Follow us on social media

Showing 108001 words to 111000 words out of 148866 words

Chapter 37 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

28

Baby, wasa nake miki. Zo in ya bi kwalliyar. Na san dai ni aka ma ko?"

Ya ƙarasa maganar yana kallon cikin idanuwanta, ta lumshesu tare da ɗaga masa kai. Ba zato ta ji saukar bakinsa saman nata ya haɗa ya fara kissing ɗinta. Tana jinsa ta kasa hanashi ta ƙara damƙe idanunta. Sosai ya yabi kwalliyar, bai barta ba sai da yaji duk ɓacin ransa ya gushe.
Bayan komai ya lafa ya rumgumeta cikin jikinshi, hancinta yaja ganin tana lumlumshi ido.

"Kar kimin barci raguwa."

Murmushi Nuratu tayi ta rufe idonta cike da kunya jin abinda yace. Wato ya lura barci take daga zaran komai ya lafa. To shiɗin ne bana wasa ba, sai ya gajiyar da ita lis.
Tana jinsa ya sumbaci lips ɗinta ya miƙe, ba zato ta ji an ɗagata sama. Da sauri ta buɗe idanunta tana tattaro bedsheet ta rufe jikinta da shi ta riƙosa. Cikin bathroom ya ajiyeta duk yanda ya so ya taimaka mata ƙi tayi, ya rabu da ita ya fita, gyara jikinta tayi kafin ta fito ya shiga. Ɗakinta ta wuce ta canza kaya ta gabatar da sallar la'asar kafin ta sauƙo.

Dr Awwab masallaci ya wuce ya dawo, sai lokacin wajen ƙarfe huɗu su ka ci abincin rana. Haka suka wuni a gidan Nuratu tana lura da shi minti minti sai ya yi tsaki. Ganin bai sanar da ita ba ya sata kasa tambayarshi dalili. Haka har dare ya kwasheta suka haura sama, babu abin da ya mata ya sata cikin jikinshi su kayi barci.
...

Washegarin babu in da yaje a gida ya wuni har lokacin ransa dai a haɗe, duk ƙoƙarinshi ganin ya kawar da abin a ransa ya kasa. Sai ya ga Nuratu yake ƙoƙarin kawar da komai ganin duk itama ta hana kanta walwala. Ita ma duk yanda ta san zata cire masa damuwarshi ta yi.
Bai leƙa gidan Ummi ba ranar har dare ya saka Nuratu ta shirya suka fita. Abaya ta saka da mayafinsa ta samesa a wajen mota ta shiga.

"Anya za mu fita kuwa."

"Lafiya wani abun ya faru?"
Nuratu ta tambaya tana bin jikinta da kallo ganin shima idonshi na yawo a jikinta.

"Kinyi kyau ne, ina kishi. Gaskiya sai dai ki zauna a cikin mota."

Murmushi tayi tace.
"Eh na ji zan zauna."

Faɗar haka shi ya sashi jan motar suka bar harabar gidan. Cikin gari su kayi ya saya musu kayan ciye ciye suka dawo gida. A falon suka baje su ka ci, shi ya ci kazar da ya siyo Nuratu ice cream ta sha ta ci gaba da kallo.

Sai da ya gama ya kai komai kitchen, ya fito ya sunkuceta suka wuce sama, ganin ya nufi ɗakinsa tace.

"Zan shirya dan Allah Doctor."

"Na ƙi wayon."

Yace suka wuce sama sai ɗakinsa, wutar ɗakin ya kashe. Akan gado ya ajiyeta ya bi yana sumbata tare da buɗe musu sabuwar shafin soyayyarshi da ya rikita Nuratu, domin daren ranar manya manyan sakwanninshi ya koyar mata kuma yace yana son ta koya. Bata fahimci komai ba dan sun rikitata sun fi ƙarfinta. Barci ne ya kwashe kamar kullum bayan komai ya lafa, ganin haka ya miƙe yayi wanka ya dawo ya kwanta.

...

Kwana biyun ya yi sune tamkar ya jawo su dawo kusa. Yana buƙatar ƴarsa kusa da shi, yaga halin da take ciki.

A bakin gadon ya tsaya tare da rankwafowa saman kanta ya tsura fuskarta ido, ruwan saman gashin kansa ya fara ɗiga saman fuskar Nuratu da take barci hankali kwance, ta duƙunƙune cikin bargo sai fuskarta kaɗai a waje. Fuskarta fiyau sai yaga tayi haske, jajayen leɓɓenta ya zuba ido tamkar ba daren jiya ya moresu ba son ransa.
Ya shagala da kallonta ya mance da shirin da zai yi. Motsa idanuwanta ta fara tare da motsa leɓɓenta cikin magagin barci. Bai matsa ba bai kuma ɗauke kansa daga gareta ba har ta buɗe idanunta ras a kansa.

Murmushi ya sakar mata tare da shafa kumatunta.
"Good morning sleeping beauty."

Kallonsa tayi karo na biyu sai lokacin ta lura dagashi sai rigar wanka ya ɗaure. Idanuwanta ta mayar ta rufe. Murmushi ya kuna saki yana matsawa.
"Buɗe ki kalli sadakinki Babyna, halal ɗinki ne, shaidu sun shaida."

Girgiza kai tayi tare da jan bargon har saman kanta ta rufe, wani muguwar kunyane ya kamata. Shirinsa ya hau yi cikin ƙananan kaya kamar kullum riga fari an rubuta PUBG a gaban rigar sai wando baƙi na jeans. Turare ya fesa da ya kauraye ɗakin da ƙamshi.

"Na kamaki. Na miki ƙyaune?"

Ya faɗa yana juyawa tare da nufan kan gadon. Tun da ya fara fesa turaren ta ciro kanta sanin sai ya gama shiryawa yake shafawa. Ta cikin madubi ya ganta sai dai bai bari ta gane ya ganta ba sai da ya gama.
Zama yayi gefenta ya yaye bargon ya buɗe fuskarta.

"A farashin nawa kika kalleni?"

"Ni fa ba kai nake kallo ba."

Tace tana tura baki. Ganin kallon da yake mata ya sata rufe fuskarta da tafin hannunta. Hannunsa yasa ya cire fuskarsa ɗauke da murmushi.

"Wannan bakin... A biyani da shi sai in yafe."

Jin ya canza salon maganar ya sata itama cewa.
"Bari nayi wanka."

"Wayo ko?"

Marairaice masa tayi tana girgiza kai, dan tasan ya kamasa ba bari zai yi kusa ba. Miƙewa yayi tsaye yana ɗagata ta tashi zaune.

"Zan ɗan fita kafin ki gama, bazan jima ba. Ki kularmin da kanki."

Daga haka ya sunkuya ya sumbaci kumatunta da leɓɓenta kafin ya fita ta bisa da kallo. Yayi mutuƙar yin kyau sosai.

...

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE 51.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.



***

Cike da farin ciki Binta ta miƙe ta shiga ɗaki ta fito cikin ƙamshi ta gyara fuskarta cikin kwalliya. Ta samu Hanan da ta hana fita suka fita tare. Yana ganin fitowarsu ya hango hannunsu sarƙe da juna. Hakan ya mutuƙar ɓata masa rai ya ƙara haɗa rai sosai.

Ƙwanƙwasa gilashin motar Binta tayi, ya sauƙe ya ɗaura idonsa saman Hanan.

"Daddy."

Tace da ƙarfi tana son kwace hannunta Binta ta hanata tana bin Dr Awwab da kallon ƙauna tsagwaran tace.
"Daddyn Hanan mu shiga ciki mana ka gaishe da Mama, ta samu labarin zuwanka fa."

Sai lokacin ya kalli Binta suka haɗa ido, da sauri ya kawar da kansa, baya son ko ganin fuskarta balle jin muryarta.

"Ki sakar mini hannun yarinya ta shiga mota."

Ƙara ƙasa da murya tayi cikin salon takunta da ta shirya masa.

"Haba Doctor kayi haƙuri mana, cikin mintuna da bai fi biyar za ku gaisa."

Binta tace tana rankwafo da kanta. Ji yayi ya kasa mata musu yace.
"Matsa a ƙofar."

Da sauri Binta ta matsa ya buɗe motar ya fito, ganin haka Hanan ta isa wajensa ya ɗagata sama suka nufi cikin gidan, Binta a gaba tana kwarkwasa.
Da hoton Nusaiba dake maƙale a falon ya fara cin karo, tayi kyau fuskarta ɗauke da murmushi, tana sanye da abaya. Ya so kamannin Hanan ya zamto nata, sai dai Allah yasa da shi za tayi kama.

Kansa ya ɗauke yana zama saman kujera, Hanan ta haye kan cinyarshi. Da sauri Binta ta wuce ciki ta ƙira Mama suka fito tare. Binta tana ɗauke da jakan kayan Hanan.

"Ina wuni Mama."
Dr Awwab yace da ƙyar yana miƙewa tsaye. Da hannunsa ɗaya ya ɗauka jakan kayan Hanan. Ya riƙo hannunta da ɗaya.
Mama da take binsa da kallo ta girgiza kai tana cewa.

"Lafiya lau Awwab, ba za kasha ko ruwa ba?"

"Bana buƙata."
Yace ya fita. Ganin haka da sauri Binta ta bi bayanshi, har ya shiga mota ta zagaya ta tsaya gefenshi.

"Haba Doctor me yasa baka mantuwa? Kayi hakuri mana, abin da ya faru ya riga ya faru ya wuce, ɗan adam ajizine, munyi kuskure mun gane laifinmu."

Wani kallo ya watsa mata ya juyar kansa kan titi. Tamkar bazai tanka mata ba kusan mintuna biyu, motar ya kunna kafin ya kalli Binta da ta tsaresa da manyan idanuwanta.
"Magana ɗaya zan faɗa miki, babu ku babu Hanan, kamar yanda ku ka ƙi mahaifiyarta haka bana son yarinyata ta sanku."

Ba ta daddara ba ta gyara tsayuwarta tana faɗin.

"Oh dom Allah ka daina wannan maganar. Wallahi mun gane kuskurenmu kamar yadda na sanar da kai. Ko ba kaga hakan ba?"

Bai kulata ba ko ƙara wani maganar balle gama sauraronta ya ja motar yana barin gurin. Ya bar Binta cike da takaicinsa, sam ya kasa manta abin da ya faru balle har ta samu gurbi cikin zuciyarsa.
'Anya kuwa haƙarsu za ta cimma ruwa?

...

Tafiya yake sai lokacin yaji hankalinsa ya kwanta ganin gudan jininsa cikin ƙoshin lafiya. Kallonsa ya kai kan Hanan ya ga ta zubawa titi ido.

"My Love babu wani abin da suka miki?"

"Babu komai Daddy, Aunti ta bani abu masu daɗi, haka Mama ma. Su waye su?"
Amsar da Hanan ta basa a jere, ƙarshe ta sako masa tambaya.

"Good."
Yace kawai yana shafa kanta, tare da kaucewa tambayarta na ƙarshe. Gidan Ummi ya nufa dan cewarshi sai ya gama amarci kafin ya ɗaukota gaba ɗaya.

...

"Ga ta kuma na dawo da ita. Wallahi idan yarinyata ta ƙara taka ƙafarta ta fita ba tare da sanina ba sai nayi mummunan ɓata muku rai. Oya ku tashi ku bani guri."

Sum ƴan biyu suka wuce ciki tare da kayan Hanan zuwa ɗakinsu.
Ummi da Hanan suka sauƙo tare dan tana zuwa wajenta ta wuce ta rukumkumeta. Fuskar Ummi babu fara'a ta ƙarasa ta zauna.

"Hanan je ki wajen Aunti Husna."

Ta faɗa, babu musu yarinyar ta wuce ɗakin ƴan biyu. Ummi ta juya ta kalli Dr Awwab da shima ransa a haɗe.

"Wato sai da ka ɗaukota. Me yasa kake haka Awwab?"

Sai lokacin ya ɗan saki ransa ganin mahaifiyarsa ranta a haɗe. Ana jimawa kafin aga ɓacin ranta. Cikin kwantar da murya yace.

"Ummi kwana biyu fa kika ce, kuma naga ya cika."

Girgiza kai tayi tace.
"Haka nace, amma ba yana nufin kwana biyu tal ba Awwab. Zuwa wani lokacin tun da hutun makaranta take."

"Ummi bazan iya barinta cikinsu ba, gani nake za su cutar mini da ita kamar yadda suka cutar da mahaifiyarta."

Hannunta ta ɗaura saman nasa. Abin da hakan yake jimawa bai faru tsakaninsu ba, dan wani lokaci tana masa fulako shi yasa shima bai cika sakewa da ita ba.

"Sun canza Awwab ba ka gani ba? Tsoron Allah da dana sani ya shigesu. Basu da burin da ya wuce su shiga cikinmu. To kai me yasa ba za ka manta abin da ya faru ba. Ka bar yarinya ta san dangin mahaifiyarta."

Miƙewa tsaye Dr Awwab yayi bayan ya zare hannunsa yace.
"Kiyi hakuri Ummi abune mai wuya a guri na. Ku kula min da ita."

Daga haka ya fice, Ummi ta tashi ta koma sama tana mamakin rashin mantuwar Awwab akan abin da ya faru a baya. Ita kam ta yafe musu dana basu mata wani laifin ba. Ta sakar musu fuska kamar kowa, ko ba komai jini ya haɗa ta dalilin Hanan.

...

Shuru falon babu komai babu kowa sai ƙaran Tv, har zai haura sama yaji ƙaran ruwa a kitchen, da sauri ya sauƙa ya nufi can. Tana tsaye tana juya miyarta sanye take da dogon wando da riga ya bi jikinta ya mata kyau, dan tsantsine da shi kayan, kanta cikin hula mai kyau ta juya bayanta.
Bayan ya bi da kallo, ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi, domin kwalliyar ya tafi da tunaninsa, idanu kawai ya zuba mata.

A jikinta Nuratu ta ji ana kallonta, ga ɗan duhu da ta gani a kitchen din alamar an tare ƙofa. Cikin sauri ta juya baya, idanun Dr Awwab ƙyam a kanta. Ba shiri ta juya baya domin ba ta tsammaci ganinshi yanzu ba, masa cigaba da aikin tayi.

Ji tayi an dafa kafaɗarta ta runtse idanunta da sauri. Juyo da ita yayi, sosai ta bashi dariya ganin ta rufe idanunta, yayi murmushi ya kai hancinsa kan nata ya goga.

"Kinyi kyau sosai My Baby. Zan ba da kyautar wannan kwalliyar, fatan duk kin haddace karatunmu."

Kunya sosai Nuratu ta ji ta ƙara runtse idanunta tana yin ƙasa da kanta jin maganarshi na ƙarshe. Sauƙar lips nasa ta ji bisa kumatunta zuwa wuyanta yana sumbata. Kusan mintuna biyar kafin ya saketa, da sauri ta juya masa baya ta ji yace.

"Bari in yi sallah."

Ba ta iya basa amsa ba ya fita, dafa inda take tayi tana sauƙe numfashi. Bayan nutsuwarta ya dawo ta sauke miyar ta kwashe a flask ta kai dinning, kafin ta wuce ɗakinta, dama shine ƙarshe dan ta riga ta gama haɗa tuwo. Sallah ta gabatar sai kuma ta ji kunyar fita haka ta canza riga zuwa dogo ta sauƙo.
Da ya dawo daga masallaci ya sameta haka ya haɗa rai.

"Ina kwalliyar nawa?"

"Nayi girki da kayan shine na cire."

"Wayo dai, ai akwai wasu kayan."
Yace yana zama gefenta har jikinsu na gugar juna.

"Zan saka wataran. Abinci fa."
Tace tana canza maganar, dan ita kam wannan kayan ba yanzu za ta saka su ba, sai ta saba dashi sosai dan har yanzu tana jin kunyarsa.

"Kawo mana nan, na gaji da zaman table."

Miƙewa tayi ta kwaso komai ta kawo falon kafin ta zauna ya sauƙo ta zuba musu suka hau ci. Ta ji daɗin ganin yau ya saki fuskarshi ba kamar kwana biyun da ya wuce ba. Kuma taji daɗi yadda ya zage ya ci abincin.

...

Kwana biyun soyayya mai tsayawa a rai Dr Awwab yake nunawa Nuratu, wani mugun kunyarsa take ji sosai har ta rasa dalili, ba ta taɓa tsammani za taji kunyarsa haka ba sai yanzu da yake matsayin mijinta. Kullum sai yaje gidan Ummi duba Hanan da suke rabuwa da rigima sai ta bisa gurin Nuratu.
Amarci yake baya fita aiki dan hutun da ya ɗauka, in abun ya kama yayi a laptop, baya fita ko ina daga gida sai gidan Ummi.

Nuratu tana ƙiran ƴan gida suna ƙiranta dan jin lafiyarta.
Yau ta cika sati ɗaya za'a mata bakwai kamar yadda al'ada ya tsara.

Ummi tun da safe ta turo ƴan biyu suka taimaka Nuratu ta tsife kanta, har da Hanan da ta biyo su ta maƙale mata. Tana son yarinyar.

Bayan sun gama Hussaina tace.

"Aunti kitso za kiyi ko wankewa, amma kanki babu datti sai ƙamshi, kiyi kitso Allah zai fi kyau."

"Duk yanda ku kace shi zan yi."

"Mu ko Yaya Awwab? Ai shi za a yi wa kwalliyar."
Hassana tace tana dariya Hussaina ma ta saka dariya jin abin da Nuratu tace, sai kawai Nuratu ta fara kallonsu domin sun burgeta, komansu ɗaya dan kama suke sosai. Ji tayi da Allah ya bata tana so musamman da Dr Awwab in suka ɗauko kyansa.

Hassana ce ta tsagaita dariyarta tace.
"Bari in ƙira mai lallen ta zo. Har da me kitson, sun iya sosai."

To Nuratu tace tana kama gashin kanta bayan Hussaina ta taje mata. Cikin mintuna talatin mai lallen ta iso ta fara aikinta, lallen ja ta fara saka mata a yatsu maroon kafin baƙi. Mintuna kaɗan me kitso ta iso ta fara mata.
Awa ɗaya da sakawa suka tsinci muryar Aunti Rahma da Aunti Hasiya.
Nuratu kamar tayi tsalle ta rumgume su musamman wacce ta gani a bayansu. Mami ce da Aunti Zarah ta zo ganin ɗakin ƴarta, kamar yadda ake yi ran bakwai uwa za tazo ganin ɗakin ƴarta.

"Mamina don Allah ki zo kusa da ni, ko in tashi in taka lallen."

Nuratu tace kamar tayi kuka. Mamin ma tayi kewar ƴarta da sauri ta matsa kusa da ita, Nuratu kanta ta ɗaura saman cinyar Mami cikin shagwaɓa tace.
"Nayi kewarki Mamina. Fatan kina lafiya."

"Lafiya lau Autana, ya zaman aure?"
Tace tana shafa gashin Nuratu.

Kunyane ya kama Nuratu ta kasa magana. Ta gaishe da Aunti Zarah da Rahma da Hasiya kafin ƴan biyu suka gaishesu suna mamakin wannan ahli.

"Ƙannansa ne."
Nuratu tace da su Aunti Rahma ganin kamar basu ganesu ba, sai da Nuratu ta faɗi haka suka tuna sun gansu ran buɗan kai a gidan Ummi, duk tsammaninsu mutum ɗaya ke wulgawa.

Aunti Zarah ne da Rahma suka ma Mami jagora ta ga falon ƴarta da ɗaki, kafin ta sauko tana yaba ƙyan gidan da godewa Allah da ya bawa ƴarta miji nagari da arziki mai albarka.

Wajen karfe sha biyu Ummi ta iso da nata jama'ar ganin gidan ɗanta. Lokacin Nuratu ta cire lallen ƙafarta dana hannu, an mata kitso ƙanana, tayi wanka ta saka atamfa mai blue da ratsin ruwan toka tayi kwalliya, tayi kyau ga kyallin amarci da take yi.
Kafin zuwan su Ummi Aunti Rahma da Hasiya da Aunti Zarah sun haɗa abinci mai yawa dan baƙi tare da abin sha, haka kuwa bayan gaisuwa suka zuba aka hau ci da sha.
Nuratu dai sama ta hau da yayunta suka sata tsakiya da tambayar lafiyarta. Kunya ya hanata faɗin komai sai murmushi da tayi ta ɓoye fuskarta. Dama suka ba hakan suke son ji ba, fatansu tana jin dadin zama, ta tabbatar musu da haka. Daga nan su ka ci gaba da bata shawarwari.

...

Ta shiga ruɗani sosai, ganin babbar mace da ake ƙira da uwar amarya tayi kama da yarinyar da take ƙira da mai kama da ƴarta Sumayya. Ganin fuskar Mami ya ƙara rikita zuciyar Ammi, domin gani tayi tafi kama da shi akan ƴarta da kuma yarinyar, domin su biyun kamanninsu har ya ɓaci, duk da ta kasance mace shi kuma fuskar girma ya sameshi.

'Lallai akwai ayar tambaya kan waɗannan bayin Allah. Kuma dole sai na binciko.'
Zuciyarta ya faɗa da ta ji tana neman mai amsa mata.

'Ta ya? Ta ina sata soma?'
Ta watsa zuciyarta tambayar da ta rasa mai amsa mata, sai ta nutsu tayi tunani.
Duk inda Mami da Aunti Rahma suka wulga sai ta bisu da ido tana ƙare musu kallo ko akwai inda ta kuskuro cikin kamanninsu. Sai ta ga kallon da take musu yafi ƙara hasko mata tsantsar kamansu, domin komai Aunti Rahma take gani take tamkar Sumayyar ta.

...

'Ba zan taɓa daina ganin kamanninsu da ita ba.'
Faɗin Ummi cikin zuciyarta, da tun ranar da ta saka idonta saman fuskarta ta kasa dai na tunanin hakan. Ta rasa wa za ta tunkara da wannan maganar.

'Awwab da ya jawo komai, kuma ya nuna bai ga hakan ba, sannan ya nuna tamkar bai san meke faruwa ba.  Ko kuma waye?'
Wani sashi na zuciyarta ya faɗa mata haka.

...

Dr Awwab bai san meke faruwa ba, dan tun fitarshi na safe ya wuce ɗaurin auren abokinsa daga masallacin juma'a. Ƙarfe biyu da mintuna ya shigo gidan, tun a harabar gidan ya ga motar Ummi da sabbi wasu kusan biyar. Sai da ya isa kofar falon ya ji hayaniya ya buɗe ya shiga.
Ummi da baƙinta suna Awwab a sama, Mami da nata baƙin a falon ƙasa. Bini bini Nuratu ta cukwuikuye Mami, duk faɗar Aunti Hasiya haka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login