha yace.
"You can start."
A hankali ta ɗauki fork din ta fara cin abincin da ya zuba mata ya ajiye, Dr Awwab bai yi gigin saka hannu ba dan kar ya takura mata ya zuba mata ido yana kurɓan tea kaɗan kaɗan, movement din da ya shuɗe yanzu yake masa yawo a kai, bai ƙi ya kara ba yake ji.
Sai da taci sosai kafin ta tura alamar ta ƙoshi, ganin haka Dr Awwab ya ja plate ɗin gabanshi ya ajiye mata cup ɗin hannunsa.
"Ki sha na ƙoshi ni ma."
Sai lokacin ta kalleshi, ya kafeta da lumshashshun idanuwansa, da sauri ta kawar kanta ta ɗauki cup din ta sha kaɗan ta ajiye, tana kallo ya hau cin wanda ta rage. Tana ajiyewa ta miƙe.
"Ina za ki je?"
Ya tambayeta yana bin ɗinkin jikinta da kallo, kayan sun zauna a jikinta sosai.
"Zan gyara ɗaki."
Tace tana wucewa sama ya bita da kallo har ta ɓacewa ganinshi. Nuratu ɗakinta ta gyara duk da bai yi wani datti ba ta fito ta sauƙa ta wuce kitchen ta ɗauko tsintsiya da parker da mopper ta koma ɗakinta, Dr Awwab yana gamawa ya wuce ɗakinsa, hakan shi ya bata daman zirga-zirga. Da ta gama ta sauƙo falon ta tattare dinning din ta kai kitchen ta share falon da shima ba datti, ta gyara ta wuce kitchen ta wanke kayan da su ka ɓata, bayan ta gama ta tsaya kallon kitchen ɗin da yayi mata kyau sosai. Mami da yayunta sunyi ƙoƙari, sun mata kayan zamani da gara da laifi.
Falonta koma tana mamakin shurun da ta ji.
Ko Dr Awwab ya fita bai sanar mata ba?
Ta tambayi kanta.
Ɗakinta ta shiga ta ɗauki wayarta ta fito falon ta zauna tana ƙiran Maminta.
"Mamina ina kwana."
Nuratu tace bayan Mami ta amsa sallamarta. Daga ɓangaren Mami tace.
"Lafiya lau Nuratu, ya gajiyar biki."
"Allahamdulillahi Mami."
"Ina su Aunti Rahma? sun tafi?"
"Eh ba su gama tafiya ba sai anjima ko gobe."
"Ai wallahi Mami fushi na ke musu, za su tafi su barni ni ɗaya."
Nuratu tace tana bata rai kamar tana gabanta.
Murmushi Mami tayi tace.
"To sai hakuri. Ki ci gaba da hakuri da biyayya Allah baku zaman lafiya."
Ameen Nuratu ta amsa ƙasa ƙasa, nasiha Mami ta ci gaba da mata kafin suyi sallama. Kwanciya ta yi sama doguwar kujeran da take ta faɗawa tunani. Wai yau ita ce matar aure. Abin da bata taɓa tsammani ba.
Ba ta ji shigowarsa ba sai tafiyan tsutsa da ta ji ana ma kafarta, a tsorace ta janye kafar tana miƙewa zaune ta ga Dr Awwab ne.
"Tunanin me ki ke haka. Ni? Gani nan."
Dr Awwab yace yana zama gefen gadon kusa da Nuratu da ta sunkuyar kanta ƙasa.
"Me ki ke tunani Babyna?"
Ya faɗa yana kamo yatsun hannunta ya murza.
"Babu komai, kawai gida na ke tunawa."
Tace tana turo baki, tare da ƙoƙarin janye yatsunta.
Bakin yabi da kallo yana murmushi yace.
"Tun yau Babyna, yanzu fa aka soma."
"Ni dai nayi kewar su. Ka ɗauko min Hanan don Allah."
"Hanan dai?"
Yace yana sakin dariya ya kwantar kanshi saman gadon bayan ya ba ta dama ta zare yatsunta cikin na sa, duk ya lura da ita amma ya basar.
Ganin ya kwanta ta juya tana fuskantar shi.
"Eh mana, ka ga za ta ɗauke mini kewa."
"Hakane, amma ba yanzu ba, sai mun gama amarci."
Shuru ta masa taƙi masa magana, ganin haka ya ɗago kansa yana kallonta.
"Hanan za ta dawo amma ba yanzu ba. Na je gida Ummi tana gaishe ki."
Ƙasa ƙasa tace.
"Ina amsawa."
Kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa ya tashi zaune yana riƙo hannunta ya maida ita ta zauna.
"Waya ce miki amarya tana aiki. Please ki huta."
Kai ta gada tana jan baya kaɗan, ta ɗauki wayarta ta kunna Data, sakwanni su ka yi ta shigowa na ƙawayenta da basu samu zuwa ba, tana ta mamakin ina su ka ji dan ba tayi gayya ba sai wanda suka samu labari su ka zo.
Ganin shurun ya yi yawa ya sa shi dubanta, hankalinta akan wayarta, murmushi ta ke dimples na ta yana lotsawa dukka biyu. Zaune ya miƙe ya kai yatsansa cikin ramin gurin ya tura.
"I love your dimples Baby."
Tin lokacin da ta ji sauƙar yatsarsa saman fuskarta ta fara ƙoƙarin kawarwa gefe ya riƙe sosai yana gyara zamansa.
"Ki na mini rowar kan ki wallahi. Ni kuma babu sassaucin da zan miki. Yes Baby, ko in fara gwada miki."
Ya ƙara faɗa ganin har lokacin tana ƙoƙarin kwace jikinta. Ba ta yarda da batunsa ba sai da ta ji hannunsa cikin rigarta saman shafeffiyar tumbinta. A mugun tsorace ta riƙe hannunsa.
"Ka bari mana don Allah."
Bai kulata ba dan ya lura tana son nuna masa ƙauyenci a wannan harkar. Shi kuwa hakan baya tsarinsa, a ci soyayya a nuna juna so tamkar babu gobe. Ƙara shiga cikin jikinta ya yi sosai ya tura fuskarsa tsakanin wuyanta yana shaƙar fititinannen ƙamshin jikinta da ke tashi, yayin da hannunsa ke shafa saman tumbinta, tsantsi da laushin fatar jikinta na jefasa cikin wani yanayi.
"Zan ma ka kuka."
Nurata tace ganin ya kasa dai na abin da ya ke mata. Jin abin da ta faɗa ya sa ka Dr Awwab ɗago fuskarsa ya zuba mata idanunsa da su ka fara canza launi, su ka ƙanƙance cike da fitina. Runtse idanunta ta yi, hakan ya basa damar haɗa bakinsu ya fara tsotsan bakinta.
Shuɗaɗɗiyar lokacin da ya wuce ya dinga dawowa ƙwaƙwalwar Nuratu, tuna hakan ya sa ta kwace bakinta ta fashe masa da kuka. Rumgumeta ya yi yana shafa bayanta, bai zai iya mata abin da ba ta so ba, amma shi kam ba haka ya so ba.
Cikin sanyin jiki yace.
"Shish is ok My Baby."
Ajiyar zuciya ta fara sauƙewa bayan tsagaita kukanta, ɗumin jikinsa yana ratsata da ya haifar mata da kasala ta ƙara kwancewa a kirjinsa ba ta ankara da hakan ba. Kusan mintuna biyu kafin ya ɗagota jin ta yi shuru numfashinta ya dawo dai dai.
Yatsunsa ya saka yana goge guntun hawayenta, ya kalli gaban rigarsa.
"Aww dubi kin ɓata mini riga da baƙin kwalli."
"Sorry don Allah."
Tace cikin sanyin murya, sai ta ji duk babu daɗi. Duk abin da ta ke masa bai taɓa nunawa ya yi fushi ba, sai dai ma ya maida abin wasa, ya ci gaba da nuna mata cewa yana sonta ko ya yane.
Suna zaune shuru baƙi suka fara zuwa dan ganin gidan amarya hakan yasa Dr Awwab fita ya bar gidan.
...
Bayan fitan Dr Awwab a gidan Ummi da safe, Ammi da jikokinta su ka shigo gidan dan yau ake wunin gidan ango. Ba ta da ƴaƴa mata sai marigayiya Sumayya da ta bar mata ƴaƴanta uku riƙonsu ya dawo hannunta. Sai Yayunta maza biyu da kannenta maza uku. Kwana ta yi ta tashi da fuskar da ta gani mai kama da na Sumayyar ta. Hakan shi ya fama mata rashin Sumayya, ta farka cikin rashin walwala har ta taho gidan wunin.
"Ammi me ya faru ne? Na lura ba ki da walwala yau kwata kwata."
Ummi tace ganin yanayin matar yau sam babu walwala a tattare da ita. Numfashi ta sauƙe.
"Ummin Awwab na kasa samun nutsuwa tun jiya, bacci kirki na kasa yi, fuskar yarinyar nan ya kasa barin zuciyata. Ba dan Babansu Aliyu bai taɓa sanar da ni cewa bashi da wasu ƴan uwa ba, da zan ce tabbas yaran nan akwai jini a tattare da su, musamman wannan babbar cikinsu."
Ummi da ita ma hakan ɓangarenta tun ba yau ba, jiya ma abin ya ƙara dilmaye lissafinta da tunaninta, da damunta bayan kuma wanda kwanaki ya sakata ta kafa ayar tambaya tace.
"Hakane Ammi, tabbas akwai wani abun ɓoyayye tsakaninsu. Amma ba mu san ta ina ba. Ta ya? Ba su taɓa sanar mana ba. Mahaifin Awwab har ya koma ga mahaliccin shi ba mu taɓa maganar wa su danginshi ba, balle ma bana jin su ɗin sun haɗa dangi da su, sai dai ikon Allah babu ta in da baya bayyana abu."
Shuru dukkansi biyun du ka yi kafin Ummi ta miƙe dan fita amsa ƙira da aka mata.
"Ki kwantar da hankalinki, InshaAllah Allah zai bayyana komai."
Ummi tace ta fita ta bar Ammi cikin juya wannan lamarin da ta rasa me warware mata.
...
Gidan amarya Nuratu bai rabu da masu ganin gidan ba bar karfe biyar. Aunti Ikhram da Zaituna duk sun zo, har Hassana da Hussaina da Hanan da ta maƙalewa Nuratu ta zauna a jikinta. Bayan an fara watsewa su ka tattare mata gidan su ka gyara su ka saka mata turaren wuta ganin babu ƴan uwanta, kuma tana buƙatan hakan, kafin su fara haramar tafiya.
"Tashi mu tafi Hanan."
Faɗin Hussaina tana ɗaukar jakarta ta miƙawa Hanan hannu, maƙalewa ta yi jikin Nuratu.
"Ku barta mana."
Nuratu tace ita ma, dan tana son hakan ko dan ta rage mata kewa.
"Rufamin asiri. Zo mu tafi Hanan."
"Ni da Aunti Noor zan zauna."
Tace tana make kafaɗa.
...
Tun shigowar su gidan ba ta hau saman ba balle ganin ɗakin amarya, dan ta shaƙa iya shaƙa ganin dukiyar da aka narkar a gidan. Ta ji haushi sosai kuma har lokacin ta ci alwashin shigowa cikin gidan.
Ganin shuru Hussaina ba ta sauƙo da Hanan ba ya saka Aunti Ikhram aikenta ta ƙirata.
Ba ta so ba ta hau saman, banka ƙofar ɗakin ta yi, da ya saka Nuratu da Hussaina kallon ƙofar su ka ga Binta tsaye ranta haɗe.
"Hussaina ku sauƙo mu tafi in ji Aunti Ikhram."
"Hanan ce ta ƙi, ku bar mini ita."
Nuratu cikin sanyi ganin kamar Binta ba ta da daɗi.
Tsaki Binta ta ja bayan ta watsa Nuratu harara da kallon ba ki isa ba, ta ƙarasa shigowa ɗakin ta finciko Hanan daga jikinta ta dauƙeta, ganin haka Hanan ta saka kuka sai ta zauna, ba ta saurareta ba ko bin abin da Nuratu take cewa m ta fice a ɗakin. Ganin haka Hussaina ta yi wa Nuratu sallama ta fita suka barta ita ɗaya. Tashi ta yi ta buɗe labulen windown ɗakinta, tana kallo Hanan na kuka suka sakata a mota suka wuce. A sanyaye ta sake labulen ta fita.
Sun gyara falon sun gyara ko ina sai ƙamshi yake, ɗakinta ta koma tayi wanka ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar magriba.
Tana cikin sallar Dr Awwab ya shigo cikin sallama, ganin tana sallah ya zauna ta idar ta miƙe ta linke darduman ya miƙe tsaye.
"Ki same ni a falo, saura kuma ki jima."
To tace ya fita ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗauki riga doguwa na material marar nauyi da hayaniya ta saka, turare kawai ta saka ganin dare yayi ta yafa kanta ƙaramin gyale ta fita.
A falonta ta sameshi zaune yana kallon labarai ta zauna ɗayan kujera. Hankalinsa ya dawo da shi kan Nuratu da ta ɗaura idonta saman Tv kamar mai fahimtar wani abu. Remote ya ɗauka yayi searching zuwa MBC Bollywood ya kai mata.
"Na san mata da son kallon Indian drama."
Murmushi tayi bata ce komai ba dan ba ƙarya in bata da abin yi tana kallon shirin su da American. Hira jifa jifa ya ke mata dan kawar da shurun, sama sama ta ke amsawa da eh da a'a har suka gangaro hiran gobe yace.
"Yanzu dole goben nan sai kin je."
"Eh mana, kaya kawai zan karɓa in dawo ai."
Ganin yadda ta yi da fuskarta ya sa shi ya murmusa.
"To Allah kai mu lafiya. Na godewa Allah ma da aka yi auren nan, da yanzu babu auren nmfa can wani ƙasar za su tura min ke. Tab da kin ga zirga zirga."
"Sai ka je, ai ba'a bari."
Nuratu tace da sauri tana kallonshi, yayi murmushi ta mayar da hankalinta kan Tv ta ji yace.
"Na shiga wani ƙasa ma balle zuwa wani garin. Kin manta ance garin masoyi baya nisa."
Ba tace komai ba dan ta yarda zai aikata, dai-dai lokacin ana ƙiran sallar isha'i ya miƙe.
"Bari in yi sallah in dawo, zan kai mintuna talatin zuwa sama a waje kar ki ji shuru."
"A dawo lafiya."
Tace ya amsa da ameen ya fita, kafin ita ma ta miƙe dan sallar ta shige ɗakinta. Tana idar da sallar ta dawo ta zauna ta ci gaba da kallon dan dawowarsa.
...
#vote.
#comment
#share.
MADUBIN GOBE (Haske) 47.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Ƙarfe tara Dr Awwab ya shigo gidan, kitchen ya wuce ya ɗauki plate da cup, falon ƙasan ya kashe wuta da komai ya hau sama, falon Nuratu ya shiga ya sameta kwance saman doguwar kujera tana kallo. Tana jin ya shigo ta miƙe zaune.
"Sannu da zaman kaɗaici."
Ya faɗa mata da murmushi yana ƙarasa ciki.
"Yawwa Barka da dawowa."
Nuratu tace tana gyara zamanta sosai. Shima zaman yayi kusa da ita yana ajiye abin hannunshi ya ce.
"Je kiyi alwala ki zo muyi sallah ko? Mu godewa masa."
"Nayi sallah ai."
Tace ƙasa ƙasa cike da tsoron da ya fara sauƙa mata, har wani tsuma jikinta ya fara, tasan yau duk gudunta duk wayonta babu mai iya kwatarta hannun Dr Awwab da ta hango babu alamar sassauci ko ɗaga ƙafa a tare da shi.
Dariyar da ya ke tasowa Dr Awwab yayi ƙoƙarin dannewa amma duk da hakan bai hanasa murmusawa ba ya juya yana fuskantarta, ƙamshin da yake tashi a jikinta kaɗai ma ya fara tasiri a jikinsa, ya fara amsarshi tun yanzu. Kallonta ya yi alamun tsoro duk ya bayyana a jikinta musamman fuskarta.
"Na sani ai, wannan dabanne. Ki fito mana da abin sallah, bari in yi alwala nima."
Dr Awwab yace ta miƙe ya fita, Nuratu kamar tayi kuka ta miƙe ta wuce ɗakinta, alwala ta yi ta saka hijabinta ta ɗauko sallayu biyu ta fito ta samu ya shigo. Karɓa yayi ya taimaka mata ta shimfiɗa ya kashe Tv kafin yaja su suka gabatar da sallah raka'a biyu, ya jima yana musu addu'a tana amsawa da ameen a hankali, haka ya juyo ya dafa kanta ya mata kamar yadda Annabinmu Muhammad (SAW) ya koyar damu.
Nuratu duk ta tsorata, zuciyarta sai buguwa yake tamkar ya fito, tsoro ya cika ilahirin jikinta. Abu biyu ya sakata tsoro, farkon kasancewarta da namiji da kuma abin da ya wuce ya ke dawo mata.
Yadda jikinta ke rawa har Dr Awwab