Follow us on social media

Showing 120001 words to 123000 words out of 148866 words

Chapter 41 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

20

wayarsa a aljihu. Danne danne ya yi ya kafa a kunne.

"Kun gama?"
Shine abun da ya faɗa.

Can na gefen bansan me yace ba naga Dr Awwab ya dafe kansa. Kamar ba zai ce komai can yace.
"Shikenan, ka ƙara dagewa don Allah."

Daga haka ya kashe wayar jin motsin taɓa ƙofar bathroom. Kallonsa ya kai gurin, daga ita sai towel daidai gwuiwarta, duk ba ta ankara da zamansa ba, tana goge fuskarta da ƙaramin towel. Har tsakiyar ɗakin ta tako ta tsaya a gaban madubi, towel din da ta ajiye shi ya ba ta damar hangosa ta cikin madubi. Ihu ta sakar ba shiri tana neman abin rufe jikinta. Har ga Allah ta tsorata dan bata tsammaci ganinsa ba.
Babu komai kusa da ita sai ƙaramin towel, shi ta ɗauka ta kare kirjinta da sauri. Baki ya taɓe yana miƙewa ya nufeta, ai sai ta ƙara tsorata. Tana gani ya iso gareta ta runtse idanuwanta. Rumfa ya mata yana rankwafowa saman kanta ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta. Da sauri ta buɗe idonta su ka shiga cikin nasa.

"Wai don Allah kunyata ki ke ji?"
Ya faɗa yana ɗaga mata gira ɗaya.

Kai ta ɗaga sai kuma ta girgiza dan yanzu sai ya mata abin da zai ƙara sakata wani kunyar. Murmushin gefen ba ki yayi ya matsa baya.

"Ki gama shiryawa."

Sanin tana buƙatar kimtsa jikinta ya faɗi haka yana fita. Ajiyar zuciya ta sauƙe ta nufi ƙofar ta sawa key, kafin ta gyara jikinta ta shirya tayi shafe shafenta ta fita. A dinning ta samesa yana waya, yana ganinta ya sanar da wanda suke wayar za su yi magana anjima.
Ba ta zauna ba ta hau zuba musu abincin, sai da tagama kafin ta zauna. Ɗago ido tayi ta kallesa ganin ya kafeta da idanu. Murmushi tayi ta ɗauke idonta.

"Allah ya miki albarka Noor."

"Ameen Ya Allah."

Tace tana murmusawa don ta ji daɗin addu'ar. Hannu ta kai za ta ɗauki spoon ya ɗauke, dubansa tayi ya ɗaga mata gira.

"Bari in ciyarki, nasan kin gaji."

"Zan yi da kaina fa."

"No, buɗe bakin kawai."

Yace ya ɗebo abincin ya kai bakinta, dole ta buɗe ya samata, daga nan ya ci gaba da bata har ta ƙoshi kafin ya hau ci. A nutse suka gama abunsu yana mata hira dangane da service ɗinta.
Bayan sun gama ta tattare wajen ta kai kitchen ta hau wankewa. Shi kuma ya zauna falo yana danna wayarsa.
Ta gama wanke wanken ganin sha biyu saura ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana. Ƙwanƙwasa ƙofar kitchen ɗin ya yi yana tsayawa. Barin wanke kayan miyar da take ta yi ta juya.

"Kana buƙatar wani abu?"

Kai ya girgiza mata.
"Kiyi dayawa akwai baƙi masu zuwa."

To tace ta bi bayansa ganin ya fita, bai san tana binsa ba har ƙofar falon ya buɗe ta riƙe ganin zai kulle. Da mamaki ya juya sai ta sunkuyar kanta ƙasa. Matsawa yayi ya jata jikinsa yana zagaye hannunsa a bayanta, hakan ya bata damar ɗaura hannunta saman kirjinsa.
Sumbatar saman hancinta ya yi, ganin yana shirin yin ƙasa da bakinsa ya sata kifa kanta a kirjinsa.

"Yau kuma rowa ki ke mini?"

Kai ta girgiza masa ta kasa ɗagowa. Rumgumeta yayi gaba ɗayanta, sonta da ƙaunarta na shigarsa.

"Zan je gidan Ummi na dawo, me zan kawo miki."

"Babu komai, ka gaisheta."

"Za ta ji. Koma kiyi aikinki na hutarki rakiyar."

Ya faɗa yana sakinta, sai da ya ga ta shiga kitchen ya fita. Gidan Ummi yaje ya gaisheta daga nan ya fita dan abin da ya fito da shi.
Sai azahar ya dawo gidan don zuwan baƙinsu. A harabar gidan ya samesu suna jiransa, musabaha su kayi kafin ya musu jagora zuwa ciki. Shi ya fara shiga dan tabbatarwa ba ta falon kafin ya ba su izinin shiga ciki.
Babu kowa falon, bayan ya ba su izinin shiga, ya wuce sama dan ƙiran matar gidan su gaisa. Kwance ya sameta barci ya fara fisgarta, gefenta ya zauna yana shafa bayanta da tayi rubda ciki.

Idanuwanta ta buɗe tana gyara kwanciyarta.
"Sannu da dawowa."

"Yauwa ya gajiya. Tare muke da baƙi, ki canza kaya ki fito ku gaisa."

Kai ta ɗaga masa daga haka ya fita, ta shi ta yi ta canza kayanta zuwa doguwar rigar atamfa ta yafa mayafi ganin dagasken mijinta na kishinta. Tana gamawa ta fita, ba ta jin hirarsu sosai har sai da ta shigo falon sosai ta tsinkayi muryar mutane biyun da su ke da mutuƙar mutunci a gareta.

"Col! Yaya Al-ameen!!"

Ta faɗa da ɗan ƙarfi tana ƙarasawa wajensu, murmushin su ke suka amsa mata. Rasa inda zata sa ranta tayi dan murna ta hau gaishesu, har da guntun hawayenta.

"To me na kukan kuma? Duk shagwaɓa ce?"
Col. Ahmad yace yana murmushi. Murmushi ta yi tana share hawayenta ta girgiza kai, juyawa gurin Yaya Al-ameen ta yi.

"Yaya yaushe ka zo? Ina su Amma? Ya aiki?"

"Lafiya lau ƙanwata, ya amarci."

Kunya ta ji ta rufe fuskarta ta miƙe. Cikin sauri ta haɗa musu fruit salad da juice din kwakwa da abarba ta jefa kankara, bata da matsalar abinci dan ta haɗa kala biyu da gashashshiyar kaza, bayan ya sanar da ita akwai baƙi. Tsaf ta jera komai saman dinning ta gama ta koma gurinsu.

"Abinci fa an kammala."

"Ayi haka kuma Nuratu, a matsayina na Baba in zo gidan ƴata inci abinci."
Col. Ahmad ya faɗa cikin zolaya.

"Kai Yaya Ahmad, don Allah fa. Doctor ka masa magana."

Dr Awwab da ya ke jin duk shari'arsu ya yi murmushi ya miƙe.
"Ni na isa shiga faɗar Baba da ƴa. Al'ameen zo muje mu cika cikinmu."

Yaya Al'ameen da ya miƙe tuni yariga Dr Awwab isa table din dan dama a yunwace yake. Ganin haka Col Ahmad ya miƙe.

"Wasa nake miki."

Daga haka shima ya isa wajensu, zama tayi a falon ta juya musu baya. Yaya Al'ameen shi ya yi serving ɗinsu, kowa sheƙe da plate, ga kofuna cike da juice ga bowl plate da fruit salad. A nutse su kaci sai da suka taɓa ko wanne suna santi. Bayan sun gama su ka koma falon su ka hau hira, ita kuma ta tattare gurin. Kwata kwata Dr Awwab ya manta da batun ɗauko Hanan har ƙarfe uku.
Masallacin su ka je tare suka dawo, idan ka gansu ba za ka taɓa cewa sunyi tarayya wajen son abu guda ba. Sai dai abin mamaki ga su waje guda.
Shigowarsu gidan Nuratu ta sanar da shi maganar ɗauko Hanan. A kiɗime ya zaro wayarsa ya ƙira Hussaina ta ɗaukota ta kawota dan yana da baƙi.
Bai samu nutsuwa ba har tsawon mintuna goma Hussaina tayi sallama tare da Hanan. Kusan tare suka amsa ta gaishesu su ka amsa, daga nan suka wuce sama da Nuratu tare, Hussaina ce ta yi wa Hanan wanka ta canza mata kaya, ta sauƙo ta ɗauko musu abinci.

Duk motsinta akan idonsa, shima kuma duk motsinsa akan idonsa, yana addu'a da fatan hasashensa ya zamto gaskiya akan wannan bawa.

...

Sai biyar saura suka bar gidan, Nuratu sai ta ji duk babu daɗi dan tana ƙaunar mutane biyunnan tsakani da Allah so na ƴan uwantaka. Haka suka mata sallama bayan doguwar nasiha da kyauta mai tsoka da su ka mata, tana kuka tana musu godiya su kayi sallama. Tare suka fita da Dr Awwab ya musu rakiya gidansu Col Ahmad suka gaishe da Umma.

Sai ƙarfe takwas ya dawo gidan sanin tana tare da Hussaina zata ɗebe mata kewa. Bayan ya dawo yayi wanka ya ƙira Nuratu ta kai masa abinci falonsa, anan ya tsareta ya hanata komawa wajensu. Bayan ya gama ya sanar Ummi dare yayi Hussaina zata kwana, da ƙyar ta barta akan gobe ya barta ta dawo, da to ya amsa ya kashe wayar.
Haka Nuratu tana ji tana gani ya hanata komawa, shima anan yayi sallar isha'i, duk kumbure kumburen fuska haka ya hanata har lokacin barci ya kwasheta suka kwanta, duk da yasan babu abin da zata masa.
Hussaina da Hanan ganin shiru bata dawo ba suma suka kwanta.

...

Washegari har tara Dr Awwab ya hana Nuratu fita a ɗakin, duk da ya tabbatar mata Hussaina za tayi komai. Hakanne kuwa domin tun bakwai ta farka ta fara gyaran gidan, bayan ta gama ta haɗa breakfast, kafin ta yi wa Hanan wanka ta shiryata, tsaf ta gama komai ta shiga wanka. Har ta fito ta shirya babu alamun mutanen gidan, ita dai mamaki ma da kunya yake damunta. Babu yadda ta iya ganin Hanan za tayi letti dole ta nufi falon Dr Awwab. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi tare da sallama.
Daga can rigima ake tsakanin Dr Awwab da Nuratu, sam ya dage sai sunyi wanka tare, ita kuwa tace hakan ba zai taɓa yi wa ba wannan kayan kunyar, bayan hakama tana buƙatar kimtsa jikinta kafin ta fara wankar. Fahimtar haka yace mata ya yarda ta kimtsa jikinta sai suyi wankar, ai kafin su gama ba zata ɓata jikinta ba. Hakan da ya faɗa ya ƙara bata tabbacin dai ya dage, ita kuwa ba zata iya ba ta fara ƙoƙarin fita ya cafkota yana ɗaukarta sama.
Bathroom ya nufa da ita suka ji ƙwanƙwasa ƙofa, dakatawa yayi ya ji an sake ci gaba. Sauƙeta yayi ya kalleta, kanta kasa ga hawaye kwance saman fuskarta. Hancinta ya lakace.

"Allah ya taimake ki yarinya, da yau kinga yadda ake wanka."

Wani mugun ajiyar zuciya ta sauƙe tana share hawayenta. Murmushi ya yi ya shiga bathroom ya barta tsaye. Ganin haka da sauri ta nufi waje. Ƙofar ta buɗe su kaci karo da Hussaina.

"Aunti ina kwana."
Tace tana ƙasa da kanta.

"Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya."
Faɗin Nuratu taba yabawa da hankalin yaran.

Kai ta ɗaga tana cewa.
"Hanan za tayi letti."

"Zai fito yanzu."
Tace suna barin gurin ta wuce ɗakinta, Hussaina kuma ta sauƙa ƙasa.

Nuratun tayi mamakin ganin ko ina fes sai ƙamshi yake. Murmushi tayi tana godema ta a zuciyarta. Ganin haka ta shiga wanka tana yi tana murmushin tuna rigimar Dr Awwab, haka ta gama ta fito ta shirya cikin riga da skirt na les me kalar maroon da sea green. Kayan ya mata kyau, kwalliya kaɗan tayi ta feshe jikinta da turare ta fito, daidai Dr Awwab shima fito. Yana ganinta ya buɗe hannayensa, bata da zaɓi da ya wuce ta isa garesa ta faɗa kirjinsa ya mayar hannayen ya rumgumeta.
Shinshinar wuyanta yake yana sumbata kusan mintuna biyu, kafin ta fara zamewa tunawa basu kaɗai bane ga Hanan tana jiransa.
Kallonsa tayi, shi ma ita ɗin yake kallo da idanuwansa da suka fara ƙanƙancewa.
Fuskarsa takai hannunta ta shafa kwantaccen sajensa tare da kashe masa ido ɗaya.

"Bamu ɗaya bane."

Daga haka tayi gaba ta barsa tsaye tamkar an dasashi, bayanta ya bi da kallo. Da tana sallah yau da babu abin da zai hanasa nuna mata tasirin abun da ta masa, ba baƙi ba ko Hanan sai dai tayi letti ko ta fasa zuwa islamiyyar. Ya kusa mintuna da ƙyar ya samu nutsuwarsa ya sauƙo falon ƙasa. A dinning gaba ɗaya ya samesu, Hussaina da Hanan sunyi breakfast tana tattara plate ɗinsu.
Bayan ya amsa gaisuwar Hussaina da Hanan yace.

"Mu je idan na sauƙeta na kai ki gida."

To tace masa ta kai kayan kitchen ta fito ta wuce ɗauko hijabinta. Ganin haka ya ƙarasa wajen Nuratu da tayi tamkar ba ita ba. Hucin numfashinsa ta ji saman fuskarsa, a razane ta matsa ya ƙara matsota. Marairaice masa tayi.

"Hanan fa tana kallonmu."

Wani kallo ya jefa mata ta yi kasa da kanta.
"Kin ci bashi yarinya, ki guji ranar shiga hannuna."

Daga haka ya matsa yana kallon Hanan da ta kafesu da ita. Harararta yayi yace.
"Taso mu je kin wani sakawa mutane ido."

Babu musu yarinyar ta miƙe ta bi bayansa tana yi wa Nuratu sai anjima. Haka Hussaina ta sauko tamata sallama ta wuce. Bayan fitarsu ita ma ta ƙira Mami suka gaisa.

Sai goma saura ya dawo tare da wanda yayi mutuƙar tsorata Nuratu. Suna yin sallamar ta hangosa bayan Dr Awwab da gudu ta bar wajen tana hayewa saman, ba ta tsaya a falo ba ta wuce ɗaki ta kulle kanta sai kuka.
Ganin haka ya saka Awwab taran baƙonsa cikin girmamawa da mutunci, ya nuna masa wajen zama ya zauna.

"Bari in ƙirata Baba, nasan tana cikin ruɗune."

"Babu komai."
Ya faɗa fuskarsa tsantsar damuwa ganin gudan jininsa na gudunsa.

...

Can ɗaki kuwa Nuratu kuka take ta yi tana mamakin ganinsa cikin gidanta. Tsawon shekaru huɗu rabon da ta sakasa a idanuwanta a matsayinsa na ubanta.
Me ya zo nema wajenta? Me ya ke buƙata? Ruguza farin cikin da ta samu gidan aurenta domin tasan burinsa kenan a rayuwa, ya hanata jin daɗin ciki...

Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ya hanata ƙarasa maganar zuci ta miƙe cike da tsoro.

"Babyna buɗe ƙofar ni ne."

Ta tsinci muryar Dr Awwab, cikin sassarfa ta isa tana buɗe masa, sai da ta leƙa ganin babushi ta buɗe ƙofar gaba ɗaya. Yana shigowa ta faɗa jikinsa tana fashe masa da kuka, rumgumeta yayi su ka isa bakin gado ya zauna ya zaunarta jikinsa, hannu ya saka yana shafa bayanta da bubbugawa alamar lallashi.
Sai da tayi me isarta ta fara sauƙe ajiyar zuciya.

"Ki daure mu je ku gaisa, ki ji me zai faɗa miki."

Girgiza kai tayi tana ɗago kanta wani hawayen na silalowa a idanuwanta.
"Ba zan iya ba, zai cutarni, ya tsaneni."

"Kiyi hakuri, mu saurari me yazo da shi."

Yace yana saka hannu ya share mata hawayenta. Za tayi magana ya ɗaura yatsarsa saman bakinta, dole tayi shuru. Ganin haka ya miƙe ya ɗauka mata mayafi ta rufe jikinta. Yana riƙe da hannunta su ka fito, jikinta rawa yake lokacin da suka shigo falon. Durƙushewa tayi lokacin da suka iso tsakiyar falon, muryarta na rawa tace.

"Ina kwana Baba."

Wani sanyi yaji cikin ransa jin rana ta farko ta ƙirasa Baba. Kai ya jingina ya amsa da.
"Lafiya lau Nuratu. Ya zaman ibada."

Ba ta iya amsawa ba sai kai ta girgiza masa. Ganin uba da ƴar suna buƙatar samun guri ya saka Dr Awwab miƙewa.

"Bari in amsa ƙira."

Daga haka ya fita ya basu guri. Ganinsa ya saka Nuratu ƙarfin halin zama, ganin kuma ya fita ya sata jin tsoro sai dai kalaman da Alhaji Mamman ya fara mata ya sa ta dubansa.

"Autar Mami kiyi haƙuri kinji, nasan ke me hakurice ki ƙara hakuri. Ina neman yafiyarki badan na cancanta ba sai dai gudun haɗuwata da Allah, kiyi hakuri ki yafemin."

Kuka Nuratu take ta rasa na farin ciki ko akasin haka, mahaifintane yake neman gafarta bisa abubuwan da ya aikata mata, tabbas duk me rai baya wuce rahmar Ubangiji.

"Ki daina kuka kin ji, kar kice ba za ki yafewa mahaifinki ba, nasan ni mai laifine a wajenki, amma gani yau ina neman gafararki don Allah."

"Baba ka daina roƙona."

Nuratu tace tana share hawayenta.
Hannu ya miƙa mata, babu musu ta saka nata cikin nasa ta rarrafa wajensa tana ɗaura kanta saman cinyarsa. Wani kukan ta fashe da shi, duk abin da ya aikata mata amma take wani muguwar sonsa da ƙaunarsa suke lulluɓeta, mahaifi dabanne, ƙaunarsa dabanne.
Kukanta tasha har ta fara sauƙe ajiyar zuciya, har lokacin kanta saman cinyarsa yana shafa mata kai, shi ma nasa ɓangaren ji yayi zuciyarsa ta raunana, ya yi wa shaiɗan da aboki ala tsine yafi cikin kwando.
Ƙaunar ƴarsa da sonta na ratsa jininsa. Tsakanin iyaye da yara fa sai Allah, domin akwai wani sihirtaccen kauna a tsakani da Allah kaɗai yasan iyakarsa.

Sun jima a haka kafin Nuratu ta ɗago kanta da idanuwanta da su kayi jajir, murmushi ya mata ta mayar masa tana yin ƙasa da kanta.

"Ba ki ce komai ba."

"Baba ni fa dama ban riƙe ka ba. Na yafe wallahi duniya da lahira."

"Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya."

Kunya ya hanata amsawa ta miƙe, kitchen ta shiga ta jido masa duk abin da tasan zai iya ci da sha. A saman table na tsakiyar falon ta ajiye masa.
Da murmushi ya kalleta.

"Baba kasha wani abun."
Tace tana buɗe murfin jug ta tsiyaya masa a cup ta miƙa masa, babu yadda ya iya ya karɓa ya kurɓa yana ajiyewa tare da miƙewa.

"Zan wuce Nuratu sai munyi waya."

Turɓune fuska tayi kamar za tayi kuka.
"Baba daga zuwa, ka ga ko hira ba muyi ba."

"Karki damu za muna waya. Saka mini lambarki."

Babu musu ta karɓi wayarsa ta saka masa lambar. Har ƙofar falo ta masa rakiya anan suka haɗu da Dr Awwab ya masa rakiya zuwan bakin mota, sun ɗan tattauna kafin ya shiga motarsa ya wuce shi kuma ya nufi cikin falon. Ta tattare komai ta mayar kitchen, murmushi take wani sa'in hawaye ya zubo ta share dan farin ciki, ta rasa wa zata fara nunawa farin cikinta.
Ba zato taji an ɗagata sama, ihu za tayi jin ƙamshin turaren Awwab ya sa ta sakin ajiyar zuciya. Sauƙeta yayi ya rumgumeta.

"Babyna tana cikin farin ciki naga alama."

Juyawa tayi ta ɗaura hannunta ta saƙalo saman wuyarsa, ganin haka shima ya ɗaura hannunsa saman kugunta ya rankwafo yana haɗa goshinsu. Ba zato yaji sauƙar bakinta saman nasa ta fara kissing ɗinsa, a rikice ya fara mayar mata da martani duk ya rikicemata, abin da ya jima yana burin samu daga gareta.
Sun jima haka ganin za ta fitarsa hayyacinsa ta kasa magance masa ya sa ta zare bakinta. Tsam ya rumgumeta yana sauƙe numfashi tare da tagwayen ajiyar zuciya.

...

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE Haske 56.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

"Ina cikin farin ciki marar misaltawa yau, haƙiƙa yau rana ta dabanne a gareni dama na kusa da ni, ko yau na komawa Ubangiji allahamdulillahi burina ya cika."

Sakinta yayi daga rumgumar da ya mata ya riƙo fuskarta, sumbatar leɓɓanta ya yi.
"Ni ma naga hakan a zahirance da aikatance. Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki Matata."

"Ameen na gode, kaima haka Awwab AbdulRamat."

Ta ƙare maganar tana ɗaura kanta saman kirjinsa ta lumshe idanuwanta tana shaƙar ƙamshin turarensa.
Shock Dr Awwab ya ji jin yau rana na farko da ta ƙira sunansa, wani kasala ya sauƙar masa, da ƙyar ya riƙeta mai kyau suka fito, a saman kujera ya zubarsu yana ƙara kamkameta.

"Maimaita sunan saman harshenki please."

Yace yana tallafo fuskarta, idanu ta lumshe ta buɗe tana sakar masa murmushi har dimple ɗinta suka lotsa tace.
"Awwab AbdulRamat mijin Nuratu Mamman Bashir, Baban Hanan da ƙannenta."

"Kina sona?"

Ya tambayeta da rawar jiki, gaba ɗaya jikinsa tsuma yake. Kalamanta ne suka haddasa masa hakan.
Kanta ta mayar saman kirjinsa.

"Sosai ma, idan har abin da nake ji idan mun kasance mu biyun so ne, to na daɗe da sonka a raina tun ba yau ba, tun ranar dana dawo hayyacina daga wancan duniyar. Ban tantance hakan ba sai dana zauna da kai. Ina ƙaunarka fisabilillahi."

Shuru kawai ya yi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login