Follow us on social media
Showing 126001 words to 129000 words out of 148866 words
Chapter 43 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
gora ɗaya da cup ta dangwarar ta wuce ɗakinta. Girgiza kai Amma tayi ta miƙe.
"Ina zuwa minti ɗaya."
Daga haka ta nufi ɗakin Ameera. Ruwan Nuratu ta zuba a cup ta miƙawa Dr Awwab, kai ya girgiza yace.
"Ki sha."
"Ka fara."
Karɓa yayi ya kurɓa ya miƙa mata ta amsa dai-dai Amma da Ameera sun fito. Ranta a haɗe ta zauna, ita ma Ameera ta zauna tana cewa.
"Ina wuninku."
Daga haka bata ƙara komai ba su ka ci gaba da zama sai Nuratu da Amma suke hira. Dr Awwab wayarsa yake dannawa, yayinda Ameera ke musu kallon ƙasan ido tana taɓe baki.
Kusan mintuna Dr Awwab ya musu sallama zai je ya dawo zuwa azahar. Bayan fitarsa Amma da Nuratu suka wuce Kitchen ta taimaka mata suka haɗa abincin rana. Suna gamawa Rukayya da Walida suka yi sallama.
Wani ihu Nuratu ta saka ta fito da gudu ta ɗale kan Rukayya ganin Walida cikinta ya fito.
"Allah sarki ni Walili."
Faɗin Walida ganin ta ƙi rumgumeta.
Sakin Rukayya tayi ta ɗan rumgumo Walida.
"Ke ɗince kin fara zama kaya."
Dariya suka kwashe da shi, Walida tayi wani dariyar mugunta.
"Yarinya kina layi. Waya sanima ko Dr yayi ajiya a wannan shafaffan cikinki."
Harara Nuratu ta watsa mata tana yin gaba, Rukayya ta kwashe da dariya tana cewa.
"Da gaske Walida maganarki ya zama gaskiya. Ji daga magana."
"Kwa sani magulmata."
Ta faɗa tana ɗaukar yara ƴan biyu na Rukayya mace. Wasa ta fara mata tana tambayarta, yaran dai sun ganeta dan suna da ɗan wayo, namijinne ma ya nuna rashin sabo sai kuma ya sake ganin ƴar uwarsa ta sake da ita.
Hirane ya barke tsakanin ƴan uwa, ƙawaye, makusantan juna da suka yi kewar juna. Rabin hirar duk tsokanar Nuratu suke, sai dai ta girgiza kai tana dariya, na haushi kuma ta hararesu. Har azahar suna falon, su dai sunyi mamakin ganinta cikin gidansu, amma sun bar abun a ransu, bayan hakama sun bari akan kafin dawowar Abbansu za ta tafi.
Amma dai cikin ɗaki ta tafi ta barsu dan basu waje.
Har azahar suka wuce ɗakin Amma suka yi sallah, kafin su fito. Zuwan Aunti Hasiya da Rahma ne tare da yaransu ya saka Nuratu hawaye duk suna mata dariya. Ta ɗauki wannan yaron ta sauƙe, ta sumbaci wannan duk son yaran yayunta take.
"Kena dai kin kusa samun naki."
Walida tace tana kai abinci bakinta.
Shuru Nuratu tayi tamkar ba da ita ake ba ta ci gaba da bawa ƙaramar ƴar Aunti Hasiya abinci.
"Ke kam dai Allah ya shirya ki Walida. Gaba daya kin ƙara fitsarancewa ga sa ido."
Faɗin Aunti Rahma.
Aunti Hasiya da sai lokacin ta saka baki tace.
"Ta ji me ake ji a auren ba dole ba, tasan sirrin. Ta sawa autan Mami ido. Ita ma gata kamar me yaron ciki."
Dariya suka sanya gaba ɗaya ban da Nuratu kamar tayi kuka tace.
"Aunti wallahi sharri suke mini. Ni yauma na fara sallah."
"Sallah ki Godewa Allah da ya baki kyauta ba."
Faɗin Rukayya tana yin wani dariyar.
Aunti Rahma Nuratu ta kalla, tasan ita kaɗai zata fahimceta ta kwaceta wajensu. Hakan kuwa yayi tasiri, Aunti Rahma ta haɗa rai tana cewa.
"Kai ya isheku kun takurawa autan Mami. Ko laifine in tayi cikin, ai ba'a kanta aka fara ba, ko kuma dama mun kaiwa Doctor ne ya sata a gaba yana kallo. Kun san dai dole nan da wasu watanni Mami ta samu jika a wajen autarta."
Ta ƙarasa maganar tana murmushi. Nuratu dai taga ta kanta tace. Haka suka yi ta mata daga ƙarshe Aunti Hasiya ta kwaceta a gurinsu ta tsare su. Duk da kowa ƙasan zuciyarsa cike ya ke da tambayoyi akan zuwan Nuratu gidan kuma sunsan tsakaninta da Abbansu.
Ƙarfe biyu Alhaji Mamman ya dawo gidan daga kasuwa wanda ba laifi kasuwa ya fara dawowa. Amma Jidda ne ta sanar musu. Gaba ɗaya suka dungama da yaransu zuwa gaisuwa, anan suka tarar Muhsin da ya dawo daga aiki. Da fara'a ya amshi yaransa abin alfaharinsa. Ɗaya bayan ɗaya suka gaishesa, abin mamaki wajensa kai tsaye Nuratu ta nufa ta zauna kusa da kafafunsa.
Kanta ya shafa yana mai da hankalinsa gaba ɗaya kanta.
"Autar Mami kun iso lafiya?"
Kai ta ɗaga masa tana cewa.
"Lafiya lau. Na sameka ƙalau."
Shi ma ɗaga mata kai yayi, daga haka ta ƙarasa wajen Muhsin suka gaisa. Yana tambayarta gida. Gurinta ta koma kusa da Abbansu.
Kallon yaran yayi ya hango tsagwaran mamaki da al'ajabi saman fuskokinsu, kuma yasan suna buƙatar ƙarin haske. Ban da ma dalilin wannan taruwarsu anan gaba ɗaya.
..
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 57.
Pharty Bb.
Wattpad Pharty BB.
***
"Kun ga duk abun da ba ku tsammaci gani ba ko? To haka Allah yake abun sa. Sannan komai da ya faru ƙaddara ce da son zuciya. Babu maganar tone tone akan abin da ya wuce. Magana ta gaba shine maganar da mu ka yi kwanaki da ku akan Mamin ku, na ji shuru."
Dukkansu farin ciki ne ya mamaye zuƙatansu ganin uba da ƴar sun sasanta kansu, abin da suka jima suna burin gani.
"Abba za mu mata magana Insha Allah, za a samu mafita da yardar Allah."
Aunti Rahma fada. Nuratu da ta gano kan zancen ta ƙara da cewa.
"Idan ma danni take ji zan sameta."
Anan kowa ya dinga bada ta shi shawarar har Muhsin da baya yawan magana shi ma ya saka baki. Haka dai har kusan la'asar kafin suka koma ɓangaren Amma Jidda da ba tasan me ake tattaunawa ba. Muhsin da Abbansu su ka wuce masallaci.
Bayan sallar la'asar da su ka gabatar Nuratu ta ɗauki wayarta ta lallaɓa ta fice a ɓangaren. Mijinta ta ƙira cike da kewarsa tana tambayarsa ya ci abinci.
"No Babyna."
Ya faɗa yana daga kwancen da ya ke cikin katafaren hotel ɗin da ya kama.
Narkar da murya ta yi ta ce.
"Haba dan Allah Hayat, ka daura ka sa wani abu a cikinka."
"Haka aka damu da ni Noor?"
"Sosai ma Hayati."
Ta basa amsa cikin kulawa.
"Noor."
"Hayat."
Su ka faɗa ta basa amsa tsammaninsa ko suɓutar baki tayi, shuru dukkansu suka yi suna jin hucin numfashin juna cike da saƙwannin da yake kai kawo a zuƙatansu. Dr Awwab ne kaɗai ya fahimci abin da su ka faɗa. Cikin murya ƙasa ya ce.
"Kece haskena ni ne rayuwarki *NoorHayat*."
Nuratu da ba tasan hakan ba sai yanzu, murmushi ta yi da ya ji sautinsa.
"Tabbas hakane."
"Akwai babban tukwuici da zan ba ki."
Dariya ta kuma sawa tace.
"Godiya nake ranka daɗe."
Kusan mintuna goma suna wayar ya tambayeta ta ci abinci kafin shi ya ci ta basa amsa da eh, anan suka yi sallama bayan ya tabbatar mata zai ci. Daga nan ta tafi inda za ta je bayan ta tabbatar babu mai kallonta, kuma tasan tana da ishashshen lokaci.
Sai bayan magriba Dr Awwab ya dawo gidan. Har ɓangaren Abba aka masa rakiya suka gaisa kafin a kai sa ɓangaren baƙi, abincin da Amma Jidda ta haɗa ta saka Nuratu ta kwasa ta kai masa. Da kunya dai haka ta ɗauka dan ma su Rukayya sun koma gidajensu bayan sunsha hira ta musu alƙawarin za ta je kafin su koma.
Abincin ta ajiye saman center table ta fara ƙoƙarin zuba masa ya riƙo hannunta. Fizgota ya yi ta fado jikinsa ya rumgumeta.
Ba ta yi yunƙurin hanasa ba dan tasan babu mai shigowa sai ma ƙara lafewa da ta yi a jikinsa, suna shaƙar turaren juna.
"Za mu je gidan Mami fa."
Yace yana ɗago fuskarta. Fara'a ne ya bayyana a fuskartan.
"To ka ci abinci sai muje."
"Za ki bani a baki?"
"Idan wani ya shigo fa."
Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa dan zuba masa.
"Mijinki ki ke ciyarwa."
Murmushi ta yi ta ɗauki plate ta zuba masa ta saka spoon ta koma saman kujeran gefensa ta zauna, plate ɗin ta ɗaura saman cinyarta ta saka hannu ta ɗauki spoon. Ganin haka ya sa ka Dr Awwab riƙo spoon ɗin yana mata nuni da hannu da ido. Fahimtar haka ya sa ta tashi ta wanko hannunta ta dawo ta zauna. Hannunta ta saka kamar yadda ya so ta ɗeba ta kai bakinsa, buɗe bakin yayi ta zuba masa ya fara ci. Bai tsammaci za ta iya basa bai sai ga shi ta basa mamaki.
Tana bana basa yana ci suna hira sama sama tana basa labarin yayunta. Kaɗan ya ci yace ya ƙoshi ta dakata.
"Saura ke."
Ya faɗa ya karɓi plate ɗin zai zuba ta riƙe.
"Wallahi a ƙoshe nake."
"Sai ki ƙara. Ni ma ina son ladar."
Ganin ya dage ta sakesa ya zuba kaɗan ya hau bata ita ma. Kaɗan ta ci dan a ƙoshe ta ke, kafin ta musu jagora zuwa bangidan da ke falon suka wanke hannu suka dawo. Tattare komai tayi ta kai cikin gidan ta yi wa Amma sai anjima za su je gaishe da Mami, ta shiga gurin Abba ma ta masa sallama. Samunsa tayi har ya shiga motar ta shiga suka bar gidan.
Tafe suke shuru ya ɗan ratsa cikin motar kafin Dr Awwab ya riƙo hannunta.
"Gobe za mu koma fa."
"Gobe kuma? Na ɗauka ganin gida na zo ai."
Murmushi yayi me sauti ya dubeta yana maida kallonsa kan titi.
"Ke da ganin gida sai kin zo wankan jego, in har lokacin na ji zan iya barinki."
Marairaicewa tayi ta kamo damtsen hannunsa.
"Ina son zuwa gidan su Aunti Rahma da Hasiya, har da Rukayya da Walida. Akwai wata friend nawa ma idan har ka bani izini ina son kai mata ziyara Please."
Shuru yayi ya ƙi mata magana hakan yasa ta fara masa kukan shagwaɓa.
"Ni wallahi ka yarda."
Dariyace ta kwace masa jin tana mintsilinsa a hannu. Hannunta ya riƙo da ɗayan hannunsa, ɗaya nakan sitiyari.
"Is ok My Baby. Wannan muguntar zan rama. Zan yarda amma za ki rakani hotel mu kwana tare. Da nayi niyar barinki gidan Mami ki kwana."
Ƙara turɓune fuska tayi ga samu ga rashi.
"Dan Allah fa Hayat."
"Zan duba."
Ya faɗa daidai sun iso babban mall din da ya faka. Ba ta ma lura ba sai yanzu tsabar taɓara da take zuba masa. Kallonsa tayi yana shirin fita yace.
"Fito mu ma Mami tsaraba da yaranmu."
Da sauri ta fito ya rufe suka shiga ciki yana kamo hannunta. Turaruka masu ƙamshi ta ɗaukawa Mami da katan na maltina da peack milk. Ƴaran Aunties kuma tace ya bari gobe idan za ta je ta siya musu abu. Yayi na'am da hakan yasan duk wayo take son masa. Gurin biyan kuɗi suka nufa ya biya. Mai kula da gurin ya ƙira yaron shagonsu ya zo ya kai musu.
Cikin sauri ya iso gurin yana rissinawa. Kayan aikin shagonne jikinsa, blue riga an rubata WALID PROVISION STORE, da baƙin jeans na wando. Kansa ƙasa ya ce.
"Oga Khamis bayanan ya barmini aikinsa."
Ya faɗa cikin girmamawa.
"Oh hakafa. To MUFID ɗauki ka kai musu mota."
Tun sanda ya iso komenta ya tsaya cak, dariyar da take yi Dr Awwab na tsokanarta shaf ya ɗauke, jikinta mugun rawa yake musamman da aka ƙira sunansa ta tabbatar shi ne.
Dr Awwab da ya ji shuru yayi yawa ya ɗago kai ya kalleta, ganinta yayi tamkar an kafata. Hannunsa ya ɗaura saman kafaɗunta ya taɓata.
"Noor! Noor!!"
Ya faɗa da hakan ya dawo da ita hankalinta, ba zato ta kankamesa.
"Ka fitar ni anan."
Ta faɗa cikin rawar murya tare ƙara riƙesa.
Maganarta ya saka Dr Awwab ganin cikin mall ɗin ko ta ga wani abune, ganin mai dosowa garesu ya fahimci me ta gani. Hannunta ya jawo su ka fita waje, shi dai mai karɓar kuɗi ya bisu da kallon mamaki.
Sai da ya shigar da ita ya ga ta zauna ya fara ƙoƙarin fita ya ga amma sai waige waige ta ke.
"Bari in sallamesa."
Girgiza kai tayi tana shirin fashe masa da kuka.
"Haƙƙinsa ne fa."
Shuru ta masa tana kawar kanta gefe hawaye na kwaranya bisa kumatunta. Dr Awwab bai so ba ya fita. Ya samu Mufid ya gama saka musu kaya yana tsaye. Ba don a sallame sa ba sai dan yana son tunkararsu ya rasa ta ina zai fara. Fitowar Dr Awwab ya sa shi yin ƙasa da kansa cike da kunya, yasan dawowa ya yi ya masa rashin mutunci kawai ko tozartasa har wanda basu sanshi wanene ba su sani yau.
Amma abin mamaki hannu Dr Awwab ya miƙa masa tare da ƙiran sunansa. Idanuwansa masu kyau ya ɗago ya dubesa ya girgiza kai. Ba zai iya haɗa hannu da mutun mai daraja irin wannan ba.
Ganin ya ƙi amsa Dr Awwab ta kamo hannunsa ya saka cikin nasa suka yi musabaha.
"Baka son samun lada kenan."
Girgiza kai Mufid yayi yana ƙasa da kansa. A hankali ya buɗe baki ya ce.
"Ku yafemin, ka nemamin yafiyarta don Allah ko zan ga daidai a rayuwata."
Kafaɗunsa Dr Awwab ya dafa.
"Haƙiƙa da a irin rayuwar da na sanka na sake ganinka zan ji baƙin ciki da takaici rashin shiryuwarka, amma babu tantana na ga dana sani sosai a tare da kai. Ina jin baƙin ciki da haushinka na wanda ya ƙetawa matata mutunci bazan ɓoye maka ba, amma babu yadda na iya haka Allah ya ɗaura babu yadda muka iya. Maganar yafiya kuma zan tayaka roƙarta. Idan ta yafe maka walillahil hamd."
"Na gode sosai. Allah ya ku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba."
Faɗin Mufid na share hawayensa. Sai yau ya ji wani sanyi a zuciyarsa tun abun da ya ma Nuratu, duk da bata ce ta yafe masa ba amma yana sa ran albarkacin mijinta za ta yafe masa.
Sauƙar abu ya ji sama hannunsa ya sa shi dubawa. Kuɗi ne me yawa Dr Awwab ya damƙa masa.
"Ka kula da kanka, sai wani lokaci."
Daga haka ya juya ya koma mota. Cike da mamaki da karamcin wannan bawa ya bisa da kallo. Lallai wasu basa saka sharri da sharri sai alheri da sharri da zai saka mutum da na sani. Da ana haka da an daina yawan bibiyar mutum da sharri. Ciki ya koma jiki a sanyaye bayan ya ƙirga kuɗin dubu hamsin ya saka a aljihunsa yana murna, rabon da ya samu kuɗi me yawa har ya manta, dan kuɗin sallamarshi aiki dubu gome ne a wata.
'Lallai yau Daddy da Ummu za su ci daɗi.'
Ya faɗa yana shiga cikin shagon.
Wai yau shi Mufid ke murnar samun dubu hamsin, abin da shekarun baya bai kuɗin askin sa ba ko yankan farce.
Tun da yaga ba shi da mafita a rayuwa ya bazama neman aiki, inda Allah ya taimake sa ya samu kula da shagon ana sallamar sa, duk da aikin ba wani aiki bane sai kula da customers da kai musu kaya mota. Allahamdulillahi hakan ma yana jin daɗinsa domin gidansu ya zama kowa shi ya ɗauki nauyin kansa hatta abinci.
Mazajen yaran Alhaji Kashim Mufid suna bawa gidansa taimako daidai gwargwado da abin da Allah ya basu dan taimakawa surikin su da ahlinsu.
Alhaji Kashim da Hajiya Hindatu rayuwa ta musu juyin waina, babu kuɗi babu mulki duk sun yi sanyi. Hakan ya dasa tausayin su a zuciyar Mufid har ya zamto komai ya samu sai ya basu rabon su.
Hajiya Batul ta aurar yaranta biyu saura Suwaiba. Iyayenta da yayunta masu akwai su suke taimaka mata da wasu kuɗin buƙata.
Rayuwa kanan, Allah ka mana kyakkyawar ƙarshe. Ameen!
...
Tun da su ka ɗauka hanyar gidan Mami babu wanda ya yi ko tari, sai lokaci zuwa lokaci Nuratu ke sharar hawaye. Ita kanta ta rasa na menene, ba na ganin Mufid ba bana tausayin sa.
Bayan Dr Awwab yayi fakin tana shirin fita ya riƙota, ta ɗago za ta masa magana ya ɗaura bakinsa saman nata, idanu ta rufe tana jinsa yana yadda yaga dama, ba ta hanasa ba kusan mintuna har ta samu nutsuwa ta fara mayar masa da martani kafin ya saketa ya rumgumeta suna sauƙe ajiyar zuciya.
Sai da ya ga ta daidaita kafin ya saketa ya shafar fuskarta.
"Muje ko."
Kai ta ɗaga masa suka fita, shi ya ɗauki kayan ita kuma ta ɗauki ledar suka shiga da sallama. Mami tana ɗaki Suwaiba tana kallo ta ji sallamar. Amsawa ta yi ta bisu da kallon rashin sani.
"Su waye ku?"
Ta tambaya tana yatsine fuska. Nuratu da mamaki ta dubeta ita ma cikin rashin sani. Sannan ta duba Dr Awwab tace.
"Mu shiga Doctor."
Tare hanyar Suwaiba tayi tana hararar Nuratu.
"Ku shiga ina. Hajiya tana hutawa tace kar a tasheta..."
Ba ta rufe baki ba Nuratu ta hankaɗata gefe dama a cike take, ta yi tangal tangal da ƙyar ta dafa kujera ta bi bayanta ganinta nufi hanyar ɗakin Mami. Dr Awwab dai murmushi yayi yana mamakin ashe ta iya faɗa.
Da gudu Nuratu ta ƙarasa gadon ta faɗa jikin Mami da take zaune bakin gado tana duba wasu kaya a iPad ɗinta da za'a mata sari a ƙasar Turkiyya.
Ba za to taji hakan ta ɗago a tsorace, sai dai ganin Nuratu ya bata mamaki. A ruɗe take tambayarta me ya faru.
"Gurinki na zo ai, tare muke da Doctor."
"Haba dai..."
Suwaiba da ta shigo ta rissina.
"Hajiya na hanata ta shigo."
Murmushi tayi ta ce.
"Babu komai Suwaiba Auta ce."
Da mamaki Suwaiba ta kalli Nuratu ai kuwa saƙon harara ta sanu tana yatsine fuska. Rissinawa tayi ƙasa.
"Ina wuni Autar Mami."
"Lafiya."
Tace ta kawar kanta, ganin haka ta fita simi simi, tasan ita ce me laifi. Mami kallon ƴarta tayi.
"Me ya faru na ga kin ɓata ran ganinta."
Ta san dai Nuratu ba kasafai take nuna abu ba.
"Bata da kunya Mami, amma bar zancenta. Mu je ku gaisa da Doctor."
Murmushi Mami tayi ta ɗauki hijabi ta saka tana mamakinta, babu kunya ta dameta ta je su gaisa da mijinta.
A falon suka samesa Suwaiba ta cika masa table da kaya, bai ko kalli komai ba ya ci gaba da kallonsa. Sallamar Nuratu da Mami ya sauƙa ƙasa suka gaisa, Mami tana tambayarsa hanya. Cike da kunya ya amsa mata.
Kusan rabin awa yana gidan ganin Nuratu ta samu nutsuwa ya musu sai da safe zai zo ya kaita gidan yayunta da ƙawarta in ta shirya ta ƙirasa. Har mota ta rakosa ta koma.
Bayan tafiyarsa Mami da Nuratu suka shige ɗaki sai hira, sallar isha'i ta gabatar ta canza kaya zuwa doguwar rigar marar nauyi da ta ɗauka cikin sabbin kayan Mami na sayarwa, ta ɗale gado tana tayata zaban kayan da za'a mata sari.
Sun jima suna hira Nuratu na bata labarin abubuwan da suka faru har ta gangar zuwan Abbanta gidanta, sai dai ta ɓoye dalilin zuwanta yau akan maganar komawarta ne gidan Abbansu. Ita dai Mami shuru tayi tana jinta sai dai ƙasan ranta hakan ya mata daɗi bayan shekaru ashirin da huɗu ya shirya da ƴarsa.
Da safe har ƙarfe goman safe Nuratu tana barci, Mami bata tasheta ba dan kanta ta tashi ta shiga wanka. Suwaiba tun safe ta