Follow us on social media

Showing 18001 words to 21000 words out of 148866 words

Chapter 7 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

12

ya gagari kowa, ƙarshe suka koreshi. Abin yayiwa Alhaji Kashim ciwo, amma son Mufid ya rufe mishi ido yace karatu dan a samu kuɗi ake yi kuma yana dashi dan haka yayi zaman shi gida ko nawa yake buƙata zai bashi, haka ya cigaba da zama a gida yana bashi kuɗi ko nawane, ya yi abinda yake so daga mahaifinshi da mahaifiyarshi.

Ranar da suka samu Mufid yana shan sigari sun mishi faɗa sosai daga baya suka watsar abun cewa wataran zai bari. Amma abin sai gaba yake.
Ƴan mata kuwa yaudaran su kawai yake babu na aure, baya soyyaya da mace sai soyayyar shan minti ya samu ya rage zafi zai watsar dake.

...

Da safiyar Rufaida ta fito cikin shirin makaranta ƙarfe tara sai sauri take dan ta kusa latti.

"Ummu na tafi."
Tace tana ɗaukar bottle na ruwa tayi hanyar waje.

"Tsaya na sauƙe ki."
Mufid da yake zaune ya miƙe tsaye.

Rufaida da Hajiya Hindatu su ka kalleshi yayi tamkar bai gani ba ya fita, Rufaida bata so ba haka ta shiga motar shi ya ɗauke ta.

Kunya take ji a ganshi a matsayin yayanta, wani shegen three quarter ne a jikinshi da riga body hug daya kama shi, kanshi wani arniyar aski.
Mufid farine kyakkyawan saurayi bafulatani ne da kyan ɗan macijine dashi domin babu kyan hali balle na zuciya.

Shuru su kayi dukkan su biyu har suka isa cikin makarantar da sauri Rufaida na ƙoƙarin fita taji yayi magana da ya sakata duban shi da sauri.

"Wacece ita? Menene sunanta?"

"Waye kenan?"
Tace da sauri cikin rawar murya.

"Wacce ki ka je dinner party na auren Sufyan dan ita."

Zuciyarta ne ya buga, ba dai Nuratu yake magana a kai ba.

"Ban gane ta ba."
Rufaida tace tana shirin fita ya daka mata tsawa.

"Zaki faɗa min ko sai na saka ki kinyi missing lecture."

Tana tsoron shi balle ance ɗan Shaye-Shaye da hauka yanzu zai iya kai mata bugu banda abinda ya faɗa ta san zai aikata.

"Sunanta Nuratu Mamman Bashir, class ɗaya muke."

Murmushi yayi da yake ɗauke hankalin mata dashi yace.
"Ko ke fa ƙanwata. Je ki fito ina jiranki zan mai dake gida."

Ya cire lock da sauri ta fita tana jan tsaki ciki ciki. Allah kiyaye a ganta dashi ta zama abin ƙyama.

Nuratu fa? Taji zuciyarta ya tambaye ta. Ba zata taɓa barin shi ya raɓeta ba, dan ta san bada alheri yake nemanta ba. Haka ta ƙarasa aji ta samu Nuratu tazo Fa'iza bata shigo ba, gaisawa kawai su kayi lecture ya shigo aka nutsu ya fara koyar musu.

Bayan fitar shi suka fita dan shi kaɗai ne yau dasu. A in da ta bar motar shi ta ganshi yana ciki yana jiranta.

"Friend sai gobe kin ga ana jirana."
Rufaida ta faɗawa Nuratu, murmushi Nuratu tayi murmushi tace.
"To shikenan ki gaishe da mutanen gida."

"Za suji, bayan har yau kin ƙi zuwa gaishe Ummu."
Rufaida tace tana hararanta.

"Zan zo inshaAllah kiyi hakuri."
Cewar Nuratu tana yin gaba ganin Rufaida ta nufi motar da yake jiranta.

Tayi nisa a tafiya taji horn a bayanta ta juya da sauri taga motar da Rufaida ta shiga cikine. Ido biyu suka haɗa dashi, lumshashshun idanuwansa ya zuba mata.

"Shigo mu rage miki hanya."
Yace mata cikin husky voice ɗinshi.

Nuratu ta kawar kanta gefe.
"Nagode."

Taci gaba da tafiya ya juya ya kalli Rufaida yana mata wani kallo ta fita da sauri a motar ta bi bayan Nuratu.

"Dan Allah sister ki zo muje."

"Kuje kawai friend zan nemi abin hawa."
Nuratu tace tana girgiza kai.

"Dan Allah dan annabi na haɗa ki dashi, haba friend ina rokon ki kamar ni kin ƙi ji."

Ganin ran Rufaida ya ɓaci, roƙo take da take buƙatar yardarta ya saka Nuratu amincewa. Baya ta buɗe ta shiga Rufaida ta shiga gidan gaba yaja motar yana barin makarantar.

Tafe suke shuru a hanya sai kiɗan wani mahaukacin mawaki ke tashi har suka shigo cikin gari.

"Bari mu fara sauƙe ki ko?"
Mufid yace yana gyaran mudubin mirror dan ganin fuskar Nuratu da kyau suka haɗa ido da Nuratu dai-dai lokacin ta ɗago kanta.

Da sauri ta juyar da kanta.
"Ku sauƙe ni kawai a bakin cross zan nemi abin hawa."

"Why? Saboda baki yarda dani ba ko baki yarda da Rufaida ba. Take me as your elder brother."

"Mufid mu sauƙe ta kawai a bakin cross."
Rufaida tace da sauri da tsakaninta da Allah bata son abin da yayanta yake hararowa akan Nuratu.

"Shut up I'm not talking with you."
Yace wa Rufaida a tsawace ta kama bakinta tayi shuru ya maida hankali kan Nuratu.

"Faɗa min unguwar ku."

A hankali ta sanar dashi ya canza hanya suka nufi unguwar, tana nuna mishi har bakin layinsu tace ya sauƙeta yaƙi dole ta nuna mishi har ƙofar gidansu ta sauƙa.

"Nagode."
Ta faɗa tana fita ya bita da kallo yana ɗaga mata kai dan ya kasa bata amsa. Sai da yaga shigewarta cikin gidan yaja motar shi.

Suna isa gida ya faka motar yaga Rufaida bata da niyar fita ya dubeta.
"Fita min a mota, kin gama min amfani."

"Dan Allah Mufid kar ka shiga rayuwar Nuratu in ba da alheri zaka je mata ba, dan Allah na haɗa ka dashi, ita ɗin ba irin sauran bane."

Rai ya haɗa ya tamke fuska.

"Sai akace miki mai zan mata, aurenta zanyi in ajiyeta ina kallo, she's so hot and beautiful baki gani ba."

Girgiza kai tayi cikin jin haushin maganar shi tasan duk abinda yake kai shi gurin mace.
"Ni dai na haɗa ka da Allah, kuma in ka cutarta Allah ba zai barka ba, sannan nima ba zan yafewa kai na ba da nayi sanadin ka santa."

Sauƙar mari taji saman fuskarta ta kasa ƙarasa maganar ta dafe gurin.

"Sauƙa min a mota kar min miki mugun duka."

Cikin hawaye Rufaida ta buɗe motar ta fita tace.
"Allah ya isa na mugu kawai."

Kanta yayi yana niyar fita a motar tayi cikin falonsu da gudu. Ummu da ta ga haka tana tambayarta lafiya ta wuce ɗaki da gudu ta saka lock.

Mufid da ya shigo yaga haka zai bita Ummu ta tare shi.
"Kai lafiya wai?"

"Ummu zan karya yarinyar nan in ballata wallahi in tana min rashin kunya."

"Allah baka hakuri mai yayi zafi."

Kwafa yayi ya wuce ɗakin shi cikin jin haushi. Nuratu take kowa sonta yake kuma aurenta zai yi ba irin son da ya saba faɗawa sauran ƴan matanshi ba yake mata.
Murmushi ya suɓuce masa tunawa da yayi sunyi magana har ya gano gidansu yasan komai zai zo da sauƙi, sai yanzu ya tabbatar ba ƙanwar matar Sufyan bace sai dai yar uwarta ganin gidansu daban..

....

Nuratu da ta koma gida bata sanar da Mami komai ba taci gaba da lamuranta dan dai ta san dalilin Rufaida abu ya haɗata da yayanta.

Da daren yaya Al-ameen ya ƙirata suka sha soyayya yake ce mata ta kusa shiga aji biyu suyi aure dan yaga sauran yayunta duk hakane.

"Tab ai ni sai na kammala tas."
Nuratu tace cike da zolaya.

"Allah ko zamu gani. Burina kullum in buɗe ido in ga kin shiga aji biyu in taso da maganar auren mu shine yanzu zaki kawo kin wani iyayi ko, shekaru biyu fa ƙanwata ki tausaya min mana."

Dariya Nuratu tayi tace.
"Wasa nake maka Yaya amma dai zaka bar ni inci gaba da karatuna kamar sauran yayuna."

"InshaAllah ƙanwata sai kin gaji da kan ki."

Taji daɗin haka su kaci gaba da hira har dare ya tsala kafin su kashe wayar cike da son kasancewa da juna.

***

Hawayen da ya zubo saman fuskarta ta share murmushin zafi da ciwon soyayyarshi yana yawo a zuciyarta.
Taso Yaya Al-ameen kuma har yanzu tana jin abu a ranta game dashi amma ƙaddararta ya rabasu.

Tun daga ranar da ta dawo hankalinta taji maza da duk abinda ya shafe su ta tsana, mutum uku da Yaya Al-ameen na hudu take iya kebewa dasu har ta iya musu magana. Suma ta lura da duk take takensu amma bata jin abinda suke buƙata shine zata saka musu dashi dan karamci da taimako da suka mata a rayuwa.
Kowa da rawar da ya taka a rayuwarta bayan rushewar farin cikin ta.

Miƙewa tayi tai sallar magriba ta fita wajen Mami, duk yanayinta ya canza Mami tana binta da kallo amma bata tambayeta ba. Abinci ma ba taci ba na daren ta musu sallama zata kwanta sai da safe, da to suka bita dashi.
Bayan shigarta ta canza kaya tayi sallar isha'i ta kwanta.

Agogo fuskar wayarta ta kalla taga goma ta gota na dare tayi mamakin wucewar lokaci amma ba tayi mamaki ba dan ta daɗe cikin tunanin abin da ya wuce.

Idanuwanta ta runtse ko zata samu bacci amma kuma tunanin da ta fara ya kasa barinta runtsawa. Ta runtse idanunta da karfi dan jin abinda ya wuce tamkar yanzu yake faruwa.

....

Vote.
Comments.
Share.

MADUBIN GOBE (Haske)
11.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

...

"Na samu new Baby, she's black but hot and beauty."

Mufid yake sanar abokansa Faisal da AA yayin da yake ɗaukar ƙaramin cup na glass cike da abin maye ya jefashi cikin cup ɗin dake ɗauke da ƙanƙara kafin ya ɗauka ya fara sha hankali kwance.

Club ne da ya tara gagararrun ƴan iska maza da mata kowa na nashi iskancin da rashin tsoron Allah, waɗansu busar hayaki suke wasu ruwan maye suke sha, wasu na rawa da ƴan mata kiɗa na tashi kamar zai fasa club ɗin da hakan daɗin shi suke ji.

Faisal da AA da suke shan nasu ruwan mayen har sun kusa shanyewa Faisal yace.
"A ina take? Kun dai-daita?"

"No, hasalima bata san abinda nake nema wajenta ba but soon zan sanar da ita, but i think da kyar ta amince, she's so innocent."

AA da sai lokacin yayi magana yace.
"And so what! in taƙi amincewa. Ba sai mu bi wancan hanyar ba. Force her."

Ɗan yamutsa fuska Mufid yayi yana kurɓar wine na hannunshi.
"Not now because yadda nake jinta ba kamar sauran bane."

"No MKM don't tell us that you love her seriously."
Faisal yace cikin mamaki yana dafa cinyar Mufid dan neman tabbas.

"I really don't know guys."

Mufid yace har cikin ranshi ya yarda da hakan. Daga haka ya miƙe.
"See you tomorrow."

Hannu kawai suka ɗaga mishi yasa kai ya fita suka cigaba da tsula tsiyarsu. Kafin Mufid ya isa gida abinda yasha ya jika da kyar ya iya kai kanshi gida ya danna wani horn da ƙarfi mai gadi ya wangale get ɗin ya shiga yayi wani wawan parking ya fita ya bar motar a kunne.

Bai iya gane su waye a falon ba ya wuce ɗakinshi Ummu da Rufaida dake zaune suka bishi da kallo, kai kawai Ummu ta girgiza, Rufaida kuwa baƙin ciki ne ya rufeta a ga wannan a ƙirashi da yayanta.

...

Washegarin Mufid ya karɓi kuɗaɗe gurin Daddyn shi bai ƙirga ko nawa ba ya cire ya bashi ya karɓa yana godiya. Shopping mall ya nufa ya saya kaya sabi da takalma da duk abubuwan buƙatar shi ya dawo gidan. Sabon wanka yayi ya saka riga jeans da t-shirt ya fesa turare tare da gyaran gashin kanshi da yake ɗauke da shegen wani aski, gashi mai kyau na fulanin Yola kwantacce amma bai samu gyara ba.

Bayan ya shirya ya fito ya ɗauki mukullin motarshi da jiya bayan shigarshi ɗaki driver da ya gyara parking ya kawo. Gidan su Nuratu ya nufa kai tsaye.

Bai mance hanyar gidan ba har kofar gidan yayi parking unguwar ta fara cika da mutane ba kamar shekarun baya ba, yana zaune cikin motar shi yana bin gidansu da kallo neman ɗan aike yake babu yara sosai hakan yasa ya fito.

Bakin kofar gidan ya isa yayi sallama sau biyu ya dakata kusan mintuna goma mai aikinsu budurwa ta fito tana amsawa.

"Noor tana nan? Ita nake nema?"
Ya tambaya kai tsaye.

"Nuratu ko Noor?"
Ta tambaya shi cike da mamaki tana ƙare mishi kallo ganin kyau da zubin halitta da Allah ya zuba a gurin.

Kafaɗu ya ɗaga.
"Whatever? Noor she's inside."

Bata fahimce mai yace ba kawai tace.
"Ta tafi makaranta in dai Nuratu ce."

Bai jira ta ƙarasa maganarta ba ya bar gurin ya koma motar shi cikin jin haushi. Ganin haka itama ta koma gidan ta rasa wa zata sanar dan Mami bata nan taje karɓo wasu kaya da tayi order.

Har karfe uku saura yana zaune yana jiranta ba batun sallah balle zikiri sai ma chatting da yake bayan sigari daya banka a cikin shi cewarshi zai rage yunwa.
Yana nan zaune yaga tsayuwar mashin adaidaita ya ga ta fito daga ciki da sauri ya fito a motar.

"Noor!"
Yace da ɗan karfi cikin husky voice, ganin zata shiga gida ta juya jin kamar ita ake ma magana tayi ido biyu dashi ta ɗan koma baya kaɗan.

"Ina wuni."
Tace dashi tana mamakin ganin shi kofar gidansu.

Lumshashshun idanuwansa saman kanta yana ƙare mata kallo sosai, murmushi ɗauke saman fuskarshi.

"Lafiya ƙalau. Baby kin hanani bacci tun daren dana fara ganinki dan ba jiyanne farkon ganina gareki ba."

"Ni kuma?"
Tace da mamaki tana gyara tsayuwarta tare da zaman jakarta.

Lumshashshun idanuwansa ya zuba mata.
"Yes and i means it, i love you."

Murmushi Nuratu tayi dimple ɗinta yana lotsawa duka biyu.
"Thank you for the love, amma ina da wanda nake so kuma zan aura."

Bata jira mai zai ƙara cikin zancensa ba ta shiga gida ta barshi tsaye cikin mamaki. Mace bata taɓa cewa bata sonshi kai tsaye ba tunda yake sai yau akan Nuratu da ba zai iya hakura da ita ba. Motarshi ya koma yaja yana barin gurin.

"Kin yi bako, wani yazo zubin larabawa yana neman ki."
Munirat take faɗawa Nuratu bayan shigewarta cikin gida.

"Mun haɗu dashi, nima ban san shi ba, rabu dashi kawai bar zancen."
Tace tana tambayarta Mami ta sanar da ita ta fita.

....

Washe gari haka wajen karfe sha biyu da ta fito zata tafi makarantar ta samu yana jiranta, binta yake da motarshi kafin ta samu abun hawa, da ta shiga ya kaita ƙi tayi har ta samu abin hawa ta yi tafiyar ta.
Kwana biyun haka duk ya takura mata da kwata kwata wani kyau nashi da kuɗi da take gani ya kasa ɗauke hankalinta zuwa gurinshi dan wani haushinsa take ji ba dan Rufaida da ba, da ta mishi rashin mutumci.

Tsakanin ta da Yays Al-ameen har yanzu suna nan yadda suke burin su suyi aure kawai, da zaran ta rubuta exam ta gama suka tafi level two hundred zai zo ayi maganar aurensu.

...

Yau bata dawo da wuri ba sai wajen karfe biyar na yamma lis, ya lura duk ranar bata dawowa da wuri. Tana sauƙa a adaidaita ya isa gurinta tana ganin haka ta nufi cikin gida ya saka hannu ya fizgota.

"Mace taso ni ma ina mata wulaƙanci balle ta wulaƙanta ni, imagine Baby."
Mufid yace yana matse kafaɗunta cikin jin haushi.

Tana ƙoƙarin kwacewa cikin tsoro dama ta lura da shigan ƴan isa da yake yi.
"Let me go."

Tace cikin ɓacin rai ganin yaƙi sakinta.

"No Baby, listen to me."
Yace yana kai hannunshi saman fuskarta ya shafa, a mugun tsorace taja baya tana kwace jikinta da ya hau rawa, ganin zai ƙara kamata ta kwasa da gudu tayi cikin gida.

"Ke lafiyarki zaki shigo min da gudu."
Mami dake shirin alwalar sallar magriba ta tambayi Nuratu.

"Babu komai sauri nake."
Nuratu tace tana wucewa cikin falon da saurinta. Da kallo kawai Mami ta bita.

Nuratu tunani ta shiga dan nemawa kanta mafita da kaucewa wannan bawa da bata san sunanshi ba balle wani abu akan shi. Rufaida kawai zata samu suyi magana ta sanar da shi akwai wanda take so ya rabu da ita.
Da wannan shawara data yanke ta iya sakin ranta ta samu runtsawa.
Da safiyar ranar asabar da misalin ƙarfe tara ta ƙira Rufaida sai da ta ƙira sau biyu ana uku ta ɗauka idonta cike da bacci.

"Na tashe ki ko Ruffy."

"Babu komai, ina kwana ya su Mami."

"Lafiya ƙalau, dama Ruffy magana nake so muyi, Wallahi maganar tana da muhimmanci Please."
Nuratu ta ƙarasa maganar cikin nuna lallai tana bukatar yin maganar dagaske.

"Ki zo gidanmu mana."

Da sauri Nuratu tace.
"A'a dan Allah akwai matsala ne, ki taimaka min mu haɗu a makaranta."

'Dagaske take tana buƙatar suyi magana wanda ba kokonto ko ɗaya akan Mufid ne' Zuciyar Rufaida ya bata amsa.

"Shikenan zuwa 11 sai mu haɗu."

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa.
"Nagode sai mun haɗu."

Daga haka su kayi sallama Nuratu ta miƙe, ɗan ayyukan ta tayi data saba duk weekend tayi wanka, wanki ma da take yi kasa yi tayi burinta suyi magana da Rufaida ko hankalinta zai kwanta.

Karfe sha ɗaya saura minti biyar ya sameta a makaranta bayan ta yiwa Mami ƙarya ta samu fita.

Har sha ɗaya da mintuna ashirin kafin Rufaida ta zo dan har ta fara cire rai za tazo ga ta ƙira bata ɗauka ba.

"I'm sorry Nuratu ban samu fita da wuri ba."
Cewar Rufaida tana zama kusa da Nuratu.

Murmushi tayi tace.
"Babu komai "

"Ina sauraronki."
Faɗin Rufaida tana zubawa Nuratu idanu.

Tun daga farkon zuwa gidansu da yayi har zuwa zirga-zirga da take ganin yanayi da duk zama da yake a kofar gidansu da cikin unguwa har jiya da yayi ƙoƙarin taɓata ta sanarwa Rufaida bata ɓoye mata ba, ƙarshe ta ƙara da cewa.
"Rufaida Yayanki ne ina ganin girmanshi albarkacin ki, dan haka ki sanar dashi ya fita daga rayuwata ina da wanda nake so balle ma ko bani da kowa banga abin so a tattare dashi ba."

Numfashi Rufaida ta sauƙe.
"Kinyi gaskiya Mufid bashi da hali na gani aso, Mufid yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, ban zan faɗi abu dan in kareshi ba amma sam bashi da hali mai kyau, dan haka abin da zan iya faɗa miki shine kiyi gaggawar yin aure kiyi nisa dashi, in ba haka ba babu mai iya hanashi abinda yaga dama ko Daddy ne, dan in har ya kyalle ido yaga mace to sai fa ya ɓata mata rayuwa zai barta sannan ba mai iya ɗaukar mataki. Ni na jawo miki komai amma wallahi ba a son raina bane Nuratu dole ya min kiyi hakuri ki yafe mini."

Hawayen data gani idanuwan Rufaida shi ya bata tabbacin dagaske take, tsoro ne ya ziyarci zuciyarta. Rayuwarta yana cikin hatsari, hatsari mafi muni.

"Nagode da shawarar da kika bani inshaAllah zanyi ƙoƙarin ganin na kaucewa duk hanyar da nasan zai haɗamu, Allah zai kareni dashi na dogara."

Kai Rufaida ta girgiza halin Mufid ya isheta ta tsanesa ta tsani halinsa, kowa ma cikin gidan banda Daddy da Ummu babu mai sonshi kuma duk sune silar lalacewarsa.

Anan suka rabu kowa ya nufi gida Rufaida bata sanar da kowa ba amma ta ɗauki aniyar tunkarar Mufid da maganar ko da kuwa zai daketa ne sai ta sanar dashi ya rabu da Nuratu.

....

Nuratu tunda suka rabu ta kasa cire maganganun Rufaida a ranta hatta Mami ta lura da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login