Follow us on social media

Showing 69001 words to 72000 words out of 148866 words

Chapter 24 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

40

ya zubo mata ta share tana gyaɗa kai ta ƙira Aunti Rahma, a nutse ta sanar da ita abin da ta samu labari. Tashin hankali da ta shiga tace za ta je gidan ta samu Mami ta sanar da ita, Rukayya ta hanata ta sanar da ga yadda su kayi da mijinta ta amince.
Bayan ita ta sanar da Aunti Hasiya gobe su haɗu a gidan Mami akwai maganar da za suyi ta ɓoye mata gaskiya gudun tashin hankalinta ita ma.

***

NIGER.

Da daren Kawu Muhammadu da ya dawo kafin suka gaisa da Al'ameen yana tambayarshi hanya da kuma wajen mahaifiyarshi kasancewar ya ganeshi kuma ya bayyana masa kanshi.

"Lafiya ƙalau Kawu duk suna gaishe ku."

"Sosai muna amsawa. Kun haɗu da ƙanwar ka."

"A'a wallahi Kawu."
Al'ameen yace da saurin shi.

"Ikon Allah ɗazu sunce za su tafi kasuwa da Nazifa, ko dai sun biya wani gurin."

"Hakane dama gurinka na zo Kawu, magana ce akan Nuratu."

"To ina sauraron ka."

Kawu Muhammadu yace yana sauraran bayanin Al'ameen har ya gama. Tun farkon haɗuwarsu da soyayyar da su kayi da Nuratu har zuwa abin da ya faru ya dakata har zuwa yanzu da ya dawo da niyar aurenta.

"Ai kuwa mai suna an yi ba'a yi ba an raka bako ya dawo. Domin na tura wancan Likitan gurin mahaifinta duk da ya ce ya mata miji, za su samu yayanshi za'a yi abu ɗaya. Jiya jiyan nan ya tafi, yaron sai zirga zirga yake a kanta kuma ga abin da yake shirin faruwa, kawa na yanke hukuncin ya aureta."

Idanuwansa kaɗai zaka gani ka hango tsantsan tashin hankali da ya shiga, girgiza kai yake alamar kar hakan ya kasance gaskiya ya kasa magana.

Kawu Muhammadu da jikinshi yayi sanyi jin shima Al'ameen ɗin yana so sai dai Allah ya riga ya saka ba matar shi bace yace.
"Hakuri za kiyi mai suna ka karɓi ƙaddara, Allah ya riga ya rubuta hakan sai ya faru shi yasa tsawon shekaru aure bai yu a tsakaninku ba."

Nasiha sosai Kawu Muhammadu ya yi ta yi wa Al'ameen na yarda da ƙaddara har ya ji zuciyarshi yayi sauƙi daga raɗaɗin da yake ji. Haƙiƙa ya so Nuratu tun ba yau ba ya so aurenta musamman yanzu da rayuwarta ya shiga wani hali dan ya share mata hawayenta ya nuna mata itama mace ce kamar ko wace mace mai ƴan ci.
Sai da yaji zuciyarshi ya samu nutsawa ya ɗago idanuwansa yana kallon Kawu Muhammadu da shi.

"Haƙiƙa Kawu na so auren Nuratu, na so ganin na share mata hawaye amma Allah ya riga ya rubuta ba ita bace matata, ba ni bane mijinta. Allah yasa haka shi yafi alheri, Allah ya basu zaman lafiya."

"Ameen ya Allah. Ina ƙara baka hakuri mai suna."
Kawu Muhammadu yace cikin sanyin jiki hakan bai mishi daɗi ba kwata kwata ko dan mahaifiyarshi da ta riƙe ƴaƴan ƙanwar sa.

Suna cikin haka Nuratu da Nazifa suka shigo da sallama, runtse idanuwansa Al'ameen yayi jin muryarta ya san da wuya ya mance Nuratu da soyayyarta a cikin ranshi.
Kawu ne ya iya amsawa Al'ameen ya miƙe.

"Zan je in dawo Kawu."

Kai ya gyaɗa masa ya fita bai ko kalli in da Nuratu take ba da ta bishi da kallon mamaki ganin shi wannan lokaci kuma yaƙi tsayawa su gaisa ya nuna tamkar bai ganta ba.

"Kawu yaushe ya zo?"
Ta tambaya tana ajiye abin hannunta.

"Tun safe ya zo."
Ya bata amsa maimakon ya ga damuwa tattare da ita sai yaga akasin haka yana mamaki. Sai ya ji ranshi yayi sanyi ganin kamar ita bata ma damu dashi ba shi yake son, ya ga alamar tafi shiri da Dr duk da shima tana nuna masa hali.

...

Da safe Al'ameen ya ma Kawu sallama ya tafi bai jira ya yi wa Nuratu magana ba. Da ta farka ta ji labari sai ta ji abin bai mata ba, ta ƙira lambar shi har ya gama ringing bai ɗauka ba ta hakura.

Sai da ya isa gida ya huta ya sanar da Amma Jidda yanda su kayi, ba ta ji daɗi ba sosai abin da su kayi, Al'ameen yayi ta kwantar mata da hankali ya nuna mata shi fa ya hakura. Yanayin sa take kallo har wani yar rama yayi.

"Al'ameen zan samu Mami muyi magana ta sanar sa Dr Awwab ya hakura kawai."

"Amma na hakura fa babu kyau neman aure cikin aure kin sani."
Yace yana girgiza kai zuciyarshi cike da damuwa fuskarshi ɗauke da murmushin dole.

"Shikenan Allah sa shine mafi alheri."

Ameen ya amsa dashi ya miƙe ya wuce ɗakin Muhsin da yake sauƙa ya mayar nashi. Sai lokacin ya ji son ƙiran Nuratu ya ɗauki wayar shi ya ƙira numbern da ya gani na Nijar ya san nata ne.

...

Tana zaune tana figar yakuwa da za su ɗaura abincin dare dashi ƙarar wayar ya ankarar da ita daga tunanin da ta shiga na son ƙiran Dr Awwab ta tambayeshi sun isa lafiya kuma maganinta ya kusa ƙarewa zuwa wani sati tana buƙata.
Ɗauka tayi ta ga Yaya Al'ameenn ne ta kara a kunnenta tare da sallama.

"Ƙanwata!"

Ya faɗa mata kamar kullum ta amsa da.
"Ina wuni Yaya Al-ameen ya hanya? Zuwa babu sanarwa kuma ko ka tsaya mu gaisa ka koma."

"Wani uzuri ya taso min. Ya kike?"
Ya faɗa yana ƙoƙarin danne abinda yake taso masa.

"Lafiya ƙalau ina Amma?"

"Tana lafiya. Shikenan sai anjima zan ƙira ki wani lokaci."

"To sai na gani."

Tace ta kashe ta ajiye wayar, muryarshi ya canza mata da yanayin shi gaba ɗaya.

***

DAMATURU.

Ƴan matan Mami sun sata gaba daga mai faɗa sai mai hawayen abin da mahaifinsu ya aikata, daɗin su ɗaya da Mami ta sanar da su yadda su kayi da Kawu Muhammadu akan Dr Awwab da ya ƙira ya sanar mata komai, ta ji daɗi amma har ranta ta so Al'ameen aka bawa wannan damar dan irin son da ta ga yake yi wa Nuratu. Sannan ta gargadesu kar su sanar da Nuratu dan bata da labari kuma za tace ba za tayi auren ba ya zama anyi gudun gara. Sosai sun ji daɗin hakan musamman Aunti Rahma tace.

"Wallahi dama sonta yake. Kin ga yadda yake zirga-zirga bawan Allah ta dinga masa wulaƙanci. Ashe shine mijin."

Hasiya da ta cika tayi fam jin abin da ubansu yayi da yanzu sun fara ganin baƙin shi ta ƙara da.
"Ai wallahi ya burge ni. Ita ma banza sai kace a kanta aka fara ƙaddara. Ai da Mufid ɗin ne ma ya ɗan cimin kaniyarta."

Dariya suka kwashe dashi ban da Mami, Rukayya tace.
"Amma wallahi ina tausayin Yaya Al'ameen, shi ma yana sonta tun ba yanzu ba. Allah sarki yayi ta dakon so."

"Rabu dashi shima bashi da niyar auren, masu niya sun fito da su za'a yi."
Aunti Hasiya tace dan dama bata son soyayyar su tun asali faɗa ne taƙi.

Har dare suna gidan kafin su mata sallama su tafi mazajen su su kazo ɗaukar su.

....

Bayan kwana biyu ya kama ranar asabar.

RANA BATA ƘARYA.

....

#vote
#comments
#share.

MADUBIN GOBE  35.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
....


Da safiyar ranar asabar ƙarfe goma dai-dai Alhaji Inuwa ya samu ƙiran Dr Awwab da mutanen shi sun iso. Tun daren jiya ya iso gidan Alhaji Mamman zaton Alhaji Mamman duk dan auren Nuratu da Mufid da za'a ɗaura ne safiyar gobe.

Gidan duk ya cika da mutane abokan Alhaji Mamman da ya gayyato su dan zuwa shaida ɗaurin auren Nuratu da Mufid.

Alhaji Inuwa na zsune yana duba agogo burin shi Dr Awwab ya ƙira shi kar lokaci ya ƙure musu kamar yadda suka ɗiba ya samu ƙiran da shigowar su kenan. Cikin sauri ya ɗauka ya musu kwatancen gidan kafin ya koma ya samu ana haɗa haɗar ɗaura aure Alhaji Kashim ya iso da nashi mutanen. Ciki har da Mufid da yasha bakin yadi da ya amsa sunanshi dan kuɗi da aka zuba aka kwashi kayan, yayi kyau sosai kamar ba ɗan shaye-shaye Mufid ba, dan ma daren jiya sai da su kayi tatil dakyar yau ya samu ya farka ya shirya ya taho sai washe baki yake Faisal da AA suna mara mishi baya.

Alhaji Inuwa da ya iso yana jiransu Dr Awwab ya dubi ƙaninshin Alhaji Mamman yace.
"Mamman ka ɗan ban lokaci akwai bakina da za su iso cikin ƙanƙanin lokaci."

Ganin idon jama'a da kuma yayan shi ne ya sashi cewa.
"Shikenan Yaya amma suyi sauri, mahaifin yaron nan sun iso tun ɗazu."

Sallamar Alhaji Abubakar ne da mutanen shi ya hana Alhaji Inuwa magana ya tashi ya tare su suka ƙaraso cikin babban falon da yake cike da mutanen da za su shaida auren. Dr Awwab da yayan mahaifinshi Alhaji Abubakar da abokinsa ɗaya da abokin marigayi Alhaji AbdulRamat mahaifi ga Dr Awwab su huɗu.
Alhaji Mamman da Alhaji Abubakar kallon kallo su kayi a junansu, Alhaji Mamman na tunanin ina ya san malallakiyar fuska mai irin nashi. Zuciyarshi ya kasa bashi macece ko namiji? Babba ne ko yaro?.

"Ga baƙina. Bismillah Docter ku zauna."
Alhaji Inuwa yace yana nuna musu kusa da Alhaji Mamman suka zauna tare da gaishe da mutanen wajen alhazzai masu ruwan kuɗi abokai ga Alhaji Kashim da su kazo shaida ɗaurin auren tilon ɗan sa.

Mufid ido kawai ya sakawa Dr Awwab cikin bakin gilashin da ke manne a idanun shi, ya gane shi shekaru huɗu da suka wuce shine Docter da ya bada shaida a kotu shi ya kula da Nuratu bayan barinsu nan. Dole ya masa godiya in an gama ɗaurin auren shi da Baby Noor.

Dr Awwab yayi kyau cikin farin yadin da ɗinkin ya zauna a jikin shi, hula da yake saman kanshi da farin gilashin dake manne a idonshi ya fitar da kyan kyakkyawar fuskarshi. Fuskarshi ba zaka bambance wani yanayi yake ciki ba, babu fara'a kuma ba'a haɗe ba.

"Ayi shuru za'a fara gudanar da ɗaurin aure."
Faɗin mutane masu roƙo dan samun nutsuwar mutanen gurin. Tuni guri ya ɗau shuru kowa ya zuba kunne.

Gefe ɗaya Alhaji Inuwa da Dr Awwab da yake kusa da Alhaji Mamman ta damanshi, gefe ɗaya kuma Alhaji Kashim da yake hannun hagunshi dasu Mufid.

"Mamman."
Alhaji Inuwa ya ƙira sunan shi da ya saka gurin gaba ɗaya sauraron mai zai faɗa har shi kansa Alhaji Mamman ɗin ya amsa.

"Mamman ka ɗauke ni matsayin uba kamar yadda mahaifin mu ya faɗa maka kafin rasuwar shi ka ɗauke ni tamkar shi, ka min biyayya kar ka saɓa umarni na, in har ka saɓa hakan to ka tabbata yana fushi da kai haka Mama ma maganarta na ƙarshe a duniya in za ka tuna."

"Yaya mai ya kawo maganar nan ana cikin shirin ɗaura aure."
Alhaji Mamman yace ƙasa ƙasa da wanda suke kusa duk sun ji kasancewar falon an yi shuru.

"Shine dai Old man ka bari daga baya kuyi komai."
Faisal yace Mufid ya watsa masa wani kallo bayan ya cire gilashin idonshi.
"Rufewa mutane baki."

Girgiza kai Alhaji Inuwa yayi.
"Na isa inyi iko da kai in baka umarni. Tambayar ka nake?"

"Sosai ma Yaya. Menene kuma?"
Alhaji Mamman cije da tashin hankalin da yake taso masa.

Ajiyar zuciya Alhaji Inuwa ya sauƙe ya juya ya kalli Dr Awwab da kan shi yake ƙasa yana jin komai.
"In har na isa da kai ka bawa Dr Awwab auren Nuratu yanzu kuma a ɗaura aure, in kuma ba haka ba, ka sani babu ni babu kai sannan ka sani har abada ina fushi da kai. Kar ka manta maganar Baba."

"Akan me Yaya? Me yasa zaka min haka? Ga can yaron da na zaɓa mata zai aureta mai ya kawo wannan maganar dan Allah?"
Alhaji Mamman yake wannan tambayoyin cikin tashin hankalin jin furucin Yayanshi baya ma jin maganganun da ya kaure a falon.

Alhaji Kashim na bin Alhaji Mamman da wani kallo, Mufid da abokansa na kudunduma ashar da wasu suka saki baki suke gani suke ji.

Alhaji Inuwa ko a jikinshi yana duban Alhaji Mamman.
"Umarni na baka in har zaka iya, in kuma a'a shikenan."

"Ba zan iya ba."
Yace yana girgiza kansa.

Shi ya zai yi? Ya zai yi da Alhaji Kashim da Mufid? Kuɗin da suka bashi fa? Ko matsayi da suka ƙara masa? Ba zai iya mai da ko ɗaya ba sannan ba zai iya bin umarnin yayan shi ba amma yana gudun fushin mahaifinshi da ranar haɗuwar shi da Allah.

Miƙewa Alhaji Inuwa yayi, dama ya san da kyar Alhaji Mamman ya amince.
"Shikenan Mamman amma ka sani babu ni babu kai har abada kar ka ƙara zuwa in da nake ko nuna ka sanni har abada na faɗa maka. Hatta ƴaƴan ka. Sannan ka shirya karɓar tsammaci bisa tauyewa yarinya haƙƙinta da kayi tsawon shekaru ni da kai babu sani babu sabo."

Daga haka ya juya ya kalli Dr Awwab da Alhaji Abubakar da mutanen sa da abun ya zama musu wani iri. Can kuma Mufid da Alhaji sun daina zage zagensu jin Alhaji Mamman yaƙi amincewa.

"Mu je Docter."
Yace yasa kai zai fita suka miƙe, Dr Awwab ya kasa dan ji yayi kafafunsa sun kasa ɗaukar shi. Yana ji yana gani zai yi asaran Nuratu.
Ina! Yace har maganar zuci ya fito fili ya matsa kusa da Alhaji Mamman.

"Dan Allah Baba kar ka hanani aurenta, Noor bata dace da wannan yaron ba."

Kallon shi Alhaji Mamman yayi kyakkyawan saurayi matashi da ba zaka rantse yayi auren fari ba ko shekarun sa sun haura talatin ba, ya gane sarai. A sanya juya ya kalli yayan shi da yake shirin fita maganganun shi ɗaya bayan ɗaya na dawo masa suna masa yawo a kai.
Da sauri ya dakatar da shi ta hanyar cewa.

"Na amince Yaya zan bashi ka dawo dan Allah kar na haɗu da fushin Baba."

"Akan wani dalili."

Cewar Mufid yana buga wani tsalle ya shiga tsakanin su, Alhaji Kashim ya miƙe shima yana cewa.

"Saboda mai yasa? Ka san dai mai zai biyo baya."

"Alhaji za muyi magana daga baya."
Alhaji Mamman yace da yaji gwara ya mai da masa da arzikin sa da ya haɗu da fushin Allah da mahaifin sa.
'Wannan yarinya masifa ce.' Yace a
ranshi yaji ya ƙara tsanar Nuratu.

"Ba zai yiwa ba!"
Alhaji Kashim yace cike da masifa jin za'a hana tilon ɗan sa cikar burinshi bayan shiri da suka shirya shi da Ummu.

Alhaji Inuwa da ya dawo baya shi da Alhaji Abubakar da mutanen shi ya dubi Alhaji Kashim ya masa wani kallo.
"Za ku iya bamu guri Please."

Ashar Alhaji Kashim ya danna mishi ko kunyar mutanen gurin bai ji balle ɗan shi da abokan ɗan shi.

"Ka amince kanan?"
Alhaji Inuwa yace da Alhaji Mamman da ya zama mutum mutumi tsabar baƙin ciki ya cika zuciyarshi da tsanar Nuratu.

Kai kawai ya ɗaga, Alhaji Inuwa yayi murmushi yana duban Alhaji Abubakar.
"Alhaji ka amince za ka karɓawa yaronka auren Nuratu Mamman Bashir."

Alhaji Abubakar da sai yanzu ya saka baki yace.
"Abubuwan da ke faruwa akwai ɗaure kai, ina bukatar sanin wasu abubuwan duk da na fahimci in da maganar ya fara dosa."

"Baffa dan Allah ka ce ka amince abar ko wani magana daga baya."
Dr Awwab yace cikin sauri bayan ya cire kunya ya ajiye a gefe.

Kallon shi kawai Alhaji Mamman yake jin muryar Alhaji Abubakar irin na wanda fuskar ke masa gizau ne, hatta muryar iri ɗaya da har lokacin ya kasa tantance ina ya san malallakiyar fuskar.

Murmushi Alhaji Abubakar yayi da ya ƙara jefa zuciyar Alhaji Mamman ruɗani da tunani yace.
"Shikenan na amince."

"Kun fito da kuɗi?"
Alhaji Inuwa ya buƙaci sani.

"Eh akwai."
Alhaji Abubakar yace yana saka hannu cikin aljihunsa ya ciro kuɗaɗen ciki.

"To ku biya sadaki a ɗaura aure kawai tun da mahaifin yarinya ya amince ya bada ita ni zan zama waliyanta ga shaidu su shaida ɗaurin aure."

"Wallahi baku isa ba sai na kashe ka in ka auri Baby Noor."
Mufid ke wannan hargowan aka riƙe shi Faisal da AA cikin sauri ganin yayin kan Dr Awwab.

"Mu tafi Faisal ku sashi a mota. Mamman ka shirya haɗuwar mu"

Daga Alhaji Kashim yace ya kaɗa babban rigarshi ya sa kai ya fita Faisal da AA su ka bi bayansu suna riƙe da Mufid da ashar kawai yake ɗurawa son ranshi yana cewa sai ya kashe Dr Awwab in har ya auri Nuratu.
Mutanen Alhaji Kashim ganin wanda su ka zo dan shi ya fita ya sa suka kwashi takalmansu suka fice cike da jimamin wannan lamari, dama mamaki suke wani ubane na gari zai ɗauki ƴarshi ya bawa Mufid sai dai lalatacciya ƴar uwar shi.

Kankara kaf kuɗin jikinshi Dr Awwab ya ciro da shi, Alhaji Abubakar ma haka suka haɗa dubu ɗari uku sadaki suka damƙawa Alhaji Mamman da ya ji kamar ya watsar dan bai ɗauke shi kuɗi ba, ga in da za'a bashi miliyan biyar sadaki ya ƙare da dubu dari uku.
A gurin a take jama'a suka shaida ɗaurin auren AWWAB ABDULRAMAT da NURATU MAMMAN BASHIR akan sadaki dubu ɗari uku. Alhaji Inuwa ya zama waliyanta Alhaji Musa (Abokin mahaifin Dr Awwab) ya zama waliyin Dr Awwab.

Hamdala Dr Awwab yayi ta jerowa cikin zuciyarsa jin an shafa fatihar auren shi da Noor sai kuma diramar da zasu ɗeba in ta ji labari. Idanuwansa ya lumshe ya buɗe yayi murmushi.

"Haƙiƙa ka cika min burina Mamman haka ake so ɗa ya bi umarnin iyayenshi ko basa raye. Allah yaji ƙan Mama da Baba."

Ameen mutanen gurin suka amsa dashi ya ƙara da cewa.
"Bani sadakin zan kaiwa Sadiya ta ajiye mata, arziƙinta ne."

Babu musu ya miƙa masa dan bai ɗaukesu kuɗi ba, ya kasa cewa komai kamar wanda aka rufewa baki ido kawai yake zuba musu har suka gama gaisuwa da murna murnan su suka miƙe dukkan su.

"Alhaji mun gode Allah ya saka da alheri."
Alhaji Abubakar yace yayin da ya miƙe, da kallo Alhaji Mamman ya bishi da shi har lokacin zuciyarshi ta kasa tantance masa malallakiyar fuskar.

Yana kallo suka fice ɗaya bayan daya daga falon suna masa sallama har abokansa suka watse kaf, reception da suka haɗa basu samu damar gudanar dashi ba kenan. Ya jima zaune kafin ya miƙe ya nufi cikin gidan sai lokacin bakin shi ya buɗe.

"Ni Sadiya za ta wulaƙanta ta tozarta cikin ɗimbin jama'a, ta ciwa fuska cikin taron jama'a a idon duniya, wallahi dai nayi shari'a da ita."
Faɗin Alhaji Mamman yayin da yake shiga cikin falon.

Amma Jidda da tayi jigum tana jimamin abin da yake faruwa ta ji ya fadi haka ta dubeshi lokacin da yake zama saman kujeran falon.

"Mai kuma tayi? Ita kullum cikin laifi."

"Wannan yaron shege ta turo da Yaya Inuwa dan ta ci min fuska ta saka ni na bashi auren yarinyar nan, har an ɗaura fa. To wallahi kotu za ta rabamu in Alhaji Kashim ya nemi kuɗin shi dan ita ma sai ta biya."

"Dama sai da yar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login