Follow us on social media

Showing 174001 words to 177000 words out of 190973 words

Chapter 59 - Mutallab CC Soyayya Mai Boye Sirri By Nimcyluv.txt

Nimcyluv   

24 Aug 2026

161

auren ya je ya auri daidai da shi, domin wannan yarinyar idan ya kashe musu ita wallahi tallahi har ya mutu yana gidan Wan'kande"" Mama Zaituna ta yi furucin da mamaki da takaici kuma, tana ™ara jinjina kyan Safiyyerh a fili. Inna Binta ta ce ""Au ke jira za ki yi? Ai a yau Win nan zan nemo gidan iyayenta na labarta musu komai, ba mamaki na dawo da tukuici mai girman gaske, suna sane suka nema masa aurenta ai saboda sunga ΄ar masu kuWi ce zakka ba zata shige su ba"" Inna"

Binta ta ce tana mi™ewa.

"""Ke Binta sokar aure za ki je yi kenan ko? Ba kyau ba"""

"""Zauna nan Zaituna, da sanyin safe ake kama fara wallahi """

"Safiyyerh, kanta a ™as ta ™arasa wajan motar uncle Musbah, shima yana ganinta ya buWe motar ya fito"

"cikin sauri ta ce ""Good morning uncle"" ya yi murmushi ya ce ""Morning daughter, ya kwanan amarci kuma? Hankalinki ya kwanta ko? Kin samu Mutallab"" a hankali ta ce ""Uncle ka fahimce ni"" ya jinjina mata kai ya ce ""Na fahimta ai, na jima da fahimtarki Safiyyerh fahimtar ce ma ta saka na ce haka, kuma na miki uzuri hakan kuma ya faru ne saboda lack of parent guidance and careless, iyayenki sune silar komai, sai ™uruciya da balagar zuciya dake Wawainiyya dake, ina miki addu'ar kar bijirewar Prof da kika wani abu ya shafe ki, domin na karaya ainun da yadda naga ya amince kuma hawaye na fita daga cikin idanunsa. Safiyyerh hawayen iyaye masifa ne, ba zan yi mata ya zama masifa a gare ki ba domin bayin kan ki bane sakacin tarbiyyarki aka samu, wanda kuma ance icce tun yana Wanye ake tan™wara shi,"

"amma su sun yi sake ya bushe har yana neman karye musu, wannan shine kuskure na wasu iyayen,"

"yanzu duk abin da suke bu™ata ki yi ba za ki iya yi ba, saboda kin yi nisa ba za ki taSa jin muryarsu ba,"

"balle sunanki da suke kira"""

"""I am sorry uncle"""

"""Sorry for yourself Safiyyerh, kawai na ji ina jin tausayin ki da kuma auren naki, daka ke har mijin naki"

"kuna bu™atar kulawar iyaye sosai. Safiyyerh ki gane da gidan mahaifinka Professor da nan gidan surukanki akwai bambanci, kar ki yi tsammanin samun abin da kike samu a gida, ki zama mai ha™uri da Wauke kai, mai jajircewa akan mijinta, ki zama mai taimaka masa a kodayaushe kin ji ko?"" Ta jinjina kanta, hawaye na cika mata cikin idanunta sai ta samu kanta da tambayar ""uncle daddy, Ummeyh?"" Ya dinga"

kallon ta da tausayi a fuskarsa sai kuma ya kalli sama jin ™arar jirgi ya ce

"""Idan wannan bai zama jirginsu ba, to jirgi na gaba nasu ne, daga airport na zo nan, nima Win zan yi tafiya"

"shima Abba Nasim ya shige"""

"Safiyyerh sai ta ji kamar ita kaWai ta rage, wata kewa ta mamaye jikinta so da ™aunar iyayenta na"

"girmama kansu a zuciyarta ta dinga kuka ita Waya tana ajjiyar zuciya ""Kukan mene? Kin samu abin da kike so ai, no more crying"" sai ta ji zuciyarta na cewa ""Yes uncle, I'm not alone Mutallab is here"" a fili kuma ta"

"ce ""Yaushe za su dawo to uncle?"""

"""I don't know"" ya ce yana Waga kafaWarsa. Bayan mota ya buWe ya sakko da jakar kayanta, da uniform da"

"komai, amma banda takardun makaranta, takalma da bags Winta da duk tarkacan kayanta na mata har ma da wayarta. Ya ce ""Ga kayanki nan"""

"""Thank you uncle"" ta faWa a hankali, sai kuma wani Wan murmushi ya suSuce mata ashe haka ake kai"

"amarya? So ko wacce amarya haka ake aurenta dama? Shikenan ta zama matar Mutallab? Allah,"

"Allahamdulilah! ""Ga wannan"" ya mi™a mata zoben gold Winta,ta amsa ta saka a hannunta ya ce ""Zan tafi, Allah Ya sanya albarka kin ji gudaliya"""

"Ta yi shiru, sai ya ce ""Akwai wani abu da kike bu™ata ne Safiyyerh? FaWi kafin na shige nima"""

"""Uncle ka bani kuWi na siyawa bestie kaya shima, please uncle"" ta ji ta samu kanta da cewa haka. Uncle"

"Musbah ya dinga kallon Safiyyerh sai kuma ya ce ""Ai na san mijinki, na taSa masa kyautar kuWi ya™i amsa, yana da zuciyar nema na yarda da shi, zan aiko miki da kayan ok? Ga kuWi sai ki ri™e a hannunki ko? Kinga ba gida ne dake ba balle a yi maganar shirgin kayan mata furnitures, ko gara sai sanda kukai gidan kan ku"" ta yi murmushi ya mi™a mata bandir Win kuWi masu yawan gaske ta amsa tana masa godiya, da hannu ya kira Mutallab da yake shirin tafiyarsa makaranta hankali ™wance. Mutallab ya Wan yi sak kamar ba za shi ba, sai kuma ya ™arasa yana Wan sunkuyar da kan shi kansa ""Mutallab ga kayan matarka nan, ka shigar mata dasu ciki?"" Ya jinjina kai kawai, sai uncle Musbah ya Wora da faWin ""Safiyyerh ta zama Mutallab, Mutallab ya zama na Safiyyerh, Bestien beastie. Ina neman alfarma daka tsayawa Safiyyerh"

"don Allah ka ji yaron arzi™i?"""

"Mutallab ya kalli uncle Musbah, can ya nisa ya ce ""Uncle, idan kana ce mini yaro sai na ji ba zan iya ba"

"kuma"" ya faWa yana yin kicin-kicin da fuska. Uncle Musbah ya ce ""Waye mutum, ai kai babban mutum ne"

"irin ku basu da yawa, ina da mata kana da mata kaga babu batun yaro ko?"" Bai ce komai ba, ya Wauki kayan Safiyyerh ya yi cikin gidan dasu a hannunsa biyu."

"""Na gode sosai uncle"""

"Ya jinjina mata kai, ya dinga kallon ta sai ya ji gabansa na faWuwa haka kawai musamman murmushi da"

"kuma hawayen da yake gani at the same time. ""Safiyyerh"" ya kira sunanta, sai ya mi™a mata hannu bayan ta Wago kanta da sauri ta ™arasa ya rungumeta a jikinsa yana jin wani iri, yana jin kamar yana rabuwa da tsaginsa ne, ya ji tsoron barin Safiyyerh da gaske, amma bashi da wani zaSi haka ta nema kuma ta samu da ™yar ya zame ta a jikinsa ya ce ""Allah Ya yi miki Albarka"" ya ce a hankali har ya shiga mota tana tsaye, sai kuma ta fashe da kuka tana juya da sauri zuwa cikin gidan a zaure sukai karo da Mutallab zai fito, tana ganinsa taga bata da wanda ya shige shi, ba kuma da wanda zata iya tisawa a gaba ta yi wa kuka sai shi Win, only him ya rage mata, da sauri ta faWa jikinsa tana fashe masa da kuka ta ™an™amesa da kyau tana gunjin kuka, bai hanata ba, kuma bai mata shamaki da jikinsa ba, tunda ya fahimci jikinsa na Waya daga cikin abubuwan dake sanya zuciyarta nutsuwa ya daina hanata hakan. Suna"

"tsaye har ya gaji ya yi Wan gyaran murya, sannan ta Wago kan ta a hankali daga jikinsa"

"""He lefted"" ta ce."

"""Hmm"""

"""Ya tafi, ba zai dawo ba"""

"""And? Ki bi shi mana"""

"Sai ta yi murmushi ta ce ""Ai ba zan iya ba ka sani, salon ka auri wata ko? Bayan yanzu kai kawai nake da"

"shi, kai nawa ne ka ji?"""

"Komawa ya yi ciki, ta bi bayansa, cikin sauri ta shirya tsaf kayan sun mata kyau sosai, ya jingina da jikin"

"bango yana zuba mata idanu har ta gama shiryawa ta ce ""Na yi kyau ko? Ka ce na yi kyau, nima ai na faWa maka cewa ka yi kyau"" ya ™an™antar da idanu ya™i magana, s haka Ammo ta shigo ta ce ""Ba za ki karya ba, zauna ki sha kunu da ™osai kafin a kammala Wumame"" Safiyyerh ta yi shiru ""Zauna mana"" ™o™arin zama ta fara sai suka ji ya ce ""zan ta fi, ta fito kawai"" ya ce yana yin waje."

Da sauri kuma ta bi bayansa.

*

"Kamar yadda yake a Wabi'ar makarantar sai da aka yi assembly kana aka fara shiga class, Safiyyerh ta"

"dinga rarraba idanun ganin Aafiyyah amma babu ko inuwar Aafiyyah, haka babu Kimiyya. Kinal ta ce ""Safiyyerh wai ya jikin Aafiyyah ne? Na yi ta ™o™arin kiran numberta amma bata shiga, har ya yayanta na kira amma baya tafiya is she ok? Lafiya take?"""

"""Safiyyerh!"" Kinal ta sake kirata fuskarta Wauke da damuwa, domin tana da tabbacin Safiyyerh ta san"

"komai ta san inda zata samu Aafiyyah, domin ko a school idan Aafiyyah ta Soye ana nemanta Safiyyerh ke nemo inda take kodayaushe. A hankali Safiyyerh ta kalli Kinal ta ce"

"""Me kika ce?"""

"""I asked you Aafiyyah, where she is?"" Ta faWa loudly."

"""An yi mata aure, kamar yadda aka yi mini kuma ba'a ™asar zata zauna ba, Aafiyyah da Nigeria har abada,"

"nima Win na nemi numberta bana samu kullum"""

"""Safiyyerh?"""

"""Kinal"""

"""Ita Aafiyyah a kaiwa aure? Kin san Aafiyyah da karatu?"""

"Safiyyerh ta watsa hannunta ta ce ""Ohh Kinal, ba za ki fini sanin Aafiyyah ba dai ko? Kawo wayarki na"

"saka miki wata number ™ila ki same ta ko?"" Cikin jin daWi Kinal ta bawa Safiyyerh wayarta itama Safiyyerh ta amsa."

"In few minutes, ta goje number kimiyya tas, ta goge ta Aafiyyah haka ta goge da Mj daga wayar Kinal, sai"

ta saka mata wasu fake ta kuma saka mata wata as Aafiyyah's new number kana ta bata number. Haka

ma ta amshi wayar Nahyan ta goge komai. Mutallab dai hankalinsa na kan littafi gabansa duk da yana jin conversation Win su.

"""Safiyyerh ana kira a office na principle"" cewar Class captain na su Safiyyerh. Sai ta yi sak can kuma ta"

"mi™e ta fice ta jima har aka tashi daga makarantar bata dawo ba. Mutallab sai ransa ya Saci sosai, ya yi gaba zai tafi sai ya hangota zaune ita Waya ta ci kuka idanunta ya kumbura sosai gently ya ™arasa wajan, madadin ya yi magana sai ya cake mata aka ta Wago ta kalle shi, sai ta mi™a masa envelop Win hannunta ya saka hannunsa ya amsa, muryarta a rarrabe ta ce ""An kore ni, na yi failed exam har sau uku"" sai ta sake fashewa da kuka sosai fuskarta ta yi jajur, ta mi™e tsaye tana mustsika fuska sosai sai kuma ta kalli Mutallab tana dariya while hawaye na zuba cikin idanunta ta ce ""Na zama drop out, ko out of school wanne, sun kore ni daga makarantar innalillahi, bestie ba zan sake zuwa makaranta ba"" ta faWa tana sakin raunataccen kuka jikinta har wani kakkarwa yake sosai. Mutallab ya kasa ce mata komai, ta dinga"

"kuka ita Waya yana tsaye a gabanta sai data gaji da kuka ta ce ""Mu je"""

"Yana tafiyar nan tasa majestically, a zuciyarsa yana nanata ""Ke kika ja komai, ke ce Safiyyerh"" a wannan"

"tafiyar kuma tunanin Mutallab ya sauya, tunanin kula da Safiyyerh, tunanin yadda zata samu wata makarantar, ko kuma ya yi musu karatu duk abin da ya zama ai kamar ita ce, a wannan tafiyar ya ji ya yi believing na duka wasi™un wajansa, ya ji ya gamsu da su, ya kuma yarda cewa Yes, yana son wasi™un"

"yana kuma son mai wasi™un he trust Safiyyerh so much a lokacin, ya amince he loves Safiyyerh, without"

"knowing yadda love Win yake, ba tare da sanin mene gaskiyar abin da ke zuciyarsa ba, bai kuma ya yarda"

"ya zauna ba, ya ji cewa duka wasi™un is belong to Safiyyerh's. Har suka fita yana nanata sunan FGC a"

zuciyarsa.

"A cikin napep ya same ta zaune yana shiga ta ce ""Kai ta tafiya kana bubbuWawa haba bestie"""

"Ya cije lips, yana kallon ta."

"""Uhm, i feel like crying"""

"Ya yi shiru ""Na kwanta a cinyarka? Bacci nake ki kai na ciwo yake mini sosai"""

"""Uhmmm"" ya ce."

"Sai ta zame ta Wora kanta a gefen kafaWarsa, shi kuma ya gyara hannunsa yana yin game a wayarsa suna"

"tafe bacci ya Wauke ta. A hankali ya kama hannunta yana kallo, tare da zoben dake jikin madaidacin hannunta sai a lokacin kuma ya ji jikinta zafi ga cikin na ™ogi ashe fa ko karyawa ba ta yi ba. Ji ta yi yana taSa kumatunta ta mi™e bakinta Wauke da addu'a sai ta yi murmushi ta ce ""Thank you da auron wajan"

"bacci"""

"Zata Wakko kuWi cikin jakarta sai taga ya mi™awa mai napep Win kuWi ta Wan tsaya ta ce ""Kabar naka zan"

"ba yar fa"" ko kallon ta bai yi ba. Maimakon ya shiga cikin gidan sai ya yi gaba abinsa, bata kula shi ba ta shige cikin gidan, wannan karan tarin yaran da suke zaune a tsakar gidanne suka zaba mata na mujiya sai"

"kuma Malam ta dur™usa ta ce ""Ina yini Aby"""

"""Safiyyerh ko?"""

"""E, Aby"""

"""Ke kin zaSi zama da wannan tantirin yaron ko? Kin zaSi bijirewa iyayenki saboda wannan yaron da bashi"

"da wata makoma mai kyau ko? Wannan yaron ko kinwa iyayenki adalci kenan yanzu idan ya kashe ki me za ki cewa iyayenki eh?"" A hankali Safiyyerh ta ce ""In sha Allah Aby ba zai kashe ni ba, in sha Allah"" ran Aby ya Saci ya ce ""Saboda ke nake magana idan don tashi ne wallahi ko a jikina, tashi ki je duk abin da kika jawa iyayenki shikenan ai"" ta mi™e jiki a sanyaye ta shiga Wakin Ammo ta sameta zaune tana Waura"

man ™uli Sa'adah kuma na yanka alawar madara lokacin bikin Sa'adah saura kwana biyar ciff.

"""Barka da gida Ammo, Yaya"""

"""Sannu Safiyyerh, ya makarantar?"" Ammo ta tambaya da kulawa tana ajjiye abin hannunta ta ce ""Ki fara"

"yin wanka sai ki yi alwala tunda magariba ya kusa sai kici abinci ko"". Safiyyerh ta ce ""To Ammo"" uniform Win ta cire ta saka towel ta saka hijab, sabon soson wanka ta gani an bata da sabulu ta amsa, da ™yar ta yi wankan a tsaye tsigar jikinta na tashi a haka ta yi ta fito. Sanda ta shiga Wakin ba kuwa a ciki haka ta sutale kayan jikinta tana shafa mai a jikinta, ganin tana ™o™arin cire towel Win gabaWaya ya yi gyara murya, ta juyo da sauri a ™o™arin Waukan riga sai towel Win ya faWi ™asa, shi kuma ya Wago kai ganin ta fasa ™ara tana ™an™ame jikinta ta rasa inda za ta yi, ko inda take bai sake kallo ba ya mayar da hankalinsa kan alawar madarar da yake kwasa yana dannawa a cikin bakinsa hankali kwance. Ganin ba kulata zai ba"

"ta saki kuka ta ce ""Ba zaka tashi ka fita ba, kaya zan saka fa, ni ka tashi"" ta ce tana yarfa hannunta."

"Ta fara diddire masa ™afa ""Please mana, ka tashi"" ta ce silently."

"""Bestie"""

"Ya yi iska da ita, ta sake cewa ""Bestie kaya zan saka ka fita"""

"Ya Wago kan shi, suna haWa ido ta rufe idanunta sai ya tsuke fuska ya mayar da kan shi akan bokitin"

alawar madarar hankali ™wance.

"""Bestie. ,"""

"""Damn it..!"""

"Ya ce yana mi™ewa, ya yi kamar zai fita sai ya dawo baya idanunsa sun nutsa ciki yana mata wani irin"

"numfashi, harshensa na yin tsartuwa ya dun™ule hannunsa da yake jin kunama na yawo a ciki. Sai kawai ya girgiza kai ya ce ""Shhh"" numfashinta na fita da ™yar bata taSa jin tsoron shi irin yau ba, sai taga kamar ba shi ba, jikinta ya Wauki rawa sosai a hankali ta ga ya yi baya yana cillo mata rigar data yar a ™asa."

"Šauka ta yi ta zura da sauri ko halpvest Win bata saka ba, tana gama sakawa ta Wauki hijjabi ta yar da sallah, har kuma ta idar bai kalle ta ba. Ta juya taga ya juye gurasa irin ta wajan masu balangon nan ta sha romo a faranti, taga hadda nama da kuma awara mai kyau sau turiri da ™amshi suke yi. Tunda taga ya Wan kalle ta kaWan ta san magana yake son yi mata amma kuma bai san ne zai ce ba, sai taga ya share ta ya fara cin gurasar murmushi ta yi ta ™arasa gabansa tare da tan™washe ™afarta, juyawa ta yi zata"

Wauki cokali sai taga babu hannunta ta saka cikin farantin ta fara cin naman.

"Suna cikin cin abincin Ammo ta shiga, ta kalle su ta jima tana kallon su musamman yadda Safiyyerh ke ta"

"yi masa hira shi kuma kamar baya wajan, sai ta juya ta bar musu Wakin kawai. Shi ya fara Wauke hannunsa ya mi™e ya fice yana fita itama ta fice ta wanke hannunta."

"Cikin Wakin ya dawo ya zauna, Ammo ta ce ""An kawo kaya naka ne Muhammad?"" Da sauri Safiyyerh ta"

"ce ""E, nasa ne"""

"""Tom""."

"""Yau zaman gida kake da shi kenan? Ba zaka fita ba?"""

"""Ammo ki na fita ne?"" Cewar Mutallab yana kame fuska"

"""Ban sani ba don gidanku"" ta ce tana mi™ewa, saman katifa ya samu ya kwanta yana ware ™afa WaiWai"

"bacci ya ke ji sosai, yana kwanciya bacci ya Wauke shi, Safiyyerh ma kusa da shi ta samu ta kwanta, bacci ya Wauke ta lokacin data gama shigewa jikinsa yayinda shi kuma ya zagaye ta da hannunsa gabaWaya ba tare daya sani ba, sau biyu Ammo na shigowa tana ganinsu rungume suna bacci ta rasa kunya ke kamata ko mene? Ita dai ba zata jure wannan abin ba, duk da tana da ya™inin basu gama sanin mene auren ba yanzu. A dawowa ta uku kuma sai taga gabaWaya Safiyyerh ta haye ruwan cikin Mutallab tana bacci"

hankali kwance ta ™an™amesa kamar ta samu filo cikin sauri ta saki labulen ta fita.

*

Switzerland/ Bern

"Yanayin ™asar tana matakin hadari ne, sama-sama mizanin saukar ruwan sama 5% sai laimar iska 93%"

daIska km/s 6 sai hakan ya saka gabaWaya yanakin Waukan wani irin sanyi mai rasa jiki da ™asasuwan

"mutane, kowa ka gani da rigar sanyi jikinsa da kuma takalmi babba snow nata sauka a jikin mutane da kyau kamar yayyafin ruwan sama domin ita ke sauka madadin ruwan da ake saka ran samu a yau Win."

"A cikin haWaWWan gidan ma hakanne, sai ya zama gidan shiru kamar ba kowa. A hankali ya murWa handle"

"Win ™ofar Wakin da hannunsa da yake cikin safa ya shiga, idanunsa ya dinga rarrabawa ta cikin ba™in glasses Win daya saka, gano ta ya yi tsakiyar gadon da rufe jikinta sosai tana bacci peacefully. A hankali ya ™arasa ya tsaya sai kuma ya nemi waje ya zauna ya saka hannunsa mai Wan sauran sanyi duk da safar hannun ya zame duvet Win data rufe kanta da shi, ko ya ce aka rufe mata. Farar fuskarta ta bayyana, ya zuba mata ido ta yi wata ramewa ta ban mamaki, ya sake haske sai siririn hancinta da ya sake yin tsayi ™warai, hannunta Waya cikin bakinta ta ™an™ame teddy Win dake kusa da ita, ga azkar Win dake kuma gefe, ya mi™a hannunsa ya kama hannunta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login