Follow us on social media

Showing 24001 words to 27000 words out of 148866 words

Chapter 9 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

15

ta miƙe zaune jin zuciyarta kamar zai faso kirjinta, wayar ta ajiye gefe tana matsawa. Mutum ɗaya ne zai ƙirata da sunan da ta tsana ji ta tsani mai furta shi. Cikin rawar jiki ta danna saman numbern ta saka shi cikin black list.

"Ke lafiyarki ƙalau?"
Mami da ta fito a ɗakinta ta hango Nuratu zaune cikin wannan halin. Hawaye take ma bata san ya fito ba sai da taji maganar Mami ta san da hakan. A tsorace take duban Mami tana nuna mata wayarta da hannu ɗaya ta kasa magana, maganar ya maƙale a bakinta.

"Menene ya faru? Meye a cikin wayar?"
Faɗin Mami cikin sauri tana ƙarasawa wajenta ta ɗauki wayar ta buɗe, ta dudduba babu komai sai datar ta a buɗe, ta kashe ta ajiye tana kallonta.

"Menene Nuratu? Faɗa min."
Tace ta riƙo hannunta tana danƙewa da ya saka Nuratu kallonta tare da faɗawa jikinta ta rirriƙeta, ta fashe da kuka.
Mami duk ta shiga damuwa bata son ganinta cikin wannan halin, lallashinta ta hau yi har ta samu ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take sauƙewa.

"Menene Nuratu na?"
Mami tace tana dafa kanta, Nuratu ta riƙo hannunta.
"Mami shine wallahi. Mufid ne, ya ƙi barin rayuwata na huta."

"A ina? Ƙiran ki ya yi ko menene, kimin bayani."

Shuru tayi kafin ta sanar da ita saƙonsa data samu ta WhatsApp yanzu. Mami kanta ta tsorata amma dan kwantar mata da hankali tace.

"Ki bari ki ƙara bincike a kai ki tabbatar shine. Mufid baya nan yayi nisa da rayuwarki. Wani daban ne can bashi ba. Kuma tunda kin rufe layin bashi da damar sake miki magana. Ki kwantar da hankalin ki."

Kai Nuratu ta ɗaga mata, haka Mami tayi ta kwantar mata da hankali har ta nutsu taji damuwar da take ciki ya ragu. Anan ta sanar mata Dr Awwab zai zo ran asabar shi da Hanan.
Allah kawosu lafiya Mami tace cikin ranta tana wani tunani daban akansu dukkan su.

Ganin ta samu nutsuwa ya saka Mami tashi ta koma ɗaki taci gaba da aikinta ta bar Nuratu. Ranar Munirat ta samu ƙira daga wajen kakarta ta musu sallama ta tafi, haushi Nuratu kamar tayi ihu haka ta daure ta dama musu kunu ta haɗa ƙosai da abincin da za suci in ansha ruwa. Ta gaji ta galabaita sosai sai daf da magriba ta gama ta watsa ruwa tare da ɗauro alwala, ta fito kenan ana ƙiran sallar magriba. Ruwa suka sha kafin su gabatar da sallah suka dawo dan cin sauran abinci.

Washegarin a gida ta wuni dan makaranta ya ƙare sai jiran sakamakon mai kyau da shirin fita service. Haka kwanakin da ya biyo baya cikin hutu tayi su, bata ƙara samun saƙo daga wani daban ba, hakan yasa hankalinta ya kwanta.

***

Ranar asabar.

Tun safe aikinta tayi dan taran baƙonta da Hanan, da farko ta haɗa zobo mai kyau ta saka a fridge kafin ta haɗa fried rice da kaza yasha kayan lambu, tana gamawa ta shiga wanka. Bayan ta fito ta saka riga da skirt da ya zauna jikinta ba tayi wani kwalliya mai yawa ba sai hoda da kwalli da jambaki kalar kayanta maroon ta saka a bakinta. In ka kalli fuskarta za kace babu wani damuwa ko kunci a tattare da ita.

Sai karfe biyu kafin Dr Awwab ya ƙirata cewa ya shigo yanzu zai ƙaraso. Tashi tayi ta ƙara kimtsa falon ta feshe jikinta da turare, har Mami na mamakinta a ranta tana cewa ko dai shine gwarzon.

A waje yayi parking motarshi suka fito da Hanan yana riƙe da hannunta suka shiga cikin gidan da sallama, Nuratu da taji ta fito ta amsa tana musu sannu da zuwa murmushi kwance saman fuskarta da yake ƙara fito da dimple ɗinta gaba ɗaya yake lotsawa.
Hanan tana ganinta da gudu ta sake hannun mahaifinta ta ƙarasa wajenta tana rumgumeta.
Ɗagata sama Nuratu tayi ta rumgume yarinyar, ta mata kyau kamar kullum cikin riga t-shirt da wando kanta rufe da hula, ba wai dan babu gashin ba sai dan mutunta shi.

Dr Awwab da ya zuba musu ido yana kallo, murmushi yake zubawa hannunshi cikin aljihun ƙananan kayan jikin shi. In yace basu burgeshi ba ya yaudari zuciyarshi.

"Ni fa?"
Ya samu kansa da furta hakan da ya saka Nuratu duban shi tamkar bashi yayi maganar ba.

"Mu shiga daga ciki."
Tace cikin basar da maganar bayan ta watsa mishi harara ta wuce cikin falon tana ɗauke da Hanan, ganin haka shima Dr Awwab ya bi bayansu cikin sallama yana zuba murmushi, idanuwan burgeshi suke duk lokacin da ta masa wannan kallon.

Babu kowa cikin falon hakan yasa ya zauna saman kujera, sai lokacin Nuratu ta gaishe sa ya amsa yana tambayarta Mami ta miƙe ta ƙirata ta fito suka gaisa kafin ta koma ciki ta basu guri.
Sama sama suke hiran dan yawanci hiran tsakanin Nuratu da Hanan ne kafin Nuratu ta gabatar musu da abinci da zoɓo da tayi. Kaɗan yaci sai dai yasha zoɓon sosai dan ya mishi daɗi. Hanan kam taci abincin sosai musamman kazar dan yaro da kwaɗayi ba kara.

Sai bayan ya dawo daga sallar la'asar kafin yace za su koma. Hanan bata so ba, kamar tayi kuka suka fito waje bayan Nuratu ta cika ta da kayan zaƙi da ta saya ta ajiye musamman dan ita. Cikin mota Dr Awwab ya buɗe mata ta shiga tana ma Nuratu bye bye itama ta ɗaga mata hannu. Ya juya yana kallon Nuratu kafin yace wani abun ta rigashi.

"Nagode Dr, Allah ya bar zumunci. Haƙiƙa naji daɗin zuwan Hanan yau."

Nuratu ta faɗawa Dr Awwab haka da bai shiga cikin motar ba dan akwai sauran maganganun da baya son Hanan taji. Jin Nuratu na mishi godiya ya mai da hankali sosai kanta.

"Ni ne da godiya Noor. Sai dai hanzari ba gudu ba. Ina da buƙata a wajenki, ni a gurina babba ne amma ban san ke ya zaki ɗauka ba. Ba maganar wasa bane Noor, ina so kiyi tunani a kai bazan takura miki ba. In har kin amince ina son auren ki Noor please ki bani wannan damar."

Tun daga farkon soma maganar shi ta san in da ya dosa, bata ji haushinsa ko kaɗan ba ballantana Dr Awwab yana cikin jerin mutanen da suka taimaki rayuwarta, tana ganin mutuncinshi ko dan taimakon da ya mata a rayuwa.

Murmushin saman fuskarta bai gushe ba tace.
"Na ji Dr Allah ya saka, sai dai babu aure a cikin kundin rayuwar Nuratu, muci gaba da mutumcin mu ci gaba da mutunci kamar yadda mu ka saba."

"Kar ki ce haka Noor, kar ki yanke hukunci cikin lokaci ɗaya na baki lokaci zan iya jiranki ko nan da yaushe ne."
Shi kanshi mamakin kanshi yake yadda yake buɗe baki yake mata maganar aure.

Ta san dama dakyar ya amince ko ya yarda tamkar sauran dan haka tana shirin shiga gida tace.
"Shikenan zanyi tunani, Nagode sosai Dr."

Daga haka ta shige gida ya juya ya shiga motarshi su ka bar gurin ko ba komai yaji kalamai daga gurin Nuratu mai daɗi.

Tausayin halin da ta shiga tun ranar da ya fara ganinta shi ya rinjayi zuciyarshi akanta, wanda ya ɗauki abin ya ɗaura a mizanin tausayi daga baya ya ga sam ba haka bane. Duk da yayi ƙoƙarin kawar da hakan a ranshi amma zuciyarshi ta kasa nutsuwa. Tun bayan da mahaifiyar Hanan ta yi nesa dashi ya tarkata soyayya da komai ya jingina a gefe yaci gaba da kula ƴarshi kwaya ɗaya da Allah ya mallaka masa.

***

Dr Awwab yana cikin jerin mutanen da take girmama su, suka mutunta ta suka taimaka mata lokacin da take tsananin buƙatar taimako. Bata san ta ya ya zata kaucewa buƙatarshi ba shi da sauran. Bata da komai bata da abinda zata saka musu dasu.

Nuratu ke wannan tunanin yayin da take kwance cikin kujeran falon bayan ta dawo daga raka Dr Awwab, maganganun shi suke mata yawo a kai da ya sakata faɗawa tunanin rayuwarta kamar kullum yadda ta saba.

Runtse idanunta tayi tamkar yanzu abubuwan suke faruwa.

****

Tana ji tana kallo Mufid ya hawo jikinta tare da shafarta ta ko ina, mutsu mutsun kwace kanta take har lokacin bakinta bai daina ambaton Allah ba da roƙarsu akan su kyaleta. Hannunta ɗaya da yake iya motsi tasa take dukan Mufid dashi tare da ture shi iya ƙarfinta.

"Ku riƙe min ita."

Cewar Mufid cikin jin haushin yadda ta hana shi sakewa a jikinta. Jin haka AA da Faisal suka matsa tare da rirriƙe masa ita kafin ya afka mata cikin ƙarfi.
Ba ya ji ba gani kawai ya fara ƙoƙarin shigarta domin ta riƙita shi sosai.
Nuratu ji tayi wani azababben zafi ya ratsata ta fasa ihu da ƙarfi, cikin sauri AA ya rufe mata bakinta da hannunshi.

Ihu Nuratu take ba ya fita, idanunta tamkar garwashi tsabar fitar hawaye da azaban zafi da take ji yana shigarta yana ratsa dukkan ilahirin jikinta. Tun tana ihu su saketa har tazo ta gagara yin komai jikinta ya sake idanunta suke rufe ta daina jin komai da kowa numfashinta ya ɗauke.

Mufid bai ma sani ba domin yi yake yana sakewa dan ya samu abinda yake so, yana shirin sakewa Faisal ya dakatar dashi.

"Ai ya ishe ka Mufid, sai ka bari mu yi ai."
Faisal yace ko duba da halin da Nuratu take ciki baya yi.

"Ai baku ku ka kawota ba."
Mufid yace yana sake komawa kan Nuratu.

Kamar daga sama suka ji ƙarar bindiga sau biyu a ƙofar gidan da ya saka su tashi tsaye gaba ɗayan su cikin tsoro, kafin suji an fara sanarwa cikin loud speaker cike da umartan su.


....

#vote
#comments
#share

MADUBIN GOBE 14.

Pharty Bb
Wattpad phartybb.

***

Cikin umarnin da tsoratarwa aka fara sanar dasu cewa.

"Ku fito da kan ku, ko in muka shigo mu harbeku! Wanda yayi yunƙurin guduwa in har mu ka kamashi bayan azaba da zamu gana mishi akwai hukuncin kisa ta hanyar wulaƙanci."

AA da Faisal sun tsorata sosai musamman Faisal dan ya fisu tsoro da ma, Mufid kayan jikinshi yake maidawa ko a jikinshi, in dai irin wannan kamu ne ansha musu kuma ana yin belin su mai na jin tsoro.

"MK ya za muyi, wallahi tsoro nake ji. Mu gudu mu haura gini yadda ba su isa su kama mu ba."
Faɗin Faisal a gigice.

"Calm down Fai you have me. So mai ka ke jin tsoro? Mintuna kaɗan za muyi a cell mu fita kuma kasan haka, so mai abun tsoro to? Mu je kawai."

Faɗin Mufid yana nufan kofar waje ko a jikinshi, an sha kama su da kayan maye, harkar fyaɗe duk suna tsira to menene kuma sabo. Suma sun san hakan domin in dai an kamasu to mahaifin Mufid duk in da zai shiga zai shiga ya fita sai ya fitar da ɗanshi da su, amma yau haka kawai suka ji tsoro.

Hannunsu a sama sun sadauƙar suka fito, Mufid ne a gaba sai AA da Faisal a bayanshi suna ƙare kansu, hasken motocin police da na Ahmad ya haskasu sosai.

"Go down."

Ɗan sanda ya basu umarni yana nunasu da bindigar hannunshi, ba musu suka durƙusa saman gwuiwowinsu a ƙasa duk da anyi ruwan sama caɓi ya ɓata ƙasar, hannayen su a sama Mufid ya ɗaga ido suka haɗa ido da Ahmad da ranshi haɗe tamkar bai taɓa dariya. Ahmad ji yake zai iya kashe Mufid da da bindiga a hannunshi.

Ganin dukkansu sun fito cikin sauri Ahmad ya nufi cikin tare da ƴan sanda biyu suka fara bincike. Tun a falon suka fara cin karo da hijabin Nuratu da yake yashe. Ɗakuna biyu a jere wanda yake buɗe idanuwan Ahmad suka kai gurin da sauri ya nufa nan.

Abinda ya gani ya mugun tayar mishi da hankali, tashin hankalinshi ya ƙaru, idanuwansa ya runtse dan ba zai iya juran ganin halin da take ciki ba, dakatawa yayi ya juya sauran ƴan sandan suka ƙaraso wajen.

"Ka sameta Sir?"
Ɗaya daga cikin ƴan sanda investigator Lawan ya faɗa yana ƙoƙarin shiga da sauri Ahmad ya tare shi yana tare hanyar, ransa a mutuƙar ɓace.

"Ƙira motar emergency daga asibiti, sun riga sunyi raping ɗinta, Ina ga babu numfashi a tare da ita."

Su kansu ƴan sandan sun ji abin wani iri, duk da ba yau suka sa ba samun case na fyaɗe ba domin abin ya zamto musu kamar karatu ba'a kwana biyu ba'a kawo musu case na fyaɗe ba, abin ya zama tamkar cin tuwo a rayuwar yanzu, yiwa yara, ƴan mata, matan aure fyaɗe ƙarfi da ya ji.

Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya fita ya sanar da Ogansu, investigator Lawan ya fara ɗaukar rahoto dan samun shaida.
Cikin sauri Oga Salisu ya bada umarni aka ƙira emergency tare da sakawa su Mufid ankwa aka jefasu a cikin mota.
Mintuna goma sai ga motar emergency ta iso suka shiga cikin gidan, abinda suka gani ya basu mamaki, zuciyoyinsu suka cika da tausayi da rauni tare da ruɗani, Nurse biyu aka haɗasu da shi suka zo mace da namiji.  Macen tsorata tayi jikinta ya hau rawa, Namijin ne yayi ƙoƙarin rufe jikin Nuratu sai ya kasa ɗaukarta ya ɗaurata saman ƙaramin gadon da suka shigo dashi, ganin haka Ahmad da yake baƙin kofa ya juyo ya ga ya rasa ta ina zai ɗagata.

Cikin sauri ya iso ya saka hannun sa ya ɗauketa tare da bismillah suka fita.
Cikin motar ya kwantarta saman gadon Nurse ya fara ƙoƙarin saka mata Oxygen ganin bata numfashi.

Tafiya kawai suke motar ƴan sandan ta wuce da su Mufid Police station bayan sun bar saura biyun sun bi motar asibiti,  Ahmad daya koma motarshi shima yana bin bayansu. Ƙiranshi ake a waya ya duba ya ga mahaifiyarshi ce tun tasowar shi take ƙiran.
Ɗauka yayi bai iya jira ta faɗa abinda zata faɗa ba ya tari maganarta.

"Umma dan Allah kiyi hakuri, na shigo Damaturu ruwa ya tare ni a hanya, ki bani mintuna talatin yanzu zan shigo garin."

"Ka koma inda ka fito bama buƙatar ka."
Bata jira mai zai ƙara faɗa ba ta kashe wayarta.

...

Suna isa asibitin aka karɓi Nuratu aka wuce da ita ɗakin aikin gaggawa, Dr Sadiq da yake duty ya shiga ya fito ya samu ƴan sanda da Ahmad da suke tsaye.

"Is a rape case."

"Yes we know it, kayi aikin ka ka ceto ran yarinyar nan, and i need proof. Dan billahil azim ba zan bar yaran nan ba sai an musu hukunci dai-dai da abin da suka aikata."
Ahmad yace har lokacin ransa a haɗe, bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan ranar ba.

Jin haka ya saka Dr Sadiq komawa ɗakin ya fara taimakawa Nuratu da duk abinda ya san zai iya, shi kanshi ya wahala domin Mufid ya mata rauni sosai ban da gurɗewar da hannunta yayi. Numfashinta ya samu ya dawo dai-dai ya kimtsa ta ya saka mata drip da alluran bacci ciki, tare da taimakon Nurse ɗin suka rufeta suka fito.

Awansu biyu kafin su fito har lokacin Ahmad tsaye yake kyam ya kasa ko motsawa, ganin fitowar Dr ya nufeshi.

Ofishin Dr Sadiq suka nufa da Ahmad da investigator Lawan bayan sun zauna, yana dubansu.

"Numfashinta ya dawo dai-dai, tana bacci zata iya farkawa ko yaushe, ta ji ciwo sosai saboda ƙarfi suka nuna mata, amma Insha Allahu na shawo kan matsalar, zata warke amma zai ɗan jima sai an haɗa mata da magunguna da wasu abubuwa "

"Kana ɗaukar jawabin sa?"
Cewar Ahmad ga investigator Lawan bayan ya gama sauraron bayanin Dr Sadiq.

"Yes Sir."
Cewar investigator Lawan da yake ɗauke da takarda da biro yana rubuta duk abinda Dr Sadiq ya faɗa.

Miƙewa Ahmad yayi tsaye.

"Mungode Dr fatan in an ƙira ka gaban kotu zaka maimaita abinda ka faɗa yanzu."

"InshaAllah zan faɗi komai cikin abinda na faɗa har da wanda zan sani nan gaba domin akwai bincike da za muci gaba da yi dan samun cikakken shaida."
Faɗin Dr Sadiq bai ji ko dar a jikinshi ba domin shi kanshi ya tausaya yarinyar, kuma ya ji zai iya bada shaida ko dan a hukunta waɗanda suka aikata mata haka.

"Mungode Dr, ka kula da ita abar mata Nurse ɗaya a wajenta, za mu koma Division."

To Dr Sadiq ya faɗawa Ahmad da investigator Lawan kafin suka wuce. Suna zuwa Division suka samu an saka su Mufid a cell.

"Zan wuce Maiduguri da ma wucewa na ke Allah ya ƙaddara zan shiga cikin lamarin kamar yadda na sanar da ku. Ga card nawa dan in wani abin zai taso ina buƙatar sani, may be gobe da safe zan shigo. And lastly wallahi kar wanda ya bada belin su, idan iyayensu sun zo ku sanar dasu mu haɗu a court domin babu bailing. Batun iyayen yarinya kuma idan ta farka za ta sanar da Dr a ƙirasu su zo, kar ku damu da wannan."
Ahmad ke wannan bayani har ya gama ba wanda yayi magana.

"Ok Sir za'a yi yadda ka faɗa."
Cewar DPO Salisu ya karɓi card ɗin Ahmad ya jefa cikin wardrobe ɗinshi kafin suyi musabaha Ahmad ya wuce.

Cikin daren ya kama hanyar Maiduguri, ƙarfe goma saura ya isa cikin unguwar su GRA kai tsaye gidansu ya nufa bayan yayi parking ya wuce babban falon babu kowa hakan yasa ya hau stairs ya duba ɗakin Umma bata nan ya wuce ɗakin mahaifin shi, gaba ɗayan su har ƙannenshi mata suna nan.

Jin motsi da sallamar shi ya saka su juyawa suka dube shi babu wanda ya tanka.

"Ka fita ka koma in da ka fito."
Cewar Umma tana sharan hawaye.  Da sauri Ahmad ya ƙarasa ciki.

"Umma dan Allah kiyi hakuri, wallahi wani case na tarar ya sani dakatawa dan ɓullowa lamarin amma yanzu allahamdulillahi gani na zo lafiya."

Girgiza kai ta yi.
"Yanzu Ahmad in mahaifinka ya mutu kace me? Shekaru nawa mu ke binka ka zo? Yanzu mun samu ka taho shine ka tsaya a wani hargitsi da bai shafeka ba."

"Ki yi hakuri Umma."
Ahmad yace dan shima ya san bai kyauta ba.

Jikin mahaifinsu ya duba ya ga yana bacci hakan yasa ya fita, ɗakin da babu komai ya shiga yayi wanka ya canza kayan jikinshi kafin ya gabatar da salloli ya fito.
A falo ya samesu zaune harda ƙannen shi masu aure wasu da ƴaƴan su. Yarinyar da ya gani ƴar shekara biyu zaune tana wasa ya ɗauka.

"Babyn waye?'
Yace yana ma yarinyar wasa.

"Ƴar Suwaiba ce."
Cewar Umma dan sauran duk sunƙi masa magana kuma yasan fushi suke da shi. Ya kasance shine babba kuma shekara huɗu tinda ya tafi bai waiwaye su sai waya.

"Shi yasa na ganta mummuna."
Yace yana jan kumatun yarinyar.

"Wallahi ta fika kyau."
Cewar Suwaiba jin an zaga mata ƴa hakan ya sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login