Follow us on social media

Showing 15001 words to 18000 words out of 148866 words

Chapter 6 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

16

zauna saman kujera, ta gaishe sa ya amsa yana cewa.
"Ina Mami?"

"Ta tafi gidan Aunti Zarah."
Nuratu tace tana kashe iron ɗin ta miƙe ta kawo mishi ruwa ta ajiye.

"Zauna magana za muyi dama dan ke nazo."
Tana shirin barin gurin taji yace.

Zuciyarta ne ya amsa mata ta zauna ɗayan kujera babu mutsu tana sauraran shi.
Nutsuwa yayi dan yana son ta fahimce zancensa ta masa fassara mai kyau.



"Nuratu!"

"Na'am."
Ta amsa jin yadda ya faɗa sunan sai taji yafi kowa iya faɗar shi.

"Ina so muyi magana na fahimtar juna amma ban san ya zaki ɗauka ba, Please ki fahimce ni bada wasa nazo ba ko na faɗa miki haka ba. Idan har baki da wani a zuciyar ki, ni Muhammad Al-ameen ina sonki zan aure ki in har kin amince. Ba abin gaggawa bane ko takura, na san kina makaranta kuma sai kin gama za kiyi aure may be ma sai kin shiga wani, ina so ne kawai ki san da zamana in da hali a karɓi tayin soyayyata Please Nuratu."

Ita kuwa in dai haka ake cewa shine so to tabbas tana jin Yaya Al-ameen a cikin ranta da zuciyarta tun bayan rabuwarsu, amma kunyar amsar da zata bashi take ji, lokaci ɗaya tace ta amince taji ba zata iya ba.

"Ke nake saurara ƙanwata, kar kice min dai akwai wanda ya rigani dan ba zan hakura ba sai in da karfina ya ƙare."
Ya ƙarashe maganar yana murmushi.

Cike da kunya Nuratu ta murmusa tana girgiza kai tare da saka hannu ta rufe fuskarta.

"Ka bani lokaci zan yi tunani."

"Wani tunani kuma da lokaci. Nagode miki kawai da kika karɓa tayi na, inshaAllah zaki sameni cikakken masoyi na har abada. Ba zan miki alƙawura ba amma zan yi ƙoƙarin baki farin ciki da kyautatawa a rayuwarmu mu biyu inshaAllah."

Ita dai Nuratu kunyane ya kamata kanta ƙasa tana tana wasa da yatsum hannunta, murmushi mai tsada kwance saman fuskarta, maganganun da Yaya Al-ameen yake faɗa mata suna shiga cikin zuciyarta suna samun guri ɗaya bayan ɗaya.

Yaya Al-ameen ganin bata da niyar masa magana ya sashi tashi dan barinta tayi aikinta.
"Zan tafi gida, nima cikin satin nan zan koma makaranta."

"Allah kiyaye."
Ta iya faɗa mishi ya fita cikin farin ciki.

Nuratu kasa cigaba da aikinta tayi tana juya maganarshi cikin ranta, lokaci zuwa lokaci sai tayi murmushi. Ashe haka so yake. Take tambayar kanta.

Har Mami ta dawo ta lura ƴartan tana cikin farin ciki da nishaɗi, bata tambaye ta ba ta bar abin a ranta.

Ranar Litinin su Nuratu da Walida suka koma makaranta sun zama manyan yan mata.

...

Bayan sati biyu.

Wata ranar Alhamis Mami ta samu baƙoncin Amma Jidda. Kamar yadda take taran ta haka ta tareta cikin farin ciki suka gaisa ta kawo mata ruwa da abinci data girka.

"Har yau kin ƙi zuwa ganin ɗakin yaran nan."

Murmushi Mami tayi.
"Zanje ai ke nake jira kimin jagoranci."

"Haba dai ai baki sanar dani ba, ni ma sai shekaran jiya naje duk na ɗauka kinje sai da naje suke sanar dani."

"Zan je dai amma ba yanzu ba."

"To Allah kaimu. Wata magana nake so mu yi Mamin Rahma."
Amma Jidda tace tana canza hiran.

"Ina jinki, fatan dai lafiya?"
Cewar Mami.

"Lafiya lau, Muhammad Al-ameen ne ya zomin da wata magana, ban yarda da gaske yake ba sai da naga ya tabbatar min da hakan. Auren Nuratu yake nema in har zaki bashi. Na nuna mishi karatu take yace zai iya jiranta, dan har sunyi magana da ita Nuratun tace za tayi tunani, to har yanzu shuru bai samu amsa daga gareta ba, kuma yana so iyaye su san da maganar."

Shuru Mami tayi har Amma Jidda ta gama magana kafin tace.

.....

Vote.
Comments.
Share.

MADUBIN GOBE 9.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

....

"Ba zan hana Nuratu son Al-ameen ba haka ba zan hana Al-ameen auren Nuratu ba, domin na yarda da tarbiyyarshi da nutsuwar shi. Sai dai hanzari ba gudu ba dukkkan su karatu suke mai zai hana a bari su ƙarasa in yaso sai ayi maganar, sai yaje can Nijar ya samu Yaya Muhammad suyi magana."

Amma Jidda ta gamsu da maganarta kuma gaskiyar ta.
"Hakan ma yayi, dama shima cewa yayi a san da zaman shi ne amma zan ƙara tunatar dashi hakan."

"Ba komai sai ya cigaba da neman amincewar Nuratu balle ma ina ga ta amince."

Da murmushi kan fuskar Amma Jidda tace.
"Yaran zamani sai dai muji labari a wajensu bamu san lokacin da suka haɗa kansu ba."

"Wallahi fa."
Cewar Mami tana mamakin wannan lamarin, ko ba komai tayi farin ciki da Muhammad Al-ameen ya nemi auren Nuratu shi da yasan komai na rayuwarta tsakaninta da mahaifinta akan wani bare da watarana dole ya mata gori ba fata take ba.

Suna cikin hira Nuratu ta dawo daga makaranta ta gaishe da Amma Jidda da taji wani kunyarta ya kamata daga gaisuwar ta wuce ɗakinta suka bita da kallo. Jin ana ƙiran sallar la'asar ya saka Amma Jidda yiwa Mami sallama ta tafi.

Da dare Mami da Nuratu suna zaune gaba ɗaya hankalinta a kan kallon da take Mami na mitar ta hanata kallon wa'azi da za'a gabatar, ganin an fita talla ya saka Nuratu kallon Mami.

"Mami ki saya min waya dan Allah, har Ameera tana da waya. Ni kaɗai ce bani dashi."

"Ki samu damar yin hira da saurayinki ko?"

Wani tashi zaune Nuratu tayi ta zauna tana duban Mami ta kasa magana.

"Kin saka min ido kamar zaki cinye ni, ba gaskiya bane. Wato har kun gama magana da Al-ameen baki sanar dani komai ba."

Kunya ne ya kama Nuratu ta kasa magana, wato dai Yaya Al-ameen dagaske yake har ya sanar da Amma dan ta san ita kaɗai ce zata sanar da Mami.
Ji tayi Mami tana cewa.

"Ba zan hanaki soyayya dashi ba ko aure, amma ina da burin kiyi karatu Nuratu ki samu ilimi mai amfani ki tsaya da kafafun ki."

"Kiyi hakuri Mami amma har yanzu ban faɗa mishi hukuncin dana yanke ba, zan sanar dashi yayi hakuri kawai in har hakan zai faranta miki rai, in yi karatu nima ina son hakan."

"A'a, bance ba. Jidda tamin abinda bani da abinda zan saka mata dashi sai aura miki ɗan ta. Ki sanar dashi kin amince in har kina son shi. Maganar waya ina sane dake cikin satin nan nake son saya miki dama."

Kan Nuratu ƙasa tace.
"Nagode Mami Allah ƙaro buɗi."

Daga haka ta maida hankali kan tv a zahiri kallo take cikin zuciyarta kuma tunani take.

...

Haka kuwa a kayi cikin satin Mami ta harhaɗa kuɗaɗen bashin da take bin mutane ta bawa Nuratu tare da jagorancin Rukayya ta rakata ta siyo waya haɗe da gidan layi. Nuratu tayi murna sosai.

"Sai ki saka numbern Yaya Al-ameen ya daina damuna da ƙira dan jin lafiyarki."
Rukayya dake kwance ta faɗawa Nuratu haka yayin da take duba wayar Nuratu.

"Kai sister kin saka min ido, babu komai tsakanin mu fa."

"Hakane kuma fa, shi yasa ya ke damuna da ƙira dan jin lafiyarki. Waye bai san sonki yake ba, Ni kam dai bana son ƙauyen ci, ki saki jiki kuyi soyayya naga dai ba aure za kuyi yanzu ba sai kun gama karatu, in baki nuna mishi kulawa ba can wata zata ɗauke mishi hankali."

"Allah dagaske sister."
Nuratu tace tana neman ƙarin bayani.

"Zauna nan kiga ikon Allah."
Rukayya tace taci gaba da bata shawarwari har da saka mata numbern shi ta mata saving da My Dear kafin ta miƙa mata.

"Zan tura mishi contact naki ya ƙira ki."

Karɓa Nuratu tayi ta saka wayar a charge, Sai yamma lis Rukayya ta tafi gida dan ƙaryar tana da lecture tama Abban ta ya barta tazo, amma dai Amma Jidda ta san inda za tazo.

Da daren ta samu ƙiran Yaya Al-ameen ta ga My Dear raɗau ya fito a screen ɗin, cike da kunya ta ɗauka.

"Ƙanwata."
Ya ce bayan ta ɗauka ta amsa tana gaishesa.
"Ina wuni ya karatu?"

"Lafiya ƙalau sai kewarki, amma yanzu komai yazo da sauƙi tun da munyi waya kullum za ina jin muryarki."

Murmushi kawai tayi yaci gaba da zuba mata zance daga Um sai a'a take bashi amsa har wajen karfe tara kafin suyi sallama ta kwanta.

Tun daga lokacin wanda ya kamata su san san cewa Yaya Al'ameen da Nuratu suna soyyaya sun sani in ka cire iyayen shi da Alhaji Mamman da kuma can Nijar.
Aunti Rahma, Hasiya, Walida sun fi kowa farin ciki in ka cire Ameera da haka kawai bata so dan ko hiran ake barin gurin take dan wani haushin Nuratu take ji, ganin kowa yinta yake, ko gidansu bata cika zuwa ba.

***

Rayuwa sai tafiya yake abubuwa sai faruwa suke a cikin shekara ɗaya daya wuce kusan sau biyar Yaya Al-ameen ya zo Damaturu dan ganin Nuratu, soyayya suke cikin nutsuwa babu wani zurfafawa.
Su Nuratu sun gama makaranta har sun samu cigaba a digiri. Yaya Al-ameen ya gama karatu ya samu aiki a kamfanin MTN a can Zaria.

An saka ranar auren Rukayya, Aunti Rahma ta haifi ɗa namiji, Aunti Hasiya ne shuru har yanzu ba labarin ciki.

Sun shirya event biyu kafin aure da bayan ɗaurin aure za suyi kamu da dinner. Wannan lokacin Mami ta sanar da ƴan Nijar wanda suka samu labari sun zo dan mata kara da murna, hatta Yaya Muhammadu ya zo.

Ana washegarin ɗaurin aure suka shirya kamu a Gat hotel, atamfa su kayi mai shudiyar color da ratsin yellow duk ƴan matan, manya nasu daban, sai na yara. Amarya da ango sunsha kyau abin su cikin nasu kayan.
Taro a kayi cikin nutsuwa ga kawayen amarya da ango da wasu daga wani gari ma sun zo dan abokantakar su da shi.

Nuratu da sune gaba kan komai su shiga su fita cikin hall din ta samu saƙon Yaya Al-ameen.

*"Ki nutsu ki zauna ƙanwata, tun ɗazu sai shiga da fita kike."*

Murmushi tayi ta tura mishi da amsa inshaAllah za tayi hakan.

Waje ta fita dan taro ƙawayenta biyu data gayyata ƴan makarantar su, sun iso sun kasa shiga, suma sunyi ƙoƙarin yin anko dan har mamaki suka bata.

"Kinyi kyau ƙanwar amarya."
Rufaida tace dan ba laifi Nuratu tayi kyau sosai kayan ya karɓi baƙin fatarta.

"Nagode."
Tace tana murmushi da ya saka gefe gefen kumatunta lotsawa ya ƙara fito da kyan fuskarta.

"Ki tsaya muyi hoto gaskiya."
Cewar ɗayar tana ciro wayarta a jaka. Hakan ya saka Nuratu da Rufaida tsayawa ta ɗaukesu, itama ta tsaya da Nuratu kafin a ɗaukesu ta ɗaga tana musu selfie.

"Ya isa Fa'iza."
Cewar Nuratu suka shiga cikin hall ɗin ta nema musu gurin zama.

....

Zafin ƙunar wuta da yaji yana ratsa yatsun hannunshi ya ankarar dashi daga inda yake kallo ya yarfar da sauri yana yamutsa fuska, ya bi sigarin da ko rabi bi sha ba iska ya kwashe yace.
"Oh God."

Cikin motar shi ya koma ya zauna sosai, siffanta da kyakkyawar fuskarta yana mishi yawo.

"She's damn pretty."

Ya furta yana rufe idanuwanshi ya buɗe. Kamar an mintsile shi ya tashi ya fita da sauri ya nufi cikin hall ɗin da zuwansu da abokansu sunyi sunyi ya shiga yaƙi yace zai zauna a waje, wanda ya bashi damar zugar sigarin shi da bai samu sha ba tun safiya. Ya fara kenan ya hango fitowar Nuratu da yaji ta kusa tafiya da numfashinsa da ruhin sa.

Bayan shigarsa cikin hall ɗin ya isa wajen abokai ya zauna yana baza idanu dan hangota ya ganta zaune da ƙawayenta biyu da suka shiga ciki tare, ciki har da ƙanwar shi Rufaida da yayi mamakin ina ta santa. Bata kama da amarya sannan bata kama da ango, shigar jikinta ya bashi tabbacin tana da alaƙa da amarya. Murmushi take yi ya zuba mata ido.

"Mufid!"

Abokin shi na kusa dashi ya ƙira shi jin hankalinshi ya koma wani guri daban. Juyowa yayi ya kalleshi da lumshashshun idanuwansa bai amsa ba.

"Ana ƙiran abokan ango su fito."

Filin gurin ya kalla yaga babu mata wanda hakan bai mishi ba ya girgiza kai alamar ba zai je ba.

Daga haka yaci gaba da kallon in da take, yaga bata gurin ta tashi ta nufi wajen amarya da ango tare da Rufaida da ɗayar da bai su. Bayan ta mata magana suka fita haka shima ya bashi damar miƙewa ya bi bayansu ya samu ta musu rakiya ta juyo dan komawa ciki.

Nuratu tana ƙoƙarin shiga ciki ta samu ƙiran Yaya Al-ameen ta ɗauka tana komawa baya. Tsaye ta same shi ya harde hannunshi saman kirjinshi.

"Kin yi kyau ƙanwata, ban so kina yawo haka ba wasu su ganki."

Kunyane ya kamata tace.
"Sorry Yaya."

"Ya zanyi tunda bikin Rukayya ake ƴar uwa rabin jiki."

Dariya tayi da ya ƙara mata kyau, shi kanshi Yaya Al-ameen da yake kallonta kullum baya gajiya da ganinta. Hira suka taɓa kaɗan ta ce zata koma ciki yace yana jiranta a tashi ya mai data gida tace to.

Ganinta da wani tsaye ya haddasa Mufid jin wani abu a kirjinshi da yaji ya tokare masa zuciya ya kasa ƙarasawa wajenta ya tsaye kallon su har suka gama magana ta zo ta wuce ta gefenshi bata lura ba. Kwakkwaran motsi ya kasa yi ƙarshe ya koma motarshi ya shiga.

Mai yake damunsa akan yarinyar da bata san da zamanshi ba. Yan mata sai dai ya zaɓi na zaɓa ya yaudara amma baya jin komai a kansu akan yadda yake ji yanzu akan Nuratu. Yarinya kowacce irice daga ya mata magana take amincewa ta so shi ya yaudara ya bar su baya jin komai a kan su sai ita bata san ma yanayi ba.

Yana zaune har aka tashi yaga sai fitowa ake ana tafiya ya hangota ta fito ta shige mota suna barin gurin. Sigarin hannunshi da ya zuƙa na uku kenan ya zuge gilashi motar ya jefar ragowar yana jan motar yabi bayansu.

Tafiya suke yana bin bayansu har ƙofar gidan su amarya ya faka motarshi gefe da wanda take ciki kaɗan. Yana gani ta fito ta shige cikin gidan kafin ya ja motar shi yana barin gurin. Gida ya nufa kai tsaye bayan ya kashe motar ya shiga cikin falon da ƙannensa mata kusan biyar ya samu a falon ciki har da Rufaida data jima da dawowa har ta canza kaya.

Ɗakin shi ya wuce yana banka kofar ya saka lock, tunanin mafita kawai yake yadda zai yi ya sameta. Son ta yake a cewar nashi zuciyar da take neman yaudaran shi. Kanshi ya hau caji sosai ganin ciwon kai na neman kamashi ya sashi tashi cikin inda yake ajiye cigarinshi ya ɗauki kwali ɗaya ya fara zuga duk ya cika ɗakin da hayaki.

Bugun kofar ɗakin ake cikin magagi yace.
"Waye zai balla min kofa."

"Uwarka ce, ka buɗe min ƙofar nan."

Bai kashe sigarin ba ya buɗe ƙofar Hajiya Hindatu ta shiga tana maida kofar ta rufe kafin ta juya kanshi.

"Yanzu Mufid duk faɗan da ubanka ya maka baka ji ba sai da ka sake sha mishi sigari a gida."

"To Ummu ya zanyi, tunani ya min yawa shine zan sha dan in samu sauƙi."
Yace yana hura hayakin bakinshi ta toshe hanci.

Cikin kulewa ta kai hannu zata kwace ya hanata. Tana cewa.
"Ubanka kai da tunanin, mai nace maka kayi duk abinda za kayi a layi kar ka kuma yi a gida, yanzu in babanku yazo wuce fa yaji, ka san dai baya son wannan bushe bushe da ka ke yi a gida ko dan ƙannen ka su gani. Bani nan."

"Saura kaɗan bari in shanye daga shi na gama."

Yace ya zuge sauran tas ya murje ƙarshen, tana gani ta ɗauki turare ta feshe ɗakin dashi ta haɗa da room fresh kafin wari da hayakin sigarin ya ragu ta fita.

MAFARIN HARGITSIN.

Vote.
Comments.
Share.

MADUBIN GOBE 10.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.



Mufid Kashim Mufid shine mafarin hargitsewar rayuwar Nuratu. Daga haske zuwa duhun da ya mamaye. Ƙaddarar rayuwarta ya canza.
Ɗa na biyar a wajen Alhaji Kashim Mufid mai kuɗi da ake ji dashi, matan sa biyu Hajiya Hindatu da Batula, Bafulatanin Yola da zama da harkar kasuwanci ya kawo shi Damaturu.
Ƴaƴan Hajiya Hindatu bakwai mata huɗu sai Mufid da mata biyu da suke binshi. Ganin duk mata take haifa Alhaji Kashim ya auri Hajiya Batula da Allah ya azurta itama mata ta haifi mata gudu huɗu.
Ya aurar da yayun Mufid da ƙanwar shi ɗaya saura Rufaida, Suwaiba, Zakiyya, Sadiqa, Khadijah.

MKM laƙabin shi kenan, sangartaccen yaro da iyaye suka jawo masa tsabar gata da kuɗi da suka nuna mishi, shi ɗaya ne namiji a gidan da Allah ya azurta Alhaji Kashim Mufid dashi hakan yasa komai yake so yake masa tun yana ƙarami haka ɓangaren Hajiya Hindatu itama sai abin da yaso.

Bayan gama karatunshi ya turashi ƙasar waje dan cigaba, ba kamar sauran ƴan uwansa mata ba da a Nijeriya su kayi suna gamawa ya aurar dasu.
Zuwan Mufid ƙasar waje ba idon iyaye shine silar fara lalacewarsa ya haɗu da abokan banza, sune zuwa party, gidan rawa har ya zama sun koya mishi Shaye-Shaye banda neman mata da suke yi suna ƙoƙarin koya masa ya nuna sam baya so dan ƙyama yake.
Dalilin ƙara lalacewarsa kuɗi da Alhaji Kashim yake tura mishi da zaran ya nema, hakan yasa ya watsar da karatun ya faɗa harkar duniya, duniyarsu suke ci da tsinke.

Shekaru shida yaci a ƙasar ganin bashi da niyar kammala karatun ya saka Alhaji Kashim bin diddigi ya samu labari ba karatu yaje ba sai tsiya da yake tsulawa. Alhaji Kashim Mufid yaji baƙin ciki haka ya tura mishi kuɗin jirgi sau biyu ya dawo yana cinyewa yana kashewa, ana uku ya dawo dakyar dan alƙawarin yayi ba zai ƙara tura mishi ba sai dai talauci ya kashe shi.

Ranar daya dawo Hajiya Hindatu taga tashin hankali ganin tilon ɗanta ya zama abinda ya zama, banda jerin ɗan kunne harda sarƙa da zobuna kamar ɗan hip hop, hatta ga ƙannen sa tsoronsa suke ji dakyar suka fara sakewa dashi.

Bayan dawowar shi Alhaji Kashim bai hakura ha ya nema mishi wani makarantar ko zai yi karatun amma a banza dan wataran in ya fita sai sha biyun dare zai dawo a buge dan har lokacin bai rabu da Faisal da AA ba abokansa da suka yi karatu a waje.
A makaranta suka haɗu da Sufyan mijin Rukayya da wasu ɗalibai da ba mutunci yake dasu ba sai ya kama, shi da Sufyan ma mamakin abokantakar su ake dan hali ya bambanta.
Abokantakar Mufid da Sufyan ya saka Sufyan ma Mufid wa'azi da a hankali ya rage saka ɗan kunne da sarƙa da shan sigari gaban mutane sai ya ware kanshi.

Sufyan ya gama karatu ya bar Mufid da kwata kwata bashi da niyar yi hakan ya ƙara mai da Mufid ruwa tsamo tsamo ya zamto tantiri a makaranta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login