Follow us on social media
Showing 90001 words to 93000 words out of 148866 words
Chapter 31 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb
Rahma tace.
"Kinyi daidai Mami, hakan yafi ai ta je can gidanta ta yi service ɗinta, ta godewa Allah ma da garin mijin aka tura ta."
"Aunti Rahma ke ma."
Nuratu tace kamar tayi kuka.
Harara ta watsa mata tace.
"Dalla rufemin baki, ana nema miki gata kin tsaya wasa da shi. Ƙira Dr Awwab ɗin ki haɗani da shi a waya."
Gunguni Nuratu ta fara za ta bar gurin Aunti Hasiya ta fizgota rai ɓace.
"Zan ɓata miki rai wallahi banza wawiya kawai."
Kuka Nuratu ta fashe da shi ganin haka ya saka Aunti Zarah kama hannunta suka fita. Cikin ɗakin Nuratu suka shiga ta zaunarta a bakin katifarta ta zauna.
"Share hawayenki haba amaryar Awwab."
Hawayenta ta share Aunti Zarah tace.
"To me na kuka kuma Nuratu bayan an riga an ɗaura auren, komai dai daren dadewa sai kin tare. Kiyi hakuri ki tare gidanki kiyi karatun ki cikin nutsuwa. Amma yanzu kina zirga zirga da aure kina jin za ki ji daɗin haka, ko shi Dr Awwab ɗin zai so haka, ko danginshi za su so haka? Kina gani dai mahaifiyarshi har gidan nan ta taso musamman dan ke, to ko albarkacinta ai kya hakura Nuraru."
"Ni dai Aunti yayi sauri sati biyu ne wallahi."
Nuratu tace tana share guntun hawayenta.
Girgiza kai Aunti Zarah tayi.
"Bai yi ba Nuratu kwana goma sha biyar, ana kai ki da kwana biyu sai ki shiga fara zirga zirganki. Wa yaga amarya a camp."
Aunti Zarah ta ƙarashe maganar tana dariya da ya saka Nuratu jin kunya ta rufe fuskarta. Nasiha Aunti Zarah tayi ta mata har taji nutsuwa ta saka hakuri a ranta kafin ta fita ta sanar Mami cewa ta amince nan da kwana goma sha biyar. Mamu tace.
"Sai ku fara shiri ku manyan yayu, ni na gama nawa dan na riga na sayi kayan ɗaki da wasu abubuwan, tun sati biyu da ya wuce babu wanda na sanar."
Da mamaki Aunti Rahma tace.
"Shikenan zamu haɗa da Hasiya muyi sauran."
"To Allah kai mu ya bamu iko."
Aunti Hasiya tace suka amsa da ameen, anan su kayi ta tattaunawa kan bikin har ƙarfe shida kafin su bar gidan.
Da daren Dr Awwab kamar yasan mai yake faruwa ya ƙira Nuratu. Tana kwance dan ciwon kai da yake damunta ta samu ƙiran ta ɗauka. Ƙasa ƙasa ta amsa tana gaishesa.
"Me ya samu Babyna? Na ji muryarta wani iri?"
Dr Awwab yace jin muryar Nuratu ya canza.
"Bana jin daɗi kai yake ciwo."
Ta faɗa tana ƙara ƙasa da murya.
"Sorry My Baby kinsha magani? Da ina kusa nayi maganin ciwon nan amma kin hanani dama."
Shuru ta mishi tana son sanar da shi yadda su kayi da su Aunti Zarah ta kasa. A hankali tace.
"Doctor sunan mu ya fito."
"Sunan ina? Zuwa camp? Ina suka turomin ke, bana son kiyi nisa ki barni Babyna. I need you beside me."
Dr Awwab ya ƙarasa maganar cike da buƙatar hakan, dan hakurinshi ya fara gazawa.
Kamar me bata so tace.
"Maiduguri suka turo ni."
"Allahamdulillahi."
Dr Awwab yace da ƙarfi Nuratu tayi murmushi har yaji sautinshi.
Cike da farin ciki Dr Awwab yace.
"Thanks God, kamar sun san ina buƙatar matata kusa da ni. Please Babyna kafin ki tafi ya kamata ki tare gidanki, in kuma ba haka ba kin ga kin zo garinmu wallahi har camp za ina biyoki in ɗauke ki, balle ma babu zaman camp tun da kina da aure."
Baki buɗe dan mamaki tace.
"Ni dai ka rufamin asiri."
"Gani ki ke ba zan iya ba?"
"Yanzu kai sai ka ɗauke ni."
Murmushi yayi daga kwancen da yake yana cewa.
"Sa wasa ki gani, duk abin da Awwab ya faɗa sai ya aikata shi fa. In kuma so kike ki gama bautar ƙasa da jikan Ummi to shikenan."
Da sauri Nuratu tace.
"Dan Allah kayi haƙuri. Ka ƙira Aunti Rahma kuyi magana."
"Dagaske Babyna."
Dr Awwab yace cike da ɗoki tace masa eh ta kashe wayar gaba ɗaya tana juya kalamanshi. Rashin kunyarshi gareta ya fara isarta.
Dr Awwab kasa nutsuwa yayi a laliɓo lambar Aunti Rahma ya ƙirata, bayan ta ɗauka sun gaisa sai kuma ya rasa ta ina zai tambayeta hakan yasa Aunti Rahma tace.
"Kunyi magana da Nuratu ne?"
"Eh Aunti."
"To sai ka fara shiri nan da kwana goma sha biyar mun riga mun yanke ranar."
"Allah kaimu Aunti nagode."
Yace ya kashe wayar cike da farin ciki ya miƙe ya fita a gidan.
Gidan Ummi ya isa bayan sun gaisa ya sanar da ita yanda su kayi.
"MashAllah Allah kaimu da rai da lafiya, sai mu fara shiri."
"Sosai ma Ummi ban ga zama ba."
Dr Awwab ya ce yana fita a gidan ko ta kan Hanan bai bi ba.
***
"Daddy ina son cigaba da karatuna tun da na samu lafiya, ina son in gama nima in samu aikin yi in tsaya da kafafuna kamar kowa."
Alhaji Kashim yana jin mai Mufid ya faɗa har ya gama yana dubanshi ko ya koma shaye-shaye ne yace.
"Yanzu kai Mufid duk tsawon lokacin ba kayi karatun ba sai yanzu. Kar ka sani asaran kuɗi ka ga komai ya lalace bani da wasu ashasshen kuɗi yanzu."
"Shi yasa nima nace zan koma karatu dan in samu na kai na, in kuma ba zaka iya min komai ba zan fita na nema da kai na."
Cikin sauri Alhaji Kashim yace.
"Abun bai kai ga haka ba, in an koma zan nema maka gurbin karatun, sai ka gyara papers naka muga abin da Allah zai yi."
Jin abin da Daddynshi yace ya miƙe ya bar masa gurin. A gidan baya shiga harkar kowa baya fita sai ya kama, wani shuru shuru ya zama, magana ma baya yi sai dole.
***
Cikin satin dukka familyn biyun shirye-shiryen biki suke, Mami da yaranta sai shiri suke sosai kowa yana ƙoƙarin kyautawawa Nuratu. Ɓangaren Nuratu jinta take wani iri, zata shiga sabuwar rayuwa da bata taɓa kawo haka a rayuwarta ba. Mai gyara na musamman Aunti Rahma ta kawo daga Maiduguri dan ta gyarata ciki da waje. Ita dai Nuratu nata ido, domin abin da ka riga ka rasane wanda ba zai taɓa dawowa ba.
Dr Awwab nasu bangaren ma shiri suke duk ya gayyato na kusa dana nesa, duk da ya sanar da su ɗaurin auren an riga anyi reception kawai za ayi sai ɗauko amarya.
Ummi har danginta na Libya da zama ya kai su can ta sanar da su tare da basu hakurin abin yazo cikin gaggawa ne, sun mata alƙawarin zuwan mutum biyu zuwa uku inshaAllah, haka danginta na Nijar ma.
Alhaji Mamman ta bakin Amma Jidda ya samu labarin dan zirga zirga da take babu zama ta sanar da shi Nuratu ne zata tare. Murmushi yayi yace.
"Allah ya bata zaman lafiya da mijinta. Yaron yana da nutsuwa na san zai bata gatan da duk ta rasa."
"Ameen ya Allah. Hakane kam Dr Awwab akwai nutsuwa."
Amma Jidda ta amsa da shi daren ranar da ta dawo daga gidan Mami su kayi wannan maganar.
Washegarin Alhamis akan jibi Asabar Nuratu za ta tare, da safe Alhaji Mamman ya wuce kasuwa kuɗaɗenshi ya haɗa na cinikin kwana biyu dubu ɗari biyar ya nufi gidan Mami da su. Gidan mutane sun fara taruwa dan ƴan Nijar yau suka iso ciki har da Nazifa da Mama Yawuro.
A ƙofar gidan ya tsaya kafin ya shiga ciki kai tsaye matan ɗaiɗaiku da suke filin gidan suka amsa da shi ya wuce falon, babu mutane sosai domin ƴan matan sun ɗauki amarya Nuratu sun tafi gidan lalle. A falon ya zauna ya tura ƙaramar yarinya ta ƙira masa Mami.
Mami da ke cikin ɗakin tana shirya wasu kaya ta samun ƙiran ta fito. Ganin wanda yake zaune ya sata haɗa rai, ba dan Yaya Muhammadu ya ƙirata ya sanar da ita komai ba, da babu abin da zai saka ta saurareshi.
"Sannu."
Tace tana zama shima ya gyara zama yace.
"Sannu Sadiya ina wuni."
"Lafiya."
Ta amsa a kan labbenta ƙasa ƙasa.
Murmushi yayi yana mamakin har yanzu tana da zafin nan yace.
"Babu maganar tone tone yafiya na zo nema."
Kalaman da Yayanta ya faɗa mata ne suka faɗo mata akan ta yafe mishi dan haƙiƙa yaga buƙatar yafiya a idanun shi tare da nadama, hakan yasa tace.
"Allah yafe mana gaba ɗaya."
"Ameen nagode sosai. Ina Nuratu?"
Da mamaki ta dubeshi tare da alamar tambaya, yayi murmushi da ya sakata ɗauke kanta dan sai ya koma mata Alhaji Mamman Bashir ɗinta na baya yace.
"Nuratu dai?"
Sai lokacin ta fahimta tace.
"Sun fita da su Rahma amma nasan suna hanya."
Miƙewa tsaye yayi ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kuɗaɗen ciki ya ajiye saman table ɗin da yake tsakiyar falon.
"Sai sun dawo zan wuce. Ga wannan ki ƙara cikin hidimomi biki. Nasan duk abin da zan yi ba zai taɓa burgeku ba saboda na riga na shafawa kai na baƙin fenti a gurinki da gurin Nuratu ba. Haƙiƙa na so haɗuwa da Nuratu in nemi yafiyarta, amma babu komai zan taka har gidanta na je. Sai wani lokacin. Allah bata zaman lafiya."
Da kyar Mami ta samu bakin furta.
"Ameen! Amma da ka ɗauki kuɗaɗenka bama buƙata."
Bai saurari mai take faɗa ba yasa kai ya fice. Cikin sanyi jiki Mami ta tashi ta ɗauki kuɗaɗen ta wuce ɗaki da su. Kirgawa tayi ta tsorata da yawansu bata taɓa tsammani Alhaji Mamman zai yi saurin gane hanyar gaskiya ba cikin kwana kusa, tasan yayi nisa amma tayi mamakin saurin ankara da yayi ya dawo hanya.
Su Nuratu sai yamma lis bakin magriba suka dawo, tun a hanya Dr Awwab ya ƙirata bata samu ɗauka ba dan gudun su Rukayya su sata gaba da tsokana, ban da wanda suke mata yanzu. Tana dawowa ta ɗauki wayar ta shige bathroom ta ƙirashi.
Yana zaune gaban Ikhram da Zaituna ƙannenshi da suka iso tun tsawon kwana biyu tare da lefen da ya tura musu kuɗi suka haɗa. Suna lissafin abubuwan da za'a ƙara ƙiran Nuratu ya shigo. Rabon da suyi wayar kirki har ya manta, baya samun zama ga aikin asibiti ga zirga zirgan biki bai samu kiranta ba sai ɗazu kuma ba ta ɗauka ba ya barta, yasan itama tana cikin rububin biki.
A gabansu ya ɗauka yana kafawa a kunne yace.
"Babyna."
Ikhram da Zaituna har rige rigen juyawa su kayi kallonshi dan jin sunan da ya faɗa, ya watsa musu harara suka ɗauke kansu suna kunshe dariyar bakinsu.
....
#vote
#comment
#share
MADUBIN GOBE 44.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
Jin abin da ya faɗa ya saka Nuratu yin shuru har sai da yace.
"Babyna me kike shirya mana?"
"Ni babu abin da na shirya."
Nuratu tace ƙasa ƙasa tsoron kar su Walida su jiyota.
"Seriously fa maganar gaskiya?"
Ta ji Dr Awwab yace ta ƙara maƙe murya.
"Dagaske, su Walida da Aunti Rukayya dai sun dage za suyi dinner."
"Zan zo nima kenan in gayyato friends ɗina."
"Nima ban sani ba."
"Shikenan zan ƙira Walida na ji mai suke shiryawa."
To tace tana kashe wayar ta fita, bata tsaya ɗakin ba ta fita falo jin Walida ta fara mata tsiya dan duk sun ganota waya tayi a bathroom ɗin.
Gidan hayaniya sosai har ranar asabar Mami ta haɗa walima ta ƙira Malama tayi wa'azi da duk ya kashewa mutane jiki. Nuratu lulluɓe cikin abaya haɗe da alkyabba sai sharan hawaye take domin tamkar fami aka mata a nata rayuwar. Har ƙarfe biyar kafin a watse aka tashi. Mami da su Aunti Rahma sun raba kyautattuka.
Gidan su Dr Awwab reception ya haɗa tare da abokansa da ƴan uwansa samari daga Libya da Nijar da kuma ƴaƴan Baffa Abubakar. An ci ansha anyi taro lafiya domin Dr Awwab ya kashe kuɗi sosai babu harkar reni. Kayan jikinsa kaɗai ma abin kallone, banda hall da ya kama da kayan ciye ciye da kuɗi kawai ya zuba aka haɗa komai, ga masu ɗaukan hoto sama da mutum biyar. Da ka ganshi murmushi kawai yake zubawa cike da farin ciki.
Bayan an kusa tashi ya sanar da su akwai dinner a Damaturu karfe takwas na dare, duk da mai buƙatar zuwa. Anan suka yanke shawarar tafiya su kwana in an gama gobe da safe su ɗauko amarya su juyo. Kowa yayi na'am da shawaran, bayan sun tashi ƙarfe biyar suka ɗauko hanya.
Karfe shida suka iso, sallah suka gabatar kafin Dr Awwab ya kama musu hotel, duk da Aunti Rahma ta matsa su je gidan da aka basu su kwana ya nuna babu komai.
Karfe bakwai motoci suka taru a kofar gidansu Nuratu dan tafiya wajen dinner da yayunta suka haɗa mata tare da taimakon Col. Ahmad da Yaya al'ameen da kwana biyu da zuwansu kenan suka taimaka musu suka shirya komai.
Kowa ya fito ya shiga motar sai amarya da ake jira ta fito tare da Walida, cikin lace material ruwan gold da ya amshi baƙin fatarta da yake glowing. Tayi kwalliya dan mai kwalliya suka ɗauka ta tsara mata kwalliya da ya karɓi fuskarta babu wani tarukuce amma tayi mutuƙar yin kyau.
Har cikin motar da Dr Awwab yake ciki da ya bawa abokinsa yake ja ya koma baya ta shigar Nuratu ciki, kanta sunkuye a ƙasa, zuciyarta sai bugawa yake dan ma ba su biyu bane. Babu wanda yayi magana cikin su har aka fara tafiya kafin ta ji maganar Dr Awwab yace.
"Allahamdulillahi Masha Allah, just Masha Allah."
Murmushin dole Nuratu tayi ta kasa magana har lokacin kanta a ƙasa tana watsa da hannunta da yasha jan lalle da baƙi yayi kyau. Shima bai ƙara magana ba sai idanuwansa da suke yawo a jikinta yana kallon halal ɗinshi da malak.
A harabar hall din wasu suka tsaya, tasu kuma motarsu har ƙofar hall ɗin ya tsaya, kusan mintuna biyar an gama jera komai aka buƙaci su fito. Kowa ta ƙofa daban ya fito suka haɗu aka shiga gaban su da bayansu kafin a fara tafiya ciki. Babu kunya Dr Awwab ya saka hannu ya riƙo hannun matarshi da ya sakata jin wani shork ta kasa zare hannuwanta har suka isa wajen zamansu suka zauna sauran suka koma kafin a fara gudunar da bikin.
Tsawon mintuna arba'in ana abu ɗaya aka ƙira ango da amarya suka fito yanka cake. Dr Awwab ne ya fara miƙewa ya riƙo hannun Nuratu ya mikar da ita suka isa gurin. Ita dai da ido take bin su domin jinta take tamkar ba ita ba. Mamaki take wai yau ranar dinar bikin aurenta, abin da ta riga ta cire rai da tsammani.
Dr Awwab ne ya kama hannunta ya haɗa da wuƙar suka yanke cake ya ajiye ya gutsuri kaɗan ya bata da kyar ta karɓa akace ita ma ta bashi.
Kallon Dr Awwab tayi, ya ɗaga mata gira ta girgiza kai yanda zai fahimta alamar ba zata iya ba, ganin haka ya haɗa rai.
"Amarya ke ake jira."
Fadin Dj dan yadda gurin ya ɗauki shuru dan son ganin yadda za'a kaya. Ko motsi taƙi yi balle ya saka ran zata bashi da mutane gurin. Aunti Hasiya kamar ta hau saman ta mammake Nuratu ta ake ji tsabar ta bata haushi.
Ganin da gaske take Dr Awwab ya sashi matsawa kusa da ita ya saka hannunshi ya riƙota tare da kama hannunta ya haɗa da nashi ya guntsiri cake din ya kai bakinshi guntun ya tura mata a baki ƙasa ƙasa yace.
"Cinye Babyna."
Dolenta ta haɗiye ganin haka aka saka ihu tare da tafa musu Dj yayi gyaran murya yace.
"Wannan amaryar ƴar shagwaɓa ce wato sai dai su ci tare."
Nan ma ihun aka saka Dr Awwab yaja Nuratu suka koma suka zauna har lokacin yana riƙe da hannunta ta kasa kwacewa. Kwata kwata ya hanata yin rawa duk ƙiransu da ake su fito, haka shima. Ɓangaren Nuratu da ma bata iya ba balle tace za tayi, hanata tashi da yayi ya mata daɗi.
Yaya Al-ameen da yake zaune kusa da Nazifa da ta saka musu ido babu ko kiftawa, yayi dariya da ta ji sautin shi bata juya ta kalleshi ba yace.
"Sun miki kyau ne ƴar ƙauye."
"Sosai baka ganin yadda yake lallaɓa ta kamar ƙaramar yarinya."
"Kema in kina so za'a miki har yafi wannan in dai kin amince."
"Dagaske Allah?"
Ta tambaya tana juyowa da sauri tana kallonshi yana murmushi yace.
"Yes in dai kin amince za ki zama matar Al'ameen shi kuma ya amince zai miki har abinda yafi wannan."
Kallonshi take ta kasa fahimtar zancenshi, kusan mintuna biyu kafin ta miƙe da sauri ta bar gurin dan fahimtar mai yace har tana kusan cin tuntuɓe, yana dariya ya ga ta shige cikin su Walida ta ɓuya.
Tin jiya da suka haɗu zata raka Walida gidanta ɗauko wasu kayanta ya ganeta sarai ƴar Kawun Nuratu ne dan ya ganta a Nijar. Shi ya taimaka musu ya kai su gidan Walida da motar shi bayan isar su a wajen fita Nazifa tayi ƙauyencin buɗe motar ba wai dan bata iya ba sai dan ta rikice, daga nan ya fara ƙiranta ƴar ƙauye babu musu ta amsa dan ta san tayi ƙauyencin.
Yaji a ranshi in har za'a bashi aurenta kuma iyayenshi za su yarda zai aureta domin ya yarda da hankalinta da nutsuwarta.
Zuwan Col. Ahmad wajenshi ya sashi kawar da tunanin suka gaisa kafin su maida hankali kan abin da ake gabatarwa.
Karfe tara aka tashi kowa ya fito ya fara shiga mota, Dr Awwab da Nuratu kamar zuwansu haka suka shiga su biyu a bayan sai mai ja. Suna ciki kafin motoci su fara tafiya Dr Awwab ya juya yana kallonta, ƙamshin turarenta da nashi ya haɗe ya bada wani ƙamshi mai fisgar tunanin mutum.
Ƙwanƙwasa gilashin motar a kayi ta daidai inda Nuratu take, abokin Dr Awwab ya buɗe wanda ya ƙwanƙwasa ya leƙo kanshi.
A mugun tsorace Nuratu taja baya tare da faɗawa jikin Dr Awwab ta riƙo shi, shima Dr Awwab ɗin ganin haka ya sashi riƙota jikinshi sosai yana bin wanda ya leƙo da kallon mamaki.
"Congratulations Nuratu and Dr, Allah baku zaman lafiya. Na so mu zauna ko in zo har gida in nemi yafiyarki, sai dai na samu labari gobe za ku wuce. Ina neman afuwarki da yafiyarki ga duk abinda na miki. Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mini. Wallahi ni Mufid na gane gaskiya na tuba zuwa ga Allah. Allah baku zaman lafiya, Dr a riƙe mana ita amana."
Daga haka Mufid ya ajiye enbulof ɗin hannunshi ya bar gurin, Dr Awwab da Nuratu da suka bi shi da kallon mamaki sun kasa kwakkwaran motsi dukkansu biyu. Har lokacin tana jikinshi bata san da hakan ba sai da ta ga ya saka hannu ya ɗauki enbulof ɗin ya jefa aljihunsa kafin ta fara ƙoƙarin kwace jikinta ya hanata ya riƙeta.
"Ke ki ka kawo kan ki jikin mijinki fa."
Yace yana ƙara ƙarfi wajen riƙeta sosai, tana mutsu mutsun kwace jikinta tace.
"Dan