Follow us on social media

Showing 75001 words to 78000 words out of 148866 words

Chapter 26 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

32

sakewa da Babyna."

"Ni bana son sunan nan na faɗa maka."
Nuratu tace tana yin gaba ya biyo bayanta da sauri.

"Ni ina son sunan. Na faɗa miki ke Babyna ce kin ƙi yarda ko? But soon za ki yarda da hakan."

Dakatawa tayi da tafiyar da take ta watsa mishi wani kallo ta ɗauke kanta ya ƙaraso kusa da ita dai-dai lokacin iska ya kaɗa gyalen dake saman kanta zai fita har gashin saman kanta ya bayyana, da sauri ya saka hannu ya cafke gyalen ya mayar mata ta riƙe tana gyarawa. Cikin sauri tayi gaba ta barshi tsaye cike da mamakin ganin kwantaccen gashin da yake kanta, bai taɓa tsammanin tana da tsantsin gashi ba duk da kwantaccen gashin goshi da take dashi, ya ɗauka iya nan ya tsaya. A ranshi yaji kawai yana son ganin jelar gashinta ya ga iya tsawon sa.

Bayanta ya bi cikin sauri yana ƙiranta.
"Babyna! Babyna."

Nuratu kamar ta shige ƙasa dan kunyar sunan da yake ƙiranta da shi ga Nazifa da tayi gaba ta barta.

"Ki tsaya ko in na zo na baki mamaki."
Dr Awwab yace dole ya saka Nuratu dakatawa ya iso ta.

"Kin bani wahala. Mu je to"

Yace yana fara tafiya tabi shi. Bata mishi magana ba dole ya sata jerewa suka kama hanyar gidan tare, da ka gansu sun dace da junan sai bambancin launin fata dan Dr Awwab akwai haske.

....

#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE  37.

Pharty Bb
Wattpad phartybb.

***

Tafiya suke babu wanda yayi magana sai Dr Awwab da sanyi ya ishe sa yace.
"Kai garin nan akwai sanyi, Nijeriya bai kai haka ba."

"Sai cikin dare ma."
Nuratu ta bashi amsa suna cigaba da tafiyar har suka iso gida ana ƙiran sallar magriba.

A soron gidan ya dakata yace.
"Babyna."

Dakatawa Nuratu tayi ta fasa shiga cikin gidan ta tsaya tana juyawa ta kalleshi, ya sakar mata murmushin da bata iya juran kallo ba ta ɗauke idonta.

"Kin yarda ke Babyna ce?"

Taji maganar shi sai lokacin ta ankara da abin da ta aikata ta juya da sauri ta shiga cikin gida, kwata kwata bata san tayi hakan ba, bata san ta tsaya ba. Haushin kanta ne ya kamata da ta biye masa, ai sai ya tsammanin ta fara faɗawa tarkon shi.
Murmushi Dr Awwab yayi bayan shigan ta ciki, ya koma ya riga ya amince Nuratu tana son shi kawai taƙi bawa kanta da zuciyarta daman hakan ne. Yasan ko ta samu labarin da aurenshi a kanta ba zai sha wahalar shawo kanta ba.

Sai da su kayi sallar isha'i suka dawo gidan tare da Kawu Muhammadu da Musalle. Kawu Muhammadu yana cewa.

"Kai kam dai baka gajiya wallahi, kullum kana hanya, kafin ta zama mata ma kullum kana hanya balle yanzu ta zama matar kam sai ka dawo da aikin ka nan garin."

Murmushi kawai Dr Awwab yayi cike da kunya yana sosa kan shi.
"Kawu magungunan ta na kawo mata, sun kusa ƙarewa."

"Babu wani ka zo dai ganin matar ka, bana son wani gulma a dangana da magunguna. Ita ma gobe zata tafi sai ku tafi tare, na gama daku sai mun zo biki."

Sosai maganganun Kawu suka saka Dr Awwab jin kunya amma in ya tuna Nuratu zata koma tare za su tafi yaji daɗin hakan. Da daren duk yadda a kayi Nuratu ta kaiwa Dr Awwab abinci ɗaki ƙi tayi tace kanta yana ciwo aka bawa Musalle ya kai mishi.

Da safe ta samu labarin tare za su koma da Dr Awwab kamar tace ta fasa amma ba yanda ta iya haka ta gama shirya kayanta tsaf ta fito da shi ta shirya cikin riga da skirt da babban mayafinta ta yafa a jikinta.
Bayan sun yi sallama da ƴan gida suka ɗauki hanya, suna tafe babu wanda ya yi magana har sunyi nisa da tafiya Dr Awwab ya juya yana kallonta hankalinta a kan titi.

A hankali ya saka hannunshi ya riƙo hannunta da yake saman cinyarta. A wani mugun tsorace Nuratu ta juya a firgice tare da kwace hannunta ta ja baya, wani shork ta ji a jinin jikinta da ya haddasawa zuciyarta bugawa.
Guri ya samu ya faka motarshi ya juya ya kalleta ta takure guri ɗaya.
Idanuwansa kawai ya zuba mata wani mugun sonta da kaunarta yana shiga ranshi, ji yake kamar ya rumgumeta a jikinshi su haɗe su zama abu ɗaya.

Ganin ya faka motar kuma yaƙi magana ya saka Nuratu kallonshi ta ga idanuwansa yana yawo a jikinta ta haɗa rai.
"Bana son haka Docter."

"Ina son ki sosai Babyna."
Yace yana murmushi tare da ɗaura hannunshi saman cinyarta yana ƙoƙarin kamo hannunta ta ɗauke tana matsawa.

"Ni ka dai na kallona."
Tace bayan ta ɗauke idanuwanta cikin nashi.

Murmushi ya ƙara yi yace.
"Laifi ne dan na kalla abin da zan mallaka."

Baki ta tura ta juyar kanta gefe taƙi masa magana, hakan yasa ya ja motar suna barin gurin, sun yi nisa a tafiya ta ji ya fara magana.

"Noor kar ki ce dan ƙaddara ta faɗa rayuwarki ki kasa bawa zuciyar ki dama ta dubi abin da take so, kar ki hana kanki ki cuci kanki kan abin da kike so ki ke muradi. Ki rumgumi ƙaddarar ki da hannu bibbiyu ki kawar da komai ki fara rayuwar ki tamkar kowa."

Shuru Nuratu ta yi tana jin maganganun shi suna shigarta ya juya ya kalleta ya mai da hankalin shi kan titi ganin ya fara cin nasara a kanta yaci gaba da cewa.

"Ina son ki ina ƙaunar ki Noor, tun lokacin da na fara ganin ki, tausayin ki ya rinjayi zuciyana har na faɗa son ki, ban yarda da haka ba sai daga baya. Dan Allah ki bani dama Noor, zan mamaye wannan duhun da haske, zan zame miki gata, zan baki dukkan kulawa, zan baki farin ciki dai dai yadda Allah ya hore min. Ɗan adam ajizine dole wataran ya ɓatawa mutum amma Insha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na kiyaye. Ni Awwab sonki nake tsakani na da Allah ba wai dan wani abu naki ba."

Maganganun Dr Awwab ɗaya bayan ɗaya suke shiga zuciyar Nuratu suna neman gurin zama, ta kasa magana ta kasa tantance mai take ji game da maganganun shi. Jin shurunta ya saka Dr Awwab juyawa ya kalleta fuskarshi ɗauke da murmushin cin nasara, gani yayi ta mai da kanta kan kujera ta lumshe idanuwanta.

"Bacci ko?"

Kai ta ɗaga masa ya tsayar da motar yana gyara mata seat ɗin yayi baya ta gyara kwanciyarta yaci gaba da tuƙi.
Bacci ne ya kwashi Nuratu tana juya maganganun Dr Awwab a ranta, gaba ɗaya ya sata tunani.
Ta san aure shine rufin asirinta amma tunanin abin da yake cikin aure take tunawa. Ba ta san me zata tarar ba, bata san me zai faru ba, bata san yaya mijinta zai ɗauketa ba ko zai karɓeta ba, bata da komai ba, bata da abin da za ta bashi a matsayinta na ƴa mace, tsoro take wata rana ya mata gori.

Wa zata zaɓa cikinsu Yaya Al-ameen da ya jima da sonta da kaunarta itama taso shi, ko Col. Ahmad da ya tsaya mata ta kwaci haƙƙinta, ko shi Dr Awwab da ya taimaka mata ta dawo hankalinta da yanzu take jin wani abu a zuciyarta a kan shi da ta rasa taƙamemen menene.

Tana wannan tunanin bacci ya kwashe har suka shiga Geidam ya tsaya yayi sallar azahar ya saya musu abin da za suci kafin yaci gaba da tafiya. Yamma lis suka shiga kafin Nuratu ta farka, jin motsinta ya saka Dr Awwab kallonta suka haɗa ido ta watsa mishi wani kallo yayi murmushi ya ɗauke kan shi.

"Mun shigo kin farka."

"Yamma yayi sosai, nayi bacci ashe."

"Za ki biyani ladan wahalar da ni da kike."
Dr Awwab yace lokacin da ya ɗauki hanyar gidan su Nuratu.

Bata mishi magana ba ta juyar kanta, har ƙofar gida ya sauƙeta ta fita tana miƙa kafin ta shige gidan da saurinta, shi ya ciro akwatinta ya bi bayanta zuwa cikin gidan ya samu ta rukunkume Mami tana murnar ganinta kamar yarinya ƙarama.

"Ina wuni Mami?"
Dr Awwab yace yana ajiye jakan Nuratu a gefe, jin muryar Dr Awwab ya saka Nuratu sakin Mami ta kalleshi suka haɗa ido ta ɗauke kanta.

"Lafiya lau Docter ya gajiyar hanya, kun sha hanya."

Cike da kunyar Mami ya amsa ya miƙe daga durƙushen da yake.
"Mami zan wuce sai wani lokaci."

"Haba Docter ba zaka jira zuwa gobe ba? Akwai gajiya ai."

"Babu komai Mami zan wuce kawai."

"To shikenan ka gaishe da mutanen gida."

"Za su ji inshaAllah."
Yace ya nufi waje Nuratu ta bishi da kallo, Mami na ganin hakan yasa tace.

"Tashi ki raka shi mana."

Kamar jira take ta miƙe ta nufi wajen tana gyara zaman mayafinta. Murmushi Mami tayi ganin ƴartan ta fara karɓar Dr Awwab a rayuwarta ta san ko ta samu labarin da aurensa a kanta ba zata ƙi ba, ta ji daɗin da ya kasance shine mijin ƴartan ko ba komai asirinta a rufe babu wanda yasan mai ya faru cikin dangi sai in har shi ya furta wanda bata tunanin zai faɗa hakan.

Bayan fitar Dr Awwab kamar ya san Nuratu zata fito ya kunna motar ya zauna, tana fitowa ta isa wajen motar shi.

"Thank you so much Docter, ka gaishe min da Baby Hanan."

"Za taji, sai munyi waya. Yaushe zan dawo."
Ya tambayeta yana ɗaga mata gira ganin sun haɗa ido. Da sauri ta juyar kanta.
Shi kam yana mamakin yadda bata iya juran kallonshi ko na minti ɗaya, ya lura kwata kwata bata iya kallon cikin idonshi kamar mai tsoron shi.

Nuratu da ta juyar kanta tace.
"Nima ban sani ba."

"Kina so in zo kenan, kin bani damar zuwa ko wani lokaci."
Ya faɗa jin amsar da ta bashi.

Girgiza kai tayi.
"Ni dai bance ba."

"Shikenan karɓi drugs ɗinki, inshaAllah kin kusa rabuwa da shi gaba ɗaya. Ina yanzu babu ciwon kai?"

Kai ta ɗaga masa yaci gaba da cewa.
"Insha Allah in har babu wani matsalar za ki dakata da sha mu gani. Yanzu dai ki bani abun da in na gani za ina tunaki duk da hotonki kullum yana cikin zuciyana ban da na waya."

Harara ta mishi ta juya ta nufi cikin gidan sai da ta kai bakin kofa ta juyo tana cewa.

"Ka gaishe min da Ummi da Hanan."

Murmushi ya sakar mata ta shige cikin gidan da sauri ya ja motar shi yana barin gurin cike da nishadi. Da ya rasa Nuratu bai san ya zai yi ba.
Wajen taran dare ya isa Maiduguri duk ya gaji, wanka yayi ya gabatar da salloli kafin ya nufi gidan Ummi a babban falon gidan ya same su har Ummi da Hanan.

Hanan tana ganin shi ta ƙi masa magana tana fushi da shi tun safe, murmushi yayi ya saka Hassana haɗo masa abinci ta miƙe ta kawo masa tana zubawa.

"My Love fushi take dani har yanzu."

Dariya Hassana tayi.
"Ai yau mun sha rigima, gashi nan har yanzu fushi take maka sai kayi aikin lallashi."

"Dole na ai."

Yace ya ɗauki spoon ya fara cin abincin shi yana kallon Hanan. Sai ta ɗago ta kalle shi ta ɗauke kanta ko zai mata magana, ganin ya kamata tana kallon shi tana neman lallashi ayi sulhu ya sashi barin abincin ya miƙe tsaye.

"Wa zai sha ice cream muje siya?"
Yace bayan ya miƙe.

Hussaina tace.
"Yaya ni."

Hassana ma ta miƙe tace.
"Ni Yaya."

Ya girgiza kai yana nufan gurin Hanan.

"My Love nawa kaɗai zan siyawa, in ta yarda sai in saya muku."

Yace ya zauna kusa da ita da take kusa da Ummi tana jin shirmen shi da ƴar shi.

Hanan jin maganar ice cream ya sata lallaɓawa kusa da Dr Awwab.

"Za ki sha?"
Yace yana jawota jikinshi ta rumgume shi da ƙarfi ta ɗaga misa kai tace.
"Zan sha."

"Za ki daina fushi dani?"

Kai ta ɗaga masa.
"Amma zaka kai ni wajen Aunti Noor Babyn k..."

Da sauri ya rufe mata baki ya miƙe yana ɗaukarta jin zata baro masa zance suka nufi waje.

"Ummi za mu je mu dawo."

Murmushi Ummi tayi ta amsa da to, ta fahimci maganar jikarta da take nema ta saka ubanta kunya.

A gajiye yake amma dole ya saka ya kai su wajen shan ice cream ya sayawa Hanan kafin ya ɗauki hanyar gidan shi.

"My Love yau gidanmu za mu je."

"Daddy babu kowa fa."
Tace tana shagwaɓe masa.

"Yau kaɗai gobe zan maida ki."

Ba dan taso ba ta bishi suka je gidansu da bata son zaman ita ɗaya, har ɗakinshi ya kai ta bayan ta sashi ya goyeta ya ajiye saman gado. Tsalle take masa saman gadon ya rabu da ita ya ɗauki laptop ɗinsa yayi aiki ya haɗata da game tana yi har bacci ya kwashe ta. Sai da ya gama abin da zai yi kafin ya rufe ya ƙarasa bakin gadon ya musu addu'a ya shafa ya rufeta kafin ya kwanta kusa da ƴar shi ɗaya tilo abun son shi.

***

A haukace ya farka musu da safiyar cewa sai ya kashe kansa idan ba'a nemo mishi Nuratu ba. Ummu da ta kasa yi da shi ta gudu ɓangaren Hajiya Batula ta ƙira Daddy ya zo da saurin sa ya samu Mufid riƙe da wuka yana cewa.

"Wallahi ko a nemo min ita a kawo ko in kashe kai na. Ku kun san yadda nake jin zuciyana? Zafi yake min kamar ya fita. Ku nemo min ita."

Daddy da ya shigo ya ga tilon ɗan san cikin yanayi na marasa hankali ya ja baya gudun kar ya ganshi ya ƙara tunzura.

"Ina za ka je?"
Ummu tace tana ganin yana komawa baya.

"Motar asibiti zan ƙira su zo ɗaukar shi, bazan iya masa ba, bakya ganin baya hankalinshi. Wani abun yasha wallahi ya taɓa ƙwaƙwalwarsa na sani."

"Kana nufin Mufid ɗin hauka yake?"

"Ga alama nan."

Daddy yace ya nufi ɓangaren shi ya ɗauki waya ya ƙira emergency cikin gaggawa kafin ya zauna. Yama rasa wani irin tunani zai yi dan nema Mufid Nuratu. Alhaji Mamman ne yaci kuɗin shi da baya jin zai iya bar mishi sai ya biya shi.
Kusan mintuna goma motar ta iso tare da security guda uku majiya ƙarfi suka nufi falon Ummu.

Mufid duk ya hargitsa kayan falon bayan na jiya da ya farfasa aka gyara. Cikin sanɗa da dabara security biyu suka damƙe shi ɗaya ya kwace wuƙar hannunshi da sigarin kafin su fara kokuwar fita da shi.

"Ina za ku kai ni? Wani irin abune wannan. Ummu kina ganin za su tafi dani, ku rabu dani dalla."
Mufid yace yana turjewa yana kallon Ummu da take hawaye tana ji tana gani za'a ɗaura tilon ɗanta hauka.

Duk kokuwa da Mufid yake haka aka saka shi a motar suka ɗaure shi kafin likitan da ke ciki ya masa allurar bacci, tuni kagin su isa asibitin bacci ya kwashe sa. Bai san sun isa ba har ɗakin da Daddy ya kama masa aka saka shi suka ɗaure hannunshi da kafarshi jikin gadon suka fito, Docter da zai duba shi ya shiga ya fito ya samu Daddy.

Gilashin idonshi ya cire yana duban Daddy.

"Yanzu dai ba zamu iya cewa komai ba sai ya farka mun ga yanayin jikinshi. Sannan abin ya fara shafar ƙwaƙwalwarsa, zai iya sai an dangana da psychiatric hospital saboda su bincike ƙwaƙwalwarsa."

Alhaji Kashim da ya kasa ko tari balle kwakkwaran motsi yana sauraron bayanin Docter har ya gama ya miƙe yana cewa.
"Shikenan Docter zamu san yadda za ayi. Bari in je gida in dawo zan sanar da mahaifiyarshi halin da ake ciki."

To Docter yace Alhaji Kashim ya fita cike da tashin hankali abin da ya samu tilon ɗan shi namiji akan wata yarinya. Da ya koma gida ya sanar Ummu da har lokacin ta kasa tsaida hawayenta. Kuka ta ƙara fashewa da shi.

"Yanzu Mufid ne ke hauka akan mace? Wallahi ƙarya ne."

"Sai kuma kiyi ai, kina gani dai da na bar muku shi sai ya miki rauni ko ya yiwa kan shi fa."

Girgiza kai tayi tana share hawayenta ta ɗauki wayanta ta sanar da Aunti Humaira da sauran yaran halin da ɗan uwansu yake ciki. Kowa ya ji abin babu daɗi ban da Rufaida da a zuciyarta ta san haƙƙin Nuratu ne da sauran mutane ya fara bibiyar shi.

***

Nuratu washegarin ba ta farka da wuri ba har wajen ƙarfe goma tana cikin bargo har sai da Mami ta shigo ta tashe tana faɗa.

"Yanzu in kinyi auren haka za ki dinga baccin safe. Wa zai dafa mijin abinci da safe yaci ya tafi aiki? Lallai aiki ya same ki, in ma za ki gyara ki gyara wallahi."

Gunguni Nuratu tayi ta wuce bathroom ta wanke bakinta ta fito ta samu Mami ta bar ɗakin ta fita falon. Breakfast ɗinta ta samu Munirat ta zuba mata cikin flask ta ɗeba a plate ta dawo falon ta zauna ta hau ci.

"Ki gama ki saka min lambar Ahmad in ƙira shi, tun da ya tafi ba muyi waya ba."

"Ni ma wallahi Mami, bari zan ƙira shi ta wayana sai in haɗa ku."

"To ki gama."

Mami tace ta wuce kitchen dan duba kayan abinci da babu ta aiki Munirat. Bayan ta gama ta lissafa mata abubuwan da za ta siyo ta fita ta dawo falon ta samu Nuratu.

"Kiyi ki ɗaura abincin rana na aiki Munirat. Ita ma bikinta ya kusa saura sati biyar zan tura ta gida. Ga na Walida shima ya gabato saura wata ɗaya."
Mami ke wannan bayani tana zama lokacin da Nuratu ta gama ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen ta dawo ta wuce ɗakinta ta ɗauko wayarta ta dawo falon.

Col. Ahmad ta ƙira ringing ɗaya ya ɗauka yana mata sallama tare da cewa.

"Nuratu ya kike? Ya gida? Kin dawo kenan?"

Bayan ta amsa ta ce.
"Lafiya ƙalau. Ya aiki?"

"Allahamdulillahi. Ina Mami?"

"Ga ta nan za kuyi magana."

Tace ta miƙawa Mami wayar Mami tace.
"Je kiyi aikin da na saki."

Babu musu ta miƙe tana mamakin menene Mami za ta faɗawa Col. Ahmad da za ta ɓoye mata. Kitchen ta shiga ta fara hada hadar ɗaura abincin rana.

Col. Ahmad bayan ya gama sauraron bayanin Mami yace.
"Allahamdulillahi Allah ya sanya alheri, Allah yasa shine mijinta har a aljanna. Na ji daɗi wallahi da ta kaucewa wannan mutanen."

"Ameen. Ameen ya Allah."
Mami ta amsa da shi tana jin Col. Ahmad a ranta tamkar ita ta haife shi.

Col. Ahmad cike da farin ciki yace.
"Ni ma ƙarshen watan nan ina hanya. Ku bani wannan damar in sanar mata  in na zo, na san za ta ji magana na ta karɓi auren nan ko bata so."

"Shikenan an baka sai ka sanar da Dr Awwab kar yayi gaggawar faɗa mata."

"InshaAllah zan yi hakan, Nagode Mami sosai."
Yace su kayi sallama ya shiga neman lambar wayar Dr Awwab.

....

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE 38.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Hauka Mufid ya yi ta musu a asibitin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login