Follow us on social media
Showing 42001 words to 45000 words out of 148866 words
Chapter 15 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
da kyar ta samu ta sha magani ta zube a gurin ta hau bacci.
***
Ibadan.
Satin Col. Ahmad ɗaya ya ƙara ɗaukar hutu ya taho Maiduguri, gida ya fara biyawa dan a ranar Baban shi ya dawo, jiki yayi sauƙi sosai. Yayi murnan ganin ya warke tamkar ba shi ba, bayan sun gaisa da kowa ya ɗauki hanyar Damaturu.
Kai tsaye Police station ya nufa, yaci sa'a ya samu DPO Salisu akan aiki. Yayi mamakin ganin shi tsammanin shi duk ya bar case ɗin har abun ya fara damun DPO Salisu yake cewa zai ƙira shi ya ji sai kuma ya fasa.
Bayan sun gaisa da Col. Ahmad yace.
"Sai kaji shuru kuma. Uzuri ne ya taso min, sannan ita yarinyar sai kwanan nan ta samu lafiya. Fatan har yanzu maganarmu tana nan."
"Yana nan mai zai hana, shin ka shirya da shigar da ƙara?"
DPO Salisu ya tambayi Col. Ahmad.
"Shirye nake tsaf da gwagwarmaya da kowa."
Col. Ahmad ya bashi amsa dan a shirye yake tsaf.
DPO Salisu tashi yayi daga saman kujeransa ya ƙira ɗan sanda biyu, ɗaya mai rubuta jawabi ɗaya shi za'a bawa sakon.
"Rubuta takardar tuhuma zuwa koto ana ƙarar Mufid Kashim Mufid da abokansa, sun yiwa yarinya ɗaya fyaɗe a ranar ashirin ga watan Satumba."
Bayan ya rubuta ya linƙe ya miƙawa ɗaya ɗan sanda da zai kai koto DPO Salisu yace ya kai shari'a court, babu musu ɗan sandan ya fita da saurin shi.
DPO Salisu ya juya ya dubi Col. Ahmad.
"InshaAllah ina sa ran zuwa jibi za su neme mu, zan sanar da kai da zaran an neme mu, za su tura takardar tuhuma zuwa gidan su Mufid, sannan iyayen yarinyar ya kamata su sani dan su nemi lauya da zai tsaya musu."
"Nagode DPO, sai dai maganar lauya, na fi son da zan samu ta waje na, domin komai in zai faru kar iyayen yarinya su sani, sai ranar shiga koto kaɗai zan sanar dasu."
Shuru DPO Salisu yayi ya rasa Col. Ahmad wani irin mutum ne, sune dai irin mutane masu yin abu dan Allah ba dan idon mutane ba.
"Akwai lauya dana sani sunanshi Affan lauyan gwamnati ne, yana aiki a high court ya san kan aikin shi, zan baka number nashi ka ƙira shi nima zan ƙira in sanar dashi ni na turo ka."
"Nagode da taimakon da ka ke mini, Allah biya ka da alherin shi."
Col. Ahmad yace yana miƙa masa wayar shi.
"Kai za'a ma godiya ganin ka jajirce an kwatarwa yarinyar nan haƙƙinta, abinda yayi ƙaranci kenan a zamanin yanzu."
Anan su ka yi sallama bayan ya bashi numbern Lauya Affan. Bai ƙira ba sai da ya isa gida ya huta yaci abinci ya fito filin gidan nasu zuwa wajen da suke shan iska.
"Assalamu alaikum Malam Affan ne?"
Col. Ahmad yace bayan Barrister Affan ya ɗauka.
"Walaikum Salam, tabbas ni ne, an wuni ƙalau."
Barrister Affan ya amsa daga ɓangaren shi.
"Ko kunyi magana da DPO Salisu da ke garin Damaturu, shi ya bani numbern ka."
"Mun yi magana dashi yanzu bai jima ba. Ya sanar dani ƙiranka da wasu abubuwa kaɗan."
"Hakane, ina son haɗuwa da kai dan Allah in zai yiwu, saboda bamu da lokaci, abin da ya faru ya jima yanzu kuma ya zo a ƙurarren lokaci."
"Zuwa yaushe kenan?"
"Gobe dan Allah."
Da sauri Col. Ahmad yace.
"Allah kai mu, zan turo maka address ɗin in da zamu haɗu."
"Ameen Nagode sosai."
Bayan sunyi sallama Barrister Affan ya turowa Col. Ahmad address ɗin gurin da zasu haɗu.
....
Washegarin ranar Alhamis ƙarfe goma ta samu Col. Ahmad a cikin garin Damaturu, kai tsaye in da su kayi zasu haɗu da Barrister Affan ya nufa. Gurine na zama, kewaye yake sai rumfa rumfa da kujeru a zagaye gurin ba hayaniya sosai. Bayan sun gaisa suka gabatarwa da juna kai kafin Col. Ahmad ya yiwa Barrister Affan bayani abinda ke tafe dashi.
"It's rape case?"
Barrister Affan yace bayan gama sauraron bayanin Col. Ahmad.
"Yes and ina son kwatar mata haƙƙinta ko dan masu hali irin na shi, sannan in nuna uban yaron nan kuɗi ba komai yake magani ba."
Barrister Affan na sosa saman kanshi yace.
"Hakan ma yayi, ina son ganin yarinyar da duk wanda tayi mu'amala dasu kafin da bayan abin ya faru."
"Bana son su sani Barrister."
"Saboda? Haƙƙinta ne fa, ta ya za kace baka so, in ma tsoro ka ke ji suce ba zasu iya shari'a da masu kuɗi ba kar ka damu na san yadda zan ɓullo mata."
"Shikenan mu je gidansu."
Babu musu Barrister Affan ya miƙe suka fita a gurin. Basu da lokaci dan haka basu ga ta zama ba.
***
Mai gadin sai Knocking kofar falon ya ke babu wanda ya buɗe har ya juya riƙe da farin takardar da ɗan sanda ya kawo a bawa Alhaji Kashim. Yana zama aka danna horn ya tashi ya buɗe. Alhaji ne da kanshi. Bayan ya rufe get ɗin har zai zauna ya ɗauki farin takardan ya bi bayan Alhaji dashi.
"Alhaji! Alhaji!"
Yace da karfi Alhaji Kashim ya tsaya yana duban shi har ya ƙaraso ya miƙa masa farin takardan.
"Saƙo ne aka bani in baka."
Hannu yasa ya karɓa yana wucewa ciki. A falon shi ya tsaya ya samu Hajiya Hindatu tana jiran isowar shi. Ciki ya shiga ya watsa ruwa ya fito cikin jallabiya ta kawo masa abinci, yana cikin ci ya tuna saƙon da aka bashi.
"Miƙo min wancan papern Hindatu."
Hannu tasa ta ɗauka ta miƙa mishi bayan ta warware ya karɓa ya hau dubawa. Takardar tuhuma ce na Mufid da abokansa bisa fyaɗe da suka yiwa wata yarinya watanni uku da suka wuce, ana neman su ranar Litinin a koto dan amsa laifin su in basu yarda kuma ba ayi shari'a da su.
Dariya ya kwashe da shi bayan ya gama karantawa.
"Wato wannan yaron har yanzu bai hakura ba ko?"
"Wani yaro kuma?"
Cewar Ummu dan bata gane inda zancen ya dosa ba.
"Case ɗin nan ya ɗago na Mufid, ana nemansu a koto ranar Litinin dan yin shari'a, ni zai yi wa haka, to mu zuba ni da shi zan bashi mamaki."
Ummu da ta gane inda bakin zaren yake tayi ta surfa ruwan bala'i.
"Kar ki damu Hindatu, zan samu Barrister Auwal muyi magana. Ina shi Mufid ɗin?"
"Ya fita."
"In ya dawo ina neman shi."
To ta amsa dashi tana sauƙe huci ranta ɓace an sawa tilon ɗanta namiji ido.
***
"Nuratu ki buɗe baki ki sanar da shi abinda kika sani."
Col. Ahmad yace yana roƙar Nuratu da take kuka sosai. Bayan zuwansu gidan da kyar suka shawo kan Mami ta yarda da batun shiga koto. Nuratu da ta ji hakan kuka ta fara da ta rasa na farin cikin za'a kwata mata ƴancinta ne ko na tuna abinda ya shuɗe.
A hankali Nuratu ta sanar da Barrister Affan farkon haɗuwarsu da Mufid da irin kalaman da yake mata har zuwa ƙofar gidansu da yake yi da kuma ranar ƙarshe da ya ɗauketa. Anan ta dakata ta kasa ci-gaba da maganar ta fashe da kukan da yake taɓa zuciyarta da su masu sauraron ta.
"Daga nan sai suka afka miki ta ƙarfi ko da son ranki."
Barrister Affan ya tambaye ta ganin ta tsagaita kukanta.
Kallon Barrister ta yi da jajayen idanuwanta.
"Ƙarfi suka nuna min, Mufid kaɗai na san ya fara amfani dani daga nan ban ƙara sanin komai ba sai tsintar kai na nayi tamkar mahaukaciya marar amfani."
"Fatan duk abinda kika faɗa zaki iya maimaita shi a gaban alkali domin a kwatar miki haƙƙin ki a hukuntasu dai-dai da laifin da suka aikata."
Tambayar farko ta ji ya bata haushi amma faɗar haka ya bata kwarin gwiwa ta ɗaga kanta.
"Zan yi, zan faɗa komai."
Tace tana share hawayenta.
"To mun gode Malama Nuratu."
Barrister Affan yace yana rubuce rubuce, duk tambayar da ya mata dan ya tunzura zuciyarta ne ta ji haushi ta cire tsoro ta faɗi gaskiya kuma hakan yayi aiki.
"Ki zauna cikin shiri Nuratu za'a neme ki cikin satin nan. In akwai wani abin da ku ke buƙata ki sanar da ni."
Kai ta ɗagawa Col. Ahmad, kunyarshi ya kamata da ta kasa fahimtar shi a baya take mishi ganin mai laifi.
***
Bayan Barrister Auwal ya gama karanta abinda ke rubuce a papern ya kalli Alhaji Kashim.
"Wato Alhaji lokaci ya ƙure mana. Amma shawara ɗaya zan baka ka yi gaggawar fitar da Mufid a ƙasar nan ko kuma ka gargadesu kar su amsa laifinsu. Domin da zaran ya amsa komai zai kwaɓe mana. In kuma bai amsa ba zan san yadda zan ɓullowa lamarin."
"Barrister ka na ganin hakan mai yiwa ne?"
"Sosai ma, ka yarda dani kawai."
Cewar Barrister Auwal yana nuna kanshi.
"Shikenan Barrister na yarda da kai. Zan gargadi Mufid, domin maganar fitar shi a gari lokaci ya ƙure."
"Hakan za'a yi."
Faɗin Barrister ya tashi ya mishi sallama ya fita.
****
Barrister Affan da Col. Ahmad ba su zauna ba sai da suka karɓi dukkan information a gurin Dr Sadiq na abinda ya shafi Nuratu. Suka sanar da shi ya kamata ya halarci zaman koto dan bada shaida kuma ya amince domin yayi alƙawarin hakan a baya.
"Ya za'ayi mu samu sauran bayanai bayan barinta asibitin nan."
Barrister Affan ya tambaya.
Dr Sadiq yace.
"Sauran kuma suna Maiduguri asibitin da muka tura su."
Col. Ahmad yace yana duban Barrister Affan.
"Kar ka samu damuwa Barrister, zuwa gobe zan sanar da Dr Awwab."
"Shima ya kamata ya halarci zaman koto."
Faɗin Barrister Affan.
"Za muyi magana da shi."
Col. Ahmad yace suka ma Dr Sadiq godiya suka fita.
A hanya suka rabu Barrister Affan ya wuce gidanshi, Col. Ahmad ya kama hanyar Maiduguri lokacin ƙarfe biyar na yamma.
Washegarin juma'a ya samu Dr Awwab da maganar.
"Insha Allah za ku ganni."
Dr Awwab yace bayan ya bashi duk abin da ya shafi Nuratu. Godiya Col. Ahmad yayi kafin ya mishi sallama ya fita.
Baya yayi ya jingina da kujeran da yake kai ya lumshe idanuwanshi.
Yayii kewarta sosai, tunaninta ya hanashi hutu cikin sati biyun, hotonta yake gani cikin zuciyarsa, Allah Allah yake ƙarshen wata yayi ya kai mata magungunanta ya samu abinda zai fake da shi yaje kallonta ko zuciyarshi za ta samu ta barshi yayi sukuni. Shaƙuwa su ka yi ba sonta yake ba cewar shi.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 23.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Wallahi ka ji na rantse kar ka yarda ka amsa laifinka bisa ƙarar ka da ake yi. Idan ka amsa ka san dai babu abinda zai hana a hukunta ku, sannan ka sanar da su Faisal suma haka. Ka ji mai na faɗa maka."
"Na ji Daddy. Baby Noor ta dawo ne?"
Kallon Mufid Alhaji Kashim yayi yana mishi wani faɗa daban shi kuma yana tambayarshi wani abun daban.
"Ban sani ba. Tashi ka bani guri."
Yace rai a ɓace.
'Anya zai aikata abinda suka nema a gurin shi.'
Zuciyar Daddy ya tambayi shi bayan tashin Mufid a gurin.
Mufid fitarshi bai tsaya ko ina ba sai wajen shashancin su da su AA da Faisal.
"Guys Baby Noor ta dawo."
Faɗin Mufid yana ɗaukar kwalbar wine ya a zuba cup bayan ya zauna.
AA da Faisal suka zaro ido kamar zai faɗo jin maganar shi.
"Kana nufin waccan yarinyar da dalilinta muka kwana a cell."
AA ya tambaya cike da tsoro.
"Yes ita mana."
Mufid yace yana kafa cup ɗin a baki ya shanye tas kafin ya kallesu yana faɗa musu abinda Daddyn shi yace, duk sun yarda da hakan.
Mufid ya miƙe yana cewa.
"Mu je ku rakani gidansu."
"Waye ni? Ba inda zan je."
AA yace da sauri. Faisal ma ya girgiza kai alamar a'a haka yasa ya fita.
Kai tsaye gidansu Nuratu ya nufa rabon shi da zuwa tun watannin baya da ya yi ta zuwa a kulle. Kofar gidan a buɗe kai tsaye ya nufi cikin gidan yana ƙare masa kallo.
Munirat da ta fito daga kitchen ta bishi da kallo, ta so gane fuskarshi tace.
"Bawan Allah lafiya?"
"Baby Noor tana nan? Ƙiramin ita Please."
Sai yanzu ta gane fuskarshi ta haɗa rai.
"Bata nan."
Wani kallo ya watsa mata ya nufi falon gidan ta bishi da sauri, kafin ta ƙarasa ya jawo ƙofar ya kulle da ƙarfi, ta tsora ta tsaya tana bugun ƙofar ya buɗe.
"Baby Noor! Baby Noor."
Mufid yake faɗa yana buɗe buɗen ƙofofin da suke cikin falon, ɗakuna biyu ne, ya buɗe na farko ba ta ciki ya buɗe d'ayan ya hangota kwance tana bacci hankali kwance. Kamar wani mahaukaci ya ƙarasa da sauri bakin katifar da take kwance ya durƙusa ya zuba mata idanu.
A cewar shi sonta yake domin yadda zuciyarshi yake fisgar gangar jikinshi zuwa gareta.
"Baby Noor i missed you."
Yace hannunshi saman fuskarta yana zagayawa, ƙaramin bakinta ya zubawa ido.
Cikin bacci Nuratu ta ji ana taɓa mata fuska, turare da wani irin hayaki mai wari na shiga hancinta. Idanuwanta cike da bacci ta buɗe, dishi dishi take ganin mutum zaune kusa da ita har ta buɗe tas saman fuskar da ko mafarki take ba zata mance ba.
"Babyna kin farka?"
Ta ji muryar Mufid.
Wani razanannen ihu Nuratu ta sakar mishi tana ja baya, hannu ya kai zai taɓa ta ta sake fasa wani ihun iya ƙarfinta.
"Kar ka taɓa ni. Mami ki zo ki taimaka mini zan kasheni."
"Oh Baby, tsorona kike je. Ki bari ko gaisawa muyi mana sannan muyi maganar da ya kawo ni."
"Ka fita dan Allah Mufid, ka fita. Ko ka dawo ne ka ƙarasa ni ka ƙarasa sauran rayuwata."
Nuratu tace tana fashewa da kuka tana kama jikinta da duk rawa yake.
Bai damu da kukan da take ba ya ƙara matsawa kusa da ita ta ja baya, ya dakata yace.
"Ko ɗaya Baby Noor, kin san nasha faɗa miki ina son ki ko? To har yanzu ina son ki. Dan Allah ki bani dama in aureki please."
"Da na aure ka gwara na mutu ba aure. Ka fice mana a gida."
Tace cikin kuka jikinta mugun rawa yake take ta ji kanta ya fara juyawa.
"Please na ce miki dan Allah. Kin san mai yake tafe da ni, zan amsa laifina a kotu a mini hukunci in har hakan zai saka ki aure ni."
Girgiza kai tayi ta miƙe cikin sauri za ta fita ya saka hannu ya fizgota jikinshi. Nuratu abubuwan da suka wuce suka dawo mata, kamar lokacin ne ya jawota jikinshi a wancan daren. Ihu ta fasa mishi tare da kai masa cizo a dantsen hannunshi ya saketa da sauri.
Waje tayi ta taɓa kofar a kulle ta fara ƙoƙarin buɗewa ta ga ya fito. Wani ihun tayi da ya ƙara rikita Munirat dake waje tana ihu a kawo mata agaji.
Tana ganin ya nufota ta juya tana bugan ƙofar a buɗe mata. Mufid gurin ya iso ta bayanta ya saka hannu ya cire lock tana ganin haka ta fita da gudu suka haɗu da Munirat, ta faɗa jikinta.
Bai ko kula da Munirat da take surfa masa tsinuwa ba ya sa kai ya fice. Babyn shi Noor ya zo gani kuma ya ganta ya sanar da ita zai amsa laifinshi in har za ta aure shi.
Bayan fitar shi Munirat ta ɗago Nuratu dake jikinta babu numfashinta ya ɗan dakata. A mugun tsorace ta jata zuwa falo ta kwantarta tare da ɗauko ruwa ta dinga shafa mata tare da ɗiga mata a baki sai kuka take. A cikin wannan halin Mami ta dawo daga gidan Aunti Zarah da ta je dubata bata da lafiya. Ta tsorata ganin halin ƴartan tana tambayar Munirat mai ya faru ta sanar da ita abin da ta sani.
Shine! Faɗin Mami ranta a ɓace tana mamakin tsaurin ido irin na Mufid, ji tayi da tana nan ya zo babu abinda zai hanata ɗaukar hukunci a hannunta.
Da ihu Nuratu ta farka tana ƙiran Mami ta zo Mufid zai kashe ta, riƙo ta Mami tayi da kyar suka samu hankalinta ya dawo suka ɗura mata magani ta kwanta bacci ya kwashe ta.
Mami hawaye ta dinga sharewa ta zuba mata ido, shikenan Mufid bayan cuta da ya ma ƴarta ya haukata mata yarinya. Daren Nuratu ta din ga firgita haka ta hana su bacci.
***
Allah ya yi dare gari ya waye yau Allah ya kaimu wayewar garin ranar Litinin.
Misalin ƙarfe goma na safiya (10:00am).
Kotu ta cika makil ana jiran zuwan alkali, idan ka duba hagu ahlin gidan Alhaji Kashim Mufid ne da matarsa Hajiya Hindatu da shi kansa Mufid da Rufaida da Aunti Humaira da suka samu labari suka zo, gefensu AA ne da Faisal gaba ɗaya ido ya raina fata.
Gefe ɗaya kuma Mami da ƴaƴanta gaba daya har da Muhsin da ya samu labari ya zo. Amma Jidda, Aunti Zarah duk sun zo, abin mamaki har da Alhaji Mamman Bashir da Alhaji Tukur. Nuratu na kusa da Mami kanta a ƙasa tun haɗa ido da su kayi da Dr Awwab ta watsa mishi harara bata ƙara ɗago idanuwanta ba.
Yaya Al-ameen, Dr. Sadiq, Col. Ahmad da Dr Awwab na zaune a kusa da juna kowa da abinda yake saƙawa a rai.
Dr Awwab suna haɗa ido da Nuratu da ta watsa mishi harara ya jefeta da murmushin da bai san yaushe ya iya shi ba yana mamakin rigimar ta.
Shigowar Alkali ya saka kowa nutsuwa aka ce Court! aka miƙe, Alkali ya shigo ya zauna kafin aka zauna.
Alƙali ya gyara zamanshi yace.
"Rejista yau me muke da shi?"
Rejista yayi gyaran murya yace.
"Ya mai girma mai shari'a yau muna da case number YB/CV/UPC/20/2018 tsakanin Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru da Nuratu Mamman Bashir."
"Wanda ya kawo ƙara yana kotu?"
Rejista yace.
"Eh ya mai girma mai shari'a."
"Wanda ake ƙara yana nan?"
Alƙali ya tambaya.
"Eh ya mai girma mai shari'a."
Faɗin rejista.
"Ko zai iya fitowa gaban kotu."
Miƙewa rejista yayi.
"Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru ko za ku iya fitowa."
Babu musu suka miƙe jikin AA rawa ya fara aka nuna musu cikin Doc suka shiga suka tsaya.
Alƙali ya dubesu yana gyara zaman gilashin idonshi.
"Wakilci."
Faɗin alƙali.
Barrister Affan ya miƙe.
"Sunana Barrister Affan Zubair ni ne lauyan mai ƙara."
"Ni sunana Barrister Auwal Sanusi ni ne lauyan mai ƙare wanda ake ƙara."
Faɗin Barrister Auwal bayan Barrister Affan ya gabatar da kan shi ya zauna.
Investigator Lawan ya mike ɗauke da content a hannunshi ya fara karantawa.
"Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru a rana na ashirin ga watan Satumba sun aikata laifin fyaɗe a wani gida dake red bricks, misalin karfe takwas na dare, sun danne yarinya mai suna Nuratu Mamman Bashir sun sadu da ita. Kun aikata wannan laifin?"
Kafin Mufid ya yi magana AA da Faisal suka ce. A'a!
Barrister Affan da sauri ya miƙe.
"Ya mai girma mai shari'a, mun kama waɗannan yara uku sun yi wa yarinyar nan fyaɗe kamar yadda investigator ya faɗa. Mun na da shaidu da shaidar tuhumar su hakan, a bamu dama."
Ganin dama ta samu abinda suke nema su Mufid kar su amsa laifi ya saka Barrister Auwal tashi da sauri.
"Ya mai girma