Follow us on social media

Showing 1 words to 3000 words out of 148866 words

Chapter 1 - MADUBIN GOBE Sirrin Ƙaddara da Farashin Zaɓi by Pharty Bb

15 Jul 2026

6

Bismillahi Rahmanin Rahim.

MADUBIN GOBE 1.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

"Nuratu! Nuratu?"
Hajiya Sadiya dake zaune bakin katifar ƴarta tana ƙiran sunanta lokaci ɗaya tare da yaye abin da ta rufe jikinta dashi.
Motsi tayi har lokacin bata buɗe ido ba.
"Mami da sauran lokacin shan maganin, don Allah ki bar ni inyi bacci kaɗan, yanzu zan farka."

"Ki tashi kisha ko in ɓata miki rai, tun ɗazu nake faman tashinki kin ƙi ji."

Yaye abin da ta rufe jikinta dashi Nuratu tayi ta tashi ta zauna, tana mutsetstseke ido ta ce.
"Yanzu Mami bazan taɓa kwana na wuni ban sha magani ba, shikenan rayuwata haka za ta ƙare."

Sauyin yanayi da ta gani a fuskar mahaifiyarta ya sata yin shuru, ta karɓi maganin hannunta da ruwa.

"Komai zai wuce Nuratu. Ƙaddarar mu gaba ɗaya kenan ba ke ɗaya ba. In sha Allah watarana za ki kwana ki wuni ba ki sha magani ba da yardar Allah. Ko kin manta me Dr Awwab ya faɗa."

Girgiza kai Nuratu ta yi lokacin da ta saka ruwa a bakinta don kora maganin. Haka kullum ake faɗa mata cewa komai zai wuce amma ba ta taɓa kwana ta wuni abun da ya wuce bai faɗo mata a rai ba.

"To kina tuna hakan. Maza ki tashi ki shirya makaranta, ke wasu in sun kusa fara final exam basa bacci basa zama amma ke banda bacci baki da aiki."

"Ba ni da lecture ne ai, duk anyi closing, test ake yi."

Tashi Mami tayi ganin tasha maganin ta fice ta barta. Ganin haka ya saka Nuratu komawa ta kwanta. Tunanin rayuwarta ta shiga yi, ganin abun zai ɓata mata rai don har kanta ya fara ɗaukar zafi ta miƙe da sauri tana shiga bathroom.
Wanka tayi ta fito ta saka riga da skirt na lace ɗinta tare da mayafinta babba, za ka rantse matar aurece don yadda ta rufe jikinta ruf da shi. Ba tayi wani kwalliya ba ta ɗauki wayarta da jakarta na makaranta ta fita.

A falo ta samu mahaifiyarta zaune tana kallon huɗubar Jumma'ah, gefenta yarinya dake taimaka mata tana gugan kayanta.

"Mami zan leƙa makaranta, daga nan zan biya gidan Aunti Rahma?"

"To kar ki jima dai, banda shiga hayaniya. Ki gaisheta."

"Za taji."
Nuratu tace tana ɗaukar mukullin motar Mami ta fice dashi da sauri.

"Ki dawo min da mukullin nan."
Mami tace da karfi, jin ba zata dawo ba ya sa ta cewa.
"Kiyi tuƙi a hankali."

Murmushi kawai Nuratu tayi da tsakanin Mami da ƴan uwanta take yi, sai wanda ta basu muhimmanci a rayuwarta suke ganin murmushinta, shekarun baya har ta mance menene murmushi balle dariya.

Makaranta taje ta sama an manna time table, ganin babu wani abun ya sata fita ta nufi gidan yayarta Aunti Rahma. A waje tayi parking ɗin motar ta shiga.

Sallama tayi kofar falonta kafin ta shiga, Rahma dake cikin ɗaki tana hutawa bayan sallamar ƴaƴan ta sun wuce makarantar taji muryar ƙanwarta da sauri ta fito tana murmushi.

"Ashe dagaske za kizo."

"Kin san dai bana ƙarya."
Nuratu tace yayin da take zama saman kujera. Zama ita ma Rahma tayi suka gaisa tana tambayarta Mami ita kuma tana tambayarta sauran Yayunta da ɗanta Khair da yayunsa.

Ruwa ta kawo mata da abinci, Nuratu ta girgiza kai.
"Nayi breakfast tun 7, Mami bata yarda ta barni da yunwa."

"Hakane autar Mami. Amma kuwa sai kinci abincin gidana"

Rahma tace tana haɗa rai ganin haka ya saka Nuratu cin kaɗan ta bari. Suka hau hira dan sun kwana biyu basu haɗu ba. Su biyun in ka cire Aunti Hasiya mai bin Aunti Rahma da Rukayya wacce Nuratu take bi sun fi shiri, ko dan ta kasance ita ce babba ita ƙarama.

Sai wajen ƙarfe ɗaya Nuratu ta fara shirin tafiya bayan ta taimaka Aunti Rahma da abincin rana ta mata sallama.
Gida ta nufa ta samu Mami bata falon cikin sanɗa zata wuce ɗakinta taji Mami ta ƙirata.

Juyawa tayi tana sosa ƙeyarta.
"Sorry Mami."

"Kinsan dai lokacin shan maganin ki ya kusa wucewa amma ki kayi zamanki. Na ƙiraku dukkan ku ke da yayarkin ba wanda ya ɗauka."

"Kiyi hakuri Mami. Muna aikine ba mu ji ba. Magani kuma yanzu zan sha."

"Lafiyar ki nake nema miki Nuratu, kin fini buƙatar hakan sanin kan ki ne."

Shuru Nuratu tayi cikin sanyin jiki. Gaskiyar Mami, ta fita buƙatar lafiya duba da abubuwan da suka faru a rayuwarta. Ƙoƙarin ta kullum ta ganta tana walwala da farin ciki tamkar sauran al'umma. Wani lokaci ko tasha maganin in ta fara tunanin abin da ya wuce, ko yazo mata kanta, ko tayi tozali da makamancin shi zata wuni tamkar bata sha magani ba domin ciwon zai nuna alamu zai tashi, sai dai Mami tana bakin ƙoƙarinta ganin ta kawar mata shi a ranta walwalarta ya dawo.

"Kiyi hakuri Mami."
Nuratu tace ganin Mami ta nufi ɗakinta.

"Ya wuce."
Ta bata amsa dashi ta shige ɗaki ta barta.

Tana son ƴartan duk cikin ƴaƴanta. Su biyar ta haifa amma duk ciki tafi sabo da ita sun fi shaƙuwa. Ko dan a gabanta ta taso ita ɗin. Abubuwan da suka faru a rayuwarta ita da Nuratu Ƙaddarar suce da Allah ya rubutu musu ba daman kaucewa. Ita ƙaddara rubutacciyar shafine a rayuwar ko wani bawa da baya tsallakewa.
Tare suka sha wahalar su duk da sauran yaran sun tausaya musu halin da suka shiga a shekarun baya haka ma mahaifinsu da ba tayi tsammanin haka daga gare shi ba. Amma daga baya komai ya ƙara lalacewa yaci gaba da tafiya kamar da.
Tana son Nuratu tana tausayin ta kuma tana bata taimako dai-dai gwargwado da zata iya bata a matsayin ta na mahaifiyar ta.

...

11/03/1996.

DAMATURU, YOBE STATE.

Sallamar da mai gidanta yake kwalawa shi ya sata fitowa da sauri a ɗakinta. Zaune ta same shi a falo ya kurawa talabijin idanu.

"Sannu da zuwa."
Sadiya tace yayin da take zama kusa dashi sai lokacin ya farga daga tunanin da yake ya kalleta bai ce komai ba.

"Lafiya Abban Rahma?"

Shine tambayar data mishi ya kawar da idanuwanshi daga kanta yana girgiza kansa.

"Ba lafiya, amma komai allahamdulillahi."

"Ba lafiya? Ko dai bamu samu matsayin da muke nema bane?"
Ta faɗi hakan dan son sanin abinda ke faruwa.

"Ban samu ba Sadiya, sai dai fatan muyi addu'a Allah bamu Sa'a wani shekaran."

Cikin sanyin jiki tace.
"Ameen.'
Dan tasan yadda mijinta yaci burin samun babban matsayi a wajen aikinsa.

Maganar mijinta Alhaji Mamman Bashir shi ya sata dubanshi.

"Mai aka ce miki a asibitin?"

Murmushi tayi kamar mai jin kunya tace.
"Juna biyu ne kamar yadda kake zargi."

Murmushi yayi dan yana son ƴaƴa. Jin ciki jikin matarshi ya ji damuwarshi ta kau yace.
"Allahamdulillahi Allah raba lafiya. Amma zaki yaye Rukayya ko?"

"A'a, dana sanar dasu in nayi yaye in na samu ciki yaran suna jinya sai suka ce this time kar nayi yayen sai na kusa haihuwa."

"To hakan yayi. Allah kaimu lokacin."

Ameen! Ta amsa dashi suka taɓa hira wajen sha biyu yace zai leƙa wajen kasuwancin shi ba zai jima ba zai dawo.

...

Alhaji Mamman Bashir.
Ɗa na ƙarshe wajen iyayen shi. Su shida suka haifa mata huɗu maza huɗu, maza biyu sun rasu saura su huɗu. Mahaifinsu ya jima da rasuwa amma da wayonsu sai mahaifiyar su da itama bata fi wata da rasuwa ba. Duk sunyi aure da ƴaƴansu. Ɗan asalin fulanin Gombe mazauna Gombe. Sunyi karatun boko da islama ba laifi.

Alhaji Mamman Bashir ya karanci harkar kasuwanci in da ya kammala karatun shi bai samu aiki ba kuɗin gadonshi ya fara sana'a dashi Allah ya sawa kasuwan albarka ya fara bunƙasa Allah yayi zamansa a garin Damaturu jihar Yobe, anan yaci gaba da kasuwanci shi har lokacin yana neman aiki. Shiga da fita da yake yi tsakanin garuruwa a wata tafiyarshi ƙasar Nijar ya haɗu da Halimatul Sadiya ƴar asalin fulanin Nijar.

Auren soyayya su kayi bayan soyayya da su kayi na shekara ɗaya ta tare gidan mijinta dake cikin garin Damaturu jihar Yobe.

Halimatul Sadiya marainiya data taso gaban kakarta. Iyayenta sun rasu a hatsarin mota sun barta da yayunta maza uku, biyu sunyi aure a ƙasar Libya ɗaya yana aure a Doso jumhuriyar Nijar.

Tsakanin miji da matar ba laifi suna zaman lafiya dan Alhaji Mamman Bashir ba abinda ya rageta dashi yana bata kulata kuma yana son matar shi. Arziki ya ƙaru kasuwanci ya zauna masa a lokacin ya samu aiki a Company shiga da fita na kayan abinci. Samun aikin shi ya sashi neman yaron shago dan kula mishi da aikin kasuwancin, shi kuma ya fara kula da ofishin sa sai lokaci zuwa lokaci yake duba shagunan sa.

Shekara uku da auren Alhaji Mamman Bashir da Halimatul Sadiya kafin Allah ya bata haihuwar ƴa mace suka saka mata suna Rahma.
Daga nan haihuwar ya buɗe dan ranar da Rahma ta cika shekaru biyu ta haifi ƴa mace Hasiya, shekaran Hasiya ɗaya ta samu cikin Muhsin shima yana cika shekara uku ta haifi Rukayya da yanzu watanta goma ta samu cikin wata ɗaya.

Duk saurin haihuwarta Alhaji Mamman bai taɓa gajiya ba dan yana son ya'yansa. Arziki ya linku ya zama wani Alhaji. Ya kai su Hajj sun sauƙe farilla shi da matar shi.

Wannan cikin ma tun sati ɗaya da ya wuce yake roƙarta taje asibiti shi fa bai yarda da ita ba. A jikinta taji cikine da ita amma bata son zuwa. Ganin ya damu da hakan yasa taje ta tabbatar da hakan.
A yau kuma yake saka ran samun cigaban wani matsayi a gurin aikin shi da Allah bai nufa zai samu ba.

....

Hayaniyar Rahma da Hasiya sun dawo daga makaranta ya sata barin kitchen ɗin Muhsin yana bin bayanta.

Yaran ta samu cikin falon suna ta surutu ga Rukayya gefensu tana bacci.

"Kai zaku data min ita, maza ku wuce ɗakin ku ina zuwa zan cire muku kaya."

To yaran suka amsa dashi suka kwashi jakansu da takalma su a hannu suka wuce ɗakinsu ta koma kitchen ɗin ta sauƙe miyarta ta wuce ɗakin yaran. Kayansu ta canza musu zuwa na gida kafin su fito.

"Mami abinci zanci, yunwa."
Faɗin Hasiya tana tsalle saman kujera.

"Haka dai kullum kina cikin ci sai ƙiba kike ƙarawa."
Mami tace ta wuce kitchen ta zuba musu a babban tray ta kawo falon ta ajiye a tsakiya.

"Sauƙo Rahma, Muhsin kai ma ka haɗu dasu kuci."
Mami tace ta komawa kitchen ta kawo musu ruwan sha dana wanke hannu.

Gaba ɗaya suka wanke hannunsu suka zauna suka fara ci.

Kitchen Mami ta wuce ta haɗa na mijinta a food flask mai kyau da plate da spoon kafin ta fito ta wuce ɗakinta dan wanka.

Bayan ta gama ta yi sallar azahar da har lokaci ya ɗan gota, ta fito falon ta samu sun gama cin abincin Rahma tana share gurin. Gefe kuma Alhaji Mamman Bashir yana jijjiga Rukayya da surutunsu ya farkar da itatana kuka.

"Mun leƙa kina wanka."
Cewar Alhaji Mamman yana miƙa mata Rukayya.

Hannu tasa ta karɓeta yayin da take zama tace.
"Wallahi Abban su bayan na gama aikin zafi ya dame ni, ga zirga zirga na asibiti duk na gaji shine na watsa ruwa."

Zama yayi gefenta yayin da take shayar da Rukayya take tambayar shi ya kasuwa.

"Babu daɗi, ashe kayanmu duk sunyi expire yaron nan bai sanar dani ba. Fitana sai da na cire miliyin ɗaya da rabi na bashi ya ƙara da sauran cinikin da yayi ya sari wasu kayan."

"Bai kyauta ba, irin haka sai ya sanar da kai tun wuri kafin lokacin."
Hajiya Sadiya tace cike da jimamin abinda ya faru.

"Ai na mishi faɗa sosai shi da sauran yaran, wai dama akan zai sanar dani jiya ne kuma ya mance."

"Allah mayar da alheri."
Hajiya Sadiya tace tana zare Rukayya daga abincinta ganin ta ƙoshi ta miƙa Abban ta ya karɓeta yana amsawa da ameen.

"Bari in kawo maka abinci."

Kai ya ɗaga mata yana ma Rukayya wasa yasa ta wuce kitchen. Ɗaukowa tayi a babban tray har da ruwan zobo data haɗa masa ta kawo mishi falon.
Tare su kaci kasancewar ita ma bata ci abincin rana ba. Bayan sun gama ta tattare gurin.

Washegari ranar Alhamis da asuba ta samu ɗan saƙon ya sanar mata ƙiran da ake mata daga garinsu.
Bayan ta sanar da mijinta yace ta shirya taje ta ji lafiya sai tayi kwana biyu.

"Ji nake kamar ba lafiya ba Abban su."

"InshaAllah lafiya lau."

Girgiza kai tayi tana cewa.
"A jikina nake jin ba lafiya. Zan tafi dasu Rahma."

"Makarantar su fa da islamiyya."

"Yau da gobe suyi hakuri, asabar sai mu dawo su samu zuwa islamiyya Lahadi."

"To shikenan Allah kiyaye hanya."
Yace ya ɗauki dubu hamsin ya ajiye mata.

"Ga wannan ki riƙe a hannunki. Ilyas ya kai ku zan bashi kuɗi yayi full tank."

"Nagode. Nagode sosai Abban su."
Hajiya Sadiya tace tana murmushi amma cikin zuciyarta haka kawai take jin yana bugawa.

Fita tayi ta shirya yaranta ta haɗa kayansu ta haɗa nata suka fita lokacin Ilyas ya dawo daga shan mai.
Sai da Abba yaga tafiyarsu yana ma ƴaƴan shi bye bye kafin ya koma gidan shima ya shirya ya wuce aiki.

....

ƊANƊANO.

Labarin MADUBIN GOBE kenan dana dawo dashi.

MADUBIN GOBE 2.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

...

Ƙarfe ɗaya da mintuna na rana suka isa gidan, tafiyan awanni bakwai su kayi a hanya dan tsaye tsaye da suka yi.

Shigarta cikin gidan da yaranta ta samu yayanta wanda take bi ya zo, fuskar sa cike da damuwa da taji zuciyarta ya ƙara karaya.

"Yaya Muhammadu ina kaka tana lafiya?"

Girgiza kai yayi yana duban ƙanwarshi data zama wata Hajiya ga yaranta yan gayu.

"Lafiya lau Sadiya ki shiga tana ciki."

Da sauri ta faɗa ciki, yaran zasu bita ya hana su da Rukayya kawai ta shiga. Wani ɗaki ya kai su ya saka aka kawo musu abinci da ruwa. Rahma ce taci abincin kaɗan Hasiya da Muhsin sun kasa ci sai kindirmo da suka sha.

Hajiya Sadiya da kuka ta fito ganin halin da kakarta take ciki. Tamkar mahaifiyar ta take kallonta.

"Hakuri za muyi Sadiya muyi ta addu'a Allah zai bata lafiya."
Yaya Muhammadu yace dan kwantar mata da hankali.

Hawayenta ta share.
"Yaya Muhammadu ji nake kaka ba zata tashi ba."

Shima yana jin hakan saboda yadda jikinta yayi tsanani.

Daren ranar basu iya runtsawa ba. A cikin gidan aka ba Hajiya Sadiya ɗaki ita da yaranta suka kwana. Kwana tayi tana sallah da rokan Allah ba kaka lafiya.

Yaya Muhammadu a kanta ya kwana, da asuba kaka ta karɓi shahada a bakin jikinta Yaya Muhammadu. Hajiya Sadiya tana yin sallar asuba ta shiga dubata ta samu rasuwarta. Kuka ta dinga yi tana mata addu'a.

Kafin karfe goman safe gidan ya cika da dangi da ƴaƴan Kaka, da suka kasance yayun mamarsu Hajiya Sadiya da yaya Muhammadu.

Ƙarfe sha ɗaya a kayi jana'izar ta aka kaita gidanta na gaskiya suka bita da addu'a. Daga nan gidan ya zama gidan makoki aka fara shigowa musu ta'aziyya.
Alhaji Mamman Bashir bai samu labarin da wuri ba sai washegarin ya taho. Bayan ya musu ta'aziyya washegarin ya koma.

Sai da a kayi sadakan bakwai kafin Hajiya Sadiya ta fara shirin tafiya dan makarantar yaranta. Haka ta taho ta bar su har lokacin yayunsu maza biyu basu zo ba sai waya da su kayi.

...

Bayan wata biyu da faruwar haka Hajiya Sadiya ta fara mance rasuwar kaka sai addu'a da take mata.

Tsakanin ta da mijinta komai lafiya haka yaranta. Rukayya sai girma take tana wayo abinta ta fara tsayawa, cikin jikin Hajiya Sadiya watanshi uku.

***

Cikin fushi ya shigo gidan ranshi ɓace abin da yaron shagon shi ya mishi ya mutuƙar ɓata masa rai.

"Lafiya Abban su?"

Hajiya Sadiya tace tana miƙa masa ruwa a cup ganin ranshi ɓace yayin da suke zaune.

Sai da ya shanye tas ya ajiye cup ɗin alama ta ƙara masa.
"Salisu yana nema ya fara min wasa da dukiya, ganin shi ɗaya ne na yarda dashi."

"Wani abun kuma ya maka?"

"Wai yaron nan aure zai yi. Ya sanar dani in cire kuɗi cikin kuɗin jikina in bashi yaƙi ya ɗauki kuɗin cinikin mu yayi abinda zai yi dashi. Kuɗin da sai mun cinye shekara kafin mu mai da. Zan nemi wani kawai, zan nemi wani yaron."

"A'a Abban su kayi hakuri, ka sanar dashi laifin shi ya kiyaye gaba kuma ya mai da hankali bisa kasuwanci dan dawo da kuɗaɗen."

"Shikenan hakan zan yi dan ɓacin rai na kasa mishi magana wallahi."

"Hakuri za kana yi. Dana mu'amala da mutane haka ya gada komai daɗewarka da mutum."

Maganganun kwantar da hankali Hajiya Sadiya tayi tawa mijinta har ya sauƙo. Kullum yana godiya ga Allah da alfahari da samun mace kamar Sadiya.

...

Bayan sati biyu.

Bayan sati biyu da faruwar haka Alhaji Mamman Bashir ya ma Salisu faɗa akan abinda ya aikata yaron yaji haushi amma bai nuna ba.

***

"Alhaji Mamman I'm sorry about what happen. Babu sunan ka cikin masu tafiya."

"What!."
Yace da ƙarfi yana tashi tsaye sai ya tuna gaban oganshi yake ya koma ya zauna.
"Ta ya hakan zai faru?"

"I don't know. Daga can Thailand suka turo sunan wanda suka zaɓa."

Zai yi magana abokinsa dake gefenshi ya mishi alama da kar yace wani abu. Haka yasa ya hakura ya miƙe.

"Shikenan Sir."

Daga haka ya fice ranshi ɓace. Rayuwar shi ta fara canzawa tsawon watanni biyu kenan. Komai ya nema baya samu sau biyu kenan.

"Alhaji Mamman! Alhaji Mamman!"

Faɗin Alhaji Tukur kenan wanda suke aiki guri ɗaya da shi kuma abokinsa daya yarda dashi.
Dakatawa yayi yana duban shi har ya ƙarasa wajen shi.

"Sorry na tsayar ka, I'm sorry for what happen."

"It's ok ba komai."
Alhaji Mamman yace zai wuce yaji Alhaji Tukur yace.
"Sai dai kamar naga ka shiga damuwa da faruwar hakan."

"Muje office."
Abinda Alhaji Mamman yace yayi gaba da sauri Alhaji Tukur ya bishi.

"Sau biyu ina neman abu cikin Company nan bana samu, na rasa mai yasa hakan yake faruwa dani."
Alhaji Mamman yace kenan ya sanar da Alhaji Tukur abinda yake faruwa dashi.

"Lallai akwai ayar tambaya kan lamuranka, amma ba komai in har ka yarda dani zan taimaka maka?"

"Wani irin taimako kuma Alhaji Tukur?"
Alhaji Mamman ya faɗa cike da ƙaguwa.

"Zan taimaka maka inshaAllah. A weekend mu haɗu zan maka bayani."

"Kai da naji daɗi wallahi, domin abubuwan nan sun fara ishana sosai."

"Kai dai kar ka damu."
Alhaji Tukur yace ya miƙe tare da fita.

Sai lokacin hankalinshi ya kwanta. In har zai taimaka mishi ya samu cigaba a aikin shi yaji daɗi kuma dole ya mishi alheri.

Sati biyu kenan da aka ɗauki sunan masu zuwa ƙasar Thailand dan saro wasu kaya a company nasu ya saka sunansa, yaso zuwa amma yanzu ya samu labarin babu sunanshi cikin wanda aka zaɓa.

Da ya koma gida bai sanar da Hajiya Sadiya ba amma ta lura yana cikin damuwa. Haka yasa tayi ta ƙoƙarin sashi nishaɗi.

An wayi gari da mummunar labari bisa gobara da ya tashi a kasuwa yau ya koma shagunan mutane da dama.
Ciki har dana Alhaji Mamman Bashir da haukane kaɗai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login