Follow us on social media

Showing 9001 words to 12000 words out of 148866 words

Chapter 4 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

7

biyun kam tama fara mance kamarsu dan tun kafin aurenta suka bar ƙasar.

Dawowarta da sati ɗaya ta saro kaya masu yawa daga atamfofi, kayan yara, da takalma. Yau aka kawo mata kayan cikin falonta ta baza tana kallo tana ware masu tsadar da mai ƙaramin kuɗi.
Gefenta Nuratu tana wasa da kafafunta, yarinyar ƴar wata huɗu tayi wayo abinta, duhu take yi yarinyar irin na mahaifinta dan bata biyo hasken yayunta da suka ɗauka na ta ba, amma kallo ɗaya zaka mata kasan tafi su kyau duk da jaririya ce, irin baƙaƙe masu kyau ne da ake ƙira chocolate beauty.

Sallama taji daga waje cikin baƙuwar murya fita tayi tana leƙawa taga mace da zata haura shekaru talatin gefenta yaranta ne Muhsin da Rahma da Hasiya tana ɗauke da Rukayya data maƙale mata.

Ihu Rahma da Hasiya suka saka ganin Mamin su suna yin kanta da gudu ta rumgumesu cikin farin ciki tana miƙa Muhsin hannu alamar yazo ya tsaya yana son tuna inda ya santa, sai da tace.
"Muhsy na babana."
Kafin yaron ya kwace hannunshi cikin na Amma Jidda ya faɗa kan Mamin shi.

Murmushi kawai Amma Jidda take ganin burinta ya fara cika, ganin uwa da ƴaƴan sun haɗu ta dalilinta.

"Sannu da zuwa."

Mami tace tana miƙewa tsaye ganin ta barta tsaye. Murmushi kawai tayi ta girgiza mata kanta tana miƙa mata Rukayya, yarinyar taƙi zuwa.

"Ki barta kawai ta jima ne, a hankali zata tuna ni. Mu shiga ciki."

Bayan sun zauna yaran suka nufi gurin Nuratu Rahma ta ɗauketa Hasiya na ƙoƙarin karɓar ta.

"Zaku jefar ta ai. Kawo ta nan mu ganta."

Yaran basu so ba suka miƙa Amma Jidda ita ta karɓeta tana gani, Rukayya dake gefenta itama ta zauna alamar a bata yarinyar.

"Mami waye ce?"
Cewar Rahma tana leƙa fuskar Nuratu.

"Ƙanwar ku ce, sunanta Nuratu."

"Allah rayata, bamu samu zuwa ba sai yanzu."
Amma Jidda tace.

"Ameen, sai dai har yanzu ban shaida ki ba."

Shuru Amma Jidda tayi ta rasa ta ina zata sanar da ita hakan ya bawa Mami Sadiya gaskata abinda yazo ranta.

"Auntyn su Rahma."

Kai Amma Jidda ta ɗaga tace.
"Tun da naji labarin rabuwar ku hankalina ya kasa kwanciya, wallahi kinji na rantse ban aure Abban su ba dan ina son shi sai dan in haɗa kan zuri'ar ku. A rayuwata ina tausayin ya'ya da mahaifiya take barinsu ta fita. Tun bayan da ki kayi nesa dasu Rahma, bayan kwana biyu sai Aunti Zarah tazo ganinsu ko kin sani ko a'a, kwana biyu bata zo ba sai jiya, shine na tambayeta gidanki dan ina kawo miki yaran kuna samun lokaci kuna gaisawa da juna, kar gaba sun girma su manta dake musamman yanzu Rukayya da take ƙarama zata iya mantawa da komai daya shafe ki, hakan kuma ba zai min daɗi ba.
Munyi magana da Abban su yace min yazo kunyi magana amma abun bai yi ba, sam banji daɗi ba, dan Allah Mamin Rahma kiyi hakuri ki koma kan ya'yan ki, ki duba yadda su kayi kewan ki, suna buƙatar ki kusa dasu."

Tabbas in har yadda Amma Jidda ta nuna mata tana son ƴaƴanta har cikin ranta ne to ta yarda ko bayan ranta zata kula mata dasu. Gashi nan taga alama yadda suka sake da ita, da bata basu fuska ko kusa ba za su zo inda take ba balle har tayi tunanin kawo mata su.

"Dan Allah Mamin su kiyi tunani akai."

Sai lokaci Mami Sadiya ta buɗe baki.
"Kiyi hakuri amma zama ya ƙare tsakani na da Alhaji Mamman. Ga yarana na baki amana kici gaba da kula dasu, duk lokacin da kike so zaki iya kawo su in gansu bazan takura miki ba."

"Dan Allah kar kice haka ki duba yaranki."
Amma Jidda tace alaman roƙo. Mami Sadiya ta duba yaranta da sun zagaye Nuratu da take cinyar Amma Jidda hatta ɗanta Al-ameen da ido kawai ya zuba mata yana kallonta.

Tana son kasancewa tare dasu har girmansu da aurensu amma abinda mahaifinsu yake so ba za tayi ba. Gwara su su rayu da mahaifinsu da ta kai Nuratu gidan marayu ta girma.

"Ba zai yiwa, kici gaba da kula dasu ɗa na kowa ne."

Shuru Amma Jidda tayi ta rasa mafita, Mami Sadiya ta miƙe ta kawo musu ruwa da abinci data girka dan kanta. Sun ci sosai yaran anan Rukayya ta sake jikinta ta shiga cikin su, tun tana bin Mamin ta da ido har ta ganeta ta fara binta duk inda za taje haka Muhsin ma dama shikam ta saba.

Abin yayiwa Amma Jidda daɗi ganin yaran sun sake da mahaifiyar su shiga su fita tare. Awansu huɗu suka fara shirin tafiya. Anan Mami Sadiya ta ɗauka yarantan takalma iri ɗaya gaba ɗaya da kayan yara kala ɗaɗɗaya.
Rahma, Hasiya, Rukayya nasu iri ɗaya sai na Al-ameen da Muhsin iri daya. Duk yadda Amma Jidda ta hanata ƙi tayi tace su riƙe.
Godiya su kayi tayi yaran suna murna.

Sai da aka zo wajen tafiya suka ce sam sai sun tafi da Nuratu, Rukayya har da kukanta akan a bar ta, dakyar dai aka shawo kansu su ka tafi gida bayan alƙawarin ƙarya da aka musu zasu zo gobe.

Mami taji daɗin ganin yaranta, ta yaba Amma Jidda da ƙoƙarinta ganin tana kula da yaranta, ta san zata basu kulawa har girmansu, sai lokacin taji hankalinta ya kwanta.
...

Gidan Alhaji Mamman Bashir.

..

Vote.
Comments.
Share.

MADUBIN GOBE 6.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Littafin MADUBIN GOBE littafin kyauta ne❤️.

...

Gidan Alhaji Mamman Bashir.

Da dare da Alhaji Mamman ya samu labarin zuwan yaran gurin Mami Sadiya faɗa yayi tama Amma Jidda da abin ya bata mamaki har tana cewa.

"To wai naga mahaifiyarsu ce, taya zaka rabasu, duk yadda kayi fa ɗa baya gudun mahaifiyar shi."

"To ki kiyaye ni, na faɗa miki kar ki ƙara kai su tunda ita taƙi bin shawarar da na yanke ta rabu dasu."

Shuru kawai ta mishi tana juyar kanta, haushin maganganun shi take ji. Sannan ƙasan ranta tana son sanin menene Alhaji Mamman ya nemi Mami Sadiya taƙi yi har ta ke ganin gwara ta bar yaranta.

Fushin kwana biyu yayi ya sauƙo dan tace ba zata sake kai su ba amma tasan ƙarya ta mishi kawai dan ya daina fushi da ita.

....

Tun daga ranar Amma Jidda a ɓoye take kai yaran gurin Mamin su shima sai a hutun ƙarshen mako. Sannan ta gargadesu karsu ƙara sanar da Abban su.

Mami Sadiya tana jin daɗin haka dan yana ƙara mata shaƙuwa da yaranta haka kuma da yar uwar su Nuratu da in ta gansu ta dinga miƙa hannu su ɗauketa dan ta gane su.
Mami Sadiya tana ƙoƙarin kyautata Amma Jidda dan yadda ta riƙe mata ƴaƴa, kullum sai ta mata godiya sai dai Mami Sadiya tayi murmushi tace ta daina gode mata.

"To wai so kike duniya ta zage ni ace na raba uwa da ƴaƴanta, a'a ni kam bana so gwara ki zama shaidana ko da an zage ni."

Murmushi kawai Mami tayi tace.
"Bama mai zagin ki sai yabon ki."

Aunti Zarah da ta samu labari itama tayi farin ciki tana yabawa Amma Jidda dan da wuya a samu matar uba mai irin halinta.
A cikin haka Amma Jidda ta haifi ƴarta nace mai sunan mahaifiyarta tana ƙiranta Walida

****

Bayan shekaru goma.

Abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwar su da suka saka shi cikin kundin Ƙaddarar su.
Yara sun girma su Rahma sun girma shekara goma sha huɗu ba wasa ba, Hasiya mai bi mata da ita suna aji uku na sakandare, Muhsin yana ajin ƙarshe na Firamare sai Nuratu da Walida ajinsu ɗaya suna aji huɗu sai Rukayya data fi su da aji tana aji biyar, Muhammad Al-ameen ya wuce makarantar gaba da sakandare wato digiri a garin Zaria wajen dangin mahaifin shi da yake zama a can gaba ɗaya ya koma.

Tun lokacin da Nuratu ta isa shiga makaranta Amma Jidda ta haɗa da Nuratu ta sakata tare da ƴarta Walida. Mami tayi mamaki dan tana da burin sakata makarantar sauran yaran sai gashi ta shammace ta. Godiya ta mata tace sai ta bari za taci gaba da biya mata kuɗin Amma Jidda tace babu komai.

Yaran sun shaƙu da juna musammam matan, Rahma, Hasiya, Nuratu da Walida, duk ƙanƙantar su baka bambanta ya'yan waye.
Tun lokacin da Rahma da Hasiya suka fara girma suka fahimce Mami da Abban su basa tare.

Kasuwanci da Mami Sadiya take yi Allah ya sanya masa albarka sai bunƙasa yake, gidan da take ciki ta sayeshi dukka a hannun mijin ƙanwar Zarah ya zama halal ɗinta, ta ƙara gyarashi. Tsakanin ta da Zarah har yanzu suna mutumci.

Alhaji Mamman kuɗi ya zauna masa sosai, kasuwanci ya buɗe, Company sai samun cigaba yake, hankalinshi kwance yake rayuwarshi ya riga ya mance da wata Sadiya balle ƴarta da har yau bai san sunanta ba ko kamanninta.

Shekaru na ta tafiya abubuwa na ta faruwa, wani da daɗi wani babu, wani mai kyau wani marar kyau, shekaru sun ja kwanaki sun wuce sun zama satikai, sati ya shuɗe ya zama watanni.

....

Leaders Private School.

Makaranta da yayi tashe ake ji dashi a cikin garin Damaturu jihar Yobe.
Yaye ɗalibai ake na ajin ƙarshe da suka kammala karatunsu suka fita da sakamako mai kyau. Ciki har da Rahma da Hasiya da suka gama tare.

Sunyi kyau abinsu sai murna suke zasu kammala sakandare, Rukayya Nuratu da Walida da suma sun zama ƴan mata sai murna suke ganin yayunsu musamman Nuratu data kasa rufe bakinta murmushi kawai take zubawa da yake saka kumatunta lotsawa yake ƙara fito da kyan fuskarta.

Taro a kayi sosai da hotuna Alhaji Mamman yazo shi da Amma Jidda, ana zuwa yin hoton iyali dukka suka haɗu waje ɗaya har Nuratu. Bayan an ɗauki hoton Alhaji Mamman yana lura da Nuratu da duk inda yaran su kayi tana binsu tare suke.

"Wacece wannan? Kawar ku ce?"
Ya tambayi yaran.

Kafin Amma Jidda tayi magana Rukayya tace.
"Ƙanwar mu ce fa Abba, ta gidan Mami."

Kallonta yayi sosai baƙace bata da hasken fatar sauran amma tafi su kyan fuska sosai. Sai lokacin ya kalli kamannin Mami Sadiya a fuskarta dan sauran da shi suke kama ban da Rahma da itama da Mami ta ke kama hatta farin fatarta na Mami Sadiya ne.

"Ke zo nan!"
Yace a tsawace yana haɗa rai.

Nuratu da ta san da ita yake ta tashi ta taho gurin shi ta tsugunna kanta ƙasa.
Rankwashi ya kai mata da taji zafin shi har tsakar kanta tana sosa gurin idonta cike da hawaye.

"Menene haɗin ki da yarana, baki da alaƙa dasu ko kaɗan dan haka ki daina binsu kar ki shafa musu farar ƙafa. In ma uwarki ta turo ki kije ki sanar da ita haka. Idan na ƙara ganin ki dasu sai na ɓata miki rai. Tashi ki bar min guri."

Sum Nuratu ta miƙe ta bar gurin tana share hawayenta. Bata san mai ta mishi ba tun tasowarta ta nemi sanin wanene shi Mami ta kasa sanar mata sai ita da kanta ta san matsayin shi gareta. Yau kaɗai ta fara ganinshi duk yadda suke faɗan sunan Abban su amma ya faɗa mata wannan maganar.
Lokacin data fara tasowa ta ɗauka mahaifinta daban sai da tayi wayo ta gane suna duk iri ɗaya suke amfani dashi na uba. Data tambayi dalili Maminta ta sanar da ita shine mahaifinta tace mata eh ta kasa sanar da ita dalilin da yasa baya basa tare ko bata tare da ƴan uwanta. Duk yadda take son zuwa gidan su Rukayya hanata Mami take sai dai su suzo wataran har kwana suke in Abban su yayi tafiya.

To ita kuwa mai tama Abban su ya tsaneta. Mai yasa ba'a barinta taje gidan itama kamar sauran yayunta tunda shine Abban ta.

Cikin class ta shige tana cigaba da kukanta ba wanda ya biyo bayanta domin a gaba Abban su ya sasu ya musu faɗa sosai akan su daina mu'amala da ita ƙarshe ma ya ɗauke su suka wuce gida kowa yana tunanin halin da ya bar Nuratu. Amma Jidda tafi kowa shiga damuwa dan gani take bata kyauta mata ba, tare ake ɗaukarsu a sauƙeta a gida kafin sauran yaran. Bata san ta ya zata tafi gida ba yau.

Nuratu kam kukanta tasha har aka fara watsewa ta leƙo ganin wasu har sun fara tafiya ya sata fara duba su Rahma, duban duniya tayi bata gansu ba ta hakura ta zauna zaman jiran azo a ɗauke su. Har aka gama watsewa babu alamar su Rahma.
Nuratu duk tsoro ya kamata sai lokacin tunanin kar fa Abban su ya ɗaukesu yazo kanta haka ta miƙe ta fara tafiya. Tafiya nisa tsakanin makaranta da unguwar su. Haka taci tafiya sai wajen huɗu saura ta isa.

"Lafiya kika daɗe haka?"
Mami ta tambayi Nuratu da isowarta ta kwanta mata shame shame a ƙasa.

"Da kafa na dawo Mami."

"Da kafa dai? Ina Amma ɗin? Ko bata je ba."

"Amma taje tare da Abba, Mami yau naga Abban mu dasu Aunti Hasiya yake kama. Mami wai mai nama Abba ne? Ban taɓa kallon shi ko mishi magana ba, sai yau muka haɗu amma bai tare ni ko kallona a matsayin ƴarshi ba sai hantara da faɗa. Anya Mami shine mahaifina? In kuma shine mai na mishi haka ya tsane ni?"

Mami da take sauraron Nuratu ta gama maganarta kafin tace.
"Shi ya haife ki kamar sauran, wani camfi nashi can ya haddasa mishi tsanar ki, amma ba komai kar ki damu komai zai wuce ki zame masa MADUBIN GOBE. Dalilin da yasa ma bana son kije gidan su Rahma na san hakan zai faru, kinga kuwa yanzu sai ki kiyaye."

Kai kawai Nuratu ta ɗaga tana son fahimtar maganganun Maminta ganin haka Mami ta miƙe tana cewa.

"Kar kisa damuwa a ranki ko tunani, ki tashi kiyi sallolin daya same ki a hanya."

Tashi tayi tayi sallah taci abinci kasa aikin komai tayi dan ciwon kafa daya fara damunta. Da dare sai da Mami ta mata gashi da ruwan ɗumi dan ciwo ta shafa mata man zafi.

Tun daga ranar Nuratu ta kauracewa duk abinda zai haɗata da Abban ta dama ba su taɓa haɗuwa, har lokacin ƙasan ranta tana son sanin dalilin da yasa ya tsaneta.
Tsakanin ta da ƴan uwanta sai dai su zo dan an bada hutun makaranta kuma islamiyya ba ɗaya suke ba.

Alhaji Mamman duk shekarun da aka ɗauka ya tsammaci Amma Jidda taji maganar shi sai yau da ya saka yaran gaba yana musu faɗa tace ita take kai su ba laifinsu bane. Faɗar da ya mata har yana mata barazana da igiyar aurenta ta tsorata sosai ta bashi hakuri.

****

Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta da ake shi ya farkar da ita daga tunanin abin da ya shuɗe ta sake labulen window ɗakin ta juya tana bada izinin shiga.

Nuratu ne ta shigo ɗakin cikin sauri fuskarta alamun damuwa.

"Menene kuma?"
Mami ta tambaye ta.

"Mami Aunti Hasiya ba lafiya tana asibiti. Yanzu Aunti Rahma ta sanar dani."

"To ko dai labour ne."

"Ni ma shi nake tsammani. Dan Allah muje mu dubata."
Nuratu tace kamar za tayi kuka.

"To ɗauko mayafinki muje."

Ai bata jira Mami ta gama magana ba ta fita da sauri, a falo ta tarar Mami suka fita. A motar Mami suka tafi, ita take jan motar Nuratu a gefe ta buga uban tagumi. Wayarta yana ta ƙara ta kasa ɗauka.

"Ba ki ji ana ƙiran ki ba ki ɗauka mana. Haihuwa na biyu fa, ni ba dan ke ba maa ba zan zo ba, in ta haihu na je."

Kallon fuskar wayar tayi taga Dr Awwab ne yana ɗaya daga cikin mutanen da suke da muhimmanci a rayuwarta. Kasa ɗauka tayi ta tura mishi saƙon zata ƙira shi anjima ta kashe wayar. Bai ƙiranta ba bayan ya karanta saƙon.

Bayan sun isa asibitin sai kuma ta kasa shiga.
"Muje ko."

Taji Mami tace ta girgiza kai tana kama jikinta waje ɗaya, fahimtar haka ya saka Mami cewa.

"Ki kwantar da hankalin ki babu komai, muje."

"Ba zan iya shiga ba Mami."
Nuratu tace da taji kanta yana neman juyawa, anan asibitin wasu abubuwan suka faru da ba zata iya fahimtarsu ba a lokacin balle yanzu.

"Ke fa kika dame ni muzo."

"Mu koma gida kawai."
Tace tana kwantar kanta ta rufe idanunta zuciyarta yana bugawa da sauri sauri, tsoro ya fara shigarta kamar kullum in ta tuna ko tayi tozali da abun da ya shafe rayuwarta na baya.

Shurun mintuna biyu Mami tayi tana dubanta hakan yasa ta kasa shiga ta kasa komawa gida. Wayarta ta ciro ta ƙira Aunti Rahma take tambayarta tazo, Aunti Rahma ta sanar da ita Hasiya ma ta haihu tun ɗazu an sallamesu yanzu zasu wuce gidanta ba sai tazo ba.

Bayan sun kashe wayar Mami taja motar suka bar harabar asibitin. Sai da ta hau titi tace.
"Nuratu buɗe idonki mun bar asibitin."

Sai lokacin ta ji hankalinta ya fara kwanciya ta buɗe ido tana kallon titi. Mami ido kawai ta zuba mata lokaci zuwa lokaci ganin yanayinta ya canza.

Har yanzu ta kasa cire abinda ya faru a ranta, tasan dama da wuya hakan ya kasance, tayi ƙoƙari ma na ganin ta dawo da walwalarta kamar baya duk da wani lokacin tasha kamata cikin tunani ko damuwa. Girgiza kai tayi cikin ranta tana mata fatan ƙarin lafiya.

....

Vote.
Comments.
Share.
MADUBIN GOBE 7.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

....

"Nuratu?"

Da kyar ta buɗe idanunta da suka fara canza launi ta dubi Mami dake zaune gefenta bayan sun shigo gidan ta zube saman kujerun falon tayi kwanciyarta.

Hannu Mami ta saka ta kamo hannuwan Nuratu da ta bita da ido.

"Bana hana ki saka damuwa a ranki ba, bana son ciwon ki ya tashi dan Allah ki daure ki kawar da komai a ranki, ki duba halin da muka shiga dalilin haka, Nuratu in bana ganin dauriya tattare dake bana jin kwanciyar hankali a rayuwa ta, sai in ga har yanzu baki gama warkewa ba. Duk da nasan kina ƙoƙari, ki daure ki ƙara. "

Mami ta ƙarasa maganar cikin ƙarayar murya.

Murmushi Nuratu tayi ta damƙe hannun Maminta.
"Mami kai na yake ciwo, amma babu komai."

"Shikenan to tashi muje ganin babyn Hasiya, waya sani ma ko sabon miji na samu."
Mami tace tana dariya dan kawarwa Nuratu damuwarta.

Itama dariyar Nuratu tayi tana ƙoƙarin danne damuwarta, ta tambayi Mami.

"Sun koma gidane?"

"Eh muje can, in zaki zauna mata zuwa bayan suna sai ki ɗauki kaya."

To Nuratu tace ta miƙe ta shiga ɗakinta ta ɗauki kayanta cikin kits ƙarami ta fito suka fita.

...

Gidan har ya fara cika da mutane suka karɓi baby suna gani, babynta mace kyakkyawa fara tasha kayan sanyi farare. Bayan Mami ta miƙawa Nuratu babyn ta hana kowa karɓa.

Mami bata jima ba ta koma gida ganin su kansu sun isa kula da mai jego, ga Aunti Rahma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login