Follow us on social media

Showing 105001 words to 108000 words out of 148866 words

Chapter 36 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

29

gurinta ya sata juyawa ta kalli Hanan.

"Ki je wajen Aunti kinji My Love."

Make kafaɗa Hanan tayi tana kallon Binta da ta miƙa mata hannu. Ta juya ta kalli Hussaina.

"Za ta kai ni wajen Aunti Noor."
Hanan ta faɗa ta juya tana zurawa Binta manyan idanuwanta kyawawa.

Binta da taji baƙin ciki ya rufeta jin sunan da ta ƙira ta ƙirƙiro murmushi ta ɗaura saman fuskarta.
"Sosai ma zo muje."

Da gudu Hanan ta je jin hakaz ta isa wajen Binta ta ɗauketa sama ta kalli Hussaina.
"Haɗa min kayanta mu tafi. Kawo wannan in saka mata"

"Aunti Binta amma Daddyn ta fa ya hana kuma bai sani ba."

"Nace haɗa min kayanta ke kam. Kina tunanin zan cutarta ne?"

Girgiza kai Hussaina tayi tace.
"Bari in sanar da Ummi to, ko in ƙirashi a waya."

"Haɗa kayan ni bari in sanar da ita daga nan zan masa waya."

To Hussaina tace ta ɗauki ƙaramin jaka ta sakawa Hanan kayanta kala biyar dan ta san ko an kaita Dr Awwab zai dawo da ita. Binta kuma ta sakawa Hanan gown ɗin da Hussaina ta bata suka fita.

...

"Ummi zan wuce sai wani lokaci."
Binta tace ɗauke da Hanan da ta maƙale mata jin za ta kaita wajen Aunti Noor.

Ummi dai da mamakin ganin Hanan da Binta dan tasan sam Hanan bata zuwa wajenta tace.
"To ki gaishe da gida mun gode sosai Allah ya bar zumunci."

"Ameen ya Allah."
Binta ta faɗi haka ta fita da Hanan, sauƙa ƙasa tayi ta karɓi kayan Hanan wajen Hussaina ta fita. Daga nan Hussaina ta hau tattare ɗakinsu.

***

Bai sameta a falon ƙasa ba ya wuce sama, falonta kai tsaye shiga shigowar sa gidan kenan bayan ya tsaya yayi sallah a masjid. A falonta ya sameta kwance tana ganinsa ta miƙe zaune.

"Sannu da dawowa."
Ta faɗa tana gyara ɗankwalin kanta.

"Yawwa sannu Babyna."
Yace yana jin daɗin yadda take masa tarɓa in ya dawo. Zama yayi kujeran da yake facing ɗinta ya ɗaura kafafunsa saman center table.

"Abinci fa?"

Ta tambayeshi tana kai kallonta kan shi shima ita yake kallo babu kiftawa, kwalliyar ya burgesa, simple doguwar rigane jikinta na wani yadin material mai kyau. Murmushi ya mata yace.

"Ba dan zan saki wahala ba da kin kawo mana nan."

"Babu komai bari in ɗauko."
Daga haka ta miƙe ta nufi waje.

"Yawwa Babyna ƴar albarka."

Dr Awwab yace yana sauƙa ƙasa ya zauna, ta ɗauko komai ta kawo falonta cikin babban tray ta ajiye a ƙasa ta zauna ta buɗe. Idonshi ya lumshe ya buɗe jin ƙamshin abincin, tun kafin ya ci yaji yawunsa ya tsinke, ta duba musu cikin plate ɗaya, jellof ne na shinkafa da ya ji kayan lambu da kifi.

"Bismillahi."

Nuratu tace ta ajiye plate din da ta saka abincin ta saka musu spoon domin har ta saba da cin abinci da shi tare. Hannu ya saka ya ɗauki spoon ɗaya ya fara ci.

Taunawa yake ya zuba mata ido, Nuratu da take cin abinci ta ga kallon ya mata yawa tace.

"Zan kware Doctor, wannan kallon fa?"

Murmushi yayi yana shafa kwantaccen gashin kan shi, ya kai hannun ya shafi gefen kumatunta yace.
"Kin iya girki sosai Babyna, tun ba yau ba na lura da hakan."

"Nagode."
Nuratu tace cike da jin daɗi mijinta ya yaba girkinta. Haka suka gama. Bayan sun gama ta kwashe komai ta saukar ƙasa ta wanke kafin ta dawo falon. Zama tayi gefe da shi ganin yana aiki a laptop ɗinsa.

***

Tun a hanya take mata kuka ganin sun ɗauki wani hanyar ba hanyar gidansu ba. Lallashin duniyar nan ta mata ta ƙi shuru sai ma ƙara kukanta take har suka isa gidansu.
Mama da ta ga abin ya isheta tana kallon Hanan dake rizgar kuka tace.

"Yanzu ke Binta kin kwaso yarinya babu sani ubanta, sannan ga shi ta ƙi miki shuru. Wannan abun zai kai labari."

Faɗin Mama tana kallon Hanan da har farin fuskarta yayi ja dan kuka.
Cikin yarda da kai Binta tace.
"Za tayi shuru Mama zuwa gobe ne, ko babu komai yarinyar nan kamar ƴata take, ya kamata ta sanmu ta saba da mu, balle kuma ina saka ran zame mata uwa gaba kaɗan ba wata bare ba."

"Ni kam ina tsoron abin da zai je ya dawo. Kina sane fa matar nan mun nuna mata hakan tun farko ta ƙi balle shi Awwab ɗin."

"A baya kai tsaye muka je mata. Yanzu kuwa shigo shigo ba zurfi zamu musu. Dan ba zan taɓa barinta ta tashi gurin wata wacce ita ma bata riƙe tarbiyyar kanta ba."

Jingina kai Mama tayi itama ba za taso hakan ba, domin Binta ta samo musu labarin Nuratu, tun ganin farko da ta mata taji kamar ta santa, hakan ya sa ta kasa zama sai da ta samu sanin wacece ita.
Sun shiga mamaki da ruɗanin jin wacce Dr Awwab ya kwaso, da hakan ya ƙara wutar tsanarta cikin zuciyar Binta da Aunti A'isha har da Mama da ke taya ƴarta farautar zuciyar Awwab.

Gurin Hanan ta nufa ta zauna kusa da ita, duban yarinyar tayi da ba abin da ta ɗauko nasu ko na Nusaiba sai na Dr Awwab. Hannunta ta kama cikin nata ta murza.

"Idan kinyi shuru muka kwana a gidanmu yau, gobe da kaina zan kai ki gidan Auntinki."

"Da gaske?"
Hanan tace tana kallon Binta cike da farin ciki. Ta ɗaga mata kai hakan yasa ta daka tsalle ta rumgume Binta, jin haka itama Binta ta rumgume yarinyar cike da kaunarta.

Da daren ta aika aka sayo mata indomie ta dafa mata da kwai ta ci, ta mata wanka ta canza mata zuwa kayan bacci ta kwantarta kusa da ita suka kwanta tana rumgume da ita.

***

Har ƙarfe goma suna zaune falonta yana aiki yana mata hira sama sama tana amsa masa, abinci da ta sauƙa ƙasa ta dafa nan ta kawo su ka ci ta kwashe komai ta sauƙa ta gyara kitchen da fakon ta dawo. Bacci take ji amma ta ƙi tashi ta bar falon sai ta fara a saman kujeran sai ta farka. Dr Awwab duk yana lura da ita, laptop ɗinsa ya rufe yayi murmushi ya miƙe ya fita. Sai da yayi shirin bacci cikin riga da wando mai laushi fari tas, kafin ya dawo falon yadda ya barta haka ya dawo ya sameta. Gyangyaɗi take, ya kashe Tv da wutar falon ya isa gurinta ya ɗagata cak ya nufi ɗakinta.

A mutuƙar tsorace Nuratu ta buɗe idanunta jinta a sama, ta riƙo Dr Awwab a tsorace.
"Zan faɗi Doctor, ka sauƙe ni."

"Not now Babyna."
Yace da ta ita, bai tsaya a ɗakin ba ya wuce bedroom ya ajiyeta. Zip din rigarta ya fara zugewa ƙasa.

"Ki yi wanka ki fito ina jiran ki, ko in miki da kaina."

"Wallahi zan yi da kai na."
Tace tana riƙe hannunsa.

Yayi murmushi ya fita, kayan jikinta ta cire tayi wanka ta ɗaura towel ta leƙa kanta ta gani baya ɗakin. Da sauri ta fito ta isa gurin wardrobe ɗinta ta ɗauki rigar bacci, tana ƙoƙarin sawa ya shigo. Kamar ta fasa ihu musamman da taga ya nufota, tayi saurin ja baya daidai ya iso ta jingina da jikin wardrobe ɗinta. Rankwafowa yayi saman fuskarta ya goga hancinsa saman nata.

"Na lura rowar kan ki za ki mini yau ma."

Dr Awwab yace ya karɓi rigar hannunta ya ajiye gefe, ya saka hannu ya ɗauketa cak zuwa gado ya kwantar da ita. Wutan ɗakin ya kashe ya dawo saman gadon kafin ya jawota jikinshi.

"Menene kuma Babyna."

Faɗin Dr Awwab yana ƙoƙarin warware towel din jikinta ta riƙe.

Nuratu kamar tayi kuka har lokacin ta ƙi sakar masa towel ɗin tace.

"Ni wallahi akwai wahala ga gajiya."

Dariyar da Dr Awwab bai yi niya ba yayi ya sake towel ɗin ya ɗaura kansa saman kirjinta yace.
"Za ki saba Babyna, duk na lokaci ne. Kin cika ragwanta wallahi."

"Ni dai dan Allah..."

Tace cikin rawar murya da tsoro, wahalar da ta sha kawai take tunawa.

Bai bari ta ƙarasa maganarta ba ya rufe mata baki da nashi ya fara kissing ɗinta tare da aika mata sakwanninsa. Shuru ta masa tana jinsa a haka ya samu nasarar rabata da towel ɗin duk tana jinsa ta kasa hanashi, luf tayi tana jinshi yana aika mata manya manyan sakwanninsa da suka fara samun guri suna zama cikin ƙwaƙwalwarta da gangar jikinta.

Duk ɗaga ƙafar da Dr Awwab yake yiwa Nuratu da hakurin da ya mata daren ranar sai da ya fanshe abinsa. Nuratu duk ta gaji sosai sai da fara masa magiya da kukan gajiya kafin ya kyaleta ya rumgumeta tare da saka mata albarka. Ya bata wahala sosai tamkar ranar can.
Ba zai iya wanka bai tsarkake jikinsa ba, hakan yasa ya ɗaga Nuratu ya ji ta sakar masa jikinta, ya kunna wutar bedside drower ya ga tayi baccin wahala sai numfashi take fitarwa. Kwantarta yayi ya shiga bathroom ɗinta ya tsarkake jikinsa ya fito ya cire bedsheet ya canza ya mayarta kan gadon ya kwanta bayan ya musu addu'ar bacci.

Kissing ɗin forehead ɗinta yayi ƙasa ƙasa yace.
"Kin cika ragwanta Babyna."

...

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE (Haske) 50.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

"Wai yau ba za kaje gaishe da Ummi ba ne?"

Murmushi Dr Awwab yayi yana bin Nuratu da kallo yayin da take kwashe kayan da su kayi breakfast, ta masa wannan tambayar.

"Yau kallonki zanyi ta yi, babu inda zan je."

Murmushi Nuratu tayi tana tura baki ta wuce kitchen ta barsa zaune, fara wanke kwanukan tayi ta ji shigowarsa, juyawa tayi ta kalli bakin ƙofar yana tsaye ya zuba mata ido, kanta ta ɗauke, wannan kallon dai yau ya fara takura mata.
'Mutum ko motsi yayi idonsa a kanka.'
Ta faɗa cikin ranta tana tura bski gaba.

Ganin ta juya ya saka Dr Awwab ƙarasawa inda take tsaye. Tana jinsa dalilin ƙamshin turarensa da ya ƙara ƙarfi yake shiga kofofin hancinta.
Ba zato ta ji ya rumgumeta ta baya tare da saka hannuwansa ya riƙe kugunta, hakan ya hana Nuratu ci gaba da aikinta ta dakata, yaar taji tare da wani sabon abu yana bin jinin jikinta. Idanuwanta ta lumshe ta buɗe cike da shauƙi da bata san ya ɗebeta ba. Baya tayi ta kwantar ksnta sanan kirjinsa.

"Zan je wajen Ummi me zan faɗama ta."
Ta tsinci muryar Dr Awwab yana mata magana daf da kunnuwanta. Sake lumshe idanuwanta tayi ta buɗe murya can kasan makogoro tace.

"Ka gaisheta, ka taho min da Hanan."

"Ok My Sweet Baby."

Dr Awwab yace bayan ya ba ta kiss a tsakanin wuyanta ya saketa, dukkansu biyun suka sauƙe ajiyar zuciya a tare. Kasa tsayuwa Nuratu tayi ta dafa sink tana jinsa ya fita. Ta rasa me yasa duk lokacin da ya mata haka neman nutsuwar ta take ta rasa. Da kyar ta daidaita nutsuwarta ta ci gaba da aikinta tana maganganun zuci.

In ance za tayi sure ta samu farin ciki a rayuwarta baza ta taɓa yarda ba. Ta san dai bata son Dr Awwab a kayi aurensu ko tace ba ta da masaniyar hakan, amma gaba ɗaya ya fara canza mata ra'ayin zuciyarta. Ba ta taɓa tsammanin irin karɓar da Dr Awwab zai mata ba kenan a matsayinta na matarsa, shi yasa take tsoron kasancewa matar aure a rayuwarta. Ita ko da mai za ta saka masa bayan ta basa farin ciki kamar yadda yake sakata, ta basa komai da ta mallaka.

...

Gidan Ummi kai tsaye Dr Awwab ya wuce dan gaishe da ita ya kuma ga ƴarshi. Falon shuru ƴan biki sun watse kowa ya tafi. Sallama yayi har sau biyu kafin Hussaina ta amsa ta fito a kitchen.

"Babu kowa ne?"
Ya tambayeta bayan ya amsa gaisuwarta.

"Ummi tana ɗaki."

"Ina My Love?"

Da mamaki Hussaina tace.
"Hanan?"

"Eh ko tana tare da Hassana."

Tsoro ne ya ziyarci zuciyar Hussaina ganin ya juyo gaba ɗaya da hankalinsa kanta, ya kafeta da idanuwansa masu tsoratasu. Masu hana ƴan mata rashin juran gani.

"Ke nake tambaya?"
Dr Awwab yace yana haɗa giran sama da ƙasa ganin kamar bata da gaskiya.

Hussaina da idanuwanta sun cika da hawaye da ƙyar ta buɗe baki tace.
"Ba tana gidanka ba. Aunti Binta ta ɗauketa da kayanta jiya tace za ta kaita gurinka."

Mari ya kwasheta da shi yana nunata da yatsa.

"Are you mad Hussaina? Za ki bar mini yarinya da wannan matar? Ni na faɗa miki ta kawota ko wani ya saka ki."

Hussaina da hawayen idanunta sun samu zuba jikinta na rawa tana dafe da kumatunta, ganin ran yayanta ya ɓaci tana girgiza kai tace.
"Tace mini Ummi ne ta barta su tafi tare. Wallahi bani na sakata ba."

"Rufe min baki wawiya kawai."
Dr Awwab cikin ɓacin rai yana yin kanta zai daketa yaji an ƙira sunanshi.

"AWWAB."

Juyawa yayi ranshi a ɓace ya ga Ummi tana sauƙowa, dan tsawan da yake dakawa Hussaina ya sauƙo da ita. Bayan ta iso ta zauna ta dube shi tace.
"Zauna Awwab. Hussaina je ki ɗaki."

Da sauri ta bar gurin tana share hawayenta. Ummi ta juya wajen Dr Awwab da ya zauna ya dafe goshinsa da hannunshi.

"Lafiya kuwa?"
Ya ji tambayar Ummi ya ɗago kanshi idanuwansa har sun kaɗa.

"Ummi ƴata zan je in ɗauko, ba zan iya barinta wani gurin ba, bata saba da kowa ba sai mu, ta ya ya zata iya rayuwa da wasu bayan mu. Wai ma wa ya bada izinin tafiya da ita."

"Koma ka zauna."
Ummi tace ganin ya miƙe tsaye bayan gama maganarshi. Tasan ɗantan yana da sanyi amma idan ransa ya ɓaci fa yana ɗaukar zafi sosai, kuma duk abin da ya zo ransa aikata maka yake.

Dole ya koma ya zauna dan jin mai Ummi zata faɗa masa. Ganin ya zauna ya sata sauƙe numfashi.

"Ka nutsu ka saurare ni Awwab. Nusaiba ya zame mata dole ta saba da dangin mahaifiyarta, dole ta sansu ta shiga cikinsu. Dan haka ni ban ga abin damuwa ba dan Binta ta ɗauki Nusaiba ba, suma suna buƙatar zama da ita suna buƙatar kasancewarta kusa da su. Ka barta ta kwana biyu gurinsu, idan ya so sai ka ɗaukota ka. Ka ji mai nace? Ban yarda ka ɗaukota ba sai ta kwana musu biyu."

"Na ji Ummi."
Dr Awwab kawai yace ya miƙe ya fita a gidan gaba ɗaya. Da kallo Ummi ta bishi tana mamakin halin Dr Awwab da kwata kwata baya son dangin Nusaiba. Ko dan abin da ya faru a baya ne Oho.

***

Bayan sun tattauna bisa lamarin da kullum sai sunyi akai. Mami ta sauƙe ajiyar zuciya tana canza wayar zuwa kunnen damarta tana cewa.
"Shikenan Yaya ka gaishe da ƴan gida na gode. Hafiza sai ta kwana biyu zata dawo, kuma ka shirya akwai waɗanda ta turo wajenka ɗan Babar su Rahma ne, na sanshi na san halinsa, kar ka damu da wani binciken sanin halinsa ɗan gida ne."

Fara'a ɗauke saman fuskar Kawu Muhammadu ta ɓangarenshi ya amsa da.
"To Masha Allah, haka Allah yake abunsa, Allah kawosa lafiya."

"Ameen ya Allah."
Mami ta amsa da shi tana kashe wayar hannunta ta ajiye cike da jimamin wannan lamari, gefe daya kuma na zuciyarta lamarin Al'ameen da Hafiza yayi mata daɗi sosai. Ko ba komai za ta fita a kunyar Amma Jidda.

***

Cikin fushi ya shigo gidan baya ko ganin gabansa. Da sauri Nuratu ta miƙe dan taranshi.
Bayan ta gama ayyukanta tayi wanka ta yi kwalliyarta da haka kawai ta ji tana son ma Dr Awwab ya gani, cikin riga gown da ya bi jikinta ya fito da dirinta kalar purple, ba tayi wani kwalliya a fuskarta ba sai turare da yake tashi a jikinta.
Kafin ta kai ga ƙarasawa wajenshi ya haura sama ko ta kanta bai bi ba. Da kallo ta bishi baki buɗe tana jin sanda ya buga ƙofar ɗakin da ƙarfi har zuciyarta sai da ya tsinke.

Cikin sanyin jiki ta koma ta zauna tana mamakinsa, tun da suke ko tunda ta sanshi ba ta taɓa ganin ɓacin ransa haka ba. Sanyin halinsa ba zai taɓa baka cewa yana da fushi ba.

Har ƙarfe biyu bai fito ba bai sauƙo ba, dan a cikin ɗaki yayi sallah ya ci gaba da kwanciyarshi yana tunanin halin da ƴarshi take ciki.
Ba ta saba da su ba, ba ta saba da rayuwarsu ba, yana tsoron ta ga wani abun da sam bai dace ta gani ba a gurinsu, domin shi yasan su yasan su waye su. Yana tsoron su cutarta kamar yadda suka ma mahaifiyarta.

Ganin shuru ba shi da alamar sauƙowa kasa da ƙyar Nuratu ta iya yin jarumta ta nufi ɗakinsa dan ganin lafiya jin shurun yayi yawa. Falonsa a buɗe hakan yasa ta shiga cike da tsoro, baya nan ta nufi bedroom ɗinshi. Ƙofar ta taɓa a hankali ta ji a kulle tayi knocking.

Dr Awwab kallonshi ya kai kan ƙofar sai lokacin ya tuna halin da ya bar Nuratu, wani tausayinta ne ya kamasa. Da sauri ya miƙe ya buɗe ƙofar, tana tsaye jin an buɗe ƙofar ta ɗago kanta suka haɗa ido. Tsorone ya ƙara shiga zuciyarta ganin har yanzu ranshi a haɗe.

Ganin ba ta da niyar magana ya sashi barin ƙofar ya koma ya zauna bakin gado. Da ƙyar Nuratu ta ja ƙafarta ta shiga ciki, a bakin ƙofar ta tsaye ta kasa ƙarasawa wajenshi. Ta wutsiyar ido ya kalleta duk a tsorace take da shi, zai ce ma tamkar jikinta rawa yake.
Rai ya ƙara haɗawa ya kalleta ganin bata da niyar cewa komai yace.

"Ke zo nan."

Hannunta har rawa yake ta nuna kanta cikin rawar murya tace."
"Ni!..."

"Ke mana, zo nan."
Yace yana ƙara haɗa rai tamkar ba shi ba.

Idanuwan Nuratu ne suka cika da kwalla ganin zai huce a kanta da bata san me ya ɓata masa rai ba. Da ƙyar ta ja ƙafarta ta ƙarasa wajenshi kanta ƙasa, durkusawa za tayi ya saka hannu ya ɗagota tsaye. Kallonta yayi dressing ɗin jikinta ya mutuƙar masa kyau. Da ya shigo cikin daɗin rai da ya yabi kwalliyar, amma ko yanzu dole ya biyata.

"Zauna mana."
Yace da ita, da sauri ta ƙarayin ƙasa za ta durƙushe ya saka hannu ya tarota ya zaunarta kusa da shi. Jikin Nuratu mugun rawa yake ta ji yace.

"Kalle ni."

Idanuwanta ta dago da suke cike da ruwan hawaye ta kallesa da su suka haɗa ido. Rana na farko da ta kasa janye idanunta cikin nashi. Murmushi ta gani kwance saman fuskarshi ya daura hannunshi saman fuskarta ya shafa.

"Kar ki mini kuka, in kuma ba haka ba yanzu in saka ki kuka mai dalili."

Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta, bayan ta watsa mishi harara ta ɗauke idanuwanta cikin nashi ta fara ƙoƙarin tashi. Awwab ya saka hannu ya fizgota ta faɗo jikinshi ya riƙeta sosai, hannu ya saka ya tallafo fuskarta da hawayen idanunta suka zubo ya fara share mata yana cewa.

"I'm sorry My Sweet

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login