Follow us on social media

Showing 45001 words to 48000 words out of 148866 words

Chapter 16 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

34

mai Shari'a ina neman alfarma a bamu dama mu kawo namu shaidun zuwa wani zama tun da masu laifi sun ce basu aikata ba. Sannan ina rokon koto da ta ba da belin masu laifi."

Rubuce rubuce alƙali yayi ya ɗago yana dubansu.

"Mai ƙara yana da shaidu, wanda ake ƙara ta ɓangaren su basu amsa laifinsu ba kuma basu da shaidu. Kotu ta ɗaga wannan Shari'a zuwa nan da kwana goma ana fata zuwa zama na gaba za su zo da shaidunsu. Sannan kotu ta bada belin masu laifi."

Surutu ne ya kaure cikin kotun, Nuratu tana jikin Maminta tana zubar da ruwan hawaye. Ta yarda da maganar Mami cewa shari'a da mai kuɗi sai an dage. Mami da yaranta duk sun sare ganin tun farko an fara wasa da hankalinsu.

Alhaji Mamman dan neman burge idon jama'a ya fara faɗa ga masu laifi an kasa ɗaukar hukunci wannan ai ƙaryace.
Haushin maganganun shi ya saka Mami tashi ta fita tana riƙe da Nuratu bayan alƙali ya bada izinin fita. Haka sauran ma da suka zo dalilinsu duk suka fita.

"Ya haka Barrister Affan?"
Cewar Dr Sadiq dan Dr Awwab da Col. Ahmad kasa cewa komai su kayi tun a gurin har zuwa fitansu suna tsaye bakin floor na gurin. Yaya Al-ameen da shi kuma ya bi bayan su Mami bai tsaya gurinsu ba.

"Kar ku damu, wasa suke so suyi da hankalinmu, zama na gaba in har suka kasa bayyana shaidunsu zamu bayyana namu, dama da wuya yau a gabatar da komai a yanke hukunci, muyi fatan su rasa shaida ko ɗaya kuma su amsa laifinsu dan hakan shi zai bamu damar gabatar da komai."

"Ka tabbatar da haka."

Col. Ahmad yace, Barrister Affan ya ɗaga masa kai. Dr Awwab kasa magana yayi fuskar Nuratu yake gani lokacin da take fitar da hawaye, bai ƙi ace ya sameta ya lalleshata ba ya nuna mata cewa komai zai wuce.


...

"Mami na hakura, na barsu da Allah, shi zai saka mini."

Nuratu tace tana kuka da tun dawowarsu ta kasa yin shuru kowa yana faɗan albarkacin bakinsa tayi shuru tana jin su.

"Ai basu isa ba wallahi, akan me za ki ce kin hakura, mu bari mu ga zuwa zaman gaba, inshaAllah zamu samu nasara."
Muhsin yace cike da faɗa. Kowa na jimamin abinda ya faru a koton.

***

"Cheers Oga Sir."

Faisal yace yana miƙa Barrister Auwal cup cike da juice ya karɓa yana kurɓa cike da farin ciki. Kuɗi sosai Alhaji Kashim ya bashi bayan dawowarsu daga kotun ganin tun yanzu an fara samun nasara.

Mufid da suka hanashi cewa komai ya koma gefe ya saka musu ido, ƙarshe ya miƙe ya fita a falon Daddyn shi ya shige ɗakin shi, hayaki ya busa kafin ya zube saman gadonshi. Basu san yadda yake son jin Nuratu a zuciyarshi ba da ba zasu hana shi karɓar laifinshi ba.

.....

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE 24.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

...

Tun da ya dawo ya zube saman kujeran falon ya kasa samun sukuni a zuciyarshi, fuskarta kawai yake yawo a kanshi da ƙwaƙwalwarsa, zuban hawayenta jin su yake tamkar ruwan zafi. Ji yake ina ma yana da dama da ya nuna mata itama mace ce tamkar kowa, tana da gata da komai.

"Awwab lafiyar ka ƙalau?"

Ya tsinci muryar Ummi da ta jima a saman kanshi bai san da zuwanta ba, idanuwansa ya buɗe ya kalleta da su.

"Babu komai Ummi, gajiya ce kawai."

Zama tayi dan bata yarda dashi ba.

"Yanzu Awwab har ya kai ka fara ɓoye min damuwa rka?"

"Ummi ki yarda da ni, gajiya ce."

Daga haka ya miƙe tare da ɗaukan Hanan data shige jikinshi bayan kwanciyar shi saman kujera yana jinta ya kasa mata magana a haka bacci ya ɗauketa.

"Sai da safe Ummi."

"Allah kai mu."
Tace ta bishi da kallon mamaki.

Gidansa ya nufa yana isa ya kwantarta saman gadonshi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya kwanta kusa da ƴarshi bacci ya ɗauke shi.

***

"Ahmadi ya maganar mu ne?"

Faɗin Abban Col. Ahmad bayan dawowarsa daga Damaturu ya zo gaishe da mahaifinsa.
'Kullum magana ɗaya dai.' Yace a ranshi a zahiri yace.

"Abba ina nan ina dubawa ne, a taya mu addu'a."

"Kullum muna yi Ahmadi, kai ɗin ne kullum kamar yaƙice ka ake daga mata. Ko dai sun maka wani abun ne?"

"A'a Abba, ina dubawa dai."
Col. Ahmad yace yana murmushi jin maganar Abban shi.

....

Kafin zuwan kwana goma Mufid da su Faisal rayuwarsu suke cikin jin daɗi tamkar babu komai, yau sune club gobe zuwa party, ƴan mata kuwa sai sai abinda ya ƙaru, ban da Mufid da tun farko hakan bai dame shi ba sai dai ya rage zafi.
Barrister Auwal duk inda zai shiga ya samu ya lalata shari'ar abin ya gagara.

Nuratu tun ranar bata ƙara ƙoƙarin fita ba dama ba fitar take yi ba tun da suka dawo daga Maiduguri. Kullum tana ɗaki ko filin gidan bata fita, kullum cikin tunanin zaman yadda shari'ar su zata kasance. Mami na bakin ƙoƙarinta ganin ta rage shiga damuwa.

***

Zuwan kwana goma ya kama ranar talata. Misalin ƙarfe biyu aka cika kotun dan jin yau kuma mai za'a gudanar.

'Court!!!'

Aka ce zuwan alƙali aka miƙe ya zauna kafin kowa ya zauna.

Alƙali yace.
"Rejista yau me muke da shi?"

Rejista yayi gyaran murya yace.
"Ya mai girma mai shari'a yau muna da case number YB/CV/UPC/20/2018 tsakanin Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi Faisal Tahiru da Nuratu Mamman Bashir, Shari'a ne na fyaɗe."

Dafe kai alkali yayi ya miƙe tsaye cikin ɓacin rai.

"Case na fyaɗe, case na fyaɗe. Kullum case da ake gudanarwa a yanzu kenan, a kalla a rana sai munyi shari'ar case na fyaɗe sama da biyar. Wai mai yake faruwa a duniyar yanzu da aka mai da fyaɗe ruwan dare, ba'a bar ga ƙananan yara ba ba'a bar ƴan mata ba wasu har matan aure ba su bari ba. Mai yake faruwa ne? Maza mai ku ke buƙata da yake saka ku ke aikata haka?
Bakwa tunanin yaran nan da halin da za su shiga, bakwa tunanin dilmeye musu farin cikinsu da rayuwarsu, kun mai da hasken su zuwa duhu, dalilin haka rayuwar yara mata dayawa ya lalace.
Waye sanadi?
Ku ne, kun rusa musu rayuwa kun ɓata musu tarbiyya, Future na su da komai na su, suyi aure basu da nutsuwa da kwanciyar hankali, yau gori, gobe zagi, faɗa daga nan saki ya biyo baya sai lalacewar aure.
Dan Allah na roƙeku da sassauta wannan abinda kuke yi. Wace irin rayuwa ku ka ɗaukarwa kan ku? Ko kuna tunanin in kun lalata ya'yan wasu naku yayan barinsu za'a yi.
Annabi yace duk abinda kayi wa ɗan wani kai ma ɗanka za'a mishi."

Daga haka alƙali ya koma ya zauna yana goge hawayen idanuwanshi da kowa gurin jikinsa yayi sanyi banda wanda bai shiga kansu ba.

"Rejista cigaba."
Yace bayan ya saita kanshi.

Investigator Lawan ya miƙe ya fara bayani.
"Ya mai girma mai shari'a a zaman da ya gaba mun sanar muna da shaidu bisa laifin da Mufid Kashim Mufid da abokansa suka aikata bisa fyaɗe da su kayi wa Nuratu Mamman Bashir. We have four witnesses PW1 PW2 PW3 PW4."

"Wanda ake ƙara yana nan?"
Alƙali ya tambaya.

"Eh, Mufid Kashim Mufid Abdullahi Abdullahi da Faisal Tahiru."
Faɗin rajista. Babu musu suka miƙe suka shiga cikin Doc suka tsaya.

"Investigator officer cigaba da bayanin ka."

"Mufid Kashim Mufid, Abdullahi Abdullahi, Faisal Tahiru a rana na ashirin ga watan Satumba sun aikata laifin fyaɗe a wani gida dake red bricks, misalin karfe takwas na dare,  sun danne yarinya mai suna Nuratu Mamman Bashir sun sadu da ita. An kamasu anyi arresting ɗinsu an kawo su police station mun tuhume su sun aika suka ce eh. Mufid ne kuma ya amince ya yarda ya aikata ya saka hannu."

Alkali ya dube su Mufid.
"Mufid Kashim Mufid kai ka aikata wannan abin?"

"Eh ni na aikata."
Faɗin Mufid kai tsaye.

Investigator yana nuna Mufid papern da Mufid ya saka hannu ya ce.
"Can you recognize that?"

"Yes by my handwriting."
Cewar Mufid dan ya gane papern.

Investigator ya miƙawa rejista takardar da Mufid ya saka hannu ya koma ya zauna. Rajista ya miƙawa alƙali ya karɓa ya karanta ya gani.

"Lauyan wanda ake ƙara kana da abin cewa?"
Alƙali ya tambaya.

"Eh ya mai girma mai Shari'a."
Barrister Auwal yace ya miƙe ya isa gurin su Mufid.

"Malam Mufid Kashim Mufid. Ko zaka sanar damu daren ranar da abin nan ya faru da misalin ƙarfe biyar kana ina?"

"Ina ƙofar gidansu Baby Noor."

"Babu in da ka je kafin zuwanka gidansu."

"Babu, hasalima na saba zuwa kofar gidan dan jiran dawowarta ko fitar ta."

"Hakane ka tabbatar?"

Kai Mufid ya daga ko a jikinshi domin ya riga ya rantse gaskiya zai faɗa ko dan ya wanke kanshi gurin Nuratu ta aureshi.
Barrister Auwal ganin Mufid bashi da niyar bashi haɗin kai ya koma ya zauna kar yayi wani abun da zai saka ya rasa aikinshi.

Bayan zaman Barrister Auwal alƙali ya ɗago yace.
"Lauyan mai ƙara kana da abin faɗa?"

Babu musu Barrister Affan ya miƙe ya gabatar da kanshi yana ƙarawa da.

"Ya mai girma mai shari'a zamu fara gabatar da PW1 namu wato shaida na farko, shine investigator Lawan."

Alƙali ya bada damar investigator Lawan ya miƙe ya shiga cikin Doc. Barrister Affan ya isa gurinshi dan masa tambayoyi.

"Investigator ko zaka sanar damu abinda ka sani."

Hulanshi ya cire ya gabatar da kanshi yana cewa.

"Ni sunana Lawan, Misalin karfe takwas na dare muna cikin station har wasu sun fara ƙoƙarin tafiya gida saboda ruwa da ake yi ranar daga baƙin magriba zuwa karfe takwas, muka samu baƙoncin wannan bawan Allah a rikice yake cike da tashin hankali ya sanar damu an sace yarinya, duk tsammanin mu kidnapping ne har muna cewa ai war haka sun tafi da ita inda za su tafi sai ya sanar damu ya ga inda su ka kaita wato gidan da suka shiga.
Anan muka ɗauki mota mu ka bi bayansu har da Ogan mu DPO Salisu, bayan isar mu, muka samu gidan a kulle. Da loud speaker mu kayi amfani muka tsoratar su suka fito aka kama su.
Ni da Col. da Ɗan sanda John ne muka shiga gidan dan duba yarinyar anan muka samu sun riga sunyi raping ɗinta har ta suma. Rasa taimakon da zamu mata Col. Ahmad yasa aka ƙira motar emergency ta zo ɗaukarta. Daga nan aka wuce da ita asibiti yaran kuma aka wuce dasu station."

Bayan gama bayanin investigator Lawan aka nemi Barrister Auwal yana da tambaya yace a'a.

"Shaida na biyu?"
Alƙali ya buƙaci a gabatar ganin Barrister Auwal bashi da tambaya.
Barrister Affan ya miƙe yana cewa.

"Ya mai girma mai shari'a shaidar mu na biyu shine Col. Ahmad."

"Col. Ahmad ko zaka gabatar da kan ka."
Cewar alƙali ya buƙaci haka.

"Mai ya faru ko ince mai ka sani game da hakan?"
Barrister Affan ya tambayi Col. Ahmad.

Col. Ahmad da ya shiga cikin Doc idonshi akan Mufid yace.

"A rana na Ashirin ga watan Satumba misalin ƙarfe shida na yamma, na shigo garin Damaturu daga Kano, ranar anyi ruwa daga misalin ƙarfe biyar zuwa takwas na dare. Na zo wuce ta titin Maiduguri dan ba Damaturu na zo ba Maiduguri zan wuce. Anan ban ankara da zuwan Nuratu ba na bugeta da mota na, na fito dan duba halin da take ciki na samu ba taji wani ciwo ba, ina cikin tambayarta lafiya na ga zuwa wannan yaron yana cewa wai motar ne bata tashi ba sai yanzu.
Ban yarda da abinda ya faɗa ba ina ƙoƙarin isa wajenta waɗannan biyun suka iso gurin a mota suka ɗauketa da ƙarfi suka jefata cikin motar su.
Na bisu a motana har gidan da suka kaita kafin in isa sun kulle get ɗin gidan, nayi nayi in buɗe ko su buɗe sunƙi hakan yasa na isa police station mafi kusa na sanar dasu muka dawo tare dasu, kafin mu zo sun riga sun yi abinda za suyi da ita."

Shuru cikin kotun ya ɗauka kowa yana sauraran Col. Ahmad har ya gama. Barrister Affan yace.

"To mungode Col. Ahmad."

Daga haka Barrister Affan ya zauna. Mami da kowa daya danganci Nuratu hatta ita Nuratun jikinta yayi sanyi jin Col. Ahmad da taimakon da yayi ƙoƙarin bata.

"Lauyan mai kare mai laifi kana da abin faɗa?"

Cewar alƙali. Barrister Auwal ya miƙe ya isa gurin Col. Ahmad. Ba dan kar Alhaji Kashim ya ga gazawar shi ko ƙin sallamar shi ba da babu abinda zai saka shi tambaya bayan kuma Mufid ya amsa laifinshi ga kuma shaidu an kawo.

"Ahmad ko ince Col. Lokacin da ka fito dan dubawa ko ka bugeta shi Mufid ɗin ya iso gurin? Ko sai da ka fito ya iso? Kuma kana gani suka ɗauketa ba kayi yunƙurin taimaka mata ba a matsayin ka na Col. Ko baka yawo da bindigar ka?"

"Bana yawo da shi, ko in ce yana cikin mota ban fito da shi ba, kamar yadda na faɗa uzuri ya kawoni Maiduguri a Ibadan nake aiki. Lokacin dana fito dai dai lokacin Mufid ya iso, kafin in musu magana sauran suka iso."
Col. Ahmad yace ganin kamar tambayar rainin hankali Barrister yake mishi.

"Shikenan mungode."
Barrister Auwal yace ya koma ya zauna, aka sallami Col. Ahmad yaje ya zauna.

"Shaida na gaba."
Alƙali yace yana rubuce-rubuce.

"Let go to PW3 Dr Sadiq."

Bayan Barrister Affan ya miƙe ya ƙira Dr Sadiq. Dr Sadiq ya miƙe ya shiga cikin Doc, Barrister Affan ya miƙawa rajista shaidan asibiti da Dr Sadiq ya basu original kafin ya koma gurin Dr Sadiq.

"Dr Sadiq ka sanar damu iya gaskiyar abinda ka sani bisa yarinyar da aka kawo maka ranar ashirin ga watan Satumba misalin ƙarfe tara na dare."

"Ni sunana Dr Sadiq ma'aikacin likita a asibitin General, rana na ashirin ga watan Satumba da misalin karfe tara an kawo min yarinya mai ɗauke da case na fyaɗe, a yanda na dubata nayi examining nata, akwai penetration(shigar da gaban shi cikin gabanta), akwai using of forced (ƙarfi), akwai sexual intercourse (Jima'i) wato saduwa, akwai ejaculating (inzali) wato fitar da abu daga jikin shi zuwa jikinta."

Bayan sauraran bayanin Dr Sadiq Barrister Affan yayi godiya ya koma ya zauna. Barrister Auwal ya miƙe ya isa wajen Dr Sadiq.

"Haka kawai aka kawo maka yarinta aka ce an mata fyaɗe sai ka hau dubata. Baka sanar mana da su waye suka kawota ba?"

"Ƴan sanda ne biyu, sai Col. Ahmad wanda sai daga baya na san tare yake da su, kuma dama kowa ya sani in dai an kawo case na fyaɗe mu likitoci bama karɓa sai ƴan sanda sun shiga ciki."

Ƙarya ta ƙare! Cewar Barrister Auwal a zuciyarshi ya ma Dr Sadiq godiya ya koma ya zauna aka sallami Dr Sadiq ya koma ya zauna.

"Shaidarmu na gaba shine Dr Awwab PW4 ya mai girma mai Shari'a."
Barrister Affan yace yana miƙewa yana murmushin cin nasara.

"Ina Dr Awwab?"
Faɗin alƙali.

Dr Awwab ya miƙe ya shiga cikin Doc ya gabatar da kanshi. Barrister Affan ya isa kusa dashi.

"Kai ne Dr da ka ci gaba da kula da Nuratu a ɓangaren masu fama da cutar ƙwaƙwalwa."

"Hakane! Dr Sadiq shi ya turosu gurina da duk wani bincike na dangane da abinda ya jawo mata hakan. Ba komai bane illa firgici da ta shiga bisa abinda ya sameta ya haddasa mata fita hayyacinta. Amma kuma da taimakon magani da taimakon Allah muka samu ta dawo cikin hankalinta, sannan kuma har yanzu tana kan magani kuma zata daɗe tana amfani da shi zuwa shekaru biyar zuwa shida."

"To mungode Dr Awwab."
Faɗin Barrister Affan.

"Lauyan wanda ake kara yana da tambaya?"
Alƙali ya nemi sani.

"A'a babu ya mai girma mai Shari'a."
Barrister Auwal yace yana share gumi.

"To mungode Dr Awwab zaka iya komawa ka zauna."

Aka bashi dama ya koma ya zauna bayan ya kai kallon shi kan Nuratu da ta kwantar kanta a kafaɗar Mami rabin hijabinta ya rufe fuskarta, hawaye ne yake zuba a kumatunta take sharewa.

Shuru cikin kotun ya ɗauka kowa da abinda yake sakawa a rai in ka cire Hajiya Hindatu da Alhaji Kashim da suna ji suna gani za'a hukunta ɗansu akan wata yar talakawa abinda ba'a taɓa yi ba.

Nuratu kuka take ƙasa ƙasa haka sauran yayunta da zuciyarsu ya karaya tamkar yanzu abin yake faruwa. Alhaji Mamman sai baza hanci yake za'a hukunta Mufid ko ba komai duniya ba zata zageshi ba akan bai zo ba.

"Za'a je hutu ayi sallah a dawo karfe biyar."

Alƙali ya bada umarni dan samun lokaci na duba duk takardun shaida.

...

#vote
#comment
#share

MADUBIN GOBE  25.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

....

Bala'i da masifa Alhaji Kashim yake zubawa Hajiya Hindatu tana taya shi, duk laifin ɗan su ba'a taɓa hukuntashi, amma yau gashi har ana maganar zartar da hukuncin da ya dace da shi. Cewa suke basu yarda ba za su ɗaukaka ƙara, Barrister Auwal dake zaune shima ya samu nashi rabon zagin bai kulasu ba dan shi kam yayi iya ƙoƙarin shi ya kasa.

Can Nuratu sallah take tayi tare da addu'ar Allah yasa a hukunta Mufid da abokansa dai-dai da abinda suka mata, haka Mami ma da sauran da suke tare dasu.

...

Ƙarfe huɗu da mintuna aka dawo kotun, bayan shigowar alƙali kowa yayi shuru ya na sauraron bayanin alƙali.

"Kamar yadda shaidu suka bada shaida gamsashshiya bisa kan masu laifi, kotu mai adalci tayi amfani da ayar da Allah ya faɗa a cikin Suratu (Nur) aya ta biyu inda yake cewa 'Mazinaci da mazinaciya hukuncinsu shine bulala ɗari in har sun kasance basu da aure.'
Aya na uku yace 'A kowa shaidu huɗu wanda in har basu bada shaida dai-dai ba a musu bulala tamanin.'
To allahamdulillahi mun samu huɗu dai-dai kuma kowa ya bada shaida gamsashshiya da kotu tayi amfani da su wajen hukunta mai laifi.
Kotu tayi amfani da wannan ayar ta biyu zata hukunta Mufid Kashim Mufid, Faisal Tahiru da Abdullahi Abdullahi bisa laifin fyaɗe da suka aikatawa Nuratu Mamman Bashir, fatan wannan hukuncin ya zama izini ga masu yin wannan laifin.
Sannan ina jan hankalin mutane musamman ƴan sanda da ake sanar daku case na fyaɗe ya faru, da ku ke ɓata lokaci gurin zuwa inda abin ya faru wala a gida ko unguwa ko asibiti. Hakan yana jawo duk shaidar da ake samu ya goge, likitoci kuma kuna naku ƙoƙarin amma ku dage.
Sai ku iyayen yara ko wanda abin yake faruwa a kansu. Ke budurwa ko yarinya ƙarama ko babba, an miki fyaɗe ba za ki iya sanarwa a gida ba har sai abin yayi tsamari saboda kina tsoro a gida aji kar a ɗaura miki laifi.
Iyaye mata da zaran kin ga an yiwa ƴarki fyaɗe sai ki bi ki ɓoye, wani lokaci har uba baya sani sai ciki ya bayyana sannan zaku taho kotu cewa anyi wa ƴarki fyaɗe har ciki ya bayyana.
Ta ya?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login