ENGLISH DESCRIPTION
In a world where royalty is built on secrets, power, and an untold destiny, the life of Sheikh Arman Maleek Abdul-Azeez Sarki shines like a light hidden in deep darkness.
He is not just a king, but also a deeply devout scholar, a man whose gentle voice shakes the hearts of many. Yet behind this calm authority lies a heart burdened with secrets no one truly understands.
A tragic accident changes everything in a single moment, where lives hang between survival and death. In the middle of the chaos, a severely injured little girl is discovered, and she becomes the beginning of a destiny no one expected.
Meanwhile, the royal palace filled with pride, hidden conflicts, and deep family hatred begins to awaken old wounds that were never healed.
Will Sheikh Arman Maleek be able to protect his heart from the love destiny is preparing for him, or will the girl he saved become the force that destroys everything he has ever known?
Love, secrets, royalty, destiny, and faith collide in a story that will shake your emotions to the core.
HAUSA DESCRIPTION
A cikin duniyar da sarauta ke cike da sirri, iko, da kaddarar da ba a taba rubutawa ba, rayuwar Sheikh Arman Maleek Abdul-Azeez Sarki ta kasance tamkar hasken da ke ɓoye cikin duhu.
Shi ba kawai sarki ba ne, malami ne mai tsananin tsoron Allah, mai murya mai taushi da ke girgiza zukatan al’umma, amma a bayan wannan kwarjinin akwai zuciyar da ke ɗauke da nauyin sirrin da ba kowa ya sani ba.
Wata hatsaniya mai muni ta sauya komai a rayuwa cikin dakika daya, inda rayuka ke yawo tsakanin rai da mutuwa, kuma a tsakiyar wannan bala’i aka gano wata yarinya ƙarama da ta jikkata fiye da misali, amma ita ce za ta fara bude wani sabon babi na kaddarar da ba a shirya ba.
A gefe guda kuma, gidan sarauta mai cike da girman kai, rikice rikice, da ƙiyayya tsakanin dangi yana kara tada tsoffin raunuka da ba su warke ba.
Shin Sheikh Arman Maleek zai iya kare zuciyarsa daga soyayya da kaddara ke shirin rubutawa masa, ko kuma wannan yarinya da ya ceto za ta zama makamin da zai rusa dukkan tsarin rayuwarsa?
Soyayya, sirri, sarauta, kaddara, da imani suna haɗuwa a cikin labarin da zai girgiza zuciyarka.