Follow us on social media

Showing 78001 words to 81000 words out of 148866 words

Chapter 27 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

46

ƙarshe suka dangana da asibitin mahaukata da ke Maiduguri, bayan gwaje gwaje da Docter yayi ya samu harda cutar zuciya da ya kamashi dan hayakin sigarin da yake sha ya fara lalata masa. Yau suke shirin tafiya, da Ummu kaɗai sai Daddy za a tafi, daga asibitin za su wuce sun dawo gida dan shirya kayan su.

A ƙofar gidan ya yi parking ɗin motarshi, dan ya je har ofishin sa ance bai fito ba kuma baya fitowa yanzu, sannan sun samu labarin yau zai bar gari. Daga nan ya nufo gidanshi bayan kwatance da aka masa cikin sauri dan ya same shi.

Bayan sauƙar shi a motar ya ƙwanƙwasa get ɗin gidan mai gadi ya buɗe masa ya shiga.

"Alhaji Kashim yana nan?"
Alhaji Mamman ya tambaya yana gyara jakan hannunsa tare da babbar rigarshi.

"Eh yanzu ya shiga ciki amma zai fito."
Faɗin mai gadi ya bawa Alhaji Mamman gurin zama ya zauna dan jiran shi. Gidan yaje bi da kallo ɓangare ɓangare uku, gidan babba ne, an zuba kuɗi gurin mallakar shi, ga motoci kusan huɗu a fake.

Tun jiya ya harhaɗa masa kuɗaɗensa, har sai da ya haɗa da kuɗin cinikin da suka tara na sati kafin ya samu kuɗin ya cika, dan samun kuɗi gurin Alhaji Kashim bai iya ajiyewa ba ya hau kai ya kashe. Babu abin da ya rage masa sai shago da kayan ciki, kuɗaɗensa kaf ya haɗa kafin ya haɗawa Alhaji Kashim kuɗaɗensa. Duk ya rame yayi duhu dan tunanin kuɗaɗen shi da har cikin ranshi yake jin zafin rashin su.

Mintuna ashirin Alhaji Kashim ya fito da Ummu cikin sauri ɗauke da kayansu suka shiga mota, ganin haka da sauri Alhaji Mamman ya miƙe ya isa wajensu.

"Ina kwana Alhaji."

"Lafiya ƙalau. Alhaji Mamman?"
Faɗin Alhaji Kashim yana mamakin ganinshi wannan lokaci.

Jakan hannunshi ya miƙa masa cikin motar.
"Fatan abin da ya haɗa mu ya raba, ga kuɗaɗen ka nan na dawo maka da su."

"Nagode, mu je driver."

Alhaji Kashim ya faɗawa driver, kafin ya rufe gilashin motar direba ya ja motar suna fita a gidan. Ko ba komai ya ji daɗin dawo masa kuɗinshi da yayi, dan shima yana buƙatar su domin fitar da Mufid ƙasar waje dan binciken lafiyar shi.

Alhaji Mamman ji yayi ya sauƙe wani kaya, amma ya ji haushi da baƙin ciki rashin kuɗinshi da yayi.

***

Dr Awwab gyaran gidanshi yake sosai, sama da ƙasa, sama ɗakunan baccin su, ɗakuna uku ɗaya na shi, gefen shi na Nuratu, sai can daga ƙarshe na Hanan da ƙannenta masu zuwa a cewar shi. Ƙasan falo ne babba da ɗakin baki da dinning area, sai kitchen da store da ta hanyar dinning da zaka isa ciki. Ya bar fenti da sauran abubuwan sai Nuratu za ta tare.

...

Yaya Al-ameen duk yadda zai yi yayi ƙoƙarin cire Nuratu a ran shi tunawa da yanzu ta zama matar aure, da addu'a ya samu ya cire ta a ranshi yaci gaba da kallonta tamkar su Walida. Ya san babu aure tsakanin su shi yasa duk wannan abubuwan suke faruwa, har zuwa yanzu da ta auri wani bashi ba. Ganin wanda ta aura yasa hankalin shi ya kwanta, ko ba komai ya yaba da hankalin shi, ya san zai kula da ita, asirinta a rufe.
Baba nasiha ya masa sosai har ya zo ya faɗa sirrin zuciyarshi cewa dama shi baya son auren nan tun ba yanzu ba.
A lokacin ya ji gwara da bai aureta ya kawota in da nan gaba za'a mata gori ko jifanta da munanan kalamai da zai sata hawaye.

Aikin shi ya mai da hankali yake yi hankalinshi kwance, lokaci zuwa lokaci yana ƙiran Amma Jidda su gaisa yake sanar da ita ƙarshen wata yana hanya kafin bikin Walida.

***

MAIDUGURI.

A gajiye lis ya dawo gidanshi bayan aiki da su kasha fama da shi har da meeting da su ka gabatar bayan sallar azahar, bai samu zama ba sai karfe biyar ya dawo gidan. Wanka yayi ya fito, farin jallabiya kawai ya saka ya ɗauki wayarshi ya fito, har zai wuce zai sauƙa ƙasa, ya fasa ya nufi ɗakin Nuratu.
Tsaye yayi yana imagining ranar da zai buɗe ido ya ganta an kawo masa ita, bai san wani irin farin ciki zai shiga ba, ban da wanda yanxu yake ji idan ya tuna da aurenshi a kanta. Ya jima tsaye a ɗakin kafin ya sauƙa ƙasa. Takeway da ya siyo yaci ya hau sama ya ɗauki mukullin morarshi ya nufi gidan Ummi.

Babu kowa falon ya hau sama ya nufi falon ita ɗaya, tana kishingiɗe ya ƙarasa ya zauna ƙasa yana gaishe ta.

"Ya aiki Awwab, yau ko da safe baka shigo ba, wannan ƴar kan duk ta dame ni."

Murmushi yayi yana ɗaukan jug ɗin gefenta ya ga kunu ne a ciki na gyaɗa mai kyau, tsiyaya yayi a cup ya kurɓa kafin yace.

"Ummi aiki ya mini yawa. Tana ina?"

"Sun fita da su Hassana gidan Baba Abubakar."

"Hakan ya yi."

Shuru ne ya biyo baya yaci gaba da shan kunun, Ummi ne ta sako zancen da take son mishi.

"Awwab ya labarin tarewar Noor ne? Ba kuyi magana ba har yanzu?"

Shafa kwantaccen gashin kan shi yayi yana murmushi yace.
"Ba muyi ba Ummi, sai ƙarshen watan nan nake son zuwa muyi maganar. Kin san har yanzu bata da labarin auren."

Da mamaki Ummi tace.
"Me yasa ba'a sanar mata ba? Ko dai dole ka yiwa ƴar mutane Awwab."

Dariya Dr Awwab yayi, bai taɓa sanar da Ummi ko wani sirrin Nuratu ba kuma yana jin ba zai taɓa ba har abada.

"Babu komai Ummi, kar ya zama bata shirya yanzu ba ranta ya ɓaci ne. Amma InshaAllah zan sanar da ita sai daga baya muyi maganar tarewar."

"To Allah taimaka ya kaimu lokacin."

Ameen yace yana miƙewa jin an fara ƙiran sallar magriba dan fita, Hanan da ta shigo da gudunta tun a waje ta ga motar Daddyn ta ya sata shigowa da gudu tayi kan shi ya ɗagata sama yana cafkewa kafin ya riƙota.

"Kin fara nauyi My Love, gaba gaba zan dai na ɗaukar ki. Mai Aunties suka ba ki?"

"Ni dai bani da nauyi. Auntie babu abin da suka bani."
Hanan tace tana turo baki suka fita Ummi ta bisu da kallo tana mamakin soyayyar ƴa da uban.

A falon ƙasa ya ajiyeta saman kujera tana tsalle ya ɗauketa, goshinta ya sumbata yana cewa.
"Sallah zan yi in dawo, yau sai kin yi bacci zan tafi gida."

Jin haka ya saka Hanan barin shi ya wuce masallaci. Sai da yayi sallar isha'i ya dawo gidan, Hanan har ta hakura ta ɗauka ba zai dawo ba ta ganshi, da sauri ta je ta haye jikinshi ta kwanta tana kallon cartoon da aka sanya a MBC MAX na Frozen II. Wayar shi ya ɗauka ganin babu abin da zai yi ya buɗe Data ya hau WhatsApp da rabon shi da shi har ya mance.

Saƙonnin ne su kayi ta shigowa cikin wayar har suka gama ya dudduba ya gama tsaf, babu ko ɗaya na Nuratu hakan ya sa ya laliɓo numbern ta, gani yayi tana online ya tura mata saƙo.

*"Babyna nayi missing ɗinki, yaushe zan zo ganin ki?"*

...

Nuratu tana kwance saman kujera hankalinta rabi a waya rabi a Tv, hira suke a group ɗinsu na auren Walida da suka buɗe akan event da za su shirya, jifa jifa take saka musu baki dan ganin Ameera ta jajirce sai zuba rawan kai take da hakan haushi yake bawa Nuratu ta ga shigowar saƙon Dr Awwab. Fita tayi a group ɗin, da ma sun isheta ta buɗe saƙon shi ta gani.

Luf tayi kamar ruwa ya cinyeta, in zata tuna yau kusan sati ɗaya rabonsu da juna. A hankali ta miƙe ta wuce ɗakinta ta kwanta saman katifarta kafin ta fara ƙoƙarin bashi amsa.

*"Hanan nake son gani. Ita nayi missing."*

...

Dr Awwab ya cire rai da za ta bashi amsa ganin kusan mintuna biyar ya samu shigowar saƙon ta. Murmushi yayi ya tura mata amsa.

*"Ni kuma fa? Bakya missing ɗina."

Karanta saƙon Nuratu tayi ta rasa amsar da za ta bashi, kawai sai ta kashe data ta ajiye wayar. Tana shirin miƙewa ta shiga bathroom wayar ya ɗauki ƙara ta ɗauka. Dr Awwab ne ya ƙirata ganin ta sauƙa a online.
Kamar ba za ta ɗauka ba ta amsa tana kafawa a kunne ta masa shuru.

Yana jin ta ɗauka taƙi masa magana sai sauƙan numfashinta da yake ji, ajiyar zuciya ya sauƙe da ya daki dodon kunnen Nuratu ta ji tsikar jikinta ya tashi, da sauri ta zare wayar a kunnenta kafin ta mayar jin ya fara magana.

"Babyna ina son zuwa za muyi wani magana da ke. Please kar ki hana ni."

Ta san dai duk maganar ɗaya ne, bata san mai za ta faɗa musu su yarda da ita ba, su fahimceta babu aure a rayuwar ta.
Kamar ba za ta bashi amsa ba, har ya cire rai ko ya ɗauka bata ji shi ba, ko ƴan shan ƙamshin suna kusa ne yaji tace.

"Docter dan Allah in dai akan wannan maganar ne ni kam..."

"No Babyna wannan maganar yafi ko wanne muhimmanci. Please My Baby."

Mamaki take shi dai baya gajiya da zirga zirgan hanya, bayan haka ma ƙarfi da yaji ya raɗa mata wani wai Baby kamar wata yarinya, ko Hanan baya ƙira haka sai ita babba da ita. A zahiri ta sauƙe numfashi tace.

"Shikenan Allah kaimu. Yaushe za ka zo?"

"Nan da ƙarshen wata yayi."

"To sai ka zo."

"Thank you My Baby."

Kit ta kashe wayar tana ajiyewa ta yi baya ta kwanta, bathroom ɗin da bata shiga ba kenan, ta shiga tunanin me kuma Dr Awwab zai sanar da ita.

***

Ƙarfe taran dare Alhaji Mamman da Amma Jidda suna zaune ta kawo masa abinci yaci rabi yace.

"Zo ki kwashe Jidda na ƙoshi."

Abincin ta kalla ta ga kaɗan ya ci, ta dube shi gaba ɗaya ba'a nutse yake ba cikin kwana biyun, ga wani rama da ya fara tace.

"Haba Abban su Rahma, ka ɗaure ka ci ko kaɗan ne, dubi fa har wani rama kayi, ko dai abincin bai maka daɗi babe in tafasa make wani abu?"

"Ko ɗaya Jidda kawai dai bana jin daɗi ne. Ni na rasa me yake damuna a rayuwata, tun da Sadiya ta haifamin yarinyar nan babu alheri a rayuwana, kullum daga wannan sai wannan."

Amma Jidda da take jin maganganun shi har ya gama ta gyara zama tace.

"Abban su in faɗa maka wani magana? Ban san ya za ka ɗauka ba, amma maganar gaskiya babu wani abun a rayuwar Nuratu da zai shafi rayuwar ka. Ban san mai ka ke tunani ba ko hasashe ba, ka ɗauka laifi ka ɗaurawa yarinyar da bata ji bata gani ba.
Ka san ƙaddara? To wannan ƙaddara ne daga Allah dan ya jarabci imaninka. Maganar kuɗi kuma ko ƙarayar arzikin ka duk wannan ƙaddarar Allah ne. Ko bayan rabuwar ku da Mamin su Rahma kayi duba da babu wani abin da ya ƙara samun dukiyar ka sai yanzu. Yanzu kuma fa? Kai ka ɗaurawa kanka, ka karɓi tayin Alhaji Kashim ko duba da halin da ɗan sa ya saka Nuratu ba kayi ba, ka karɓi tayin shi. Baka san ta wani hanya ya samu kuɗin ba? Baka san halal ne ko haram ba? Ka ɗauka ka saka cikin dukiyar ka, gashi nan ya barka da asara. Ni na faɗa maka gaskiya in har magana na ya ɓata maka rai Allah baka hakuri."

Daga haka Amma Jidda ta miƙe ta ɗauki kwanukan abincin ta wuce kitchen, Alhaji Mamman ya bita da kallo cikin mutuwar jiki kalamanta suna ratsa ƙwaƙwalwarsa.
Baƙin tea ta haɗa ta kawo masa za ta wuce ɗakinta ya dakatar da ita.

"Maganar kayan abincin da za'a yi na ranar bikin Walida, baki ce komai ba lokaci yana ta matsowa."

"Duk abin da ka bayar yayi."
Amma Jidda tace, dama tana son masa magana, amma ganin halin da yake ciki ya sata ƙasa masa magana.

"Shikenan zuwa gobe zan ga me ya kamata ayi."

"Nagode Allah kaimu."

Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta. Alhaji Mamman ya jima zaune cikin falon ya saƙa wannan ya warware, komai ya kwaɓe masa. Ya ma rasa wani irin tunani zai yi.

***

Alhaji Kashim da Ummu suna Maiduguri asibitin Asylums center da aka riƙe Mufid, jikin Mufid kullum gaba yake, rashin shan sigari da wine ɗin ya girgiza shi sosai, ya saba ya bi jinin jikinshi da ba zai iya rayuwa babu shi ba.
Rashin shan komai shi yake ƙara birkita ƙwaƙwalwarsa kullum a rikice yake, ban da allurar bacci da magunguna babu abin da ake ɗura masa.

Ganin lafiya yaƙi samuwa Alhaji Kashim ya fara shirin fitar da shi ƙasar India dan ci gaba da duba lafiyar shi. Aunti Humaira ta zo da sauran yayun shi har Rufaida da Babynta tayi wayo. Hajiya Batula ma ta zo da ƴaƴanta.

***

Kwanaki sai tafiya suke har aka cinye sati biyu in da ya zamto daidai da ƙarshen watan Oktoba, ya kama saura kwana huɗu bikin Walida. Shiri sosai su Nuratu suke yi basa zama, anko kala uku su kayi, ɗaya kamu ɗaya bridal shower ɗaya ɗaurin aure, duk a gidan Aunti Hasiya za'a yi, dan Nuratu tace in har ba anan za'a yi ba, to baza taje gidansu ba, kafin su yarda sanin tsakaninta da Abban su.

Yau tun safiyar ranar laraba su kaje wanke kai, har yamma lis kafin su dawo gidan Aunti Hasiya gaba ɗaya su. Ameera da aka fara gama mata ta riga su zuwa gidan, sai Nuratu da Walida a ƙarshe suka taho cikin motar Mami da Nuratu ta ɗauka dan zirga zirganta, da kyar Mami ta bata har da kukanta kafin bata bayan gargaɗi da tasha.

A waje tayi parking dan tana son komawa gida dan ɗaukan wasu kayanta da ta mance a gida. Bayan tayi parking suka fito suka nufi cikin gidan, a harabar gidan taga motar da bata tsammaci gani yanzu ba.

"Yaya Al-ameen! Ko yaushe ya zo?"
Walida tace ita ma cike da mamaki dan ta gane mai motar.

Nuratu baya taja ta tsaya dan bata shirya ganin shi yanzu ba, yanzu zai tsayarta da maganganun shi, ta dubi Walida.

"Walida zan je gida in dawo, zan ɗauko kayana da na faɗa miki."

Hararanta Walida tayi tai murmushi.
"Bakya son dai ganin Yayana."

"Wallahi ba haka bane, zan je in dawo, kar ma kice tare muke, kice na wuce daga can dan Allah."

"To ki gaishe da Mami."

To Nuratu tace ta fita da sauri tana barin gidan Walida ta shiga ciki. Nuratu har cikin gida ta shigar da motar dan ba zata koma ba sai gobe.

"Ya haka kuma ke da sai wani sati."
Mami ta tambayi Nuratu da mamakin ganinta wannan lokaci.

Nuratu da ke kwance saman doguwar kujera tace.
"Ni nayi kewar ki ne na dawo, sai gobe zan koma da safe muyi lalle, da yamma ne event ɗin."

"Ke ki ka sani. Ahmad yana hanya gobe."

Sai lokacin Nuratu ta kai kallonta kan Mami tace.
"Docter ma yace yana zuwa ƙarshen wata, amma ban san yaushe bane, dan bamu ƙara magana da shi ba."

"To Allah kawo su lafiya."

Mami tace ta miƙe dan kar Nuratu ta sako mata wani zancen.
Duk waya da Walida da Rukayya suka mata ƙin ɗauka tayi, ƙarshe ta tura musu saƙon cewa kanta yana ciwo sai gobe za ta dawo.

Washegarin.

...

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE 39.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Da safe ƙarfe takwas Nuratu ta wuce gidan lalle acan suka haɗu da Walida da Rukayya da Ameera. Ameera aka fara yiwa sai Walida da ta ja lokaci sosai dan lallen amarya, kafin Nuratu. An gama mata kenan wajen karfe biyu wayarta yayi kara, Rukayya ce ta ɗauka mata ta ga Col Ahmad ne.

"Saka min a handfree Sister."

Babu musu Rukayya ta saka mata da d'ayan hannunta marar lalle, an fara mata kenan, ta ɗaurawa Nuratu wayar saman cinyarta. Bayan tayi sallama ya amsa ya sako mata tambaya.

"Na iso bakya nan in ji Mami kin tafi lalle. Ashe biki sister ku ke babu gayyata."

A hankali tace.

"Dan Allah kayi hakuri wallahi na ɗauka na sanar da kai, abin ne yazo a ƙurarren lokaci."

"Shikenan ina jiranki, za ki biyo gida in kin bar gidan lallen?"
Ya tambayeta.

"Eh zan zo."

Da to ya amsa da shi kafin ya kashe, ko ba komai za ta biya su gaisa, mutum musamman dan ita ya taso daga wani garin ya zo. Mintuna biyu da ajiyar wani ƙiran ya shigo ta kai dubanta ta ga Dr Awwab ne, ta kalli Rukayya.

"Yi hakuri sister ki ɗauka min."

Babu musu Rukayya ta amsa ta saka a handfree tare da ɗaura mata saman cinyarta.

Dr Awwab da tun ɗazu ya ƙira ya ji line busy tana waya ya kasa samun nutsuwa, haka yaci gaba da ƙira, abin da bai taɓa mata ba, dan wani mugun kishi ne ya kama shi, burin shi ɗaya ba da wani take wayan ba. Jin ta ɗauka ya watsa mata tambaya.

"Babyna da waye kike waya haka?"

Jin sunan da ya ƙirata da shi kamar ta nutse ƙasa, ido ta ɗago gaba ɗaya sun zuba mata shi. Walida na gumtse dariyarta, hakan yasa ta haɗa rai ta juyar kanta tana bashi amsa.

"Da Col. Ahmad ne."

Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan ya ji mai tace, yace.
"Ina da kishi sosai Babyna."

Shiru Nuratu tayi tana hararan Walida da ke dariya kasa ƙasa bata ce komai ba. Jin haka shima Dr Awwab yace.
"Na shigo gari shine na ƙira in sanar miki ina tafe nan da some minutes."

"Yau ɗin?"
Nuratu ta tambayeshi da sauri.

"Yes mana Babyna, na sanar miki ina hanya ai ƙarshen wata. Ko har kin manta?"

"To sai ka iso. Amma ina gidan lalle yanzu."
Nuratu tace ta ma rasa mai za tace tunawa da Col. Ahmad yana gidan.

"Lalle ki ke mini Babyna?"

"Biki muke yi na sister na."
Tace da sauri jin sai baro zance yake.

Murmushi yayi yace.
"Bari in biyo in ɗauke ki, ki turomin address."

"A'a akwai motar Mami a hannuna."

"Shikenan bari in ƙarasa mu gaisa da Mami kafin ki iso. Take care My Baby."

To tace da sauri ta kashe wayar da gwuiwar hannunta tana hararan Walida da ta kwashe da dariya.

"Su Baby manya. Anya ba da Dr Awwab za muje ba, kun ji yadda take kashe masa murya tana sha masa ƙamshi, duk ta rikita bawan Allah."

Harara Nuratu ta watsa mata.

"Sharri zaki mini Walida, ni ba wani kashe masa murya da nake balle shan ƙamshi. Duk cikin su babu wanda nake so, kallon mutunci nake musu."

Nuratu tace tana tashi tsaye.

Rukayya da sai lokacin ta saka baki dan tasan komai tace.
"To waye Baby? Muna ji ya ƙira ki da Baby kika amsa. In ba so mai ya kawo haka."

Jin maganar Rukayya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login