Follow us on social media

Showing 33001 words to 36000 words out of 148866 words

Chapter 12 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

42

yau ma ya san sunanta dan haka ya ɗaga kanshi. Murmushinta ta faɗaɗa ganin tsawon shekaru ashirin ya waiwayi baya.

"Suna General hospital amma an tura su psychiatric hospital dake Maiduguri yau."

Kwarewa yayi jin abinda ta faɗa da sauri Amma Jidda ta miƙa masa ruwan cikin kofin ya karɓa ya shanye kafin ya dai-daita kanshi.

"Jikintan yayi tsanani ne?"
Ya tambaya.

"Eh har yanzu bata san inda kanta yake ba."

Anan ta sanar dashi iya abubuwan da ta sani har tana neman izinin tafiya gobe zuwa dubata.

Bai ce komai ba harta ya gama ta miƙe ta fara tattare gurin.

"Ku shirya gobe mu je dukkan mu."

Dakatawa Amma Jidda tayi da ɗaukar babban tray da yake ɗauke da komai tana juya furucin shi. Ganin za ta fassara maganganun shi ya miƙe ya wuce ɗakin shi. Sai da ta gama ta bi bayanshi.

***

Nuratu ba ita ta farka ba sai ƙarfe bakwai na safe, ba wanda yayi gigin shiga gurinta, suna kallonta sai dube dube take ta duƙunƙune cikin blanket din saman gadon tana bin ɗakin da kallo. Yau babu wani buge buge da kuka, hakan ya musu daɗi sosai.

Ƙarfe tara Dr Awwab ya shigo dubata suka gaisa da su Mami.

"Bari mu gwada bata abinci sai a mata wanka."

To suka amsa dashi abincin da ya shigo dashi ya ajiye musu manya manyan Warmers biyu ya ɗauki plate ya zuba dankali ya buɗe gilashin ya shiga gurin Nuratu.
Tana ganinshi ta miƙe ta fara ƙoƙarin gudu ya ajiye mata abincin ya fita. Ganin haka Nuratu ta dakata ta koma baya, sai kuma da sauri ta miƙe tana leƙa abin cikin plate din, har juyar da kanta take yi dan son tuna menene.
Hannu ta saka ta taɓa ta ɗauki kwaya daya ta kai bakinta ta tauna. Cikin sauri ta fara kwasa tana turawa bakinta har da kwaruwan ta. Duk ta hargitsa wajen kafin ta bari ta koma gefe.

"A wanke mata jiki za mu shigo in bata magani. Ga breakfast ba sai kun saya ba."
Dr Awwab yace yana shirin fita bayan ganin yanayi na Nuratu da yayi.

"Harda wahala Dr."
Cewar Rahma, Mami na mamakin kirkinshi da sanyin halinshi. Ban da wasu likitoci da suke ji da kansu.

"Babu komai."

Yace ya fita kafin Rahma ta buɗe ta zuba musu, dankali da fefesun kayan ciki da ya sanar daga can gida aka girka ya biya ya ɗauka da zai taho asibitin.

Bayan sunyi breakfast su ka shiga ɗakin Nuratu ta kallesu tana miƙewa, zuwansu su biyun ya tsorata ta, ta fara jan baya ganin sun nufota.

"Nuratu!"
Mami ta ƙirata tana matsawa kusa da ita, Nuratu ta fasa ihu tana ja baya ta runtse idanunta.
"Kar ki taɓa ni!"

Dakatawa Mami tayi ta hana Rahma isa wajenta.
"Je ki waje Rahma."

Ba musu Rahma ta koma waje tana kallonsu. Mami ta ƙara matsawa kaɗan gurinta.
"Nuratu! Mami fa, Mamin ki. Buɗe ido ki gan ni gani kusa dake na zo taimaka miki, babu wanda ya isa ya cutar dake."

Idanuwanta kaɗan Nuratu ta buɗe tana duban Mami.

"Mamin ki. Babu wanda zai cutar ki gani kusa dake."
Mami tace tana matsawa kusa da Nuratu sosai.

"Mami!"
Nuratu ta furta tana zarewa Mami ido. Ta ɗaga mata kai.
"Nuratu na."

Shuru Nuratu tayi ta zubawa Mami ido tana kallonta ta komo hannayenta.
"In miki wanka kin ga kin ɓata jikin ki."

"Wanka."
Tace cikin ƙarin bayani kamar mai koyan magana. Mami ta ɗaga kai tana ɗagata suka miƙe suka nufi bathroom. Mami hawayenta take dannewa duk lokacin da za ta saka Nuratu ruwan zafi. Tana lallashinta kamar tana ji ta samu ta gasata ta ɗauraye mata jikinta ta fito da ita ta samu Rahma ta gyara ɗakin ta fita.
Kayan asibiti ta maida mata sabo ta zaunarta tana shirin fita Nuratu ta riƙota alamar kar ta fita ko ina. Hakan ya sa Mami zama kusa da ita, Nuratu ta kwantar kanta da yake ciwo saman cinyar Mami.

Abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata ta hau juyi domin kanta da ta ji yana neman tsagewa. Rahma dake waje tana shayar da Ikhram da sauri ta fita ta ƙira Dr Awwab suka shigo tare da magunguna a hannun shi. A waje Rahma ta tsaya ya shiga.
Nuratu tana ganinshi ta riƙe Mami.

"Mami. Mufid ne ya fita."
Tace da ƙarfi tana riƙe Mami.

Mami na riƙe da ita tace.
"Bashi bane, Dr ne zai baki magani. Ciwon kan ki zai daina"

Gurinta Dr Awwab ya ƙarasa ta riƙo Mami tana kallon shi. Maganin ya ɓalla ya bawa Mami ta bata yana duban Nuratu.

"Babu abinda zan miki, magani zan baki ki sha sai ciwon kai ya tafi. Babu kowa anan da zai cutar dake."

Jin maganganun shi Nuratu ta kalli Mami, Mami ta ɗaga kai alamar eh, hakan yasa ta buɗe bakinta Mami ta bata magani da ruwa ta sha har lokacin tana riƙe da ita dan ta kasa yarda da Dr Awwab. Ganin tasha ya saka Dr Awwab fita. Sai da tayi bacci kafin Mami ta samu ta fita wajen Rahma.

"Allahamdulillahi sauƙi ya fara samuwa."
Cewar Mami cikin farin ciki.

"Sosai Mami tun da ta fara yarda da mutane. InshaAllah gaba kaɗan za ta dawo normal."

"InshaAllah, nagode Allah na godewa Dr Awwab."

Sallamar Amma Jidda da Walida, Ameera da Hasiya ya katse musu hiransu su ka shigo. Bayan an gaggaisa suka tambayi mai jiki ta sanar dasu da sauƙi har ta fara gane mutane.

"Akwai baƙo a waje Mamin yara."
Cewar Amma Jidda.

Da mamaki Mami tace.
"Baƙo kuma?"

"Eh muje ku gaisa."

Ba musu Mami bata kawo komai ba ta fita bayan ta gyara zaman mayafinta.
Alhaji Mamman ta tarar yana jiranta, ganin fitowar ta ya sashi tashi tsaye.

Shekaru ashirin bai sata a ido ba, ta zama babbar mace. Duk ita ta jawo musu da ta bi shawaran shi da yanzu babu abinda zai dame su.

Albarkacin ƴaƴa Mami ta gaishesa ya amsa yana tambayar mai jiki. Maimakon ta amsa tace.
"Sai yau ka san da zamanta?"

Tsayuwar shi ya gyara.
"Sadiya kenan, yanzu ma na zo ne ko in ce na shiga cikin lamarin ne dan kar duniya ta zageni domin ko ba komai ita ma ni na haifeta."

"Oho kar duniya ta zage ka, ba dan Allah ka zo ba. To bama buƙatar ka cikin rayuwar mu, tun ranar da ka ciremu cikin rayuwarka muka cire naka babin a rayuwar mu."

Daga haka Mami ta juya ta koma cikin jin haushinsa da har yanzu yana nan da wannan banzan ƙudirunsa.

....

#vote
#share
#comments

MADUBIN GOBE (Haske) 18.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Alhaji Mamman yaji zafin maganganun Mami amma burin shi dama kar azo shari'a a nemi uban yarinya a rasa a tuhume shi da rashin kula da ita, da yana jin ko duniya zata taru a kanshi ba zai rayu da Nuratu gida ɗaya ba. Yarinyar da dalilin ta duk wata arzikin shi ya nemi karaya.

Fita yayi cikin asibitin ya nufi cikin gari bayan ya sanar da Amma Jidda ta ƙirashi bayan sun gama.

Mami fushi tayi sosai har ya shafi Amma Jidda sai taji abin ba daɗi amma ita burinta ta haɗa kan tsofin mata da mijin in da rabon aure su sake zama.

Sai bakin magriba Nuratu ta farka tana neman Mami da sauri Mami ta shiga gurinta ta sanar da ita fitsari take ji, Mami ne ta kai ta bathroom tayi ta sata tsarki da ruwan zafi kafin ta sata alwala, da kyar ta iya tunawa tayi suka fito ta nuna mata gabar ta bata hijab tace tayi sallar magriba.

"Sallah? Raka'a nawa?"
Ta tambaya.

"Uku."
Mami tace cikin tausayin ƴarta.

Sai lokacin ta tuna ta hau yi, sama sama tayi tai sallama Mami na zaune kusa da ita, taji daɗin ganin ƴarta ta fara samun sauƙi da har tana iya fara wasu abubuwa. Bayan Nuratu ta idar Mami ta dubeta.

"Za kici abinci?"

Kai Nuratu ta ɗaga Mami ta miƙe zata fita da sauri Nuratu ta riƙota tana girgiza mata kai alamar kar ta fita.

"Abinci zan ɗauko miki kici da magani."

"Za ki dawo?"

Kai Mami ta ɗaga kafin Nuratu ta saketa ta fita da sauri ta zuba mata abincin da su Amma Jidda suka kawo ta tura Rahma gurin Dr Awwab ya bata magunguna kafin ta koma. Duk abubuwan da suke suna kallonsu kowa yaji farin cikin ganin ta dawo cikin hankalinta sai tsoro da har yanzu yake damunta.

A baki Mami tayi ta bata abincin tana ci.

"Mami zan kashe su."

Faɗin Nuratu da ya saka Mami kallonta da sauri itama kallonta take. Kasa cewa komai Mami tayi dan ta san ko ta mata magana ba ganewa za tayi ba ko ta hakura.

Shigar Dr Awwab yasa su kai dubansu gurin da sauri Nuratu ta matsa gurin Mami ta ɓuya. Gurinsu ya ƙarasa yana duban Nuratu da itama shi take kallo, ya ɗauke idonshi cikin nata. Duk namiji tsoro da tsanarshi take ji.

"My patient."

Kallonshi kawai take ta kasa amsa mishi. Dr Awwab ya juya ya kalli Mami.

"Ga magungunan ta, za taci gaba da sha har zuwa nan da wani lokaci, in ta gama shan wannan zamu ɗaurata kan wani da za ta jima tana amfani dashi zuwa nan da shekaru huɗu zuwa biyar, har sai ta daina shiga damuwa ko in ta fara tunani kanta ya hau ciwo. InshaAllah komai zai dai-daita, taci gaba da shan magani tana samun kulawa zuwa nan da wata ɗaya za ta dawo normal mu sallameta."

"Mun gode Dr."
Faɗin Mami cikin murna da jin daɗin bayanin Dr Awwab.

Ya kalli Nuratu da take kallonshi har lokacin, ƙwayar idanuwanta suka sarƙe nashi yayi saurin ɗauke idonshi.
"Allah ƙara sauki."

Ameen! Mami ta amsa da shi yasa kai ya fita Nuratu ta bishi da kallo.

"Mami waye?"

"Dr Awwab ne, shi ya ci gaba da kula dake bayan Dr Sadiq."

Kai kawai ta girgiza tana son sanin mai ya faru da ita dan iya saninta tun lokacin da Mufid ya sata jin azaba ta suma bata ƙara sanin komai ba sai jiya zuwa yau da ta fara tuna abubuwan da ya faru da ita.
Hawaye ta fara mai cin rai tunawa da shikenan Mufid da abokan shi sun cuceta sun cutar da rayuwarta. Ba ta da wani ƙima ko daraja a tattare da ita a matsayin ta na ƴa mace.

'Fyaɗe aka mata! Ita ce wacce aka ma fyaɗe!'
Shikenan abinda za ana ƙiranta da shi har ƙarshen rayuwarta. Ji tayi ta tsani ko wani namiji a duniya.

"Ki daina kuka kin ji Nuratu, Allah ya riga ya rubuta ya ƙaddara hakan sai ya faru babu yanda muka iya, Allah zai saka miki. InshaAllah haƙƙin ki ba zai taɓa barinshi ya runtsa ba da yardar Allah."

Kuka kawai Nuratu take yi wanda sauran ƴan uwanta dake waje duk ya saka su zubar da hawaye. Sun san dole tayi kuka na wannan rashin imani da aka nuna mata.

Ciwon kai ya zuba mata bayan kukan da take da kyar Mami ta lallasheta ta yi shuru ta bata magani kafin ta kwanta bata jima ba bacci ya ɗauketa.

****

Ƙarfe goma ya dawo daga airport bayan tashin jirgin mahaifinsu zuwa ƙasar Egypt tare da ƙanin babansu da zai kula dashi, ya dawo gidan bayan ya sauƙe Umma bai shiga ba ta dakata.

"Fita za kayi?"

"Eh Umma ina son zuwa Damaturu in duba jikin yarinyar."

Kallon shi tayi ita dai wannan sa kai da yake cikin rayuwar mutanen da bai san su ba bata so.

"Kar ka dai dare."

Kai kawai ya ɗaga ya ja motar ta wuce cikin gida. Karfe sha biyu saura ya isa cikin Damaturu kai tsaye asibitin General ya nufa. Dr Sadiq yana duba marasa lafiya, bayan ya sallami marasa lafiya ya shiga suka gaisa.

"Ina patients ɗi ta."
Faɗin Col. Ahmad yana zama saman kujeran cikin ofishin.

"Lafiyarta lau, baka da labarin na turasu Maiduguri psychiatric hospital."

"Yaushe?"

"Kwana biyu yau. Jikin yaƙi sauƙi anan, but Allahamdulillahi munyi waya da Dr Awwab yace sauƙi ya fara samuwa dan har ta fara gane mutane da yarda dasu."

Col. Ahmad kai ya girgiza yana dafewa.
"Allah ƙara mata lafiya. Zanje dubata ka bani address ɗin."

Anan Dr Sadiq ya bawa Col. Ahmad address din asibitin da take.

Col. Ahmad yace.
"Na sani nima ɗan can ne aiki ne ya kai ni Ibadan."

Sunyi sallama cikin aminci Dr Sadiq yaci gaba da aikin shi

***

Kwana biyun duk a ƙofar gidan su yake wuni ko zai ga shigarta da fitarta amma baya ganin hakan domin gidan tamkar babu mutane. So yake ya ganta suyi maganan yarjejeniya idan har ta amince zata aure shi, shi kuma ya yarda a hukunta shi kamar yadda ubanshi ya so rufe shari'ar. Sonta yake so irin wanda bai taɓa ma wasu matan ba, ba wai dan ya aikata mata wani laifin ba. Asali ma tun farkon ganinta yake sonta, son da yake mata ne ya jawo ya aikata mata haka.

Da ya gaji da zaman jiran har yamma lis ya bar unguwar, sai da ya biya gurin shaiɗancin su ya sha wine ya zuƙi sigari kafin ya nufi gida.
A falon gidan ya samu Ummu da Rufaida, tana cin abinci dawowarta daga makaranta kenan. Saman kujera ya zauna kusa da ita ta miƙe tana toshe hanci dan warin sigari da ya bugeta.

Harara ya watsa mata da idanuwanshi da suka fara canza launi.
"Uban wa ki ke toshewa hanci?"

"Sai in zauna wari ya halakar ni ko zunubi ya shafe ni."

Kanta yayi zai kai mata mari Ummu ta tare shi da sauri dan tasan yanzu zai iya marinta dan ya saba.

"Kar ka yarda ka daka min yarinya. Ƙarya tayi ne ba warin sigarin ka ke ba. Na ga dai ranar shiryuwar ka Mufid."

Tsaki ya buga ya miƙe ya wuce ɗakin shi. Ganin haka Rufaida ta koma ta zauna.

"Ki dai bishi a hankali kin san yanzu sai ya bubbbugeki babu ruwana."
Faɗin Ummu.

Rufaida ba tayi magana ba taci gaba da cin abincin ta, ita yanzu da za'a tambayeta wata tsana a duniya zata ce shine, ta tsane shi a rayuwarta, tana jin kunya da haushi a ƙirata da ƙanwar shi.

***

Col. Ahmad ƙarfe uku ya isa garin Maiduguri, gida ya koma yayi sallah yaci abinci kafin ya nufi asibitin dasu Nuratu suke. Kai tsaye Asylums center ya nufa, bayan ya nemi ganin Dr Awwab ya sanar dashi shine wanda Dr Sadiq ya sanar dashi zai zo kasancewar bayan tafiyar Col. Ahmad, Dr Sadiq ya sanar da Dr Awwab ko shi wanene. Bayan sun gaisa Dr Awwab ya masa iso zuwa wajensu Mami.

Mami dai ta ganeshi dan yazo sau ɗaya haka Munirat ma da yau tazo dan taya Mami, Rahma dasu Amma Jidda sun koma. Kallon Nuratu yake ta cikin gilashin tana zaune shuru tunani take ta zubawa waje ɗaya ido, babu wanda ya ankara da hawayen da take zubarwa sai Dr Awwab.

"Bari in shiga in sanar da ita in ta yarda sai ka shigo."
Cewar Dr Awwab ya nufi wajen shigan duk suka bisa da ido.

*"Noor!"*

Ya ƙirata bayan ya shiga da sauri ta goge hawayenta tana kallon shi. Cikin kwana biyun ta kula shine Dr da yake zuwa dubata, in bashi ba babu kowa da yake shigowa sai ƴan gidansu da duk sun shigo kafin su tafi kuma allahamdulillahi ta ganesu, da suka fara damunta da hayaniya za su tada abinda ya wuce aka fitarsu.

Bata amsa ba sai idanu da ta zuba mishi dan ta fara yarda da shi.

"Kina da baƙo. Ya shigo?"

"Waye?"
Ta tambaye shi tana ɗauke idonta cikin nashi.

"Bari ya shigo ki ganshi."
Yace ya fita ya ƙira Col. Ahmad ya shiga da sallama.

Idanu ta zuba mishi shima ita yake kallo har ya samu guri ya zauna.

"Sannu ya jikin?"
Kamar ba zata amsa ba tana kallonshi.
Ta gane shi, shine wanda ya bugeta lokacin da take gudun ceton ranta, ta nemi ya taimaka mata yana gani Mufid da abokansa suka sakata a motarsu. Kallon Dr Awwab tayi da shima ita yake kallo.

"Ka ce ya fita."

"Why Noor?"
Dr Awwab yace yana matsawa kusa da ita, ta ja baya da sauri tana mishi wani kallo tare da watsa masa harara.

"Ka ce ya fita."

Nuratu tace tana haɗa rai, dole yasa Dr Awwab kallon Col. Ahmad da ya zubawa Nuratu ido yana kallo, sai yaji ransa bai so kallon ba.

"Mu je waje, may be bata gane ka ba."

Babu musu Col. Ahmad ya miƙe suka fita da Dr Awwab yayi wa su Mami sallama.

"Bata gane ni ba, ko ni ne bata son gani?"
Col. Ahmad yake tambayar Dr Awwab bayan fitarsu.

"Tana ganewa tunda har ta gane ƴan gidansu. Yarda da mutane ne zai yi wuya tayi cikin sauri."

"Hakane kuma? Zuwa yaushe za'a sallameta."

"Za ta kai one month? Wani abun ne?"
Dr Awwab ya faɗa dan son ƙarin bayani.

"Yeah akan case ɗin tane ina son a shigar da ƙara kafin in koma wajen aiki."

"InshaAllah kar ka damu zamu sallameta da zaran lokaci yayi, ko bata gama shan maganininta ba na wata ɗaya da zaran ya kusa ƙarewa zamu sallameta."

"To shikenan Allah ƙara mata lafiya. Zan koma gida gobe zan shigo."
Faɗin Col. Ahmad yana wuce.
Dr Awwab ya amsa da ameen ya koma office ɗinsa ya samu an kawo ƴarshi Hanan daga gida da ta matsa sai tazo wajenshi.

***

Shigar dare su kayi ana ƙiran sallar magriba, bayan an sauƙe Rahma da Hasiya da Rukayya a gidansu suka isa gida. Wangale get ɗin a kayi Alhaji Mamman ya shiga da motar yana bin motar da ke fake da kallo kamar ya gane mai motar.
Amma Jidda da ta riga ta gane tayi mamakin yaushe ya shigo bai nemeta ba.

Ciki suka ƙarasa kowa ya wuce ɗakin shi yayi sallah kafin su fito. Ana idar da sallar magriba ya dawo ya samu sun dawo. Cikin falon ya shiga da sallama, Ameera dake kusa ta amsa tana tashi ta tare shi.

"Sannun ku da dawowa ya hanya?"
Yaya Al-ameen yace yana zama kusa da Amma Jidda.

"Lafiya ƙalau yaushe a gari?"

"Ban jima da shigowa ba. Na ƙira ku duk babu wanda ya ɗauka. Ina ku ka je ne? Naje gidan Mami a kulle, ƙanwata ma numbern ta a rufe."

"Maiduguri mu ka je."
Sai kuma Amma Jidda tayi shuru tuna bashi da labarin mai ya faru da Nuratu. Tambayar da ya watsa mata ya sata miƙewa tace.
"Mu je ciki."

Ba musu ya miƙe ya bita cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ya kasa fassara abinda yake ji.
Stool ya samu ya zauna ta zauna bakin gado tana dubanshi.

"Al'ameen!"

"Na'am!"
Ya amsa ƙasa ƙasa yana sauraron mai zata furta.

"Ka san ƙaddara?"

"Na sani Amma."
Yace zuciyar shi yana bada wani sauti.

"Ka san rubuce yake baya wuce lokacin shi, kuma ana so bawa ya karɓa."

"Hakane Amma."
Yace har lokacin zuciyarshi yana bugawa. Tsoronsa ɗaya kar Amma tace Nuratu ta daina son shi ko Abba ya hanashi aurenta.

.....

#vote
#comments
#share
MADUBIN GOBE 19

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.


A hankali cikin nutsuwa da yadda zai fahimci zancen ta sanar dashi halin da Nuratu take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login